Zephaniah

Zafaniya

1

Ranar Hasalar Ubangiji a kan Yahuza

1Ubangiji ya yi magana da Zafaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza.

2“Ni Ubangiji na ce, zan shafe dukan kome Da yake a duniya.

3Zan shafe mutum da dabba, Zan shafe tsuntsayen sararin sama da kifayen teku, Zan kuma rushe gumakansu tare da mugaye, Zan kuma datse ɗan adam daga duniya.

4“Zan miƙa hannuna gāba da Yahuza Da dukan mazaunan Urushalima. A wurin nan zan datse saura waɗanda suke bauta wa Ba'al, Da kuma sunayen firistocin gumaka tare da firistocina,

5Da kuma waɗanda suke durƙusa wa rundunan sama a kan bene, Waɗanda sukan durƙusa, su rantse da Ubangiji, Duk da haka kuma sai su rantse da Milkom,

6Da kuma waɗanda suka juya, suka bar bin Ubangiji, Waɗanda ba su neman Ubangiji, ba su kuma roƙonsa.”

7Ku yi tsit a gaban Ubangiji Allah! Gama ranar Ubangiji ta gabato. Ubangiji ya shirya ranar shari'a, Ya kuma keɓe waɗanda za su aikata hukuncinsa.

8“A ranar shari'a, ni Ubangiji zan hukunta shugabanni da hakimai, Da dukan waɗanda suke bin al'adun ƙasashen waje.

9A wannan rana zan hukunta duk wanda yake tsalle a bakin ƙofa, Da waɗanda suke cika gidan maigidansu da zalunci da ha'inci.

10“Ni Ubangiji na ce, a wannan rana, za a ji kuka a Ƙofar Kifi, Za a ji kururuwa kuma daga unguwa ta biyu, Da amon ragargajewa daga kan tuddai.

11Ku yi kururuwa, ku mazaunan Maktesh, Gama 'yan kasuwa sun ƙare, An kuma datse dukan waɗanda suke awon azurfa.

12“A lokacin nan, Zan bincike Urushalima da fitilu, Zan kuwa hukunta marasa kulawa Waɗanda suke zaman annashuwa, Waɗanda suke cewa a zukatansu, “‘Ubangiji ba zai yi alheri ba, Ba kuma zai yi mugunta ba!”

13Za a washe dukiyarsu, Za a kuwa rurrushe gidajensu, Ko da yake sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba, Ko da yake sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”

14Babbar ranar Ubangiji ta gabato, Tana gabatowa da sauri. Ku ji muryar ranar Ubangiji! Jarumi zai yi kuka mai zafi.

15Wannan rana ta hasala ce, Ranar azaba da wahala, Ranar lalatarwa da hallakarwa, Ranar duhu baƙi ƙirin, Ranar gizagizai da baƙin duhu,

16Ranar busar ƙaho da yin kururuwar yaƙi Gāba da birane masu garu da hasumiyai masu tsawo.

17“Zan aukar wa mutane da wahala, Za su kuwa yi tafiya kamar makafi, Domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura, Namansu kuwa kamar taroso.”

18Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su A ranar hasalar Ubangiji ba, A cikin zafin kishinsa Dukan duniya za ta hallaka. Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.

Za a Hallaka Al'umman da suke Kewaye da Su

2

1Ya ke al'umma marar kunya, ku tattaru, ku yi taro,

2Kafin a zartar da umarni, Kafin a kore ku kamar ƙaiƙayi, Kafin kuma zafin fushin Ubangiji ya auko muku, Kafin ranar hasalar Ubangiji ta auko muku.

3Ku nemi Ubangiji, Dukanku masu tawali'u na duniya, Ku waɗanda kuke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali'u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.

4Za a bar Gaza ba kowa, Ashkelon za ta zama kufai, Za a kori mutanen Ashdod da tsakar rana, Ekron kuwa za a tumɓuke ta.

5Taku ta ƙare, ku mazaunan gaɓar teku, ke al'ummar Keretiyawa! Ya Kan'ana, ƙasar Filistiyawa, Maganar Ubangiji tana gāba da ke, Za a hallaka ki har ba wanda zai ragu.

6Gāɓar teku za ta zama makiyaya, da wurin zaman masu kiwo, Da kuma garakan tumaki.

7Gaɓar teku za ta zama ta mutanen Yahuza waɗanda suka ragu, Wurin da za su yi kiwo. Za su kwanta da maraice a gidajen Ashkelon, Gama Ubangiji Allahnsu zai kula da su, Zai kuwa mayar musu da albarkarsu ta dā.

8“Na ji ba'ar da Mowab ta yi, da zagin Ammonawa, Yadda suka yi wa mutanena ba'a, Sun yi alwashi, cewa za su cinye ƙasarsu.

9Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, Na rantse cewa, Mowab za ta zama kamar Saduma, Ammonawa kuma za su zama kamar Gwamrata. Za su zama ƙasar ƙayayuwa Da kwazazzaban gishiri marar amfani har abada. Mutanena waɗanda suka ragu za su washe su, su mallake su.”

10Wannan shi ne hakkin girmankansu, Saboda sun raina jama'ar Ubangiji Mai Runduna, Sun yi musu alfarma.

11Ubangiji zai tsananta musu, Zai kawo wa dukan gumakan da suke a duniya yunwa. Kowane mutum a duniya zai yi masa sujada a inda yake, Har da ƙasar sauran al'umma.

12“Ku kuma, Habashawa, za a kashe ku da takobina.”

13Zai miƙa hannunsa gāba da arewa, Zai hallaka Assuriya, Zai mai da Nineba busasshen kufai Marar amfani kamar hamada.

14Tumaki za su kwanta a tsakiyarta, Da kuma kowace irin dabba ta kowace ƙasa. Mujiya da bushiya za su zauna a kan ginshiƙanta, Ga muryar kuka a taga. Ga risɓewa a bakin ƙofa, Gama za a kware rufin katakan itacen al'ul.

15Wannan shi ne birnin da yake da harka, mai zaman lafiya, Wanda yake ce wa kansa, “Ba wani sai ni.” Ga shi, ya zama kufai, Wurin zaman dabbobi! Duk wanda ya wuce ta wurin, Zai yi tsaki, ya kaɗa kai.

Zunubin Urushalima da Fansarta

3

1Taka ta ƙare, kai mai tayarwa, Ƙazantaccen birni mai zalunci!

2Ba ya kasa kunne ga muryar kowa, Ba ya karɓar horo. Bai dogara ga Ubangiji ba, Bai kuma kusaci Allahnsa ba.

3Shugabanninsa zakoki ne masu ruri, Alƙalansa kuma kyarketai ne da sukan fito da maraice, Waɗanda ba su rage kome kafin wayewar gari.

4Annabawansa sakarkari ne, maciya amana. Firistocinsa sun ƙazantar da abin da yake mai tsarki. Sun kuma keta dokoki.

5Ubangiji wanda yake cikinsa mai adalci ne, Ba ya kuskure. Yakan nuna adalcinsa kowace safiya, Kowace safiya kuwa bai taɓa fāsawa ba. Amma mugu bai san kunya ba.

6Ubangiji ya ce, “Na datse al'umman duniya, Hasumiyansu sun lalace. Na kuma lalatar da hanyoyinsu, Ba mai tafiya a kansu. An mai da biranensu kufai, Ba mutumin da yake zaune ciki.

7Na ce, hakika za ka ji tsorona, Ka kuma karɓi horo. Ba za a rushe wurin zamanta ba Bisa ga hukuncin da na yi mata. Amma suka ɗokanta su lalatar da ayyukansu.

8“Domin haka ni Ubangiji na ce, Ku jira ni zuwa ranar da zan tashi in yi tuhuma. Gama na ƙudura zan tattara al'umman duniya, da mulkoki, Don in kwarara musu hasalata Da zafin fushina, Gama zafin kishina Zai ƙone dukan duniya.

9“Sa'an nan zan sauye harshen mutane da harshe mai tsabta, Domin dukansu su yi kira ga sunan Ubangiji, Su kuma bauta masa da zuciya ɗaya.

10Gama daga hayin kogunan Habasha, Masu yi mini sujada, Mutanena da suke warwatse, Za su kawo mini hadaya.

11A wannan rana ba za a kunyatar da kai ba, Saboda tayarwar da ka yi mini ta wurin ayyukanka. Gama a sa'an nan zan fitar da masu girmankai Da masu fankama daga cikinka, Ba za ka ƙara yin alfarma ba A dutsena tsattsarka.

12Zan kuwa bar mutane masu tawali'u, Da masu ladabi a cikinka, Su kuwa za su nemi mafaka a wurin Ubangiji.

13Waɗanda suka ragu cikin Isra'ila, Ba za su aikata mugunta ba, Ba kuma za su faɗi ƙarya ba, Gama harshen ƙarya ba zai kasance a bakinsu ba. Za su yi kiwo, su kwanta, Ba wanda zai tsorata su.”

Waƙar Murna

14Ki raira waƙa da ƙarfi, ya ke Sihiyona! Ki ta da murya, ya Isra'ila! Ki yi murna, ki yi farin ciki, Ya ke Urushalima!

15Ubangiji ya kawar miki da hukuncinsa, Ya kuma kori abokan gābanki. Ubangiji Sarkin Isra'ila, yana a tsakiyarki, Ba za ki ji tsoro ba.

16A wannan rana za a ce wa Urushalima, “Kada ki ji tsoro, ke Sihiyona, Kada ki bar hannuwanki su raunana.

17Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki, Mayaƙi mai cin nasara ne. Zai yi murna, ya yi farin ciki da ke. Zai sabunta ki da ƙaunarsa. Zai kuma yi murna da ke ta wurin raira waƙa da ƙarfi.

18Zan tara waɗanda suka yi makoki domin idi, Waɗanda suke tare da ke, Wato waɗanda nawayar zaman talala Ta zamar musu abin zargi.

19Ga shi kuwa, a wannan lokaci Zan hukunta masu zaluntarki, Zan kuma ceci gurgu, Zan tattara korarru, Zan mai da kunyarsu ta zama yabo, Za su yi suna a duniya duka.

20A wannan lokaci zan komo da ku gida, In tattara ku wuri ɗaya. Zan sa ku yi suna, Ku sami yabo a wurin mutanen duniya duka, A sa'ad da na mayar muku da arzikinku, Ni Ubangiji na faɗa.”