KOS NA LABARIN CETO
GIDAN MAI ALBARKA MUKASA
MALUMFASHI
1966DARASI NA FARI: HALITTAR DUNIYA
Karatu: Farawa 1:1-2:4a
Kwana na fari: 1A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya, 2duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen. 3Allah ya ce, "Bari haske ya kasance," sai kuwa ya kasance.
Kwana na biyu: 4Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu, 5ya ce da hasken, "Yini," duhu kuwa, "Dare." Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan. 6Allah ya ce, "Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu." 7Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance. 8Allah ya ce da sarari, "Sararin sama." Ga maraice, ga safiya, kwana na biyu ke nan.
Kwana na uku: 9Allah kuwa ya ce, "Bari ruwayen da suke ƙarƙashin sararin su tattaru wuri ɗaya, bari kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana." Haka nan kuwa ya kasance. 10Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, "Duniya," tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, "Tekuna." Allah ya ga yana da kyau. 11Allah kuwa ya ce, "Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa ke cikin duniya." Haka nan kuwa ya kasance. 12Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da 'ya'ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau. 13Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan.
Kwana na huɗu: 14Allah kuwa ya ce, "Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai. 15Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya." Haka nan kuwa ya kasance. 16Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin. 17Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya, 18su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19Ga maraice, ga safiya, kwana na huɗu ke nan.
Kwana na biyar: 20Allah kuwa ya ce, "Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai, bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari." 21Allah kuwa ya halicci manya manyan dodani na teku da kowane irin mai rai da yake motsi, waɗanda suke a cikin ruwaye, da kuma kowane irin tsuntsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22Sai Allah ya sa musu albarka, yana cewa, "Ku hayayyafa, ku kuma riɓaɓɓanya, ku cika ruwayen tekuna, tsuntsaye kuma ku hayayyafa cikin duniya." 23Ga maraice, ga safiya, kwana na biyar ke nan.
Kwana na shidda: 24Allah kuwa ya ce, "Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu." 25Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 26Allah kuma ya ce, "Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa." 27Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su. 28Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, "Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya." 29Allah kuwa ya ce, "Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da tsaba da yake bisa fuskar dukan duniya, da kowane itace da yake da ƙwaya cikin 'ya'yansa su zama abincinku. 30Na ba da kowane irin ɗanyen tsiro domin ci, ga kowace irin dabba da take duniya, da kowane irin tsuntsu da yake sararin sama, da kowane irin abin da yake rarrafe bisa duniya, da dai iyakar abin da yake numfashi." Haka nan ya kasance. 31Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida ke nan.
Kwana na bakwai: 2:1Da haka aka gama yin sama da duniya, da rundunansu. 2A kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa wanda ya yi. Ya kuwa huta a kan kwana na bakwai daga dukan aikinsa da ya yi. 3Domin haka Allah ya sa wa kwana na bakwai albarka, ya tsarkake shi, don a cikinsa Allah ya huta daga dukan aikin da ya yi na halitta.
Ƙarshen Magana: 4Waɗannan su ne asalin sama da duniya sa'ad da aka halicce su.
Bayyani
Cikin kwanaki uku na fari Allah ya kafa manyan wuraren duniya. Ya raba tsakanin:
haske da duhu, ruwayen da ke bisa sama da ruwaye da ke a ƙasa ruwa da busasshiyar ƙasa Manyan wuraren duniya su ne sama, tekuna, filin ƙasa. Cikin kwanaki uku na biyu, Allah ya cika wuraren duniya. Ya sa:
manyan haskoki cikin sama, kifaye cikin tekuna, da tsuntsaye cikin sararin sama, dabbobi da mutum cikin filin ƙasa. Labarin halitta ya kwatanta Allah da ma'aikaci mai kirki wanda ya tafi aikinsa da safe, ya koma gida da maraece, ya huta sai da wata safiya. Kamar misali, a kwana na fari ya yi aikin gero, a kwana na biyu ya yi aikin dawa, a kwana na uku ya yi aikin doya, a kwana na huɗu ya yi aikin auduga, a kwana na biyar ya yi aikin barkono, a kwana na shidda ya yi aikin masara. Bayan wannan ya ba da duk amfanin aikinsa wa abokinsa wanda ya ke ƙaunarshi sosai. Sannan a kwana na bakwai ya huta kuma, domin ya yi sujada wa Allah. Cikin labarin nan Allah shi ne ma'aikaci; abokinsa shi ne mutum. Allah ya yi mutum cikin surarsa bisa ga kamanninsa, domin ya ba shi sarauta a kan dukan halitta. Mutum ya samu tarayyar ikon Allah. Sai Allah kaɗai a bisa mutum ya ke.
Ga kuma yadda Allah ya halicci duniya. Ba shi da gajiya kamar mutum ma'aikaci. Ya yi duk abu ta wurin maganarsa da ikonsa mara iyaka. Allah shi ne mahaliccin sama da ƙasa, mai iko duka, mai ƙaunarmu kuma. Aka kira shi Ruhu kuma, watau iska ke nan, domin ba ya ganuwa, yana da ƙarfi kuma kamar iska. Sai dai da Yesu ya zo, an bayyana bambamcin Uba da Ɗa da Ruhu mai tsarki.
Rana ta bakwai ita ce ran Asabas. Ita ce babban rana ga Yahudawa, kamar ran Juma'a ce ga Musulmi. Amma ga Kirista Lahadi babban rana ce saboda tashin Yesu daga mutuwa a wancan rana. Saboda haka ya kamata mu yi taruwa mu yi wa Allah sujada a ran Lahadi.
Tambayoyi
- Allah ya kafa manyan wuraren duniya cikin waɗanne kwanaki?
- Allah ya cika wuraren duniya cikin waɗanne kwanaki?
- Labarin halittan duniya cikin kwana shidda ya kwatanta Allah da wanene?
- Wanene abokin Allah?
- Don me aka ce mutum shi na sura da kamanni na Allah?
- Allah ya yi sama da ƙasa ta wurin menene?
- Menene Allah?
- Me Allah ya yi a kwana na bakwai?
- Me ya kamata mu yi a ran Lahadi?
DARASI NA BIYU: MUTUM DA MACE NA FARI
Karatu: Farawa 2:4b-9,15-25
Wani labarin halitta: 2:4b A ranar da Ubangiji Allah ya yi duniya da sama, 5a sa'an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar, 6amma sai ƙāsashi yake tasowa daga ƙasa ya shayar da fuskar ƙasa duka. 7Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki. 8Ubangiji Allah kuwa ya dasa gona a Aidan, wajen gabas, a can ya sa mutumin da ya siffata. 9Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta. 10Wani kogi kuma ya malalo daga Aidan ya shayar da gonar, daga nan kuwa ya rarrabu ya zama kogi huɗu. 11Sunan na fari Fishon, shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya. 12Zinariyar ƙasar nan kuwa kyakkyawa ce. Akwai kuma duwatsu masu daraja a wurin. 13Sunan kogi na biyu Gihon, shi ne wanda yake malala kewaye da ƙasar Kush. 14Sunan kogi na uku Taigiris ne, wanda yake malala gabashin Assuriya. Kogi na huɗu kuwa Yufiretis ne.
Umurnin: 15Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta. 16Ubangiji Allah ya yi wa mutumin umarni, ya ce, "Kana da 'yanci ka ci daga kowane itace da yake a gonar, 17amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle."
Halittar dabbobi: 18Sa'an nan sai Ubangiji Allah ya ce, "Bai kyautu mutumin ya zauna shi kaɗai ba, zan yi masa mataimakin da ya dace da shi." 19Haka nan fa, daga cikin ƙasar, Ubangiji ya siffata kowace dabba ta cikin saura da kowane tsuntu na sararin sama, ya kawo su wurin mutumin, ya ga yadda zai kiraye su, duk abin da mutumin ya kirayi mai ran kuwa, sunansa ke nan. 20Mutumin ya bai wa dabbobi duka suna, da tsuntsayen sararin sama, da kowace irin dabba da take cikin saura, amma ba a sami mataimaki wanda ya dace da mutumin ba.
Halittar mace: 21Sai Ubangiji Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin. Lokacin da yake barci Ubangiji Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya cike wurin da nama, 22haƙarƙarin nan kuwa da Ubangiji Allah ya cire daga mutumin ya yi mace da shi, ya kuwa kawo ta ga mutumin. 23Sai mutumin ya ce, "Yanzu dai wannan ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne kuwa daga namana, za a kira ta mace, don daga cikin mutum aka ciro ta." 24Domin haka mutum yakan rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuwa manne wa matarsa, sun zama ɗaya. 25Da mutumin da matarsa dukansu biyu a tsiraice suke, ba su kuwa ji kunya ba.
Bayyani
An yi mutum daga turbayar ƙasa. Lumfashin da aka hura cikin hancinsa alamar rai ne. Rai yana kamar lumfashi, domin ba ya ganuwa. Ko an kashe mutum, ransa za ya rayu harabada, domin yana cikin surar Allah, yana da ilimi domin ya mallaki duniya. Dabbobi ba haka ba su ke.
Itacen rai shi ne im mutum ya ci 'ya'yansa ba za ya tsufa ba; idan ya dinga cin 'ya'yansa ba za ya mutu ba. Itacen sanin nagarta da mugunta shi ne wanda im mutum ya ci 'ya'yansa, za ya bi hanyoyin hsa'awarsa da duhun kai, ba za ya nemi hasken shawara wajen dokokin Allah ba. Idan mutum ba zai ci daga itacen sanin nagarta da mugunta ba, za ya dinga jin daɗin rai. Zai yi aiki, amma banda wahala.
Mutum ya ba dukan dabbobi sunaye. Wannan ne alama cewa yana da sarauta a kan su. Allah ya ba Adamu mace domin ya samu mataimaki mai dacewa da shi. Ya ce mutum za ya manne da matarsa, ba mata da yawa ba, amma ɗaya ce. A batun ayar nan, Yesu ya ce: "Ya zama fa daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne. Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba" (Mt 19:6; Mk 10:8-9). A lokacin nan ba sun ji kunyar tsirara ba, domin ba su yi zunubi tukuna ba, suna da hasken ganewa da ƙauna domin su yi mutuncin juna. Yanzu ana sa tufafi domin a bayyana mai girma a gaban mutane marasa ganewar girman zuciya.
Tambayoyi
- An yi mutum daga menene?
- Ko an kashe mutum, ransa me zai yi?
- Rayukan dabbobi za su rayu ban da aka yanka su?
- Menene itacen rai?
- Menene itacen sanin nagarta da mugunta?
- Cikin gonar Eden akwai aiki ga mutum?
- Cikin gonar Eden akwai wahala ko mutuwa ko rashin daɗi?
- Mutum ya ba da sunaye wa dabbobi kamar alamar yana da menene gare su?
- Don me Allah ya yi mace?
- Allah ya ba mutum na fari mata nawa?
- Yesu ya yarda a kashe aure?
- A farko miji da mace sun ji kunyar tsirara?
- Donme a kan ji kunyar tsirara yanzu?
DARASI NA UKU: FAƊOWA DA YARJEJENIYA
Karatu: Farawa 3:1-24
Zunubi: 1Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, "Ko Allah ya ce, 'Ba za ku ci daga wani itace da yake a gonar ba?'" 2Sai matar ta ce wa macijin, "Mā iya ci daga cikin itatuwan gonar, 3amma Allah ya ce, 'Ba za ku ci daga cikin 'ya'yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taɓa shi ba, don kada ku mutu.'"
4Amma macijin ya ce wa matar, "Hakika ba za ku mutu ba. 5Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta."
6Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci. 7Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa'an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.
Bincike: 8Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la'asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar. 9Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, "Ina kake?" 10Sai ya ce, "Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina." 11Ya ce, "Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?"
12Mutumin ya ce, "Matar nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci." 13Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, "Mene ne wannan da kika yi?" Matar ta ce, "Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci."
Foro: 14Ubangiji Allah ya ce wa maciji, "Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la'ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka. 15Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa." 16Ga matar kuwa ya ce, "Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki." 17Ga Adamu kuwa ya ce, "Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, 'Kada ka ci daga cikinsu.' Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka. 18"Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar. 19Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma." 20Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa'u, domin ita ce uwar 'yan adam. 21Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su. 22Sa'an nan Ubangiji Allah ya ce, "Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada." 23Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato, inda aka ɗauko shi. 24Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.
Bayyani
Maciji alamar Shaɗan ne ko aljan; duk ɗaya ne, watau mugunyar iska ke nan. Dā, Allah ya yi iskoko da yawa. Waɗansu masu kirki ne, kamar misali su mala'iku, waɗaanda su ke kawo saƙo daga wajen Allah. Amma waɗansu iskoki sun yi zunubi; aka kore su daga fuskar Allah. Sun ji ƙyashin mutumin wanda Allah ya mai da abokinsa maimakonsu. Sun yi ƙoƙari su sa mutum ya zama abokin gaba na Allah. Ba wanda ya iya tilasta wa mutum ya yi zunubi, domin yana da 'yancin nufi, amma maciji ya taushi mace, yana ɓoye muguntar abin da za ta yi, yana bayyana daɗinsa. Saboda mace ta yarda ta yi zunubi, ta faɗi cikin ion Shaiɗan, ta zama baiwarsa. Dominsa ta taushi mijinta ya yi zunubi kuma.
Irin zunubinsu shi ne girman kai. Sun ƙi shawarar Allah, suka so su ɗanɗana da kansu in kowane abu ya kamata ko ba ya kamata ba. Domin sun ƙi ganewa wadda Allah ya jiƙa masu, suka ci mutuncin juna, suka ji kunyar tsirararsu.
Allah yana yawo cikin gona da sanyin yamma kamar mutum mai gona da yana shan iska. Misali ke nan. Allah ba shi da ƙafofi domin ya taka, bu shi da jiki domin ya ji daɗin sanyin yamma, gama shi ruhu ne. Amma labarin Littafi Mai tsarki ya nuna yadda a zamanin dā Allah shi ne abokin mutum sosai. An iya yi kusa da shi da yin fira da shi.
Allah ya tambayi namiji da fari, domin yana da sarauta cikin iyali. Mutum ya sa laifi a kan mace, mace kuwa ta sa laifi a kan maciji. Allah ya la'anci maciji, sannan ya yi alkawalin zuwan mai ceto. Shi, ɗan mace ne, za ya karya ikon Shaiɗan. Macecin ɗin, shi ne Yesu Almasihu.
An yi wa mutum da mace foro kuma. Aikin haifuwa da na gona ba foro ba ne, amma wahala cikinsa foro ne. Mutuwa kuwa for na ƙarshe ke nan. Manzo Bulus ya ce: "Laifi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin laifi, har fa mutuwa ta bi kan kukan mutane, da shi ke duka sun yi laifi" (Rm 5:12). Saboda zunubin Adamu (sunan mutumin na fari ke nan), an haifi kowa da laifin haifua, ita ce rashin nufin daidai ga Allah tun daga habila.
Bayan da aka kore su Adamu da Hawa'u, an sa kerubim (ɗaya "kerub" ne) a ƙofa. Dā mutane sun yi surarsu irin da aka yi cikin hoton nan bisa. Amma surar da suka yi sai alama ce ta iskoko abokan Allah ne masu tsarewa.
Tambayoyi
- Maciji alamar menene?
- Kerubim alamar menene?
- Don me ba wanda ya iya tilasta wa mutum ya yi zunubi?
- Ina magana tafari ta maciji wa Hawa'u?
- Me mace ta amsa?
- Ina magana ta biyu ta maciji wa Hawa'u?
- Masu ƙin Allah ta wurin zunubi su ne bayin wanene?
- Wanene irin zunuban mutum da na mace na fari?
- Iyayemmu na fari suka ƙetare dokar Allah saboda muraɗin menene?
- Don me aka ce Allah yana yawo cikin gona da yanyin yamma, aka kuwa ji muryarsa?
- Allah ya yi magana da wanene da fari?
- Me Allah ya tambayi mutum?
- Me ya amsa?; sannan me Allah ya ce masa?; me mutum ya amsa?
- Me Hawa'u ta amsa wa Allah?
- Ta yaya Allah ya la'anci maciji?
- Wane alkawali Allah ya yi?
- Wanene ɗan mace da za ya ƙuje kan maciji?
- Ina foron mace?
- In foron mutum?
- Menene laifin haifuwa?
DARASI NA HUƊU: 'YA'YAN ADAMU
Karatu: Farawa 4:1-16
Aikin Kayinu da Habila: 1Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa'u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, "Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji." 2Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne. 3Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona. 4Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin 'ya'yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa, 5amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har ya kwantsare fuskarsa.
Kisan kai: Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har ya kwantsare fuskarsa. 6Ubangiji ya ce wa Kayinu, "Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har fuskarka ya kwantsare? 7In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi." 8Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa Habila, "Mu tafi cikin saura." A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan'uwansa Habila, har ya kashe shi.
Foro: 9Ubangiji ya ce wa Kayinu, "Ina Habila ɗan'uwanka?" Ya ce, "Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?" 10Sai Ubangiji ya ce, "Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa. 11Yanzu fa, kai la'ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka. 12In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya."
Ragewar foro: 13Kayinu ya ce wa Ubangiji, "Hukuncina ya fi ƙarfina. 14Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni." 15Sai Ubangiji ya ce masa, "Ba haka ba ne! Wanda duk ya kashe Kayinu, za a rama masa har sau bakwai." Ubangiji kuma ya sa wa Kayinu tabo, domin duk wanda ya iske shi kada ya kashe shi. 16Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya zauna a ƙasar Nod, gabashin Aidan.
Bayyani
Kayinu ya haifi 'ya'ya. Labari ya ci gaba a kan jikansa, Lamek ne:
Karatu: Farawa 4:23-24 a kanshi.
23Lamek kuwa ya ce wa matansa, "Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa, na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni. 24Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba'in da bakwai."
Bayyani
Saboda laifin haifuwa, mutum yana da sha'awar zunubi. Amma yana da 'yancin nufi domin ya ƙi. Allah ya ce wa Kayinu: "zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi." Gama mutum yana da iko a kan gurin zunubi, yana iya shugabantar shi.
Bayan da Kayinu ya kashe Habila, ya amsa wa Ubangiji: "Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?", watau: "Ina ruwanka? Ba shi da kunya. Kuma lokacin da Allah ya sa mashi foro, Kayinu ba ya nuna tuba ba, sai ya yi ƙaran alhakinsa. Amma da jinƙansa, Allah ya kiyaye shi, ya sa alama kamar tsaga a kan shi, domin mutane su ji tsoron ramar Allah idan su kashe shi.
Manzo Yohana ya ce: "Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna, 12kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne." (1 Yn 3:11-12).
Lamek ya bi mugun halin kakansa; ya ƙara ramar da ya yi wa abokin gabansa fiyad da na Kayinu. Ga abin da annabi Musa ya ce domin ya rage rama wadda mutanen dā suka yi: "23Lamek kuwa ya ce wa matansa, 'Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa, na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni. 24Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba'in da bakwai'" (Fitowa 21:23-25).
Yesu ya gyara shari'ar nan. Ya ce: "38"Kun dai ji an faɗa, 'Sakayyar ido, ido ce, sakayyar haƙori kuma haƙori ce.' 39Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma." (Mt 5:38-39). Ga wani abin da ya ce kuma: "21"Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, 'Kada ka yi kisankai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.' 22Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, 'Kai wofi!' Hakkinsa shiga Gidan Wuta." (Mt 18:21-22).
Tambayoyi
- Ina aikin Habila?
- Ina aikin Kayinu?
- Don me Kayinu ya kashi Habila?
- Ina gargaɗin da Allah ya yi wa Kayinu kamin da ya kashe Habila?
- Me Allah ya tambaye shi bayan da ya kashe Habila?
- Me Kayinu ya amsa?
- Ina foron da Allah ya yi mashi?
- Kayinu yana da kunya ko tuba cikin amsoyinsa?
- Me Allah ya yi don kada a kashi Kayinu?
- Sau nawa za a yi rama don Kayinu?
- Sau nawa za a yi rama don Lamek?
- Ina ramar da Musa ya ce a yi?
- Me Yesu ya ce a kan shari'ar Musa?
- Yesu ya ce za a gafarta sau nawa?
DARASI NA BIYAR: RUWAN TUFANA
Karatu: Farawa 5:1,3; 4:25; 6:1-2,5-8; 7:1-5,7,10,12,16b-17,22-23; 8:1-3a, 6-12,13b,20-22; 9:12-17
Haifuwar Set: 1A sa'ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah... 3Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu... 4:25Matarsa ta ce: "Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe."
Sauran zunubi: 6:1Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi 'ya'ya mata, 2sai 'ya'yan Allah suka ga 'yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura...
5Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin. 6Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya ɓata masa zuciya ƙwarai. 7Sai Ubangiji ya ce, "Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su." 8Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
Nuhu da jirgi: 7: 1Sai Ubangiji ya ce wa Nuhu, "Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni. 2Daga cikin dabbobi masu tsarki ka ɗauki bakwai bakwai, namiji da ta mace, marasa tsarki kuwa namiji da ta mace, 3da kuma tsuntsayen sararin sama bakwai bakwai, namiji da ta mace, domin a wanzar da irinsu a duniya duka. 4Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba'in da dare arba'in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya." 5Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
7Nuhu da 'ya'yansa da matarsa, da matan 'ya'yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana.
Zuwan ruwa: 10Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya... 12Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya yini arba'in da dare arba'in... 16Sai Ubangiji ya kulle jirgi daga baya. 17Aka yi ta kwararo ruwa bisa duniya har kwana arba'in, ruwayen kuwa suka ƙaru, har suka ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can ƙoli birbishin duniya...
22Kowane abu da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu. 23Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.
Ruwa ya rage: 8:1Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye. 2Maɓuɓɓugan zurfafa da tagogin sammai suka rufe, aka dakatar da ruwa daga sammai, 3ruwa ya yi ta janyewa daga duniya.
6A ƙarshen kwana arba'in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, 7sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya.
8Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye, 9amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi.
10Ya jira kuma har kwana bakwai, sai kuma ya sāke aiken kurciyar daga cikin jirgin. 11Kurciyar kuwa ta komo wurinsa da maraice, ga shi kuwa, a bakinta sabon tohon zaitun wanda ta tsinko, domin haka Nuhu ya gane ruwa ya janye daga duniya. 12Sai ya sāke dakatawa har kwana bakwai, ya kuma aiki kurciya, amma ba ta ƙara komowa wurinsa ba... 13 Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya.
Alkawali: 20Nuhu ya gina wa Ubangiji bagade, ya ɗiba daga cikin kowace irin dabba mai tsarki, da kowane tsuntsu mai tsarki, ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden. 21Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, "Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā. 22Muddin duniya tana nan, lokacin shuka da lokacin girbi, damuna da rani, yini da dare, ba za su daina ba."
Shaɗar alkawali: 12Allah ya ce, "Wannan ita ce alamar alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da yake tare da ku, har dukan zamanai masu zuwa, 13na sa bakana cikin girgije, ya zama alamar alkawari tsakanina da duniya. 14Sa'ad da na kawo gizagizai bisa duniya, aka ga bakan a cikin gizagizai, 15zan tuna da alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da dukan talikai. Ruwa kuma ba zai ƙara yin rigyawar da za ta hallaka talikai duka ba. 16Sa'ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da yake bisa duniya." 17Allah ya ce wa Nuhu, "Wannan ita ce alamar alkawari wanda na kafa tsakanina da dukan talikan da suke bisa duniya."
Bayyani
Set kamar ɗan Allah ne, domin yana cikin surar Adamu, wanda yana cikin surar Allah. Jikokinsa "'ya'yan Allah" ne, yawancinsun kuwa sun haɗu da 'ya'yan mutane, watau 'ya'yan Kayinu; sun bi al'adunsu marasa kyau. Saboda haka Allah ya ji fushinsu, ya kuwa hallaka duniya da ruwan tufana.A kan Nuhu aka ce: "Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya." (Ibr 11:7).
Bayan ruwan tufana, Allah ya yi alkawali da dukan mai rai, watau: mutum da "tsuntsaye, da dabbobin gida da na jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin, kowane mai rai na duniya" (9:10), ba za ya sake bugunsu daɗai. Dalilin alkawali shi ne domin foron irin wannan ba za ya gyara tunanin zuciyar mutum ba, gama tunanin zuciyarsa "mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa" (8:21). Sai a ƙarshen duniya Allah zai yi shari'ar masu rai da matattu. A lokacin nan, Yesu ya ce: "Ubanku wanda ke cikin sama ya kan sa rana tasa ta fito ma miyagu da nagargaru, yakan aiko da ruwa bisa masu adalci da marasa adalci" (Mt 5:45). Allah yana jimrewa domin ya ba mutane lokacin tuba.
Saboda jimrewar Allah, mutane da yawa suna zato ba zai yi shari'a ma masu zalunci da sauransu masu rena Allah ba. Amma manzo Bitrus (salama a gare shi) ya ce: "3Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba'a za su zo suna ba'a, suna biye wa muguwar sha'awarsu, 4suna cewa, "To, ina alkawarin dawowarsa? Ai, tun a lokacin da kakannin kakanninmu suka ƙaura, dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta." 5Da gangan suke goce wa maganar nan, cewa tun dā dā ta wurin maganar Allah sammai suka kasance, aka kuma siffata ƙasa daga ruwa, tana kuma a tsakiyar ruwa. 6Ta haka ne kuma, duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta hallaka. 7Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari'a, a hallaka su." (2 Bit 3:3-7).
Allah ya yi shaidar alkawalinsa da bakan gizo. Domin ku gane ma'anar bakan gizo, za ku fahimci ruwan tufana kamar yaƙin Allah da mutane ne. Walƙiyoyi suna kamar kibiyoyin da suka buɗe gizagizai domin ruwa ya faɗo ya rufe ƙasa. Bakan gizo kamar kayan yaƙi na Allah ne. Idan ka sa kibiya a tsirkiyarsa, kibiya ba ta miƙo wa duniya, amma wa sama. Watau, Allah ya ajiyi bakansa; ba za ya sake yin amfaninsa domin ya hallaka dukan duniya ba. Saboda haka, bakan gizo alamar salama ne.
Tambayoyi
- Ina sunan ɗa na uku na Adamu?
- Su wanene "'ya'yan Alla" da "'ya'yan mutane" cikin wannan labari?
- Don me Allah ya ji fushin 'ya'yan Allah da 'ya'yan mutane?
- Nuhu jikan wanene?
- Me Nuhu ya kawo tare da shi cikin jirgi?
- Ruwaye suna yawaita kwana nawa?
- Ruwaye suna ja da baya kwana nawa har Nuhu ya saki hankaka?
- Me hankaka ya yi?
- Me kuruciya ta yi sau na fari da ta fita?
- Me ta yi sau na biyu?
- Me ta yi sau na uku?
- Me Nuhu ya yi bayan da ya fito daga jirgi?
- Allah ya yi alkawalinsa da wanene?
- Don me Allah ba za ya sake bugun ƙasa yadda ya rigaya ya yi?
- Ina amfanin jimrewarsa ga mutane?
- Ina shaidar alkawalin Allah?
- Ina ma'anar wannan shaida?
- Yaushe za a yi hukuncin ba'ar dukan mutane?
DARASI NA SHIDDA: IBRAHIM
Bayyani
'Ya'yan Nuhu sun watsu cikin dukan duniya, har bayan tsararaki da yawa yawancinsu sun bar hanyar Allah. Allah ya sani ba zai gyara mutane ta wurin hallakansu ba. To, ya bi wata hanya. Ya zaɓi mutum ɗaya domin ta wurinsa ya kafa jama'a mai kusantar Allah. Daga kowane kabilin duniya za ya kira mutane zuwa tarayyar yarjejeniyarsa cikin jama'arsa.
Mutumin da Allah ya zaɓa, shi ne Ibrahim, wnada dā aka kira shi Abram, kamar sunan wasa. Ga labarin Ibrahim:
Karatu: Farawa 11:27 - 12:8
Asalin Ibrahim: 27Yanzu dai waɗannan su ne zuriyar Tera, Tera ya haifi Abram, da Nahor, da Haran, Haran kuwa shi ne ya haifi Lutu. 28Haran kuwa ya rasu a idon mahaifinsa Tera a ƙasar haihuwarsa, a Ur ta Kaldiyawa. 29Da Abram da Nahor suka yi aure, sunan matar Abram Saraya, sunan matar Nahor kuwa Milka, ita 'yar Haran ce, mahaifin Milka da Iskaya. 30Saraya kuwa ba ta haihuwa, wato, ba ta da ɗa. 31Sai Tera ya ɗauki ɗansa Abram da Lutu ɗan Haran, jikansa, da Saraya surukarsa, wato, matar ɗansa Abram, suka tafi tare, daga Ur ta Kaldiyawa zuwa ƙasar Kan'ana, amma da suka isa Haran, suka zauna a can. 32Kwanakin Tera shekara ce metan da biyar, Tera kuwa ya rasu a Haran.
Yarjejeniya da Ibrahim: 12:1Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Abram, "Ka fita daga ƙasarka, da danginka, da gidan mahaifinka zuwa ƙasar da zan nuna maka. 2Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka. 3Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka." 4Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba'in da biyar sa'ad da ya yi ƙaura daga Haran. 5Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan'uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran. Sa'ad da suka kai ƙasar Kan'ana, 6Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan'aniyawa suke a ƙasar. 7Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, "Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa." Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi. 8Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji.
Bayyani
Cikin yarjejeniyar nan bisa, aka ambaci abuwua uku, watau:
al'umma mai girma za ya zama daga wajen zuriyar Ibrahim za su gaje ƙasar Kan'anan saboda Ibrahim albarka za ta kasance a kan dukan duniya. Allah kuma ya ce a kan yarjejeniyar:
Karatu: Farawa 17:11-13
Shaidar yarjejeniya: 11Loɓarku za ku yanke, don alamar alkawari a tsakanina da ku. 12Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan tsararrakinku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba. 13Duka biyu, da wanda aka haifa daga gidanka, da wanda ka saya da kuɗi, za a yi musu kaciya. Da haka alkawarina zai kasance cikin jikinku, madawwamin alkawari ke nan.
Bayyani
Ga kuma shekaru da yawa suka wuce bayan da Allah ya yi yarjejeniyarsa da Ibrahim. Ibrahim yana shakka Allah ba zai ba shi ɗa ba. Ga labari:
Karatu: Farawa 15:1-5 An sake yin yarjejeniya
1Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, "Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa." 2Amma Abram ya ce, "Ya Ubangiji Allahna, me za ka ba ni, ga shi kuwa, ba ni da ɗa? Ko kuwa Eliyezer na Dimashƙu ne zai gāje ni?" 3Abram kuma ya ce, "Ga shi, ba ka ba ni zuriya ba, ga shi ma wani yaron gidana ne zai gāje ni." 4Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, "Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka." 5Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, "Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su." Sai kuma ya ce masa, "Haka zuriyarka za ta zama."
Bayyani
Saratu, matar Ibrahim, tana shakka ba za ta sami ɗa ba. Ga labarinta:
Karatu: Farawa 16:1-12 Saratu da Hajaratu
1Saraya matar Abram ba ta taɓa haihuwa ba, amma tana da baranya Bamasariya, sunanta Hajaratu. 2Sai Saraya ta ce wa Abram, "To, ga shi, Ubangiji ya hana mini haihuwar 'ya'ya. Shiga wurin baranyata, mai yiwuwa ne in sami 'ya'ya daga gare ta." Abram kuwa ya saurari murya matarsa Saraya. 3A lokacin nan kuwa Abram yana da shekara goma da zama a ƙasar Kan'ana sa'ad da Saraya matar Abram ta ɗauki Hajaratu Bamasariya, baranyarta, ta bai wa Abram mijinta ta zama matarsa. 4Abram kuwa ya shiga wurin Hajaratu, ta kuwa yi ciki. Da ta ga ta sami ciki sai ta dubi uwargijiyarta a raine. 5Sai Saraya ta ce wa Abram, "Bari cutar da aka cuce ni da ita ta koma kanka! Na ba da baranyata a ƙirjinka, amma da ta ga ta sami ciki, sai tana dubana a raine. Ubangiji ya shara'anta tsakanina da kai."
6Amma Abram ya ce wa Saraya, "Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita." Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta.
7Mala'ikan Ubangiji kuwa ya sami Hajaratu a gefen wata maɓuɓɓugar ruwa a jeji, wato, maɓuɓɓugar da take kan hanyar Shur. 8Sai ya ce, "Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?" Ta ce, "Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya."
9Mala'ikan Ubangiji ya ce mata, "Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi." 10Mala'ikan Ubangiji kuma ya ce mata, "Zan riɓaɓɓanya zuriyarki ainun har da ba za a iya lasafta su ba saboda yawansu." 11Mala'ikan Ubangiji kuma ya ƙara ce mata,
"Ga shi, kina da ciki, za ki haifi ɗa, za ki kira sunansa Isma'ilu, domin Ubangiji ya lura da wahalarki. 12Zai zama mutum ne mai halin jakin jeji, hannunsa zai yi gāba da kowane mutum, hannun kowane mutum kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zaman magabtaka tsakaninsa da 'yan'uwansa duka." Bayyani
Cikin labarin nan bisa, bangaskiyar Ibrahim ba ta tabbata sosai ba, to ya ji muryar matarsa ya yi mugu, ya shiga wurin kuyangar matarsa. Ibrahim da matarsa sai suka ji wahala saboda laifinsu. Amma Allah ya sake jinƙansu. Ga labari:
Karatu: Farawa 17:4-5,15-21; 21:1-5
Da sakewar suna, an sake yin Alkawali: Allah y ace wa Ibrahim: 4"Wannan shi ne alkawarin da zan yi maka, za ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa. 5Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al'ummai masu ɗumbun yawa...
15Allah ya ce wa Ibrahim, "Ga zancen matarka Saraya, ba za ka kira sunanta Saraya ba, amma Saratu ne sunanta. 16Zan sa mata albarka, banda haka kuma zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za ta kuwa zama mahaifiyar al'ummai, sarakunan jama'a za su fito daga gare ta."
17Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, "Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?" 18Sai Ibrahim ya ce wa Allah, "Da ma dai a bar Isma'ilu kawai ya rayu a gabanka."
19Allah ya ce, "A'a, matarka Saratu ita ce za ta haifa maka ɗa, za ka raɗa masa suna Ishaku. A gare shi zan tsai da alkawarina madawwami, da kuma ga zuriyarsa a bayansa. 20Ga zancen Isma'ilu kuwa, na ji, ga shi, zan sa masa albarka in kuma riɓaɓɓanya shi ainun. Zai zama mahaifin 'ya'yan sarakuna goma sha biyu, zan maishe shi al'umma mai girma. 21Amma ga Ishaku ne zan tsai da alkawarina, wato, wanda Saratu za ta haifa maka a baɗi war haka."
Haifuwar Isiyaku 21:1Ubangiji ya yi wa Saratu alheri kamar yadda ya alkawarta. 2Saratu kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Ibrahim ɗa cikin tsufansa a lokacin nan da Allah ya faɗa masa. 3Sai Ibrahim ya raɗa wa ɗansa wanda Saratu ta haifa masa, suna, Ishaku. 4Ibrahim ya yi wa Ishaku ɗansa kaciya yana da kwana takwas, kamar yadda Allah ya umarce shi. 5Ibrahim kuwa yana da shekara ɗari sa'ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.
Bayyani
An yi shekaru asharin da biyar bayan da aka yi yarjejeniya da Ibrahim, sai Allah ya fara cika ta ta wurin haifuwar Isiyaku. Dā, bangaskiyar Ibrahim ta yi talalaɓuwa, lokacin da yana shakka ta yarjejeniyar Allah. Ga yadda bangaskiyarsa ta zama cikakkiya:
Karatu: Farawa 22:1-18
1Bayan waɗannan al'amura Allah ya jarraba Ibrahim ya ce masa, "Ibrahim!" Sai ya ce, "Ga ni."
2Ya ce, "Ɗauki ɗanka, tilon ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi ƙasar Moriya, a can za ka miƙa shi hadayar ƙonawa a bisa kan ɗayan duwatsun da zan faɗa maka."
3Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa. 4A rana ta uku Ibrahim ya ta da idanunsa ya hangi wurin daga nesa. 5Ibrahim ya ce wa samarinsa, "Ku tsaya nan wurin jakin, ni da saurayin za mu yi gaba mu yi sujada, sa'an nan mu komo wurinku."
6Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare. 7Ishaku ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, "Baba!" Sai ya ce, "Ga ni, ɗana." Ya ce, "Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar ƙonawa?"
8Ibrahim ya ce, "Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana." Sai su biyu suka tafi tare.
9Sa'ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden. 10Sai Ibrahim ya miƙa hannu ya ɗauki wuƙar don ya yanka ɗansa. 11Amma mala'ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, "Ibrahim, Ibrahim!" Sai ya ce, "Ga ni."
12Ya ce, "Kada ka sa hannunka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ƙi ba da ɗanka, tilonka, a gare ni ba." 13Ibrahim ya ta da idanunsa, ya duba, ga rago kuwa a bayansa, da ƙahoni a sarƙafe cikin kurmi. Ibrahim kuwa ya tafi ya kamo ragon, ya miƙa shi hadayar ƙonawa maimakon ɗansa. 14Sai Ibrahim ya sa wa wurin suna, "Ubangiji zai tanada," kamar yadda ake faɗa har yau, "A bisa kan dutsen Ubangiji, za a tanada."
15Mala'ikan Ubangiji kuma ya sāke kiran Ibrahim, kira na biyu daga sama, 16ya ce, "Na riga na rantse da zatina, tun da ka yi wannan, ba ka kuwa ƙi ba da tilon ɗanka ba, 17hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka, 18ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina."
Bayyani
Saboda aikinsa na biyayya, aka ce da Ibrahim: "Ya ba dagaskiya ga Ubangiji, shi kuma lissafta wannan adalci ne gare shi" (Farawa 15:6). Ga yadda a ke yabonshi cikin Sabon Alkawali:
Karatu: Romawa 4:16-25: 16Saboda haka al'amarin ya dogara ga bangaskiya, domin ya zama bisa ga alheri, don kuma a tabbatar da alkawarin nan ga dukkan zuriyar Ibrahim, ba ga masu bin Shari'a kaɗai a cikinsu ba, har ma ga waɗanda suke da bangaskiya irin Ibrahim, shi da yake ubanmu duka. 17Kamar yadda yake a rubuce cewa, "Na sa ka uban al'ummai da yawa." Shi ne kuwa ubanmu a gaban Allah, wannan da ya gaskata, wato mai raya matattu, shi ne kuma mai kiran marasa kasancewa kamar sun kasance. 18Ibrahim kuwa ko da yake ba halin sa zuciya a gare shi, sai ya yi ta sawa, ya gaskata zai zama uban al'ummai da yawa, kamar yadda aka faɗa masa cewa, "Haka zuriyarka za ta yawaita." 19Bangaskiyarsa kuwa ba ta raunana ba, bai dubi gajiyawar jikinsa ba, don yana da shekara wajen ɗari a lokacin, ko kuma cewa Saratu ta wuce haihuwa. 20Ba kuwa wata rashin bangaskiyar da ta sa shi shakkar cikar alkawarin Allah, sai ma ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa ya yi, yana ɗaukaka Allah, 21yana haƙƙaƙewa, cewa Allah na da ikon yin abin da ya yi alkawari. 22Shi ya sa aka lasafta bangaskiyarsa adalci ce a gare shi. 23To, "Lasafta masa" ɗin nan da aka rubuta kuwa, ba saboda Ibrahim kaɗai aka rubuta ba, 24har saboda mu ma, za a lasafta mana, wato mu da muke gaskatawa da wannan da ya ta da Yesu Ubangijinmu daga matattu, 25wanda aka bayar a kashe saboda laifofinmu, aka kuma tashe shi, domin mu sami kuɓuta ga Allah.
Karanta Wasika zuwa ga Ibraniyawa 11:8-12,17-19: 8Ta wurin bangaskiya Ibrahim ya yi biyayya, sa'ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasa da zai karɓa gādo. Ya kuwa fita, bai ma san inda za shi ba. 9Ta wurin bangaskiya kuma ya yi baƙunci a ƙasar alkawari, kamar dai a ƙasar bare, suna zaune a cikin alfarwai, shi da Ishaku da Yakubu, abokan tarayya ga gādon alkawarin nan. 10Yana ta jiran birnin nan mai tushe, wanda mai fasalta shi, mai gina shi kuma, Allah ne. 11Ta wurin bangaskiya Saratu da kanta ta sami ikon yin ciki, ko da yake ta wuce lokacin haihuwa, tun da dai ta amince, cewa shi mai yin alkawarin nan amintacce ne. 12Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, aka haifi zuriya masu yawa kamar taurari, kamar yashi kuma dangam a bakin teku... 17Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa'ad da aka gwada shi, ya miƙa Ishaku hadaya, wato shi da ya yi na'am da alkawaran nan, ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa, 18wanda a kansa aka yi faɗi cewa, "Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka." 19Ya amince da cewa, ko daga matattu Allah yana da iko ya ta da mutum. Ai kuwa, bisa ga misali, sai a ce daga matattu ne ya sāke samun Ishaku.
Tambayoyi
- Ina ƙasar haifuwar Ibrahim?
- Ina sunan wasa na Ibrahim?
- Ina sunan wasa na Saratu?
- Allah ya yi da Ibrahim yarjejeniya a kan waɗanne abubuwa uku?
- Ina shaidar yarjejeniyar da Allah ya ce Ibrahim shi yi?
- Bayan da Allah ya yi jinkiri wajen ban Ibrahim ɗa, Ibrahim ya tsamani wanene zai gaje gidansa?
- Me Saratu ta ce Ibrahim shi yi?
- Allah ya shawarta Ibrahim ya ɗauki Hajaratu?
- Allah ya yarda ya kore ta?
- Allah ya kulla da yaro Isma'ilu?
- Lokacin da Allah ya ce Saratua za ta haifi ɗa, me Ibrahim ya yi?
- Ina sunan ɗan Saratu?
- Ibrahim yana da shekaru nawa lokacin da Allah ya yi masa yarjejeniya?
- Ibrahim yana da shekaru nawa lokacin da aka haifa masa Isiyaku?
- Ta yaya Allah ya gwada bangaskiyar Ibrahim?
DARASI NA BAKWAI: 'YA'YAN IBRAHIM
Bayyani
Allah yayi yarjejeyiyarsa da Isiyaku duk ɗaya ne kamr yadda ya yi da Ibrahim. Ga labari:
Karatu: Farawa 26:1-6 Yarjejeniyar da Isiyaku:
1Aka sāke yin yunwa a ƙasar, banda wadda aka yi a zamanin Ibrahim. Sai Ishaku ya tafi Gerar wurin Abimelek, Sarkin Filistiyawa. 2Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, "Kada ka gangara zuwa Masar, ka zauna a ƙasar da zan faɗa maka. 3Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka. 4Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka, 5saboda Ibrahim ya yi biyayya da muryata, ya kuma kiyaye umarnina, da dokokina, da ka'idodina, da shari'una." 6Ishaku ya yi zamansa a Gerar.
Bayyani
Cikin labarin nan bisa, Allah ya alkawalta abubuwa uku du ɗaya ne kamar yadda ya rigaya ya alkawalta da Ibrahim. An gwada bangaskiyar Isiyaku kuma, domin ya bi umurnin Allah za zama cikin ƙasarsa, ba ya gudu Masar saboda yunwa ba.
Isiyaku ya yi auren Rifkau, wadda ta haifi tagwaye. Sunan na fari Isuwa ne, amma Allah yazaɓ ƙanensa Yakubu don ya gaje yarjejeniyar. Ya ce masa:
Karatu: Farawa 28:13-15 Yarjejeniya da Yakubu:
13Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, "Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka. 14Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka. 15Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasar nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka."
Bayyani
Yakubu, wanda Allah ya ba shi sunan Isra'ila, yana da 'ya'ya maza goma sha biyu. Daga cikinsu, ya fi son Yusufu, amma Allah ya sa ya zaɓi Yahuda don ya gaji yarjejeniyar. A lokacin da yana yi kusa mutuwa, ya albarkaci Yahuda. Da fari, ya ambaci ƙarfi da iko na Yahuda:
Karatu: Farawa 49:8-10 Albarkar Yahuda:
8"Yahuza, 'yan'uwanka za su yabe ka, Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka, 'Yan'uwanka za su rusuna a gabanka. 9Yahuza ɗan zaki ne, Ya kashe ganima sa'an nan ya komo wurin ɓuyarsa. Yahuza kamar zaki yake, Yakan kwanta a miƙe, Ba mai ƙarfin halin da zai tsokane shi. 10Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i. Bayyani
Wannan annabci yana yin alkawalin sarauta ga iyalin Yahuda. Da gaske, sarauta ba ta za ba sai bayan shekaru ɗari bakwai, lokacin da Daudu ya zama sarki (shekara dubu kamin Almasihu). Kuma bayan shekaru ɗari huɗu da sha uku (587 amin Almasihu), Babilawa sun kama sarautar Yahudawa.
Sarautar sarakunan Yahudawa sai misalin sarautar Yesu Almasihu ne. Cikin annabcin Yakubu, Yesu Almasihu shi ne wanda kandiri da sandar mulki nasa ne har abada. Sarautarsa ba irin ta sarakunan wannan duniya ce ba, amma mutane suna yi masa biyayya ta wurin bangaskiya da bin dokokin Allah.
Yakubu ya ci gaba cikin annabcinsa, yana ambatan arzikin mulkin Almasihu:
Karatu: Farawa 49:11-12 Sauran albarkar Yahuda:
11Zai ɗaure aholakinsa a kurangar inabi, A kuranga mafi kyau, Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi, Ruwan inabi ja wur kamar jini. 12Idanunsa za su yi ja wur saboda shan ruwan inabi, Haƙoransa kuma su yi fari fat saboda shan madara. Bayyani
Za ya ɗaure jakinsa ga kuringar anab domin 'ya'yanta sun yi yawa ƙwarai da gaske. Ba kome idan jaki za ya ci su har ya ƙoshi. Anabuna ba za su kasa ba, domin babu ƙarshen arzikin gonar anab tasa. Kamar misali, idan mutum ya bar jakai da awaki su ci cikin filinsa na rogo, saboda yawansu, yana da arziki sosai.
Ruwan anab irin giya ne. Za ya yi yawa sosai idan mai shi ya iya wanke cikinsa, watau idan baya damu ko ya ɓada kaɗan saboda wankewa ba, domin akwai sauran da yawa. Idanunsa za su zama ja domin ya sha da yawa.
Yakubu ya faɗi wannan labarin arziki kamar misalign arzikin mulkin sama, wanda Allah zai ba mutane lokacin zuwan Almasihu.
Tambayoyi
- Ina abubuwa uku da Allah ya alkawalta wa Ishaku da Yakubu?
- Yadda aka gwada bangaskiyar Ishaku?
- Yakubu yana da 'ya'ya maza nawa?
- Wanene daga cikinsu ya sami albarkar babansa?
- Yakubu ya yi annabcin wane mai sarauta mai arziki?
- Wane irin saruta ke nan?
- Wane irin arziki ke nan?
DARASI NA TAKWAS: MUSA DA ƊAN RAGO
Bayyani
Yusufu, ɗan Yakubu, ya zama babban mutum cikin Masar. To, lokacin da yunwa ta faru cikin Kan'ana, Yakubu da iyalinsa suka tafi Masar don taimako. Ga labarinsu a can:
Karatu: Fitowa 1:1-2:22; 3:1-15
Iyalin Yakubu: 1Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, waɗanda suka tafi Masar tare da Yakubu, kowanne da iyalinsa. 2Su ne Ra'ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, 3da Issaka, da Zabaluna, da Biliyaminu, 4da Dan, da Naftali, da Gad, da Ashiru. 5Zuriyar Yakubu duka mutum saba'in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar. 6Ana nan sai Yusufu ya rasu, shi da dukan 'yan'uwansa na wannan tsara. 7Amma 'ya'yan Isra'ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.
Wulakancin 'Yan Isra'ila: 8A wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a Masar wanda bai san Yusufu ba. 9Sai ya ce wa mutanensa, "Duba, jama'ar Isra'ila sun cika yawa sun fi ƙarfinmu. 10Zo, mu san irin dabarar da za mu yi musu, don kada su riɓaɓɓanya, domin in aka faɗa mana da yaƙi, kada su haɗa kai da maƙiyanmu, su yaƙe mu, su tsere daga ƙasar." 11Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato, Fitom da Ramases. 12Amma ko da yake Masarawa sun ƙara tsananta musu, duk da haka sai suka ƙara ƙaruwa, suna ta yaɗuwa. Masarawa kuwa suka tsorata saboda Isra'ilawa. 13Suka kuma tilasta wa Isra'ilawa su yi ta aiki mai tsanani. 14Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu.
15Sarkin Masar ya ce wa ungozomar Ibraniyawa, Shifra da Fu'a, 16"Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai." 17Amma da yake ungozomar masu tsoron Allah ne, ba su yi yadda Sarkin Masar ya umarce su ba, amma suka bar 'ya'ya maza da rai. 18Don haka Sarkin Masar ya kirawo ungozomar, ya ce musu, "Me ya sa kuka bar 'ya'ya maza da rai?"
19Ungozomar suka ce wa Fir'auna, "Domin matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gama su masu ƙwazo ne, sukan haihu tun ungozomar ba su kai wurinsu ba." 20Allah kuwa ya yi wa ungozomar nan alheri. Mutanen suka riɓanya, suka ƙasaita ƙwarai. 21Allah kuma ya ba ungozomar nan zuriya domin sun ji tsoronsa.
22Fir'auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, "Duk jaririn da aka haifa wa Ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin Kogin Nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai."
Haifuwar Musa: 2:1Sai wani mutum, Balawe, ya auro 'yar Lawi. 2Matar kuwa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Sa'ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har wata uku. 3Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu. 4Ga 'yar'uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.
5Gimbiya, wato, 'yar Fir'auna, ta gangaro don ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta 'yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi. 6Sa'ad da ta tuɗe kwandon ta ga jariri yana kuka. Sai ta ji tausayinsa, ta ce, "Wannan ɗaya daga cikin 'ya'yan Ibraniyawa ne."
7'Yar'uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, "In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?"
8Sai Gimbiya ta ce mata, "Je ki." Yarinyar kuwa ta tafi ta kirawo mahaifiyar jaririn. 9Da ta zo, sai Gimbiya ta ce mata, "Dauki wannan jariri, ki yi mini renonsa, zan biya ki ladanki." Matar kuwa ta ɗauki jaririn ta yi renonsa. 10Da jaririn ya yi girma sai ta kai shi wurin Gimbiyar. Yaro kuwa ya zama tallafinta. Ta raɗa masa suna Musa, gama ta ce, "Domin na tsamo shi daga cikin ruwa."
Musa ya gudu: 11Ana nan wata rana, sa'ad da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa, sai ya ga yadda suke shan wahala. Ya kuma ga wani Bamasare yana d�kan Ba'ibrane, ɗaya daga cikin 'yan'uwansa. 12Da ya waiwaya, bai ga kowa ba, sai ya kashe Bamasaren, ya turbuɗe shi cikin yashi. 13Kashegari da ya sāke fita, sai ya ga waɗansu Ibraniyawa biyu suna faɗa da juna. Ya ce wa wanda yake ƙwaran ɗan'uwansa, "Me ya sa kake bugun ɗan'uwanka?"
14Ya amsa, ya ce, "Wa ya naɗa ka sarki ko alƙali a bisanmu? So kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren?" Sai Musa ya tsorata, ya ce, "Assha, ashe, an san al'amarin!" 15Da Fir'auna ya ji, sai ya nema ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu daga gaban Fir'auna, ya tafi, ya zauna a ƙasar Madayana. Da ya kai, sai ya zauna a bakin wata rijiya.
Musa ya yi aure: 16Ana nan waɗansu 'yan mata bakwai, 'ya'yan firist na Madayana suka zo su cika komaye da ruwa don su shayar da garken mahaifinsu. 17Sai makiyaya suka zo, suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su, ya kuma shayar da garkensu. 18Lokacin da suka koma wurin mahaifinsu, Reyuwel, wato, Yetro, ya ce musu, "Yaya aka yi yau, kuka komo da sauri haka?"
19Sai suka ce, "Wani Bamasare ne ya cece mu daga hannun makiyaya, har ya ɗebo ruwa, ya shayar da garkenmu."
20Reyuwel kuwa ya ce wa 'ya'yansa mata, "A ina yake? Me ya sa ba ku zo da shi ba? Ku kirawo shi, ya zo, ya ci abinci."
21Musa kuwa ya yarda ya zauna tare da Reyuwel. Sai ya aurar wa Musa da 'yarsa Ziffora. 22Ita kuwa ta haifa masa ɗa, ya raɗa masa suna Gershom, gama ya ce, "Baƙo ne ni, a baƙuwar ƙasa."
Kurmi mai cin wuta: 31Wata rana, sa'ad da Musa yake kiwon garken surukinsa, Yetro, firist na Madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo Horeb, wato, dutsen Allah. 2A can mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba. 3Musa kuwa ya ce, "Bari in ratse, in ga wannan abin banmamaki da ya sa kurmin bai ƙone ba."
4Sa'ad da Ubangiji ya ga ya ratse don ya duba, sai Allah ya kira shi daga cikin kurmin, ya ce, "Musa, Musa." Musa ya ce, "Ga ni." 5Allah kuwa ya ce, "Kada ka matso kusa, ka cire takalminka, gama wurin da kake tsaye, tsattsarka ne." 6Ya kuma ce, "Ni ne Allah na kakanninka, wato, Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu." Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah.
An aiki Musa: 7Ubangiji kuwa ya ce, "Na ga wahalar jama'ata waɗanda suke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu, 8don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato, ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. 9Yanzu fa, ga shi, kukan jama'ar Isra'ila ya zo gare ni. Na kuma ga wahalar da Masarawa suke ba su. 10Zo, in aike ka wurin Fir'auna domin ka fito da jama'ata, wato, Isra'ilawa, daga cikin Masar."
11Amma Musa ya ce wa Allah, "Wane ni in tafi gaban Fir'auna in fito da Isra'ilawa daga cikin Masar?"
12Sai Allah ya ce, "Zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa, ni ne na aike ka. Sa'ad da ka fito da jama'ar daga Masar, za ku bauta wa Allah a bisa dutsen nan."
Sunan Ubangiji: 13Sai Musa ya ce wa Allah, "Idan na je wurin Isra'ilawa na ce musu, 'Allah na ubanninku ya aiko ni gare ku,' idan sun ce mini, 'Yaya sunansa?' Me zan faɗa musu?"
14Allah kuwa ya ce wa Musa, "NI INA NAN YADDA NAKE," ya kuma ce, "Haka za ka faɗa wa Isra'ilawa, 'NI NE ya aiko ni gare ku.'" 15Allah kuma ya sāke ce wa Musa, "Faɗa wa Isra'ilawa cewa, 'Ubangiji Allah na kakanninku, wato, na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.' Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai.
Bayyani
Allah ya bayyana sunansa cikin harshen Libranci: "Yahweh" ne, watau NI NE, wanda ba wanda an yi ni, ni kuma na sa kome ya zama. Yahudawa suna da yawan ladabi ga wannan suna, ba su kan ambatarshi, suna karatu "Ubangiji" ko "Sunan" maimakon "Yahweh". Cikin Hausa, a kan ce "Ubangiji", domin mutane masu yawa ba za su gane "Yaweh" ba.
Karatu: Fitowa 4:10-16; 5:1-9,19-6:1
Haruna ya zama marƙin Musa: 10Amma Musa ya ce wa Ubangiji, "Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma."
11Ubangiji kuwa ya ce masa, "Wa ya yi bakin ɗan adam? Wa ya yi bebe ko kurma, ko mai gani ko makaho? Ko ba ni Ubangiji ba ne? 12Yanzu fa, tafi, zan kasance tare da bakinka, in koya maka abin da za ka faɗa."
13Amma Musa ya ce, "Ya Ubangijina, in ka yarda, ka aiki wani."
14Ubangiji kuwa ya hasala da Musa, ya ce, "Haruna ɗan'uwanka Balawe ba ya nan ne? Lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. Sa'ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa. 15Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi. 16Shi zai yi maka magana da jama'a, zai zama bakinka, kai kuwa za ka zama kamar Allah a gare shi.
Magana da Fir'auna: 1Bayan wannan Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna, suka ce, "Ga abin da Ubangjiji Allah na Isra'ila ya ce, 'Bar jama'ata su tafi domin su yi mini idi cikin jeji.'"
2Amma Fir'auna ya ce, "Wane ne Ubangiji, har da zan ji maganarsa, in bar Isra'ilawa su tafi? Ai, ban san Ubangiji ɗin nan ba, balle in bar Isra'ilawa su tafi."
3Sai suka ce, "Allahn Ibraniyawa ya gamu da mu, muna roƙonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa Ubangiji Allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi."
4Amma Sarkin Masar ya ce wa Musa da Haruna, "Me ya sa kuke hana jama'ar yin aikinsu? Ku tafi wurin aikin gandunku." 5Ya kuwa ci gaba ya ce, "Ga jama'ar ƙasar sun yi yawa, yanzu kuna so ku hana su yin aikinsu."
Fir'auna ya ƙara aikin Ibraniyawa: 6A ran nan fa Fir'auna ya umarci shugbannin aikin gandu da manyan jama'a, ya ce, 7"Nan gaba kada ku ƙara ba mutanen nan budu na yin tubali kamar dā. Ku sa su, su tafi, su tara budu da kansu. 8Duk da haka, kada su kāsa cika yawan tubalin da aka ƙayyade musu da fari. Ai, su ragwaye ne, shi ya sa suke kuka, suna cewa, 'A bar mu, mu tafi mu miƙa wa Allahnmu hadaya.' 9Ku sa mutanen su yi aiki mai tsanani har da ba za su sami damar kasa kunne ga maganganun ƙarya ba."
Manyan Isra'ila zun zarge Musa da Haruna: 19Manyan Isra'ilawa suka ga lalle sun shiga uku, da yake aka ce dole su cika yawan tubali da aka yanka musu kowace rana. 20Da suka fita daga gaban Fir'auna, sai suka sadu da Musa da Haruna, suna jiransu. 21Suka ce wa Musa da Haruna, "Allah ya duba, ya hukunta ku, gama kun sa mun yi baƙin jini a wurin Fir'auna da barorinsa, har suka ɗauki takobi don su kashe mu."
22Sai Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, "Ya Ubangijina, me ya sa ka jawo wa wannan jama'a masifa? Me ya sa ka aike ni? 23Gama tun da na tafi wurin Fir'auna, na yi masa magana da sunanka, ya mugunta wa wannan jama'a, kai kuwa ba ka ceci jama'arka ba ko kaɗan!"
6:1Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, "Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir'auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!"
Bayyani
Bayan da Fir'auna ya ƙi Ibraniyawa su tafi, Allah ya yi ma ƙasarsa foro da yawa. Bayan kowane foro, Fir'auna ya ce zai ƙyale su su tafi, amma bayan kaɗan ya sake hana su. Sai Allah ya shirya mutanensa don ranar dab a shakka za su tafi:
Karatu: Fitowa 12:1-14, 29-33, 40-41
Idin Ƙetere: 1Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna cikin ƙasar Masar, 2wannan wata zai zama wata na farko a shekara a gare su. 3A faɗa wa dukan taron Isra'ilawa cewa, "A rana ta goma ga watan nan, kowane namiji ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya daga cikin garke domin iyalinsa, dabba ɗaya domin kowane gida. 4Idan da wanda iyalinsa ba za su iya cinye dabba guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki dabba guda gwargwadon yawansu. 5Tilas ne dabbar ta kasance lafiyayyiya ƙalau, bana ɗaya. Za ku kamo daga cikin tumakinku ko awaki. 6Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato, sa'ad da dukan taron jama'ar Isra'ila za su yanka ragunansu da maraice. 7Sa'an nan ku ɗibi jinin, ku sa a dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar gidajen da za a ci naman dabbobin. 8A daren nan za ku gasa naman, ku ci da abinci marar yisti, da ganyaye masu ɗaci. 9Kada ku ci shi ɗanye ko daffaffe da ruwa, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kayan cikin. 10Kada ku bar kome ya kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi. 11Ga yadda za ku ci shi, da ɗamara a gindinku, da takalma a ƙafafunku, da sanda a hannunku, da gaggawa kuma za ku ci shi. Idin Ƙetarewa ne ga Ubangiji. 12A daren nan zan ratsa ƙasar Masar, in bugi kowane ɗan fari na ƙasar, na mutum da na dabba. Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji. 13Jinin da yake bisa gidajenku zai nuna inda kuke. Sa'ad da na ga jinin zan tsallake ku, ba kuma wani bala'in da zai same ku, ya hallaka ku, a lokacin da zan bugi ƙasar Masar. 14Ranar nan za ta zama ranar tunawa a gare ku, za ku kiyaye ta, ranar idi ga Ubangiji. Dukan zamananku za ku kiyaye ta, idi ga Ubangiji har abada.
Mutuwar 'yan fari na Masarawa: 29Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir'auna, wato, magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan 'ya'yan fari maza na dabbobi. 30Da dare Fir'auna ya tashi, shi da dukan fādawansa, da dukan Masarawa, suka yi kuka mai tsanani a Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.
Fir'auna ya ƙyale 'yan Isra'ila su tafi: 31Sai Fir'auna ya sa aka kirawo masa Musa da Haruna da daren, ya ce musu, "Tashi, ku da jama'arku, ku fita daga cikin jama'ata. Tafi, ku bauta wa Ubangiji kamar yadda kuka ce. 32Kwashi garkunanku na tumaki da awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka." 33Masarawa suka iza mutanen su gaggauta, su fita ƙasar, gama suka ce, "Ƙarewa za mu yi idan ba ku tafi ba"...
40Zaman da Isra'ilawa suka yi a Masar shekara ce arbaminya da talatin. 41A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.
Bayyani
Domin Allah ya ƙetare gidajen Ibraniyawa, ya ƙebe'ya'yansu na fari daga hallaka, su kan yi idin Ƙetare kowace shekara. Wannan idinsu ya fi kowane wani idinsu girma. Lokacin wannan idi, bayan shekaru da yawa, Yesu ya mutu a kan giciye. Yankewar ɗan rago misalign mutuwarsa ne, kamar yadda Yohana mai yin babtisma y ace: "Ga shi Ɗan Ragon Allah, ga shi wanda ke kawas da zunuban duniya." (Yn 1:29)
Tambayoyi
- Zuwa wace ƙasa Yakubu (Isra'ila ken an) da iyalinsa suka tafi?
- Don me Fir/auna ya zalunci Ibraniyawa?
- Me ya ce ungozomai su yi?
- Me ungozomai suka yi?
- Bayan wannan, me Fir'auna ya ce a yi da yara maza na Ibraniyawa?
- Ta yaya aka tsare Musa daga mutwa lokacin da she yaro ne?
- Me Musa ya gani da ya sa ya yi mamaki, ya ratse wurin da Allah ya yi Magana da shi?
- Don me Musa ya rufe fuskarsa?
- Me Allah ya ce zai yi?
- Wane sunansa Allah ya bayyana wa Musa?
- Musa ya yarda ya yi abin da Allah ya ce masa?
- Me Allah ya yi don ya taimaki Musa?
- Me Musa da Haruna suka tambayi Fir'auna?
- Me Fir'auna ya amsa?
- Me Fir'auna ya ce a yi da Ibraniyawa?
- Bayan da Allah ya hori Masar da yawa, suka kuma ƙi yarda 'Yan Isra'ila su fita, me Allah ya ce jama'ar Isra'ila su yi da ɗan rago?
- Ina horon ƙarshe da Allah ya yi wa Masarawa?
- Don me Allah ya ƙetare gidajen 'yan Isra'ila lokacin da ya ke hallaka Masarawa?
- Bayan horon nan, Fir'auna ya yarda 'yan Isra'ila su tafi?
- Shekaru nawa 'yan Isra'ila suka baƙunta cikin Masar?
- Aka yanka ɗan rago kamar misalin wanene na lokacin gaba?
DARASI NA TARA: FITOWA
Karatu: Fitowa 13:17-15:13
'Yan Isra'ila sun tashi: 17Da Fir'auna ya bar jama'a su tafi, Allah bai bi da su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ta fi kusa, gama Allah ya ce, "Don kada jama'a su sāke tunaninsu sa'ad da suka ga yaƙi, su koma Masar." 18Amma Allah ya kewaya da jama'a ta hanyar jeji, wajen Bahar Maliya. Isra'ilawa kuwa suka fita daga ƙasar Masar da shirin yaƙi. 19Musa ya kuma ɗauki ƙasusuwan Yusufu, gama Yusufu ya riga ya rantsar da Isra'ilawa su kwashe ƙasusuwansa daga Masar sa'ad da Allah ya ziyarce su.
20Sai suka ci gaba da tafiya daga Sukkot suka yi zango a Etam a gefen jejin. 21Da rana Ubangiji yakan yi musu jagora da al'amudin girgije, da dare kuwa da al'amudin wuta, don ya ba su haske domin su iya tafiya dare da rana. 22Al'amudan nan biyu kuwa, na girgijen da na wutar, ba su daina yi wa jama'a jagora ba.
Daga Etam har Tekun: 14:1Ubangiji ya ce wa Musa, 2"Faɗa wa Isra'ilawa su juya su yi zango a gaban Fi-hahirot tsakanin Migdol da bahar, a gaban Ba'alzefon. Sai ku yi zango gab da bahar. 3Gama Fir'auna zai ce, 'Aha, Isra'ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta cinye su.' 4Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji." Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.
Masarawa sun bi 'Yan Isra'ila baya: 5Da aka faɗa wa Sarkin Masar jama'a sun gudu, sai shi da fādawansa suka sāke tunaninsu game da jama'ar, suka ce, "Me muka yi ke nan, da muka bar Isra'ilawa su fita daga cikin bautarmu?" 6Ya kuwa shirya karusarsa, ya ɗauki rundunarsa tare da shi. 7Ya kuma ɗauki zaɓaɓɓun karusai ɗari shida da sauran karusan Masar duka waɗanda shugabanni suke bi da su. 8Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Sarkin Masar, sai ya bi Isra'ilawa sa'ad da suka fita gabagaɗi. 9Masarawa kuwa, da dukan dawakan Fir'auna, da karusai, da mahayan dawakansa, da askarawansa, suka bi su, suka ci musu a inda suka yi zango a bakin bahar, kusa da Fi-hahirot wanda ya fuskanci Ba'alzefon.
10Da Fir'auna ya matso, Isra'ilawa kuwa suka ɗaga idanunsu suka ga Masarawa tafe, sun tasar musu, sai suka firgita ƙwarai, suka yi kuka ga Ubangiji. 11Suka ce wa Musa, "Don ba makabarta a Masar, shi ya sa ka fito da mu, mu mutu a jeji? Me ke nan ka yi mana da ka fito da mu daga Masar? 12Ashe, ba abin da muka faɗa maka tun a Masar ke nan ba cewa, 'Ka rabu da mu, mu bauta wa Masarawa?' Gama gwamma mu bauta wa Masarawa da mu mutu a jeji."
13Sai Musa ya ce wa jama'a, "Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau. 14Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!"
An hayi Teku: 15Sai Ubangiji ya ce wa Musa, "Me ya sa kake yi mini kuka? Faɗa wa Isra'ilawa su ci gaba. 16Ɗaga sandanka, ka miƙa hannunka a bisa bahar, ka raba shi, domin Isra'ilawa su taka busasshiyar ƙasa cikin bahar, su haye. 17Ni kuwa zan taurare zukatan Masarawa domin su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir'auna da rundunansa, da karusansa, da mahayan dawakansa. 18Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na sami nasara bisa kan Fir'auna, da karusansa, da mahayan dawakansa."
19Mala'ikan Allah kuwa wanda yake tafiya a gaban rundunar Isra'ila ya tashi ya koma bayansu, haka kuma al'amudin girgijen ya tashi daga gabansu ya tsaya a bayansu. 20Ya shiga tsakanin sansanin Masarawa da zangon Isra'ilawa. Girgije mai duhu na tsakaninsu, amma ya haskaka wajen Isra'ilawa har gari ya waye, ba wanda ya kusaci wani.
21Da Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, sai Ubangiji ya sa iskar gabas mai ƙarfi ta tsaga bahar, ta tura ta baya, ta yi ta hurawa dukan dare har bahar ta bushe, ruwan kuwa ya dāre. 22Isra'ilawa kuwa suka bi ta tsakiyar bahar, a busasshiyar ƙasa. Ruwan ya zama musu katanga dama da hagu. 23Masarawa kuwa suka bi su har tsakiyar bahar, da dawakan Fir'auna duka, da karusansa, da mahayan dawakansa. 24Da asubahin fāri, Ubangiji, daga cikin al'amudin wuta da na girgije, ya duba rundunar Masarawa, ya gigitar da su. 25Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, "Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa."
26Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, "Miƙa hannunka bisa bahar domin ruwa ya koma bisa kan Masarawa, da bisa karusansu, da mahayan dawakansu." 27Gari na wayewa sai Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, ruwan kuwa ya koma kamar yadda yake a dā. Da Masarawa suka yi ƙoƙarin tserewa, sai ruwan ya rufe su. Ubangiji kuwa ya hallaka su a tsakiyar bahar. 28Ruwan ya komo ya rufe dukan karusai, da mahayan dawakai, da dukan rundunar Fir'auna waɗanda suka bi ta cikin bahar, ba ko ɗaya da ya ragu. 29Amma Isra'ilawa suka yi tafiya a busasshiyar ƙasa a tsakiyar bahar, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu.
30A wannan rana, Ubangiji ya ceci Isra'ilawa daga hannun Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin bahar. 31Isra'ilawa suka ga gawurtaccen aikin da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ji tsoron Ubangiji, suka gaskata Ubangiji da bawansa Musa.
Waƙar Musa da Mariyamu: 15:20Sai Maryamu, annabiya, 'yar'uwar Haruna, ta ɗauki kuru cikin hannunta. Mata duka suka fita, suka bi ta da kuwaru suna ta rawa. 21Maryamu tana raira musu waƙa tana cewa, "Raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara, Doki da mahayinsa, ya jefar cikin bahar."
15:1-4a,8-13,17-18:1Musa da jama'ar Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,
Zan raira waƙa ga Yahweh, * gama ya ci gawurtacciyar nasara.
Doki da mahayinsa * ya jefar cikin bahar.Yahweh ƙarfina ne, ina yabonsa, * shi ne wanda ya cece ni. Wannan ne Allahna, zan girmama shi, * Allah na kakana, zan ɗaukaka shi. Yahweh mayaƙi ne, * sunansa Yahweh. Karusan Fira'auna da rundunarsa * ya jefar cikin bahar... Da hucin lumfashin hancinka * ruwa ya tattaru. Rigyawa ta tsaya kamar tudu, * zurfafan ruwaye suka daskare a tsakiyar bahar. Magabcin ya ce, * "Zan bi, in kama su, in kwashi ganima, * muradina a kansu zai biya, zan zare takobina, * hannuna zai halaka su." Ka hura iskarka, * bahar ta rufe su, suka nutse kamar darma * cikin manyan ruwaye. Yahweh, wanene kamarka cikin alloli? * wa ke kamarka cikin ɗaukaka da tsarki? Mai banrazana ta yin al'ajibai, * mai aikata mu'ujjiza. Ka miƙa hannunka na dama, * ƙasa ta haɗiye su. Amma da ƙaunarka ka ja gorar * jama'arka da ka fansa. Ka bi da su da ƙarfinka * zuwa tsattsarkan mazauninka... Za ka kawo su, ka dasa su * a kan dutsen da ka zaɓa, wurin mazauninka, * wanda kai, Yahweh, ka kafa, tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, * wanda hannuwanka suka yi. Yahweh zai yi mulki * har abada abadin. Bayyani
- 'Yan Isra'ila sun haya Teku na gamba kamar misalin babtismarmu.
- Masar misalin zamammu na dā ne, lokacin da ba mu duba da zunubammu ba, ba mu san Allah ba.
- Fir'auna da rundunarsa misalin Shaiɗan ma miyagun iskoki ke nan.
- Teku misalin ruwan babtisma ne.
- Al'umudi na girgije da rana, da al'umudi na wuta da dare, waɗanda suka raka 'yan Isra'ila, su ne misalin Ruhu Mai Tsarki na Allah, wanda ya ke raka mu cikin sabon rai wanda muka samu ta wurin Yesu Almasihu.
- Ḍan rago ne wanda aka yanka saboda zunubammu misalin Yesu ne.
- Musa, shugaban 'yan Isra'ila, shi ne misalin fada da bishop waɗanda su ke bi da jama'a zuwa ga sabon rai wanda Yesu ya ba mu.
Amma cikin sabon rai, mutane da yawa suna cin baya, kamar Kirista waɗanda ba su nuna hali mai kyau, ko ba su zuwa Lahadi banda dalili. Ga kamaninsu cikin labari mai zuwa na jama'ar 'yan Isra'ila. Suka yi ƙara, suka rena bangaskiyarsu saboda marmarin abinci da abinsha.
Karatu: Fitowa 15:22a, 27, 16:1-17:7
Abincin menene: 22Musa kuwa ya bi da Isra'ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur...
27Daga nan suka je Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa goma sha biyu, da itatuwan giginya saba'in. A nan suka yi zango a bakin ruwa.
16:1Taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga Elim suka shiga jejin Sin wanda yake tsakanin Elim da Sina'i, a rana ta goma sha biyar ga watan biyu bayan fitowarsu daga ƙasar Masar. 2Sai dukan taron jama'ar Isra'ilawa suka yi wa Musa da Haruna gunaguni cikin jejin, suka ce musu, 3"Da ma mun mutu ta ikon Ubangiji a ƙasar Masar lokacin da muka zauna kusa da tukwanen nama, muka ci abinci muka ƙoshi. Ga shi, kun fito da mu zuwa cikin jeji don ku kashe dukan wannan taro da yunwa."
4Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, "Ga shi, zan sauko muku da abinci daga sama. A kowace rana jama'a za su fita su tattara abin da zai ishe su a yini, da haka zan gwada su, ko za su kiyaye maganata, ko babu. 5A kan rana ta shida, sai su ninka abin da suka saba tattarawa na kowace rana, su shirya shi."
6Musa da Haruna kuwa suka ce wa Isra'ilawa, "Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fisshe ku daga ƙasar Masar. 7Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, gama ya ji gunagunin da kuka yi a kansa, gama wane, mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?" 8Musa ya kuma ce, "Da yamma Ubangiji zai ba ku nama ku ci, da safe kuwa zai ƙosar da ku da abinci, gama Ubangiji ya riga ya ji irin gunagunin da kuka yi a kansa. Ai, gunagunin ba a kanmu yake ba, wane mu? A kan Ubangiji ne kuka yi."
9Musa ya ce wa Haruna, "Faɗa wa taron jama'ar Isra'ila, su matso nan a gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninsu." 10Sa'ad da Haruna yake magana da taron jama'ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije.
11Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa ya ce, 12"Na ji gunagunin Isra'ilawa, amma ka faɗa musu cewa, 'A tsakanin faɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe za ku kuma ƙoshi da abinci. Sa'an nan za ku sani, ni Ubangiji Allahnku ne.' "
13Da maraice makware suka zo suka rufe zangon, da safe kuma raɓa ta kewaye zangon. 14Sa'ad da raɓar ta kaɗe, sai ga wani abu tsaki-tsaki mai laushi, fari, kamar hazo a ƙasa. 15Sa'ad da Isra'ilawa suka gan shi, suka ce wa junansu, "Manna," wato, "Mece ce wannan?" Gama ba su san irinta ba. Musa kuwa ya ce musu, "Wannan ita ce abincin da Ubangiji ya ba ku, ku ci. 16Abin da Ubangiji ya umarta ke nan, ko wannenku ya tattara wadda ta ishe shi ci, kowa ya sami mudu daidai bisa ga yawan mutanen da suke cikin kowace alfarwa."
17Isra'ilawa suka yi haka nan, suka tattara, waɗansu suka zarce, waɗansu kuma ba su kai ba. 18Amma da aka auna da mudu, ta waɗanda suka zarce ba ta yi saura ba, ta waɗanda ba su kai ba, ba ta gaza ba. Kowane mutum ya tattara daidai cinsa. 19Musa ya ce musu, "Kada wani ya ci, ya bar saura har safiya." 20Amma waɗansu ba su kasa kunne ga Musa ba, suka bar saura, har ta kwana, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su. 21Kowace safiya sukan tattara ta, kowa gwargwadon cinsa, amma da rana ta yi zafi sai manna ɗin ta narke.
22A kan rana ta shida suka tattara biyu ɗin abin da suka saba, kowane mutum mudu biyu biyu. Sai shugabannin taron suka zo suka faɗa wa Musa. 23Shi kuwa ya ce, "Ga abin da Ubangiji ya umarta, 'Gobe ranar hutawa ce ta saduda, Asabar ce, tsattsarka ga Ubangiji. Ku toya abin da za ku toya, ku kuma dafa abin da za ku dafa. Abin da kuka ci kuka rage, ku ajiye don gobe.' " 24Suka ajiye har gobe kamar yadda Musa ya umarta, amma ba ta yi ɗoyi ba, ba ta kuwa yi tsutsotsi ba. 25Sai Musa ya ce, "Ita za ku ci yau, gama yau Asabar ce ga Ubangiji. Yau ba za ku same ta a saura ba. 26Kwana shida za ku tattara ta, amma a rana ta bakwai wadda take asabar, ba za a iske kome ba." 27Amma a rana ta bakwai ɗin waɗansu mutane suka tafi don su tattara, ba su kuwa sami kome ba.
28Sai Ubangiji ya ce wa Musa, "Har yaushe za ku ƙi kiyaye dokokina da umarnaina? 29Lura fa, Ubangiji ne ya ba ku ranar Asabar, domin haka a rana ta shida yakan ba ku abinci na kwana biyu. Kowanne ya yi zamansa a inda yake. Kada kowa ya bar inda yake a rana ta bakwai ɗin." 30Sai jama'a suka huta a rana ta bakwai.
31Isra'ilawa kuwa suka sa wa wannan abinci suna, Manna. Manna wata irin tsaba ce kamar farin riɗi. Ɗanɗanarta kuwa kamar waina ce da aka yi da zuma. 32Sai Musa ya ce, "Ubangiji ya umarta a cika mudu da ita, a adana ta dukan zamananku domin kowane zamani a ga irin abincin da ya ciyar da ku cikin jeji lokacin da ya fito da ku daga ƙasar Masar." 33Sai Musa ya ce wa Haruna, "Ɗauki tukunya, ka zuba mudu guda na manna a ciki, ka ajiye a gaban Ubangiji, a adana har dukan zamananku." 34Kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, haka Haruna ya ajiye ta a gaban akwatin alkawari don kiyayewa. 35Shekara arba'in Isra'ilawa suka yi suna cin manna, har suka kai ƙasar da take da mutane, suka ci manna, har zuwa kan iyakar ƙasar Kan'ana. 36Mudu ɗaya humushin garwa ɗaya ta gari.
Ruwa daga dutse: 1Dukan taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga jejin Sin, suna tafiya daga zango zuwa zango bisa ga umarnin Ubangiji. Suka yi zango a Refidim, amma ba ruwan da jama'a za su sha. 2Domin haka jama'a suka zargi Musa suka ce, "Ba mu ruwa, mu sha." Musa ya amsa musu ya ce, "Don me kuke zargina? Don me kuke gwada Ubangiji?"
3Amma jama'a suna fama da ƙishirwa, suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, "Don me ka fito da mu daga Masar? Ashe, don ka kashe mu ne, da mu, da 'ya'yanmu, da dabbobinmu da ƙishi?"
4Sai Musa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, "Me zan yi wa jama'ar nan? Ga shi, saura kaɗan su jajjefe ni da duwatsu."
5Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, "Ɗauki waɗansu dattawa daga cikin jama'ar Isra'ila, ka wuce a gaban jama'ar. Ka kuma ɗauki sandanka wanda ka bugi Nilu da shi, ka tafi. 6Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha." Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila.
7Sai aka sa wa wurin suna, "Masaha" da "Meriba," saboda Isra'ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, "Ubangiji yana tare da mu, ko babu?"
Bayyani
Manzo Bulus (salama a gareshi) ya ba da bayyanin karatun nan bisa. In ji shi (1 Korintiyawa 1:1-13):
1To, ina so ku sani, 'yan'uwa, dukan kakanninmu an kara su ne a ƙarƙashin gajimare, dukansu kuma sun ratsa ta cikin bahar. 2Dukansu kuwa an yi musu baftisma ga bin Musa a cikin gajimaren, da kuma bahar ɗin. 3Duka kuwa sun ci abincin nan na ruhu, 4duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne. 5Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.
6To, ai, waɗannan abubuwa gargaɗi ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. 7Kada fa ku zama matsafa kamar yadda waɗansunsu suke. A rubuce yake cewa, "Jama'a sun zauna garin ci da sha, suka kuma tashi suka yi ta rawa." 8Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak. 9Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su. 10Kada kuma mu yi gunaguni yadda waɗansu suka yi, har mai hallakarwa ya hallaka su. 11To, duk wannan ya same su ne a kan misali, an kuma rubuta shi ne don a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12Don haka duk wanda yake tsammani ya kahu, ya mai da hankali kada ya fāɗi. 13Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.
Abubuwan da Allah ya ba su 'Yan Isra'ila, su ne misalan asiran da Yesu ya ba mu. "Menene" shi ne misalin jiin Yesu, ruwa shi ne misalin jininsa, waɗanda mu ke samu cikin cimar Ubangiji.
Tambayoyi
- Allah ya raka jama'arsa ta wurin menene da rana?
- Allah ya raka jama'arsa ta wurin menene da dare?
- Me 'Yan Isra'ila suka ce bayan da Fir'auna ya bi sawunsu?
- Me Allah ya yi domin kada Masarawa su kama 'Yan Isra'ila?
- Me 'Yan Isra'ila suka ce lokacin da abinci ya kasa?
- Ta yaya Allah ya ƙosad da su?
- Musa ya ce mutane su kwashi abinci a waɗanne lokatai?
- Ko mutane sun bi abin da ya ce?
- Me 'Yan Isra'ila suka ce lokacin da ruwa ya kasa?
- Ta yaya Allah ya ƙosad da su?
- Manzo Bulus ya ce dutse wanda Musa ya buga shi ne misalin wanene?
- Abinci da abinsha waɗanda Allah ya ba 'Yan Isra'ila misalin wace kyauta ne ta Yesu Almasihu?
DARASI NA GOMA: ALKAWALI DA SHARI'A
Karatu: Fitowa 19:1-8,10,14-20; 24:12,15-18; 20:1-17; 31:18; 34:29-35
An isa Sinai: 1Isra'ilawa sun kai jejin Sina'i a farkon watan uku bayan fitowarsu daga ƙasar Masar. 2Da suka tashi daga Refidim, suka shiga jejin Sina'i, sai suka yi zango gaban dutsen.
Za a mai da jama'a limamai: 3Musa kuwa ya hau bisa dutsen don ya sadu da Allah. Ubangiji ya kira shi daga kan dutsen, ya ce, "Abin da za ka faɗa wa gidan Yakubu, wato, Isra'ilawa ke nan, 4'Kun dai ga abin da na yi da Masarawa, da yadda na ɗauke ku kamar yadda gaggafa yake ɗaukar 'yan tsakinta, na kawo ku gare ni. 5Yanzu fa, in za ku yi biyayya da ni, ku kuma kiyaye maganata, za ku zama mutanena. Dukan duniya tawa ce, amma ku za ku zama zaɓaɓɓiyar jama'ata, 6za ku zama daular firistoci da al'umma keɓaɓɓiya a gare ni.' Waɗannan su ne zantuttukan da za ka faɗa wa Isra'ilawa."
7Sa'an nan Musa ya je ya kira taron dattawan jama'a, ya bayyana musu dukan zantuttukan da Ubangiji ya umarce shi. 8Dukan jama'a kuwa suka amsa masa baki ɗaya, suka ce, "Dukan abin da Ubangiji ya faɗa za mu aikata." Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar...
10Sai Ubangiji ya ce wa Musa, "Je ka wurin jama'a ka tsarkake su yau da kuma gobe, su kuma wanke tufafinsu"...
14Da Musa ya gangaro daga dutsen zuwa wurin mutane, ya tsarkake su. Su kuwa suka wanke tufafinsu. 15Sai Musa ya ce musu, "Ku shirya saboda rana ta uku, kada ku kusaci mace."
Musa ya yau dutse: 16A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama'ar da take cikin zango suka yi rawar jiki. 17Musa kuwa ya fito da jama'a daga zango ya shugabance su, su sadu da Allah, suka tsattsaya a gindin dutsen. 18Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina'i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma'adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai. 19Da busar ƙaho ta ƙara tsananta, sai Musa ya yi magana, Ubangiji kuwa ya amsa masa da tsawa. 20Ubangiji ya sauko bisa dutsen Sina'i bisa ƙwanƙolin dutsen. Ya kirawo Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen, Musa kuwa ya hau.
Dokoki goma: 20:1Allah ya faɗi dukan waɗannan zantuttuka, ya ce, 2"Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
3"Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni. 4"Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa. 5Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina. 6Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararraki da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina.
7"Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.
8"Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki. 9Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida, 10amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Allahnka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko 'ya'yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku. 11Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji yakeɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.
12"Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
13"Kada ka yi kisankai.
14"Kada ka yi zina.
15"Kada ka yi sata.
16"Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.
17"Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka.
Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa."
31: 18Sa'ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina'i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.
Musa ya sauko daga dutse: 34: 29Sa'ad da Musa ya sauko daga Dutsen Sina'i da alluna biyu na alkawarin a hannunsa, ashe, bai sani ba, amma fuskarsa tana annuri saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji. 30Sa'ad da Haruna da dukan jama'ar Isra'ila suka ga fuskar Musa tana annuri, suka ji tsoro su kusace shi. 31Sai Musa ya kirawo Haruna tare da shugabannin jama'ar duka, suka zo wurinsa, shi kuwa ya yi magana da su. 32Daga nan jama'ar Isra'ila duka suka matsa kusa, Musa kuwa ya ba su dukan dokoki waɗanda Ubangiji ya ba shi a bisa Dutsen Sina'i. 33Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa. 34Amma duk lokacin da ya je gaban Ubangiji domin ya yi magana da shi, sai ya kware lulluɓin, har lokacin da ya fito. Idan ya fito, sai ya faɗa wa jama'ar Isra'ila abin da aka umarce shi. 35Jama'ar Isra'ila kuwa sukan ga fuskar Musa tana annuri. Sa'an nan Musa ya sāke lulluɓe fuskarsa, har lokacin da ya shiga don ya yi magana da Ubangiji.
Bayyani
Nassi nassin nan bisa sun nuna abin da Allah ya ke shirya tun farkon halitta, watau jama'ar Allah, wadda ta san Allah, ta haɗu da shi kuma ta wurin yarjejeniya. Jama'ar nan ita ce al'umma wadda Allah ya alkawalta wa Ibrahim, lokacin da ya ce zai zama uban babban al'umma. Allah ya kafa wannan jama'a domin su ba da gaskiya ga Macecin wanda zai tashi daga cikinsu. Ya kafa ta kuma domin ta ba da sanin ceto wa dukan mutanen duniya.
Allah ya ba jama'arsa shari'a domin ya nuna masu yadda za su bauta masa kamar "mulkin limamai ga Allah, al'umma mai tsarki ne" (Fit 19:6). Shari'ar Allah ta rungumi dokokin goma, da farillai da yawa kuma, sai a duba littatafai biyar na fari na Littafi Mai Tsarki domin a ga yawancinsu. An ba da waɗansu daga cikin farillan nan sai don lokacin dā. Amma cikin Sabuwar Yarjejeniya waɗansunsu sun riƙa ikonsu, kamar misali ƙaunar Allah da ƙaunar maƙwabci, da su kokoki goma kuma, waɗanda su ke bayyana ƙaunar Allah da ta maƙwabci.
Shaidar yarjejeniyar da Allah ya yi da jama'arsa wajen dutsen Sinai, ita kaciya ce ba, amma kiyaye assabas, kamar yadda Allah ya ce wa Musa (Fitowa 31:12-17): 12Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 13"Faɗa wa Isra'ilawa, 'Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku. 14Ku kiyaye ranar Asabar gama tsattsarkar rana ce a gare ku. Duk wanda ya tozarta ta, za a kashe shi, duk wanda ya yi aiki kuma a cikinta za a raba shi da jama'arsa. 15A kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai ranar hutawa ce tsattsarka ta saduwa ga Ubangiji, don haka duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta za a kashe shi. 16Domin wannan fa Isra'ilawa za su kiyaye ranar Asabar, su kiyaye ta dukan zamanansu, gama madawwamin alkawari ne. 17Ranar za ta zama dawwamammiyar shaida tsakanina da Isra'ilawa, cewa, a kwana shida ni Ubangiji na yi sama da ƙasa, amma a rana ta bakwai na ajiye aiki, na huta.'"
Shaidar nan ta dace da yarjejeniya, domin Allah ya kafa jama'arsa kamar limamai gare shi. Cikin sujadarsu ga Allah, sun nuna bangaskiyarsu, su kuwa samu tarayya cikin yarjejeniyar da Allah ya yi wa Ibrahim. Amma yarjejeniyar da Allah ya yi da mutane wajen dutsen Sinai sai shiryar Sabuwar Yarjejeniya ne.
Karatu: Wasika zuwa ga Ibraniyawa (12:18-24) ta nuna bambancin kusantar Allah yanzu tun da Yesu Almasihu ya sanad da sabuwar yarjejeniya tsakanin mu da Allah:
18Ai, ba ga abin da za a taɓa ne, kuka iso ba, ko wuta mai ruruwa, ko baƙin duhu duhu ƙirin, ko hadiri, 19ko ƙarar ƙaho, ko wata murya, wadda har masu jin maganarta suka yi roƙo kada su ƙara ji, 20don ba su iya jure umarnin da aka yi musu ba cewa, "Ko da dabba ce ta taɓa dutsen, sai a kashe ta da jifa." 21Amma ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake! Har ma Musa ya ce, "Ina rawar jiki don matuƙar tsoro." 22Amma ku kan iso Ɗutsen Sihiyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala'iku. 23Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu ke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala. 24Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.
Bayyani
Manzo Bulus ya nuna darajar Sabuwar Yarjejeniya lokacin da ya kwatanta aikin Musa da aikin manzannin Sabuwar Yarjejeniya:
Karatu: 2 Korintiyawa 3:4-13,18; 4:6
4Wannan ita ce irin amincewarmu ga Allah ta wurin Almasihu. 5Ba domin mun isar wa kanmu ba ne, har da za mu ce mu ne muke gudanar da wani abu, a'a, iyawarmu daga Allah take, 6domin shi ne ya iyar mana muka zama masu hidima na Sabon Alkawari, ba alkawarin rubutacciyar ka'ida ba, sai dai na Ruhu. Don kuwa rubutacciyar ka'ida, kisa take yi, Ruhu kuwa, rayarwa yake yi.
7Aka zana hidimar Shari'ar Musa, wadda ƙarshenta mutuwa ce, a allunan duwatsu. An bayyana hidimar nan da babbar ɗaukaka, har Isra'ilawa suka kasa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta (ga ta kuwa mai shuɗewa ce). 8Ina misalin fifikon hidimar Ruhu mafi ɗaukaka? 9Gama idan hidimar da take jawo hukunci abar ɗaukakawa ce, to lalle hidimar da take jawo samun adalcin Allah ta fi ta ɗaukaka nesa. 10Hakika a wannan hali, abin da dā take da ɗaukaka ya rasa ɗaukaka sam, saboda mafificiyar ɗaukakar da ta jice ta. 11Domin in aba mai shuɗewa an bayyana ta da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwamamme, lalle ne ya kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa.
12Tun da yake muna da sa zuciya irin wannan, to, muna magana ne gabanmu gaɗi ƙwarai. 13Ba kamar Musa muke ba, wanda ya rufe fuskarsa da mayafi, don kada Isr'ailawa su ga ƙarewar ɗaukakar nan mai shuɗewa... 18Sa'ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina'i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah... 6Domin shi Allah wanda ya ce, "Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka," shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.
Bayyani
Abin da Bulus ya ce, shi ne: Ko da manzannin Sabuwar Yarjejeniya ba su da kwarjini mai ganuwa na Musa, aikinsu ya fi na Musa daraja, domin su manzanni, iamar yanzu bishoshi da fadodi, suna ba mutanen duniya asiran Yesu Almasihu.
Yarjejeniya da shari'a waɗanda Allah ya yi da kakannimmu dā, sai shiryar yarjejeniya da shari'a ne waɗanda Yesu Almasihu ya ba mu. Cikin Sabuwar Yarjejeniyar nan babu tsoro irin da mutane suka ji a gaban dutsen Sinai, amma muna tafiya wurin Allah gab gaɗi, ta wurin Yesu Almasihu, matsakiyarmu ne. Muna kallon darajar Allah cikin Almasihu, wanda "shi ne surar Allah mara ganuwa" (Kol 1:15). Cikin Tsofuwar Yarjejeniya, Allah ya ce: "Ba za ka iya ganin fuskata ba, gama mutum ba zai gan ni ba, ya rayu." (Fit 33:20). Sanin nan na Allah ya fi sanin Allah ga mutane na Tsofuwar Yarjejeniya, amma ba za mu ga Allah a cikakke ba sai a sama, kamar yadda Manzo Bulus ya ce: "Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai" (1 Kor 13:12).
Allah ya ba mu dokoki domin ya nuna mana yadda mu zama tsatsarka cikakku, kamar yadda ya umurta Musa ya ce: "Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne" (Lawiyawa 19:2). Yesu kuma ya ce: "Sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama yake cikakke" (Mat 5:48). Musa ya bayyana yadda dokokin Allah za su tsarkaka jama'arsa: 16"Yau Ubangiji Allahnku yana umartarku ku kiyaye waɗannan dokoki da farillai. Sai ku lura ku aikata su da dukan zuciyarku da dukan ranku. 17Yau kun shaida, cewa Ubangiji shi ne Allahnku, za ku yi tafiya cikin tafarkunsa, za ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da farillansa, za ku kuma yi masa biyayya. 18Yau kuma Ubangiji ya shaida, cewa ku ne jama'arsa ta musamman, kamar yadda ya alkawarta muku. Ku kuwa za ku kiyaye dukan umarnansa. 19Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al'umman da ya yi. Za ku zama jama'a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa" (Kubawar Shari'a 26:16-19).
Banda kokoki goma, Allah ya ba da muhimman dokoki biyu cikin Tsofuwar Yarjejeniya:
1. 4"Ku ji, ya Isra'ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku" (Kubuwar Shar'ia 6:4-5). 2. "Ka ƙaunaci sauran mutane kamar yadda kake ƙaunar kanka" (Lawiyawa 19:18). Cikin Sabuwar Yarjejeniya an ce akan dokokin nan (Mark 12:28-31): 28Sai wani malamin Attaura ya zo ya ji suna muhawwara da juna. Da dai ya ga Yesu ya ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, "Wane umarni ne mafi girma duka?" 29Yesu ya amsa masa ya ce, "Mafi girma shi ne, 'Ku saurara, ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30Sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, da kuma dukkan ƙarfinka.' 31Mabiyinsa shi ne, 'Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.' Ba fa sauran wani umarni da ya fi waɗannan girma."
Yesu kuwa ya ƙara sabuwar doka: "34Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna. 35Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna" (Yn 13:34-35). 2"Wannan fa shi ne umarnina, cewa, ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato, mutum yă ba da ransa saboda aminansa" (Yn 15:12-13).
Ta wurin bin dokokin Allah za mu zama tsarkaka cikakku, za mu "ɗauki kamanin Ɗansa" (Rom 8:29), "shi da yake surar Allah" (2 Kor 4:4).
Tambayoyi
- Allah ya yi yarjejeniya da 'Yan Isra'ila domin su zama menene gare shi?
- Ina Musa ya tafi domin ya yi magana da Allah?
- Mutane suka ji tsoron zuwan Allah a kan dutse?
- Faɗi dokoki goma na Allah.
- Me Allah ya ce a kan aikin tsafi cikin doka ta fari?
- Me ya ce mutane su yi a ran Assabas?
- Ina babban rana ta Musulmi (ga darasi ta fari don amsa)?
- Ina babban rana ta Yahudawa?
- Ina babban rana ta Kirista?
- Don me Kirista su ke kiyaye Lahadi maimakon Assabas?
- Bisa ga Wasika zuwa ga Ibraniyawa, don me ba ya kamata Kirista su ji tsoron kusantar Allah ba?
- Don me Musa ya rufe fuskarsa lokacin da yana yin magana da jama'a?
- Bisa ga Wasika ta Biyu ta Bulus zuwa ga Korintiyawa, don me aikin wa'azi cikin Sabuwar Yarjejeniya ya fi aikin Musa daraja?
- Ina muhimman dokoki biyu?
- Ina sabuwar dokar Yesu?
DARASI NA GOMA SHA ƊAYA: GADON ƘASA
Allah ya yi magana da Musa yada zai tsare allunan dokoki:
Karatu: Fitowa 25:10-16
10"Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi. 11Ku dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje. Ku yi wa gyaffansa ado da gurun zinariya. 12Za ku yi wa akwatin ƙawanya huɗu na zinariya ku liƙa a kowace kusurwar akwatin, wato, ƙawanya biyu a kowane gefe na tsawon. 13Za ku kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya. 14Ku sa sandunan a kafar kowace ƙawanya da take gyaffan akwatin saboda ɗaukarsa. 15Za a bar sandunan cikin ƙawanen akwatin, kada a zare su. 16A kuma sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka a cikin akwatin.
Bayyani
Shaidar nan, ita ce allunan dokoki goma. An sa su cikin akwati mai daraja domin a nuna ladabi da dokokin Alah. An sa akwatin nan cikin ɗakin ibada tare da waɗansu abubuwa.
Karatu: Fitowa 40:1-16
Ɗakin ibada: 1Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, 2"A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada. 3Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa'an nan ka kāre shi da labule. 4Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa. 5Ka ajiye bagade na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alkawari, sa'an nan ka rataya labulen ƙofar alfarwa. 6Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada, 7ka kuma ajiye daro tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa'an nan ka zuba ruwa a ciki. 8Sai ka yi farfajiya ka kewaye wurin sa'an nan ka rataya labulen ƙofar farfajiyar.
9"Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa alfarwa da dukan abin da yake cikinta, domin ka tsarkake ta da kayayyakinta duka, za ta kuwa zama tsarkakakkiya. 10Ka shafa wa bagade na ƙona hadaya da kayayyakinsa duka man domin ka tsarkake shi, bagaden kuma zai zama mafi tsarki. 11Ka kuma shafa wa daron da gammonsa man keɓewa, da haka za ka tsarkake shi.
12"Ka kuma kawo Haruna da 'ya'yansa maza a ƙofar alfarwa ta sujada, ka yi musu wanka da ruwa. 13Sa'an nan ka sa wa Haruna tufafi tsarkaka ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mini aiki na firist. 14Sai ka kawo 'ya'yan Haruna maza, ka kuma sa musu taguwoyi. 15Sa'an nan ka shafa musu mai kamar yadda ka shafa wa mahaifinsu domin su yi mini aiki a matsayin firistoci. Shafa musu man zai sa su zama firistoci din din din dukan zamanansu."
16Haka kuwa Musa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
Bayyani
Sannan girgijen ya rufe ɗakin taruwa, darajar Ubangiji kuma ta cika mazamnin. Musa kuwa ba ya iya shiga cikin ɗaki na taruwa ba, saboda girgijen yana zamne a bisanta, darajar Ubangiji kuma ta cika mazamnin.
Karatu: Lissafi 9:15-23
15-16A ranar da aka kafa alfarwa ta sujada, sai girgije ya sauko ya rufe ta. Da maraice kuwa girgijen yana kamar wuta. 17A duk lokacin da aka gusar da girgijen, sai Isra'ilawa su kama hanya. A inda girgijen ya tsaya, nan kuma Isra'ilawa za su kafa zango. 18Da umarnin Ubangiji Isra'ilawa suke tashi, da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana bisa alfarwar, sukan yi ta zamansu a zangon. 19Ko da girgije ya daɗe a bisa alfarwar Isra'ilawa ba sukan tashi ba, sukan bi umarnin Ubangiji. 20Wani lokaci girgijen yakan yi 'yan kwanaki ne kawai bisa alfarwar. Tashinsu da zamansu sun danganta ga umarnin Ubangiji. 21Wani lokaci girgijen yakan zauna a bisa alfarwar daga maraice zuwa safiya ne kawai, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. Amma idan girgijen ya yini, ya kwana, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. 22Ko kwana biyu ne girgijen ya yi, yana zaune a bisa alfarwar ko wata guda, ko fi, sai Isra'ilawa su yi ta zamansu a zangon, ba za su tashi ba. Amma in ya tashi, sai su kuma su tashi. 23Da umarnin Ubangiji suke sauka, da umarninsa kuma suke tashi, suna bin faɗarsa, yadda ya umarci Musa.
Bayyani
Cikin jeji Allah yana tare da mutanensa ta wurin al'umudin girgije ko na wuta da dare. Lokacin da 'Yan 'Isra'ila suka shigar ƙasar Kan'ana, Allah ya dena nuna musu girgije. Sai akwatin allunan dokoki cikin ɗakin ibada ya zauna shaidar zaman Allah tare da su.
An kira ɗakin ibada "ɗakin taruwa", watau wuri ke nan inda aka gamu da Allah, aka yi magana da shi. Mutane ba su tattaru cikin ɗakin nan kamar cikin musulaci ba.
'Yan 'Isra'ila sun yi yawo cikin jeje har sun isa bakin ƙasar Kan'ana. (Duba tafiyarsu cikin hoton bisa.) Sannan Allah ya yi magana da su:
Karatu: Lissafi 33:50-56
50Sai Ubangiji ya yi magana da Musa a filayen Mowab kusa da Urdun, daura da Yariko, ya ce 51ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, "Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa ƙasar Kan'ana, 52sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu. 53Sa'an nan ku mallaki ƙasar, ku zauna a ciki, gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta. 54Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar. 55Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi. 56Idan ba ku kore su ba, zan lalatar daku kamar yadda na shirya lalatar da su."
Bayyani
Allah ya ce 'Yan 'Isra'ila su kori mazamnan ƙasas kamar misalin yadda dole ne a dena yin aikin tsafi da bin mugun hali da neman mata da yawa, bayan da aka zama Kirista.
Karatu: Yahoshuwa 1:1-3,6-7; 2:1-3:17; 4:10-18; 5:1,10-12
Allah ya gargaɗi Yahoshuwa: 1Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki, 2"Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama'ar nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra'ilawa. 3Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku, kamar yadda na alkawarta wa Musa... 6Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama'a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu. 7Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da hakanan za ka arzuta cikin dukan harkokinka.
Magewaya zuwa Yariko: 1Sai Joshuwa ɗan Nun ya aiki mutum biyu 'yan leƙen asirin ƙasa daga Shittim a asirce, ya ce musu, "Tafi, ku leƙo asirin ƙasar, musamman Yariko." Suka tafi, suka shiga gidan wata mace, karuwa, sunanta Rahab, a nan suka sauka.
2Sai aka faɗa wa Sarkin Yariko, aka ce, "Ga waɗansu mutane sun shigo nan da dad dare domin su bincike ƙasar."
3Sarkin Yariko kuwa ya aika wurin Rahab ya ce, "Fito da mutanen da suka zo wurinki, waɗanda suka shiga gidanki, gama sun zo ne domin su leƙi asirin ƙasar duka."
4Amma macen ta riga ta ɓoye mutanen nan biyu, sai ta ce, "Gaskiya ce, mutanen sun zo wurina, amma ban san ko daga ina suka zo ba, 5da maraice kuma, sa'ad da za a rufe ƙofar garin, sai mutanen suka fita, inda suka tafi kuwa ban sani ba, ku bi su da sauri, gama za ku ci musu." 6Gama ta riga ta kai su bisa rufin ɗaki, ta rufe su da ƙasheshen rama waɗanda ta shimfiɗa a bisa rufin. 7Mutanen kuwa suka tafi don su bi bayansu a hanyar Urdun har zuwa mashigai. Da fitar masu bin sawun, sai aka rufe ƙofar garin.
Yarjajeniya da Rahab: 8Amma kafin 'yan leƙen asirin ƙasar su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin, 9ta ce musu, "Na sani Ubangiji ya ba ku ƙasar, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku. 10Gama mun ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Bahar Maliya ya ƙafe a gabanku a sa'ad da kuka fito daga Masar, da irin abin da kuka yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon da Og, waɗanda kuka hallakar da su sarai. 11Da muka ji, sai zukatanmu suka narke, har ba sauran ƙarfin hali da ya ragu a kowane mutum saboda ku. Gama Ubangiji Allahnku shi ne Allahn da yake a Sama daga bisa, da duniya a ƙasa. 12Yanzu fa, ku rantse mini da Ubangiji, kamar yadda na yi muku alheri, haka ku kuma za ku yi wa gidan mahaifina, ku ba ni tabbatacciyar alama. 13Ku ceci mahaifina, da mahaifiyata, da 'yan'uwana mata da maza, da dukan abin da yake nasu, ku ceci rayukanmu daga mutuwa."
14Mutanen kuwa suka ce mata, "Ranmu a bakin naki, idan ba ki tone al'amarinmu ba, za mu yi miki alheri da aminci sa'ad da Ubangiji ya ba mu ƙasar."
15Sa'an nan ta zurarar da su da igiya ta taga, gama gidanta yana haɗe da garun birnin ne. 16Sai ta ce musu, "Tafi cikin tsaunuka domin kada masu bin sawun su same ku, ku ɓuya a wurin kwana uku, har masu bin sawun su komo, sa'an nan ku kama hanyarku."
17Mutanen suka ce mata, "Za mu kuɓuta daga rantsuwarki wadda kika rantsar da mu. 18A lokacin da za mu shigo ƙasar, sai ki ɗaura wannan jan kirtani a tagar da kika zurarar da mu, ki kuma kawo mahaifinki, da mahaifiyarki, da 'yan'uwanki, da dukan iyalin gidan mahaifinki a gidanki. 19Idan waninku ya fita daga ƙofar gidanki zuwa kan titi, to, alhakin jininsa yana bisa kansa, mu kuwa sai mu kuɓuta. Amma idan aka sa wa wani hannu wanda yake cikin gida tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu. 20Amma idan kika tone al'amarin nan namu, to za mu kuɓuta daga rantsuwar da kika rantsar da mu."
21Sai ta ce, "Bisa ga maganarku ya zama haka." Sa'an nan ta sallame su, suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan kirtanin a tagar.
22Sai suka tafi, suka shiga tsaunuka, suka yi zamansu a can kwana uku har masu bin sawun suka koma, gama masu bin sawun suka yi ta nema ko'ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba. 23Mutanen nan biyu suka sauko daga tsaunuka, suka haye zuwa wurin Joshuwa ɗan Nun, suka faɗa masa dukan abin da ya same su. 24Suka kuma ce masa, "Hakika, Ubangiji ya ba da ƙasar duka a hannunmu, banda wannan kuma mazaunan ƙasar duka sun firgita saboda mu."
An shirya jama'a: 3:1Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye. 2Bayan kwana uku sai shugabannin jama'a suka bibiya zango, 3suna umartar jama'ar suna cewa, "Sa'ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi, 4domin ku san hanyar da za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai tsakaninku da shi za ku bar rata misalin nisan kamu dubu biyu, kada ku kusace shi."
5Sai Joshuwa ya ce wa jama'a, "Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al'ajabi a tsakiyarku." 6Ya kuma ce wa firistocin, "Ku ɗauki akwatin alkawari ku wuce gaban jama'ar." Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban jama'a.
An sake yin gargaɗi: 7Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, "A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra'ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai. 8Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, 'Sa'ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.' "
9Joshuwa kuma ya ce wa Isra'ilawa, "Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku." 10Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, "Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku. 11Ga shi, akwatin alkawari na Ubangijin dukkan duniya yana wucewa a gabanku zuwa cikin Urdun. 12Yanzu fa, ku ɗauki mutum goma sha biyu daga kabilanku, wato mutum ɗaya daga kowace kabila. 13A sa'ad da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangijin dukkan duniya, suka tsoma tafin sawunsu cikin ruwan Urdun, ruwan Urdun zai yanke, ruwan da yake gangarowa zai tsaya tsibi guda."
An ƙetare: 14-15(Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama'a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe, 16sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru wuri ɗaya, ya yi soro daga nesa kusa da Adam, birnin da yake kusa da Zaretan. Ruwan kuma da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, aka yanke shi ɗungum. Jama'a kuwa suka haye daura da Yariko. 17A sa'ad da Isra'ilawa duka suke tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al'ummar ta gama hayewa...
4:10Gama firistocin da suke ɗauke da akwatin sun tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Joshuwa ya faɗa wa jama'a, da kuma bisa ga dukan abin da Musa ya umarce shi. Mutanen kuwa suka gaggauta, suka haye. 11Da jama'a duka suka gama hayewa, sai akwatin Ubangiji da firistocin suka wuce gaban jama'ar. 12Mutanen Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa kuwa suka haye tare da 'yan'uwansu da shirin yaƙi kamar yadda Musa ya umarce su. 13Mutum wajen dubu arba'in ne (40,000), mayaƙa, suka haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa filayen Yariko. 14A ranar nan Ubangiji ya ɗaukaka Joshuwa a idon dukan Isra'ilawa, har suka ga kwarjininsa dukan kwanakin ransa kamar yadda suka ga na Musa.
15Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, 16"Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin shaida, su fito daga cikin Urdun." 17Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun. 18Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā.
Ana tsoron 'Yan 'Isra'ila: 5: 1Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa...
An yi Idin Ƙetare: 10Sa'ad da Isra'ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko. 11A kashegarin idin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, waina marar yisti da busasshiyar tsaba. 12Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, mannar ta yanke, mutanen Isra'ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan'ana.
Bayyani
A batun Idin Ƙetare, duba darasi na takwas.
Karatu: Yahoshuwa 5:13-15; 6:1-27
Bayyanar Ubangiji: 13Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, "Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?"
14Sai mutumin ya ce, "A'a, gama na zo ne kamar sarkin yaƙin rundunar Ubangiji." Sai Joshuwa ya sunkuyar da kansa, ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada, ya ce masa, "Wace magana ce Ubangiji yake faɗa wa bawansa?"
15Sarkin yaƙin rundunar Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, "Cire takalmanka da suke a ƙafafunka, gama wurin da kake tsaye tsattsarka ne." Haka kuwa Joshuwa ya yi.
An kama Yariko: 1Aka rufe Yariko ciki da waje, ba mai fita, ba mai shiga saboda Isra'ilawa. 2Ubangiji ya ce wa Joshuwa, "Duba, na ba da Yariko, da sarkinta, da jarumawanta a hannunka. 3Kai da dukan mayaƙa za ku zagaya birnin sau ɗaya kowace rana har kwana shida. 4Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni. 5Sa'ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama'a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin." 6Joshuwa ɗan Nun kuwa ya kirawo firistoci, ya ce musu, "Ɗauki akwatin alkawarin, sa'an nan firistoci bakwai su ɗauki ƙaho bakwai na raguna su wuce a gaban akwatin alkawarin Ubangiji." 7Ya kuma ce wa jama'a, "Ku wuce, ku zaga birnin, masu makamai kuma su wuce a gaban akwatin Ubangiji."
8Kamar yadda Joshuwa ya umarci jama'a, firistoci bakwai da suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna a gaban Ubangiji suka wuce gaba, suna busawa, akwatin alkawari na Ubangiji yana biye da su. 9Masu makamai kuwa suka wuce gaban firistocin da suke busa ƙahonin, 'yan tsaron baya suna biye da akwati, ana ta busa ƙahoni. 10Amma Joshuwa ya umarci mutane cewa, "Ba za ku yi ihu ba, ba kuwa za ku bari a ji muryarku, ko kuwa wata magana ta fito daga bakinku ba, sai ranar da na ce muku ku yi ihu, sa'an nan za ku yi ihu." 11Ya kuwa sa akwatin Ubangiji ya zaga birnin, aka zaga da shi sau ɗaya sa'an nan suka koma zango, suka kwana.
12Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji. 13Firistoci bakwai ɗin da suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna, suka wuce gaban akwatin Ubangiji suna ta busawa, masu makamai suna tafe a gabansu, 'yan tsaron baya suna biye da akwatin Ubangiji, ana ta busa ƙahoni. 14A rana ta biyu kuma suka zaga birnin sau ɗaya, sa'an nan suka koma zango. Haka suka yi ta yi har kwana shida.
15A rana ta bakwai kuwa suka tashi da sassafe, suka yi sammako, suka zaga birnin yadda suka saba yi har sau bakwai. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai. 16A zagawa ta bakwai, sa'ad da firistoci suka busa ƙahoni, sai Joshuwa ya ce wa jama'a, "Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin. 17Amma birnin da dukan abin da yake cikinsa haram ne ga Ubangiji, sai a hallaka su. Rahab karuwar nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye 'yan leƙen asirin ƙasa da muka aika. 18Amma sai ku tsare kanku daga abubuwan da aka haramta don a hallaka su. Kada ya zama bayan da kuka haramta su ku sāke ɗaukar wani abu daga cikinsu, har da za ku sa zangon Isra'ilawa ya zama abin hallakarwa, ku jawo masa masifa. 19Amma dukan azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe keɓaɓɓu ne ga Ubangiji. Za a shigar da su cikin taskar masujadar Ubangiji." 20Jama'a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama'ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama'a kuwa suka shiga birnin, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin. 21Sa'an nan suka hallakar da dukan abin da yake a cikin birnin, da mata da maza, yara da tsofaffi, da shanu da tumaki, da jakai.
An ceci Rahab: 22Sa'an nan Joshuwa ya ce wa mutum biyu ɗin nan da suka leƙo asirin ƙasar, "Tafi gidan karuwar, ku fitar da ita, da dukan waɗanda suke nata kamar yadda kuka rantse mata." 23Sai samarin da suka leƙo asirin ƙasar suka shiga, suka fito da Rahab, da mahaifinta, da mahaifiyarta, da 'yan'uwanta, da dukan waɗanda suke nata, suka fito da dukan danginta, suka saukar da su a bayan zangon Isra'ilawa. 24Suka ƙone birnin da wuta da dukan abin da yake a cikinsa, sai dai azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe ne, suka ajiye a cikin taskar masujadar Ubangiji. 25Amma Joshuwa ya bar Rahab da rai, da ita da iyalin mahaifinta, da dukan waɗanda suke nata. Rahab ta yi zamanta wurin Isra'ilawa har wa yau domin ta ɓoye manzannin da Joshuwa ya aika don su leƙo asirin Yariko.
An la'anci Yariko: 26A lokacin nan Joshuwa ya yi musu magana da rantsuwa ya ce, "La'ananne ne mutum a gaban Ubangiji Wanda ya tashi don ya sāke gina birnin nan Yariko. A bakin ɗan farinsa zai kafa tushensa, A bakin autansa kuma zai gina ƙofofinsa."
27Ubangiji yana tare da Joshuwa, ya kuwa yi suna cikin dukan ƙasar.
Bayyani
'Yan Isr'aila sun shiga ƙasar Kan'ana kusa shekara ta alif ɗari uku (1300) kamin haifuwar Yesu Almasihu. Shigar ƙasar Kan'ana ita ce misalin yadda za mu shiga gidammu a sama: Cikin jeji 'Yan Isra'ila sun ga Allah sai ta wurin al'umudin girgije da na wuta, waɗanda suka raka 'Yan Isra'ila cikin jeji, amma suka ɓadi lokacin da 'Yan Isra'ila suka shiga ƙasar Kan'ana. Hakanan, yanzu muna san Allah sai ta wurin magnarsa wadda ya bayyana mana, amma a sama za mu gan shi fuska da fuska; ba za mu karanta a kan shi ba.
Kuma abincin da Allah ya ba mutanensa cikin jeji ya ƙare lokacin da suka shiga ƙasar Kan'ana; hakanan Allah yana ba mu cimar Ubangiji cikin wannan rai, amma zai ƙare lokacin da za mu zauna tare da Yesu cikin sama.
Ƙetaren kogin Urdun, shi ne misalin mutuwarmu lokacin da za mu "gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya" (Mt 25:34). An yi yaƙi don a kama birnin Yariko kamar misalin yadda za mu yi ƙoƙari da himma saboda mulkin sama, kamar yadda Yesu ya ce: "Tun daga zamanin Yahaya Maibaftisma har ya zuwa yanzu, Mulkin Sama yana shan kutse, masu kutsawa kuwa sukan riske shi" (Mt 11:12). Watau, kada mu ji tsoron mutane, kuma kada mu nuna ragonci cikin sha'anin addinimmu. Amma Allah yana tare da jama'arsa cikin ƙoƙarinsu; saboda haka a kan kira shi "Ubangiji Allah mai runduna" (Ishaya 6:3).
Tambayoyi
- A wane wuri Musa ya sa allunan dokokin Allah?
- Me Allah ya ce a sa cikin ɗakin ibada?
- Ta wurin menene Allah ya rak mutanensa cikin jeji?
- Me Allah ya ce mutanensa su yi bayan da suka shiga ƙasar Kan'ana?
- Wa ya zama shugaban 'Yan Isra'ila bayan da Musa ya rasu?
- A gidan wanene magewayan 'Yan Isra'ila suka zauna cikin Yariko?
- Me sarkin Yariko ya ce mata?
- Me ta yi da magewayan nan?
- Ina yarjejeniyar da ta ce su yi da ita?
- Me limamai suka ɗauka a gaban jama'a cikin hayin Urdun?
- Me limamai suka yi domin ruwaye su tsaya?
- Yaushe abincin "menene" ya ƙare?
- Me 'Yan Isra'ila suka yi da Yariko cikin kwana shidda?
- Me suka yi a kan kwana na bakwai?
- Me aka ce su yi da azurfa dazinariya da kayan jan ƙarfe da na baƙin ƙarfe?
- Me aka ce su yi dasauran dukiyar birni?
A KAN DARASU 7-11
Karatu: Ibraniyawa 11:20-31
20Ta wurin bangaskiya Ishaku ya sa wa Yakubu da Isuwa albarka a kan al'amuran da za su zo. 21Ta wurin bangaskiya Yakubu, sa'ad da yake bakin mutuwa, ya sa wa 'ya'yan Yusufu albarka dukkansu biyu, ya kuma yi sujada, yana sunkuye a kan sandarsa. 22Ta wurin bangaskiya Yusufu, da ajalinsa ya yi, ya yi maganar ƙaurar Isra'ilawa, har ya yi wasiyya a game da ƙasusuwansa.
23Ta wurin bangaskiya ne, sa'ad da aka haifi Musa, iyayensa suka ɓoye shi har wata uku, domin sun ga yaron kyakkyawa ne, ba su kuma ji tsoron umarnin sarki ba. 24Ta wurin bangaskiya Musa, sa'ad da ya girma, ya ƙi yarda a kira shi ɗan 'yar Fir'auna, 25ya gwammaci ya jure shan wuya tare da jama'ar Allah, da ya mori romon zunubi, mai saurin wucewa. 26Ya amince, cewa wulakanci saboda Almasihu wadata ce a gare shi, fiye da dukiyar ƙasar Masar, domin ya sa ido a kan sakamakon. 27Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, bai ji tsoron fushin sarki ba, ya kuwa jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa. 28Ta wurin bangaskiya ya ci Jibin Ƙetarewa, ya yayyafa jini, domin kada mai hallakar da 'ya'yan fari ya taɓa Isra'ilawa. 29Ta wurin bangaskiya suka haye Bahar Maliya ta busasshiyar ƙasa, amma da Masarawa suka yi ƙoƙarin yin haka, sai aka dulmuyar da su. 30Ta wurin bangaskiya garun Yariko ya rushe, bayan an yi ta kewaya shi har kwana bakwai. 31Ta wurin bangaskiya Rahab karuwar nan ba ta hallaka tare da maƙiya biyayya ba, ta karɓi 'yan ganganimar nan kamar aminai.
DARASI NA GOMA SHA BIYU: JIRAN ALMASIHU
Bayan da 'Yan Isra'ila suka shiga ƙasarsu, sau da yawa sun ƙetare dokokin Allah, suna bauta wa gumaka. Kowane lokacin da suka yi haka, Allah ya dena kiyaye su, maƙiyansu suka wulakanta su, sai su tuba, su kira ga Allah don taimako, sai ya ba su wani ɗan yaƙi macecinsu. Ga labarinsu cikin Zabura:
Karatu: Zabura 106:34-48
Ba su hallaka mutanen ba, * yadda Yahweh ya umurce su. Amma sun aurayya da al'ummai, * suna koyon al'adunsu. Sun kuma bauta wa gumakansu, * da suka zamam masu tarko. Suna miƙa 'ya'yansu maza * da mata ga aljanu. Suna zub da jinin adalai, * jinin 'ya'yansu maza da mata, da suka yanka wa gumakan Kan'ana, * suka ƙazanta ƙasar da jini mai yawa. Sun ƙazanta kansu da ayyukansu, * suna yin zina wajen bajirewarsu. Sannan hushin Yahweh ya yi ƙuna a kan jama'arsa, * sai ya ƙi abin gādonsa. Ya bashe su a al'ummai, * don maƙiyansu su mulke su. Magabtansu sun matsa masu lamba, * sai da suka ƙasƙantu a hannunsu. Sau da yawa ya cece su, * amma kuma suna ci gaba da taurin kansu * sai da mugun nufinsu ya komo masu. Sai dai ya tausaya wa ɓacin ransu, * yana jin kukansu. Ya tuna yarjejeniyarsa da su, * yana bi da su da yalwar alherinsa. Ya ba su rahamomi masu yawa, * a gaban dukan iyayengijinsu. Ka cece mu, Yahweh Allahnmu, * ka tattaro mu daga al'ummai, don mu gode wa sunanka mai tsarki, * mu ɗaukaka shi ta yabonka. Yabo ga Yahweh Allah na Isra'ila, * tun fil'azal har abada! * Bari dukan mutane ma su ce, "Amin". Halelu-Yah!
Bayyani
A lokacin gaba, zunuban jama'a sun yi girma. Da fari, macetansu sai sojoji ne, amma a lokacin gaba sojoji ba su isa su ceci mutane ba sai su kafa sarauta bisa dukan jama'a. Su 'yan yaƙi kuma sun zama sarakuna. Na farinsu shi ne Shawulu, wanda annabi Sama'ula ya naɗa. Shawulu ya ci baya, ya yi zunubi, sai Allah ya kore shi, ya ta da Audu daga kabilin Yahuda. Ya zama babban sarki; Allah kuwa ya yi masa yarjejeniya. Ga labarinta:
Karatu: 2 Sama'ila 7:1-29
Annabci na Natan: 1Sa'ad da sarki yake zaune a gidansa, Ubangiji kuma ya hutasshe shi daga fitinar abokan gābansa da suke kewaye da shi, 2sai sarki ya ce wa annabi Natan, "Duba, ga shi, ina zaune a gidan katakon al'ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana a alfarwa."
3Natan kuwa ya ce wa sarki, "Sai ka yi abin da yake a zuciyarka, gama Ubangiji yana tare da kai."
4Amma a daren nan Ubangiji ya yi magana da Natan. 5Ya ce, "Tafi, ka faɗa wa bawana Dawuda, ka ce, in ji Ubangiji, 'Ɗakin zama za ka gina mini? 6Har wa yau ban taɓa zama a ɗaki ba, tun lokacin da na fito da Isra'ilawa daga Masar, amma a alfarwa nake kai da kawowa daga wannan wuri zuwa wancan. 7A cikin kai da kawowata tare da dukan jama'ar Isra'ila ban taɓa ce wa wani daga cikin shugabannin Isra'ila waɗanda na sa su lura da jama'ata Isra'ila, ya gina mini ɗaki na katakon al'ul ba.' 8Abin da za ka faɗa wa bawana Dawuda ke nan, in ji Ubangiji Mai Runduna, 'Na ɗauko ka daga makiyaya inda kake kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama'ata Isra'ila. 9Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya. nuna wa jama'ata Isra'ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama'ata Isra'ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu. 12Sa'ad da kwanakinka suka ƙare, za ka rasu tare da kakanninka. A bayanka, zan ta da ɗanka, na cikinka. Zan sa mulkinsa ya kahu. 13Shi ne zai gina mini ɗaki. Ni kuwa zan tabbatar da kursiyin sarautarsa har abada. 14Zan zama uba gare shi, zai kuma zama ɗa a gare ni. Sa'ad da ya yi laifi zan hukunta shi da sanda kamar yadda mutane suke yi. Zan yi masa bulala kamar yadda 'yan adam suke yi. 15Amma ba zan daina nuna masa madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na yi wa Saul wanda na kawar daga fuskata. 16Gidanka kuwa da mulkinka za su dawwama a gabana har abada. Gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.' "
17Haka kuwa Natan ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.
Yin godiya na Dawuda: 18Sarki Dawuda ya tafi ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, "Ya Ubangiji Allah, ko ni ko iyalina ba mu cancanci dukan abin da ka yi mana ba. 19Ga shi, ka ƙara fiye da haka, ya Ubangiji Allah, gama ka yi magana, cewa, gidan bawanka zai kai kwanaki masu tsawo. Wannan ka'ida ce ta 'yan adam! 20Me kuma zan ƙara ce maka, gama ka san bawanka, ya Ubangiji Allah. 21Bisa ga alkawarinka da yardar zuciyarka ne ka aikata waɗannan manyan al'amura domin ka sa in san su. 22Bisa ga dukan abin da muka ji, kai mai girma ne, ya Ubangiji Allah. Ba kamarka, in banda kai kuma babu wani Allah. 23Ba wata al'umma kuma a duniya wadda take kama da jama'arka Isra'ila, wadda kai Allah ka fansa ta zama jama'arka. Ka mai da kanka sananne. Ka yi wa jama'arka manyan abubuwa masu banmamaki. Ka kori al'ummai da gumakansu a gaban jama'arka, waɗanda ka fansa daga Masar. 24Ka zaɓar wa kanka jama'ar Isra'ila su zama mutanenka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
25"Ya Ubangiji Allah, yanzu ka tabbatar da maganar da ka yi da bawanka da gidansa har abada. Ka aikata bisa ga faɗarka. 26Za a kuwa ɗaukaka sunanka da cewa, 'Ubangiji Mai Runduna shi ne Allah na Isra'ila har abada.' Gidan bawanka Dawuda kuma zai kahu a gabanka. 27Gama kai, ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kai ne ka sanar wa ni bawanka, cewa, za ka sa gidana ya kahu, saboda haka ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu'a a gare ka.
28"Yanzu kuwa, ya Ubangiji Allah, kai ne Allah, kana cika alkawarinka koyaushe. Ka kuwa yi wa bawanka alkawari mai girma. 29Ka yarda da farin ciki ka sa wa gidan bawanka albarka domin gidansa ya dawwama a gabanka har abada, gama kai ne ka faɗa, ya Ubangiji Allah. Ka sa albarkarka ta tabbata a gidan bawanka har abada."
Bayyani
Bisa ga yarjejenyar nan, 'ya'yan Dawuda za su riƙa sarauta idan suna da aminci ga Allah; idan sun bar aminci za su ɓata sarauta. Amma ko da waɗansu 'ya'yan Dawuda sun bar aminci, sun ɓata sarauta, Allah ya kiyaye aminci ga iyalin Dawuda, gama daga wajenta aka haifi Yesu Almasihu, wanda "mulkinsa ba shi da matuƙa" (Lk 1:33).
Allah ya albarkaci Sulaimanu, ɗan Dawuda ne, sosae, amma Sulaemanu ya bar hanyar adalci. Bayan mutuwarsa mulkin Isra'ila, wanda ya ke cikin arewa, ya rabu da mulkin Yahudiya, wada ya ke cikin kudu. (Duba hoton ƙasa, yadda mulkin Isra'ila ya rungumi Galili, Samariya, Dikafolis, Ituriya.)
Sau da yawa kuma an sake maimaita matakan nan, watau: zunubi, horo, tuba, ceto, sai mulkin Isra'ila ya faɗa cikin shekara ɗari biyar ta tamanin da bakwai (587) kamin haifuwar Almasihu. Su Assiriyawa da Babiloniyawa sun kama mulkinsu. (Duba hoto, wurin ƙasar Irak.) Sauran kaɗan mulkin Yahudiya kuma ya faɗa.
Tun da babu sauran sarakuna ga 'yan Isra'ila, annabawa, kamar misali Ishaya, Irimiya da Yahezikilu ne, sun zama shugabannin jama'a, amma suna da iko cikin sha'anin addini kawai. Bayan da 'Yan Isra'ila suka yi bauta shekaru sabain cikin ƙasar Babiloniyawa, Koresh, sarkin Faras (watau Iran ke nan, duba hoto) ya kama mulkin Babiloniya, ya kuwa ƙyale 'Yan Isra'ila su koma gida. Koresh ya riƙa sarauta bisa ƙasar Isra'ila, amma waɗansu 'Yan Isra'ila, kamar misali Isra da Nihimiya, sun zama wakilansa.
A lokacin nan 'yan Isra'ila ba su da sarauta, amma suna da 'yanci ciin sha'anin addini. Allah yana koya masu yadda mulkin Allah ba shi abin sarauta ko siyasa cikin mulkoin duniya ba, kamar yadda Yesu ya ce: "Mulkina ba na duniyar nan ba ne" (Yn 18:36). Amma mulkinsa yana cikin duniyan nan (ga Yn 17:15), idan mutanensa suna bin dokokinsa, suna da kirki da aminci ga sarakuna da ga kaƙwabtansu cikin duniya.
Ga abin da annabi Ishaya ya ce a batun zuwan Almasihu da na mulkinsa:
Karatu: Ishaya 2:1-5; 7:10-17
Salama tana zuwa: 2:1Ga jawabin da Allah ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz a kan Yahuza da Urushalima.
2A kwanaki masu zuwa, Dutse inda aka gina Haikali zai zama mafi tsayi duka. Al'ummai da yawa za su zo su yi ta bumbuntowa su zo gare shi. 3Jama'arsu za su ce, "Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa ga Haikalin Allah na Isra'ila. Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa. Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa." 4Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin manyan al'ummai, Za su mai da takubansu garemani, Masunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace, Al'ummai ba za su ƙara fita zuwa yaƙi ba, Ba za su ƙara koyon yaƙi ba. 5Yanzu fa, zuriyar Yakubu, bari mu yi tafiya a cikin hasken da Ubangiji ya ba mu! Imanu'ila: 7: 10Ubangiji ya aika wa Ahaz da wani jawabi, ya ce, 11"Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne." 12Ahaz ya amsa, ya ce, "Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba."
13Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz:
Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama'a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure? 14Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel. 15In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa. 16Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango. 17"Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama'arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra'ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya! Bayyani
An yi wannan annabci lokacin da mulkin Isra'ila da mulkan Aram (Siriya ke nan) sun haɗa kai su yi yaƙi a gaban mulkin Yahudiya. Ahaz, sarkin Yahudiya ne, yana da nufi ya kira Taglat Falasa, sarkin Assuriya ne (ƙasarsa duk ɗaya ne da Babiloniya) don taimako. Amma Ishaya ya yi wa Ahaz gargaɗi kada ya ji tsoron su sarakuna biyu abokan gabansa ne, kada kuwa ya kira Taglat Falasa don taimako, domin idan ya yi haka, Taglat Falasa zai kama mulkin Yahudiya, Ahaz kuma zai zama bawansa. Ahaz bai gaskanta maganar Ishaya ba. Domin shaidar gaskiyar maganarsa, Ishaya ya yi annabcin nan a kan zuwan Immanu'ila. Annabcin ya cika lokacin da aka haifi Hizikiyahu, magajin Ahaz ne. Kamin a yaro Hizikiyahu ya iya ƙi mummuma ya zaɓi mai kyau, za ya sha nono da zuma maimakon cin dawa. Watau, kamin da yaro yana da wayo, za a fara babban yaƙi inda za a ƙone duk gidaje da amfanin gona cikin ƙasar Isra'ila da ta Siriya. Haka ya faru, abu kuwa ya zama mamaki ga kowa.
Karatu: Ishaya 8:23-9:7
Sunayen yaro: 1Ba sauran baƙin ciki ga wadda take shan azaba. Dā an ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zabaluna da na Naftali, amma nan gaba wannan jiha za ta sami daraja, tun daga Bahar Maliya, zuwa gabashin ƙasar a wancan sashe na Urdun, har zuwa Galili kanta, wurin da baƙi suke zaune.
2Jama'ar da suka yi tafiya cikin duhu, Sun ga babban haske! Suka zauna a inuwar mutuwa, Amma yanzu haske ya haskaka su. 3Ka ba su babbar murna, ya Ubangiji, Ka sa su yi farin ciki. Suna murna da abin da ka aikata, Kamar yadda mutane suke murna sa'ad da suke girbin hatsi, Ko sa'ad da suke raba ganima. 4Gama ka karya karkiyar da ta nawaita musu, Da kuma sandan da ake dukan kafaɗunsu da shi. Kai ne, ya Ubangiji, ka kori al'ummar Da ta zalunci jama'arka, ta kuma zambace su, Daidai da yadda dā ka kori rundunar sojojin Madayana tuntuni. 5Takalman sojojin da suka kawo yaƙi Da dukan tufafinsu da suka birkiɗe da jini, Za a ƙone su da wuta! 6Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, "Mashawarci Mai Al'ajabi," "Allah Maɗaukaki," "Uba Madawwami," "Sarkin Salama." 7Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka. Bayyani
Sunayen da aka ba yaro Immanu'ila suna bayyana halinsa kamar halin kakanninsa ne: yana da hikimar shawara ta Sulaimanu, yana da ikon Dawuda, yana da girma da adalci na Musa da na Ibrahim. Bayan haka, shi ne Allah.
Karatu: Ishaya 11:1-9 Sarki mai adalci:
1Daga cikn tsutsugen Yesse toho za ya fito, reshe kuma daga cikin sauyoyinsa za ya ba da 'ya'ya. 2Ikon Ubangiji zai ba shi hikima, Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa. Zai kuwa san nufin Ubangiji, ya kuma yi tsoronsa, 3Zai ji daɗin yin hidimarsa. Ba zai yi shari'ar ganin ido ko ta waiwai ba. 4Zai yi wa matalauta shari'a daidai. Zai kuma kāre hakkin masu tawali'u. Bisa ga umarninsa za a hukunta ƙasar, Mugaye za su mutu. 5Zai yi mulkin mutanensa da adalci da mutunci. 6Kyarketai da tumaki za su zauna tare lafiya. Damisoshi za su kwanta tare da 'yan awaki. 'Yan maruƙa da kwiyakwiyan zaki za su yi kiwo tare, Ƙananan yara ne za su lura da su. 7Shanu da beyar za su yi kiwo tare, 'Yan maruƙansu da kwiyakwiyansu za su kwanta lafiya. Zaki zai ci ciyawa kamar sā. 8Jariri zai yi wasa kusa da maciji mai mugun dafi Amma ba zai cuta ba. 9A kan Sihiyona, dutse tsattsarka, Ba wani macuci ko mugu. Ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji Kamar yadda tekuna suke cike da ruwa. Bayyani
A farkon wannan annabci, Yesse shi ne baban Dawuda. Tsutsugen Yesse shi ne iyalinsa. Toho ko reshe wanda zai fito daga iyalinsa shi ne wani jikansa, watau Almasihu ke nan. Sh ne sarki mai adalci wanda ba za ya yi shari'a bisa ga abin da ya bayyana ga ido ba, ko bisa ga abin da mutane suka faɗi masa ba, amma bisa ga gaskiyar da ta ke cikin zuciyar mutum, domin shi ya san dukan tunanin mutane. Cikin mulkinsa dabbobin daji masu hauka za su zauna tare da dabbobin gida cikin salama, watau cikin mulkinsa ba za a ji tsoron zalunci ba, domin dukan mutanensa suna da sanin Ubangiji.
Ga kuma abin da annabi Irimiya ya ce:
Karatu: Irimiya 23:5-6
5"Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalci daga zuriyar Dawuda Wanda zai ci sarauta. Zai yi sarauta da hikima, Zai aikata abin da ke daidai a ƙasar. 6A zamaninsa za a ceci Yahuza, Isra'ila kuwa za ta zauna lafiya. Sunan da za a kira shi da shi ke nan, 'Ubangiji Adalcinmu.' Bayyani
Sarkin nan Almasihu ne. Yahuda shi ne ɗan Yakubu (duba darasi na bakwai), wanda ya zauna cikin kudu na ƙasar Kan'ana. An kira jiharsa "Yahudiya" (duba bisa) ko "Yahuda' kawai. Isar'ila duk ɗaya ne da Yakubu. An kira sauran ƙasar Kan'ana "Isra'ila" lokacin da ya rabu da Yahudiya da aka yi mulki biyu. An yi wannan annabci lokacin da mulkokin nan suka faɗa cikin hannun Babiloniyawa. Watau, a lokacin gaba za a ceci Yahuda da Isra'ila, sarki ɗaya Almasihu ne zai yi mulki bisa su biyu. Sunansa "Ubangiji Adalcimmu" ne, watau shi ne Allah wanda ya kawo adalci zuwa ga mutanensa.
Karatu: Irimiya 31:31-34
Sabuwar yarjeniya: 31Ubangiji ya ce, "Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza. 32Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da ya ke ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa. 33Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata. 34Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, 'Ka san Ubangiji' ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba."
Bayyani
Tsofuwar yarjejeniya ita ce wadda Allah ya yi da mutanensa ta wurin Musa a dutsen Sinai (duba darasi na 10). Sabuwar yarjejeniya ita ce wadda Yesu Almasihu ya yi da jininsa. Wasika zuwa ga Ibraniyawa ya bayyana wannan nassi cikin sura ta takwas da ta goma.
Lokacin de zuwan Almasihu yana kusa, Allah ba ya koya jama'arsa darajar mulkinsa kawai ba, amma ya nuna masu kuma ba za su sami darajar mulkinsa sai ta wurin shan wahala. Littafin Ayuba ya nuna mutum zai sha wahala ko shi mai adalci ne ko mara laifi. Ishaya ya yi annabcin yadda Almasihu zai sha azaba domin mutane su samu yafewar zunubansu:
Karatu: Ishaya 50:4-11 Maganar bawan Ubangiji:
4Ubangiji ya koya mini abin da zan faɗa, Domin in iya ƙarfafa marar ƙarfi. A kowace safiya yakan sa in yi marmarin jin abin da zai koya mini. 5Ubangiji ya ba ni fahimi, Ban kuwa yi masa tayarwa ba Ko in juya in rabu da shi. 6Na tsiraita ga masu dūkuna. Ban hana su sa'ad da suke zagina ba, Suna tsittsige gemuna, Suna tofa yau a fuskata. 7Amma zaginsu ba zai yi mini ƙari ba, Gama Ubangiji Allah yana taimakona. Na ƙarfafa kaina domin in jure da su. Na sani ba zan kunyata ba, 8Gama Allah yana kusa, Zai tabbatar da ni, marar laifi ni, Ko akwai wanda zai iya kawo ƙararraki game da ni? Bari mu je ɗakin shari'a tare! Bari ya kawo ƙararrakinsa! 9Ubangiji kansa zai kāre ni, Wa zai iya tabbatar da ni mai laifi ne? Dukan waɗanda suke sarana za su shuɗe, Za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye! 10Ku duka da kuke tsoron Ubangiji, Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa, Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai, Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku. 11Dukanku da kuke ƙulle-ƙullen hallaka juna Ƙulle-ƙullenku za su hallaka ku! Ubangiji kansa zai sa wannan ya faru, Za ku gamu da mummunar ƙaddara. Bayyani
Bawan Ubangiji a nan shi ne Almasihu. Wannan annabci ya nuna shi ne mutum, ba mutum kawai ba, amma mutum da gaske, wanda ya iya sha wahala. Ya yarda ya sha wahala kuma domin ya bi nufin Allah Ubansa ne. Shi ya ba shi ƙarfin zuciya cikin azabarsa, domin kada ya shiga uku da ɓacin rai. Cikin gargaɗi ana kira dukan mutane su bi misalin Bawan Ubangiji lokacin da su ke cikin masifa. An kum alkawalta wutar Lahira wa masu ba da zalunci. Masu "ƙulle=ƙullen hallaka juna", ko "masu hura wuta", su ne waɗanda su ke za zafin hali ga maƙwabtansu.
Karatu: Isaya 52:13—53:12 Bawan Ubangiji ya sha azaba don cetommu.
4Ubangiji ya koya mini abin da zan faɗa, Domin in iya ƙarfafa marar ƙarfi. A kowace safiya yakan sa in yi marmarin jin abin da zai koya mini. 5Ubangiji ya ba ni fahimi, Ban kuwa yi masa tayarwa ba Ko in juya in rabu da shi. 6Na tsiraita ga masu ūna. Ban hana su sa'ad da suke zagina ba, Suna tsittsige gemuna, Suna tofa yau a fuskata. 7Amma zaginsu ba zai yi mini ƙari ba, Gama Ubangiji Allah yana taimakona. Na ƙarfafa kaina domin in jure da su. Na sani ba zan kunyata ba, 8Gama Allah yana kusa, Zai tabbatar da ni, marar laifi ne, Ko akwai wanda zai iya kawo ƙararraki game da ni? Bari mu je ɗakin shari'a tare! Bari ya kawo ƙararrakinsa! 9Ubangiji kansa zai kāre ni, Wa zai iya tabbatar da ni mai laifi ne? Dukan waɗanda suke sarana za su shuɗe, Za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye! 10Ku duka da kuke tsoron Ubangiji, Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa, Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai, Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku. 11Dukanku da kuke ƙulle-ƙullen hallaka juna Ƙulle-ƙullenku za su hallaka ku! Ubangiji kansa zai sa wannan ya faru, Za ku gamu da mummunar ƙaddara. Karatu: Ishaya 52:13-53:12 Bawan Ubangiji ya sha azaba don cetonmu
13Ubangiji ya ce, "Bawana zai yi nasara a aikinsa, Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai. 14Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi, Ya munana har ya fita kamannin mutum. 15Amma yanzu al'ummai da yawa za su yi mamaki a kansa, Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki. Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba." 53:1Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu? Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan? 2Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girma Kamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da wani maƙami ko kyan ganin Da zai sa mu kula da shi. Ba wani abin da zai sa mu so shi, Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi. 3Muka raina shi, muka ƙi shi, Ya daure da wahala da raɗaɗi. Ba wanda ya ko dube shi. Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne. 4Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce, Raɗaɗin da ya kamata mu ne za mu sha shi. Mu kuwa muna tsammani wahalarsa Hukunci ne Allah yake yi masa. 5Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya 'yantar da mu, Dūkun da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke. 6Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata, Ko wannenmu ya kama hanyarsa. Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa, Hukuncin da ya wajaba a kanmu. 7Aka ƙware shi ba tausayi, Amma ya karɓa da tawali'u, Bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya, Bai ko ce uffan ba. 8Aka kama shi, aka yanke masa shari'a, Aka tafi da shi domin a kashe shi, Ba wanda ya kula da ƙaddararsa. Aka kashe shi saboda zunubin mutanenmu. 9Aka yi jana'izarsa tare da maguye. Aka binne shi tare da masu arziki Ko da yake bai taɓa yin laifin kome, ko ƙarya ba. 10Ubangiji ya ce, "Nufina ne ya sha wahala, Mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kawo gafara, Saboda haka zai ga zuriyarsa, Zai yi tsawon rai, Ta wurinsa nufina zai cika. 11Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu. 12Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma, Matsayi a cikin manyan mutane masu iko. Da yardarsa ya ba da ransa Ya ɗauki rabon masu laifi. Ya maye gurbin masu zunubi da yawa, Ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi. Ya yi roƙo dominsu." Tambayoyi
- Labarin 'Yan Isra'ila bayan da suka shiga ƙasar Kan'ana shi ne labarin z_________, f_________, t_________, c__________.
- Wanene sarki na fari na Isra'ila?
- Wanene babban sarki wanda Allah ya yi yarjejeniya da shi?
- Wane annabi ya kawo masa labarin yarjeniya?
- Me Allah ya alkawalta masa?
- Me ya amsa domin ya nuna wa Allah ladabi da godiya?
- Wa ya zama sarki bayan da Dawuda ya mutu?
- Ina sunayen manyan annabawa uku na lokacin da mulkokin Isra'ila da na Yahudiya suka rushe?
- Wa ya ceci 'Yan Isra'ila daga bauta cikin Babiloniya?
- Ta wurin rashin sarauta cikin duniya, me Allah ya koya wa jama'arsa a batun darajar mulkinsa?
- Annabi Ishaya ya ce wanene za ta haifi Almasihu?
- Bisa ga cewar annabi Irimiya, Allah zai rubuta shari'arsa a kan menene cikin sabuwar yarjejeniya?
- Me Ishaya ya ce Almasihu zai yi lokacin da a ke zalunce shi?
- Ishaya ya ce menene amfanin azabar Almasihu?
DARASI NA GOMA SHA UKU: GA SHI NAN
Yahudawa sun ji daɗi da kwanciyar rai lokacin da sarakunan Faras suna da mulkin ƙasarsu. A shekara ɗari uku da talatin da ɗaya (331) kamin zuwan Almasihu, Aligazanda Babba, sarki ne na Giris, ya kam sarkin Faras, sarautar ƙasar Isra'ila kuwa ta zama tasa. Yahudawa sun ji daɗi lokacin Aligazanda da magnanshi, sai sarki Antiyokus na huɗu Mai daraja ne ya shiga haikali, ɗakin ibada ne na Urushalima, ya kwashe dukiyarshi, a shekara ɗari da sittin da bakwai (167) ne kamin Almasihu. A zamanin Antiyokus da magadanshi, Yahuda na Makkabi da 'yan'uwanshi huɗu sun bishe Yahudawa cikin tawaye gaban su waɗadan suka matsa musu su su bar addininsu. Sun yi nasara lokacin da mulkin Giris ya ja baya. Amma daga shekara ɗari da huɗu (104) kamin Almasihu, jikunan Siman Makkabi (ƙanen Yahuda Makkabi da magajinsa ne) suka yi faɗa juna, suka kuma yi sarautarsu saboda amfani nasu maimakion amfanin jama'ar ƙasa.
A lokacin nan a kafa ƙungiyoyi uku na Yahudawa, waɗanda suka zama abokan gaban juna, kamar yadda su ke a lokacin Almasihu. Watau akwai:
- Farisiyawa (ma'anar suansu "rababbu" ne, waɗanda suka rabu da marasa tsarki bisa ga tsamaninsu), waɗanda suka da anniya ƙwarai don girman ƙasarsu, don kowace karamar doka da al'adar ibada kkuma.
- Sadukiyawa tare da limamai na haikali, waɗanda ba su yarda da yawan koyaswar Farisiyawa ba. "Sadukiyawa sun ce, suna cewa ba tashin matattu, ba kuma mala'iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai (Ayyukan Manzanni 23:8).
- Isseniyawa, limamai ne waɗanda suka rabu da limamai na Urushalima da sujadarsu, domin suka ce limamai na Urushalima sun lalata addini. Sun kiyaye al'adu duk ɗaya ne kamar sistoci da birododi da waɗansu fadodi yau, watau: (a) ba su da kuɗi nasu, sai shugabansu ya kula da kuɗin da bukatan jama'a, (b) ba su yin aure, (c) Suna biyayyar shugabanninsu. Isseniyawa kuma sun tabbata zuwan Almasihu yana kusa, sun saurare shi da anniya.
A shikara sittin da uku (63) kamin Almasihu, Fomfeyus, sarkin sojojin Roma ne, ya kama Urushalima Romawa sun yi sarautar Yahudiya ta wurin sarakunan gargajiya. Sun mai da Hirudus Antifas wakili na fari na Roma. A shekara arba'in (40) kamin Almasihu, Romawa sun naɗa Hirudus Babba, ɗan Hirudus Antifas ne, sarkin Yahudiya. Shi abokin gaban 'Yan Makkabi ne. To, bayan shekaru uku ya kashe Antigonus, jika na ƙarshe na Siman Makkabi. A lokaci ɗaya ne ya kori Isseniyawa daga wurinsu kusa Teku na Mutwa zuwa wata ƙasa. Amma sun dawo a shekara ta huɗu (4) kamin Almasihu, shekara ɗaya ce da aka haifi Yohanna Maibabtisma.
Karatu: Luka 1:1-80
Kan magana: 1Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al'amura da suka tabbata a cikinmu, 2daidai yadda waɗanda suke shaidu tun farkon al'amari, masu hidimar Maganar, suka rattaba mana, 3da yake kuma na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya mafifici Tiyofalas, 4domin kă san ingancin maganar da aka sanar da kai baki da baki.
Iyayen Yohana Maibabtisma: 5A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu. 6Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi. 7Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.
Jibrilu ya bayyana ga Zakariya: 8Ana nan, wata rana Zakariya yana a kan hidimarsa ta firist, a kan ƙungiyarsu, 9bisa ga al'adar hidimar firistoci, sai kuri'a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare. 10A lokacin ƙona turare kuwa duk taron jama'a suna waje, suna addu'a, 11sai wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, yana tsaye a dama da bagadin ƙona turare. 12Da Zakariya ya gan shi ya firgita, tsoro ya kama shi. 13Amma mala'ikan ya ce masa, "Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.
14Za ka yi murna da farin ciki, Mutane da yawa kuma za su yi farin ciki da haihuwarsa. 15Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji, Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki Tun yana cikin mahaifiyarsa. 16Zai kuma juyo da Isra'ilawa da yawa ga Ubangiji Allahnsu. 17Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya. Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu, Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai, Ya tanada wa Ubangiji jama'a, domin ya same su a shirye." 18Sai Zakariya ya ce wa mala'ikan, "Ta ƙaƙa zan san haka? Ga ni tsoho, maiɗakina kuma ta kwana biyu." 19Sai mala'ikan ya amsa ya ce, "Ni ne Jibra'ilu da nake tsaye a gaban Allah. An aiko ni ne in yi maka magana, in kuma yi maka wannan albishir. 20To, ga shi, za ka babance, ba za ka iya magana ba, sai a ran da al'amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta." 21Jama'a suna ta jiran Zakariya, suna mamakin jinkirinsa a Haikali. 22Da ya fito, ya kāsa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Haikalin. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma ba ya magana. 23Sa'ad da kuma kwanakin hidimarsa suka cika, ya koma gida.
24Bayan kwanakin nan mata tasa Alisabatu ta yi ciki. Sai ta riƙa ɓuya har wata biyar, tana cewa, 25"Haka Ubangiji ya yi mini a kwanakin da ya dube ni da rahama, domin yă kawar mini da wulakanci a wurin mutane."
Jibrilu ya bayyana ga Mariyamu: 26A wata na shida Allah ya aiko mala'ika Jibra'ilu zuwa wani gari a ƙasar Galili, mai suna Nazarat, 27gun wata budurwa da aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu, na zuriyar Dawuda, sunan budurwar kuwa Maryamu. 28Sai mala'ikan ya je wurinta, ya ce, "Salama a gare ki, yake zaɓaɓɓiya, Ubangiji yana tare da ke!" 29Amma ta damu ƙwarai da maganar, ta yi ta tunani ko wannan wace irin gaisuwa ce. 30Mala'ikan kuma ya ce mata, "Kada ki ji tsoro. Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. 31Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haife ɗa, ki kuma raɗa masa suna Yesu.
32Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki.
Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda, 33Zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada, Mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa." 34Sai Maryamu ta ce wa mala'ikan, "Ta ƙaƙa wannan zai yiwu, tun da yake ba a kai ni ɗaki ba?" 35Mala'ikan ya amsa mata ya ce,
"Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki. Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah. 36Ga shi kuma, 'yar'uwarki Alisabatu ma ta yi cikin ɗa namiji da tsufanta, wannan kuwa shi ne watanta na shaida, ita da ake ce wa bakararriya. 37Ba wata faɗar Allah da za ta kāsa cika."
38Sai Maryamu ta ce, "To, ga shi, ni baiwar Ubangiji ce, yă zama mini yadda ka faɗa." Sai mala'ikan ya tashi daga gare ta.
Mariyamu ta je gun Alisabatu: 39A kwanakin nan Maryamu ta tashi da hanzari, ta tafi wata ƙasa mai duwatsu, zuwa wani gari na ƙasar Yahuza. 40Ta shiga gidan Zakariya ta gai da Alisabatu. 41Sai ya zamana da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, jariri ya motsa da ƙarfi a cikinta. Aka kuwa cika Alisabatu da Ruhu Mai Tsarki, 42har ta tā da murya da ƙarfi, ta ce, "Ke mai albarka ce a cikin mata, ɗan cikinki kuma mai albarka ne! 43Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da mahaifiyar Ubangijina za ta zo gare ni? 44Domin kuwa da jin muryarki ta gaisuwa a kunnena, sai jaririn ya motsa da ƙarfi a cikina domin farin ciki. 45Albarka tā tabbata ga wadda ta gaskata, domin za a cika abubuwan da Ubangiji ya aiko a faɗa mata."
Waƙar Maryamu: 46Sai Maryamu ta ce,
Zuciyata na ɗaukaka shi Ubangiji, * Allah Macecina * da shi ruhuna yake ta farinciki. Domin fa shi ya dubi ƙasancinta ne baiwa tasa, * ai ga shi jama'a ta dukan zamani * mubarika ce za su ce mani nan gaba. Domin fa shi da ya ke yana Mai iko, * ai manya-manyan al'amurra yai mani, * sunansa ko labudda tsattsarka yake. Daga zamani har dai zuwa wani zamani, * tausansa na ga waɗanda ke tsoro nasa. Al'amari babba da ƙarfinsa ya yi, * ya watsa duk mutakabbirai sun watse. Ya firfitad da sarakuna a sarauta, * ya ɗaukaka masu zaman ƙasƙanci. Mayunwata ya yalwata da abubuwan alheri, * ya sallame su da babu, masu wadata. Ya taimaka wa baransa Isra'ila, * domin yana tune dai da yin rahama tasa. Ita ya yi alkawari ga kakannimmu, * tutur ga Ibrahim da duk zuriya tasa. Haihuwar Yahaya Maibaftisma: 57To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji. 58Sai maƙwabta da 'yan'uwanta suka ji yadda Ubangiji ya yi ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki. 59Sai ya zamana a rana ta takwas suka zo yi wa ɗan yaron kaciya. A dā za su sa masa sunan mahaifinsa, Zakariya, 60amma mahaifiyarsa ta ce, "A'a, Yahaya za a sa masa." 61Sai suka ce mata, "Ai kuwa, ba wani ɗan'uwanku mai suna haka." 62Sai suka alamta wa mahaifinsa, suna neman sunan da yake so a sa masa. 63Sai ya nema a ba shi allo, sa'an nan ya rubuta, "Sunansa Yahaya." Duka suka yi mamaki. 64Nan da nan ya sami baki, kwaɗon harshensa ya saku, ya fara magana, yana yabon Allah. 65Sai tsoro ya kama dukan maƙwabtansu. Aka yi ta baza labarin duk waɗannan al'amura ko'ina a dukan ƙasa mai duwatsu ta Yahudiya. 66Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, "Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?" Gama ikon Ubangiji yana tare da shi.
Waƙar Zakariya: 67Sai aka cika mahaifinsa Zakariya da Ruhu Mai Tsarki, ya yi annabci, ya ce,
Ubangiji Allah na Isra'ila * a gare shi ne lalle yabo ke tabbata, * don ya kula, ya fanshi ma jama'a tasa. Ya ta da Maceci mai iko domin mu, * daga zuriya ta baransa Dauda, yadda a tuntuni ya faɗa fa ta bakunan * su annabawa nasa tsarkakan nan: ya cece mu a gun su abokan gabammu, * har ma a hannun dukan maƙiyammu. Don nuna rahama ne ga kakannimmu, * ya tuna da alkawari nasa tsattsarkan nan. Shi ne rantsuwan nan wadda yai wa Ubammu Ibrahimu, * y cece mu gun su abokan gabammu, ya ba mu baiwa don mu dai bauta masa, * a gabansa ba a cikin halin tsoro ba ne, sai dai cikin tsarki da halin gaskiya, * dukan iyakar kwanakin nan namu. Kai kuma, yaro, za a kira ka annabi ne na Maɗaukaki, * za ka riga Ubangiji gaba, ka shisshirya hanyoyi nasa, ka sanad da su cetonsu su jama'a tasa, * watau na samun gafarar zunubai nasu. Saboda tsananin rahamar Allahmmu, * daga can sama ne hasken alfijir zai keto mana, har ya haskaka su na zaune can cikin duhu a bakin halaka, * har ma ya dai bishe mu hanyar lafiya. Bayyani
Yohana Maibabisma, kamar yadda aka riga cewa, jikan Haruna ne. Haruna ɗan'uwan Musa ne, jikan Lawi ɗan Yakubu ne. Allah ya zaɓi kabilin Lawi su yi aikin hidima cikin Ɗakin Ibada.
"Yohana ya zauna a jeji." An yi tsamanin ya zauna a wani wuri a bakin arewa ga yamma na Tekun Mutwa. Sunan wuri Ƙumran ne. Can, a wannan lokaci, akwai gidan Isseniyawa, waɗanda suna da makaranta ta yara. Isseniyawa limamai ne, sun ce su jikokin Haruna ne ta wurin Sadok, babban limami ne lokacin Sarki Dawuda. Tun da Zakariya limami ne kuma, zai so su limamai na Ƙumran su koya ɗansa Yohana.
Karatu: Luka 2:1-39
Haihuwar Yesu a Baitalami: 2:1A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa. 2Wannan ita ce ƙidaya ta fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya. 3Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi. 4Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa), 5don a rubuta shi, duka da Maryamu wadda yake tashin, wadda take kuma da ciki. 6Sa'ad da suke a can kuwa, sai lokacin haihuwarta ya yi. 7Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani kwamin dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.
Makiyaya da Mala'iku: 8A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin, suna tsaron garken tumakinsu da daddare. 9Sai ga wani mala'ikan Ubangiji a tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, har suka tsorata gaya, 10Sai mala'ikan ya ce musu, "Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane. 11Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji. 12Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri a rufe da zanen goyo, kwance a kwamin dabbobi." 13Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala'ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa,
14"Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, a can cikin Sama mafi ɗaukaka.
A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa."
15Da mala'iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, "Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu." 16Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn a kwance cikin kwamin dabbobi. 17Da suka gan shi, suka bayyana maganar da aka faɗa musu a game da wannan ɗan yaro. 18Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al'ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu. 19Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana bimbini a zuci. 20Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.
Kaciyar Yesu: 21Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, aka raɗa masa suna Yesu, wato sunan da mala'ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.
Miƙa Yesu a Haikali: 22Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari'ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji 23(kamar dai yadda yake a rubuce a Shari'ar Ubangiji cewa, "Duk ɗan farin da aka haifa, za a ce tsattsarka ne shi na Ubangiji,") 24su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Shari'ar Ubangiji cewa, "Kurciyoyi biyu, ko kuwa 'yan shila biyu."
Waƙar Simiyan: 25To, akwai wani mutum a Urushalima, mai suna Saminu, adali, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin ta'aziyyar Isra'ila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi. 26Ruhu Mai Tsarki kuwa ya riga ya bayyana masa, cewa ba zai mutu ba sai ya ga Almasihun Ubangiji. 27Ruhu yana iza shi, sai ya shiga Haikalin. Da iyayen suka shigo da ɗan yaron nan Yesu, su yi masa yadda ka'idar Shari'ar ta ce, 28sai Saminu ya rungume shi, ya yi wa Allah godiya, ya ce,
Yanzu kam ya Mamallaki, * sai ka sallami bawanka lafiya, * bisa faɗan nan da ka faɗa. Don na ga cetonka zahiri, * da ka shirya a gaban kabilun nan duka, Haske mai yi wa sauran al'ummai buɗi * abin kuma ɗaukaka jama'arka Isra'ila. 33Mahaifiyarsa da mahaifinsa kuwa suna mamakin abin da aka faɗa a game da shi, 34Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu mahaifiyar Yesu, "Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin fāɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa a cikin Isra'ila, Zai kuma zama alama wadda ake kushenta, 35Domin tunanin zukata da yawa su bayyana. I, ke ma, takobi zai zarta zuciyarki."
Hannatu ya yi magana a kan Yesu: 36Akwai kuma wata annabiya, mai suna Hannatu, 'yar Fanuyila, na kabilar Ashiru. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukarta na budurci, 37da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Haikalin, tana bauta wa Allah dare da rana ta wurin yin addu'a da azumi. 38Nan tāke ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukan masu sauraron fansar Urushalima.
39Bayan sun ƙare kome da kome bisa ga Shari'ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat.
Karatu: Sauran labari daga hannn Matiyu, 2:1-23
Masana daga gabas: 1Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, 2"Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada." 3Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima. 4Sai ya tara dukan manyan firistoci da malaman Attaura na jama'a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu. 5Sai suka ce masa, "A Baitalami ne, ta ƙasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta cewa,
6'Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.' "
7Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana. 8Sa'an nan ya aike su Baitalami, ya ce, "Ku je ku binciko mini ɗan yaron nan sosai. In kun same shi, ku kawo mini labari, don ni ma in je in yi masa sujada." 9Su kuwa da suka ji maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda ɗan yaron nan yake. 10Da suka ga tauraron sai suka yi matuƙar farin ciki. 11Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da mahaifiyarsa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwa tare da zinariya, da lubban, da mur. 12Amma da aka gargaɗe su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
Gudu zuwa Masar: 13Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, "Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi." 14Yusufu kuwa ya tashi ya ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa da daddare, ya tafi Masar, 15ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin annabin cewa, "Daga Masar na kirawo Ɗana."
Kisan 'Yan Yara: 16Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan. 17A lokacin ne aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa,
18"An ji wata murya a Rama, Ta kuka da baƙin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta. Ba za ta ta'azantu ba, don ba su." Komowa Nazarat: 19Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce, 20"Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi ƙasar Isra'ila, don masu neman ran ɗan yaron sun mutu." 21Sai ya tashi, ya ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ya zo ƙasar Isra'ila. 22Amma da ya ji Arkilayus ya gāji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya ratse zuwa ƙasar Galili. 23Sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, "Za a kira shi Banazare."
Bayyani
Su masana masu binciken taurari ne. Mutanen zamanin nan, tun ba cikin ƙasar Faras (Iran ne) ba, suna ta yin kallon taurari, su kan karanta abin da suka tsamani a rubuce a cikinsu ne, su kan yi annabci ta wurinsu. Masan nan arna ne masu ilimi waɗanda su ke neman Allah, Allah kuwa ya jawo su zuwa ga Almasihu. Dā, Annabi Bil'am ya kwatanci Almasihu da tauraro. In ji shi (Liss 24:17):
Ina ganinsa, amma ba yanzu ba, Ina hangensa, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila, Zai ragargaje goshin Mowabawa, Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka. Yesu kuwa ya ce wa Manzo Yohana: "Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske" (Wah 22:16).
Abubuwa da yawa cikin wannan labarin Matiyu sai hanyar labari ne. Kamar yadda masu waƙar yabo su kan ƙara kome da kome saboda adon labari, hakanan mutanen zamanin Yesu su kan yi amfanin maganar annabawa cikin labarunsu domin su girmama ayyukan Allah da ya ke yi a zamaninsu. Matiyu ya ba da labarin tauraro, yana kwaikwayan maganar Bil'am domin shi nuna yadda Yesu ne hasken duniya. Ya ba da labarin su masana domin shi nuna yadda dukan mazaunan duniya za su yi wa Yesu sujada da biyayya, yana kwaikwayan maganr Ishaya da zaburar Dawuda. Mu ji su:
Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa. Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi. Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi! (Ish 60:6) Sarakunan Tarshishi da na tsibirai * su kakkawo masa haraji. Sarakunan Shiba da na Saba * su ba shi kyautayi. Dukan sarakuna su durƙusa a gabansa, * dukan al'ummai su bauta masa! (Zb 72:10-11) Karatu: Luka 2:41-52
Yesu a Ɗakin Ibada: 41To, iyayensa sukan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa. 42Da Yesu ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi tare da shi bisa ga al'adarsu a lokacin idi. 43Da aka gama idin kuma, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba. 44Su kuwa suka yi ta tafiya yini guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi ta cigiyarsa cikin 'yan'uwansu da idon sani. 45Da ba su same shi ba, suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa. 46Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin yana zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi. 47Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al'ajiin irin fahimtarsa da amsoshinsa. 48Da suka gan shi suka yi mamaki, sai mahaifiyarsa ta ce masa, "Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace." 49Sai ya ce musu, "Me ya sa kuka yi ta nemana? Ashe, ba ku sani wajibi ne in yi sha'anin Ubana ba?" 50Amma ba su fahimci maganar da ya yi musu ba. 51Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuwa tana riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.
52Yesu kuwa ya yi ta ƙaruwa da hikima, da girma, da kuma tagomashi wurin Allah da mutane.
Karatu: Yohana 1:1-14
Kalmar Allah: 1Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. 2Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. 3Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. 4Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.
6Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.
9Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. 10Dā yana duniyar ma ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'arsa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, 13wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.
14Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.
Bayyani
Ana kira Yesu Kalma, wato wanda ya fito daga bakin Allah. Baki da kalma dabam dabam ne, amma tunani ɗaya ne ya sa baki ya buɗe da kalam ta fita. Hakanan Alloah yana da tunani ɗaya da azanci ɗaya da nufi ɗaya da iko ɗaya banda rabawa. Amma akwai bambamci tsakanin Uba wnda ya ke kamar baki, da Ɗa wanda ya ke kamar kalma, mai zaune cikin baki, ko da ya ke ya zo gare mu, ya zama mutum.
Ta haka ne Yesu Ɗan Allah ne, ba saboda haifuwarsa da jiki ba. Allah ba shi mijin Maryamu ba ne, domin shi ruhu ne, ba shi da jiki da zuriya. Kamar yadda Allah ya halicci Adamu daga turbayar ƙasa, hakanan da ikonsa ya sa Maryamu ta samu juna biyu. Wannan mamaki na ikon Allah ne, amma ba saboda wannan Yesu Ɗan Allah ne ba. Yesu Ɗan Allah ne saboda aka haife shi kamar kalma daga bakin Allah kamin dukan zamanai.
Tambayoyi
- Da fari mulkin Isra'ila cikin hannun sarakuna nasu ne, sannan cikin hannun sarakunan Babiloniya, sannan na Faras, sannan na ____________, sannan na ____________.
- Farisiyawa su wanene?
- Sadukiyawa su wanene?
- Isseniyawa su wanene?
- Wanene sarkin Yahudiya, ƙalƙashin Romawa, lokacin da aka haifi Yohana Maibabtisma da Yesu Almasihu?
- Ina sunayen iyayen Yohana Maibabtisma?
- Me Zakariya ya ke yi lokacin da mala'ika ya bayyana mashi?
- Ina sunan mala'ikan ɗin?
- Me mala'ika ya ce mashi?
- Zakariya ya gaskata abin da mala'ika ya ce?
- Me ya yi da jama'a bayan da ya fita?
- Alisabatu tana da ciki wata nawa sai Jibrilu ya bayyan ga Maryamu?
- Ina magana ta fari ta Jibrilu wa Maryamu?
- Me Maryamu ta yi saboda wannan magana?
- Ina magana ta biyu da Jibrilu ya faɗi?
- Wace wuya Maryamu ta ji?
- Ta yaya Jibrilu ya ce Maryamu za ta samu ciki?
- Me Maryamu ta amsa bayan da Jibrilu ya gama dukan maganarsa?
- Me Alisabatu ta ce wa Maryamu?
- Me Maryamu ta ce cikin waƙarta a batun Ibrahim?
- Maryamu ta zauna wata nawa da Alisabatu?
- A wane lokaci Yahudawa su kan yi wa yara kaciya?
- Ta yaya Zakariya ya nuna sunan ɗansa?
- Me Zakariya ya ce cikin waƙarsa a batun Dawuda da Ibrahim?
- Bayan da ya yi girma, zuwa ina Yohana ya tafi da ya zauna?
- Wanene Kaisar (sarki) na Roma lokacin haifuwar Yesu?
- A wane birni aka haifi Yesu?
- A wane wuri cikin birni aka haife shi?
- Ta yaya makiyaya suka samu labarin haifuwar Yesu?
- Me makiyaya suka yi bayan da suka ga Yesu?
- A wane lokaci aka ba Yesu suna?
- Da kwanakin tsarkakewa suka cika (kwana arba'in ne bayanhaifuwa), me aka yi da Yesu a Urushalima?
- Wa ya rungumi Yesu cikin Ɗakin Ibada?
- Ina sunan mace wadda ta tarbi Yesu cikin Ɗakin Ibada?
- Lokacin da su masana suka zo Urushalima, suka sauka gun wa?
- Ta yaya aka sanar wa Hirudus wurin da za a haifi Almasihu?
- Me Hirudus ya ce su masana su yi?
- Me masana suka miƙa wa Yesu?
- Me masana suka yi bayan da suka gai da Yesu?
- Zuwa ina Yusufu ya gudu da iyalinsa?
- Me Hirudus ya yi da yara maza na Baitalami?
- A wane lokaci Yusuf ya koma da iyalinsa zuwa ƙasar Isra'ila?
- A wane gari suka zauna?
- Me Yesu ya yi bayan da ya koma Nazarat?
- Yesu yana da shekaru nawa lokacin da shi da iyayensa suka tafi Urushalima don Idi?
- Me Yesu ya ke yi lokacin da ya tsaya a Urushalima?
- Me Maryamu ta ce mashi lokacin da ta same shi?
- Me Yesu ya amsa mata?
- Me Yesu ya yi bayan da ya koma Nazarat?
- Yesu yana da uba bisa ga jiki?
- Don me Manzo Yohana ya ce da Yesu "Kalma"?
- Yesu, Kalmar Allah ne, yana da farko tare da Allah?
- Kalmar nan yana da tunani da iko nashi, dabam ne daga na Uba?
- Yesu ya zama mutum domin ya ba masu gaskatawa da sunansa menene?
DARASI NA GOMA SHA HUƊU: ƊAN RATO YA FITO
Almasiu sarke da limami ne: Kamar su Isseniyawa waɗanda ya zauna da su, Yohana Maibabtisma ba ya yi aure ba, ba y sha giya ba, ya kuwa ci farori gasassu. Kamar su kuma, ya ce: Ni ne "muryar mai kira a jeji na cewa, ku shirya wa Ubangiji tafarki." Kamar su, ya yi wa'azin shari'ar Allah mai zuwa, wadda za ta raba dawa daga ƙaiƙai, za ya hallaka masu mugunta da wuta. Su Isseniyawa sun yi aikin tuba, sun kuwa yi babtisma. Aka yi babtisma tasu kowace rana, amma aka yi babtisma ta Yohana sai sau guda, lokacin da mutum zai yi kasaitacciyar tuba.
Yohana ya zo, yana shelar zuwan Almasihu wanda ya ke tukuna cikin duniya, amma Isseniyawa suna jiran ba almasihu ɗaya ba, amma biyu ne: na ɗaya limami, jikan Haruna da Lawi ne, na biyu sarki, jikan Audu da na Yahuda ne. A lokacin nan an yarda sai jikokin Haruna su zama limamai. Saboda haka, Isseniyawa ba su iya gane ba yadda almasihu ɗaya, jikan Audu da sarki ne, zai zama limami kuma. Wasika zuwa ga Ibraniyawa, wadda aka rubuta ta saboda Isseniyawa waɗanda su ke zama Kirista, ta ba da amsar wuyarsu. Domin ku gane abin da Wasika zuwa ga Ibraniyawa ta ce, ku koma yanzu, ku karanta labarin Malkizadik, wanda ya gai da Ibrahim bayan da Ibrahim ya komo daga yaƙi inda ya yi nasarar sarakuna waɗanda suka kama ɗan'uwansa Lot ne:
18Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato, Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki. 19Ya kuwa sa wa Abram albarka ya ce, "Shi wanda ya yi sama da ƙasa, Allah Maɗaukaki ya sa wa Abram albarka. 20Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!" Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka. (Farawa 14: 18-20).
Ga kuma annabci na Zabura 110:
Yahweh ya ce da ubangijina,
"Zauna a kursiyin dama da ni. * Na mai da magabtanka kujera, * matashin ƙafafunka." Ya ƙera sandarka mai nasara, * Yahweh na Sihiyona ya koɗa ta. Shi Ikonka ne a cikin yaƙin magabtanka, * Ƙarfinka kuma a ranar nasararka. Tsattsarkan Mai Tallafinka ya bayyana, * Asubahin rayuwarka * Raɓar ƙuruciyarka. Yahweh ya rantse, * ba ma zai canza nufinsa ba: "Kai firist ne na Madauwami, * bisa ga alkawalinsa, hakikantaccen sarkinsa [= Malkizadek], ubangijina, * yadda hannun damanka ya shaida." Ya runtumi sarakuna a ranar hushinsa, * ya karya al'ummai. Ya jibge gawarwaki, * ya rafke kawuna * a bisa ƙasa mai fāɗi. Mai Zaɓen Sarakuna ya naɗa shi, * Maɗaukakin Zati ya ɗaga matsayinsa. Yanzu ga yadda Wasika zuwa ga Ibraniyawa ta amsa wuyar Isseniyawa:
Karatu: Ibraniyawa 7:1-28
1Shi wannan Malkisadik, Sarkin Urushalima, firist na Allah Maɗaukaki, ya gamu da Ibrahim a lokacin da Ibrahim yake dawowa daga kisan sarakuna, ya sa masa albarka. 2Shi ne kuwa Ibrahim ya ba shi ushirin kome. Da farko dai, kamar yadda ma'anar sunansa take, shi sarkin adalci ne, sa'an nan kuma Sarkin Urushalima ne, wato, sarkin salama. 3Shi ba shi da uwa ko uba, ba a kuma san asalinsa ba. Ba shi da ranar haihuwa balle ranar mutuwa, yana dai kama da Ɗan Allah, firist ne har abada.
4Kai, ku dubi irin girmansa! Har kakanmu Ibrahim ma ya ba shi ushirin ganima! 5Ga shi kuma, waɗansu na zuriyar Lawi, in sun sami matsayin firist, akan umarce su bisa ga Shari'a su karɓi ushiri a gun jama'a, wato a gun 'yan'uwansu, ko da yake su ma zuriyar Ibrahim ne. 6Amma wannan, wanda ma ba a asalin Lawi yake ba, ya karɓi ushiri a gun Ibrahim, har ya sa masa albarka, shi ma da aka yi wa alkawarai. 7Ai, ba abin musu ba ne, cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. 8Ga shi, a nan masu karɓar ushiri, mutane ne masu mutuwa, a can kuwa mai karɓar wanda aka shaida shi, rayayye ne. 9A ma iya cewa ko Lawi ma da kansa, mai karɓar ushiri, ya ba da ushiri ta wurin Ibrahim, 10don shi Lawi yana daga tsatson kakansa Ibrahim, sa'ad da Ibrahim ɗin ya gamu da Malkisadik.
11Gama da a ce kammala tana samuwa ta wurin firistoci na zuriyar Lawi (don ta gare su ne jama'a suka karɓi shari'a), wace bukata kuma ake da ita ta wani firist dabam ya bayyana kwatancin ɗabi'ar Malkisadik, wanda za a ambata ba kwatancin ɗabi'ar Haruna ba? 12Domin in an sauya matsayin firistoci, sai tilas a sauya Shari'a kuma. 13Domin kuwa shi wannan da aka faɗi waɗannan abubuwa a game da shi, ai, na wata kabila ne dabam, wadda ba waninta da ya taɓa hidimar bagadin hadaya. 14Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba a game da kabilar nan a kan zancen firistoci.
15Wannan kuma ya ƙara fitowa fili sosai, sa'ad da wani firist dabam ya bayyana kamar Malkisadik, 16wanda kuwa ya zama firist, ba bisa ga wata ka'ida ta al'adar 'yan adam ba, sai dai ta wurin ikon rai marar gushewa. 17Domin an shaide shi shi da cewa, "Kai firist ne na har abada, Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik."
18Ta wani hali an soke wani umarni ta dā saboda rauninsa da kuma rashin amfaninsa, 19don Shari'a ba ta kammala kome ba, ta wani hali kuma an shigo da wani bege wanda yake mafi kyau, ta wurinsa kuwa muke kusatar Allah.
20Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. 21Waɗancan sun zama firistoci, ba tare da an yi musu rantsuwa ba, amma wannan kam, sai da aka yi masa rantsuwa, da Allah ya ce masa, "Ubangiji ya rantse, Ba kuwa zai ta da maganarsa ba cewa, 'Kai firist ne har abada.' "
22A sanadin wannan ne Yesu ya zama lamunin alkawarin da ya fi wancan nesa.
23Waɗancan firistoci, an yi su da yawa, domin mutuwa ta hana su tabbata a aikin. 24Amma shi da yake madawwami ne, yana da matsayinsa na firist wanda ba ya komawa hannun wani. 25Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.
26Irin babban firist wanda muke bukata ke nan, mai tsarki, marar aibu, marar cikas, keɓaɓɓe daga masu zunubi, ɗaukakke kuma birbishin sammai. 27Ba zai miƙa hadaya kowace rana kumar waɗancan manyan firistocin ba, wato, da farko saboda zunubansa, sa'an nan kuma saboda na jama'a. Wannan ya yi ta ne sau ɗaya tak, lokacin da ya miƙa kansa hadaya. 28Wato shari'a tana sa mutane su zama manyan firistoci duk da rauninsu, amma maganar nan ta rantsuwa da ta sauko bayan Shari'a, ta sa Ɗa wanda yake kammalalle har abada.
Karatu: Matiyu 3:1-17
Wa'azin Yohana Maibabtisma: 1A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya, 2yana cewa, "Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato." 3Wannan shi ne wanda Annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce,
"Muryar mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji tafarki, Ku miƙe hanyoyinsa.' "
4Yahaya kuwa yana saye da tufa ta gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma. 5Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk ƙasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurinsa, 6yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.
7Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, "Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8Ku yi aikin da zai nuna tubarku. 9Kada kuwa ku ɗauka a ranku cewa, Ibrahim ne ubanku, domin ina gaya muku, Allah yana da ikon ya halitta wa Ibrahim 'ya'ya daga duwatsun nan. 10Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar bata bada 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.
11"Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. 12Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar bituwa."
Babtismar Yesu: 13A lokacin nan ne Yesu ya zo daga ƙasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma. 14Yahaya kuwa ya so ya hana shi, ya ce, "Ni da nake bukatar kai ka yi mini baftisma, ka zo gare ni?" 15Amma Yesu ya amsa masa ya ce, "Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci." Sa'an nan Yahaya ya yardar masa. 16Da aka yi wa Yesu baftisma, nan da nan da ya fito daga ruwan, sai ga sama ta dāre, ya ga Ruhun Allah yana saukowa da kamar kurciya, har ya sauka a kansa. 17Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, "Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai."
Bayyani
Mutane sun karɓi babtismar Yohana kamar alamar tuba, don a gafarta musu zunubansu (Lk 3:3). Yesu ya karɓi babtismar Yohana domin a cika dukan aikin gaskiya (Mt 3:15), watau domin a cika adalci duka. Azancin "gaskiya" ko "adalci" ɗin shi ne yin daidai ga Allah da ƙin zunubi. Yesu ba shi da zunubi, amma ya zama sarkin dukan mutane, da ya kamata ya ƙi zunubi saboda dukan 'yan'adam. Bulus ya ce: "15Amma fa baiwar nan dabam take ƙwarai da laifin nan. Ai, in laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa masu ɗumbun yawa mutuwa, ashe ma, alherin Allah, da kuma baiwar nan, albarkacin alherin Mutum ɗaya, Yesu Almasihu, sai su yalwata ga masu ɗumbun yawa fin haka ƙwarai... 19Kamar yadda masu ɗumbun yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma ta wurin biyayyar Mutum ɗaya za a mai da masu ɗumbun yawa masu adalci. Adamu ya yi laifi, ya kuwa ba duk 'ya'yansa laifi. Yesu ya ƙi laifin duk 'yan'Adam cikin babtismarsa, ya kuwa miƙa musu rai. Watau, cikin babtisma wadda ya kafa, ya kan ba da Ruhu Tsattsarka, wanda ya kan tsabtace, ya kuwa kan raya kamar wuta (Mt 3:11).
Karatu: Luka 4:1-13
Shaiɗan ya gwada Yesu:
1Yesu kuma cike da Ruhu Mai Tsarki sai ya dawo daga Kogin Urdun. Ruhu yana iza shi zuwa jeji, 2har kwana arba'in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa. 3Iblis ya ce masa, "In dai kai Ɗan Allah ne, ka umarci dutsen nan ya zama gurasa," 4Yesu ya amsa masa ya ce, "A rubuce yake, 'Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba.' " 5Sai Iblis ya kai shi wani wuri a bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkokin duniya a ƙyiftawar ido. 6Iblis ya ce masa, "Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, nakan kuma bayar ga duk wanda na ga dama. 7In kuwa za ka yi mini sujada, duk za su zama naka." 8Yesu ya amsa masa ya ce, "A rubuce yake cewa, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai za ka bauta wa.' " 9Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, "In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan, 10don a rubuce yake cewa, 'Zai yi wa mala'ikunsa umarni a game da kai, su kiyaye ka,' 11da kuma 'Za su tallafe ka, Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.' " 12Sai Yesu ya amsa masa ya ce, "Ai kuwa an ce, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.' " 13Bayan da Iblis ya gama irin dukan gwaje-gwajensa, ya rabu da shi ɗan lokaci tukuna.
Bayyani
Bayan babtisma, Yesu ya ci gwadawar kwana arba'in domin ya cika misalin Isra'ilawa waɗanda suka ƙetare Jan Teku (ƙetarensu kamar babtisma ne) da aka gwada su cikin tafiyarsu shekaru arba'in cikin jeji. Isra'ilawa ba su ci jarabawa sosai ba, amma Yesu ya yi nasarar Shaiɗan.
Akwai kamani kuma tsakanin jarabawar Hawa'u da ta Yesu da na abin da Manzo Yohana ya faɗi a kan iri dabam dabam na jarabawa. Ga kamani:
Farawa 3:6 Lk 4:1-13 1 Yohana 2:16 Macen ta lura itacen Shaiɗan ya ce Yesu Duk abin da ke duniya: Yana da kyau domin ci ya mai da dutse burodi burin-zuciya, Abin sha'awa ga idanu ya karɓi mulkin duniya muguwar sha'awar ido, Abin marmari domin ba da hikima. Ya dira ƙasa a gaban idon mutane
banda samun rauni.Alfarmar banza ne. Karatu: Yohana 1:35-51
Almajiran Yesu na fari: 35Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu. 36Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, "Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!" 37Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suke bi Yesu. 38Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, "Me kuke nema?" Suka ce masa, "Ya Rabbi, wato, Malam ke nan, ina kake da zama?" 39Sai ya ce musu, "Ku zo ku gani." Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa. 40Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan'uwan Bitrus. 41Sai ya fara nemo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, "Mun sami Almasihu," wato, shafaffe. 42Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, "Wato, kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas," wato, Bitrus.
43Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, "Bi ni." 44Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus. 45Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, "Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato, Yesu Banazare, ɗan Yusufu." 46Nata'ala ya ce masa, "A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?" Sai Filibus ya ce masa, "Taho dai, ka gani." 47Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, "Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!" 48Nata'ala ya ce masa, "A ina ka san ni?" Yesu ya amsa masa ya ce, "Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka." 49Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, "Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!" 50Yesu ya amsa ya ce, "Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al'amuran da suka fi haka ma." 51Yesu kuma ya ce masa, "Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum."
Bayyani
A cikin su almajiran Yesu na fari, na ɗaya Andarawas ne, na biyu Yohana Manzo ne, ko ba a ambaci sunansa ba. Cin bishararsa, Yohana bai taɓa ambatan sunansa; sai ya ce: ni ne "almajirin da Yesu ke ƙauna."
Natana'ilu ɗin duk ɗaya ne da Bartalamawas. Lalle cikin inuwar ɓaure yana hanga, yana tunani a kan zuwan Almasihu. Yesu ya karanta zuciyarsa; saboda haka, Natana'ilu ya yi mamaki, ya kuwa ba da gaskiya.
"Masihi" ko "Almasihu" duk ɗaya ne da Kristo, watau "shafaffe" kamar sarki. Ma'anar "Bitrus" dutse ne.
Domin ka gane maganar mala'ikun suna hawa da sauka, sai ka koma zuwa labarin Yakubu. Kamin da Allah ya yi masa alkawarin ubansa Ibrahim, akwai wannan labarin Farawa 28:10-12:
10Yakubu ya bar Biyer-sheba ya kama hanya zuwa Haran. 11Da ya isa wani wuri, sai ya kwana can a wannan dare, don rana ta riga ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun da suke wurin, ya yi matashin kai da shi, ya kwanta, ya yi barci. 12Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala'ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa!
Cikin maganarsa, Yesu ya mai da kansa tsani wanda ya haɗa sama da ƙasa. Ta wurinsa ana hawa zuwa wurin Allah Uba, alherin Allah ma yana saukowa gare mu.
Tambayoyi
- Don me Isseniyawa su ke jiran almasihu biyu?
- Wanene Malkizadik?
- Almasihu limami ne, kwatankwacin wanene?
- A wane wuri Yohana ya yi wa'azinsa?
- A wane wuri ya yi babtisma?
- Yohana ya yi babtisma saboda me?
- Yohana ya ce mai zuwa bayanshi zai yi babtisma da me?
- Me Yohana ya ce lokacin da Yesu ya biɗui babtisma daga wajensa?
- Don me Yesu ya so a yi mashi babtisma?
- Da Yesu ya fito daga ruwa, me aka ga yana sauko daga sama?
- Me aka ji daga sama?
- Yesu ya zauna cikin jeji yana azumi kwana nawa?
- Me Iblis ya ce Yesu shi yi da dutse?
- Me Yesu ya amsa?
- Me Iblis ya nuna wa Yesu daga wuri nan a bisa?
- Wane irin dukiya Iblis ya miƙa wa Yesu?
- Me Yesu ya amsa?
- Me Iblis ya ce Yesu shi yi a bisa tsororuwar Ɗakin Ibada?
- Me Yesu ya amsa?
- Su wanene almajirai biyu na Yohana Maibabtisma waɗadanda suka ratse bin Yesu?
- Siman ɗan'uwan wanene?
- Ina sunan da Yesu ya ba Siman?
- Filibus ya yi menene bayan da ya sadu da Yesu?
- Me Natana'ilu ya ce a kan Nazarat?
- Me Filibus ya amsa?
- Me ya sa Natana'ilu ya ce wa Yesu, "Kai Ɗan Allah ne"?
DARASI NA GOMA SHA BIYAR: SHAIDA
Karatu: Yohana 2:1-11
Mu'ujiza a Kana: 1A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana nan, 2aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa. 3Da ruwan inabi ya gaza, mahaifiyar Yesu ta ce masa, "Ba su da sauran ruwan inabi." 4Yesu ya ce mata, "Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna." 5Sai mahaifiyar Yesu ta ce wa barorin, "Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi." 6A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al'adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce tana cin wajen tulu shida shida. 7Sai Yesu ya ce musu, "Ku cika randunan nan da ruwa." Suka ciccika su fal. 8Sa'an nan ya ce musu, "To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin." Sai suka kai. 9Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango, 10ya ce, "Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa'an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!"
11Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.
Bayyani
Yesu ya yi mu'ujizar nan na fari saboda roƙon mammarsa. Ya ce sa'arsa bai zo tukuna ba. Nufin "sa'arsa" lokacin ɗaukakarsa ta wurin mutuwa da tashinsa ke nan. Cikin mu'ujizar da ya yi, Yesu ba ya nuna cikakkiyar ɗaukakarsa ba, amma ya nuna ikonsa da alamar ɗaukakarsa mai zuwa ta tashinsa.
Yesu ya ce da Maryamu "iya", watau "mace" ke nan idan an juya daidai daga harshen Girik. Lokacin da yana rataya bisa giciye, Yesu ya ce duk ɗaya ne wa Yohana: "Iya (ko mace), ga ɗanki nan" (Yn 19:26). Ana yin kamani da maryamu da Hawa'u (Duba darasi na fari). Kamin da Adamu ya ce da matarsa "Hawa'u", an kira ta "mace" kawai. Hawa'u ta zama tataimakiyar Adamu cikin zunubi. Maryamu ta zama mataimakiyar Yesu cikin aikin ceto. An ba matar Adamu sunan "Hawa'u" domin, bisa ga ma'anarsa cikin harshen Libranci, ta zama "uwar masu rai duka" (Far 3:20). Hakanan, saboda ta haifi Macecin mutane, Maryamu ta zama mammar dukan masu ba da gaskiya ga Yesu.
Cikin mu'ujizar da ya yi a Kana, Yesu ya nuna kuma ya yarda da bikuna har da shan giya—ruwan inabi irin giya ne—idan za a sha da hankali; ba ya yarda da maye ba.
Bayan mu'ujizar a Kana, Yesu ya nuna ikonsa da ƙaunarsa ga mutane cikin waɗansu mu'ujizai na warkewa. Ga labarin:
Karatu: Markus 1:21-45
Yesu ya warkad da mai baƙin aljan: 21Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar ne kuwa, ya shiga majami'a yana koyarwa. 22Sun yi mamakin koyarwarsa, domin yana koya musu da Iko, ba kamar malaman Attaura ba. 23Nan take sai ga wani mutum mai baƙin aljan a majami'arsu, yana ihu, 24yana cewa, "Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai tsarkin nan ne na Allah." 25Yesu ya kwaɓe shi ya ce, "Yi shiru! fita daga cikinsa!" 26Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa yana rawa, ya yi ihu, ya fita daga cikinsa. 27Duk suka yi mamaki, har suka tanttambayi juna suna cewa, "Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙuwar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma yake yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya!" 28Nan da nan sai ya shahara a ko'ina duk kewayen ƙasar Galili.
Ya warkad da surukasr Siman Bitrus: 29Da fitarsu daga majami'a, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawas, tare da Yakubu da Yahaya. 30Surukar Bitrus kuwa tana kwance tana zazzaɓi, nan da nan suka ba shi labarinta. 31Sai ya matso, ya kama hannunta, ya tashe ta, zazzaɓin kuwa ya sake ta, har ta yi musu hidima.
32Da magariba, bayan fāɗuwar rana, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, da masu aljannu. 33Sai duk garin ya haɗu a ƙofar gidan. 34Ya warkar da marasa lafiya da yawa, masu cuta iri iri, ya kuma fitar wa mutane aljannu da yawa. Bai ko yarda aljannun su yi wata magana ba, domin sun san shi.
35Da assussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu'a a can. 36Sai Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka bi shi. 37Da suka same shi, suka ce masa, "Duk ana nemanka." 38Ya ce musu, "Mu tafi garuruwan da suke gaba, in yi wa'azi a can kuma, domin saboda haka ne na fito." 39Ya gama ƙasar Galili duk yana wa'azi a majami'unsu, yana kuma fitar wa mutane da aljannu.
Yesu ya warkad da kuturu: 40Wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, yana durƙusawa a gabansa, yana cewa, "In ka yarda kana da iko ka tsarkake ni." 41Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, "Na yarda, ka tsarkaka." 42Nan take sai kuturtar ta rabu da shi, ya tsarkaka. 43Ya kwaɓe shi ƙwarai, ya sallame shi nan da nan, 44bayan ya ce masa, "Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta." 45Amma ya tafi, ya shiga sanar da maganar, yana baza labarin al'amarin ko'ina, har ya zamana Yesu bai ƙara shiga wani gari a sarari ba, sai ya zauna a waje a wuraren da ba kowa. Mutane kuwa suka yi ta zuwa wurinsa daga ko'ina.
Bayyani
Mu'ujizai sun nuna Yesu yana da ikon Allah. Ga kuma shaidar bakin Yohana Maibabtisma:
Karatu: Yohana 3:22-36; Luka 3:13-20; 7:18-23
Shaidar Yohana Maibabtisma: 22Bayan haka, Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin baftisma. 23Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma. 24Domin a sa'an nan ba a sa Yahaya a kurkuku ba tukuna.
25Sai fa almajiran Yahaya suka tasar wa wani Bayahude da muhawwara a kan maganar tsarkakewa. 26Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, "Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa." 27Sai Yahaya ya amsa ya ce, "Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama. 28Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne ni riga shi gaba. 29Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron maganarsa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika. 30Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.
31"Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa. 32Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa. 33Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe, cewa, Allah mai gaskiya ne. 34Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba. 35Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa. 36Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi."
An tsare Yohana Maibabtisma: Lk 3: 18Ta haka, da waɗansu gargaɗi masu yawa, Yahaya ya yi wa jama'a bishara. 19Amma sarki Hirudus, wanda Yahaya ya tsawata wa a kan maganar Hirudiya, matar ɗan'uwansa, da kuma dukan mugayen ayyukan da ya yi, 20sai ya ƙara da kulle Yahaya a kurkuku.
Yohana Maibabtisma ya yi tambaya: 7: 18Sai almajiran Yahaya suka gaya masa dukan abubuwan nan. 19Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya cewa, "Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?" 20Da mutanen nan suka isa wurinsa, suka ce, "Yahaya Maibaftisma ne ya aiko mu a gare ka, yana tambaya, cewa, 'Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?' " 21Nan tāke Yesu ya warkar da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani. 22Sai ya amsa musu ya ce, "Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka gani. Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara. 23Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni."
Bayyani
Yohana Maibabtisma ya yarda banda shakka Yesu ne Almasihu. Duk da haka, ya tambaya, "Kai ne Maezuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?" Ga nufinsa: "Idan kai ne Almasihu, don me ba ka yin aikin Almasihu?" Watau, Yohana, kamar yawacin Yahudawa na zamaninsa, ya tsamanta Almasihu zai zo da girma da daraja, zai shar'anta duniya da wuta (Ga Mt 3:11-12). Yesu ya amsa yana ambaton kalmomin Ishaya 61:1-2, waɗanda a wani lokaci, cikin majami'ar Nazarat, ya ce aka rubuta su a kan shi:
Lk 4:18"Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne, 19In yi shelar zamanin samun karɓuwa ga Ubangiji."
Watau, aikin jinƙai da Yesu ya ke yi shaida ne mai dacewa da Almasihu. Ya ƙara cewa, "Albarka ta tabbata ga wanda ba ya ƙosawa da ni." Watau, kada mutum shi damu idan Almasihu ba ya shar'anta duniya tukuna. In ji Yesu: "Allah bai aiko Ɗansa duniya ya yanke mata hukunci ba, sai dai don duniya ta sami ceto ta hanyarsa" (Yn 3:17). Zai yi shari'ar duniya, amma sai ya sake zuwa a ƙarshen duniya. In ji Bulus: "1Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanɗa zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanarsa da kuma mulkinsa, 2ka yi wa'azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa" (2 Tim 4:1-2).
Karatu: Mark 6:17-29
Mutuwar Yohana Maibabtisma: 17Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan'uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura. 18Don dā Yahaya ya ce wa Hirudus, "Bai halatta ka ƙwace matar ɗan'uwanka ba." 19Hirudiya kuwa tana riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba, 20don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake yana murna da jinsa. 21Amma wani sanadi ya zo, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, ya yi wa hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan ƙasar Galili biki. 22Da 'yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta gamshi Hirudus da baƙinsa. Sai fa sarki ya ce wa yarinyar, "Ki roƙe ni kome, sai in ba ki." 23Ya kuma rantse mata, ya ce, "Kome kika roƙe ni zan ba ki, ko da rabin mulkina ne." 24Ta fita, ta ce wa mahaifiyarta, "Me zan roƙa?" Uwar ta ce, "Kan Yahaya Maibaftisma." 25Nan da nan sai ta shigo wurin sarki da gaggawa, ta roƙe shi, ta ce, "Ina so yanzu yanzu ka ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi." 26Sai sarki ya yi baƙin ciki matuƙa, amma saboda rantsuwar da ya yi da kuma kunyar baƙinsa, ba ya so ya hana ta. 27Nan take sai sarki ya aiki dogari, ya yi umarni a kawo kan Yahaya. Dogarin ya tafi ya fille wa Yahaya kai a kurkuku, 28ya kawo kan a cikin akushi, ya ba yarinyar, yarinyar kuwa ta ba mahaifiyarta. 29Da almajiran Yahaya suka ji labari, sai suka zo suka ɗauki gangar jikinsa, suka sa ta a kabari.
Bayyani
Hakanan ne shaidar Yohana Maibabtisma mai girma. Bayan haka, waɗansu Yahudawa suka zargi Yesu saboda ya warkad da marar lafiya a ran Asabas. Yesu ya amsa, ya nuna shaidu uku masu hakikanta shi ya zo aikakke dag Allah Uba:
Karatu: Yohana 5:31-47
Daga Yohana Maibabtisma: 31In na shaida kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce. 32Akwai wani mashaidina dabam, na kuwa san shaidar da yake yi a kaina tabbatacciya ce. 33Kun aika wajen Yahaya, shi kuma ya shaidi gaskiya. 34Duk da haka shaidar da na dogara da ita ba ta mutum ba ce. Na dai faɗi haka ne domin ku sami ceto. 35Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.
Daga mu'ujizai: 36Amma shaidar da ni nake da ita ta fi ta Yahaya ƙarfi. Domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da nake yi, ai, su ne shaidata a kan cewa, Uba ne ya aiko ni. 37Uban kuma da ya aiko ni, shi kansa ya shaide ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ko ganin kama tasa. 38Maganarsa kuwa ba ta zauna a zuciyarku ba, domin ba ku gaskata wanda ya aiko ba.
Daga annabawa: 39Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata. 40Duk da haka, kun ƙi zuwa wurina ku sami rai. 41Ba na karɓar girma wurin mutane. 42Amma fa na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci. 43Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa. 44Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa? 45Kada ku zaci zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. 46Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, domin labarina ya rubuta. 47In kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?"
Bayyani
"Musa ya rubuta labarina," in ji Yesu. Watau, bisa ga tsamanin mutanen zamanin Yesu, Musa ya rubuta littattafai biyar na fari na Tsofuwar Yarjejeniya, daga Farawa har zuwa Kubuwar Shari'a. Kun ga abin da suka faɗi a batun Yesu cikin darasi na ɗaya har na goma.
Tambayoyi
- A wane wuri Yesu ya mai da ruwa ruwan inabi?
- Me ya sa ya yi haka?
- Me uban biki ya ce bayan da Yesu ya yi mu'ujizar nan?
- Yesu ya yarda baƙaƙen aljannu su yi magana da shi?
- Yesu ya yarda ya zauna wuri ɗaya da mutanen da su ke son shi?
- Me Yohana Maibabtisma ya ce lokacin da almajiransa suka gaya mashi kowa yana bar shi, ana bin Yesu?
- Saboda me an tsare Yohana?
- Ko Hirudus ya so firar Yohana?
- Donme Yohana ya tambayi Yesu ko shi ne Almasihu mai zuwa?
- Ta yaya Yesu ya amsa masa?
- Me ya sa Hirudus ya yi umarni a kashi Yohana?
- Yesu ya ambaci waɗanne shaidu uku masu hakikanta shi Ɗan Allah ne?
DARASI NA GOMA SHA SHIDA: BANGASKIYA
Karatu: Mark 2:1-12
Yesu na gafarta zunubai: 1Bayan 'yan kwanaki, da ya sāke komowa Kafarnahum, sai aka ji labari yana gida. 2Aka kuwa taru maƙil har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa'azin Maganar Allah. 3Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu suna ɗauke da shi. 4Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayyen yake kwance a kai. 5Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce wa shanyayyen, "Ɗana, an gafarta maka zunubanka." 6To, waɗansu malaman Attaura suna nan zaune, suna ta waswasi a zuciyarsu, 7suna cewa, "Don me mutumin nan yake faɗar haka? Ai, sāɓo yake yi! Wa yake da ikon gafarta zunubi in banda Allah kaɗai?" 8Nan da nan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, "Don me kuke a waswasi haka a zuciyarku? 9Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, 'An gafarta maka zunubanka', ko kuwa a ce, 'Tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya?' 10Amma don ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya"mūsasai ya ce wa shanyayyenmūsa 11"Na ce maka, tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida." 12Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a kan idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna, "Ba mu taɓa ganin irin haka ba!"
Bayyani
Lokacin da Yesu ya ce, "An gafarta maka zunubanka," malamai ba su gaskanta ba, suka ce ƙarya ya ke yi. Amma Yesu ya yi abin wuya wanda sai Allah ya iya yi, watau ya warkad da shanyayye. Ta haka, ƙarya ta wuce, ya nuna yana da ikon gafarta zunubi kuma, domin yana da ikon Allah. Jama'a sun gaskanta, amma malamai ba su gaskata ba, ko da ya ke aka yi mamaki mai ganuwa.
Yesu ya ce da kansa "Ɗam Mutum". Da wannan suna, Yesu ya nuna shi ne mutum mai gaske, gama haka ne ma'anar "ɗam mutum". Amma wannan suna kuma ya nuna Yesu ne fiyad da mutum, domin an ɗauka wannan suna daga annabcin annabi Dani'ilu (7:13-14):
13"A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, Aka kai shi gabansa. 14Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa. Mulkinsa, madawwamin mulki ne, Wanda ba zai ƙare ba. Sarautarsa ba ta tuɓuwa." Karatu: Markus 2:13-17
Yesu ya kira Lawi: 13Yesu ya sāke fita bakin teku. Duk jama'a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu. 14Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, "Bi ni." Sai ya tashi ya bi shi.
15Wata rana Yesu yana cin abinci a gidan Lawi, masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa kuma suna ci tare da shi da almajiransa, don kuwa da yawa daga cikinsu masu binsa ne; 16da malaman Attaura na Farisiyawa suka ga yana cin abinci tare da masu zunubi da masu karɓar haraji, sai suka ce wa almajiransa, "Don me yake ci yake sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?" 17Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, "Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi."
Bayyani
Lawi wani sunan Matiyu, mai rubutan bishara ta fari ne. Masu karɓar haraji ba su da tagomashi a cikin mutane, saboda su ke aiki domin su Romawa waɗanda suka kama mulkin ƙasas, kuma domin su ke yin cutar mutane cikin karɓar haraji domin su cika aljihunansu. Yesu ya ci abinci da masu zunubi domin suna da anniyar tuba. A wani wuri ya ce wa manyan malamai, "Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah" (Mt 21:31). Watau, rashin bangaskiya na malamai zunubi ne wanda ya fi na waɗancan girma.
Karatu: Markus 3:1-12
Mai shanyayyen hannu: 1Sai ya sāke shiga majami'a. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. 2Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa. 3Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, "Fito nan fili." 4Ya ce musu, "Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?" Amma sai suka yi shiru. 5Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, "Miƙo hannunka." Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 6Da Farisiyawa suka fita, nan da nan sai suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi.
7Sai Yesu ya tashi tare da almajiransa, suka je bakin tekun. Taro mai yawan gaske kuwa daga ƙasar Galili ya biyo shi, har ma daga ƙasar Yahudiya, 8da Urushalima, da ƙasar Edom, da hayin Kogin Urdun, da kuma wajen Taya da Sidon, babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da yake yi. 9Don gudun kada taron ya marmatse shi kuwa, sai ya ce wa almajiransa su keɓe masa ƙaramin jirgi guda, 10saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta suna dannowa wurinsa domin su taɓa shi. 11Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa'ad da suka gan shi, sai su fāɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, "Kai Ɗan Allah ne." 12Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.
Bayyani
Ga shi, yadda Farisiyawa suka yi haushi lokacin da Yesu ya warkad da mai shanyayyen hannu, amma taron talakawa suka so shi, suka ba da gaskiya.
Karatu: Markus 3:13-30
Manzannin Yesu sha biyu: 13Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa. 14Ya zaɓi mutum goma sha biyu su zauna tare da shi domin ya riƙa aikensu suna wa'azi. 15Ya kuma ba su ikon fitar da aljannu. 16Ga waɗanda ya zaɓa, Bitrus, 17da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan'uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato, 'ya'yan tsawa. 18Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, da Saminu Bakan'ane, 19da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bāshe shi.
Malamai sun zargi Yesu: Sa'an nan ya shiga wani gida. 20Taron kuwa ya sāke haɗuwa har ya hana su cin abinci. 21Da 'yan'uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, "Ai, ya ruɗe." 22Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, "Ai, Ba'alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu." 23Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, "Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan? 24Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba. 25Haka in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba. 26Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewarsa ce ta zo. 27Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa'an nan kuma ya washe gidansa.
28"Hakika, ina gaya muku, za a gafarta wa 'yan adam duk zunubansu, da kowane sāɓon da suka hurta, 29amma fa, duk wanda ya sāɓi Ruhu Mai Tsarki ba ya samun gafara har abada, ya yi madawwamin zunubi ke nan." 30Wannan kuwa don sun ce, "Yana da baƙin aljan ne."
Bayyani
Zargen malamai zunubin ƙin haske ke nan. Saboda haka, an ce suka saɓi Ruhu Tsattsarka. Da sauran duk zunubai mutum ba y rena sarautar Allah ba, kamar missali, lokacin da ya ke wasa, ko yana fushi, ko lokacin da mutane suka yi wa Yesu laifi saboda abin da ya yi kamar mutum ne, suna cewa: "Ga nan mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi" (Lk 7:34). A batun wannan irin zunubi, in ji Yesu: "Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa". —Mai yin wannan irin zunubi yana da kaɗan tsoron Allah tukuna, kirkinsu ba ya mutu ba sam-sam; to, suna iya warke.— "amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba (Lk 12:10)," saboda ya ƙi sarautar Allah, ba shi da tsoronshi ko kaɗan, yas mutu sosai, ba y iya warke ba, sai Allah ya yarda ya yi mu'ujiza, ya raya matacce.
Karatu: Markus 3:31-35
31Sa'an nan mahaifiyarsa da 'yan'uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa ya je. 32Taro kuwa yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, "Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna nemanka a waje." 33Ya amsa musu ya ce, "Su wane ne tsohuwata da 'yan'uwana?" 34Sai ya waiwayi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, "Ga tsohuwata a nan da 'yan'uwana! 35Ai, kowa ya yi abin da Allah ke so, shi ne ɗan'uwana, ita ce 'yar'uwata, ita ce kuma tsohuwata."
Bayyani
Su 'yan'uwan Yesu lalle duk ɗaya ne da su waɗanda aka ambata cikin labarin malamai masu zargen Yesu nan bisa, watau su 'yan'uwa suka fita su kamo Yesu, suka ce, "Ai ya ruɗe." A batunsu, Yohana (7:3-5) ya ba da labari: "3Sai 'yan'uwansa suka ce masa, "Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi. 4Ai, ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da yake kana yin waɗannan al'amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya." 5Domin ko dā ma 'yan'uwansa ba su gaskata da shi ba.
Amma Maryamu da waɗansu 'yan'uwan Yesu kaɗan ne sun gaskata da shi. Amma tun da suna tare da sauran 'yan'uwa marasa gaskata da shi, Yesu ba ya rena su ba, ba y yabe su ba; sai ya yarda kowa ya yi abin da Allah ke so, shi ne danginsa. Watau, dangin ruhu ya fi dangin jiki. Maryamu mai albarka biyu ce, domin ta haɗu da Yesu saboda jiki da kuma saboda ruhu ta wurin bangaskiya.
Tambayoyi
- Ta yaya shanyayyen mutum ya shiga gida inda Yesu ya ke?
- Me Yesu ya ce mashi?
- Me malaman Attaura suka ce a zuciyarsu?
- Ta yaya Yesu ya nuna yana da ikon gafarar zunubai?
- Don me Yesu ya ce da kansa "Ɗam Mutum"?
- Ina aikin Lawi ɗan Alfayas?
- Ina wani sunansa?
- Me ya rubuta?
- Don me mutanen ƙasar Yesu suka rena masu karɓar haraji? (Akwai dalilai biyu.)
- Don me Yesu ya ci da ya sha tare da masu zunubi?
- Don me zunubin malamai ya fi na karuwai da na sauran masu zunubi sharri?
- Menene saɓon Ruhu Tsattsarka?
- Don me wanda ya saɓi Ruhu Tsattsarka ba za a gafarta masa ba?
- 'Yan'uwan Yesu suka gaskata da shi?
- Yesu ya ce su wanene 'yan'uwansa ne da gaske?
SASHI NA BIYU NA SABUWAR YARJEJENIYA: KOYAWAR YESU
Yar yanzu an ga yaya ta wurin mu'ujizansa Yesu ya nuna kansa aikakke ne daga Allah Uba. Ya zo da ikon Allah domin ya koya mana hanyar ceto, ya kuwa jawo mu cikin hanyar ceto, tun da shi shugabammu da matsakiyarmu ne ga Allah.
Cikin sashin nan na biyu na Sabuwar Yarjejeniya za a duba sabuwar shari'a, watau koyawar Yesu a batun hanyar ceto. Cikin sashi na uku za a duba mutuwar da tashin Yesu. Cikin sashi nas huɗu za a duba asiran Ikiliziya da na sakramenti.
DARASI NA GOMA SHA BAKWAI: SABUWAR SHARI'A
"Saurara, ke ɗiya, ki gani, * ki kasa kunne" (Zb 45:11a). Ga babban jawabin Yesu: Karatu: Luka 6:17-26
Jama'a ta tattaru: 17Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da suke bakun bahar, waɗanda su zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu. 18Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su. 19Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
Hanyar albarka da hanyar wahala: 20Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce,
"Albarka tā tabbata a gare ku, ku matalauta, domin Mulkin Allah naku ne.
21"Albarka tā tabbata a gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da ku.
"Albarka tā tabbata gare ku, ku da ke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.
22"Albarka tā tabbata a gare ku sa'ad da mutane suka ƙi ku, suka kama ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum. 23Ku yi farin ciki a wannan rana, ku yi tsalle don murna, domin ga shi, sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.
24"Amma kaitonku, ku masu arziki domin kun riga kun sami taku ta'aziyya.
25"Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa.
"Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.
26"Kaitonku in kowa yana yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya."