Titus
1Daga Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, saboda bangaskiyar zaɓaɓɓun Allah, da kuma inganta sanin gaskiyar ibadarmu, 2duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil'azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi, 3ya kuwa bayyana maganarsa a lokacin da ya ƙayyade, ta wa'azin da shi Allah Mai Cetonmu ya amince mini in yi, bisa ga umarninsa, 4zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka. Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.
5Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman domin ka ƙarasa daidaita al'amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikilisiya a kowane gari, kamar yadda na nushe maka, 6sai wanda ya kasance marar abin zargi, mai mace ɗaya, wanda 'ya'yansa suke masu ba da gaskiya, waɗanda ba a zarginsu da aikin masha'a ko na kangara. 7Lalle ne kuwa, kowane mai kula da ikilisiya, da ya ke shi riƙon amana saboda Allah ne, ya zama marar abin zargi, ba mai taurinkai ba, ko mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai saurin dūka, ko mai kwaɗayin ƙazamar riba. 8Amma ya kasance mai yi wa baƙi alheri, mai son abu nagari, natsattse, mai kirki, tsarkakakke, mai kamunkai, 9mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin ya iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta. 10Don kuwa akwai kangararrun mutane da yawa, da masu surutan banza, da masu ruɗi, tun ba ma ɗariƙar masu kaciyar nan ba. 11Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama'a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa. 12Wani annabi na Karitawa ya ce, “Karitawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye, haɗamammu.” 13Shaidar nan tasa kuwa gaskiya ce. Saboda haka, dai ka tsawata musu da gaske, domin su zama sahihai a wajen bangaskiya, 14a maimakon su mai da hankali ga almarar Yahudawa, ko kuwa dokokin mutane masu ƙin gaskiya. 15Ga masu tsarkin rai duk al'amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al'amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne. 16Suna cewa sun san Allah, amma suna sāɓa masa ta wurin aikinsu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani a wajen yin aiki nagari.
1Amma kai kam, sai ka faɗi abin da ya dace da sahihiyar koyarwa. 2Dattawa su kasance masu kamunkai, natsattsu, mahankalta, masu sahihiyar bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimiri. 3Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar kyakkyawan abu, 4ta haka su koya wa mata masu ƙuruciya su so mazansu da 'ya'yansu, 5su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah. 6Haka kuma, ka gargaɗi samari su yi kamunkai. 7Kai ma sai ka zama gurbi na aiki nagari ta kowace hanya, da koyarwarka kana nuna rashin jirkituwa, da natsuwa, 8da kuma sahihiyar maganar da ba za a kushe mata ba, don a kunyata abokan hamayya, su rasa hanyar zarginmu. 9Bayi su yi biyayya ga iyayengijinsu, su kuma gamsar da su ta kowane hali. Kada su yi tsayayya, 10ko taɓe-taɓe, sai dai su riƙi amana sosai, don su ƙawatar da koyarwar Allah Mai Cetonmu ta kowane hali.
11Alherin Allah ya bayyana saboda ceton dukkan mutane, 12yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha'awace-sha'awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah, 13muna sauraron cikar begen nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, 14wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama'a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.
15Ka yi ta sanar da waɗannan abubuwa, kana gargaɗa su, kana tsawatarwa da ƙaƙƙarfan umarni. Kada ka yarda kowa ya raina ka.
1Ka riƙa tuna musu yi wa mahukunta da shugabanni ladabi, suna yi musu biyayya, suna kuma zaune da shirinsu na yin kowane irin kyakkyawan aiki. 2Kada su ci naman kowa, kada su yi husuma, sai dai su zama salihai, suna yi wa dukan mutane matuƙar tawali'u. 3Mu kanmu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, an ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha'awa da nishaɗi iri iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi waɗansu. 4Amma sa'ad da alherin Allah Mai Cetonmu da ƙaunarsa ga 'yan adam suka bayyana, 5sai ya cece mu, ba don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a'a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sāke haihuwa, da kuma sabuntawar nan ta Ruhu Mai Tsarki, 6wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Almasihu Mai Cetonmu. 7Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami. 8Maganar nan tabbatacciya ce. Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane. 9Amma ka yi nesa da gardandamin banza, da ƙididdigar asali, da husuma, da jayayya a kan Shari'a, domin ba su da wata riba, aikin banza ne kuma. 10Mutumin da yake sa tsattsaguwa kuwa, in ya ƙi kula da gargaɗinka na farko da na biyu, to, sai ka fita sha'aninsa. 11Ka dai sani irinsa ɓatacce ne, mai yin zunubi, shi kansa ma ya sani haka yake.
12Sa'ad da na aiko Artimas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi matuƙar, ƙoƙari ka zo wurina a Nikafolis, don na yi niyyar cin damuna a can. 13Ka yi himmar taimakon Zinas, masanin shari'a, da Afolos, su kamo hanya, ka kuma tabbata ba abin da ya gaza musu. 14Jama'armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.
15Duk waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gayar mini da masoyanmu, masu bangaskiya. Alheri yă tabbata a gare ku, ku duka.