HANYAR GICIYE
BISA GA LABARIN MATIYU[S. = Shugaba; J. = Jamaa]
S. Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah makaɗaici, har abada abadin.
J. Amin.S. Ya Ubangiji, ka buɗe lebunana.
J. Halshena zai raira yabon alherinka da ƙarfi.S. Ya Allah, ka cece ni.
J. Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni.S. Ɗaukaka ga Uba da ga Ɗa da ga Ruhu Mai Tsarki.
J. Kamar yadda ya ke tun a farko, yanzu, har abada, daga zamani zuwa zamanu. Amin.Waƙa
S. Ga shi tutar Sarki tana zuwa
giciyensa ne ya bayyana.
A bisan shi mutum ya rataya,
shi wanda ya hallicci mutum ne.J. Ya Allah, mai tsarki!
Ya Mai inganci, mai tsarki!
Ya Marar mutuwa, mai tsarki!
ka yi mana jinƙai.S. Kai ice mai ado mai kyau,
shafaffe da jini da ruwa,
Waɗanda da kwiɓinsa Yesu ya zuba,
domin ya wanke laifofimmu.J. Ya Allah, mai tsarki!
Ya Mai inganci, mai tsarki!
Ya Marar mutuwa, mai tsarki!
ka yi mana jinƙai.S. Mai rataya bisa giciye, ranka ya daɗe,
kai fatammu makaɗaici ne.
Ka ƙara mana adilci,
ka gafarta zunubammu.J. Ya Allah, mai tsarki!
Ya Mai inganci, mai tsarki!
Ya Marar mutuwa, mai tsarki!
ka yi mana jinƙai.(Kamin kowane tashi)
J: Muna yin sujada ga giciyenka, ya Ubangiji, muna yabon tashinka mai tsarki mai daraja. Gama saboda icen giciye murna ta zo cikin dukan duniya.(Bayan ayoyin Zabura)
J: Ya Ubangiji, ka yi jinƙai
Ya Kristo, ka yi jinƙai.
Ya Ubangiji, ka yi jinƙai.1. Dabarar Mutuwar Yesu
Mt 26:3-4, 14-16:
3 Sai manyan malamai da shugabannin jama'a suka taru a gidan Babban Malamin, mai suna Kayafas. 4 Suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci su kashe shi. 14 Sai ɗaya daga cikin Sha biyun nan, mai suna Yahuda Iskariyoti, ya je wurin manyan malamai 15 ya ce,"Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?" Sai suka ƙirga kuɗin azurfa talatin, suka ba shi. 16 Tun daga lokacin nan ne ya nemi hanyad da zai bashe shi.
Zab 55
Ba magabci ba ne * wanda ya yi mani cin fuskar da nike jurewa.
Ba maƙiyi ba ne ya ɓata mani suna, * balle in ɓuya daga gare shi.
Amma kai ne, aminina, * abokina da na amince da shi.
Mun saba yin shirin zaune tare * a cikin Gidan Allah, * inda muke cudanya da taron jama'a.2. Cimar Ubangiji
Mt 26:21-29
21 Suna cikin cin abinci, sai ya ce, "Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni." 22 Sai suka yi baƙinciki gaya, suka fara ce da shi daidai da daidai, "Ni ne, ya Ubangiji?" 23 Sai ya amsa ya ce, "Wanda mu ke ci akushi ɗaya, shi ne zai bashe ni. 24 Ɗam Mutun zai tafi ne, yadda labarinsa, ke rubuce, duk da haka muturnin nan da ke ba da Ɗam Mutun ya shiga uku! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa." 25 Sai Yahuda da ya bashe shi ya ce, "Ko ni ne, ya Shugaba?" Yesu ya ce masa, "Ga shi kai ma ka faɗa." 26 Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, "Ungo, ku ci. Wannan jikina ne." 27 Sai ya ɗauki ƙoƙo, kurna bayan ya yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, "Dukkanku ku shassha. 28 Don wannan jinina ne na tabbatar Alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubansu. 29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranan nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana."
Zab 102
Magabcina yana zagina, * Mai tonona yana yin biki da ni.
Toka ce abincina, * daga kwallana nike samun ruwan sha.
Saboda haushinka da hushinka, * kā ɗaga ni, ka kuma jefad da ni.3. Tafiya Zuwa Jatsamani
Mt 26:30-35
30 Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun. 31 Sai Yesu ya ce musu, "Duk za ku ƙosa da ni a wannan daren. Don a rubuce ya ke, cewa, 'Zam buge makiyayi, tumakin garken kuwa su fasu.' 32 Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili." 33 Bitrus ya ce masa, "Ko duk sun ƙosa da kai, ni kam ba zan ƙosa ba faufau." 34 Yesu ya ce masa, "Hakika, ina gaya maka, ko a wannan daren, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku." 35 Bitrus ya ce masa, "Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba." Haka ma duk almajiran suka ce.
Zab 22
Kada ka yi nesa da ni, * gama masu tsananta sun yi kusa, * ba ma wani mataimaki.
Bajimai masu yawa suna kewaye ni, * ƙarfafan bajimai daga Bashan suna sa ni tsaka.
Suna buɗe mani bakinsu, * kamar zakoki masu kāwa masu hauka.4. Cikin Jatsamani
Mt 26:36-46
36 Sannan Yesu ya zo da su wani wurin da a ke kira Jatsamani. Ya ce da almajiransa, "Ku zauna nan, ni kuwa zan je can in yi addu'a." 37 Sai ya ɗauki Bitrus da 'ya'yan nan na Zabadi guda biyu, ya fara baƙinciki da damuwa ƙwarai. 38 Sai ya ce musu, "Raina na shan wahala matuƙa, har ma kamar na mutu. Ku dakata nan, ku zauna a faɗake tare da ni." 39 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya faɗi ƙasa, ya yi addu'a ya ce, "Ya Ubana, im mai yiwuwa ne, ka ɗauke min shan wahalan nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka." 40 Sai ya komo wurin almajiran, ya samu suna barci, sai ya ce da Bitrus, "Ashe ba za ku iya zama a faɗake tare da ni ko da sa'a ɗaya ba? 41 Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a kada ku faɗa ga gwaji. Zuciya kam ta ɗauka, jiki ne rarrauna." 42 Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu'a, ya ce, "Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, a aikafa nufinka." 43 Har yanzu dai ya dawo ya samu suna barci, don duk barci ya cika musu ido. 44 Har wa yau ya sake barinsu, ya koma ya yi addu'a ta uku, yana maimaita maganar dā. 45 Sai ya komo wurin almajiran, ya ce musu, "Har yanzu barci ku ke yi, kuna hutawa? To, ga shi lokaci ya yi kusa. Am ba da Ɗam Mutun ga masu zunubi. 46 Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe nin nan ya matso!"
Zab 69
Ka cece ni, Allah, * domin ruwa ya kai wuyana.
Na nutse cikin Taɓo mai zurfi, * inda ba damar tsayawa.
Na shiga zuzzurfan ruwa, * inda igiyoyin ruwa suke cina.
Na gaji da kuka, * maƙogwarona ya bushe.
Idanuna sun fara dushewa, * sa'ad da nike dako, ya Allah.5. An danƙe Yesu
Mt 26:47-56
47 Kamin ya rufe baki sai ga Yahuda, ɗaya daga cikin Shabiyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan malamai da shugabanni ne suka turo su. 48 To, mai bashe shin nan ya riga ya ƙulla da su cewa, "Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi." 49 Nandanan sai ya matso wurin Yesu ya ce, "Ranka ya daɗe, ya Shugaba!" Sai ya yi ta sumbantarsa. 50 Yesu ya ce masa, "Abokina, abin da ya kawo ka ke nan?" Sai suka matso suka danƙe Yesu, suka kama shi. 51 Sai ga ɗaya daga cikin waɗanda ke tare da Yesu ya miƙa hannu ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan Babban Malamin sara, ya ɗauke masa kunne. 52 Sai Yesu ya ce masa, "Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zari takobi, takobi ne ajalinsa. 53 Kuna tsammani ba zan iya neman taimako gun Ubana ba, nandanan kuwa ya aiko min fiye da rundunonin mala'iku goma sha biyu? 54 To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai Tsarkaka kan lalle wannan abu ya kasance?" 55 Nan take Yesu ya ce da taron jama'a, "Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗam-fashi? Kowace rana na kan zauna a Ɗakin lbada ina koyarwa, amma ba ku karna ni ba. 56 Amma duk wannan ya auku ne don a cika Littattafan Annabawa." Daganan sai duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.
Zab 88 & 41
Ka sa abokaina yin nesa da ni, * don na zama abin ƙyama a gare su.
Ina kurkuku, bana iya gudu, * idanuna sun rage gani saboda wahala.
Har ma abokina * wanda na amince da shi,
wanda muke ci a kushi ɗaya, * yana ƙulla ƙarairayi a kaina.6. Shari'a a gaban Manyan Yahudawa
Mt 26:57-68
57 Sai waɗanda suka kama Yesu suka tafi da shi wurin Kayafas, Babban Malamin, inda malaman Attaura da shugabanni su ke tare. 58 Amma sai Bitrus ya bi shi daga nesanesa, har cikin gidan Babban Malamin. Da ya shiga daga ciki sai ya zauna cikin ma'aikatan Ɗakin lbada, don ya ga ƙarshen abin. 59 To, sai manyan malamai da duk majalisa suka nemi ƙazafin da za a yi wa Yesu don su samu su kashe shi. 60 Amma ba su samu ba, ko da ya ke masu shaidar zur da yawa, sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso, 61 suka ce, "Wannan ya ce wai zai iya rushe Wurin nan Tsattsarka na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku." 62 Sai Babban Malamin ya miƙe ya ce, "Ba ka da wata amsa? Shaidad da mutanen nan ke yi a kanka fa?" 63 Amma Yesu na shiru. Sai Babban Malamin ya ce da shi, "Na garna ka da Allah Rayayye, faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah." 64 Sai Yesu. ya ce masa, "Ai kai ma ka faɗa. Ina kuwa gaya muku nan gaba za ku ga Ɗarn Mutun zaune a hannun dama na Mai iko, yana kuma zuwa kan gajimare." 65 Sai Babban Malamin ya kyakketa tufafinsa, ya ce, "Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi! 66 Me kuka gani?" Suka arnsa suka ce, "Ya cancanci kisa!" 67 Sai suka tattofa masa yawu a fuska, suka nannaushe shi, wasu kuma suka marnmare shi, 68 suna cewa, "Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!"
Zab 35
Mashaidan ƙarya sun tayar mani, * waɗanda ban sani ba sun yi mani tambayoyi.
Sun saka mani alheri da mugunta, * suna baƙanta ruhuna.
Amma ni, lokacin da suka busa sarewa, * na sa tsumma. * Na hori kaina ta wurin azumi.7. Birus ya rena Yesu
Mt 26:69-75
69 To, Bitrus kuwa na zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya kansa, ta ce, "Kai ma ai tare ka ke da Yesu Bagalile!" 70 Amma sai ya musa a gabansu duka ya ce, "Ni ban san abin da ƙi ke nufi ba." 71 Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shl, ta ce da waɗanda ke tsaitsaye a wurin, "Ai mutumin nan tare ya ke da Yesu Banazarel" 72 Sai ya sake musawa har da rantsuwa ya ce, "Ban ma san mutumin nan ba." 73 Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce da Bitrus, "Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka." 74 Sai ya fara la'anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, "Ban ma san muturnin nan ba." Nandanan sai zakara ya yi cara. 75 Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu, cewa, "Kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku." Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.
Zab 69 & 38
Saboda kai ne na sha zagi, * cin mutunci ya rufe fuskata.
Na zama baƙo ga 'yan'uwana, * bare kuma ga 'ya'yan da muke uwa ɗaya.Aminaina da abokan tafiya * sun kauce daga damuwata, * dangina sun yi nesa da ni.
8. Yesu a gaban Bilatus
Mt 27:1-3, 11-14
Da gari ya waye sai duk manyan malamai da shugabannin jama'a suka yi shawara a kan Yesu su kashe shi. 2 Sai suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Gwamna Bilatus. 11 To, sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamnan kuma ya tambaye shi, "Ashe kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?" Yesu ya ce masa, "Yadda ka faɗan." 12 Amma da manyan malaman da shugabanni suka ɗaɗɗora masa laifi, bai ce komai ba. 13 Sai Bilatus ya ce masa, "Ba ka ji yawan maganganun da su ke ba da shaida a kanka ba?" 14 Amma bai ba shi wata amsa ko da ta laifi guda da aka ɗora masa ba, har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.
Zab 38
Bala'i da lalacewa * suke yi mani fata dukan yini.
Amma na yi kama da bebe da baya ji, * kamar kurma da baya magana.
Na zama kamar beben da baya ji, * wanda babu wata tsawatawa daga bakinsa.9. An yanke mas hukuncin kisa
Mt 27:15-26
15 To, a lokacin Idi kuwa gwanma ya saba sakam ma jama'a kowane fursuna guda da su ke so. 16 A lokacin kuwa da wani shaharraren fursuna, mai suna Barabbas. 17 Da suka taru sai Bilatus ya ce da su, "Wa ku ke so in sakarn muku? Barabbas ko kuwa Yesu da a ke kira Almasihu?" 18 Don ya sani saboda hassada ne suka bashe shi. 19 Ban da haka kuma, lokacin da ya ke zaune kan gadon shari'a, sai matatasa ta aiko masa da cewa, "Fita sha'anin marar laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai game da mafarkinsa." 20 To, sai manyan malamai da shugabanni suka rarrashi jama'a a kan su zaɓi Barabbas, Yesu kuwa a kashe shi. 21 Sai gwamnan ya sake ce da su, "Wanene a cikin biyun nan ku ke so in sakarn muku?" Sai suka ce, "Barabbas." 22 Bilatus ya ce musu, "To, ƙaƙa zan yi da Yesu da a ke kira Almasihu?" Duk sai suka ce, "A giciye shi!" 23 Ya ce "Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?" Amma su sai ƙara hayagaga su ke yi, suna cewa, "A giciye shi!" 24 Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai ma hargitsi na shirin tashi, sai ya ɗebi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama'a, "Ni karn na kuɓuta daga alhakin jinin mai gaskiyan nan. Sai ku ji da shi." 25 Sai duk jama'a suka amsa suka ce, "Alhakin jininsa a wuyammu, mu da 'ya'yammu!" 26 Sannan ya sakarn musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a giciye shi.
Zab 55
Na ga tashin hankali da hargitsi a cikin birnin. * Dare da rana suna kewaye da shi.
A kan garunsa akwai ƙeta da fitina. * Daga tsakkiyarsa ayyukan mugunta suna fitowa,
daga tsakkiyarsa ba su dena zuwa ba, * daga dandalinsa zalunci da zamɓa suna watsuwa.10. An wulakanci Yesu
Mt 27:27-32
27 Sai sojan gwamna suka kai Yesu cikin faɗar gwamna, suka tara dukkan kamfanin soja a kansa. 28 Sai suka tube shi, suka yafa masa wata jar alkyabba. 29 Sai suka yi wani kambi na ƙaya, suka sa masa a ka, suka ɗanka masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna masa ba'a suna cewa, "Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!" 30 Suka tattofa masa yawu, suka karɓe sandan, suka ƙwala masa a ka. 31 Da suka gama yi masa ba'a, sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufatin, suka tafi da shi su giciye shi. 32 Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Siman. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki giciyen Yesu.
Zab 69
Ina tunanin dukan ɓacin raina a cikin azumina, * wulakanci kuma ya zama rabona.
Na mai da tsummoki tufafina, * na zame masu abin dariya.
Har 'yan bikin da mashaya * suna wallafa waƙoƙin shegantaka a kaina.11. An giciye Yesu
Mt 27:33-44
33 Da suka isa wurin da a ke kira Golgota, wato, Wurin Ƙoƙwan Kai, 34 sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha. 35 Da suka giciye shi, sai suka yi ƙuri'a suka rarraba tufafinsa a junansu. 36 Sai suka zauna a nan suna gadinsa. 37 Daidai kansa sai aka kafa sanarwar laifinsa cewa, "Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa." 38 Sai kuma aka giciye 'yam-fashi biyu tare da shi, ɗaya ta dama, ɗaya ta hagun. 39 Masu wucewa suka yi ta yi masa bakar magana, suna kada kai, 40 suna cewa, "Kai da za ka rushe Wuri Tsattsarka, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to, sauko daga giciyen mana!" 41 Haka kuma manyan malamai da malaman Attaura da shugabanni suka riƙa masa ba'a suna cewa, 42 "Ya ceci waɗansu, ya kuwa ƙasa ceton kansa. Ai Sarkin Bani Isra'ila ne, yă sauko mana daga giciyen yanzu, mu kuwa ma gaskata da shi. 43 Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne." 44 Har 'yam-fashin nan da aka giciye su tare ma suka zazzage shi kamar waɗancan.
Zab 22
Gama karnuka sun kewaye ni, * ƙungiyar miyagu ta sa ni a tsaka,
sun cinye naman hannuwana da ƙafafuna. * Na iya ƙirga dukan ƙasusuwana.
Ga yadda suke kallona, suke zura mani ido.12. Yesu ya mutu bisa Giciye
Mt 27:45-55
45 To, tun daga tsakar rana, sai duhu ya rufe ƙasa, duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 46 Kuma waien ƙarfe ukun sai Yesu ya daga murya da ƙarfi ya ce, "Eli, Eli, lama sabaktdni?" wato, "Ya Allahna, ya Allahna, dom me ka yashe ni?" 47 Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, sai suka ce, "Mutumin nan na kiran Iliya ne." 48 Sai nandanan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jika shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha. 49 Amma sai sauran suka ce, "Ku bari mu gani ko Iliya zai zo ya cece shi." 50 Sai Yesu ya sake daga murya da ƙarfi, sannan ya ba da ransa. 51 Sai Labulen Wuri Tsattsarka ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa kuma ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage. 52 Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da ke barci kuma suka tashi. 53 Da suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birni, suka bayyana ga mutane da yawa. 54 Sa'ad da kyaftin da waɗanda ke tare da shi suna gadin Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya rufe su, suka ce, "Hakika wannan Ɗan Allah ne!" 55 Akwai kuma wasu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima. 56 Cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu da Yusufu, da kuma uwar 'ya'yan Zabadi.
Zab 22
Amma ni tsutsa ne, ba mutun ba, * mafi renanne wurin mutane, * abin ba'a ga kowa.
Duk waɗanda ke ganina suna maishe ni abin dariya, * suna tsaki, suna kaɗa kai, suna cewa:
"Ya bi Yahweh, bari ya kuɓutad da shi; * sai ya cece shi in ya so shi."13. Jana'izar Yesu
Mt 27:57-62
57 La'asar lis sai wani mai arziki ya zo, muturnin Arimatiya, mai suna Yusufu, shi ma kuwa almajirin Yesu ne. 58 Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya yi umarni a ba shi. 59 Sai Yusufu ya ɗauki jikin, ya sa shi a likkafanin linen mai tsabta, 60 ya kwantad da shi a wani sabon kabarin da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi abinsa. 61 Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun suna nan zaune a gaban kabarin.
Zab 88
An lissafta ni tare da masu zuwa Rami, * na zama mutun mara ƙarfī.
A fadar Mutuwa tabarmana yake, * kamar yankakku, * gadona yana Kabari,
inda ba ka tunawa da su, * tun da an yanke ƙaunarka daga gare su.
Kā jefa ni ƙuryar Rami, * a wurare masu duhu da zurfi.14. Tashin Yesu
Mt 28:1-10
To, bayan Asabar, da asussuba a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun, suka je ganin kabarin. 2 Sai kuwa aka yi wata babbar rawar-ƙasa, domin wani mala'ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai. 3 Kamanninsa na haske kamar walkiya, tufafinsa kuma farare fat kamar alli. 4 Saboda tsoronsa sai masu gadin suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu. 5 Amma sai mala'ikan ya ce da matan, "Kada ku ji tsoro, don na san Yesu ku ke nerna, wanda aka giciye. 6 Ai ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da ya kwanta. 7 Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa cewa ya tashi daga matattu. Ga shi kuma zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. To, na fa gaya muku." 8 Sai suka tafi daga kabarin da gaggawa da tsoro, game da matuƙar farinciki, suka ruga a guje su kai wa almajiransa labari. 9 Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce,"Salama alaikum!" Sai suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada. 10 Sai Yesu ya ce da su, "Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa 'Yan'uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni."
Zab 63
Ya Allah, Allahna, * kai ne nike marmari.
Raina yana jin ƙishinka, * jikina na begenka,
fiye da yadda busasshiyar ƙasa * ke marmarin ruwa.
A tsattsarkan mabautarka bari in zuba ido gare ka, * ina kallon ikonka da ɗaukakarka.Theotokion (Byzantine Vespers)
Ya Managarci, haifaffe ne daga budurwa domimmu,
ka sha raɗaɗin giciye, sai ta mutuwarka ka kashe mutuwa, ka kuma tashi, domin kai Allah ne. Kada ka rena mu halittarka,
Kai mai jinƙai, ka nuna ƙaunarka ga mutane, ka ji addu'ar Mahaifiyarka Uwar Alla ce, mai yi mana roƙo. Kai Macecimmu, ka ceci jama'arka masu karayar zuciya. Waƙar Maryamu
Zuciyata na ɗaukaka * shi Ubangiji
Allah Macecina * da shi ruhuna ke ta farinciki.Domin fa shi ya dubi * ƙasancinta ne baiwa tasa,
ai ga shi jamaa ta dukan zamani * mubarika ce za su ce mani nan gaba.Domin Mai iko yai mani manya-manyan alamurra, * sunansa ko labudda tsattsarka yake.
Daga zamani har dai zuwa wani zamani, * tausansa na ga waɗanda ke tsoronsa.
Alamari babba da ƙarfinsa ya yi, * ya watsa duk mutakabbirai sun watse.Ya firfitad da sarakuna a sarauta, * ya ɗaukaka masu zaman ƙasƙanci.
Mayunwata ya yalwata da abubuwan alheri, * ya sallame su da babu, masu wadata.Ya taimaka wa baransa Israila, * domin yana tune dai da yin rahamarsa.
Ita ya yi alkawari ga kakannimmu, * tutur ga Ibrahim da duk zuriyarsa.Ƙarshe
S. Ubangiji ya zama gare ku
J. A a gare ka kuma.S. Mu yi addu'a.
Ya Allah, ka yarda Ɗanka makaɗaici ya sha azabar giciye saboda zunubammu,
ya kuwa tashi domin ya cece mu.
Muna roƙonka, ka sa mu girmama asirai na fansarmu haka
domin ta tarayya da azabar Yesu
mu sami rabo da tashinsa mai daraja.
Muna roƙon ka....S. Albarka ga Ubangiji.
J. Mun gode wa Allah.