TOBI

1

1 Labarin Tobiya, ɗan Tobi, ɗan Hananiya, ɗan Aduwal, ɗan Gabayal, na gidan Asiyel, na kabilar Naftali, 2 wanda a zamanin Shalmanesar, Sarkin Assuriyawa ne, ya zama kamammen yaƙi a Tisbe, garin da ke kudancin Kedesh ta Naftali a arewacin Galili, kusa da Hazor da Fogor.

Tobi a garin Nineba

3 Ni, Tobi, na yi zamana bisa ga gaskiya da adalci a dukan kwanakin raina, iia kuma aikata ayyukan alheri ga yanuwana da mutanen ƙasarmu waɗanda aka kai mu ƙasar Assuriya tare, zuwa garin Nineba. 4 A lokacin da nake a ƙasarmu, wato ƙasar Israila, da ƙuruciyata, dukan kabilar Naftali kakannina ne, suka rabu da gidan Dawuda da Urushalima. Wannan ne garin da aka zaɓa tun dā, inda ya kamata dukan kabilan Israilawa su yi hadaya. Can ne kuma aka gina mazaunin zatin Maɗaukaki, aka ma tsarkake shi domin dukan tsararraki bar abada. 5 Dukan dangina da dukan kabilar Naftali sukan yi hadaya bisa dukan tsaunukan ƙasar Galili, ga kuma dan mararcin zinariya wanda Yerobowam, Sarkin Israila, ya yi a birnin Dan.

ɓ Sau da yawa ni kaɗai nake tafiya haji a Urushalima, ina cika dokar da ta haɗa dukan Israilawa gu ɗaya. Sai in kai tumun farin gona da yan fari na dabbobi, da ushirin kuɗina, da fatun yayan fari na tumakina, 7 in ba firistoci, wato zuriyar Haruna, a wurin bagaden. Lawiyawan da ke hidima a Urushalima nakan ba su ushirin hatsi, da ruwan inabi, da man zaitun, da rumman, da yayan ɓaure, da sauran yayan itatuwa. Kowace shekara, banda ta bakwai ta hutu, na ɗauki wani ushirin kuɗina, in je in ba da sadaka a Urushalima. 8 Bayan kowace shekara ta uku, na ba da wani ushirin kuɗi, ta uku ke nan, ga marayu, da mata gwauraye, da kuma baƙin da ke zaune a Israila,

nakan shirya musu liyafa da ushirin. Da muka ci, sai muka bi kaidodin Attaura ta Musa da gargaɗin Debora, mahaifiyar ubanmu Tobiya, gama tsohona ya mutu, ya bar ni maraya.

9 Lokacin da na isa mutum, sai na auri wata mata daga cikin danginmu mai suna Hannatu, ta kuma haifar mini ɗa wanda na kira Tobiya. 10 Bayan da aka kama ni, aka kai ni birnin Nineba, dukan yanuwana da dangina suka ci abincin ama, 11 amma ni, na ƙi ci. 12 Da ya ke kuma na amince da Allahna da dukan zuciyata, 13 sai Maɗaukaki ya yi mini goshin gari gun Shalmanesar, na zama ɗan cefanen sarkin. 14 Har gabanin mutuwarsa, ina ta ratsa Mediya, ina ta saye da sayarwa da sunan sarki, har na ajiye jakunkunan azurfa guda goma a wurin ɗanuwana Gabayal ɗan Gabari, wanda ke zaune a Ragesa ta Mediya. 15 Da Shalmanesar ya rasu, sai ɗansa Sennakerib ya hau gadon, sai hanyoyin zurga‑zurgana zuwa Mediya suka Ialace, na kasa zuwa wuraren da na saba.

1ɓ A zamanin Shalmanesar nakan ba yanuwana da kabilata sadaka, 17 nakan ba mayunwata abinci, waɗanda ake tsiraice kuma, tufafi. In na ga matacce daga kabilata, wanda aka yar bayan garin Nineba, sai in rufe shi. 18 Na ma rufe gawawwaki waɗanda Sennakerib ya kashe. Gama lokacin da ya ja da baya daga Yahudiya, da Sarkin Sama ya hore shi kan saɓonsa, da fushinsa, sai shi Sennakerib ya yi ta kisan Israilawa. Amma sai in kwashe gawawwakinsu a asirce, in rufe su, ta haka Sennakerib ya neme su, amma ba ya samunsu. 19 Sai wani dan ƙasar Nineba ya sanar wa sarki, cewa ni nake rufe su. Da na ji sarki na nemana don ya kashe ni, na ɓoye, sai tsoro ya sa na bar ƙasar. 20 Daga baya aka ƙwace dukan kayana, aka watsa su a baitulmali, ba a bar ni da kome ba, sai matata Hannatu da ɗana Tobiya.

21 Ba a yi kwana arbain ba daganan, sai yayan sarki, su biyu, suka kashe shi, daganan suka gudu zuwa dutsen Ararat. Sai ɗansa Esar‑haddon ya gaje shi. Ahikara kuma, dan ƙanena Anayal, aka zaɓe shi maajin mulkin, yana jan ragamar dukan mulkin. 22 Sai Ahikara ya roƙi sarki domina, har aka dawo da ni Nineba, tun da ya ke Ahikara shi ne mai aikin sarki, shi ne ke kula da hatiminsa, shi ne ma wakilinsa, maaji ne kuma tun zamanin Sennakerib, Sarkin Assuriyawa. Esar‑haddon, sabon sarki ma, sai ya yi naam da shi a mulkinsa. Shi Ahikara ɗanuwana ne, ɗan ƙanena.

2. Tobi ya Makance

1 Ta haka, a zamanin mulkin Esarhaddon, sai na koma gida, aka mayar mini da matata Hannatu da ɗana Tobiya. A ranar Idinmu na Fentikos, wato idin bayan mako bakwai, sai aka shirya mini liyafa mai kyau. Na zauna gaban abincin, 2 aka girke mini tebur, aka kawo abinci iri iri a gabana. Saan nan na ce wa ɗana Tobiya, Tafi, ɗana, ka nemo matalauci mai biyayyar gaske daga cikin korarrun mutanenmu da ke a birnin Nineba, ka kawo shi, mu ci abincina tare. Zan dakata, ɗana, har ka dawo tukuna.

3 Sai Tobiya ya fita neman wani matalauci daga cikin kabilarmu. Amma ya dawo da baya, ya ce Baba!

Na amsa, na ce, Me ya faru, ɗana?

Ya zarce da magana ya ce, Baba, yanzun nan aka kashe wani daga cikin kabilarmu, maƙare shi aka yi, aka jefar bayan kasuwa, yana can ma har yanzu.

4 Sai na yi zabura na miƙe, ko taɓa abincina ma ban yi ba, na ɗauko mutumin da aka yar bayan gari, na kai shi wani ɗaki a giɗana, na kwantar, ina dakon rana ta faɗi, in rufe shi. 5 Na sāke komawa, na yi wanka, na ci abincina da baƙin ciki, ɓ ina tunanin jawabin Annabi Amos a kan garin Betel, inda ya ce,

Bukukuwanki, zan maishe su makoki,
      In sa dukan wakokinku na muma su zama na makoki.

Sai na rusa kuka. Da rana ta faɗi, na tafi, na gina kabari, na rufe shi.

8 Maƙwabtana suka yi mini dariya, suna cewa, Nnhn! Ba ya ma ko jin tsoro! Kafin wannan lokaci ya yi gudun fid da kai game da alamarin. Duk da haka kuwa ga shi nan, ya ma koma kan aikinsa na rufe matattu!

9 A daren nan na yi wanka, na tafi tsakar giɗana, na kwanta gindin katanga. Da ya ke zamanin jiɓi ne, sai na bar fuskata a buɗe. 10 Ban sani ba, ashe, akwai tsuntsaye da yawa a kan katangar a bisa kaina, sai suka yi ta yiwo mini kāshi mai ɗumi a idanu. Sai kāshin ya zama yāna. Na tafi gun likitoci su yi mini maganinsa. Amma duk da yawan maganin da suka sa mini, abin sai ƙara haukata yake yi, yana ƙara makanta ni, daga ƙarshe ma, sai na makance ɗungum. Ina zaune ba gani har shekara huɗu, dukan yanuwana suka yi bakin ciki har suka haƙura, Ahikara ya yi ta ɗawainiya da ni har shekara biyu, sai da aka sauya shi zuwa Alimaisa.

11 A lokacin, matata Hannatu tana ƙodagon saƙa tufafi, irin dai aikin da mata suka saba yi. 12 Duk abin da aka ce ta saƙa, sai ta saƙa. In ta gama, ta mayar, a biya ta kuɗinta. Wata rana da rani sai ta gama wata yar saƙa, ta ba wanda ya sa ta. Suka biya ta duk abin da aka ƙayyade a kan aikin, har aka game mata da ɗan akuya don ta sha romo. 13 Da aka kawo ɗan akuyan gida, sai ya fara kuka. Na kira matata, na ce mata, Daga ina ne aka kawo wannan halittar? In sato shi aka yi fa, maza, ki mai da shi. Ba mu da damar cin sataccen abu.

14 Sai ta ce, Aa, ai, kyauta ce aka yi mini ƙari a kan aikina.

Ban gaskata abin da ta cc ba, na sāke ce mata ta mayar wa mai shi. Na ma husata da ita ƙwarai a kan wannan magana.

Saan nan ta ce mini, To, kai sadakar da kake yi fa? Ayyukan alheran da kake yi fa? Yanzu kowa ya gane ainihin halinka!

3

1 Saan nan da ɓacin rai, na yi ajiyar zuciya, na fara addua ta makoki, na ce:

2 Ai, kai mai adalci ne, ya Ubangiji,
      Dukan ayyukanka kuma masu adalci ne.
Dukan hanyoyinka na alheri ne da gaskiya,
      Kai ne alkalin duniya.
3 Saboda haka, ya Ubangiji, ka tuna da ni, ka dube ni,
      Kada ka hore ni a kan laifofina ko kan saɓe‑saɓena,
Ko kuma dai na kakannina gama sun saɓa maka,
      4 Sun karya dokokinka.
Sai kuwa kā danƙa mu, aka kwashe ganima daga gunmu,
      Aka mai da mu bayin yaƙi, har aka kashe waɗansu,
Muka zama abin hira, madariya har aka riƙa yi mana zunde
      Cikin dukan kabilan da ka yi ɗaya ɗaya da mu a ciki.
5 Horon da ka yi mini mai yawa bisa ga gaskiya ne,
      Saboda laifofina, haka ma na kakannina,
Tun da ya ke ba mu bi dokokinka ba,
      Ba mu ma bi hanyar gaskiya a gabanka ba sam.
6 Don haka yanzu ka yi mana duk abin da ka ga dama,
      Ka ma ɗauke mini numfashin raina daga guna,
Don in bar duniya, in korna ƙasa.
      Na gwammace mutuwa da raina,
Gama an zage ni ba gaira ba dalili,
      An kuma bakanta mini rai gaba da kima.
Ya Ubangiji, ina jiran umaminka kurum,
      Ka fanshe ni daga baƙin cikin nan.
Ka bar ni in korna lahira,
      Kada ka juya mana baya, ya Ubangiji.
Gama ya fi kyau in mutu, da in wanzu a wannan wahala,
      Na gaji da jin ƙasƙanci kullum!

Saratu a garin Ekbatana

7 A ranan nan kuma ya faru Saratu, yar Raguwal, wadda ke zaune a Ekbatana a ƙasar Mediya, aka caɓa mata magana, wato ta bakin baiwar ubanta. 8 An tabbatar fa da aure‑aurenta har bakwai, Asamadayas, wani bakin aljan, ya kashe mata angayen bi da bi, tun ma kafin su yi kwana aure da ita. Sai baiwar babanta ta ce, I, ke ce mai maƙare angayenki. Ga shi, an aure ki sau bakwai, amma har yanzu ba ki yi jami da ko ɗayansu ba. 9 Saboda me ya sa kike dūkanmu? Don mazanki sun mutu? Ke ma ki bi su mana, kada kuma Allah ya sa mu ga wani ɗa ko ya naki!

10 A ran nan fa, ta yi baƙin ciki, ta yi hawaye, har ta tafi ɗakin bene na mahaifinta da nufin ta rataye kanta. Amma sai ta shiga gandun tunaninta, ta ce, Ga ubana za su sa wa laifin fa! Za su ce, Kana da ya tilonka wadda kake ƙauna, ga shi, yanzu ta rataye kanta don rashin katari. Ba na iya muzanta wa ubana rai, har baƙin ciki zai aika da shi gidan gobe. Bai kamata in rataye kaina ba, amma ya kamata in roƙi Allah ya kashe ni, kada in zauna a ƙara yi mini wani gori! A nan sai ta ɗora hannuwanta kan taga, ta yi adduan nan, ta ce,

Mai albarka kake, ya Ubangiji Allah mai jinƙai!
      Albarka ta tabbata ga sunanka mai tsarki, mai daraja har abada!
      Ka sa dukan abin da ka yi ya yabe ka har abada abadin!
12 To yanzu, ya Ubangiji, na ɗaga fuskata sama,
      Na ma juya idanuna gare ka.
13 Ka sa a fanshe ni daga duniya,
      Ba na iya daure wa cin fuskar da ake yi mini.
14 Ya Ubangiji, kai ne ka sani,
      Ni dai, har yau ban taɓa yin zunubi da namiji ba.
15 Ban ɓata sunana ba, ko na ubana
      A ƙasar da na yi baƙunci.
Ni tilo ce a gun ubana,
      Ba shi da wani ɗa da zai gaje shi.
Ba shi ma da sauran ɗanuwa a kusa da shi duk a danginsa ko daya
      Wanda zan jira in aure shi.
Ai, tun yanzu na yi rashin maza bakwai,
      Me ma ya sa nake rayuwa ne?
In ba ka son ɗauke raina,
      To, ka dube ni da idon rahama,
      Ba na iya daure wa cin fuskar da ake yi mini.

16 A wannan karo, sai aka kai adduar dukansu biyu a gaban Allah mai girma. 17 Aka kuma aiki Rafayal ya kawo wa kowannensu maganin matsalarsa, dukansu biyu. Aka ce ya ɗauke wa Tobi yānar da ke idanunsa, domin ya sāke ganin hasken Allah da idanunsa, Saratu kuma, yar Raguwal, ya aurar wa Tobiya ɗan Tobi ita, ya kuma tserar da ita daga hannun Asamadayas, baƙin aljanin nan. Gama Tobiya ne dangi mafi kusa wanda ke halal ya aure ta.

Tobi yana shigowa gida ke nan, sai Saratu, yar Raguwal, take gangarowa daga kan bene.

4 Gargadin Tobi ga Ɗansa Tobiya

1 A rana daya ne, Tobi ya tuna da azurfa da ya ajiye gun Gabayal a Ragesa a ƙasar Mediya. Ya yi tunani, ya ce, 2 Yanzu da na kai ga roƙon mutuwa, ya fi kyau in kira ɗana Tobiya, in gaya masa zancen kuɗin, tun ban mutu ba. 3 Sai ya kira ɗansa Tobiya. Da ya zo, ya ce masa, In na mutu, ka yi mini janaiza mai ƙayatarwa. Ka girmama mahaifiyarka, kada ka yashe ta a dukan kwanakin ranta. Ka yi mata duk abin da take so, kada ma ka ɓata mata rai ta kowane hali. 4 Ka tuna fa, ɗana, da dukan ɗawainiyar da ta sha da kai lokacin da kake cikin ciki. In ta mutu kuma, ka rufe ta gab da ni a kushewa ɗaya.

5 Dana, ka kasance mai aminci ga Ubangiji dukan kwanakin ranka. Kada ka bari saɓo ya ga damarka, ko ka bauɗe wa kaidodin. Ka aikata alheri dukan kwanakin ranka, kada ka bi mugayen hanyoyi, 6 gama in ka aikata gaskiya, za ka ci nasara cikin dukan ayyukanka, yadda kai da dukan masu aikata gaskiya za su more.

7 Ka keɓe wani sashi na wadatarka don ba da sadaka. Kada ka juya wa matalauci baya, Allah ma ba zai juya maka ba. 8 Yi sadakarka bisa ga wadatarka. In kana da tuli, to, ka bayar da yawa, in kuwa kana da ƙalilan, to, ka bayar da kima, amma kada ka ji tsoron ba da sadaka. 9 In kana yin haka, za ka tara wa kanka dukiya a ranar shan wuyar gobe. 10 Gama ba da sadaka yana tsare mutum daga mutuwa, ya ma ƙwato mutane da dama da aka yi niyyar kai wa mulkin kurwoyi. 11 Ai, duk masu ba da sadaka suna yin hadaya mai karɓuwa a gaban Maɗaukaki.

12 Dana, ka guji zina. Ka zaɓi mata yar zuriyar kakanninka. Kada ka auri baƙuwa wadda ba daga kabilar ubanka take ba, gama mu yayan annabawa ne. Ka tuna dai da Nuhu, da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kakanninmu na farkon farawa. Dukansu, ai, auren zumunci suka yi, aka kuwa sa musu albarka da yaya, kabilarsu kuma za ta mallaki makekiyar ƙasa. 13 Kai ma, ya ɗana, dole ne ka ƙaunaci naka yanuwa. Kada ka raina yanuwanka, wato yayan kabilarka mata da maza, ka zaɓi matarka ma daga cikinsu. Gama girmankai na kawo koma baya da damuwar gaske. Ragwanci ma yake jawo bukatar abu da talauci, gama ragwanci ne uban yunwa.

14 Kada ka ce wa yan ƙodagonka, Kuɗinku sai gobe. Da sun gama aiki, ka biya su nan take. In ka yi wa Allah bauta, za ka sami lada. Ka yi hankali, ɗana, cikin dukan abin da kake yi, ai, gani ga wani, ya isa tsoron Allah. Ka hori kanka a dukan maamalarka. 15 Kada ka yi wa wani abin da kai ba ka so a yi maka. Kada ka sha giya har ka bugu. Kada ka bari maye ya zama tsabiarka.

16 Ka ba waɗanda ke jin yunwa abinci. Ka suturta masu tsiraici. Duk abin da kake da shi da yawa, ka keɓe wani sashi don ba da sadaka. In kana ba da sadaka kuwa, kada ka yi gunaguni a kanta. 17 Ka riƙa ba da sadakar giya da abinci a janaizar adalai, amma kada ka yi wa masu mugunta.

18 Ka nemi gargaɗin duk mutum mai hikima, kada ma ka yi wa gargaɗi mai amfani zunɗe. 19 Ka yabi Ubangiji Allah a kowane abu, ka roƙe shi ya bi da kai a tafiyarka, ya ma sa ka ka ci nasara a duk abin da kake yi, ko shirin yi. Gama ba kowace kabila ce ke da shawara mai basira ba, amma Ubangiji shi kansa ya ba da dukan alherai. Bisa ga nufinsa ne yake ɗaga mutum, ko ya kā da shi zuwa zurfin lahira. Don haka yanzu, ɗana, ka tuna da wasiyyuna, kada ka bari su faɗi daga zuciyarka.

20 To yanzu, ɗana, dole ne in gaya maka, na ajiye jakunkunan azurfa goma wajen Gabayal, ɗan Gabari, wanda yake zaune a Ragesa a ƙasar Mediya. Kada ka ji tsoro, ɗana, wai don mun shiga fatara. Za ka sami wadata mai yawa in kana da tsoron Allah, in ka guje wa kowane irin zunubi, ka yi abin da Ubangiji Allah ke so.

5. An Samo wa Tobiya Ɗan Rako

1 Saan nan Tobiya ya amsa wa mahaifinsa Tobi, ya ce, Ubana, zan bi dukan abin da ka faɗa mini. 2 Amma yaya zan iya samun kuɗin nan daga gunsa? Bai san ni ba, ni ma ban san shi ba. Wace shaida zan ba shi yadda zai gaskata har ya ba ni azurfar? Bayan haka ma, ban san hanyar da zan bi, mai kai ni Mediya ba.

3 Sai Tobi ya amsa wa ɗansa Tobiya, ya ce, Kowannenmu ya sa hannu a wata guntuwar takarda wadda aka yaga biyu, don haka kowannenmu yana riƙe da rabin. Na ɗauki falle guda, na haɗa gudan da azurfar. Don yau shekara ashirin ke nan tun da na bar masa ajiyar azurfar. To yanzu, ɗana, sami wani mutumin kirki, ku tafi tare, za mu biya shi in kun dawo. Amma tafi, ka karɓo kuɗin daga Gabayal.

4 Sai Tobiya ya fita neman mutumin da ya san hanyar da za su bi zuwa Mediya. A waje sai ya tarar da malaika Rafayal a tsaye yana fuskantarsa, ko da ya ke bai gane malaikan Allah ne ba. 5 Sai Tobiya ya ce masa, Daga ina ka fito, aboki?

Malaikan ya ce, Ni ɗaya ne daga cikin yanuwanka Israilawa, na zo nan garin neman aiki.

Tobiya ya tambaye shi, ya ce, Ka san hanyar zuwa Mediya?

6 Malaikan ya ce, Da farin sani kuwa! Na sha zuwa can ma, har na haddace hanyoyin duka. Na je can sau barkatai; ina kwana gidan Gabayal, ɗanuwan nan namu da ke zaune a Ragesa a Mediya. Ai, tafiyar kwana biyu ce daga Ekbatana zuwa Ragesa. Ragesa ma gari ne bisa duwatsu, amma Ekbatana karkara ce ta milla ta tafi.

7 Tobiya ya ce, To, tsaya ni, abokina, in je in gaya wa mahaifina. Ina bukatar mu tafi tare, zan ba ka lada gwargwado.

8 Malaikan ya ce, To madalla, zan jira ka, amma kada ka daɗe. 9 Tobiya ya tafi, ya gaya wa mahaifinsa, cewa ya sami wani daga cikin Israilawa.

Sai uban ya ce, Ka ce ya shigo! Ina so in san iyayensa da kabilarsu. Dole ne in gani in abokin tafiyar kirki ne ka samu, ɗana.

Sai Tobiya ya fita waje, ya kira. shi, ya ce, Abokina, ka zo, ubana na son ganinka. 10 Malaikan ya shiga gidan. Tobi ya fara gaishe shi. Malaikan ya amsa, yana yi wa Tobi fatar alheri.

Tobi ya ce, Ashe, ni zan sami wani alheri ke nan? Ni makaho ne, ba na iya ganin gari, ina zaune zugudum kamar waɗanda suka mace, ba su ƙara ganin haske. Ai, ni na mutu da sauran raina, ina ji ana magana, amma ba na iya ganin mai yi.

Malaikan ya ce, Ka taazantu, ba da dadewa ba, Allah zai warkar da kai. Ka taazantu.

Sai Tobi ya ce, Ɗana Tobiya yana son tafiya zuwa Mediya. Za ka raka shi, ka yi masa jagora? Zan ba ka lada, ɗanuwana.

Malaikan ya ce, Na yarda, zan tafi tare da shi, gama na san dukan hanyoyi, na je Mediya sau da yawa, na ratsa karkararta da duwatsunta, hanyoyin kuwa ba wanda za ta ɓace mini.

11 Tobi ya ce, Danuwana, suwanene iyayenka, wace kabila ce kai? Za ka gaya mini, ɗanuwana.

12 Ina ruwanka? Kana neman kabila ko kuwa wanda za ka biya ya raka danka?

Tobi ya sāke cewa, Ina so ne in tabbata ko kai ɗan wanene da sunanka kuma.

13 Malaikan ya ce, Ni ne Azariya, ɗan dattijo Hananiya, ɗaya daga cikin danginka.

14 Sai Tobi ya ce, Sannu da zuwa, ɗanuwana! Kada ka damu don na tambayi gaskiya a kan iyayenka. Yanzu na gane kai ɗanuwanmu ne, daga iyayen kirki ka fito ka haihu. Na san Hananiya da Nataniya, yaya biyun na dattijo Shemaiya. Na saba zuwa Urushalima tare da su, muna yin sujada tare a can, ba su taɓa bauɗe wa hanyar gaskiya ba dadai. Yanuwanka mutanen kirki ne, ka zo daga dangi mai kyau. Kai, sannu da zuwa!

15 Ya ci gaba da cewa, Zan rika ba ka kuɗin aiki na kowace rana, da abin da kai da ɗana za ku bukata don tafiya. 16 In kun tafi kun dawo lafiya, kai da ɗana, zan ma wuce abin da muka shirya zan ba ka.

17 Malaikan ya ce, Zan tafi da shi. Kada ka yi wani fargaba. Za mu tafi mu kuma dawo lafiya, ai, hanyar lafiya lau take.

Tobi ya ce, Allah ya sa maka albarka, kai ɗanuwana! Saan nan ya juya gun ɗansa, ya ce masa, Ɗana, ka shirya abin da kuke bukata na tafiya, ku tafi, kai da ɗanuwanka. Allah na Sama ya kiyaye ku a can, ya kuma dawo mini da ku lafiya lau! Ya sa malaikansa ya raka ku, ya kiyaye ku, ɗana!

Sai Tobiya ya sumbaci mahaifinsa da mahaifiyarsa, suka kama hanya. Tobi ya ce, Ku dawo lafiya!

18 Sai mahaifiyarsa ta rusa kuka, ta ce wa Tobi, Don me ka tura ɗana wani wuri? Ba shi ba ne jagoranmu mai yi mana kaiwa da kawowa? 19 Ai, maɗi bai kai ya zuma ba! Kuɗi sun kai darajar ɗanmu ne? 20 Ai, abin da Allah ya ba mu ya isa.

21 Tobi ya ce, Kada ki yi wannan tunani! Ɗanmu zai je tafiya, ya kuma dawo lafiya. A ranar da zai dawo gida za ki gan shi ya iso tangaran . 22 Kada ki yi irin wannan tunani, kada ma ki damu a kansu, uwargida! Ai, malaikan kirki zai raka shi, za su yi tafiya mai kyau, su dawo, su same mu lafiya lau, sai alheri. 23 Saan nan ta shafe hawayenta.

6. An Kama Kifi

1 Sai yaron ya tafi tare da malaikan, karensu kuma ya fito daga gidan, ya bi su daga baya. Suka yi tafiyarsu, su biyu. Da yamma ta yi, sai suka yi zango a bakin Kogin Taigiris. 2 Sai yaron ya gangara kogi don ya wanƙe ƙafafu. A lokacin kuwa wani babban kifi ya dako tsalle da nufin ya haɗiye ƙafar yaron. Da yaron ya fasa ƙara, 3 sai malaikan ya ce masa, Kamo kifin, kada ka bari ya kuɓuce. Yaron ya shaƙo kifin, ya jefo shi kan tudu.

4 Malaikan ya ce, Yanka shi, ka cire matsarmama, da zuciya, da kuma hanta, amma ka jefar da sauran yan ciki. Ka ajiye matsarmama, da zuciya, da hanta, gama suna yin magani. 5 Sai yaron ya feɗe kifin, ya ɗebe matsarmama, da zuciya, da hanta. Ya raba kifin, ya soya wanda zai ci, ya kuma ƙyafe sauran don hanya. 6 Saan nan suka ci gaba da tafiya, sai da suka kusa kai Mediya.

7 Saan nan yaron ya yi wa malaikan tambayan nan, ya ce, Ɗanuwana Azariya, wace irin cutar zuciya, da hanta, da matsarmamar kifi za su iya warkarwa?

8 Malaikan ya ce, Ka ƙona zuciyar kifin da hantarsa, in hayaƙinsu ta taɓa, shi ne zai yi wa namiji ko mace magani wanda aljani ko muguwar iska ta taɓo, duk irin wannan taɓin zai warke, ba ma zai sake kamuwa ba. 9 Matsarmamar kuma, ita abin shafawa ce in yānā ta kama idon wani, in ka goga ta, hura idon kawai za ka yi, sai ta yiwo tsalle, ta fito daga idon.

10 Sai suka isa Mediya, har sun kusa kai Ekbatana, 11 kana Rafayal ya ce wa yaron, Danuwana Tobiya!

Tobiya ya ce, I ye?

Malaikan ya ci gaba, ya ce, Yau a gidan Raguwal ne za mu kwana, ɗanuwan nan naka. Yana da ya mai suna Saratu. 12 Amma bayan Saratu ba shi da sauran da mace ko namiji. Yanzu kai ne danuwanta mafi kusa. Ita halaliyarka ce, ya hakkanta ka ci gadon mahaifinta. Ita ma tana da hankali, ya ce mai kyan diri, ga mazakuta, mahaifinta ma, ai, yana ciwon sonta. 13 Tun da ya ke ita halaliyarka ce ga aure, ji nan, ɗanuwana, yau da yamman nan zan yi magana da uban a kan yar, in shirya yadda za ka kai mata toshi, da ka dawo daga Ragesa, sai ku yi aurenku. Na tabbata kuwa, Raguwal ba shi da hujar hana maka ita, ba shi ma da ikon ba wani ita. In ya ba wani ita, ai, ya keta haddi, kamar dai yadda aka zana a Attaura ta Musa. Ya san dangantakarku ta ba ka aurenta. Don haka ka saurara, ɗanuwana! Da yamma nan za mu yi maganar aure a kan yarinyar domin a sa muku rana. Lokacin da muke dawowa daga Ragesa, za mu ɗauke ta, mu taho gida da ita.

14 Tobiya ya amsa wa Rafayal, ya ce, Ɗanuwana Azariya, an gaya mini, an ce ta yi aure har sau bakwai, amma kowane lokaci sai angon ya mutu a dakin amaryar. A daren da ya shiga ɗakin, ran nan ne yake kwana lahira. Na ma ji mutane na cewa wani aljani ne yake kashe su. 15 To, ina tsoron wannan aljani, gama yana sonta, ba ya yi mata wani lahani, amma nan da nan da wani mutum ya matse ta, sai aIjanin ya aika da shi garinsu na kaito. Ni kaɗai ne gun mahaifina. In na mutu da sauri haka, iyayena za su yi baƙin cikin da zai kashe su. Ba su da wani ɗa, balle ya rufe su.

16 Malaikan ya ce, Har ka mance da gargaɗin mahaifinka? Ai ma, cewa ya yi, ka yi aure daga cikin danginka. Ka saurara, ɗanuwana, kada ka damu da aljanin, aure ta! Na yi maka wannan alkawari, da sanyin yamman nan za ta zama matarka. 17 Saan nan da ka shiga ɗakin amaryar, ɗauki ɗan sashin zuciya da hantar kifin nan, ka barbaɗa a kaskon wuta. Hayaƙin zai yi sama, da aljanin ya ji ƙanshin, zai yi waje, ba sauran wata muguntar da za ta sami yarinyar nan gaba. Saan nan, kafin ka yi kwanan aure da ita, dukanku biyu ku tashi tsaye, ku yi addua tukuna. Ka roƙi Ubangijin Sama ya ba ku alheri, ya yi muku tsari. Kada ka ji tsoro, ai, kai ne, aka ƙaddara wa ita tun farko, kai ne kuma za ka cece ta. Za ta bi ka, in kuma tabbatar maka, za ta haifa maka yaya waɗanda za su zama daidai da yanuwa a guna. Kada ka damu!

Da Tobiya ya ji Rafayal ya ce haka, ya kuma gane Saratu yaruwarsa ce, ya ce daga dangin ubansa, sai ya ƙaunace ta har matuƙa, yadda har ya rasa abin cewa.

7. Raguwal ya ba Tobiya Saratu

1 Da suka shiga garin Ekbatana, sai Tobiya ya ce wa malaikan, Ɗanuwana Azariya, kai ni gidan danuwanmu Raguwal nan da nan.

Sai malaikan ya nuna masa hanyar zuwa gidan Raguwal, suka same shi zaune a kofar gida. Suka fara gai da shi tukuna, ya amsa ya ce, Yauwa! Sannunku dai da zuwa, yanuwana! Ina fata kun zo lafiya. Sai ya shigar da su gida. 2 Sai ya ce wa matarsa Adama, Kai, wannan ɗa ya yi kama da ɗanuwana Tobi.

3 Adama ta tambaye su daga inda suke, suka ce, Mu jikokin Naftali ne da aka mayar bayin yaƙi a Nineba.

4 Sai ta ce, Kun san ɗanuwanmu mai suna Tobi?

Suka ce, I, mun san shi.

Ta kuwa ce, 5 Yana nan lafiya ƙalau?

Suka ce, Har yau yana da rai, lafiya lau yake.

Sai Tobiya ya ƙara da cewa, Ai, shi ne babana.

6 Sai Raguwal ya yi tsalle, ya sumbace shi, yana kuka don farin ciki.

7 Amma da ya ji Tobi ya makance, sai ya yi matuƙar baƙin ciki, har ya ɓarke da kuka. Saan nan, da samun kansa, sai ya ce, Allah ya sa maka albarka, ɗana! Ai, kai dan mutumin kirkin gaske ne. Abin baƙin ciki ne yadda irin wannan mutum mai gaskiya mai alheri, zai makance! Sai ya rungume dan garinsu Tobiya, ya sāke barkewa da kuka. 8 Matarsa Adama ma ta yi kuka, haka kuma yarta. Saratu.

9 Sai Raguwal ya yanka rago, aka shirya musu ƙasaitaccen liyafa. Bayan sun yi wanka, suka zauna cin abincin, sai Tobiya ya ce wa Rafayal, Ɗanuwana Azariya, ka roƙar mini Raguwal, ya ba ni yaruwata Saratu. 10 Ashe, har Raguwal ya ji, sai ya ce wa saurayin, Ci, ka sha, ka hole wannan yamma, ba wanda ke da halalin auren yata Saratu—ba shi sai ko kai, ɗanuwana. Ko da ƙaƙa, ni, a bisa ga nawa gani, bai hakkanta ba in ba wani ita, tun da ya ke kai ne danuwanmu mafi kusa. Duk da haka kuma, ɗana, dole ne in gaya maka ƙashin gaskiya. 11 Ai, na yi ƙoƙarin samar mata mijin kirki, har sau bakwai a danginmu, amma dukansu sun mutu tun daren farko, da suka shiga ɗakinta. Amma yanzu, ɗana, ci, ka sha, Ubangiji ne zai yi maka alheri da salama.

12 Sai Tobiya ya maganta, har ya ce, Ba zan ji ci ko sha ba, sai ka ba ni amsa a kan yarka da nake nema.

Raguwal ya amsa, ya ce, Da kyau! Kamar dai yadda ka ce, bisa ga Attaura ta Musa, an ba ka ita, Allah ma ya ƙaddara ta zama taka. Saboda haka ina danƙa maka yaruwarka a hannunka. Daga yanzu kai ɗanuwanta ne, ita kuma yaruwarka. Daga yau an ba ka ita har abada. Ubangijin Sama ya ba ka saa a daren nan, ɗana, ya ma yi maka alheri da salama.

Raguwal ya kira yarsa Saratu, ya kama hannunta, ya danƙa wa Tobiya, yana cewa, Na danƙa ta a hannunka bisa ga sharia. A bisa ga kaidar da Littatin Musa ya ƙunsa, an ƙaddara ta ta zama matarka. Ɗauke ta, ɗauke ta, ka tafi da ita gidan ubanka da hankali kwance. Allah na Sama ya sa ku kai gida lafiya da salama. 13 Sai ya juyo ga mahaifiyarta, ya ce ta nemo masa takardar rubutu, don ya zana ɗaurin auren na yadda ya ba da yarsa aure ga Tobiya bisa ga kaida a Attaura ta Musa. Sai uwarta ta kawo takardar, Raguwal ya rubuta ɗaurin auren, ya sa mata hatiminsa.

14 Bayan haka sai suka fara ciye‑ciye da shaye‑shaye. 15 Sai Raguwal ya kira uwargidansa Adama, ya ce mata, Uwargiɗana, ki shirya ɗaki na biyu, ki kai ta can.

16 Ta tafi, ta shirya gado kamar yadda ya dai umarta, ta kai yarta a kai, ta yi ɗan kuka a kan yar. 17 Saan nan ta shafe hawayenta, ta ce wa yar, 18 Ki taazantu, yata! Ubangijin Sama ya mai da baƙin cikinki farin ciki! Ki taazantu, yata! Kana ta sa kai, ta fita.

8. An Kori Aljanin

1 Lokacin da suka gama ciye‑ciye da shaye‑shayen barci ya isa ga mai hankali, sai aka kai angon ɗaka. 2 Tobiya ya tuna da gargadin da Rafayal ya yi masa, ya je gun burgaminsa, ya duntsi zuciyar kifin da hantar, ya zuba su a kaskon wuta. 4 Sai hayaƙin kifin ya gallabi baƙin aljanin, ya fita fir, ya bi iska zuwa kudancin Masar. Rafayal ya runtume shi can, ya kama shi, ya shaƙe, ya ɗaure bajau. Nan da nan Rafayal ya dawo.

4 Da iyayen suka tashi suka rufe ƙofa, sai Tobiya ya tashi tsaye daga kan gadon, ya ce wa Saratu, Tashi tsaye, yaruwata! Ni da ke, dole mu yi wa Ubangiji addua da roƙe‑roƙe domin ya ba mu alheri da kiyayewarsa. 5 Ta tashi tsaye, sai suka fara addua don kiyayewa. Ga yadda suka yi addua.

Yabo ya tabbata gare ka, ya Allah na kakanninmu,
      Ai, sunanka ma mai albarka ne har abada abadin.
Bari sammai su yabe ka,
      Da dukan abubuwan da ka yi dai, har abada ba fashi.
Ai, kai ne ka halicci Adamu,
      Ka kuma ba shi matarsa Hawwau
Don ta zama mataimakiyarsa mai tallafi,
      Daga biyun nan ne kabilar yan adam ta yaɗu.
Kai ne, ai, ka ce, Bai kyautu mutum ya kasance shi kaɗai ba,
      Bari mu yi masa mataimakiya mai dacewa.
Yanzu, ya Ubangiji, ka sani na auri yaruwata,
      Ba da nufin fasikanci ba,
      Amma da nufin gaskiya.
Ta alherinka ka yi mata jinƙai, da ni kuma,
      Ka sa mu mu kai tsufanmu lafiya.

8 Sai suka ce, Amin, amin.

9 Saan nan suka kwanta.

10 Amma Raguwal ya kira barorinsa, su taimake shi ya gina kabari, domin ya ce, In Tobiya ya mutu, za a yi mana baƙar magana da gori.

11 Da aka gama ginin kushewar, sai Raguwal ya koma gida ya kira matarsa. Ya ce mata, Aika da baiwa, ta je ta gani in Tobiya na nan da rai har yanzu. Gama in ya mutu, sai mu rufe shi, ba tare da kowa ya sani ba.

13 Aka kira baiwa wadda ta kunna fitila, ta buɗe ƙofa ta shiga ɗakin. Sai ta tarar suna ta sharar barcinsu abinsu. 14 Sai ta jawo jiki, ta yi wa Raguwal da Adama raɗa, ta ce, Ai, bai mutu ba, sun kwana garau. 15 Sai Raguwal ya yabi Allah, ya ce,

Albarka ta tabbata gare ka, ya Allah
      Ka cancanci tsattsarkan yabo.
Dukkan zaɓaɓɓunka sai su yabe ka,
      Su yabe ka ba fasawa!
Albarka ta tabbata gare ka, tun da aka faranta raina,
      Abin da nake wa fargaba bai faru ba,
      Maimakon haka ka yi mana babban jinƙai.
Albarka ta tabbata gare ka, saboda jinƙanka
      A kan tilon dan nan da tilon yan nan.
Yanzu sai ka kiyaye su da alherinka,
      Ka sa su yi zamansu lafiya, da farin ciki.

18 Saan nan sai ya sa barorinsa su cika kabarin kafin rana ta fito.

19 Ya ce wa matarsa ta yi burodi mai yawan gaske, ya je garkensa ya jawo bijimai biyu, da tumaki hudu, ya ce a yanka, a shirya su, shirin biki. 20 Sai ya kira Tobiya, ya ce masa, Na rantse da Alllah, ba na so in ji labarin tashinka daga nan har na mako biyu. Ka zama a inda kake mana, kana ci kana sha tare da ni. Za ka faranta wa yata rai saboda dukan ɓacin ranta. 11 Bayan haka, zan ba ka rabin dukan abin da nake da shi, saan nan ka korna gidan ubanka, ba wata jayayya. Lokacin da ni da matata muka mutu ma sai ka dawo, ka kwashe sauran rabin. Ka ƙarfafa, ɗana! Ai, ni ne ubanka, Adama uwarka. Mu ne iyayenka nan gaba, kamar yadda muke na yaruwarka Saratu. Ka ƙarfafa, ɗana!

9. Bikin Aure

1 Saan nan Tobiya ya juya wajen Rafayal, ya ce masa, 2 Ɗanuwana Azariya, ka kwashe barori huɗu da raƙuma biyu, ka tafi Ragesa. Je ka gidan Gabayal, ka ba shi guntuwar takardan nan, ka amso kuɗin, kana ka gayyato shi ya zo gun bikin aurena. 3 Ka sani, yanzu ubana yana ƙidayar kwanakin. In na taushe hannu ko da kwana ɗaya, zai damu ƙwarai. 4 Ko da rantsuwar da Raguwal ya yi, ba zan iya karya ta ba. 5 Sai Rafayal ya tafi Ragesa cikin Mediya da barori huɗu da raƙuma biyu. Suka sauka a gidan Gabayal, kana Rafayal ya nuna masa guntuwar takardar. Ya faɗa masa labarin bikin auren Tobiya ɗan Tobi, ya kuma gayyato shi gun bikin auren. Sai Gabayal ya shiga ƙirga masa jakunkuna ɗinkakku na kuɗi, aka jibga wa raƙuman.

6 Kashegari da sassafe sai suka tafl bikin tare, suka isa gidan Raguwal inda suka iske Tobiya yana kai wa ka. Sai Tobiya ya miƙe domin ya gai da Gabayal. Shi kuwa Gabayal sai ya ɓarke da kuka, ya kuma sa masa albarka, ya ce, Da mai fifiko na uban da ba ya muzantuwa, mai adalci da alheri a dukan abin da yake yi! Ubangiji ya sa maka albarkar sama, kai da matarka, da uban da kuma uwar matarka! Yabo ga Allah da ya ƙaddara mini ganin wannan siffa ta ƙanen Tobi.

10

1 A kowace rana da suke can, sai Tobi ya yi ta ƙirga sauran ranakun da suka ragu na tafiyarsu ta komowa gida. Da kwanakin suka ƙare, amma ɗa nasa bai shigo ba, 2 sai ya yi tunani, ya ce, Watakila an tsayar da shi a can, ko kila kuma Gabayal ya mutu, bai kuwa sami wanda zai ba shi kuɗin ba. 3 Har dai ya fara damuwa kuma.

4 Sai matarsa Harmatu ta nace cewa, Ɗana ya mace! Ai, ba ya cikin rayayyu yanzu! Sai ta fara kukan makoki a kan ɗanta. 5 Ta yi ta cewa, Allah Sarki! Na ƙyale ka ka bar ni, ɗana, kai da kake hasken idanuna.

6 Sai Tobi ya ce mata, Kash, uwargiɗana! Kada ki yi mugun tunani irin haka. Ai, lafiya lau yake. Wani abu ne kawai ya tsai da su. Abokin tafiyarsa wanda za mu iya amince wa ne, ai, danuwanmu ne ma. Kada ki karaya, uwargiɗana. Ba da daɗewa ba zai shigo.

7 Amma sai kawai ta ce, Ni dai, ka rabu da ni, kada ka yi koɗarin ruɗina. Na sani ɗana ya rasu. A kowace rana sai ta fita dawa, tana ta kallon hanyar da ɗanta ya bi, ba ta cin kome. Da rana ta faɗi, sai ta koma gida kuma, ta yi ta kukan makoki dukan dare, har ba ta iya barci.

8 Da kwana goma sha huɗu da Raguwal ya keɓe na bikin auren yarsa suka cika, sai Tobiya ya je gunsa, ya ce, To, bari in tafi gida. Na sani yanzu ubana da uwata har sun fid da zuciya ga ganina ma sam. Ina roƙonka, Baba, ka bar ni in koma gidan mahaifina. Na gaya maka halin da yake ciki a lokacin da na baro shi.

9 Sai Raguwal ya ce wa Tobiya, Share gindi, ka zauna, ɗana, mu zauna tare. Zan aika da saƙo gun ubanka Tobi, in ba shi labarinka.

Amma dai Tobiya, sai ƙara matsa lamba yake yi, har ya ce, Aa. Ina roƙonka, in koma gidan ubana.

10 Ba tare da ƙin manufa ba, sai Raguwal ya ba Tobiya da Saratu, amaryarsa, rabin abubuwan da yake da su, bayi mata da maza, da bijimai, da tumaki, da jakai, da raƙuma, da tufafi, da kuɗi, da kayan gida. Sai ya sallame su. Lokacin da suke tashi, sai ya ce wa Tobiya, Ku sauka lafiya, ɗana, ku kuma yi zaman lafiya! Ubangijin Sama ya yi muku alheri, kai da matarka Saratu! Ina fatar ganin jikokina kafin in mutu. 11 Sai ya sumbaci yarsa Saratu, ya ce mata, Ki girmama surukanki, tun da ya ke yanzu iyayenki ne kamar iyayen da suka haife ki. Ki sauka lafiya, yata, ina fata ba abin da zan ji a kanki sai dai alheri a dukan kwanakina. Sai ya ce, Gamun alheri, ya sallame su, suka tafi.

13 Adama ita kuma sai ta ce wa Tobiya, Ya ɗana, ɗanuwana, Allah ya kai ka gida lafiya! Ina fata Allah ya ba ni tsawon rai in ga jikokina da yata za ta haifa maka kafin in mutu. A gaban Ubangiji na danƙa yata a hannun Allah da hannunka. Ko watan wata rana kada ka ɓata mata rai. Ku sauka lafiya, ɗana! Daga yau ni ce uwarka, Saratu kuma yaruwarka. Allah ya sa dukanmu mu yi farin ciki dukan kwanakin ranmu! Sai ta sallami dukansu biyu da sumba.

14 Tobiya ya baro gidan Raguwal da rai kwance. Da farin cikinsa har ya yabi Ubangijin Sama da ƙasa, Sarkin dukan abin da ya wanzu, don sun yi gamon katar da tafiyarsu. Ya ma sa wa surukansa Raguwal da Adama albarka, ya ce, Allah ya sa in girmama ku dukan kwanakin raina. Sai suka tashi, suka kama hanya zuwa gida.

11. An Warkar da Makantar Tobi

1 Da suka kusa kai wa Kasarina, kusa da Nineba, sai Rafayal ya ce, Ka san halin da muka bar ubanka a ciki. 2 Mu yi gaba, mu shirya gidan, matarka ta taho da sauran mutane. 3 Sai suka yi gaba tare, Rafayal ma ya ce wa Tobiya ya riƙe matsarmamar a hannu. Sai karen nan ya bi su a baya.

5 Hannatu na zaune, tana duban hanyar da ɗanta zai biyo. 6 Da ta hango shi, ta gane shi ne, sai ta ce wa mijin, Ga danka nan tafe, tare da abokin tafiyarsa.

7 Kafin su isa gidan, sai Rafayal ya ce wa Tobiya, Na alkawarta maka, cewa idanun mahaifinka za su bude. 8 Ka shafe idanunsa da matsarmamar kifin, maganin zai tauye yānār, nan da nan za ta fito daga idanun mahaifinka, zai sami gani, ya dubi hasken gari.

9 Sai Hannatu ta ruga da gudu, ta rungume ɗanta, ta ce, To, yanzu na iya mutuwa, tun da na sāke ganinka. Ta yi kuka kuma.

10 Tobi ya miƙe, ya yi sassarfa, ya fita ya tafi tarya. Tobiya ya doso shi, 11 yana da matsarmamar kifin a hannu. Sai ya riƙe uban, ya hura idanunsa, yana cewa, Ka taazantu, mahaifina! 12 Da ya ce haka, 12 sai ya shafa maganin a idanu, sai idanun suka yi yaji. 13 Saan nan ya sa hannuwa biyu, ya gwale idaun, ya ɗibi yānā. Da Tobi ya ga dansa, sai ya rungume shi, yana kukan daɗi. Har ya yi magana, ya ce, Ina iya ganinka, ya ɗana, hasken idanuna! 14 Har ya ƙara da cewa,

Albarka ta tabbata ga Allah!
      Ai, babban sunansa ma mai albarka ne!
Albarka kuma ga malaikunsa masu tsarki!
      Ai, babban sunansa ma mai albarka ne
      Har abadan abada!
Gama dā ya raunata ni,
      Amma yanzu ya warkar da ni,
      Har na ga yarimana Tobiya!

Sai Tobi ya shiga gidan, yana yabon Allah da babbar murya. Saan nan Tobiya ya ba mahaifinsa labari yadda abin ya faru, yadda ya yi ta cin karo da saa a tafiyar, har kuma ga azurfa ya amso, da yadda ya auri Saratu, yar Raguwal, da yadda take binsa yanzu, da yadda suke gab da Nineba.

16 Tobi, sai ya nufi ƙofar garin Nineba a guje don ya taryi surukarsa, yana yin muma, yana ta yabon Allah. Da mutanen Nineba suka ga yana tafiya kisim‑kisim, ba jagora kuma, sai suka yi mamaki. 17 Sai Tobi ya ba su labari yadda Allah ya ji tausayinsa, ya buɗe idanunsa. Saan nan Tobi ya ce, Sannu dai da zuwa, yata! Yabo ga Allahnki da ya aiko mana da ke, ya yata. Allah ya sa wa mahaifinki da mahaifiyarki albarka da kuma ɗana Tobiya, da ke kanki, yata! Barkanki da zuwa gidanki da farin ciki da albarka! Shigo gida, shigo gida, yata!

18 Ran nan dukan Yahudawan da ke Nineba sun yi muma. Har Ahikara, da ɗan kanensa, Nadab, suka zo domin su taya Tobi muma. An yi kwana bakwai ana bikin auren Tobiya, ana farin ciki, ana ma ba shi bayabaye masu yawa.

12. Rafayal ya Bayyana ko shi Wanene

1 Da aka gama bikin, Tobi ya kira ɗansa Tobiya, ya ce masa, Ya ɗana, ai, ko ya kamata ka biya abokin tafiyarka hakkinsa kuwa, ka biya shi fiye da abin da aka ƙayyade can dā.

2 Ya amsa, ya ce Mahaifina, nawa ya kamata a ba shi don taimakon da ya yi? Ai, ko rabin dukiyar da muka kawo na ba shi, ai, ba ni da hasara. 3 Ya fa kawo ni gida gunka lami lafiya, ya warkar da matata, ya amso kuɗin nan, ga shi kuma, yanzu kai ma ya warkar da kai. Me ya kamata in ba shi kan duk wannan abu?

4 Sai Tobi ya ce, Ya kamaci rabin abin da ya kawo.

5 Saan nan Tobiya ya kira abokin tafiya, ya ce masa, Ka kwashe rabin abin da ka kawo, shi ne ladanka a kan dukan taimako da ka yi. Ka karɓa da haƙuri, Allah ya kai ka gida laflya kuma.

6 Saan nan Rafayal ya kira su waje guda, ya ce musu, Ku yabi Allah, ku yabe shi, ku yi masa hamdala a gaban dukan mutane a kan alheran da ya yi muku, kuna yabonsa, kuna raira waƙar sunansa. Ku bayyana ayyukan Allah da kuma bangirma a gaban dukan yan adam, ku yi masa godiya ba fasawa. 7 Daidai ne a ɓoye asirin sarki, amma a bayyana ayyukan Allah a fili. Ku yi masa godiya da bangirma, ku aikata alheri, ba muguntar da za ta same ku. 8 Ai, addua da azumi suna da kyau. Amma sadaka da adalci sun fi. Ai, kaɗan tare da adalci ya fi wadata tare da zalunci. Ba da sadaka ya fi tara ɗumbun zinariya, 9 gama ba da sadaka ke fansar mutum daga mutuwa, ya kuma wargaje kowane irin saɓo. Masu ba da sadaka za su more dukan kwanakinsu. 10 Mai yin saɓo da aikata mugunta ya yi wa kai nasa.

11 Zan gaya muku ƙashin gaskiya, ba zan ɓoye muku kome ba. Na riga na gaya muku cewa, ya kamata a ɓoye asirin sarki, amma a bayyana aikin Allah da bangirma. 12 Don haka ina sanar muku, a lokacin da kai, Tobi, da Saratu ke yin addua, ni ne, ai, na miƙa, na kuma karanta rokerokenku a gaban Allah. Haka na yi ma a loton da kake rufe matattu. 13 Ai, lokacin da ka tashi ka bar abincinka, bai dame ka ba, don ka rufe matattu, ni ne aka aiko don a gwada bangaskiyarka. 14 A lokaci guda ne kuma aka aiko ni na warkar da kai da surukarka Saratu. 15 Ni ne Rafayal, ɗaya daga cikin malaikun nan bakwai waɗanda suke tsaye shirye a kullum domin su shiga su yi hidima gaban ɗaukakar Ubangiji.

16 Dukansu biyu, da Tobi da Tobiya, mamaki ya kama su, suka gurfana a ƙasa, suka yi sujada. 17 Amma malaikan ya ce, Kada ku ji tsoro, salama ma ta kasance gare ku. Ku yabi Allah har abada. 18 Ai, a lokacin da muke tare, zamana da ku ba alherina ba ne, amma na Allah ne. Shi ne ma za ku yaba kowace rana. 19 A tsammaninku kun gan ni ina ci ina shan abinsha, amma kama ce kawai. 20 Yanzu dai sai ku tashi daga ƙasa, ku yabi Allah. Ni kuma zan koma gun wanda ya aiko ni. Ku rubuta dukan abin nan da ya faru. Sai ya tashi fir cikin iska. 21 Da suka tashi tsaye, ba su kara ganinsa ba. 22 Sai suka raira waƙoƙin yabon Allah, suka gode masa saboda manyan abubuwan da ya aikata lokacin da malaikan Allah ya bayyana gare su.

13. Waƙar Tobi a kan Urushalima

1 Daganan sai Tobi ya wallafa waƙan nan ta muma, ga abin da ya ce:

Yabo ga Allah wanda ke raye har abada,
      Gama mulkinsa ya tabbata har abada!
2 Yana raunanawa, yana yin jinƙai,
      Yana aikawa da mutane zurfafan lahira,
Ya kuma zaro su daga babbar halaka,
      Ba mai iya kuɓuta daga hannunsa, ai.
Ku yabe shi a gaban alummai mana,
      Ku da kuke Israilawa!
Ai, ko da ya yi daidai da ku a tsakaninsu,
      A can ma ya nuna muku ikonsa a fili.
Ku ɗaukaka shi a gaban dukan mutane,
      Gama shi ne Ubangiji Allahrimu fa,
      Shi ubanmu ne da Allahnmu, har abada abadin.
5 Ko da ya ke ya hore ku a kan zunubanku,
      Ai, zai maji tausayin dukanku,
Zai tattaro ku gu daya daga sauran alumma,
      Daga duk inda aka yi ɗaya ɗaya da ku a dā.
6 In dai kun juya gare shi da dukan zuciyarku,
      Kuna aikata aikin gaskiya a gabansa,
Saan nan zai juyo gare ku, shi ma,
      Ba kuma zai kara ɓoye muku fuska ba.

Ku dubi dai irin abin kirkin da ya yi muku,
      Ku gode masa mana, kai jamaa!
Ku yabi Ubangijin adalci,
      Ku kuma ɗaukaka Sarkin dukan zamanai.

Ai, ni ma nakan yi waƙar yabonsa
      A lokacin da nake bawan yaki a wani gari.
Na sanar da ikonsa da girmansa a fili
      Ga alummar da take yin saɓo kuwa.
Ai, ku masu saɓo, sai ku juya gunsa,
      Ku dai ku kasance da hali mai kyau,
Lalle zai yi muku alheri,
      Ya kuma ji tausayinku.

7 Ni ma ina ɗaukaka Allah,
      ƙaina kuma yana yin fari fat da Sarkin nan na Sama.
8 Bari girmansa ya zauna a bakin dukan mutane,
      A yi waƙar yabonsa a Urushalima.
9 Ya Urushalima, birni mai tsarki.
      Allah ya raunana ki a kan gumakan da kika yi,
      Amma duk da haka zai ji tausayin yayanki, adalai.
10 Ki gode wa Allah saboda alherinsa,
      Ki yabi Sarkin dukan zamanai!
Domin za ki yi farin ciki
      Da ganin an sāke gina masujadarsa a cikinki,
Zai kuma dawo miki da bayin yaƙinki,
      Ya taazanta su a cikinki,
Dukan wadanda ke baƙin ciki zai ƙaunace su a cikinki
      Har dukan zamanai masu zuwa.

11 Ai, hasken haske zai haskaka a kan duk sashe na duniya,
      Kabilai za su bangazo gare ki daga wurare masu nisa,
Daga wannan bangon duniya zuwa wancan,
      Domin su ji labarin alherin da Ubangiji ya yi miki,
      Suna da kyautai a hannunsu domin Sarkin Sama.
A cikinki, tsara za ta bi tsara,
      Suna bayyana matuƙar farin cikinsu a kanki.
Har ga yan zamanin nan na gaba,
      Kowa zai san Allah ya zaɓe ki.

12 Duk wanda ya ci mutuncinki laananne ne,
      Haka ma wanda ya hallaka ki ya rushe garunki,
Da wanda ya tunkuɗe hasumiyoyinki,
      Ya ƙone gidajenki ƙurmus,
Amma albarka ta tabbata har abada
      Ga duk wadanda suka sāke gina ki.

13 Yanzu dai, sai ki yi muma da yayanki, adalai,
      Gama za a tara su duka a gu ɗaya,
      Su yabi Ubangijin dukan zamanai.
14 Albarka ta tabbata gun masu ƙaunarki
      Da wadanda ke naam da zaman salamarki,

Masu albarka ne su da ke makoki a kan dukan wahalarki,
      Ai, ba da daɗewa ba za su yi muma,
      Suna ganin farin cikinki har abada.

15 Raina ya yabi Ubangiji, Sarki mai girma,
      Tun da ya ke za a sāke ginin Urushalima
      Don mazauninsa har abada abadin.
Ai, faida ce gare ni in ko ɗaya ne ya ragu daga cikin yayana,
      Ya yabi Sarkin Sama domin ganin ɗaukakarki.
Za a sake gina ƙofofin Urushalima na azurfa da yakutu,
      Katangun kuma na duwatsu masu. daraja.
Ai, hasumiyoyin Urushalima da zinariya za a sāke su,
      Da garkuwoyin garu kuma na zinariya zahiri.

17 Za a yi wa hanyoyin garin Urushalima ado
      Da yakutu da duwatsu daga ƙasar Ofir.
18 A ƙofofin Urushalima za a sāke jin amo
      Na waƙokin nan na muma.
A dukan gidajenta kuma za a ce,
      Alhamdu lillahi!
Yabo ga Allah wanda ya tashe ki,
      A yabe shi har abada abadin!
      Gama a garinki za su yabi sunansa mai tsarki har abada abadin.

Ƙarshen waƙar Tobi ke nan.

14. Wasiyyar Tobi ga Tobiya

Tobi ya mutu da salama, yana da shekara ɗari da goma sha biyu, aka kuwa yi masa janaiza mai ƙayatarwa a garin Nineba. 2 Yana da shekara sittin da biyu ne, ya makance. Da aka warkar da makantar kuma, ya ɗade yana zaman jin daɗi, yana ba da sadaka, kullum yana yabon Allah yana yabon babbar ɗaukakarsa.

3 Da ya kusa mutuwa, sai ya kira dansa Tobiya da yayansa bakwai duk, ya yi masa gargaɗin nan, ya ce, Ya ɗana, kwashe yayanka , 4 Ka gudu zuwa Mediya, tun da ya ke na gaskata da maganar Allah wadda Annabi Nahum ya hurta a kan Nineba. Duk abin zai zama gaskiya, kome ya tabbata yadda manzannin Allah, annabawa, suka faɗa a kan Assuriya da Nineba. Ai, kalmarsu ko ɗaya ba za ta fāɗi ƙasa ba, za ta tabbata a kan karinta. Za ka fi zama lafiya a Mediya fiye da Assuriya ko Babila, tun da ya ke ni na tabbata abin da Allah ya faɗa zai tabbata dole, ai, haka ne kuwa zai zama, ba za a fasa cika ko kalma ɗaya ta annabcin ba.

Yanuwanmu da ke zaune a ƙasar Israila za a warwatsa su duka, a kuma kama su, a ta da su daga cikin tasu ƙasa. Dukan ƙasar Israila dungum za ta zama kufai. Samariya da Urushalima za su zama faƙo. Haikalin Allah kuma, za a ƙone ƙurmus, ya zama kufai da ɗan daɗewa. 5 Saan nan Allah zai sāke yi musu jinƙai, ya dawo da su ƙasar Israila. Za su sāke ginin Haikalin Allah, ko da ya ke ba zai kai ƙyan na farkon ba, har lokaci ya cika. Saan nan ne, duk yayan Urushalima za su dawo daga bauta, su sāke gina ta, da dai dukan ɗaukakan nan tata, a sāke gina Haikalin Allah a cikinta. I, za a sāke gina shi, ya zama har abada, kamar dai yadda annabawan nan na Israilawa suka ce tuni. 6 Saan nan dukan alumman duniya za su tuba, za su ji tsoron Allah da sahihancin zuciya. Duk za su raina yan allolin nan nasu da ke sa su bauɗewa, suna yankan jeji. 7 Za su yabi Allah madawwami da halin adalci. Dukan Israilawan da aka keɓe a ranakun nan za su tuna da Allah da sahihan zukatansu. Za su zo duk, su hallara gu ɗaya a Urushalima, su yi ta zaman lafiya a ƙasar Annabi Ibrahim, wadda za ta zama tasu gaba ɗaya. 9 Masu ƙaunar Allah da gaske za su yi murna. Amma waɗanda suka yi saɓo za a dulmuyar da su daga duniya.

9 To yanzu, ku yayana, na bar muku wannan wasiyya, ku bauta wa Allah da gaskiya, ku yi abin da ke faranta masa rai. Ku koya wa yayanku su ɗau halin adalci, su ba da sadaka, su tuna da Allah a zuci, su yabe shi kullum da gaskiya, gwargwadon iyawarsu.

10 Ai, don haka, ya ɗana, tashi maza daga Nineba, kada ka zauna a cikinta. Da ka rufe mahaifiyarka a kusa da tawa kushewar, ka bar garin ran nan, ko da wane lokaci ne. Kada ka yi ta lilo a wannan gu da mutanen ba su da kunya, ba tsoron ido, inda zalunci da ƙeta suke ta tohowa. Yi tunani, ɗana, da dukan abin da Nadab ya yi saad da ya yi agolanci a gun Ahikara. Nadab ya rufe shi da rai a kurkuku ƙarƙashin ƙasa. Amma Allah ya saka wa wanda aka kwara ɗin nan take, wato reshe ta juye da mujiya, tun da ya ke Ahikara ya fito zuwa haske, amma sai Nadab ya gangara madawwamin duhun lahira don ƙetar da ya shirya yi wa Ahikara. Ai, saboda sadakar da Ahikara ya ba ni ne, Allah ya sa ya ƙetare tarkon muguntar da Nadab ya ɗana masa, sai Nadab ya fāɗa tsundum a ramin muguntar da ya gina. 11 To, yayana, kun ga sakayyar ba da sadaka fa, da kuma sakayyar aiki mugunta, yadda take kai wa mahallaka. Amma kash! Ga shi, na shaƙe yanzu.

ƙarshen Kwanakin Tobiya

12 Sai suka kwantar da Tobi a gadonsa, ya mutu, aka yi masa janaizar gatanci. Da mahaifiyar Tobiya ta mutu kuma, sai ya rure ta gab da kushewar mahaifinsa. Saan nan ya tashi zuwa Mediya, shi da matar da yayansu. Ya zauna a Ekbatana tare da Raguwal, surukinsa. Ya kula da tsofaffin nan da yarsu, ba yunwa ba ƙishi. Da aka jima, tsofaffin nan suka mutu, sai ya rufe su a Ekbatana ta ƙasar Mediya. Tobiya ya gāji dukiyar Raguwal da ta mahaifinsa Tobi. 14 Aka girmama shi kwarai, ya yi shekara ɗari da goma sha bakwai. 15 Bai mutu ba sai da ya ga kangon Nineba. Ya ga yadda ake kwasar Ninebawa a bayin yaƙi, ana kai su Mediya, in ji Sarkin Kayazarisa na Mediya. Ya gode wa Allah a kan hukuncin da Allah ya yi wa Ninebawa da Assuriyawa. Bai ma mutu ba sai da ya yi farin ciki a kan tangaɗin da Nineba ta yi, ya yabi Mai Sama, ya ce, Yabo ga Ubangiji Allah har abada abadin. Amin, amin.

*      *      *      *      *
*      *      *
*