LINJILA

SABON ALKAWARIN
UBANGIJIMMU
YESU ALMASIHU
MACECIMMU

Bible Society, 1961

—meant especially for Kano and the Hausa heartland—


BISHARA TA HANNUN
MATIYU

1

Salsalar Yesu

Littafin salsalar Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, bani Ibrahim ke nan.

2 Ibrahim ya haifi Isiyaku, Isiyaku ya haifi Yakubu, Yakubu ya haifi Yahuda da ’yan’uwansa, 3 Yahuda kuwa ya haifi Farisa da Zaraha, ’ya’yayan Tamara, Farisa ya haifi Hasaruna, Hasaruna ya haifi Arama, 4 Arama ya haifi Aminadabu, Aminadabu ya haifi Nabashuna, Nahashuna ya haifi Salmuna, 5 Salmuna ya haifi Bu'azu, ɗan Rahaba, Bu'azu ya haifi Obida, ɗan Ra'uta, Obida ya haifi Yassa, 6 Yassa ya haifi Sarki Dawuda.

Dawuda kuma ya haifi Sulaimanu, dam matar Uriya, 7 Sulaimanu ya haifi Rahabama, Rahabama ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa, 8 Asa ya haifi Yahushafata, Yahushafata ya haifi Yuramu, Yuramu ya haifi Uzaya, 9 Uzaya ya haifi Yutamu, Yutamu ya haifi Ahazu, Ahazu ya haifi Hizikiya, 10 Hizikiya ya haifi Manassa, Manassa ya haifi Amunu, Amunu ya haifi Yushiya. 11 Yushiya ya haifi Yakunya da ’yan’uwansa, wato a lokacin da aka ɗebe su zuwa Babila.

12 Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yakunya ya haifi Sha’altilu, Sha’altilu ya haifi Zarubabila, 13 Zarubabila ya haiƙ Abihuɗu, Abihuɗu ya haifi Aliyakimu, Aliyakimu ya haifi Azuru, 14 Azuru ya haiƙ Saduƙu, Saduƙu ya haifi Akimu, Akimu ya haifi Aliyudu, 15 Aliyudu ya haifi Ali’azaru, Ali’azaru ya haifi Matanu, Matanu ya haifi Yakubu, 16 Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda a ke kira Almasihu.

11 Wato dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai su Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Kuma daga ɗebe su zuwa Babila.

12 Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yakunya ya haifi Sha’altilu, Sha’altilu ya haifi Zarubabila, 13 Zarubabila ya haifi Abihuɗu, Abihuɗu ya haifi Aliyakimu, Aliyakimu ya haifi Azuru, 14 Azuru ya haifi Saduƙu, Saduƙu ya haifi Akimu, Akimu ya haifi Aliyudu, 15 Aliyudu ya haifi Ali’azaru, Ali’azaru ya haifi Matanu, Matanu ya haifi Yakubu, 16 Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda a ke kira Almasihu.

17 Wato dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai su Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Kuma daga ɗebe su zuwa Babil zuwa kan Almasibu, zuriya goma sha huɗu.

HAIFUWAR YESU

18 To, ga yadda haifuwar Yesu Almasihu ta ke. Sa’ad da aka yi wa Yusufu baiwa da uwatasa Maryamu, tum ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Tsattsarka. 19 Yusufu mijinta kuwa da ya ke mutun ne mai gaskiya, ba ya kuma so ya ba ta kunya a gaban jama’a, sai ya yi niyyar rabuwa da ita a asirce. 20 Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi cikin mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, don cikin nan nata daga Ruhu Tsattsarka ne. 21 Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, don shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” 22 An yi wannan ne duk don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin Annabi Ishaya, cewa,

23 “Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa,
Kuma za a sa masa suna Immanu’el.”
(Ma’anar Immanu’el kuwa, Allah na tare da mu).

24 Da Yusufu ya farka daga barci, sai ya be umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki matatasa, 25 amma bai san ta ’ya mace ba, har bayan ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.

2

Masana daga Gabas

To, sa’ad da aika haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin Sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, 2 “Ina wanda aka haifan nan Sarkin Yahudawa ya ke? Don mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo yi masa sujada.” 3 Da Sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukkan mutanen Urushalima. 4 Sai ya tara dukkan manyan malamai da malaman Attaura na jama’a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu. 5 Sai suka ce masa, “A Baitalami ne ta ƙasar Yahudiya, don haka Annabi Miƙa ya rubuta, cewa,

6 ‘Ke kuma ya Baitalami, ta ƙasar Yahuda,
Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta ba a cikin manyan garuruwan Yahuda,
Don daga cikinki za a haifi wani mai mulki,
Wanda zai zama makiyayin jama’ata Bani Isra’ila.’”

7 Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbatar daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana. 8 Sa’an nan ya aike su Baitalami, ya ce, “Ku je ku binciko mini ɗan yaron nan sarai. In kun same shi, ku kawo mini labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” 9 Su kuwa da suka ji maganar sarki, sai suka yi tafiyarsu. Ga shi kuwa tauraron da suka gani a gabas na tafe a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda ɗan yaron nan ya ke. 10 Da suka ga tauraron sai suka yi farinciki gaya matuƙa. 11 Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron tare da uwatasa Maryamu, suka faɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya da lubban da mur. 12 Amma da aka gargaɗe su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suk koma ƙasarsu ta wata hanya daban.

Gudu zuwa Masar

13 To, da suka tashi, sai ga wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da uwatasa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na waiwaye ka, don Hirudus na shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.” 14 Yusufu kuwa ya tashi ya ɗauki ɗan yaron da uwatasa da dad dare, ya tafi Masar, 15 ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin Annabi Hosiya, cewa, “Daga Masar na kirawo Ɗana. “

16 Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika aka karkashe dukkan ’yan yara maza da ke Baitalaml da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon tsawon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan. 17 A lokacin ne aka cika faɗar Annabi Irimiya, cewa,

18 “An ji wata murya a Rama,
Da kuka da kuma gunji,
Rahila ce ke kuka saboda ’ya’yayanta.
Ta ƙi a sanyaya mata zuciya, don ba su.”

Komowa Nazarat

19 Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce, 20 “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da uwatasa, ka tafi ƙasar Bani Isra’ila, don masu neman ran ɗan yaron sun mutu.” 21 Sai ya tashi, ya ɗauki ɗan yaron da uwatasa, ya zo ƙasar Bani Isra’ila. 22 Amma da ya ji Arkilayas ya gaji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya janye zuwa ƙasar Galili. 23 Sai ya je ya zauna a wani gari wai shi Nazarat, don a cika faɗar annabawa, cewa, “Za a kira shi Banazare.”

3

Wa’azin Yohana Maibabtisma

A wannan zamanin ne Yohana Maibabtisma ya zo, yana. wa’azi a jejin Yahudiya, 2 yana cewa, “Ku tuba, don Mulkin Sama ya kusato.” 3 Wannan shi ne wanda Annabi Ishaya ya yi maganarsa ya ce,

“Muryar mai kira a jeji na cewa,
Ku shirya wa Ubangiji tafarki,
Ku miƙe hanyoyinsa.”

4 Yohana kuwa na saye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da warki, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma. 5 Sai mutanen Urushalima, da na dukkan Yahudiya, da na duk ƙasashen bakin Ƙogin Urdun, suka yi ta zuwa wurinsa, 6 yana yi musu babtisma a Ƙogin Urdun, suna bayyana zunubansu.

7 Amma da Yohana ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa sun taho don a yi musu babtisma, sai ya ce musu, “Ku macizan ƙaiƙayi! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa azaban nan mai zuwa? 8 Ku yi aikin da zai nuna tubanku. 9 Kada kuwa ku riya a ranku cewa Ibrahim ne ubanku, don ina gaya muku, Allah na iya halitta wa Ibrahim ’ya’yaya da duwatsun nan. 10 Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyad da ba ta yi ’ya’yaya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.

11 “Ni kam, da ruwa na ke muku babtisma saboda tubanku, amma mai zuwa bayana ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku babtisma da Ruhu Tsattsarka, da kuma wuta. 12 Kwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai-sarai, ya taro alkamarsa ya sa a taskarsa, amma ɓuntun sai ya ƙone shi a wuta marar kasuwa.”

Babtismar Yesu

13 A lokacin nan ne Yesu ya zo daga Ƙasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yohana don ya yi masa babtisma. 14 Yohana kuwa ya so hana shi, ya ce, “Ni da na ke bukatar kai ka yi min babtisma, ka zo gare ni?” 15 Amma sai Yesu ya amsa masa ya ce, “A dai yi haka yanzu, don haka ya dace mu cika dukkan aikin gaskiya.” Sa’an nan Yohana ya yardam masa. 16 Da aka yi wa Yesu babtisma, nandanan sai ya fito daga ruwan, sai ga Sama ta dare, ya ga Ruhun Allah na saukowa kamar kurciya, bar ya sauka kansa. 17 Kwamfa sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana Ƙaunataceena, wanda na ke farinciki da shi ƙwarai.”

4

Shaiɗan ya Gwada Yesu

A Sannan sai Ruhu Tsattsarka ya kai Yesu jeji domin Iblis yă gwada shi, 2 Da ya hana kansa abinci kwana arba’in dare da rana, daga baya sai yunwa ta kama shi. 3 Sai Maigwadawan nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama burodi.” 4 Amma sai Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce ya ke, cewa,

‘Ba da burodi kaɗai mutun zai rayu ba,
Sai dai da kowace maganad da ke fitowa daga bakin Allah.’”

5 Sa’an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Ɗakin Ibada, 6 ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa. Don a rubuce ya ke, cewa,

‘Zai yi wa mala’ikunsa umarni game da kai,’

kuma

‘Za su tallafe ka,
Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’

7 Sai Yesu ya ce masa, “Kuma a rubuce ya ke, cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’” 8 Har wa yau dai sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukkan mulkin duniya da ɗaukakarsu. 9 Ya kuma ce masa, “Duk waɗannan zam ba ka in ka faɗi a gabana ka yi mini sujada.” 10 Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan kai Shaiɗan! don a rubuce ya ke, cewa,

‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’” 11 Sa’an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala’iku sun zo suna yi masa hidima.

Yesu a Ƙasar Galili

12 To, da Yesu ya ji an tsare Yohana, sai ya janye zuwa ƙasar Galili. 13 Sai kuma ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tafki, a kan iyakar Ƙasar Zebulun da Naftali, 14 don a cika faɗar Annabi Ishaya, cewa,

15 ‘Ƙasar Zebulun da Ƙasar Naftali,

Da bakin bahar, da ƙetaren Kogin Urdun,
Da kuma Ƙasar Galili ta sauran al’umma,
16 Mazauna duhu sun ga babban haske,
Mazauna bakin halaka da fargabatata,
Haske ya keto musu.”

17 Tun daga lokacin nan Yesu ya fara wa’azi yana cewa, “Ku tuba don Mulkin Sama ya kusato.”

Almajiransa na Farko

18 Yana tafiya a bakin Tafkin Galili ke nan, sai ya ga wa da ƙane, Siman da a ke kira Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, suna jefa taru a tafki, don su masunta ne. 19 Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zam mai da ku masu tsamo mutane.” 20 Nandanan sai suka watsad da tarunansu, suka bi shi. 21 Da ya ci gaba sai ya ga wasu mutum biyu kuma, su ma kuwa wa da ƙane ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan’uwansa Yohana, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su. 22 Nan take suka bar jirgin duk da uban nasu, suka bi shi.

23 Sai ya zazzaga duk Ƙasar Galili, yana koyarwa a majami’unsu, yana yin Bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkad da kowace cuta da rashin lafiya na mutane. 24 Ta haka ya shahara a cikin duk Ƙasar Sham. Aka kuwa kakkawo masa dukkan marasa lafiya, masu fama da cuta iri-iri, da masu shan azaba, da kuma masu taɓin aIjannu, da masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkad da su. 25 Taro masu yawan gaske suka bi shi daga Ƙasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da Ƙasar Yahudiya, har ma daga ƙetaren Kogin Urdun.

5

WA’AZI A KAN DUTSE

Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Kuma da ya zauna sai almajiransa suka zo gunsa. 2 Sai ya buɗe baki ya koya musu, yana cewa,

3 “Albarka tā tabbata ga masu ƙanƙan-da-kai, don Mulkin Sama nasu ne.
4 “Albarka tā tabbata ga masu nadama, don za a sanyaya musu rai.
5 “Albarka tā tabbata ga masu sanyin-hali, don za su gaii duniya.
6 “Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga aikin gaskiya, don za a biya musu muradi.
7 “Albarka tā tabbata ga majiya tausayi, don su ma za a ji tausayinsu.
8 “Albarka tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, don za su ga Allah.
9 “Albarka tā tabbata ga masu ƙulla aminci, don za a ce da su ’ya’yan Allah.
10 “Albarka tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikin gaskiya, don Mulkin Sama nasu ne.
11 “Albarka tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma ƙaga muku kowace irin mugunta, saboda ni. 12 Ku yi murna da farinciki matuƙa, don sakamakonku mai yawa ne a Sama, gama haka aka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

13 “Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sane, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran wani amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.

14 “Ku ne hasken duniya. Ai birnin da aka gina bisa tudu ba ya ɓoyuwa. 15 Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa’an nan ta ba duk mutanen gida haske. 16 To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, don su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da ke Sama.

17 “Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da Littattafan Annabawa. Na zo ne ba don in shafe su ba, sai dai don in cika su. 18 Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko digo na Attaura ba za su gogu ba, sai an cika dukkan komai. 19 Don haka duk wanda ya ya da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnin nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a cikin Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, bar ya koyad da su, za a ce da shi mai girma a cikin Mulkin Sama, 20 Ina dai gaya muku, in gaskiyarku ba ta fi ta malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.

Umarni iri-iri

21 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka yi kisankai; kuma kowa ya yi kisa, za a hukunta shi.’ 22 Amma ni ina gaya muku, kowa ke fushi da ɗan’uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan’uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga wutar Jahannama. 23 Saboda haka in kana cikin miƙa baikonka Wurin Baikon, kuma a nan ka tuna ɗan’uwanka na da wata magana game da kai, 24 sai ka dakatad da baikonka Wurin Baikon tukuna, ka je ku shirya da ɗan’uwanka, sannan ka zo ka miƙa baikonka. 25 Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari’a, don kada mai ƙararka ya bashe ka ga alkali, alkali kuma ya miƙa ka ga yari, a kuma jefa ka kurkuku. 26 Hakika ina gaya maka, ba za ka fita daga nan ba sai ka biya duk, babu sauran ko anini.

27 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28 Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha’awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita. 29 In idonka na dama na sa ka laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Jahannama. 30 In kuma hannunka na dama na sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Jahannama.

31 “An kuma ce, ‘Kowa ya saki matatasa, sai ya ba ta takardar saki.’ 32 Amma ni ina gaya muku, kowa ya saki matatasa, im ba a kan laifin zina ba, ya sa ta hanyar zina ke nan. Wanda kuma ya auri sakakkiya, ya yi zina.

33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse kan ƙarya, sai dai ka cika wa’adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’ 34 Amma ni ina gaya muku, Kada ma ku rantse sam, ko da da Sama, don ita ce gadon sarautar Allah, 35 ko da da ƙasa, don ita ce matashin ƙafarsa, ko kuma da Urushalima, don shi ne birnin Babban Sarki. 36 Kada kuwa ka rantse da kanka, don ba za ka iya mai da ko da gashi ɗaya fari ko baki ba. 37 Abin da duk za ku faɗa, ya tsaya kan ‘I’ ko ‘A’a’ kawai. In dai ya zarce haka, daga Mugun ya fito.

38 “Kun dai ji an faɗa, ‘Sakayyar ido, ido ne, sakayyar haƙori kuma, haƙori ne.’ 39 Amma ni ina gaya muku, Kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma. 40 In kuma wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, bar masa mayafinka ma. 41 In kuma wani ya tilasta maka ku yi tafiyar mil guda tare, to, ku yi tafiyar mil biyu ma. 42 Kowa ya roƙe ka, ka ba shi, mai neman rance a wurinka kuwa, kada ka hana shi.

43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan’uwanka, ka ƙi magabcinka.’ 44 Amma ni ina gaya muku, Ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke Sama. Domin ya kan sa ranatasa ta fito kan miyagu da kuma nagari, ya kuma sako ruwan sama ga masu gaskiya da marasa gaskiya. 46 In masoyanku kawai ku ke ƙauna, wane lada ne da ku? Ashe ko masu karɓar haraji ma ba haka su ke yi ba? 47 In kuwa ’yan’uwanku kaɗai ku ke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe ko sauran al’umma ma ba haka su ke yi ba?

48 Saboda haka sai ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na Sama ke cikakke.

6

Ibadar Gaske

“Ku yi hankali kada ku yi ibadarku ta sadaka a idon mutane, wai don su gan ku. Don in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da ke Sama ba.

2 “Wato in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai ke yi a majami’u da kuma kan titi, wai don mutane su yabe su. Gaskiya na ke faɗa muku, sun sami iya ladansu ke nan. 3 Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama ke yi, 4 don sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da a ke yi a asirce, zai saka maka.

5 “Kuma in za ku yi addu’a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son su yi addu’a a tsaye a cikin majami’u da kan kwăna, wai don mutane su gan su. Gaskiya na ke gaya muku, sun sami iya ladansu ke nan. 6 Amma in za ka yi addu’a, sai ka shiga turakarka ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanku wanda ke ɓoye, Ubanku kuwa da ke ganin abin da a ke yi a asirce, zai sāka maka.

7 “In kuwa kuna addu’a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda sauran al’umma ke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu. 8 Kada ku zama kamarsu, don Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.

Ya Koya wa Almajiransa yin Addu’a

9 Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka:

‘Ya Ubammu da ke Sama,
A keɓe sunanka a tsarkake.
10 Mulkinka yă bayyana,
A aikata nufinka a nan ƙasa tamkar a can Sama.
11 Ka ba mu abincimmu na yau.
12 Ka yafe mana laifuffukammu,
Kamar yadda mu ma muka yafe wa waɗanda suka yi mana laifi.
13 Kada ka kai mu ga gwaji,
Amma ka tsarshe mu daga Mugun.’

14 Don in kun yafe wa mutane laifuffukansu, Ubanku na Sama zai yafe muku. 15 In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.

16 “Kuma in kuna hana kanku abinci, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don su kan yanƙwane fuska wai don mutane su ga suna hana kansu abinci. Hakika, ina gaya muku, sun sami iya ladansu ke nan. 17 Amma in kana hana kanka abinci, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke ido, 18 don kada mutane su ga alamar kana hana kanka abinci, sai dai Ubanku da ke ɓoye ya gani. Kuma Ubanku da ke ganin abin da a ke yi a asirce, zai sāka maka.

Dukiya a Sama

19 “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke ɓatawa, inda ɓarayi kuma ke karyawa su yi sata. 20 Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata inda kuma ba ɓarayin da za su karya su yi sata. 21 Don kuwa inda dukiyarka ta ke, a nan ranka ma ya ke.

22 “Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka ma sai ya cika da haske. 23 In kuwa idonka da lahani, duk jikinka sai ya cika da duhu. To, in hasken da ke gare ka duhu ne, wa ke gane min irin yawan duhun!

Bautar Allah da Bautar Dukiya

24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku iya bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.

25 “Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu batun rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi dai tsuntsaye. Ai ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma ɗurawa a rumbu, amma kuwa Ubanku na Sama na ci da su. Ashe ba ku fi su martaba nesa? 27 Wanene a cikinku, don damuwatasa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwatasa? 28 To, don me ku ke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda su ke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, 29 duk da haka ina gaya muku, ko Sulaimanu ma shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. 30 To, ga shi Allah na ƙawata tsiretsiren jeji ma haka, waɗanda yau su ke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 31 Don haka kada ku damu kuna cewa, ‘Me za mu ci? ko, ‘Me za mu sha? ko kuwa, ‘Me za mu sa? 32 Ai sauran al’umma ma na ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka. 33 Muhimmin abu na farko sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma samun karɓuwa a gareshi, sai ma har a ƙara muku da dukkan waɗannan abubuwa.

34 “Saboda haka kada ku damu don gobe, ai gobe ta Allah ce. Don wahalce-wahalcen yau ma sun isa wahala.

7

Laifi Tudu ne

Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku. 2 Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku. 3 Dom me ka ke duban ɗan hakin da ke idon ɗan’uwanka, amma gungumen da ke naka idon ba ka kula ba? 4 Ko kuwa yaya za ka iya ce da ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin nan daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka idon? 5 Kai munafiki! Sai ka fara cire gungumen da ke idonka tukuna, sa’an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan’uwanka.

6 “Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu’ulu’unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.

7 “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta buga ƙofa, za a kuwa buɗe muku. 8 Duk wanda ya roƙa, a kan ba shi, mai nema na tare da samu. Wanda ya buga ƙofa kuma za a buɗe masa. 9 To, wanene a cikinku ɗansa zai roƙe shi burodi, ya ba shi dutse? 10 Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji? 11 To, ku da ku ke miyagu ma, kuka san yadda za ku ba ’ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku da ke Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa? 12 Saboda haka duk abin da ku ke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu. Don wannan shi ne ƙashin Attaura da Littattafan Annabawa.

Hanyar Rayuwa da Hanyar Halaka

13 “Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa; gama ƙofar zuwa halaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa. 14 Don ƙofar zuwa rai madawwami ƙunƙunta ce, hanyarta kuwa mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.

15 “Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda su kan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kuraye ne masu ƙwace. 16 Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin kaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙiya? 17 Haka kowane icen kirki ya kan haifi kyawawan ’ya’ya. Mummunan ice kuwa ya kan haifi munanan ’ya’ya. 18 Kyakkyawan ice ba dama ya haifi munanan ’ya’ya. Haka kuma mummunan ice ba dama ya haifi kyawawan ’ya’ya! 19 Duk icen da ba ya’ya’ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. 20 Don haka da irin aikinsu za ku gane su.

21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, Ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da ke Sama ke so. 22 A ranan nan da yawa za su ce da ni, ‘Ya Ubangiji, Ya Ubangiji, ashe ba mu yi faɗin Maganar Allah da sunanka ba? Ba mu fid da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al’ajabi masu yawa da sunanka ba? 23 Sa’an nan zan ce da su, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’

24 “Saboda haka kowa ke jin maganan nan tawa, ya ke kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan harsashin dutse. 25 Da ruwa ya sako, kogi ya cika ya bai daji, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, don an gina shi a kan harsashin dutse ne. 26 Kowa ya ji maganan nan tawa, kuma bai aikata ta ba, za a misalta shi da wawan mutun, wanda ya gina gidansa a kan rairayi. 27 Da ruwa ya sako, kogi ya cika ya bai daji, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar rugurgujewa kuwa!”

28 Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwatasa, 29 don yana koya musu a tabbace, ba kamar malamansu na Attaura ba.

8

AYYUKAN ALAJABI

Yesu ya Warkad da Kuturu

Da ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawan gaske suka bi shi. 2 Sai ga wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda ka iya tsarkake ni.” 3 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take kuturtarsa ta warke. 4 Sai Yesu ya ce da shi, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa komai. Sai dai ka je wurin malami ya gan ka, ka kuma yi baiwa don tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

Ya Warkad da Shanyayye

5 Yana shiga Kafarnahum ke nan, sai wani kyaftin ya zo gunsa ya roƙe shi, 6 ya ce, “Ya Ubangiji, yarona na kwance a gida, ya zama shanyayye, yana shan azaba ƙwarai.” 7 Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkad da shi.” 8 Sai kyaftin ɗin ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, ban ma isa har ka zo gidana ba, amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa sai ya warke. 9 Don ni ma a hannun wani na ke, da kuma soja a hannuna, sai in ce da wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce da bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.” 10 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce da mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Bani Isra’ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba. 11 Ina kuma gaya muku, da yawa za su zo daga gabas da yamma su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Isiyaku da Yakubu a Mulkin Sama, 12 ’ya’yan Mulki na gado kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da gama haƙora.” 13 Sai Yesu ya ce da kyaftin ɗin, “Je ka, ya zame maka gwargwadon bangaskiyad da ka yi.” Nan take yaronsa ya warke.

14 Da Yesu ya shiga gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus na kwance da zazzaɓi. 15 Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima. 16 Da maraice ya yi, sai suka kakkawo masa masu taɓin aljannu da yawa. Da buɗe baki kawai sai ya fid da aljannun, ya kuma warkad da dukkan marasa lafiya. 17 Wannan kuwa don a cika faɗar Annabi Ishaya ne, cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cuce-cucemmu.”

18 To, da Yesu ya ga taro masu yawan gaske sun kewaye shi, sai ya yi umarni a koma wancan ƙetare. 19 Sai wani malamin Attaura ya zo ya ce masa, “Ya Shugaba, zam bi ka duk inda za ka je.” 20 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramunansu, tsuntsayn kuma da wurin kwanansu, amma Ɗam Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.” 21 Sai ɗaya daga cikin almajiran ya ce masa, “Ye Ubangiji, ka bar ni tukuna in je im binne tsohona.” 22 Amma sai Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne ’yan’uwansu matattu.”

Ya Tsauta wa Iska da Ruwan Tafki

23 Da ya shiga jirgi, sai almajiransa suka bi shi. 24 Sai ga wani babban hadiri ya taso a tafki, bar raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci. 25 Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu mun halaka!” 26 Sai ya ce musu, “Dom me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sannan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit. 27 Sai mutanen suka yi al’ajabi, suka ce, “Wane irin mutun ne wannan, wanda har iska da ruwan tafki ma ke masa biyayya,”

Ya Warkad da Masu Tabin AIjannu

28 Da ya isa wancan ƙetaren a Rasar Gadarawa, sai mutum biyu masu taɓin aljannu suka fito daga makabarta suka tare shi. Don kuwa su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bi ta wannan hanya. 29 Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai ‘Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” 30 Kuma nesa kaɗan akwai wani babban garken alade na kiwo. 31 Sai aljannun suka roƙe shi suka ce, “In ka fid da mu, tura mu cikin garken aladen nan.” 32 Ya ce musu, “To, ku je.” Sai suka fita, suka shigi aladen. Sai kuwa duk garken suka rugungunto ta gangaren, suka faɗa tafkin, suka halaka a cikin ruwa. 33 Sai ’yan kiwon aladen suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, da kuma abin da ya auku ga masu taɓin aljannun. 34 Sai ga duk jama’ar garin sun firfito su tari Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar musu ƙasarsu.

9

Yesu na Gafarta Zunubai

Da ya shiga jirgi, sai ya haye ya je garinsu. 2 Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a kan gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce da shanyayyen, “Ɗana, ka yi farinciki, an gafarta maka zunubanka.” 3 Sai wasu malaman Attaura suka ce a ransu, “Wannan mutun ai saɓo ya ke!” 4 Yesu kuwa, da ya ke ya san tunaninsu, sai ya ce, “Dom me ku ke mugun tunani a zuciyarku? 5 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka’, ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’? 6 Amma don ku sakankance Ɗam Mutun na da ikon gafarta zunubi a duniya”—sai ya ce da shanyayyen—“Tashi, ka ɗauki gadonka ka. tafi gida.” 7 Sai kuwa ya tashi ya tafi gida. 8 Da taron suka ga haka, sai tsoro ya rufe su, suka ɗaukaka Allah, wanda ya ba mutane iko haka.

Yesu ya Kira Matiyu

9 Da Yesu ya yi gaba, sai ya ga wani mutum mai suna Matiyu zaune yana aiki a ofishin karɓar haraji. Sai ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.

10 Sa’ad da kuwa Yesu ke cin abinci a cikin gida, sai ga masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa. 11 Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce da almajiransa, “Dom me shugabanku ke ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 12 Amma da Yesu ya ji haka, sai ya ce, “Ai lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. 13 Sai ku fahinci ma’anar wannan tukuna, ‘Ni kam tausayi na ke nema a gareku, ba hadaya ba.’ Ba don kiran masu gaskiya na zo ba, sai masu. zunubi.”

14 Sai almajiran Yohana suka zo wurinsa, suka ce, “Dom me mu da Farisiyawa mu ke yawan hana kammu abinci, amma naka almajiran ba sa hanawa?” 15 Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙinciki tun ango na tare da su? Ai lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su hana kansu abinci. 16 Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle, don mahon zai kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa. 17 Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Im ma an ɗura, sai salkunan su fashe, ruwan inabin ya zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi ai sai sababbin salkuna. Ta haka an tserad da duka biyu ke nan.”

Ya Ta da ’Yar Yayirus

18 Yana cikin yi musu magana haka, sai ga wani shugaban jama’a ya zo ya yi masa sujada, ya ce, “Yanzu-yanzu ’yata ta rasu, amma ka zo ka ɗora mata hannu, za ta rayu.” 19 Sai Yesu ya tashi ya bi shi tare da almajiransa. 20 Sai ga kuma wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa. 21 Don ta ce a ranta, “Ko da mayafinsa ma na taɓa, sai in warke.” 22 Sai Yesu ya juya, yā gan ta, ya ce, “’Yata, ƙi yi farinciki, bangaskiyarki ta warkad da ke.” Nan take matar ta warke.

23 Da Yesu ya isa gidan shugaban jama’ar, ya kuma ga masu busa sarewa da taro suna ta hayaniya, 24 sai ya ce, “Ku ba da wuri, ai yarinyar ba a mace ta ke ba, barci ta ke yi.” Sai suka yi masa ɗariyar raini. 25 Amma da aka fid da taron waje, sai ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta tashi. 26 Wannan labarin kuwa ya bazu a duk ƙasar.

Ya Warkad da Makafi Biyu

27 Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai wasu makafi biyu suka bi shi, suna daga murya suna cewa, “Ya ɗan Dawuda, ka ji tausayimmu.” 28 Da ya shiga wani gida sai makafin suka zo gare shi. Yesu ya ce musu, “Kun gaskata zan iya yin haka?” Sai suka ce masa, “I mana, ya Ubangiji!” 29 Sa’an nan ya shafa idanunsu, ya ce, “Yă zame muku gwargwadon bangaskiyarku.” 30 Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.” 31 Amma sai suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk ƙasar.

32 Sun tashi ke nan sai aka kawo masa wani bebe mai taɓin aljan. 33 Bayan an fid da aljanin, sai beben ya yi magana; taron kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Kai! ba a taɓa ganin irin wannan ba a cikin Bani Isra’ila.” 34 Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai da ikon sarkin aljannu ya ke fid da aljannu.”

35 Sai Yesu ya zazzaga dukkan garuruwa da kauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana yin Bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkad da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36 Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, don suna cikin wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki ba makiyayi. 37 Sai ya ce da almajiransa, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. 38 Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbin ya turo masu girbi, su yi masa girbi.”

10

Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon 10 fid da baƙaƙen aljannu, da warkad da kowace irin cuta da rashin lafiya.

Sunayen Manzanni Sha Biyu

2 To, ga sunayen Manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Siman, wanda a ke kira Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan’uwansa Yohana, 3 da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Alfayas, da Tadawas, 4 da Siman Bakan’ane, da kuma Yahuda Iskariyoti wanda ya bashe shi.

Am Bayyana irin Aikinsu

5 Su Sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni ya ce, “Kada ku shiga cikin sauran al’umma, ko kuma kowane garin Samariyawa. 6 Sai dai ku je wurin ɓatattun tumakin Bani Isra’ila, 7 kuna tafiya kuna wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’ 8 Ku warkad da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fid da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta. 9 Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurka, ko na tagulla a ɗamararku, 10 kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma’aikaci ya cancanci hakkinsa. 11 Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi. 12 In zaku shiga gidan, ku yi sallama. 13 In gidan na kirki ne, amincinku yă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, yă komo muku. 14 Kowa kuma ya ƙi yin na’am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku. 15 Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari’a za a fi hakurce wa ƙasar Saduma da ta Gamurata a kan garin nan.

16 “Ga shi na aike ku kamar tumaki a cikin kuraye. Don haka sai ku yi wayo kamar dila, da kuma lafiya kamar tinkiya. 17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisu, su kuma yi muku bulala a majami’unsu. 18 Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, don ku ba da shaida a gabansu, kuma a gaban sauran al’umma. 19 Lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin. 20 Don ba ku ne ke magana ba, Ruhun Ubanku ne ke magana ta bakinku. 21 Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. ’ya’ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su. 22 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu. 23 In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukkan garuruwan Bani Isra’ila, Ɗam Mutun zai zo.

24 “Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba ya fin ubangijinsa. 25 Ya isam ma almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba’alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?

26 “Don haka kada ku ji tsoronsu, don ba abin da ke rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da ke ɓoye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da na ke gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye. 28 Kada ku ii tsoron masu kisan mutun, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da ke iya hallaka kurwar da jikin duka a Jahannama. 29 Ashe ba gwara biyu ne kwabo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba. 30 Ai ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye ya ke. 31 Kada ku ji tsoro. Ai martabarku ta fi ta gwara masu yawa. 32 Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zam bayyana yarda gare shi a gaban Ubana da ke Sama. 33 Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubana da ke Sama.

34 “Kada dai ku zaci na zo ne in kawo aminci duniya. A’a, ban zo don in kawo aminci ba, sai dai takobi. 35 Don na zo ne in haɗa mutun da ubansa gaba, ’ya da uwatata, matar da kuma da surukatata. 36 Zai zamana kuma magabtan mutun su ne mutanen gidansa. 37 Wanda duk ya fi son ubansa ko uwatasa a kaina, bai ancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko ’yatasa a kaina, bai caucanci zama nawa ba. 38 Wanda kuma bai shafa jini a wuyansa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba. 39 Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi ya yi.

40 “Wanda ya yi na’am da ku, ya yi na’am da ni ke nan. Wanda ya yi na’am da ni kuwa, to, ya yi na’am da wanda ya aiko ni. 41 Wanda ya yi na’am da wani mai yin faɗin Maganar Allah don shi mai yin faɗin Maganar Allah ne, zai sami ladan mai yin faɗin Maganar Allah. Wanda kuma ya yi na’am da mai aikin gaskiya don shi mai aikin gaskiya ne, zai sami ladan mai aikin gaskiya. 42 Kowa ya ba ɗaya daga cikin ’yan yaran nan ko da moɗa guda ta bakin ruwa kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa laɗansa ba.”

11

Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan don ya koyar, ya kuma yi wa’azi a garuruwansu.

YESU DA YOHANA MAIBABTISMA

2 To, da Yohana ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa, 3 su ce masa, “Kai ne Maizuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 4 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yohana abin da kuka ji, da abin da kuka gani. 5 Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta Bishara. 6 Albarka td tabbata ga wanda ba ya ƙosawa da ni.”

7 Sun tafi ke nan sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yohana, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska ke kaɗawa? 8 To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa masu adon alharini a fada su ke. 9 To, dom me kuka fita? Ku ga wani annabi? I, lalle kuwa, har ya fi annabi nesa. 10 Wannan shi ne wanda labarinsa ke rubuce, cewa,

‘Ga shi na aiko manzona ya riga ka gaba,
Wanda zai shirya maka hanya gabanninka.’

11 Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yohana Maibabtisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙasƙanci a cikin Mulkin Sama ya fi shi. 12 Tun daga zamanin Yohana Maibabtisma har ya zuwa yanzu, ana ta firmitsawa ana faɗawa cikin Mulkin Allah, masu kwazo su ke faɗawa ciki. 13 Don dukkan Littattafan Annabawa da Attaura sun yi faɗin annabci bar ya zuwa kan Yohana. 14 Kuma in za ku karɓa, shi ne Iliya da dā ma zai zo. 15 Duk mal kunnen ji, yă ji.

16 “To, da me zan kwatanta zamanin nan? Kamar yara ne da ke zaune a kasuwa, suna kiran abokan wasansu, suna cewa,

17 ‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba;
Mun yi kukan mutuwa, ba ku koka ba.’

18 Ga shi Yohana ya zo, ya ƙi ciye-ciye da shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai yana da iska.’ 19 Ga Ɗam Mutun ya zo, yana ci yana sha, sai suka ce, ‘Ga nan mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka hikimar Allah, ta aikinta ne a ke tabbatad da gaskiyatata.”

20 Sai ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin ayyukansa na al’ajabi a cikinsu, don ba su tuba ba. 21 “Kin shiga uku Kurazinu! Kin shiga uku Baitsaida! Da mu’ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Sur da Saida, da tuni sun tuba suna saye da tsumma, suna hurwa da toka. 22 Amma ina gaya muku, a Ranar Shari’a, za a fi haƙurce wa Sur da Saida a kanku. 23 Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaukaka ƙi Sama kuwa? La! Kasƙantad da ke za a yi har Hades. Da mu’ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau. 24 Amma ina gaya muku, a Ranar Shari’a, za a fi haƙurce wa Saduma a kanki.”

Bautata Sassauƙa ce—Kayana Marar Nauyi ne

25 A wannan lokacin sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, don ka ɓoye waɗannan al’amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga farin-shiga. 26 Hakika na gode maka ya Uba, don wannan shi ne nufinka na alheri. 27 Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, kuma ba wanda ya san Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya buɗa wa. 28 Ku zo gare ni dukkanku masu wahala, masu niƙi-niƙi da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku. 29 Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni. Don ni mai sanyin hali ne, kuma mai tawali’u ne, za ku kuwa sami kwanciyar rai. 30 Don bautata sassauƙa ce, kayana kuma marar nauyi ne.”

12

Farisiyawa sun Takali Yesu

A lokacin nan a ran Asabar, Yesu na ratsa gonakin alkama 12AImajiransa kuwa na jin yunwa, sai suka fara zagar alkamar suna ci. 2 Amma da Farisiyawa suka ga haka sai suka ce masa, “Ka ga! almajiranka na yin abin da bai halatta a yi ba ran Asabar.” 3 Sai ya ce musu, “Ashe ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa’ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 4 Yadda ya shiga Ɗakin Allah ya ci keɓaɓɓen burodin nan, wanda bai halatta ya ci ba, ko abokan tafiyarsa ma su ci, sai dai malamai kaɗai? 5 Ko kuwa ba ku taɓa karantawa a cikin Attaura ba ne, yadda a ran Asabar, malamai a Ɗakin Allah su kan keta dokar Asabar, ba tare da yin wani laifi ba kuwa? 6 Ina dai gaya muku, ga wanda ya fi Ɗakin Ibada a nan. 7 Da ma kun san ma’anar wannan, cewa, ‘Ni kam tausayi na ke nema a gare ku, ba hadaya ba’, da ba ku ga laifin marasa laifi ba. 8 Don ‘Ɗam Mutun shi ne Ubangijin Asabar.”

9 Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami’arsu. 10 Akwai wani mutun a nan kuwa mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu, suka ce, “Ya halatta a warkar a ran Asabar?” Wannan kuwa don su samu su zarge shi ne. 11 Ya ce musu, “Misali, wanene a cikinku in yana da tinkiya, ta faɗa rami ran Asabar, ba zai kama ta ya fid da ita ba? 12 Sau nawa mutun ya fi tinkiya daraja? Don haka ya halatta a yi alheri a ran Asabar. 13 Sannan ya ce da mutumin, “Miƙe hannunka.” Sai ya miƙe. Sai ya koma lafiyayye kamar ɗayan. 14 Amma sai Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.

15 Da Yesu ya gane haka sai ya janye jiki daga nan. Sai jama’a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkad da su duka. 16 Sai ya kwaɓe su kada su bayyana shi. 17 Wannan kuwa don a cika faɗar Annabi Ishaya ne, cewa,

18 “Ga barana wanda na zaɓa!
Kaunataceena, wanda na ke farinciki da shi ƙwarai.
Zan sanya masa Ruhuna, zai kuma sanad da sauran al’umma hanyar gaskiya.
19 Ba zai yi husuma ko magana sama-sama ba,
Kuma ba wanda zai ji muryatasa a titi.
20 Kyauron da ya fasu ba zai kakkarye shi ba,
Fitilad da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,
Har ya sa gaskiya ta ci nasara.
21 Sauran al’umma kuma za su sa zuciya ga sunansa.”

Beben Makaho Mai taɓin Aljan

22 Sai aka kawo masa wani beben makaho mai taɓin aljan, ya kuwa warkad da shi, har beben ya yi magana, ya kuma gani. 23 Mutane duk suka yi al’ajabi, suka ce, “Shin ko wannan shi ne Ɗan Dawuda?” 24 Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai da ikon Ba’alzabul sarkin aijannu kawai wannan ya ke fid da aljannu.” 25 Da ya ke Yesu ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu kan gāba, zai lalace. Ba kuma gari ko gidan da ya rabu kan gāba, yă ɗore. 26 In Shaiɗan na fid da Shaiɗan, yā rabu kan gāba ke nan. To, ta yaya mulkinsa zai ɗore? 27 In kuwa da ikon Ba’alzabul na ke fid da aljannu, to, ’ya’yanlcu fa, da ikon wa su ke fitarwa? Saboda haka su ne za su zama alkalanku.

28 Ni kuwa in da ikon Ruhun Allah na ke fid da aljannu, ashe Mulkin Allah ya aukam muku ke nan. 29 Yaya za a iya shiga gidan ƙato a washe kayansa, im ba an fara ɗaure ƙaton ba? Sa’an nan ne za a iya washe gidansa. 30 Wanda ba nawa ba ne, gāba ya ke da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa ya ke yi.

Saɓon Ruhu Tsattsarka

31 “Don haka ina gaya muku, A gafarta wa mutane kowane zunubi da saɓo, amma wanda ya saɓi Ruhu Tsattsarka, ba za a gafarta masa ba. 32 Kowa ya aibaci Ɗam Mutun, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibaci Ruhu Tsattsarka, ba za a gafarta masa ba duniya da Lahira.

33 “Ko dai ku ce icen kyakkyawa ne, ’ya’yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce icen mummuna ne, ’ya’yansa kuma munana. Don ice, da ’ya’yansa a ke gane shi. 34 Ku macizan ƙaiƙayi! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku miyagu ne? Don abin da ya ci rai, shi mutun kan faɗa. 35 Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciyatasa ya kan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciyatasa ya kan yi mugun abu. 36 Ina dai gaya muku, a Ranar Shari’a duk hululun da mutun ya yi, za a bincike shi. 37 Maganarka ce za ta kuɓutad da kai, ko kuma ta hukunta ka.”

All’alaman Attaura na Neman Alaama a gun Yesu

38 Sai wasu malaman Attaura da Farisiyawa suka amsa masa suka ce, “Ya Shugaba, muna so mu ga wata alama daga gare ka.” 39 Sai ya amsa musu ya ce, “Mugun zamani maci amana su ke nema su ga wata alama! Amma ba wata alamad da za a nuna musu sai dai ta Annabi Yunusa. 40 Wato kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana a cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗam Mutun zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa. 41 A Ranar Shari’a mutanen Ninawi za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa’azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan. 42 A Ranar Shari’a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta kā da su, don ta zo ne daga bangon duniya ta ga hikimar Sulaimanu. Ga kuma wanda ya fi Sulaimanu a nan.

43 “Baƙin aljan in ya rabu da mutun, sai ya bi ta wurare marasa ruwa neman hutu, amma ba ya samu. 44 Sa’an nan sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ Sa’ad da kuwa ya koma, sai ya tarad da gidan ba kowa a ciki, shararre, ƙawatacee. 45 Daganan sai ya je ya ɗebo wasu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutun ya ƙasa ƙasau ke nan. Haka zai zame wa wannan mugun zamani.”

Tsohuwar Yesu da ’Yan’uwansa

46 Yana cikin magana da taro, sai ga uwatasa da ’yan’uwansa suna tsaye a waje, suna nema su yi magana da shi. 47 Sai wani ya ce masa, “Ga tsohuwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.” 48 Sai ya amsa wa wanda ya gaya masa ya ce, “Wacece tsohuwata, suwanene kuma ’yan’uwana?” 49 Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa, ya ce, “Ga nan tsohuwata da ’yan’uwana! 50 Ai kowa ya yi abin da Ubana da ke Sama ke so, shi ne ɗan’uwana, shi ne ’yar’uwata, shi ne kuma tsohuwata.”

MISALAI KAN MULKIN SAMA

13

A ran nan Yesu ya fita daga gidan, ya je ya zauna a bakin tafki. 2 Taro masu yawan gaske suka haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi, ya zauna. Duk taron kuwa suka tsaya a bakin gaci.

Misalin Mai Shuka

3 Sai ya gaggaya musu abubuwa da yawa da ba da misalai, ya ce, “Wani mai shuka ya tafi shuka. 4 Yana cikin yafa iri sai wasu kwayoyi suka fantsama a kan hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su. 5 Wasu kuma suka fantsama a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nandanan sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa. 6 Da rana fa ta daga, sai suka yankwane; da ya ke ba su da saiwa sosai, sai suka bushe. 7 Wasu kuma suka fantsama cikin ƙaya, sai ƙaya ta tashi ta sarƙe su. 8 Wasu kuma suka zuba a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba, wasu riɓi ɗari-ɗari, wasu sittin-sittin, wasu kuma talatin-talatin. 9 Duk mai kunnen ji, yă ji.”

10 Sai almajiran suka zo, suka ce masa, “Me ya sa ka ke musu magana. da misalai?” 11 Ya amsa musu ya ce, “Ku kam an yarje muku ku san zurfafan al’amuran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba. 12 Don mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da ya ke da shi ma, sai an karɓe masa. 13 Shi ya sa na ke musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahinta. 14 Lalle a kansu ne aka cika faɗin annabcin Ishaya, cewa,

‘Za ku ji kam, amma ba za ku fahinta ba faufau,
Za kuma ku gani, amma ba za ku gane ba faufau,
15 Don zuciyar jama’an nan ta yi kanta,
Sun toshe kunnuwansu,
Sun kuma runtse idanunsu,
Wai don kada su gani da idanunsu,
Su kuma ji da kunnuwansu,
Su kuma fahinta a zuciyarsu,
Har su juyo gare ni in warkad da su.’

16 Albarka tā tabbata ga idanunku don suna gani, da kuma kunnuwanku don suna ji. 17Hakika, ina gaya muku, annabawa da masu gaskiya da yawa sun yi dokin ganin abin da ku ke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da. ku ke ji, amma ba su ji ba. 18 “To, ga ma’anar misalin mai shukan nan’. 19 Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahince ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyatasa. Wannan shi ne irin da ya fantsama a kan hanya. 20 Wanda ya fantsama a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda, da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farinciki. 21 Amma kuwa ba shi da tushe, kuma rashin ƙarko gare shi, har in wani kunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya ƙosa. 22 Wanda ya fantsama cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya su kan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani. 23 Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda ke jin Maganar, ya kuma fahince ta. Hakika shi ne mai yin amfani, har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”

Misali da Shukar Ciyawa

24 Sai ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonatasa. 25 Sa’ad da mutane ke barci, sai abokin gabansa yă je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa. 26 Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana. 27 Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, ‘Maigida., ashe ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?’ 28 Sai ya ce musu, ‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.’ Sai bayin suka ce masa, ‘To, kana son mu je mu cire mu tara ta? 29 Amma sai ya ce, ‘A’a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma. 30 Ku bari su zauna tare har lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami-dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.’ “

Misali da Ƙwayar Mastad

31 Sai kuma ya kawo musu wani misali ya ce, “Mulkin Sama kamar ƙwayar mastad ya ke, wadda wani mutun ya je ya shuka a lambunsa. 32 Ita ce mai ƙanƙanta a cikin kwayoyi, amma in ta girma, sai ta fi duk sauran ganye, har ta zama bishiya, har tsuntsaye su zo su kwana a rassanta.”

Misali da Yisti

33 Sai kuma ya ba su wani misali ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti ya ke, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”

34 Yesu ya gaya wa taro duk waɗannan abubuwa da misalai. Ba ya faɗa musu komai sai da misali. 35 Wannan kuwa don a cika faɗar Annabi Ishaya ne, cewa,

“Zan yi magana da misalai,
Zan sanad da abin da ke ɓoye tun farkon duniya.”

Ma’anar Shukar Ciyawar

36 Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma. suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawar gonar.” 37 Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗam Mutun. 38 Gonar kuwa, ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, shi ne ’ya’yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, ’ya’yan Mugun ne. 39 Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala’iku ne. 40 Kamar yadda a ke tara ciyawa a ƙone ta, haka zai kasance a ƙarshen duniya. 41 ‘Ɗam Mutun zai aiko mala’ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fid da su daga Mulkinsa, 42 su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da gama haƙora. 43 Sa’an nan ne masu gaskiya za su haskaka kamar rana a cikin Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.

Misali da Ɓoyayyiyar Dukiya

44 “Mulkin Sama kamar dukiya ya ke da ke binne a gona, wadda wani ya samu, ya sake binnewa. Yana tsaka da murnatasa, sai ya je yă sai da dukkan mallakatasa, ya sayi gonar.

45 “Har wa yau kuma Mulkin Sama. kamar attajiri ya ke, mai neman lu’ulu’u masu daraja. 46 Da ya sami lu’ulu’u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je yă sai da dukkan mallakatasa, ya saye shi.

Misali da Taru

47 “Har wa yau kuma Mulkin Sama. kamar taru ya ke da aka jefa a tafki, ya kamo kifi iri-iri. 48 Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsine kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar. 49 Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala’iku za su fito, su ware miyagu daga masu gaskiya, 50 so jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za so yi kuka da gama haƙora.

51 “Kun fahinci duk wannan?’ Sai suka ce masa, “I.” 52 Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida ya ke, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”

Yesu ya je Nazarat

53 Da Yesu ya gama. waɗannan misalai, sai ya tashi daga nan. 54 Kuma da ya zo garinsu, sai ya koya musu a majama’arsu, har suka yi mamaki, suka ce, “Ina mutumin nan ya sami wannan hikima haka, da kuma mu’ujizan nan? 55 Ashe wannan ba ɗan kafintan nan ba ne? Uwatasa ba sunanta Maryamu ba? ’Yan’uwansa kuwa ba su ne Yakubu da Yusufu da Siman da kuma Yahuda ba? 56 ’Yan’uwansa mata ba duk tare da mu su ke ba? To, ina ne mutumin nan ya sami wannan abu duka?” 57 Sai suka ƙosa da shi. Amma sai Yesu ya ce musu, “Ai annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.” 58 Bai kuma yi mu’ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.

14

Kisan Yohana Maibabtisma

A lokacin nan Sarki Hirudus ya ji labarin sbaharar Yesu. 2 Sai ya ce da barorinsa, “Wannan ai Yohana Maibabtisma ne, shi aka tasa daga matattu, shi ya sa a ke aikata mu’ujizan nan ta kansa.” 3 Don dā ma Hirudus ya kama Yobana ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan’uwansa Filibus. 4 Don dā ma Yohana ya ce masa bai halatta ya zauna da ita ba. 5 Ko da ya ke yana son kashe shi, yana jin tsoron jama’a, don sun ɗauka shi annabi ne. 6 To, da ranar haifuwar Hirudus ta kewayo, sai ’yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, bar ta ba Hirudus sha’awa, 7 har ma ya yi mata rantsuwa zai ba ta duk abin da ta tambaya. 8 Amma da uwatata ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yohana Maibabtisma a cikin akushi yanzu-yanzu.” 9 Sai sarki ya yi baƙinciki, amma saboda rantsuwatasa da kuma baƙinsa, sai ya yi umarni a ba ta. 10 Sai ya aika aka fille wa Yohana kai a kurkuku, 11 aka kuwa kawo kan a cikin akushi, aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa uwatata. 12 Sai almajiransa suka zo, suka ɗauki gangar-jikin, suka binne; suka kuma je suka gaya wa Yesu.

Ya Ci da Mutun Dubu Biyar

13 Da Yesu ya ji haka sai ya janye jiki daga nan, ya shiga jirgi zuwa wani wuri inda ba kowa, don ya kaɗaita. Amma da taron jama’a suka ji haka, sai suka fito daga garuruwa suka bi shi da ƙafa. 14 Da ya fita daga jirgin sai ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkad da marasa lafiya a cikinsu. 15 Da maraice ya yi, sai almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su sai wa kansu abinci.” 16 Yesu ya ce, “Ba lalle su tafi ba. Ku ku ba su abinci mana.” 17 Sai suka ce masa, “Ai burodi biyar da kifi biyu kawai mu ke da shi a nan.” 18 Sai ya ce, “Ku kawo mini su nan.” 19 Sa’an nan ya umarci taron su zazzauna a kan ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar ɗin da kifi biyun, sai ya daga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura burodin, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama’a. 20 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu. 21 Waɗanda suka cin kuwa misalin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara.

Yesu ya yi Tafiya a kan Ruwa

22 Sai ya sa almajiransa suka shiga jirgi su riga shi hayewa kafin ya sallami taron. 23 Bayan ya sallami taron, sai ya hau dutse shi kaɗai don ya yi addu’a. Har magariba ta yi yana can shi kaɗai 24 Sa’an nan kuwa jirgin na tsakiyar tafki, raƙuman-ruwa na mangaratasa, don iska na mai da su baya. 25 Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tafkin. 26 Sa’ad da kuwa almajiran suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka firgita suka ce, “Fatalwa ce!” Sai suka yi kururuwa don tsoro. 27 Sai nandanan ya yi musu magana ya ce, “Ba komai, ni ne, kada ku ji tsoro.”

28 Sai Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, in kai ne, to, ka umarce ni in zo gare ka ta kan ruwan.” 29 Sai ya ce, “Zo mana.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin, ya taka ruwa ya je gun Yesu. 30 Amma da ya ga iskar ta yi ƙarfi sai ya ji tsoro. Da ya fara nutsewa sai ya ɗau kururuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, cece ni!” 31 Nandanan sai Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, dom me ka yi shakka?” 32 Da shigarsu jirgin sai iskar ta kwanta. 33 Sai na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.

Ya Warkad da Dukkan Marasa Lafiya

34 Da suka haye, sai suka sauka a ƙasar Janisarata. 35 Da mutanen garin suka shaida shi, sai suka a’aika ko’ina a duk karkarar, aka kakkawo masa dukkan marasa lafiya, 36 suka roƙe shi su taɓa ko da gezar mayafinsa ma, ɗakwacin waɗanda suka taɓa kuwa suka warke.

Al’adun Kakanni da Umarnin Allah

15

Sai wasu Farisiyawa da malaman Attaura suka zo wurin Yesu daga Urushalima, suka ce, 2 “Dom me almajiranka ke keta al’adun shugabarmi? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.” 3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma dom me ku ke keta umarnin Allah saboda al’adunku? 4 Don Allah ya yi umarni ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwatasa sai lalle a kashe shi.’ 5 Amma ku ku kan ce, ‘Kowa ya ce da ubansa ko uwatasa, Duk abin da da za ku samu a gare ni am ba Allah, to, ba lalle ya girmama ubansa ba ke nan.’ 6 Wato, saboda al’adunku kun banzanta Maganar Allah. 7 Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi faɗin annabci a kanku, da ya ce,

8 ‘Al’umman nan a baka kawai su ke girmama ni,
Amma a zuci nesa su ke da ni.
9 A banza su ke bauta mini,
Don ka’idodin da su ke koyarwa umarnin ɗan’adan ne.’ “

10 Sai ya kira taro ya ce musu, “Ku saurara, ku fahinta. 11 Ba abin da ke shiga mutun ta baka ne ke ƙazanta shi ba, sai abin da ke fita ta baka shi ke ƙazanta mutun.” 12 Sai almajiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganan nan?” 13 Ya amsa ya ce, “Duk dashen da ba Ubana da ke Sama ne ya dasa ba, za a tumɓuke shi. 14 Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai duk biyu sai su faɗa rami.” 15 Amma sai Bitrus, ya ce da shi, “A yi mana fassarar misalin nan.” 16 Yesu ya ce, “Ku ma ashe har yanzu ba ku da fahinta? 17 Ashe ba ku gane ba cewa komai ya shigi mutun ta baka, cikinsa ya shiga, ta haka kuma zai fice? 18 Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci ya ke, shi ne kuwa ke ƙazanta mutun. 19 Don daga zuci miyagun tunani ke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur da yanke. 20 Waɗannan su ke ƙazanta mutun. Amma a ci da hannu marar wanki ba ya ƙazanta mutun.”

21 Sai Yesu ya tashi daga nan, ya janye zuwa ƙasar Sur da Saida. 22 Sai ga wata Bakan’aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi ’yata, ba yadda ta ke.” 23 Amma bai ce da ita kanzil ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Sallame ta mana, tana bimmu tana cika mana kunne da kuka.” 24 Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin Bani Isra’ila kaɗai aka aiko ni.” 25 Amma sai ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, taimake ni mana!” 26 Ya amsa ya ce, “Ai bai kyautu a bai wa na daji abincin ’yan gida ba.” 27 Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai na daji su kan ci suɗin ’yan gida. “ 28 Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa ta ke! Yă zame miki yadda ƙi ke so.” Nan take ’yatata ta warke.

29 Sai Yesu ya tashi daga nan, ya bi ta bakin Tafkin Galili. Sai ya hau dutse ya zauna a can. 30 Taro masu yawan gaske suka zo wurinsa, suka zazzo da guragu, da masu dungu, da makafi, da bebaye, da kuma waɗansu da yawa, suka ajiye su a gabansa cikin hanzari, ya kuwa warkad da su. 31 Har jama’ar suka yi ta al’ajabi da ganin bebaye na magana, masu dungu sun sami gaɓoɓinsu, guragu na tafiya, makafi kuma na gani; sai suka ɗaukaka Allahn Bani Isra’ila.

Ya Ci da Matun Dubu Hudu

32 Sai Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa son in sallame su da yunwa haka, kada su ƙasa a hanya.” 33 Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo burodi a jeji haka da zai isa ci da ƙasaitaccen taro haka?” 34 Yesu ya ce musu, “Burodi nawa gare ku?” Suka ce, “Bakwai, da kananan kifaye kaɗan.” 35 Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. 36 Da ya ɗauki burodi bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na bai wa jama’a. 37 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, bar suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai. 38 Waɗanda suka cin kuwa maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara. 39 Da ya sallami taron sai ya shiga jirgi ya tafi ƙasar Magadan.

16

Sai Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo suka roƙe shi ya nuna musu wata alama daga Sama, don su gwada shi. 2 Ya amsa musu ya ce, “Im magariba ta yi, kuka ga sama ta yi ja, ku kan ce, ‘Aha, gari zai yi sarari.’ 3 Da safe kuma in kuka ga sama ta yi ja, ta kuma gama gira, ku kan ce, ‘Yau kam za a yi hadiri.’ Kuna iya gane yanayin sararin sama, amma ba kwa iya gane alamun zamanin nan. 4 Mugun zamani maci amana su ke nema su ga wata alama, amma ba wata alamad da za a nuna musu, sai dai ta Yunusa.” Sai ya bar su ya tafi.

5 Da almajiran suka isa wancan ƙetare, ashe sun manta ba su kawo burodi ba. 6 Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.” 7 Sai suka yi magana da juna suka ce, “Ba mu kawo burodi ba fa!” 8 Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, dom me ku ke magana da juna a kan ba ku zo da burodi ba? 9 Ashe har yanzu ba ku gane ba? Ba ku tuna da burodi biyar ɗin nan na mutun dubu biyar ba? Kwando nawa kuka ɗauka? 10 Ko kuma burodin nan bakwai na mutun dubu huɗu, manyan kwanduna, nawa kuka ɗauka? 11 Yaya kuka ƙasa ganewa? Ba zancen burodi na yi ba, sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da. na Sadukiyawa.” 12 Sa’an nan ne fa suka fahinta cewa ba ce musu ya yi su yi hankall da yistin burodi ba, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da ta Sadukiyawa.

Babbar Bayyana Yarda ga Yesu

13 To, da Yesu ya shiga ƙasar Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane ke cewa Ɗam Mutun ya ke?” 14 Sai suka ce, “Wasu na cewa Yohana Maibabtisma, wasu kuwa, Iliya, wasu kuma, Irimiya ko kuwa ɗaya daga cikin annabawa.” 15 Ya ce musu, “Amma ku fa, wa ku ke cewa na ke?” 16 Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye.” 17 Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Siman Bar-Yona! Don ba ɗan’adan ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da ke Sama. 18 Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, kuma kan dutsen nan ne zan gina ikiliziyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ba. 19 Kuma zam ba ka mabuɗan Mulkin Sama. Kome ka ƙulla a duniya, a ƙulle ya ke har a Sama ma. Komai ka warware a duniya, a warware ya ke bar a Sama ma.” 20 Sai ya kwaɓi almajiransa ƙwarai kada su gaya wa kowa shi ne Almasihu.

Yesu ya yi Faɗim Mutuwarsa da Tashinsa

21 Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa lalle ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri-iri a hannun shugabanni da manyan malamai da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi. 22 Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, “Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!” 23 Amma Yesu ya juya ya ce da Bitrus, “Ka yi nesa da ni, Shaiɗan! Kā tare gabana. Ba ka tattalin al’amuran Allah sai na mutane.”

24 Sai Yesu ya ce da almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya shafa jini a wuyansa a, ya bi ni. 25 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi. 26 Me mutun ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutun zai iya bayarwa ya fanshi ransa? 27 Don Ɗam Mutun zai zo cikin ɗaukakar Ubansa tare da mala’ikunsa. A sa’an nan ne zai sāka wa kowane mutun gwargwadon aikinsa. 28 Hakika, ina gaya muku, akwai wasu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗam Mutun na zuwa cikin Mulkinsa.”

17

Kamanninsa ya Sake a kan Dutse

Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus da Yakubu da ɗan’uwansa Yohana, ya ja su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. 2 Sai kamanninsa ya sake a gabansu, fuskatasa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske. 3 Sai ga Musa da Iliya sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu. 4 Sai Bitrus ya ce da Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da mu ke nan wurin. In kana so, sai in kafa bukkoki uku a nan, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta lliya.” 5 Yana cikin magana sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana Ƙaunataccena, wanda na ke farinciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.” 6 Da almajiran suka ji haka, sai suka faɗi ƙasa duk tsoro ya rufe su. 7 Amma sai Yesu ya zo ya taɓa su, ya ce: “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8 Da suka daga kai ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.

9 Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin nan da kuka gani, sai an ta da Ɗam Mutun daga matattu.” 10 Sai almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, yaya kuwa malaman Attaura ke cewa lalle ne Iliya ya riga zuwa?” 11 Sai ya amsa ya ce, “Lalle Iliya zai zo ne, zai kuwa raya dukkan abubuwa. 12 Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗam Mutun zai sha wuya a hannunsu.” 13 Sa’an nan ne almajiran suka gane ashe zancen Yohana Maibabtisma ya ke musu.

Ya Warkad da Yaro Mai Farfaɗiya

14 Da suka isa wurin taro, sai wani mutun ya zo gare shi, ya durƙusa a gabansa, ya ce, 15 “Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa ya kan faɗa wuta da kuma ruwa. 16 Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkad da shi ba.” 17 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku kawo min shi nan.” 18 Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke. 19 Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a keɓe, suka ce, “Me ya sa mu muka ƙasa fid da shi?” 20 Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Don hakika, ina gaya muku, in da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da sai ku ce da dutsen nan, ‘Kau daga nan, ka koma can!&8221;, sai kuwa ya kau. Babu kuwa abin da zai gagare ku. 21 Ai irin wannan ba ya fita sai da addu’a da hana kai abinci.”

Yesu ya Sake yin Faɗin Mutuwarsa

22 Tun suna ƙasar Galili, sai Yesu ya ce da su, “Za a ba da Ɗam Mutun ga mutane, 23 za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙinciki ya rufe su.

24 Da suka zo Kafarnahum sai masu karɓar rabin shekel na gudummawar Ɗakin Ibada suka je wurin Bitrus, suka ce, “Shugabanku na ba da gudummawar?” 25 Ya ce, “I, ya kan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani Siman? Wurin wa sarakunan duniya ke karɓar kuɗin fito ko haraji, wurin ’ya’yansu, ko kuwa wurin wasu?” 26 Sa’ad da kuma ya ce, “Wurin wasu mana,” sai Yesu ya ce masa, “Wato, ’ya’yan an ɗauke musu ke nan. 27 Duk da haka, don kada mu ba su haushi, sai ka je tafki ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato nawa da naka.”

18

Misali da Ƙaramin Yaro

A lokacin nan sai almajiran suka zo wurin Yesu, suka ce, “Wa ya fi girma duka a Mulkin Sama?” 2 Sai ya kira wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, 3 ya ce, “Hakika, ina gaya muku im ba kun juyo kun zama kamar kananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba. 4 Duk wanda ya ƙasƙantad da kansa kamar ɗan yaron nan, ai shi ne mafi girma a Mulkin Sama.

5 Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. 6 Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen nika a wuyansa, a kuma nutsad da shi a zurfin teku.

7 Kaiton duniya saboda sanadin ɗaukar zunubi! Lalle sanadin ɗaukar zunubi ba shi da makawa, duk da haka wanda shi ne sanadin ya shiga uku! 8 In kuwa hannunka ko ƙafarka na sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga mulkin rai madawwami da dungu ko da gurguntaka, da a jefa ka madawwamiyar wuta da hannu biyu ko ƙafa biyu. 9 In kuwa idonka na sa ka laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga mulkin rai madawwami da ido ɗaya, da a jefa ka wutar Jahannama da ido biyu.

10 Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara. Ina gaya muku, mala’ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da ke Sama. 11 Don Ɗam Mutun ya zo ne musamman ceton abin da ya ɓata. 12 To, me kuka gani? In wani na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta sangarta, ashe ba zai bar casa’in da taran nan a gindin dutse, ya je neman wadda ta sangartan ba? 13 In kuwa ya samo ta, labudda, ina gaya muku, ai farincikin da ya ke yi a kanta ya fi na casa’in da taran nan da ba su taɓa sangarta ba. 14 Haka ma, ba nufin Ubanku da ke Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara ya halaka.

In Ɗan’uwanka ya yi maka Laifi

15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, sai ka je, ka gaya masa laifinsa, kai da shi ku kaɗai. In ya saurare ka, to, kā maido ɗan’uwanka ke nan. 16 In kuwa bai saurare ka ba, sai ka tafi da mutun ɗaya ko biyu, don a tabbatad da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku. 17 In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikiliziya. In kuma har ya ƙi sauraron ikiliziyar, sai ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji. 18 Hakika, ina gaya muku, komai kuka ƙulla a duniya, a ƙulle ya ke har a Sama ma. Komai kuka warware a duniya, a warware ya ke har a Sama ma. 19 Har wa yau dai ina gaya muku, im mutum biyu daga cikinku ra’ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da ke Sama zai yi musu shi. 20 Don kuwa inda mutum biyu ko ijku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.”

21 Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan’uwana zai yi min laifi in yafe masa? Har sau bakwai?” 22 Yesu ya ce masa, “Ba sau bakwai kawai na ce maka ba, sai dai bakwai har sau saba’in.

23 “Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da ke son ya yi ƙididdigar dukiyarsa da ke hannun bayinsa. 24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda ya ke bi talanti dubu goma bashi. 25 Da ya ke ya gagara biya, sai ubangijinsa ya yi umarni a sai da shi da matatasa da ’ya’yansa da kuma duk abin da ya mallaka, a biya kuɗin. 26 Sai bawan ya faɗi a gabansa ya yi masa ladabi, ya ce, ‘Ya ubangiji, ka yi min haƙuri, zam biya ka tsaf.’ 27 Saboda tausayin bawan nan sai ubangijinsa ya sake shi, ya yafe masa bashin. 28 Amma wannan bawan, da fitarsa sai ya tarad da wani abokin bautarsa, wanda ya ke bi dinari ɗari bashi. Sai ya cafi wuyansa, ya ce, ‘Biya ni abin da na ke binka.’ 29 Sai abokin bautarsa ya faɗi a gabansa, ya yi ta roƙonsa ya ce, ‘Ka yi min haƙuri, ai zam biya ka.’ 30 Amma ya ƙi, ya kuma je ya sa shi a kurkuku har sai yā biya bashin. 31 Da abokan bautarsa suka ga abin da ya faru, sai suka yi baƙinciki gaya, bar suka je suka gaya wa ubangijinsu duk abin da ya gudana. 32 Sai ubangiiin nasa ya kira shi, ya ce masa, ‘Kai mugun bawa ne! Na yafe maka duk bashin nan saboda ka roƙe ni, 33 ashe bai kyautu kai ma ka ji tausayin abokin bautarka, kamar yadda na ji tausayinka ba?’ 34 Sai ubangijinsa ya yi fushi, ya ba da shi ga masu azabtarwa har sai yā biya duk bashin da a ke binsa. 35 Haka kuma Ubana da ke Sama zai yi da kowannenku, im ba kun yafe wa ’yan’uwanku da zuciya ɗaya ba.”

19

To, da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya bar ƙasar Galili, ya shiga ta Yahudiya, wadda ta ke ƙetaren Kogin Urdun. 2 Taro mai yawan gaske suka bi shi, ya kuwa warkad da su a can.

Maganar Kisanaure

3 Sai wasu Farisiyawa suka zo wurinsa su gwada shi, suka ce, “Halal ne mutun ya saki matatasa a kan kowane dalili?” 4 Ya amsa ya ce, “Ashe ba ku taɓa karantawa ba ne, cewa wanda ya halicce su tun farko dā ma ya yi su ne namiji da mace?” 5 Ya kuma ce, “Don haka fa sai mutun ya bar uwatasa da ubansa, ya tsaya ga matatasa. Haka su biyun nan su zama jiki guda. 6 Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne. Abin da Allah fa ya gama, kada mutun ya raba.” 7 Sai suka. ce masa, “To, dom me Musa ya yi umarni a ba da takardar kisan-aure, a kuma saki matar?” 8 Ya ce musu, “Don taurin-kanku ne Musa ya yarje muku ku saki matanku, amma ba haka ya ke ba tun farko. 9 Kuma ina gaya muku, kowa ya saki matatasa, im ba a kan laifin zina ba, ya kuma auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”

10 Sai almajiran suka ce masa, “In ko haka tsakanin mutun da matatasa ya ke, ashe ma rashin yin aure ya fi amfani. 11 Amma sai ya ce musu, “Ba duk mutun ne zai iya ɗaukar maganan nan ba, sai dai waɗanda aka yarje wa. 12 Akwai waɗanda aka haifa babanni, akwai kuma waɗanda mutane ne suka mai da su babanni. Akwai kuma waɗanda suka mai da kansu kamar babanni don ƙaunar Mulkin Sama. Duk mai iya ɗaukar maganan nan, yă ɗauka.

13 Sa’an nan aka kawo masa yara ƙanana don ya ɗora musu hannu, ya yi musu addu’a, amma almajiran suka kwaɓe su. 14 Yesu kuwa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai Mulkin Sama na irinsu ne.” 15 Sai ya ɗora musu hannu, ya yi tafiyarsa.

Saurayi Mai Neman Rai Madawwami

16 Sai ga wani ya matso wurinsa, ya ce, “Ya Shugaba, wane aiki nagari ne da lalle zan yi in sami rai madawwami?” 17 Sai ya ce masa, “Dom me ka ke tambayata kan abin da ke nagari? Ai Managarci ɗaya ne. In kuwa kana so ka sami rai madawwami, to, sai ka kiyaye Umarnin nan.” 18 Sai ya ce masa, “Waɗanne?” Yesu ya ce, “Kada ka yi kisankai, Kada ka yi zina, Kada ka yi sata, Kada ka yi shaidar zur, 19 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma, Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.” 20 Sai saurayin ya ce da shi, “Ai duk na kiyaye waɗannan, me kuma ya rage mini?” 21 Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sai da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, sai ka sami taskar dukiya a Sama. Sannan ka zo ka bi ni.” 22 Da saurayin nan ya ji haka, sai ya tafi yana mai baƙinciki, don yana da arziki ƙwarai.

23 Sai Yesu ya ce da almajiransa, “Hakika, ina gaya muku, da wuya mai arziki ya sami shiga Mulkin Sama. 24 Har wa yau ina gaya muku, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta ƙofar allura, a kan mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 25 Da almajiran suka ji haka, sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?’ 26 Amma sai Yesu ya dube su, ya ce da su, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.” 27 Sai Bitrus ya amsa ya ce, “To, ai ga shi mun ya da komai, mun bi ka. Me za mu samu ke nan?” 28 Sai Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, in aka sabunta halitta, sa’ad da Ɗam Mutun ya zauna a kan gadon sarautarsa na ɗaukaka, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kan gadajen sarauta goma sha biyu, kuna hukunta kabilun nan goma sha biyu na Bani Isra’ila. 29 Kowa ya bar gidaje, ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata, ko uwa, ko uba, ko ’ya’ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu ɗari, ya kuma gaji rai madawwami. 30 Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.

20

Biyan Leburorin Garkar Inabi

Mulkin Sama kamar wani maigida ya ke, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki leburori don aikin garkarsa ta inabi. 2 Da ya yi lada da su a kan dinari guda a wuni, sai ya tura su garkarsa. 3 Wajen ƙarfe tara kuma da ya fita, sai ya ga wasu na zaman banza a bakin kasuwa. 4 Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata, zan kuwa biya ku gwargwado.’ Sai suka tafi. 5 Da ya sake fita wajen tsakar rana, da kuma azahar, sai ya sake yin haka dai. 6 Wajen la’asar kuma sai ya fita ya sami wasu a tsaitsaye, ya ce musu, ‘Dom me ku ke zaman banza wuni zubur?’ 7 Sai suka cemasa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ Sai ya ce musu, ‘Kuma ku tafi garkata.’ 8 Da magariba ta yi, sai mai garkar inabin ya ce da wakilinsa, ‘Kirawo leburorin, ka biya su hakkinsu, ka fara daga kan na ƙarshen har zuwa na farko.’ 9 Da waɗanda aka ɗauka wajen la’asar suka zo, sai kowannensu ya sami dinari guda. 10 To, da na farkon suka zo sai suka zaci za su sami fiye da haka. Amma sai su ma aka ba kowannensu dinari guda. 11 Da suka karɓa sai suka yi ta yi wa maigidan gunaguni, 12 suna cewa, ‘Na bayan nan ai aikin sa’a guda kawai suka yi, ka kuwa daidaita mu, mu da muka wuni zubur muna shan wahala da ƙunar rana.’ 13 Sai ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Abokina, ai ban cuce ka ba. Ashe ba mu yi lada da kai a kan dinari guda ba? 14 Sai ka karɓi halalinka ka tafi. Ni ne na ga damar ba waɗannan na ƙarshen daidai da yadda na ba ka. 15 Ashe ba ni da ikon yin abin da na ga dama da abin da ke mallakata? Ko kuwa kana jin haushin alherina ne?’ 16 Saboda haka na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma za su koma na ƙarshe.”

17 Yesu na cikin tafiya Urushalima, sai ya ɗauki almajiran nan goma sha biyu waje ɗaya. Suna cikin tafiya sai ya ce musu, 18 “To, ga shi za mu Urushalima, kuma za a ba da Ɗam Mutun ga manyan malamai da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, 19 su bashe shi ga sauran al’umma, su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma giciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.

Roƙon Uwar ’Ya’yan Zabadi

20 Sa’an nan sai uwar ’ya’yan Zabadi ta matso wurinsa tare da ’ya’yanta, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi wani abu. 21 Sai ya ce da ita, “Me ƙi ke bukata?’ Ta ce masa, “Ka yi umarni waɗannan ’ya’yana biyu su zauna, ɗaya a hannunka na dama, ɗaya a na hagu, a mulkinka.” 22 Amma sai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ku san abin da ku ke roƙo ba. Kwa iya sha da ludayina?” Suka ce masa, “Ma iya.” 23 Sai ya ce musu, “Lalle kwa sha da ludayina, amma zama a hannuna na dama da hannuna na hagun, ba nawa ba ne da zam bayar, ai na waɗanda Ubana ya riga ya shirya wa ne.” 24 Da almajiran nan goma suka ji haka, sai suka ji haushin ’yan’uwan nan biyu. 25 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun san cewa sarakunan sauran al’umma su kan nuna musu iko, hakimansu ma su kan gasa masu iko. 26 Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. 27 Wanda duk kuma ke son ya shugabance ku, lalle ne ya zama banwanku, 28 yadda Ɗam Mutum ma ya zo ne ba don a bauta masa ba, sai dai don shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Ya Warkad da Makafi Biyu

29 Suna fita daga Yariko ke nan, sai wani babban taro ya bi shi. 30 Sai ga mutum biyu makafi zaune a bakin hanya. Da suka ji dai Yesu ne ke wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Ubangiji, ka ji tausayimmu, ya Ɗan Dawuda!” 31 Sai jama’a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya su ke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiii, ka ji tausayimmu, ya Ɗan Dawuda!” 32 Sai Yesu ya tsaya, ya yi kiransu ya ce, “Me ku ke so in yi muku?” 33 Suka ce da shi, “Ya Ubangiji, mu dai mu sami gani!” 34 Don kuma tausayi, sai Yesu ya shafa idanunsu, nan take suka sami gani, suka bi shi.

21

YESU A URUSHALIMA

Mutanen Urushalima sun Marabci Yesu

Da suka kusato Urushalima suka zo Baitafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da ke gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure da kuma ɗanta. Ku kwanto su. 3 Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne ya ke bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nandanan.” 4 An yi wannan kuwa don a cika faɗar Annabi Zakariya ne, cewa,

5 “Ku ce da ’yar Sihiyona,
Ga Sarkinki na zuwa gare ki,
Yana mai ƙanƙan-da-kai,
Yana kuma kan aholaki, wato ɗan jaki.”

6 Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu. 7 Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa musu mayafansu, ya hau. 8 Yawancin jama’a suka shisshimfiɗa mayafansu a kan hanya, wasu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a kan hanya. 9 Taron jama’a da ke tafiya a gabansa da kuma na bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga ɗan Dawuda! Yabo ya tabbata ga Maizuwa da sunan Ubangiji! Allah yă yi masa albarka daga Sama mafi ɗaukaka!” 10 Da ya shiga Urushalima sai dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Yau kuma wannan wanene?” 11 Sai jama’a suka ce, “Ai wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”

Ya Kori Masu Saye da Sayarwa a Ɗakin Ibada

12 Sai Yesu ya shiga Ɗakin Ibada ya kokkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburan ’yan-canjin-kuɗi da kujerun masu sai da tattabaru. 13 Ya ce musu, “A rubuce ya ke, cewa, ‘Za a kira gidana Ɗakin addu’a’, amma ku kun maishe shi kogon ’yam-fashi.”

14 Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Ɗakin Ibada, ya kuwa warkad da su. 15 Amma da manyan malamai da malaman Attaura suka ga abubuwan al’ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Ɗakin Ibada suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi. 16 Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan ke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba ne, cewa,

‘Kai ne ka ƙaddara ’yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”

17 Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Baitanya, ya sauka a can.

Labarin Ɓaure Marar Haifuwa

18 Washegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa. 19 Da ya ga. wani ɓaure a gefen hanya, sai ya je wurin, amma bai sami komai ba sai ganye kawai. Sai ya ce da ɓauren, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe. 20 Da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nandanan?” 21 Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce da dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku. 22 Komai kuka roƙa da addu’a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”

23 Da ya shiga Ɗakin lbada yana cikin koyarwa, sai manyan malamai da shugabannin jama’a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini ka ke yin abubuwan nan, kuma wa ya ba ka izinin?” 24 Sai Yesu ya amsa musu, ya ce “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini na ke yin abubuwan nan. 25 To, babtismad da Yohana ya yi, daga ina ta ke? Daga Sama ta ke, ko kuwa ta mutun ce?” Sai suka yi ta muhawara da juna, suna cewa, “Im muka ce, ‘Daga Sama ta ke,’ sai ya ce mana, ‘To, dom me ba ku gaskata shi ba?’ 26 In kuwa muka ce, ‘Ta mutun ce,’ ai muna jin tsoron jama’a, don duk kowa ya ɗauki Yohana a kan annabi ne.” 27 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini na ke yin abubuwan nan ba.

28 “To, me kuka gani? An yi wani mutum mai ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’ 29 Sai ya ce, ‘Na ƙi. Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi. 30 Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, “To, za ni, baba,’ amma bai je ba. 31 To, wanene a cikin su biyun ya yi abin da ubansu ke so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah. 32 Ga shi Yohana ya zo wurinku yana aikin gaskiya, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, kuma duk da ganin haka, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.

Miyagun Masu Sufuri

33 “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garka inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata ’yar hasumiyar tsaro. Ya ba wasu manoma sufurin garkar, sa’an nan ya tafi wata ƙasa. 34 Da kakar inabi ta yi kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar. 35 Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya duka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya. 36 Har wa yau ya sake aiken wasu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka. 37 Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sa ga girman ɗana.’ 38 Amma da manoman suka ga ɗan, sai suka ce da juna, ‘Ai wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gadonsa ya zama namu.’ 39 Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi. 40 To, sa’ad da ubangijin garkan nan ya zo, me zai yi manoman nan?” 41 Sai suka ce masa, “Sai ya yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba wasu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”

42 Yesu ya ce musu, “Ashe ba ku taɓa karantawa ba ne a Littattafai Tsarkaka? cewa,

‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ya zama babban dutsen harsashin gini.
Wannan aikin Ubangiji ne,
A gare mu kuwa abin al’ajabi ne’.

43 Don haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al’umma mai aikata abin da Mulkin ke haddasawa. 44 Kowa ya faɗo kan dutsen nan, sai ya rugurguje. Amma. wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”

45 Da manyan malamai da Farisiyawa. suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane ashe da su ya ke. 46 Amma da suka nemi kama shi, sai suka ji tsoron jama’a, don su sun ɗauke shi kan annabi ne.

22

Bikin ɗan Sarki

Sai Yesu ya sake yi musu magana da misalai ya ce, 2 “Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki. 3 Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatan suka ƙi zuwa. 4 Har wa yau sai ya sake aiken wasu bayin, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, Ga shi na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya komai, su zo bikin mana!’ 5 Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gonatasa, wani kuma cinikinsa. 6 Sauran kuwa suka kame bayin nasa, suka wulakanta su, suka kashe su. 7 Sai sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus. 8 Sa’an nan ya ce da bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9 Saboda haka ku tafi kofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’ 10 Sai bayin suka yi ta bin titi-titi, suka riƙa taro duk waɗanda suka samu, miyagu da nagari duka, bar wurin bikin ya cika maƙil da baki.

11 “Da sarki ya shigo ganin bakin, sai ya ga wani mutun a can wanda bai sa riga irin ta biki ba. 12 Sai ya ce masa, ‘Malan, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba? Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13 Sai sarki ya ce da barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da gama haƙora.’ 14 Da yawa a ke kira amma kaɗan a ke zaɓe.”

Harajin Kaisar

15 Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganatasa. 16 Suka aiko almajiransu wurinsa tare da wasu mutanen Hirudus, suka ce, “Haba Malan, ai mun san kai mai gaskiya ne, sai koyad da tafarkin Allah sosai ka ke yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai. 17 To, faɗa mana abin da ka gani. Shin daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?” 18 Yesu kuwa don ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Me ku ke haƙa mini rami? Ku munafukai! 19 Ku nuna min kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari. 20 Yesu ya ce da su, “Suran nan da sunan nan na wanene?” 21 Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa’an nan ya ce musu, “To, ai sai ku mayar wa da Kaisar abin da ke na Kaisar, ku kuma mayar wa da Allah abin da ke na Allah.” 22 Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.

Yesu ya Tuƙe Hanzarin Sadukiyawa

23 A ran nan sai wasu Sadukiyawa, su da ke cewa wai ba Tashin Matattu, suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya, 24 suka ce, “Malan, Musa dai ya ce, ‘Im mutun ya mutu, bai bar baya ba, sai lalle ɗan’uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’ 25 To, an yi wasu ’yan’uwa maza bakwai a cikimmu. Na farkon ya yi aure, da ya mutu, kuma da ya ke bai haifu ba, sai ya bar wa ɗan’uwansa matatasa. 26 Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai din. 27 Bayansu duka sai matar ta mutu. 28 To, a Tashin Matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”

29 Amma sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, don ba ku san Littattafai Tsarkaka ba, ba ku kuma san ikon Allah ba. 30 Don a Tashin Matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala’ikun da ke Sama a ke. 31 Game da Tashin Matattu, ashe ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce da ku ba? cewa, 32 ‘Ni ne Allahn Ibrahim, kuma Allahn Isiyaku, kuma Allahn Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.” 33 Da jama’a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwatasa.

Umarni Mafi Girma

34 Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, sai suka taru. 35 Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya yana gwada shi, ya ce, 36 “Malan, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?” 37 Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukan hankalinka. 38 Wannan shi ne babban umarni kuma na farko. 39 Na biyu kuma kamarsa ya ke, Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka. 40 A kan umarnin nan biyu duk Attaura da Littattafan Annabawa suka rataya.”

Tun Farisiyawa na tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya, 42 ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wanene?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.” 43 Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu Tsattsarka, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,

44 Ubangiji ya ce da Ubangijina,
Zauna a hannuna na dama,
Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’

45 Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?” 46 Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin-halin sake tambayarsa wani abu.

23

Yesu ya Tsawata wa Farisiyawa

Sa’an nan Yesu ya yi wa jama’a da almajiransa magana, ya ce, 2 “Malaman Attaura da Farisiyawa su suka tsaya a matsayin Musa. 3 Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma ban da aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa. 4 Su kan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi. 5 Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har iya gwiwa. 6 Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami’u, 7 a kuma gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa kiransu ‘Alaramma’. 8 Amma ku kam, kada a kira ku ‘Alaramma’, don Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ’yan’uwa ne. 9 Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya gare ku, wanda ke Sama. 10 Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, don Shugaba ɗaya gare ku, Almasihu. 11 Amma wanda ke babba a cikinku shi zai zama baranku. 12 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantad da shi. Mai ƙasƙantad da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.

13 “Kun shiga uku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga. 14 Kun shiga uku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Ku kan ci kayan matan da mazansu suka mutu, ku kan yi doguwar addu’a don bad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani. 15 Kun shiga uku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Ku kan ƙetare koguna, ku kuma ƙetare kashin giwa don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, ku kan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.

16 “Kun shiga uku, makafin jagora, ku da ke cewa, ‘Kowa ya rantse da Wuri Tsattsarka ba komai, amma duk wanda ya rantse da zinariyar Wuri Tsattsarka, sai rantsuwarsa ta kama shi.’ 17 Ku makafi wawaye! Wanne ya fi girma, zinariyar ce ko kuwa Wuri Tsattsarkan da ke tsarkake zinariyar? 18 Kuma ku kan ce, ‘Kowa ya rantse da Wurin Baiko, ba komai. Amma duk wanda ya rantse da baikon da aka ɗora a Wurin, sai rantsuwarsa ta kama shi.’ 19 Ku makafi! Wanne ya fi girma, baikon ne ko kuwa Wurin yinsa da ke tsarkake baikon? 20 Don haka kowa ya rantse da Wurin Baikon, ya rantse ke nan da shi, da duk abin da ke kansa. 21 Kuma duk wanda ya rantse da Wuri Tsattsarka ya rantse ke nan da shi, da kuma wanda ke zaune a cikinsa. 22 Kuma kowa ya rantse da Sama, ya rantse ke nan da gadon sarautar Allah, da kuma wanda ke zaune a kansa.

23 “Kun shiga uku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Ku kan fid da zakkar na’ana’a, da anise, da lafsur, amma kun ya da muhimman jigajigan Attaura, wato gaskiya da tausayi da amana. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da ya da sauran ba. 24 Makafin jagora, ku kan tace ƙwaro dam mitsil, amma ku kan hadiye raƙumi!

25 “Kun shiga uku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Ku kan wanke bayan kwarya da akushi, amma ta ciki sai zalunci da zari. 26 Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin, don bayansu ma ya tsarkaka.

27 “Kun shiga uku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kama kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa ku ke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri-iri. 28 Haka ku ke masu gaskiya a idon mutane, amma ta ciki sai munafunci da mugun aiki.

29 Kun shiga uku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Ku kan yi gini a kan kaburburan annabawa, kuna ƙawata masu gaskiya. 30 Kuna cewa, ‘Da mun zauna a zamanin kakannimmu, da ba mu taya su zub da jinin annabawa ba.’ 31 Ta haka kuka shaidi kanku ku ne ’ya’yan masu kisan annabawa. 32 To, ai sai ku noma gandun kakanninku. 33 Ku macizan ƙaiƙaiyi! Yaya za ku tsere wa hukuncin Jahannama? 34 Saboda haka na ke aiko muku da masu yin faɗin Maganar Allah, da masu hikima, da masana Attaura, za ku kashe wasunsu, ku giciye wasu, ku kum yi wa waɗansu bulala a majami’unku, kuna binsu gari-gari kuna gwada musu azaba. 35 Don alhakin jinin dukkan masu gaskiya da aka zubar a duniya yă komo kanku, tun daga jinin Habila mai aikin gaskiya, har ya zuwa na Zakariya dam Barakiya, wanda kuka kashe tsakanin Wuri Tsattsarka da Wurin Baiko. 36 Hakika, ina gaya muku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani.

Wohoho mutanen Urushalima! Woho mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko gareku! Sau nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza ke tattara ’yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi! 38 Ga shi am bar muku gidanku a yashe! 39 Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Yabo ya tabbata ga Maizuwa da sunan Ubangiji.’”

24

Yesu Ya Yi Faɗi kan Rushe Ɗakin Ibada

Yesu ya fita Ɗakin Ibada, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo suka nuna masa gineginen Ɗakin Ibadar. 2 Amma sai ya amsa musu ya ce, Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan’uwansa ba a baje shi ba.”

Dawowar Yesu da kuma Ƙarewar Zamani

Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Kuma mecece alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?” 4 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku. 5 Don mutane da yawa za su zo suna aron sunana, suna cewa su ne Almasihu, har su ɓad da mutane da yawa. 6 Za ku kuma riƙa jin labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lalle ne a yi haka, amma ƙarshen tukuna. 7 Kabila za ta tasam ma kabila, mulki ya tasam ma mulki. Za a kuma yi yunwa da raurawar ƙasa a wurare dabandaban. 8 Amma fa duk wannan somin azaba ne tukuna.

9 “Sa’an nan za su bashe ku, a kuntata muku, kuma su kashe ku. Duk al’ummai za su ƙi ku saboda sunana. 10 A sa’an nan da yawa za su ƙosa, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna. 11 Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa. 12 Saboda kuma yaɗuwar mugun aiki, sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi. 13 Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu. 14 Za a kuma yi Bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya don shaida ga dukkan kabilu. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.

Mummunan Aikin Sabo Mai ban Ƙyama

15 “Don haka sa’ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai ban ƙyama, wanda Annabi Ɗaniyelu ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Tsattsarka, (mai karatu fa yă fahinta), 16 to, sai waɗanda ke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu. 17 Wanda ke kan soro, kada ya sauko garin ɗaukar kayan da ke gidansa. 18 Wanda ke gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa. 19 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! 20 Ku yi addu’a kada gudunku ya zo cikin damuna, ko ran Asabar. 21 A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada. 22 Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba bil’adan ɗin da zai tsira. Amma albarkacin zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin. 23 A sa’an nan kowa ya ce muku, ‘Kun ga, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Ga shi can!’ kada ku yarda. 24 Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al’ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in da zai yiwu. 25 To, na dai gaya muku tun da wuri. 26 Saboda haka in sun ce da ku, ‘Ga shi can a jeji,’ kada ku fita. In kuwa sun ce, ‘Yana can cikin turaka,’ kada ku yarda. 27 Kamar yadda walkiya ta ke wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka komowar Ɗam Mutun za ta zama. 28 Inda mushe ya ke, ai a nan ungulu kan taru.

Alamonzin Dawowatasa

29 “Bayan tsabar wahalan nan, nandanan sai a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari kuma za su farfaɗo daga sararin sama, Za a kuma girgiza manya-manyan abubuwan da ke sararin sama. 30 A sa’an nan ne alamar Ɗam Mutun za ta bayyana a sararin sama, duk kabilun duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗam Mutun na zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa. 31 Zai kuwa aiko mala’ikunsa su busa ƙaho, mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato daga wannan bangon duniya zuwa wancan.

32 “Ku yi koyi da icen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan. 33 Haka kuma in kun ga duk waɗannan abubuwa, ku san cewa ya kusato, a bakin ƙofa ma ya ke. 34 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun anku. 35 Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.

36 “Amma fa wannan rana da wannan sa’a ba wanda ya sani, ko mala’ikun da ke Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 37 Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar ‘Dam Mutun za ta zama. 18 Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana, ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranad da Nuhu ya shiga jirgi, 39 ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗam Mutun za ta zama. 40 A sa’an nan za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 41 Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 42 To, ku kula fa, don ba ku san ranad da Ubangijinku zai dawo ba. 43 Amma dai ku san cewa, da maigida zai san ko a wane lokaci ne cikin dare ɓarawo zai zo, da sai ya zauna a fadake ya hana a shigam masa gida. 44 Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, don a lokacin da ba ku ata ba, Ɗam Mutun zai zo.

45 “Wanene amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangijinsa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari? 46 Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangijinsa ya dawo zai samu yana yin haka. 47 Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukkan mallakatasa. 48 Amma im bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ 49 sa’an nan ya soma dukan abokan bautarsa, yana ci yana sha tare da mashaya, 50 ai ubangijin wannan bawan zal zo a ranad da bai zata ba, kuma a lokacin da bai sani ba, 51 yă farfasa masa jiki da bulala, ya haɗa shi da munafukai. Nan za a yi kuka da gama haƙora.

25

Labarin ‘Yammata Goma

“Sa’an nan za a kwatanta Mulkin Sama da ’yammata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango. 2 Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima. 3 Don kuwa lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe ba su riƙo mai ba. 4 Masu hikiman nan kuwa sun riƙo ƙwalaben mai da fitilunsu. 5 Da ya ke angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su. 6 Can tsakad dare sai aka ji kira, ana cewa, “Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!” 7 Sai duk ’yammatan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu. 8 Sai wawayen nan suka ce da masu hikimar, ‘Ku sam mana ɗam manku kaɗan mana, fitilummu na mutuwa!’ 9 Amma sai masu hikimar suka amsa suka ce, ‘Ai watakila ba zai ishe mu mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’ 10 Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda ke shirye sai suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa. 11 Daga baya sai waɗancan ’yammatan ma suka iso, suka ce, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, buɗe mana mana!’ 12 Sai ya amsa ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, ni ban san ku ba.’ 13 Don haka, sai ku kula, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa’ar.

Mai Ɗanka wa Bayinsa Talanti

14 “Kamar mutun ne, da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya ɗanka musu dukiyatasa. 15 Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa’an nan ya tafi. 16 Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nandanan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri. 17 Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri. 18 Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangiiin nasa. 19 To, da aka daɗe sai ubangijin bayin nan ya dawo ya yi ƙididdigar lissafi da su. 20 Shi wannan da ya karɓi talanti biyar sai ya matso ya kawo wasu talanti biyar, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyar, ga shi kuma na ci ribar biyar.’ 21 Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farinciki tare da ubangijinka.’ 22 Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni taland biyu, ga shi kuma na ci ribar biyu.’ 23 Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farinciki tare da ubangijinka.’ 24 Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, na san kai mutun ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne. 25 Shi ya sa na ji tsoro, har na je na yi tono na ɓoye talantinka. To, ga kayanka nan!’ 26 Sai ubangijinsa ya amsa masa ya ce, ‘Kai mugun bawa, malalaci! Ashe ka san ina girbi inda ba ni na shuka ba, kuma ni mai son banza ne? 27 Ashe da sai ka sa kuɗin nawa a banki, da na dawo, kuma da sai in karɓi abina bar da riba! 28 Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan. 29 Don duk mai abu a kan ƙara was har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da ya ke da shi ma, sai an karɓe masa. 30 Ku kuma jefa banzan bawan nan a cikin baƙin duhu. Nan za a yi kuka da gama haƙora.’

Zuwan Ɗam Matun cikin Daukakatasa

“Sa’ad da Ɗam Mutun ya zo cikin ɗaukakatasa tare da mala’iku duka, sa’an nan ne zai zauna a kan gadon sarautarsa na ɗaukaka. 32 Za a tara dukkan al’ummai a gabansa, zai kuma wawware su daban-daban, kamar yadda makiyayi ke ware tumaki da awaki. 33 Zai sanya tumaki a hannunsa na dama, awaki kuwa a na hagu. 34 Sa’an nan ne Sarki zai ce da waɗanda ke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku sami gado cikin mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya. 35 Don na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi bakunci, kun saukad da ni. 36 Na yi huntanci, kun tufatad da ni.’ Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’ 37 Sa’an nan ne masu gaskiya za su amsa masa su ce, yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayad da kai? 38 Kuma yaushe muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufatad da kai? 39 Ko kuma yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?’ 40 Kuma Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da ya ke kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafiya ƙasƙanci, ai ni kuka yi wa.’ 41 Sa’an zai ce da waɗanda ke hannunsa na hagu, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala’ikunsa. 42 Don na ji yunwa, ba ku ba ni abinci ba. Na ji ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba. 43 Na yi baƙunci, ba ku sauke ni ba. Na yi huntanci, ba ku tufatad da ni ba. Na yi rashin lafiya, kuma ina kurkuku, ba ku kula da ni ba.’ 44 Sa’an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa, ko d ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba? 45 Sa’an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da ya ke ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafiya ƙasƙanci ba, ai ni ma ba ku yi mini ba.’ 46 Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu gaskiya kuwa rai madawwami.”

MUTUWAR YESU

26

Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya ce da almajiransa, 2 “Kun san Idin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗam Mutun a giciye shi.”

3 Sai manyan malamai da shugabannin jama’a suka taru a gidan Babban Malamin, mai suna Kayafas. 4 Suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci su kashe shi. 5 Amma sai suka ce, “Badai a lokacin Idi ba, don kada jama’a ta yi hargowa.”

An Shafa Masa Man Ƙanshi

To, sa’ad da Yesu ke Baitanya a gidan Siman Kuturu, 7 sai wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulu na man ƙanshi mai tsadar gaske, ta tsiyaye masa a ka, lokacin da ya ke cin abinci. 8 Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce. “Wannan almubazzaranci fa! 9 Gama da an sai da man nan kuɗi mai yawa, am ba gajiyayyu!” 10 Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Dom me ku ke damun matan nan? Ai alheri ta yi mini, na gaske kuwa. 11 Kullum kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum ne ku ke tare da ni ba. 12 Zuba man nan da ta yi a jikina, ta yi shi ne don tanadin jana’izata. 13 Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi Bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

Yahuda ya Bashe Shi

14 Sai ɗaya daga cikin Sha biyun nan, mai suna Yahuda Iskariyoti, ya je wurin manyan malamai 15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗin azurfa talatin, suka ba shi. 16 Tun daga lokacin nan ne ya nemi hanyad da zai bashe shi.

17 To, a ranar farko ta Idin Burodi Marar Yisti sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, “Ina ka ke so mu shirya maka cin Jibin Ƙetarewa?” 18 Sai ya ce, “Ku shiga cikin gari wurin wane, ku ce masa, ‘Shugaba ya ce lokacinsa ya yi kusa; zai ci Jibin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.’” 19 Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

Yesu ya Tona Yahuda

20 Da magariba ta yi, sai ya zauna cin abinci tare da almajiran nan goma sha biyu. 21 Suna cikin cin abinci, sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 22 Sai suka yi baƙinciki gaya, suka fara ce da shi daidai da daidai, “Ni ne, ya Ubangiji?” 23 Sai ya amsa ya ce, “Wanda mu ke ci akushi ɗaya, shi ne zai bashe ni. 24 Ɗam Mutun zai tafi ne, yadda labarinsa, ke rubuce, duk da haka mutumin nan da ke ba da Ɗam Mutun ya shiga uku! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.” 25 Sai Yahuda da ya bashe shi ya ce, “Ko ni ne, ya Shugaba?” Yesu ya ce masa, “Ga shi kai ma ka faɗa.”

26 Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.” 27 Sai ya ɗauki ƙoƙo, kuma bayan ya yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, “Dukkanku ku shassha. 28 Don wannan jinina ne na tabbatar Alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubansu. 29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranan nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.”

30 Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun. 31 Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku ƙosa da ni a wannan daren. Don a rubuce ya ke, cewa, ‘Zam buge makiyayi, tumakin garken kuwa su fasu.’ 32 Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.” 33 Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun ƙosa da kai, ni kam ba zan ƙosa ba faufau.” 34 Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan daren, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.” 35 Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.

Yesu da Alniajiransa a Jatsanzani

36 Sannan Yesu ya zo da su wani wurin da a ke kira Jatsamani. Ya ce da almajiransa, “Ku zauna nan, ni kuwa zan je can in yi addu’a.” 37 Sai ya ɗauki Bitrus da ’ya’yan nan na Zabadi guda biyu, ya fara baƙinciki da damuwa ƙwarai. 38 Sai ya ce musu, “Raina na shan wahala matuƙa, har ma kamar na mutu. Ku dakata nan, ku zauna a faɗake tare da ni.” 39 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya faɗi ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubana, im mai yiwuwa ne, ka ɗauke min shan wahalan nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.” 40 Sai ya komo wurin almajiran, ya samu suna barci, sai ya ce da Bitrus, “Ashe ba za ku iya zama a faɗake tare da ni ko da sa’a ɗaya ba? 41 Ku zauna a faɗake, ku yi addu’a kada ku faɗa ga gwaji. Zuciya kam ta ɗauka, jiki ne rarrauna.” 42 Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, a aikafa nufinka.” 43 Har yanzu dai ya dawo ya samu suna barci, don duk barci ya cika musu ido. 44 Har wa yau ya sake barinsu, ya koma ya yi addu’a ta uku, yana maimaita maganar dā. 45 Sai ya komo wurin almajiran, ya ce musu, “Har yanzu barci ku ke yi, kuna hutawa? To, ga shi lokaci ya yi kusa. Am ba da Ɗam Mutun ga masu zunubi. 46 Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe nin nan ya matso!”

Sun Ɗanƙe Yesu

47 Kamin ya rufe baki sai ga Yahuda, ɗaya daga cikin Shabiyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan malamai da shugabanni ne suka turo su. 48 To, mai bashe shin nan ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi.” 49 Nandanan sai ya matso wurin Yesu ya ce, “Ranka ya daɗe, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa. 50 Yesu ya ce masa, “Abokina, abin da ya kawo ka ke nan?” Sai suka matso suka danƙe Yesu, suka kama shi. 51 Sai ga ɗaya daga cikin waɗanda ke tare da Yesu ya miƙa hannu ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan Babban Malamin sara, ya ɗauke masa kunne. 52 Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zari takobi, takobi ne ajalinsa. 53 Kuna tsammani ba zan iya neman taimako gun Ubana ba, nandanan kuwa ya aiko min fiye da rundunonin mala’iku goma sha biyu? 54 To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai Tsarkaka kan lalle wannan abu ya kasance?” 55 Nan take Yesu ya ce da taron jama’a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗam-fashi? Kowace rana na kan zauna a Ɗakin lbada ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. 56 Amma duk wannan ya auku ne don a cika Littattafan Annabawa.” Daganan sai duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.

57 Sai waɗanda suka kama Yesu suka tafi da shi wurin Kayafas, Babban Malamin, inda malaman Attaura da shugabanni su ke tare. 58 Amma sai Bitrus ya bi shi daga nesanesa, har cikin gidan Babban Malamin. Da ya shiga daga ciki sai ya zauna cikin ma’aikatan Ɗakin lbada, don ya ga ƙarshen abin. 59 To, sai manyan malamai da duk majalisa suka nemi ƙazafin da za a yi wa Yesu don su samu su kashe shi. 60 Amma ba su samu ba, ko da ya ke masu shaidar zur da yawa, sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso, 61 suka ce, “Wannan ya ce wai zai iya rushe Wurin nan Tsattsarka na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.” 62 Sai Babban Malamin ya miƙe ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidad da mutanen nan ke yi a kanka fa?” 63 Amma Yesu na shiru. Sai Babban Malamin ya ce da shi, “Na gama ka da Allah Rayayye, faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.” 64 Sai Yesu. ya ce masa, “Ai kai ma ka faɗa. Ina kuwa gaya muku nan gaba za ku ga Ɗam Mutun zaune a hannun dama na Mai iko, yana kuma zuwa kan gajimare.” 65 Sai Babban Malamin ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi! 66 Me kuka gani?” Suka amsa suka ce, “Ya cancanci kisa!” 67 Sai suka tattofa masa yawu a fuska, suka nannaushe shi, wasu kuma suka mammare shi, 68 suna cewa, “Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!”

69 To, Bitrus kuwa na zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya kansa, ta ce, “Kai ma ai tare ka ke da Yesu Bagalile!” 70 Amma sai ya musa a gabansu duka ya ce, “Ni ban san abin da ƙi ke nufi ba.” 71 Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce da waɗanda ke tsaitsaye a wurin, “Ai mutumin nan tare ya ke da Yesu Banazarel” 72 Sai ya sake musawa har da rantsuwa ya ce, “Ban ma san mutumin nan ba.” 73 Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce da Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka.” 74 Sai ya fara la’anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nandanan sai zakara ya yi cara. 75 Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu, cewa, “Kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

27

Yesu a Gaban Bilatus

Da gari ya waye sai duk manyan malamai da shugabannin jama’a suka yi shawara a kan Yesu su kashe shi. 2 Sai suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Gwamna Bilatus.

3 Sa’ad da Yahuda mai bashe shin nan ya ga an yanke masa hukuncin kisa, sai ya yi nadama, ya mayar wa da manyan malamai da shugabanni kuɗin azurfa talatin ɗin nan, 4 ya ce, “Na ɗau zunubi da na da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwammu? Kai ka jiyo!” 5 Sai ya watsad da kuɗin azurfan nan a Wuri Tsattsarka, ya fita ya je ya rataye kansa. 6 Amma sai manyan malamai suka tsince kuɗin suka ce, “Bai halatta mu zuba su a Baitalmalin Ɗakin lbada ba, don kuɗin ladan kisankai ne.” 7 Sai suka yi shawara, suka sayi Filin Maginin Tukwane da kuɗin don makabartar baƙi. 8 Don haka, har ya zuwa yau, ana kiran filin nan, Filin Jini. 9 Ta haka aka cika faɗar Annabi Irimiya, cewa, “Sun ɗauki kuɗin azurfa talatin ɗin nan, wato awalajar shi wannan da wasu Bani Isra’ila suka yi wa ƙima, 10 suka sayi Filin Maginin Tukwane da su, yadda Ubangiji ya umarce ni.”

11 To, sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamnan kuma ya tambaye shi, “Ashe kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗan.” 12 Amma da manyan malaman da shugabanni suka ɗaɗɗora masa laifi, bai ce komai ba. 13 Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji yawan maganganun da su ke ba da shaida a kanka ba?” 14 Amma bai ba shi wata amsa ko da ta laifi guda da aka ɗora masa ba, har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.

An Yanke Masa Hukuncin Kisa

15 To, a lokacin Idi kuwa gwanma ya saba sakam ma jama’a kowane fursuna guda da su ke so. 16 A lokacin kuwa da wani shaharraren fursuna, mai suna Barabbas. 17 Da suka taru sai Bilatus ya ce da su, “Wa ku ke so in sakam muku? Barabbas ko kuwa Yesu da a ke kira Almasihu?” 18 Don ya sani saboda hassada ne suka bashe shi. 19 Ban da haka kuma, lokacin da ya ke zaune kan gadon shari’a, sai matatasa ta aiko masa da cewa, “Fita sha’anin marar laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai game da mafarkinsa.” 20 To, sai manyan malamai da shugabanni suka rarrashi jama’a a kan su zaɓi Barabbas, Yesu kuwa a kashe shi. 21 Sai gwamnan ya sake ce da su, “Wanene a cikin biyun nan ku ke so in sakam muku?” Sai suka ce, “Barabbas.” 22 Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da a ke kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A giciye shi!” 23 Ya ce “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?” Amma su sai ƙara hayagaga su ke yi, suna cewa, “A giciye shi!”

24 Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai ma hargitsi na shirin tashi, sai ya ɗebi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama’a, “Ni kam na kuɓuta daga alhakin jinin mai gaskiyan nan. Sai ku ji da shi.” 25 Sai duk jama’a suka amsa suka ce, “Alhakin jininsa a wuyammu, mu da ’ya’yammu!” 26 Sannan ya sakam musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a giciye shi.

27 Sai sojan gwamna suka kai Yesu cikin faɗar gwamna, suka tara dukkan kamfanin soja a kansa. 28 Sai suka tube shi, suka yafa masa wata jar alkyabba. 29 Sai suka yi wani kambi na ƙaya, suka sa masa a ka, suka ɗanka masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna masa ba’a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” 30 Suka tattofa masa yawu, suka karɓe sandan, suka ƙwala masa a ka. 31 Da suka gama yi masa ba’a, sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufatin, suka tafi da shi su giciye shi.

32 Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Siman. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki giciyen Yesu.

An Giciye Yesu

33 Da suka isa wurin da a ke kira Golgota, wato, Wurin Ƙoƙwan Kai, 34 sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha. 35 Da suka giciye shi, sai suka yi ƙuri’a suka rarraba tufafinsa a junansu. 36 Sai suka zauna a nan suna gadinsa. 37 Daidai kansa sai aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.” 38 Sai kuma aka giciye ’yam-fashi biyu tare da shi, ɗaya ta dama, ɗaya ta hagun. 39 Masu wucewa suka yi ta yi masa bakar magana, suna kada kai, 40 suna cewa, “Kai da za ka rushe Wuri Tsattsarka, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to, sauko daga giciyen mana!” 41 Haka kuma manyan malamai da malaman Attaura da shugabanni suka riƙa masa ba’a suna cewa, 42 “Ya ceci waɗansu, ya kuwa ƙasa ceton kansa. Ai Sarkin Bani Isra’ila ne, yă sauko mana daga giciyen yanzu, mu kuwa ma gaskata da shi. 43 Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.” 44 Har ’yam-fashin nan da aka giciye su tare ma suka zazzage shi kamar waɗancan.

45 To, tun daga tsakar rana, sai duhu ya rufe ƙasa, duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 46 Kuma wajen ƙarfe ukun sai Yesu ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Eli, Eli, lama sabaktdni?” wato, “Ya Allahna, ya Allahna, dom me ka yashe ni?” 47 Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, sai suka ce, “Mutumin nan na kiran Iliya ne.” 48 Sai nandanan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jika shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha. 49 Amma sai sauran suka ce, “Ku bari mu gani ko Iliya zai zo ya cece shi.” 50 Sai Yesu ya sake daga murya da ƙarfi, sannan ya ba da ransa.

51 Sai Labulen Wuri Tsattsarka ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa kuma ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage. 52 Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da ke barci kuma suka tashi. 53 Da suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birni, suka bayyana ga mutane da yawa. 54 Sa’ad da kyaftin da waɗanda ke tare da shi suna gadin Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya rufe su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”

55 Akwai kuma wasu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima. 56 Cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu da Yusufu, da kuma uwar ’ya’yan Zabadi.

Jana’izar Yesu

57 La’asar lis sai wani mai arziki ya zo, mutumin Arimatiya, mai suna Yusufu, shi ma kuwa almajirin Yesu ne. 58 Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya yi umarni a ba shi. 59 Sai Yusufu ya ɗauki jikin, ya sa shi a likkafanin linen mai tsabta, 60 ya kwantad da shi a wani sabon kabarin da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi abinsa. 61 Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun suna nan zaune a gaban kabarin.

62 Washegari, wato bayan Ranar Shiri, sai manyan malamai da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus, 63 suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu. 64 Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa’an nan su ce da mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar yayyau za ta fi ta farkon ke nan muni.” 65 Sai Bilatus ya ce musu, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare shi iyakar ƙoƙarinku. 66 Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka gine dutsen nan, suka kuma sa sojan.

28

Tashin Yesu daga Matattu

To, bayan Asabar, da asussuba a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun, suka je ganin kabarin. 2 Sai kuwa aka yi wata babbar rawar-ƙasa, domin wani mala’ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai. 3 Kamanninsa na haske kamar walkiya, tufafinsa kuma farare fat kamar alli. 4 Saboda tsoronsa sai masu gadin suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu. 5 Amma sai mala’ikan ya ce da matan, “Kada ku ji tsoro, don na san Yesu ku ke nema, wanda aka giciye. 6 Ai ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da ya kwanta. 7 Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa cewa ya tashi daga matattu. Ga shi kuma zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. To, na fa gaya muku.” 8 Sai suka tafi daga kabarin da gaggawa da tsoro, game da matuƙar farinciki, suka ruga a guje su kai wa almajiransa labari. 9 Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama alaikum!” Sai suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada. 10 Sai Yesu ya ce da su, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa ’Yan’uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”

11 Suna cikin tafiya ke nan, sai wasu daga cikin sojan nan suka shiga birni, suka ba manyan malamai labarin dukkan abin da ya auku. 12 Su kuwa da suka taru da shugabannin jama’a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka, 13 suka ce, Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo dad dare suka sace shi kuna barci. 14 In kuwa labarin nan ya kai ga kunnen gwamna, ma rarrashe shi mu tsare ku daga wahala.” 15 Sai suka karɓi kuɗin, suka yi yadda aka koya musu. Wannan maganar kuwa sai ta bazu cikin Yahudawa bar ya zuwa yau.

Wa’azi ga Dukkan Al’ummai

16 To, sai almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su. 17 Da suka gan shi sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18 Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “Am mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa. 19 Don haka sai ku je ku almajirtad da dukkan al’ummai, kuna yi musu babtisma su zama mallakar Uba da ta Ɗa da kuma ta Ruhu Tsattsarka, 20 kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har matuƙar zamani.”


BISHARA TA HANNUN
MARKUS

1

Farkon Bisharar Yesu Almasihu, Ɗan Allah, ke nan:

2 Yadda ya ke a rubuce a littafin Annabi Ishaya, cewa,

“Ga shi na aiko manzona ya riga ka gaba,
Wanda zai shirya maka hanya.
3 Muryar mai kira a jeji na cewa,
Ku shirya wa Ubangiji tafarki,
Ku miƙe hanyoyinsa.”

4 Yohana Maibabtisma ya bayyana a jeji, yana wa’azi mutane su tuba a yi musu babtisma don a gafarta musu zunubansu. 5 Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukkan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunubansu, yana yi musu babtisma a Kogin Urdun. 6 Yohana kuwa na saye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da warki, abincinsa kuwa fara ce da ruan zuma. 7 Ya yi wa’azi ya ce, “Wani na zuwa bayana wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in sunkuya im ɓalle ba. 8 Ni da ruwa na yi muku babtisma, amma shi da Ruhu Tsattsarka zai yi muku.”

9 Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yohana ya yi masa babtisma a Kogin Urdun. 10 Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga Sama ta dare, Ruhu Tsattsarka na sauko masa kamar kurciya. 11 Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana Ƙaunataccena, ina farinciki da kai ƙwarai.”

12 Nandanan sai Ruhu Tsattsarka ya iza shi jeji. 13 Yana cikin jeji har kwana arba’in, Shaiɗan na gwada shi; yana tare da namomin daji, mala’iku kuma na yi masa hidima.

YESU A ƘASAR GALILI

14 To, bayan an tsare Yohana, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin Bisharar Allah, 15 yana cewa, “Lokaci ya yi, Mulkin Allah ya kusato. Ku tuba, ku gaskata da Bishara.”

Almajiran Yesu na Farko

16 Yana wucewa ta bakin Tafkin Galili, sai ya ga Siman da Andarawas ɗan’uwansa, suna jefa taru a tafki, don su masunta ne. 17 Sai Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zam mai da ku masu tsamo mutane.” 18 Nandanan kuwa sai suka watsad da tarunansu, suka bi shi. 19 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan’uwansa Yohana, suna cikin jirginsu suna gyaran taruna. 20 Nandanan sai ya kira su, suka bar ubansu Zabadi a cikin jirgin tare da lebura, suka bi shi.

Yesu ya Warkad da Mai Baƙin Aljan

21 Sai suka shiga Kafarnahum. Da yin Asabar kuwa sai ya shiga majami’a yana koyarwa. 22 Sun yi mamakin koyarwatasa, don yana koya musu a tabbace, ba kamar malaman Attaura ba. 23 Nan take sai ga wani mutum mai baƙin aljan a majami’arsu, yana ihu, 24 yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wanene kai, Tsattsarkan nan ne kai na Allah.” 25 Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” 26 Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa na rawa, ya yi ihu, ya rabu da shi. 27 Duk suka yi mamaki, bar suka tantambayi juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙawar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma ya ke yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya.” 28 Nandanan sai ya shahara a ko’ina duk kewayen ƙasar Galili.

29 Da fitarsu daga majami’a, sai suka shiga gidan su Siman da Andarawas, tare da Yakubu da Yohana. 30 Surukar Siman kuwa na kwance tana zazzaɓi, nandanan sai suka ba shi labarinta.

31 Sal ya matso, ya kama hannunta, ya tashe ta, zazzaɓin kuwa ya sake ta, har ta yi musu hidima.

32 Da magariba, bayan faɗuwar rana, sai aka kakkawo masa dukkan marasa lafiya, da masu taɓin aIjannu. 33 Sai duk garin ya haɗu a ƙofar gidan. 34 Ya warkad da marasa lafiya da yawa, masu cuta iri-iri, ya kuma fitar wa mutane aIjannu da. yawa. Bai ko yarda aljannun su yi wata magana ba, domin sun san shi.

35 Da asussuba sai ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu’a a can. 36 Sai Siman da waɗanda ke tare da shi suka bi shi. 37 Da suka same shi, sai suka ce masa, “Duk ana nemanka.” 38 Ya ce musu, “Mu tafi garuruwan da ke gaba in yi wa’azi a can kuma, don saboda haka ne na fito.” 39 Ya gama ƙasar Galili duk yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar wa mutane aljannu.

40 Sai wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, yana durƙusawa a gabansa, yana cewa, “In ka yarda ka iya tsarkake ni.” 41 Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.” 42 Nan take sai kuturtar ta rabu da shi, ya tsarkaka. 43 Ya kwaɓe shi ƙwarai, ya sallame shi nandanan, 44 ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa komai. Sal dai ka je wurin malami ya gan ka, ka kuma yi baiwa saboda tsarkakewarka don tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.” 45 Amma sai ya tafi, ya shiga sanad da maganar, yana baza labarin al’amarin ko’ina, har ya zamana Yesu bai ƙara iya shiga wani gari a sarari ba, sai ya zauna a waje a wuraren da ba kowa. Mutane kuwa suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina.

2

Yesu na Gafarta Zunubai

Bayan ’yan kwanaki, da ya sake komowa Kafarnahum, sai aka ji labari yana gida. 2 Aka kuwa taru makil har ba sauran wuri, ko da a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa’azin Maganar Allah. 3 Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu na ɗauke da shi. 4 Da suka kasa kusantarsa don yawan mutane, sai suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, sai suka zura gadon da shanyayyen ke kwance a kai. 5 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce da shanyayyen, “Ɗana, an gafarta maka zunubanka.” 6 To, waɗansu malaman Attaura na nan zaune, suna ta wuswasi a zuciyatasu, 7 suna cewa, “Dom me mutumin nan ke faɗar haka? Ai saɓo ya ke! Wa ke iya gafarta zunubi ban da Allah kaɗai?” 8 Nandanan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, “Dom me ku ke wuswasi haka a zuciyarku? 9 Wanne ya fi sauƙi, a ce da shanyayyen, ‘An gafarta maka zunubanka’, ko kuwa a ce, ‘Tashi ka ɗauki gadonka ka yi tafiya’? 10 Amma don ku sakankance Ɗam Mutun na da ikon gafarta zunubi a duniya”—sai ya ce da shanyayyen— 11 “Na ce da kai, tashi, ka ɗauki gadonka ka tafi gida.” 12 Sai ya tashi nandanan, ya ɗauki gadonsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Kai! ba mu taɓa ganin irin haka ba.”

Yesu ya Kira Lawi

13 Sai Yesu ya sake fita bakin tafki. Duk jama’a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu. 14 Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Alfayas a zaune yana aiki a ofishin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.

15 Wata rana Yesu na cin abinci a gidan Lawi, masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa kuma suna ci tare da shi da almajiransa, don kuwa da yawa daga cikinsu masu binsa ne; 16 to, da malaman Attaura na Farisiyawa suka ga yana cin abinci da masu zunubi da masu karɓar haraji, sai suka ce da almajiransa, “Dom me ya ke ci ya ke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 17 Da Yesu ya ji haka, sai ya ce musu, “Ai lafiyayyu ba ruwansu da Iikita, sai dai marasa lafiya. Ba don kiran masu gaskiya na zo ba, sai masu zunubi.”

18 To, almajiran Yohana da na Farisiyawa suna hana kansu abinci, sai aka zo aka ce da shi, “Dom me almajiran Yohana da na Farisiyawa ke hana kansu abinci, amma naka almajiran ba sa hanawa?’ 19 Sal Yesu ya ce musu, “Ashe abokan ango sa iya hana kansu abinci tun ango na tare da su? Ai muddar suna tare da angon, ba za su iya hana kansu abinci ba. 20 Ai lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su hana kansu abinci. 21 Ba mai mahon tsofuwar tufa da sabon ƙyalle. Im. ma an yi, ai sai sabon ƙyallen ya kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa. 22 Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Im ma an ɗura, sai ruwan inabin ya fasa salkunan, a kuma yi hasaratasa da ta salkunan. Sabon ruwan inabi ai sai sababbin salkuna.”

Yesu a Gonakin Alkama

23 Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama; suna cikin tafiya sai almajiransa suka fara zagar alkamar. 24 Sai Farisiyawa suka ce masa, “Ka ga! Dom me su ke yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba?” 25 Sai ya ce musu, “Ashe ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da ya matsu da yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 26 Yadda ya shiga Ɗakin Allah a zamami da Abiyata ke Babban Malami, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, wanda bai halatta kowa ya ci ba, sai malamai kaɗai, har ma ya ba abokan tafiyarsa?” 27 Sai ya ce musu, “Ai Asabar don mutun aka yi ta, ba mutun aka yi don Asabar ba. 28 Saboda, haka Ɗam Mutun shi ne Ubangijin bar Asabar ma.”

3

Mai Shanyayyen Hannu

Sai ya sake shiga majami’a. Akwai wani mutun a nan kuwa ma shanyayyen hannu. 2 Sai suka yi haƙonsa su ga ko za warkad da shi ran Asabar, don su samu su zarge shi. 3 Sai ya ce da mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.” 4 Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? a ceci rai, ko a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru. 5 Da ya duddube su cikin fushi yana baƙinciki da taurin-zuciyarsu, sai ya ce da mutumin, Miƙe hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye 6 Da Farisiyawa suka fita, nandanan sai suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi.

7 Sai Yesu ya janye tare da almajiransa, suka je bakin tafkin. Taro mai yawan gaske kuwa daga ƙasar Galili ya biyo shi, bar ma daga ƙasar Yahudiya, 8 da Urushalima, da ƙasar Idumiya, da bayan Kogin Urdun, da kuma wajen Sur da Saida, babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da ya ke yi. 9 Don gudun kada taron ya mammatse shi kuwa, sai ya ce da almajiransa su keɓe masa ƙaramin jirgi guda, 10 saboda ya riga ya warkad da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta na dannowa wurinsa don su taɓa shi. 11 Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa’ad da suka gan shi, sai su faɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, “Kai ɗan Allah ne.” 12 Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.

Manzannin Yesu Sha Biyu

13 Sai ya hau dutse, ya kira waɗanda ya ke so, suka je wurinsa. 14 Ya zaɓi mutun goma sha biyu su zauna tare da shi, ya riƙa aikensu suna wa’azi. 15 Ya kuma ba su ikon fid da aljannu. 16 Ya sa wa Siman suna Bitrus; 17 Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan’uwansa Yohana, ya sa musu suna Buwanarjis, wato ’Ya’yan Tsawa. 18 Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Alfayas, da Tadawas, da Siman Bakan’ane, 19 da kuma Yahuda Iskariyoti wanda ya bāshe shi.

Sa’an nan ya shiga wani gida. 20 Taron kuwa ya sake haɗuwa bar ya hana su cin abinci. 21 Da ’yan’uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai ya ruɗe.” 22 Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai Ba’alzabul ne ya ban shi, kuma da ikon sarkin aljannun ya ke fid da aljannu.” 23 Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fid da Shaiɗan? 24 Ai im mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba. 25 Haka kuma in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba. 26 Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewatasa ce ta zo. 27 Ba mai iya shiga gidan ƙato ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaton, sa’an nan kuma ya washe gidansa.

28 “Hakika, ina gaya muku, a gafarta wa ’yan’adan duk zunubansu, da kowane saɓon da suka furta, 29 amma fa duk wanda ya saɓi Ruhu Tsattsarka ba shi samun gafara, bar abada, ya ɗau madawwamin zunubi ke nan.” 30 Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.”

Uwar Yesu da ’Yan’uwansa

31 Sa’an nan uwatasa da ’yan’uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa yă je. 32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da ’yan’uwanka suna nemanka a waje.” 33 Ya amsa musu ya ce, “Su wanene tsohuwata da ’yan’uwana?” 34 Sai ya waiwayi waɗanda ke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga nan tsohuwata da ’yan’uwana! 35 Ai kowa ya yi abin da Allah ke so, shi ne ɗan’uwana, shi ne ’yar’uwata, shi ne kuma tsohuwata.”

4

Misalin Mai Shuka

Ya kuma fara koyarwa a bakin tafki ke nan, sai babban taro ya haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi a tafkin, ya kuwa zauna a ciki. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tafkin. 2 Sai ya koya musu abubuwa da yawa da ba da misalai. A cikin koyarwatasa bar ya ce musu, 3 Ku saurara! Wani mai shuka ya tafi shuka. 4 Yana cikin yafa iri sai waɗansu kwayoyi suka fantsama a kan hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su. 5 Wasu kuma suka fantsama a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nandanan kuwa sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa. 6 Da rana fa ta ɗaga, sai suka yankwane, da ya ke ba su da saiwa sosai sai suka bushe. 7 Wasu kuma suka fantsama cikin ƙaya, sai ƙayar ta tashi ta sarƙe su, ba su yi tsaba ba. 8 Wasu kuma suka zuba a ƙasa mai kyau, suka yi yabanya, suka girma, suka yi tsaba, waɗansu riɓi talatin-talatin, wasu sittin-sittin, wasu. ma bar ɗari-ɗari.” 9 Sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

10 Da suka kaɗaita, sai masu binsa da su Sha biyun nan suka tambaye shi ma’anar misalan. 11 Sai ya ce musu, “Ku kam an yarje muku ku san zuzzurfan al’amarin Mulkin Allah, amma ga waɗanda ba sa cikinku, komai sai a cikin misali; 12 don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahinta ba; don kada su juyo a yafe musu.” 13 Ya ce musu, “Ashe, ba ku fahinci wannan misalin ba? Ƙaƙa za ku fahinci sauran ke nan? 14 Mai shukan nan fa Maganar Allah ya ke shukawa. 15 Waɗanda suka fantsama a kan hanya kuwa, su ne kwatancin waɗanda aka shuka Maganar a zuciyatasu. Da zarar sun ji, nandanan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauke Maganad da aka shuka a zuciyatasu. 16 Haka kuma waɗanda aka shaka a wuri mai duwatsu, su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar sai su karɓa da farinciki. 17 Su kam ba su da tushe, kuma rashin ƙarko gare su, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru don wannan Magana, nandanan sai su ƙosa. 18 Waɗansu kuma su ne kwatancin waɗanda suka fantsama cikin ƙaya, su ne waɗanda ke jin Maganar, 19 amma taraddadin duniya, da jarabar dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, su kan shiga zuci su sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani. 20 Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin waɗanda ke jin Maganar, su karɓa, su kuma amfana, waɗansu riɓi talatin-talatin, wasu sittin-sittin, wasu ma bar ɗari-dari.”

Misafai kan Mulkin Sama

21 Sai ya ce musu, “Shin ana kawo fitila don a rufe ta da masaki, ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado ne, ba don a ɗora ta a kan maɗorinta ba? 22 Ba abin da ke ɓoye, sai don a bayyana shi a gaba. Ba kuma wani abin da ke asiri, sai don a bayyana shi a gaba. 23 In da mai kunnen ji, yă ji.” 24 Sai ya ce musu, “Ku iya ji. Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a ƙara. 25 Don mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da ya ke da shi ma, sai an karɓe masa.”

26 Kuma ya ce, “Mulkin Allah kamar mutun ya ke mai yafa iri a ƙasa. 27 A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma, bai kuwa san ta yadda aka yi ba. 28 Ƙasa da kanta ta kan ba da amfani, tsiro shi ne na farko, sa’an nan kai, sai kuma ƙwaƙƙwarar ƙwaya a kan. 29 Sa’ad da amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nandanan, wato ƙaƙa ta yi ke nan.”

30 Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulkin Allah? Ko kuwa da wane misali za mu misalta shi? 31 Kamar ƙwayar mastad ya ke, wadda, in an shuka ta, ko da ya ke ita ce mafi ƙanƙantar ƙwayoyi a duniya, 32 duk da haka in an shuka ta, sai ta girma, ta fi duk sauran ganye, ta yi manyan rassa, har tsuntsaye su iya sauka a inuwatata.”

33 Da misalai da yawa irin waɗannan Yesu ya yi musu Maganar Allah, daidai gwargwadon ganewatasu. 34 Ba ya faɗa musu komai sai da misali, amma a keɓe ya kan bayyana wa almajiransa komai.

Labarin Hadiri a Tafki

35 A ran nan da maraice sai ya ce musu, “Mu haye can ƙetare.” 36 Da suka bar taron, sai suka tafi da shi yadda ya ke a cikin jirgin; waɗansu jirage kuma na tare da shi. 37 Sai wani babban hadiri mai iska ya taso, raƙuman-ruwa kuma na ta fantsama cikin jirgin, har jirgin ya tasam ma cika da ruwa. 38 Yesu kuwa na daga ƙarshen baya na jirgin a kan matashi, yana barci. Sai suka tashe shi, suka ce masa, “Shugaba, za mu halaka ba ka kula ba ko?” 39 Sai ya farka, ya tsawata wa iskar, ya kuma ce da ruwan tafkin, “Nutsu! Ka yi shiru!” Sai iskar ta kwanta, wurin duk ya yi tsit. 40 Ya ce musu, “Dom me kuka firgita haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?” 41 Sai suka tsorata, matuƙar tsoro, suka ce da juna, “Wa ke nan kuma wanda har iska da ruwan tafki ma ke masa biyayya?”

5

Yesu a Ƙasar Garasinawa

Sai suka iso ƙetaren tafki a ƙasar Garasinawa. 2 Da saukarsa daga jirgin, sai ga wani mai baƙin aljan daga makabarta ya tare shi. 3 Shi kuwa makabarta ce mazauninsa. Ba mai iya ɗaure shi kuma, ko da da sarƙa ma. 4 Don dā an sha ɗaure shi da mari da sarƙa, amma sai ya tsintsinka sarƙar, ya gutsuntsuna marin, har ma ba mai iya bi da shi. 5 Kullum kuwa dare da rana yana cikin makabarta, da kan duwatsu, yana ta ihu, yana kukkuje jikinsa da duwatsu. 6 Da dai ya hango Yesu, sai ya sheƙo a guje ya faɗi a gabansa, 7 ya ƙwala ihu ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu ɗan Allah Maɗaukaki? Na gama ka da Allah, kada ka yi mini azaba.” 8 Don kuwa Yesu ya ce masa ne, “Rabu da mutumin nan, kai wannan baƙin aljan!” 9 Sai Yesu ya tambaye shi, “Me sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Tuli, don muna da yawa.” 10 Sai ya roƙi Yesu da gaske kada ya kore su daga ƙasar. 11 To, wurin nan kuwa wani babban garken alade na kiwo a gangaren dutsen. 12 Sai aljannun nan suka roƙe shi suka ce, “Tura mu wajen aladen nan mu shige su.” 13 Ya kuwa yardam musu. Sai baƙaƙen aljannun suka fita, suka shigi aladen. Garken kuwa wajen alade dubu biyu, suka rugungunto ta gangaren, suka faɗa tafkin, suka halaka a cikin ruwa.

14 Daganan sai ’yan kiwon aladen suka gudu, suka ba da labari birni da ƙauye. Jama’a suka zo su ga abin da ya auku. 15 Da suka zo wurin Yesu suka ga mai aljannun nan a zaune, saye da tufa, kuma cikin hankalinsa, wato mai aljannun nan masu yawa a dā, sai suka tsorata. 16 Waɗanda aka yi abin a kan idonsu kuwa, suka farfaɗi abin da ya gudana ga mai aljannun da kuma aladen. 17 Sai suka fara roƙon Yesu ya bar musu ƙasarsu. 18 Yana shiga jirgi ke nan, sai mai aijannun nan a dā ya roƙe shi izinin zama a gunsa. 19 Amma Yesu bai yardam masa ba, sai ya ce da shi, “Tafi gida wurin ’yan’uwanka, ka faɗa musu irin manyan abubuwan da Ubangiji ya yi maka, da kuma yadda ya ji tausayinka.” 20 Sai ya tafi, ya shiga baza labari a Dikafolis na irin manyan abubuwan da Yesu ya yi masa. Duk mutane kuwa suka yi al’ajabi.

Labarin ’Yar Yayirus

21 Da Yesu ya sake hayewa ƙetare cikin jirgi, sai babban taro ya kewaye shi. Shi kuwa yana bakin tafkin. 22 Sai ga wani daga cikin shugabannin majami’a, mai suna Yayirus. Da ganin Yesu kuwa sai ya faɗi a gabansa, 23 ya roƙe shi da gaske, yana cewa, “ ’Yata ƙarama tana bakin mutuwa. Da dai a ce ka zo ka ɗora mata hannu, da sai ta warke ta rayu.” 24 Sai suka tafi tare. Babban taro kuwa na biye da shi, suna matsatasa.

25 Sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana, zub da jini, 26 ta kuma sha wahala da gaske a hannun masu magani da yawa, bar ta ɓad da duk abin da ta ke da shi, amma duk a banza, sai ma gaba-gaba cutar ta ke yi. 27 Da ta ji labarin Yesu, sai ta raɓo ta bayansa cikin taron, ta taɓa mayafinsa. 28 Don tā ce a ranta, “Ko da tufarsa ma na taɓa, sai in warke.” 29 Nan take zubar jininta ya tsaya, ta kuma ji a jikinta, an warkad da cutarta. 30 Nandanan kuwa da Yesu ya ji wani iko ya fita daga gare shi, sai ya waiwaya a cikin taron, ya ce, “Wa ya taɓa tufata?” 31 Sai almajiransa suka ce masa, “Kana ganin taro na matsarka, ka ce, wa ya taɓa ka?” 32 Sai Yesu ya juya don ya ga wadda ta yi haka. 33 Matar kuwa da ta san abin da aka yi mata, sai ta zo a tsorace, tana rawar jiki, ta faɗi a gabansa, ta faɗa masa kashin gaskiya. 34 Sai ya ce mata, “’Yata, bangaskiyarki ta warkad da ke. ƙi sauka lafiya, ƙi warke daga cutarki.”

35 Yana cikin magana, sai ga waɗansu daga gidan shugaban majami’a suka ce, “Ai ’yarka ta rasu, me kuma za ka wahal da Malamin?” 36 Amma Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, ya ce da shugaban majami’a, “Kada ka ji tsoro, ka ba da gaskiya kawai.” 37 Bai bar kowa ya bi shi ba sai Bitrus, da Yakubu, da kuma Yohana ɗan’uwan Yakubu. 38 Da suka isa gidan shugaban majami’a, sai ya ji ana hayaniya, ana kuka, ana kururuwa ba ji ba gani. 39 Da kuma ya shiga, sai ya ce musu, “Dom me ku ke hayaniya kuna kuka haka? Ai yarinyar ba, a mace ta ke ba, barci ta ke yi.” 40 Sai suka yi masa ɗariyar raini. Shi kuma bayan ya fid da su duka waje, sai ya ɗauki uban yarinyar, da uwatata, da kuma waɗanda ke tare da shi, ya shiga inda yarinyar ta ke. 41 Sai ya kama hannunta, ya ce mata, “Talita ƙumi”, wato, “Ke yarinya, ina ce da ke, tashi.” 42 Nan take yarinyar ta tashi ta yi tafiya, don ’yar shekara goma sha biyu ce. Nandanan kuwa sai mamaki ya rufe su. 43 Sai ya kwaɓe su gaya matuƙa kada kowa ya ji wannan labari. Ya kuma yi umarni a ba ta abinci.

6

An ƙi Yesu a Nazarat

Sai ya tashi daga nan ya koma garinsu, almajiransa kuwa suka bi shi. 2 Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami’a. Mutane da yawa da suka saurare shi sai suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu’ujizan da a ke aikatawa ta hannunsa! 3 Shin wannan ba shi ne kafintan nan ba, ɗam Maryamu, ɗan’uwan su Yakubu, da Yosi, da Yahuda, da kuma Siman? Kuma ’yan’uwansa mata ba ga su tare da mu. ba?” Sai suka ƙosa da shi. 4 Sai Yesu ya ce musu, “Ai annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu, kuma cikin ’yan’uwansa, da kuma gidansu.” 5 Bai ko iya yin wata mu’ujiza a can ba, sai dai ya ɗora wa marasa lafiya kaɗan hannu ya warkad da su. 6 Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu.

Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.

Yesu ya Aiki Manzanninsa

7 Sai ya kira Sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu. 8 Sai ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko da burodi, ko burgami, kai ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai; 9 amma su sa takalmi, kuma kada su haɗa taguwa biyu. 10 Ya ce musu, “Duk gidan da kuka, sauka, ku zauna a nan har ku tashi. 11 Duk inda aka ƙi yin na’am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ku tashi, sai ku karkaɗe kurar kafafunku don shaida a kansu.” 12 Haka fa sai suka. fita, suna wa’azi mutane su tuba. 13 Suka fid da aljannu da yawa, suka kuma shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka warkad da su.

Mutuwar Yohana Maibabtista

14 Sai fa Sarki Hirudus ya ji labari, don sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yohana Maibabtisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa a ke aikata mu’ujizan nan ta kansa.” 15 Amma wasu suka ce, “lliya ne.” Wasu kuwa suka ce, “Ai annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawa.” 16 Amma da Hirudus ya ji haka, sai ya ce, “Yohana, wanda na fille wa kai, shi ne aka tasa.” 17 Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yohana, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan’uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura. 18 Don dā Yohana ya faɗa wa Hirudus, “Bai halatta ka zauna da matar ɗan’uwanka ba.19 Hirudiya kuwa na ciki da Yohana, har ta so kashe shi, amma ba ta sami hanya ba, 20 don Hirudus na tsoron Yohana, ya san shi mutun ne mai gaskiya, kuma tsattsarka, shi ya sa ya kare shi. Hirudus ya kan damu da yawa sa’ad da ya ke sauraron Yohana, ko da ya ke yana murna da jinsa. 21 Amma wani sanadi ya zo, da ranar haifuwar Hirudus ta kewayo, sai ya yi wa hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan ƙasar Galili biki. 22 Da ’yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta ba Hirudus da baƙinsa sha’awa. Sai fa sarki ya ce da yarinyar, “Roƙe ni komai, sai im ba ki.” 23 Ya kuma rantse mata ya ce, “Komai kika roƙe ni zam ba ki, ko da rabin mulkina ne.” 24 Sai ta fita ta ce da uwatata, “Me zan roƙa?” Uwar ta ce, “Kan Yohana Maibabtisma.” 25 Nandanan sai ta shigo wurin sarki da gaggawa ta roƙe shi ta ce, “Ina son yanzu-yanzu ka ba ni kan Yohana Maibabtisma a cikin akushi.” 26 Sai sarki ya yi baƙinciki gaya, amma saboda rantsuwatasa da kuma baƙinsa, bai so ya hana ta ba. 27 Nan take sai sarki ya aiki dogari, ya yi urnarni a kawo kan Yohana. Sai ya tafi ya fille wa Yohana kai a kurkuku, 28 ya kawo kan a cikin akushi, ya ba yarinyar, yarinyar kuwa ta ba uwatata. 29 Da almajiran Yohana suka ji labari, sai suka zo suka ɗauki gangar-jikinsa, suka kwantad da ita a kabari.

Mu’ujizar Ci da Mutun Dubu Biyar

30 Sai Manzannin suka komo wurin Yesu, suka faɗa masa duk iyakar abin da suka yi, da abin da suka koyar. 31 Ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita a wurin da ba kowa, ku ɗan huta.” Domin mutane da yawa suna kaiwa suna kawowa, ko damar cin abinci ma Manzannin ba su samu ba. 32 Sai suka tafi cikin jirgi wurin da ba kowa, su kaɗai. 33 Ashe mutane da yawa sun ga tafiyatasu, sun kuwa shaida su, suka fa dungumo ta tudu daga garuruwa duka, suka riga su zuwa. 34 Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, don kamar tumaki su ke ba makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa. 35 Kusan faɗuwar rana sai almajiransa suka zo gare shi, suka ce masa, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa rana ta yi kusan faɗuwa. 36 Sai ka sallame su, su shiga karkara da ƙauyuka na kurkusa, su sai wa kansu abinci.” 37 Amma ya amsa musu ya ce, “Ku ku ba su abinci mana.” Sai suka ce masa, “Wato mu je mu sayo burodi na dinari metan, mu ba su su ci?” 38 Ya ce musu, “Burodi nawa gare ku? Ku je ku dubo.” Da suka binciko sai suka ce, “Ai biyar ne, da kifi biyu.” 39 Sa’an nan ya yi umarni dukkansu su zazzauna kungiya-kungiya a kan ɗanyar ciyawa. 40 Haka suka zauna jeri-jeri, waɗansu ɗari-ɗari, wasu hamsin-hamsin. 41 Da ya ɗauki burodi biyar ɗin da kifi biyun, sai ya daga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura burodin, ya yi ta ba almajiran suna kai wa jama’a; duk kuma ya raba musu kifin nan biyu. 42 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, 43 har suka ɗauki kwando goma sha biyu cike da gutsattsarin burodin da na kifin. 44 Waɗanda suka ci burodin nan kuwa maza dubu biyar ne.

Yesu ya yi Tafiya a kan Ruwa

45 Nandanan ya sa almajiransa suka shiga jirgi su riga shi hayewa zuwa Baitsaida, kafin ya sallami taron. 46 Bayan ya sallame su, sai ya hau dutse don ya yi addu’a. 47 Da magariba ta yi, jirgin na tsakiyar tafki, Yesu kuwa na nan kan tudu shi kaɗai, 48 da ya ga suna fama da tuƙi, don iska na mai da su baya, misalin ƙarfe uku na dare sai ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, 49 amma da suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka zaci fatalwa ce, suka yi kururuwa, 50 domin duk sun gan shi, sun kuwa firgita. Sai nandanan ya yi musu magana ya ce, “Ba komai, ni ne, kada ku ji tsoro.” 51 Sa’an nan ya shiga jirgi wurinsu, iska kuma ta kwanta. Sai mamaki ya rufe su ƙwarai, 52 don ba su fahinci al’amarin burodin nan ba, saboda zuciyatasu ta taurare.

53 Da suka haye sai suka isa ƙasar Janisarata, suka ɗaure jirgin a gaɓa. 54 Da fitarsu daga jirgin sai mutane suka shaida shi. 55 Sai suka gama ƙasar da gudu, suka fara ɗaɗɗauko marasa lafiya a kan gadajensu zuwa duk inda suka ji ya ke. 56 Kuma duk inda ya shiga, birni da ƙauye ko karkara, su kan kwantad da marasa lafiya a bakin kasuwa, su roƙe shi su taɓa ko da gezar mayafinsa ma. Ɗokacin waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

7

Munafuncin Farisiyawa

To, da Farisiyawa suka taru a wurinsa tare da waɗansu daga cikin malaman Attaura da suka zo daga Urushalima, 2 sai suka lura waɗansu almajiransa na cin abinci da hannaye marasa tsarki, wato marasa wanki. 3 Domin Farisiyawa da dukkan Yahudawa ba sa cin abinci sai sun wanke hannu sarai tukuna, saboda bin al’adun shugabanninsu. 4 In sun komo daga kasuwa kuwa, ba sa cin abinci sai sun yi wanka tukuna. Akwai kuma wasu al’adu da yawa da suka gada su ke kiyayewa, kamar su wankin ƙore da tuluna da daruna. 5 Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka tambaye shi, “Dom me almajiranka ba sa bin al’adun shugabanni, sal su riƙa cin abinci da hannuwa marasa tsarki?” 6 Sai ya ce musu, “Kai! daidai ne Ishaya ya yi faɗin annabci a kanku, munafukai I Yadda ya ke a rubuce, cewa,

‘Al’umman nan a baka kawai su ke girmama ni,
Amma a zuci nesa su ke da ni.
7 A banza su ke bauta mini,
Domin ka’idodin da su ke koyarwa umarnin ɗan’adan ne.’
8 Kuna yā da umarnin Allah, kuna maƙe da al’adun mutane.”

9, Sai ya ce musu, “Lalle kun iya yā da umarnin Allah don ku bi al’adunku! 10 Don Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka’; kuma. ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwatasa, sai lalle a kasheshi.’ 11 Amma ku ku kan ce, ‘Im mutun ya ce da ubansa ko uwatasa, Duk abin da dā za ku samu a gare ni ya zama Korban,’ (wato an sadaukar), 12 shi ke nan fa ba saura ku bar shi ya yi wa ubansa ko uwatasa aikin komai. 13 Ta haka ku ke banzanta Maganar Allah ta wajen al’adunku da ku ke bari gado. Kun kuwa cika yin irin waɗannan. abubuwa.”

14 Sai ya sake kiran jama’a, ya ce musu, “Ku saurare ni duk kanku, ku kuma fahinta. 15 Ba abin da ke shiga mutun daga waje ya ƙazanta shi, sai abin da ke fita, shi ke ƙazanta shi. 16 Duk mai kunnen ji, yă ji.” 17 Bayan rabuwarsa da taron, da ya shiga gida sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar misalin. 18 Ya ce musu, “Ashe, ku ma ba ku da fahinta ne? Ashe, ba ku gane ba cewa komai ya shigi mutun daga waje, ba yadda zai ƙazanta shi, 19 tun da ba zuciyatasa ya shiga ba, cikinsa ne, ta haka kuma zai fice?” Ta haka ya halatta kowane irin abinci. 20 Ya kuma ce, “Abin da ke fita daga mutun shi ke ƙazanta shi. 21 Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutun, miyagun tunani ke fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina, 22 da kwaɗayi, da mugunta, da ha’inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta. 23 Duk waɗannan miyagun abubuwa daga ciki su ke fitowa, suna kuwa ƙazanta mutun.”

Basurofinikiya da ’Yatata

24 Daganan kuma sai ya tashi ya tafi wajajen Sur da Saida. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa ya sani ba, amma ba ya ɓoyuwa. 25 Nandanan sai wata mace, wadda ’yatata ƙarama ke da baƙin aljan ta ji labarinsa, ta zo ta faɗi a gabansa. 26 Matar kuwa Baheleniya ce, asalinta kuma Basurofinikiya ce. Sai ta roƙe shi ya fitar wa da ’yatata aljanin. 27 Yesu ya ce mata, “Bari ’yan gida su ƙoshi tukun, domin bai kyautu a bai wa na daji abincinsu ba. 28 Amma sai ta amsa masa ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai na daji su kan ci sudin ’yan gida.” 29 Sai ya ce mata, “Saboda wannan magana taki, koma gida, aljanin ai ya rabu da ’yarki. 30 Sai ta koma gida ta iske yarinyar a kwance a kan gado, aljanin kuwa ya fita.

Kurma Mai I’ina

31 Sai ya komo daga wajen Sur, ya bi ta Saida ya je Tafkin Galili ta Dikafolis. 32 Sai suka kawo masa wani kurma mai i’ina, suka roƙe shi ya ɗora masa hannu. 33 Yesu ya ɗauke shi suka koma waje ɗaya, rabe da taron, ya sa yatsunsa a kunnuwansa, ya tofad da yawu, ya kuma. taɓa harshensa. 34 Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuci, sai ya ce masa, “Iffata!” wato, “Buɗu!” 35 Sai aka buɗe kunnuwansa, aka saki kwaɗon harshensa, kuma ya yi magana sosai. 36 Yesu ya kwaɓe su kada su faɗa wa kowa, amma sau dubu ya kwaɓe su, sau dubu goma za su ƙara yaɗa labarin. 37 Sai suka yi mamaki gaba da kima, suka ce, “Kai, ya yi komai da kyau! Har kurma ma ya sa shi ji, bebe kuma ya yi magana.”

8

Mu’ujizar Ci da Mutun Dubu Huɗu

A lokacin nan da wani taro mai yawan gaske ya sake haɗuwa, ba su kuwa da abinci, sai ya kira almajiransa, ya. ce musu, 2 “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna, ba su da wani abinci. 3 In kuwa na sallame su su tafi gida da yunwa haka, ai sai su ƙasa a hanya, ga shi kuwa waɗansunsu sun fito nesa.” 4 Sai almajiransa suka amsa masa suka ce, “Ina za a iya samun burodin da zai ci da mutanen nan a daji haka?” 5 Sai ya tambaye su, “Burodi nawa gare ku?” Suka ce, “Bakwai.” 6 Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. Da ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiransa su kai wa taron, suka kuwa kakkai musu. 7 Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan. Da ya yi wa Allah godiya, sai ya ce su ma a kai musu. 8 Sai suka ci, suka ƙoshi, har suka ɗauki ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai. 9 Mutanen kuwa sun yi wajen dubu huɗu. Sai ya sallame su. 10 Nandanan kuwa ya shiga jirgi da almajiransa, ya tafi ƙasar Dalmanuta.

Farisiyawa sun yi Muhawara da Shi

11 Sai Farisiyawa suka zo suka fara muhawara da shi, suna nema ya nuna musu wata alama daga Sama, don su gwada shi. 12 Sai ya yi wata doguwar ajiyar zuci, ya ce, “Dom me mutanen zamanin nan ke neman ganin alama? Hakika, ina gaya muku, ba wata alamad da za a nuna wa mutanen wannan zamani.” 13 Daganan ya bar su, ya sake shiga jirgi, ya haye wancan ƙetaren.

14 Sun kuwa manta, ba su kawo burodi ba, sai guda ɗaya ne kawai gare su a jirgin. 15 Ya gargaɗe su ya ce, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.” 16 Sai suka yi magana da juna a kan ba su da burodi. 17 Da ya ke Yesu ya gane haka, sai ya ce musu, “Dom me ku ke zancen ba ku da burodi? Ashe har yanzu ba ku gane ba, ba ku kuma fahinta ba? Zuciyarku a taurare ta ke? 18 Kuna da idanu, ba kwa gani ne? Kuna da kunnuwa, ba kwa ji ne? Ba kwa kuma tunawa ne? 19 Da na gutsuttsura wa mutun dubu biyar burodin nan biyar, kwando nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Sha biyu.” 20 “To, burodi bakwai da na gutsuttsura wa mutun dubu huɗu fa? Manyan kwanduna nawa kuka ɗauka, cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Bakwai.” 21 Sai ya ce musu, “To, har yanzu ba ku fahinta ba?”

Makaho a Baitsaida

22 Sai suka iso Baitsaida. Aka kawo masa wani makaho, aka roƙe shi ya taɓa shi. 23 Sai ya kama hannun makahon ya kai shi bayan gari. Da ya tofa yawu a idanunsa, ya ɗora masa hannu, sai ya tambaye shi, “Kana iya ganin wani abu?” 24 Sai makahon ya ɗaga kai, ya ce, “Ina ganin mutane kam, amma kamar itatuwa na ke ganinsu, suna yawo.” 25 Sai ya sake ɗora hannu a idanunsa. Makahon kuwa ya zura ido kwar, ya warke, ya ga komai garau. 26 Sai Yesu ya sallame shi yă koma gida, ya ce, “Ko ƙauyen ma kada ka shiga.”

Babbar Bayyana Yarda ga Yesu

27 Sai Yesu ya tashi, da shi da almajiransa, ya shiga ƙauyukan Kaisariya Filibi. A hanya kuwa ya tambayi almajiransa, “Wa mutane ke cewa na ke?” 28 Suka ce masa, “Yohana Maibabtisma; waɗansu kuwa, lliya; wasu kuma, wani daga cikin annabawa.” 29 Sai Ya tambaye su, “Amma ku fa, wa ku ke cewa na ke?” Bitrus ya amsa masa ya ce, “Kai ne Almasihu.” 30 Sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa labarinsa.

Yesu ya yi Faɗin Mutuwarsa da Tashinsa

31 Sai ya fara koya musu cewa lalle ne Ɗam Mutun ya sha wuya iri-iri, shugabanni da manyan malamai da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da. rai. 32 Ya ko faɗi wannan magana a sarari. Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawatar masa. 33 Amma da Yesu ya waiwaya ya ga almajiransa, sai ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Ka yi nesa da ni, Shaiɗan! Ba ka tattalin al’amuran Allah sai na mutane.”

34 Sai ya kira taron tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai son bina, sai yă ƙi kansa, yă shafa jini a wuyansa, yă bi ni. 35 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, kuma saboda Bishara, tattalinsa ya yi. 36 Me mutun ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? 37 Me kuma mutun zai iya bayarwa ya fanshi ransa? 38 Duk wanda zai guje mini, ya kuma guje wa maganata a wannan zamani na rashin amana da yawan zunubi, Ɗam Mutum ma sai ya guje masa, sa’ad da ya zo cikin ɗaukakar Ubansa tare da mala’iku tsarkaka.”

9

Kamanninsa ya Sake a kan Dutse

Sai ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Mulkin Allah ya bayyana da iko.”

2 Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus da Yakubu da Yohana, ya ja su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. Sai kamanninsa ya sake a gabansu, 3 tufafinsa suka yi fari fat suna sheƙi, yadda ba mai wankin da zai iya fid da su haka a duniya. 4 Sai ga Iliya da Musa sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu. 5 Sai Bitrus ya sa baki, ya ce da Yesu, “Ya Shugaba, ya kyautu da mu ke nan wurin; mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” 6 Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske. 7 Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana Ƙaunataccena. Ku saurare shi.” 8 Farat haka da suka dudduba, ba su ƙara ganin kowa ba, sai Yesu kaɗai tare da su.

9 Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗam Mutun ya tashi daga matattu. 10 Sai suka bar maganar yasu-yasu, suna tambayar juna ko menene ma’anar tashi daga matattu. 11 Suka tambaye shi suka ce, “To, yaya kuwa malaman Attaura ke cewa lalle ne Iliya yă riga zuwa?” 12 Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukkan abubuwa. Yaya kuwa ya ke a rubuce game da Ɗam Mutun, cewa zai sha wuya iri-iri, a kuma wulakanta shi? 13 Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, sun kuma yi masa abin da suka ga dama, yadda labarinsa ke rubuce.”

Yaro Mai Beben Aljan

14 To, da suka komo wurin almajiran, sai suka ga babban taro ya kewaye su, malaman Attaura kuma na muhawara da su. 15 Da ganin Yesu sai duk taron suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka dungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi. 16 Sai ya tambaye su, “Muhawarar me ku ke yi da su?” 17 Sai ɗaya daga cikin taron ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ga shi na kawo maka ɗana, don yana da beben aljan. 18 Duk inda ya hau shi, sai ya doka shi da ƙasa, bakinsa na kumfa, yana tsukun haƙoransa, yana bushewa. Na kuma yi wa almajiranka magana su fid da shi, sai suka kasa.” 19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marar bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo min shi. 20 Sai suka kawo masa yaron. Da aljanin ya gan shi, nandanan sai ya buge yaron, jikinsa na rawa, ya faɗi yana ta birgima, bakinsa na kumfa. 21 Sai Yesu ya tambayi uban yaron, “Tun yaushe wannan abu ya same shi?” Sai uban ya ce, “Tun yana ƙarami. 22 Ya kuwa sha jefa shi a wuta da ruwa, don ya hallaka shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayimmu ka taimake mu.” 23 Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.” 24 Nandanan sai uban yaron ya ɗaga murya ya ce, “Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata!” 25 Da Yesu ya ga taro na dungumowa a guje, sai ya tsauta wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljani, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.” 26 Bayan aljanin nan ya yi ihu, sai ya buge shi da gaske, jikinsa na rawa, ya rabu da shi. Yaron kuma ya zama kamar matacce, har ma yawancin mutane suka ce, “Ai ya mutu.” 27 Amma Yesu ya kama hannunsa ya tashe shi, ya kuwa tashi tsaye. 28 Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a keɓe suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fid da shi?” 29 Sai ya ce musu, “Ai irin wannan ba ya fita sai da addu’a.”

30 Sai suka tashi daga nan, suka ratsa ƙasar Galili, bai kuwa so kowa ya sani ba, 31 domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗam Mutun ga mutane, za su kuwa kashe shi; sa’ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.” 32 Amma fa ba su fahinci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayatasa.

Yesu ya Koyar a Kafarnahum

33 Sai suka zo Kafarnahum. Da ya shiga gida sai ya tambaye su, “Muhawarar me kuka yi a hanya?” 34 Amma sai suka yi shiru, don a hanya sun yi muhawarar ko wanene babbansu. 35 Sai ya zauna, ya kira Sha biyun nan, ya ce musu, “Kowa ke son zama shugaba, lalle ne yă zama na ƙarshe duka, kuma baran kowa.” 36 Sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, ya rungume shi, ya ce musu, 37 “Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”

38 Sai Yohana ya ce masa, “Ya Shugaba, mun ga wani na fid da Ajannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya bimmu.” 39 Amma sai Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ai ba wanda zai yi wata mu’ujiza da sunana, sa’an nan nandanan ya kushe mini. 40 Ai duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne. 41 Kowa kuma ya ba ku ruwan sha moda guda saboda ku na Almasihu ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladansa ba ko kaɗan.

42 “Da dai wani yi sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku. 43 In kuwa hannunka na sa ka laifi, to, yanke shi. Zai fiye maka ka shiga mulkin rai madawwami da dungu, da ka shiga Jahannama da hannu biyu, wuta marar kasuwa kuwa, 44 inda azaba ba ta ƙarewa, wutar kuma ba a kashe ta. 45 In kuwa ƙafarka na sa ka laifi, to, yanke ta. Zai fiye maka ka shiga mulkin rai madawwami da gurguntaka, da a jefa ka Jahannama da ƙafa biyu, 46 inda azaba ba ta ƙarewa, wutar kuma ba a kashe ta. 47 In kuma idonka na sa ka laifi, to, ƙwaƙule shi. Zai fiye maka ka shiga Mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka a wutar Jahannama da ido biyu, 48 inda azaba ba ta ƙarewa, wutar kuma ba a kashe ta. 49 Da wuta za a tsarkake kowa, kamar yadda a ke tsarkake abu da gishiri. 50 Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sane, da me za a daɗaɗa shi? Sai ku kasance da gishiri a zuciyarku, ku yi zaman lafiya da juna.”

YESU A KASAR YAHUDIYA

10

Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma ƙetaren Kogin Urdun. Taro kuma ya sake haɗuwa wurinsa, ya kuma sake koya musu kamar yadda ya saba.

Maganar Kisan-aure

2 Sai wasu Farisiyawa suka zo wajensa don su gwada shi, suka tambaye shi suka ce, “Halal ne mutun ya saki matatasa?” 3 Sai ya amsa musu ya ce, “Me Musa ya umarce ku?” 4 Suka ce, “Musa ya ba da izini a rubuta takardar kisanaure, a kuma saki matar.” 5 Yesu ya ce musu, “Don taurin-kanku ne Musa ya rubuta muku wannan umarni. 6 Amma tun farkon halitta Allah ya halicce su, namiji da mace.’ 7 ‘Don haka fa sai mutun yă bar uwatasa da ubansa, yă tsaya ga matatasa. 8 Haka su biyun nan su zama jiki guda.’ Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne. 9 Abin da Allah fa ya gama, kada mutun ya raba.”

10 A cikin gida kuma sai almajiransa suka sake tambayarsa wannan magana. 11 Sai ya ce musu, “Kowa ya saki matatasa, ya auri wata, zina ya ke da ta biyun. 12 In kuma matar ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

Yesu ya yi wa Yara Ƙanana Albarka

13 Suna kawo masa wasu yara ƙanana ke nan don ya shafa su, sai almajiransa suka kwaɓe su. 14 Da Yesu ya ga haka, sai ya ji haushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai Mulkin Allah na irinsu ne. 15 Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na’am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro ke yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.” 16 Sai Yesu ya rungume su, yana ɗora musu hannu, yana yi musu albarka.

17 Ya fara tafiya ke nan, sai ga wani ya sheƙo a guje, ya durƙusa a gabansa, ya tambaye shi ya ce, “Ya Shugaba managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?” 18 Sai Yesu ya ce masa, “Dom me ka kira ni managarci Ai ba wani managarci sai Allah kaɗai. 19 Ka dai san Umarnin nan: ‘Kada ka yi kisankai, Kada ka yi zina, Kada ka yi sata, Kada. ka yi shaidar zur, Kada ka yi zamba, Ka girmama mahaifinka da mahaiƙyarka.’” 20 Sai ya ce masa, “Ya Shugaba, ai duk na kiyaye waɗannan tun kuruciyata.” 21 Sai Yesu ya dube shi duban ƙauna, ya ce masa, “Abu guda ne kawai ya rage maka. Sai ka je, ka sai da duk mallakarka, ka ba gajiyayyu, sai ka sami taskar dukiya a Sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.” 22 Da jin wannan magana sai gabansa ya faɗi, ya tafi yana mai baƙinciki, don yana da arziki ƙwarai.

23 Daga nan sai Yesu ya duddubi almajiransa, ya ce musu, “Kai! Ina ji wa masu dukiya wuyar shiga Mulkin Allah!” 24 Almajiran kuwa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ya sake ce musu, “Ya ku ’ya’yana, ina ji wa masu dogara da dukiya wuyar shiga Mulkin Allah. 25 Zai fiye wa rakumi sauƙi ya bi ta ƙofar allura, a kan mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 26 Sai suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ce masa, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?” 27 Yesu ya dube su, ya ce, “Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba ne, amma fa ba ga Allah ba. Don kowane abu mai yiwuwa ne a gun Allah.” 28 Sai Bitrus ya fara ce masa, “To, ai ga shi, mu mun ya da komai, mun bi ka.” 29 Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko ’yan’uwansa maza, ko ’yan’uwansa mata, ko uwatasa, ko ubansa, ko ’ya’yansa, ko gonakinsa, sabili da ni da kuma Bishara, 30 sa’an nan ya ƙasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, na gidaje, da ’yan’uwa maza, da ’yan’uwa mata, da iyaye mata, da ’ya’ya, da gonaki, amma game da tsanani, a Lahira kuma ya sami rai madawwami. 31 Da yawa na farko za su koma na ƙarshe, na ƙarshe kuma za su zama na farko.”

Yesu a Hanyar Urushalima

32 Suna cikin tafiya Urushalima, Yesu kuwa na tafe gabansu, sai suka yi mamaki, mutanen da ke biye kuma suka tsorata. Sai ya sake keɓe Sha biyun nan, ya fara shaida musu abin da zai same shi. 33 Ya ce, “Ga shi za mu Urushalima, kuma za a ba da Ɗam Mutun ga manyan malamai da malaman Attaura, za su kuwa yi masa hukuncin kisa, su bāshe shi ga sauran al’umma. 34 Za su yi masa ba’a, su tofa masa yawu, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi.”

Roƙon ’Ya’yan Zabadi

35 Sai Yakubu da Yohana, ’ya’yan Zabadi, suka kusato shi, suka ce masa, “Ya Shugaba, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙe ka.” 36 Sai ya ce musu, “Me ku ke so in yi muku?” 37 Suka ce masa, “Ka yarje mana, ranar ɗaukakarka, mu zauna ɗaya a hannunka na dama, ɗaya a na hagu.” 38 Amma sai Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da ku ke roƙo ba. Kwa iya sha da ludayina? Ko kwa iya jure dumbun wahalad da zan jure?” 39 Suka ce masa, “Ma iya.” Sai Yesu ya ce musu, “Ludayin da na sha, da shi za ku sha, dumbun wahalad da na jure kuma ita za ku jure; 40 amma zama a hannuna na dama, ko na hagu, ba nawa ba ne da zan bayar, ai na waɗanda aka riga aka shirya wa ne.” 41 Da almajiran nan goma suka ji haka, sai suka fara jin haushin Yakubu da Yohana. 42 Yesu ya kira su ya ce, musu, “Kun san cewa waɗanda aka san su da mulkin sauran al’umma su kan nuna musu iko, hakimansu ma su kan gasa musu iko. 43 Ba haka zai zama a tsakaninku ba. Amma duk wanda ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. 44 Wanda duk kuma ke son ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawan kowa. 45 Don Ɗam Mutum ma ya zo ne ba don a bauta masa ba, sai dai don shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Bartimawas Makaho

46 Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi da almajiransa da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho mai bara, wai shi Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya. 47 Da ya ji dai Yesu Banazare ne, sai ya fara daga murya yana cewa, “Ya Yesu, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 48 Sai wasu da yawa suka kwaɓe shi ya vi shiru. Amma sai ƙara daga murya ya ke yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 49 Sai Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kirawo shi.” Sai suka kirawo makahon suka ce masa, “Albishirinka! Taso, yana kiranka.” 50 Sai ya ya da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu. 51 Yesu ya ce masa, “Me ka ke so “in yi maka?” Makahon ya ce masa, “Rabboni, in sami gani mana!” 52 Sai Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkad da kai.” Nan take ya sami gani, ya bi Yesu suka tafi.

11

Mutanen Urushalima sun Marabci Yesu

Da suka kusato Urushalima da Baitafaji da Baitanya, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da ke gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi. 3 Kowa ya ce da ku, ‘Dom me ku ke haka? ku ce, ‘Ubangiji ne ke bukatarsa, zai kuma komo da shi nandanan.”’ 4 Sai suka tafi, suka tarad da aholakin a ɗaure a ƙofar gida a bakin hanya, suka kwance shi. 5 Sai waɗanda ke tsaitsaye a gun suka ce musu, “Dom me ku ke kwance aholakin nan?” 6 Sai suka faɗa musu abin da Yesu ya ce. Sai kuwa suka ƙyale su suka tafi. 7 Suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfiɗa mayafansu a kai, ya hau. 8 Sai mutane da yawa suka shisshimfiɗa mayafansu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza ganyen da suka kakkaryo a saura. 9 Da na gaba da na baya suka riƙa sowa suna cewa, “Hosanna! Yabo ya tabbata ga Maizuwa da sunan Ubangiji! 10 Yabo ya tabbata ga mulki mai zuwa na kakammu Dawuda! Allah ya yi masa albarka daga Sama mafi ɗaukaka!”

11 Sai ya shiga Urushalima, ya shiga Ɗakin Ibada. Da dai ya dudduba komai, da ya ke magariba ta yi, sai ya fita ya tafi Baitanya tare da Sha biyun nan.

Ɓaure Marar ’ya’ya

12 Washegari da suka tashi daga Baitanya, sai ya ji yunwa. 13 Da ya hango wani ɓaure mai ganye kore shar, sai ya je ya ga ko ya sami ’ya’ya. Da ya isa wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne. 14 Sai ya ce da ɓauren, “Kada kowa ya ƙara cin ’ya’yanka har abada!’ Almajiransa kuwa na ji.

Yesu a Ɗakin Ibada

15 Sai suka iso Urushalima. Ya shiga Ɗakin Ibada ya fara korar masu saye da sayarwa a ciki, ya kuma birkice teburan ’yan-canjin-kuɗi da kujerun masu sai da tattabaru; 16 ya kuma hana kowa ratsa Ɗakin Ibada ɗauke da wani abu. 17 Sai ya yi musu gargaɗi ya ce, “Ashe ba a rubuce ya ke ba, cewa, ‘Za a kira Ɗakina Ɗakin addu’a na dukkan al’ummai’? Amma ku kun maishe shi kogon ’yam-fashi.” 18 Sai manyan malamai da malaman Attaura suka ji wannan magana, suka kuma nemi hanyar hallaka shi, saboda sun tsorata da shi, don duk jama’a na mamaki da koyarwatasa. 19 Kowace yamma kuwa Yesu ya kan fita gari.

20 Suna wucewa da safe, sai suka ga ɓauren nan ya bushe har saiwarsa. 21 Bitrus kuwa ya tuna, sai ya ce masa, “Ya Shugaba, dubi! Ɓauren nan da ka la’anta ya bushe ƙangarau!” 22 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku gaskata da Allah. 23 Hakika, ina gaya muku, kowa ya ce da dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ bai kuwa yi shakka a zuci ba, amma ya gaskata cewa abin da ya faɗa zai auku, sai a yi masa shi. 24 Don haka ina dai gaya muku, komai kuka roƙa da addu’a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu. 25 Koyaushe kuka tsaya yin addu’a, in akwai wanda ku ke jin haushi, ku yafe masa, domin Ubanku da ke Sama shi ma yă yafe muku laifuffukanku. 26 Amma im ba kwa yafewa, haka Ubanku da ke Sama ma ba zai yafe muku laifuffukanku ba.”

27 Sai suka koma Urushalima. Yana zaga cikin Ɗakin Ibada sai manyan malamai, da malaman Attaura, da shugabannin jama’a suka zo wurinsa, 28 suka ce masa, “Da wane izini ka ke yin waɗannan abubuwa, ko kuwa wa ya ba ka izinin yin haka?” 29 Sai Yesu ya ce musu, “Zan yi muku wata tambaya. Ku ba ni amsa, ni kuwa in gaya muku ko da wane izini na ke yin abubuwan nan. 30 To, babtismad da Yohana ya yi, daga Sama ta ke, ko kuwa ta mutun ce? Ku ba ni amsa.” 31 Sai suka yi muhawara da juna, suka ce, “Im muka ce, ‘Daga Sama ta ke,’ sai ya ce, ‘To, dom me ba ku gaskata shi ba?’ 32 Ma kuwa ce, ‘Ta mutun ce?’” Suna kuwa jin tsoron jama’a, don duk kowa ya tabbata cewa Yohana annabi ne. 33 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini na ke yin abubuwan nan ba.”

12

Misali kan Garkar Inabi

Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutun ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata ’yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa’an nan ya tafi wata ƙasa. 2 Da kakar inabin ta yi, sai ya aiki wani bawansa wurin manoman nan ya karɓo masa gallar garkar. 3 Manoman kuwa suka kama shi, suka yi masa duka, suka kore shi hannu banza. 4 Sai ya sake aika musu wani bawan. Shi kuma suka yi masa rotsi, suka wulakanta shi. 5 Ya sake aiken wani, shi kam sai suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wasu da yawa, ana dukan wasu, ana kashe wasu. 6 Har yanzu dai yana da sauran ɗaya tak, shi ne makaɗaicin ɗansa. Daga ƙarshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ‘Sa ga girman ɗana.’ 7 Amma manoman nan sai suka ce da juna, ‘Ai wannan shi ne magajin. Ku zo mu kashe shi, gadon yă zama namu.’ 8 Sai suka kama shi, suka kashe shi, suka jefad da shi bayan shinge. 9 To, me ubangijin garkan nan zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar. 10 Ashe ba ku taɓa karanta wannan Nassin ba? cewa,

‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ya zama babban dutsen harsashin gini.
11 Wannan aikin Ubangiji ne,
A gare mu kuwa abin al’ajabi ne.’

12 Sai suka nemi kama shi, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama’a. Don haka suka ƙyale shi, suka tafi abinsu.

Harajin Kaisar

13 Sai suka aiko masa da wasu Farisiyawa da mutanen Hirudus, don su burma shi cikin maganatasa. 14 Da suka zo, sai suka ce masa, “Haba Malan, ai mun san kai mai gaskiya ne, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyad da tafarkin Allah sosai ka ke yi. Shin daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa? 15 Mu biya, ko kada mu biya?” Shi kuwa da ya gane makircinsu, sai ya ce musu, “Me ku ke haƙa mini rami? Ku kawo min dinari in gani.” 16 Suka kawo masa. Ya ce musu, “Suran nan da sunan nan na wanene?” Suka ce masa, “Na Kaisar ne.” 17 Sai Yesu ya ce musu, “To, ku mayar wa da Kaisar abin da ke na Kaisar, ku kuma mayar wa da Allah abin da ke na Allah.” Sai suka yi mamakinsa ƙwarai.

Sadukiyawa—Tashin Matattu

18 Sai Sadukiyawa, su da ke cewa wai ba Tashin Matattu, suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce, 19 “Malan, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan’uwan mutun ya mutu, ya bar matatasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ’ya’ya. 20 To, an yi wasu ’yan’uwa maza guda bakwai. Na farkon ya yi aure, ya mutu bai bar baya ba. 21 Na biyun kuma ya aure ta, shi ma ya mutu ba da. Na ukun ma haka. 22 Haka dai duk bakwai ɗin ba wanda ya bar ɗa. Daga ƙarshe kuma ita matar ta mutu. 23 To, a Tashin Matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? don duk bakwai ɗin sun aure ta.”

24 Sai Yesu ya ce musu, “Ba ko wannan ne ya sa kuka ɓata ba? da ba ku san Littattafai Tsarkaka ba, ba ku kuma san ikon Allah? 25 Don in an tashi daga matattu, ba a aure, ba a aurarwa, amma kamar mala’ikun da ke Sama a ke. 26 Game da tashin matattu kuma, ashe ba ku taɓa karantawa a Littafin Musa ba, a Nassin Sarƙakiya, yadda Allah ya ce masa, ‘Ni ne AlIahn Ibrahim, kuma Allahn Isiyaku, kuma Allahn Yakubu’? 27 Ai waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Kun ɓata da gaske.”

Umarnin Allah Mafi Girma

28 Sai wani malamin Attaura ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu ya ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wane umarni ne mafi girma, duka?” 29 Yesu ya amsa masa ya ce, “Mafi girma shi ne, ‘Ku saurara, ya Bani Isra’ila; Ubangiji Allahmmu, Ubangiji ɗaya ne. 30 Kuma sai ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka, kurna da dukkan ƙarfinka.’ 31 Mabiyinsa shi ne, ‘Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.’ Ba fa sauran wani umarnin da ya fi waɗannan girma.” 32 Sai malamin Attaura ya ce masa, “Hakika gaskiyarka Malan, Ubangiji ɗaya ne, babu kuwa wani sai shi. 33 A ƙaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukkan hankali, da dukkan ƙarfi, a kuma ƙaunaci ɗan’uwa kamar kai, ai ya fi dukkan hadayar ƙone-ƙone da yanke-yanke nesa.” 34 Da Yesu ya ga ya yi masa magana da fasaha, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da Mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya yi ƙarfin-halin sake tambayarsa wani abu.

35 Sa’ad da Yesu ke koyarwa aƊakin Ibada sai ya ce, “Kaka malaman Attaura za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne? 36 Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Tsattsarka ya ce,

‘Ubangiji ya ce da Ubangijina,
Zauna a hannuna na dama,
Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’

37 Dawuda kansa ya kira shi Ubangiji. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?” Babban taron mutane kuwa sun saurare shi da murna.

38 A cikin koyarwatasa har ya ce, “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo cikin manyan riguna, da son a gaishe su a kasuwa, 39 da kuma son mafifitan mazaunai a majami’u, da mazaunan alfarma a wurin biki. 40 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, da yin doguwar addu’a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

41 Sai ya zauna gaban baitalmalin Ɗakin lbada, yana duban yadda jama’a ke zuba kuɗi a ciki. Waɗansu masu arziki da yawa suna zuba kuɗi masu tsoka. 42 Sai ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta zo, ta zuba sisin kwabo biyu a ciki, wato kwabo ke nan. 43 Sai ya kira almajiransa, ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiyar gwauruwan nan ta zuba cikin baitalmalin nan ya fi na sauran duka. 44 Su duk sun bayar daga yalwatasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk abin da ta ke da shi, duk ma kuɗinta na abinci.”

13

Alamomin Karshen Zamani

Yesu na fita daga Ɗakin Ibada, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Kai! Ya Shugaba, dubi irin duwatsun nan da gine-ginen nan!” 2 Sai Yesu ya ce masa, “Ka ga manyan gine-ginen nan ai! Ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan’uwansa, ba a baje shi ba.”

3 Yana zaune a kan Dutsen Zaitun wanda ke kallon Ɗakin Ibada, sai Bitrus da Yakubu da Yohana da Andarawas suka tambaye shi a keɓe suka ce, 4 “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa’ad da su ke shirin aukuwa?” 5 Sai Yesu ya fara ce musu, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku. 6 Mutane da yawa za su zo suna aron sunana, suna cewa su ne ni, har su ɓad da mutane da yawa. 7 In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da jita-jitarsu, kada hankalinku ya tashi. Lalle ne wannan ya auku, amma ƙarshen tukuna. 8 Kabila za ta tasam ma kabila, mulki ya tasam ma mulki. Za a yi ta raurawar ƙasa a wurare daban-daban, da kuma yunwa. Amma fa duk wannan somin azaba ne tukuna.

9 “Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisu, a kuma yi muku duka a majami’u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, don ku ba da shaida a gabansu. 10 Amma lalle sai an fara yi wa dukkan kabilu Bishara. 11 Sa’ad da suka kai ku gaban shari’a suka miƙa ku, kada ku damu kan abin da za ku faɗa. Amma duk abin da aka yi muku baiwa da shi a lokacin nan, shi za ku faɗa, don ba ku ne ke magana, ba, Ruhu Tsattsarka ne. 12 Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. ’ya’ya kuma za su tayar wa iyayensu bar su sa a kashe su. 13 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe zai cetu.

14 “Sa’ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai ban ƙyama a wurin da bai kamata ba, (mai karatu fa yă fahinta), to, sai waɗanda ke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu. 15 Wanda ke kan soro kuma kada ya sauko ya shiga gida garin ɗaukar wani abu. 16 Wanda ke gona kuma kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa. 17 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! 18 Ku yi addu’a kada abin nan ya auku cikin damuna. 19 A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon halittad da Allah ya yi har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada. 20 Ba don Ubangiji ya taƙaita kwanakin nan ba, da ba bil’adan ɗin da zai tsira. Amma albarkacin zabaɓɓun nan da ya zaɓa, sai ya taƙaita kwanakin. 21 To, a lokacin nan kowa ya ce muku, ‘Kun ga, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Kun ga, ga shi can!’ kada ku yarda. 22 Don almasihan karya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna alamu da abubuman al’ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 23 Amma ku kula! Na dai gaya muku komai tun da wuri.

24 “Amma a lokacin nan, wato, bayan tsabar wahalan nan, za a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. 25 Taurari za su riƙa fadowa daga sararin sama, za a kuma girgiza manya-manyan abubuwan da ke sararin sama. 26 A sa’an nan ne za a ga Ɗam Mutun na zuwa cikin gajimare, da iko mai girma da ɗaukaka. 27 Sa’an nan sai ya aiko mala’ikunsa su tattaro zabaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato daga iyakar duniya har ya zuwa iyakar sama.

28 “Ku yi koyi da icen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan. 29 Haka kuma sa’ad da kuka ga waɗannan abubuwa na aukuwa, ku san cewa ya kusato, a bakin ƙofa ma ya ke. 30 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku. 31 Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.

32 “Amma fa wannan rana ko wannan sa’a ba wanda ya sani, ko mala’ikun da,ke Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 33 Ku kula, ku zauna a faɗake, kuna addu’a, don ba ku san sa’in da lokacin zai yi ba. 34 Kamar mutun ne mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta yaransa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai jiran ƙofa ya zauna a faɗake. 35 To, ku kula fa, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, da yamma ne, da tsakad dare ne, da carar zakara ne, ko da safe ne, 36 kada ya zo kwaram ya samu kuna barci. 37 Abin kuwa da na gaya muku, ina gaya wa kowa ne, shi ne ku kula.”

14

Sauran kwana biyu a yi Idin Ƙetarewa da Idin Burodi Marar Yisti, sai manyan malamai da malaman Attaura suka nemi hanyar kama Yesu da makirci, su kashe shi, 2 don sun ce, “Ba dai a lokacin Idi ba, don kada jama’a su yi hargowa.”

Yesu a Gidan Siman Kuturu

3 Yesu na Baitanya a gidan Siman Kuturu, yana cin abinci ke nan, sai ga wata mace ta zo da wani ɗan tulu na man ƙanshi na nardia tsantsa, mai tsadar gaske. Sai ta fasa tulun, ta tsiyaye masa man a ka. 4 Waɗansu kuwa da suka ji haushi, sai suka ce da juna, “Menene na ɓata mai haka? 5 Gama da an sai da shi fiye da dinari ɗari uku, am ba gajiyayyu!” Sai suka hasala da ita, suna gunaguni. 6 Amma Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Dom me ku ke damunta? Ai alheri ta yi mini, na gaske kuwa. 7 Kullum kuna tare da gajiyayyu, kuma koyaushe kuka so, kwa iya yi musu alheri, amma ba kullun ne ku ke tare da ni ba. 8 Ta yi iyakacin ƙoƙarinta. Ta shafa jikina da mai gabannin jana’izata. 9 Hakika kuwa ina gaya muku, duk inda za a yi Bishara a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa, don tunawa da ita.”

10 Sai Yahuda Iskariyoti, ɗaya daga cikin Sha biyun nan, ya je wurin manyan malamai don ya bashe shi a gare su. 11 Da suka ji haka sai suka yi murna, har suka yi alkawarin ba shi kuɗi. Shi kuwa ya riƙa neman hanyar bashe shi.

Cin Jibin Ƙetarewa

12 A ranar farko ta Idin Burodi Marar Yisti, wato ran da aka saba yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa, sai almajiransa suka ce masa, “Ina ka ke so mu je mu shirya maka cin Jibin Ƙetarewa?” 13 Sai ya aiki almajiransa biyu, ya ce musu, “Ku shiga gari, can za ku gamu da wani mutun ɗauke da tuhun ruwa, ku bi shi. 14 Duk gidan da ya shiga, ku ce da maigidan, ‘In ji Shugaba, ina masauƙinsa da zai ci Jibin Ƙetarewa da almajiransa?’ 15 Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.” 16 Sai almajiran suka tashi, suka shiga cikin gari, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

17 Da magariba ta yi, sai ya zo tare da Sha biyun nan. 18 Suna cin abinci ke nan, sai Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni, wanda mu ke ci tare kuwa.” 19 Sai suka fara baƙinciki, suna ce da shi daidai da daidai, “Ni ne?” 20 Sai ya ce musu, “Ɗaya daga cikin Sha biyun nan ne dai, wanda mu ke ci akushi ɗaya. 21 Don Ɗam Mutun zai tafi ne, yadda labarinsa ke rubuce, duk da haka kuwa mutumin nan da ke ba da Ɗam Mutun ya shiga uku! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”

22 Suna cikin cin abinci, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Ungo, wannan jikina ne.” 23 Sai ya ɗauki ƙoƙo, kuma bayan ya yi godiya ga Allah, sai ya ba su, dukkansu kuwa suka shassha. 24 Sa’an nan ya ce musu, “Wannan jinina ne na tabbatar Alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa. 25 Hakika, ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranan nan da zan sha wani sabo a Mulkin Allah.”

26 Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun. 27 Yesu ya ce musu, “Duk za ku ƙosa ne, don a rubuce ya ke, cewa, ‘Zan buge makiyayi, tumaki kuwa su fasu.’ 28 Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.” 29 Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun ƙosa, ni kam ba zan ƙosa ba.” 30 Sai Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan daren, kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.” 31 Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi yana cewa, “Ko da za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Dukkansu ma haka suka ce.

Yesu a Jatsamani

32 Sai suka isa wani wuri, wai shi Jatsamani. Ya ce da almajiransa, “Ku zauna nan har in yi addu’a.” 33 Sai ya ɗauki Bitrus da Yakubu da Yohana, ya kuma fara jin wahala gaya, yana damuwa ƙwarai. 34 Sai ya ce musu, “Raina na shan wahala matuƙa, har ma kamar na mutu. Ku dakata nan, ku zauna a faɗake.” 35 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya faɗi ƙasa, ya yi addu’a ko ya yiwu a ɗauke masa wannan lokaci. 36 Sa’an nan ya ce, “Ya Abba, Uba, kowane abu mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini shan wahalan nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.” 37 Sai ya komo ya samu suna barci, sai ya ce da Bitrus, “Siman, barci ka ke? Ashe, ba za ka iya zama a faɗake ko da sa’a ɗaya ba? 38 Ku zauna a faɗake, ku yi addu’a kada ku faɗa ga gwaji. Zuciya kam ta ɗauka, jiki ne rarrauna.” 39 Sai ya sake komawa, ya yi addu’a, yana maimaita maganar dā. 40 Har wa yau kuma ya sake dawowa, ya samu suna barci, don duk barci ya cika musu ido ƙwarai, sun kuwa rasa abin da za su ce masa. 41 Ya sake komowa zuwa na uku, ya ce musu, “Har yanzu barci ku ke yi kuna hutawa? Ya isa haka. Lokaci ya yi. Am ba da Ɗam Mutun ga masu zunubi. 42 Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe nin nan ya matso!”

Yahudawa sun Kama Yesu

43 Nandanan, kamin ya rufe baki sai ga Yahuda, ɗaya daga clkin Sha biyun nan, da taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan malamai da malaman Attaura da shugabanni ne suka turo su. 44 To, mai bashe shin nan ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi, ku tafi da shi a rirriƙe.” 45 Da zuwansa kuwa sai ya zo wurin Yesu, ya ce masa, “Ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa. 46 Su kuwa suka danƙe Yesu, suka kama shi. 47 Amma ɗaya daga cikin na tsayen sai ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan Babban Malamin sara, ya ɗauke masa kunne. 48 Sai Yesu Ya ce musu, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗamfashi? 49 Kowace rana ina tare da ku a Ɗakin lbada ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. Amma an yi haka ne fa don a cika Littattafai Tsarkaka.” 50 Daganan sai duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.

51 Sai wani saurayi, daga shi sai mayafi, ya bi shi. Suka kai masa cafka, 52 shi kuwa ya bar musu mayafin, Ya gudu huntu.

Yesu a Gaban Kayafas

53 Daganan sai suka tafi da Yesu wurin Babban Malamin. Duk manyan malamai da shugabanni da malaman Attaura suka taru a wurinsa. 54 Bitrus kuma ya bi shi daga nesa-nesa, har cikin gidan Babban Malamin, ya zauna cikin ma’aikatan Ɗakin lbada, yana jin wuta. 55 To, sai manyan malaman da ’yam majalisa duka suka neml shaidad da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi, amma ba su samu ba. 56 Da yawa kam sun yi masa shaidar zur, amma bakinsu bai zo ɗaya ba. 57 Daga baya kuma waɗansu suka taso, suka yi masa shaidar zur suka ce, 58 “Mun ji ya ce wai zai rushe Wurin nan Tsattsarka da mutane suka gina, ya gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba.” 59 Duk da haka dai shaidar tasu ba ta zo ɗaya ba. 60 Sai Babban Malamin ya miƙe ya yi tsakiyatasu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidad da mutanen nan ke yi a kanka fa?” 61 Amma yana shiru abinsa, bai amsa komai ba. Sai Babban Malamin ya sake tambayarsa, “To, ashe kai ɗin nan ne Almasihu Ɗam Maɗaukaki?” 62 Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuma ga Ɗam Mutun zaune a hannun dama na Mai iko, yana kuma zuwa cikin gajimare.” 63 Sai Babban Malamin ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Wace shaida kuma za mu nema? 64 Kun dai ji saɓon da ya yi! Me kuka gani?” Duk suka yanke masa shari’a a kan ya cancanci kisa. 65 Waɗansu ma suka fara tattofa masa yawu, suka ɗaure masa idanu, suka nannaushe shi, suna ce masa, “Mu ga annabci!” Ma’aikatan Ɗakin Ibada kuma suka yi ta marinsa.

Bitrus Ya yi Musun Sanin Yesu

66 Bitrus na ƙasa a filin cikin gida, sai wata baranyar Babban Malamin ta zo. 67 Da ta ga Bitrus na jin wuta, sal ta zura masa ido, ta ce, “Kai ma ai tare ka ke da Banazaren nan Yesu!” 68 Amma sai ya musa ya ce, “Ni ban ma san abin da ƙi ke faɗa ba, balle in fahinta.” Sai ya fito zaure. Zakara kuwa sai ya yi cara. 69 Sai baranyar ta gan shi, ta sake ce da waɗanda ke tsaitsaye a wurin, “Wannan ma nasu ne.” 70 Amma sai ya sake musawa. Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka ce da Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don Bagalile ne kai.” 71 Sai ya fara la’anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan da ku ke faɗa ba.” 72 Nandanan sai zakara ya yi cara ta biyu. Bitrus kuwa ya tuna da maganad da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.” Ko da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.

15

Yesu a Gaban Gwamna Bilatus

Da wayewar gari sai manyan malamai da shugabanni da malaman Attaura da dukkan ’yammajalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Bilatus. 2 Bilatus ya tambaye shi, “Ashe kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Yadda ka faɗan.” 3 Sai manyan malamai suka yi ta ɗora masa laifin abubuwa da yawa. 4 Bilatus ya sake tambayarsa ya ce, “Ba ka da wata amsa? Dubi yawan maganganun da su ke ba da shaida a kanka!” 5 Yesu dai har yanzu bai yi wata magana ba, har Bilatus ya yi mamaki.

6 To, a lokacin Idi kuwa Bilatus ya saba sakam musu kowane da ke ɗaure, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin tawayen. 8 Jama’a fa suka matso, suka fara roƙon Bilatus ya yi musu abin da ya saba yi. 9 Sai ya amsa usu, ya ce, “Wato kuna so ne in sakam muku Sarkin Yahudawa?” 10 Don ya gane cewa saboda hassada ne manyan malamai suka bashe shi. 11 Amma sai manyan malaman suka zuga jama’a gwammna ya sakam musu Barabbas. 12 Sai Bilatus ya sake ce da su, “To, ƙaƙa zan yi da wanda ku ke kira Sarkin Yahudawa?” 13 Sai suka sake ihu suka ce, “A giciye shi!” 15 Bilatus kuwa da ya ke yana son ƙayatad da jama’a, sai ya sakam musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a giciye shi.

16 Sai soja suka tafi da shi cikin fada, wato fadar gwamna, suka tara dukkan kamfanin soja. 17 Sai suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura, suka kuma yi wani kambi na ƙaya, suka sa masa a ka. 18 Sai suka fara gaishe shi, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” 19 Suka riƙa ƙwala masa sanda a ka, suna tattofa masa yawu, sa’an nan suka durƙusa, wai suna masa ladabi. 20 Da suka gama yi masa ba’a, sai suka yaye masa alkyabba mai ruwan jar garurar, suka sa masa nasa tufafin, suka kai shi waje don su giciye shi.

An Giciye Yesu

21 Sai ga wani mai wucewa, wai shi Siman Bakurane, uban Iskandari da Rufas, yana zuwa daga ƙauye. Suka fa tilasta masa ya ɗauki giciyen Yesu. 22 Suka kai Yesu wani wuri wai shi Golgota, wato, Wurin Ƙoƙwan Kai. 23 Suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, amma ya ƙi sha. 24 Sa’an nan suka giciye shi, kuma suka rarraba tufafinsa a junansu, suna ƙuri’a a kansu, su ga abin da kowa zai samu. 25 Da ƙarfe tara na safe suka giciye shi. 26 Aka kuma rubuta sanarwar laifinsa sama da shi, wato, “Sarkin Yahudawa.” 27 Suka kuma giciye ’yam-fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagu. 28 Wannan shi ne cikar Nasin nan da ya ce, “An lasafta shi a cikin masu laifi.” 29 Masu wucewa suka yi ta masa baƙar magana, suna kaɗa kai, suna cewa, “Ahaf! kai da za ka rushe Wuri Tsattsarka, ka kuma gina shi cikin kwana uku, 30 to, sauko daga giciyen, ka ceci kanka mana!” 31 Haka kuma manyan malamai da malaman Attaura suka riƙa masa ba’a a junansu suna cewa, “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa, 32 Almasihun nan Sarkin Bani Isra’ila yă sauko mana daga giciyen yanzu, mu kuwa mu gani mu ba da gaskiya.” Waɗanda aka giciye tare da shi su ma suka zazage shi.

33 Daidai rana tsaka, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 34 Da ƙarfe ukun sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” wato, “Ya Allahna, ya Allahna, dom me ka yashe ni?” 35 Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, sai suka ce, “Kun ji yana kiran Iliya.” 36 Sai ɗayansu ya yiwo gidu, ya jiƙo wani soso da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha, yana cewa, “Bari mu gani ko Iliya zai zo ya sauko da shi.” 37 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, kuma ya cika. 38 Sa’an nan Labulen Wuri Tsattsarka ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. 39 Sa’ad da kyaftin ɗin da ke tsaye yana kallon Yesu, ya ga yadda ya mutu haka, sai ya ce, “Hakika mutumin nan Ɗan Allah ne!”

40 Akwai kuma waɗansu mata da ke hange daga nesa, cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu ƙarami da Yosi da kuma Salome, 41 su ne waɗanda suka biyo shi, sa’ad da ya ke ƙasar Galili, suna yi masa hidima; da kum mata da yawa ma da suka rako shi Urushalima.

Jana’izar Yesu

42 La’asar lis, da ya ke Ranar Shiri ce, wato gobe Asabar, 43 sai Yusufu ya zo, mutumin Arimatiya, wani ɗam-majalisa mai mutunci, wanda shi ma kuwa ke sauraron bayyanar Mulkin Allah, ya yi ƙarfin-hali ya shiga wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 44 Bilatus ya yi mamakin cewa har ya mutu. Sai ya kira kyaftin ɗin, ya tambaye shi ko Yesu ya jima da mutuwa. 45 Da ya san haka daga bakin kyaftin ɗin sai ya bai wa Yusufu gawar. 46 Sai Yusufi ya sayi likkafanin linen. Da ya sauko da Yesu, sai ya sa shi a likkafanin linen ɗin, ya kwantad da shi a wani kabarin da aka fafe dutse aka yi, ya kuma mirgina wani dutse a bakin kabarin. 47 Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yosi sun ga inda aka kwantad da shi.

16

Yesu ya Tashi daga Matattu

Da Asabar ta wuce, sai Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma Salome, suka sayo kayan ƙanshi, don su ji su shafa masa. 2 A ranar farko ta mako, da asussuba suka tafi kabarin, da fitowar rana sai suka isa. 3 Suna ce da juna, “Wa zai mirgine mana dutsen nan daga bakin kabarin?” 4 Da suka ɗaga kai, sai suka ga ashe an mirgine dutsen waje ɗaya, ga shi kuwa ƙato ne ƙwarai. 5 Suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi a zaune daga dama, saye da farar riga. Sai suka firgita. 6 Shi kuwa ya ce musu, “Kada ku firgita. Yesu Banazare ku ke nema, wanda aka giciye. Ai ya tashi, ba ya nan. Kun ga ma wurin da suka kwantad da shi! 7 Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa, duk da Bitrus, cewa zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.” 8 Sal suka fita, suka ruga a guje daga kabarin, suna rawar jiki a ruɗe. Ba su kuma ce da kowa komai ba, don suna tsoro.

9 Da ya tashi da rai da wuri ranar farko ta mako, sai ya fara bayyana ga Maryamu Magadaliya, wadda ya fitar wa da aljannu bakwai. 10 Ita kuwa ta tafi ta faɗa wa waɗanda da ke tare da shi, ta tarar suna baƙinciki, suna kuka. 11 Amma da suka ji yana da rai, har ma ta gan shi, sai suka ƙi gaskatawa.

12 Bayan haka sai ya bayyana da wata kama ga waɗansu biyu daga cikinsu, sa’ad da su ke tafiya ƙauye. 13 Su ma suka koma suka gaya wa sauran, su ma kuwa ba su gaskata su ba.

14 Daga baya sai ya bayyana ga Sha ɗayan nan su kansu sa’ad da su ke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba. 15 Sai ya ce musu, “Ku tafi ko’ina cikin duniya, ku yi wa dukkan ’yan’adan Bishara. 16 Duk wanda ya ba da gaskiya, kuma aka yi masa babtisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi. 17 Za a ga waɗannan mu’ujizai wurin masu ba da gaskiya, wato, albarkacin sunana za su fid da aliannu; za su yi magana da wasu baƙin harsuna; 18 za su iya ɗaukar maciji, kowace irin guba kuma suka sha, ba za ta cuce su ba ko kaɗan; za su kuma ɗora wa marasa lafiya hannu, su warke.”

Yesu ya Hau Sama

19 To, bayan Ubangiji Yesu ya yi musu jawabi, sai aka ɗauke shi aka kai shi Sama, ya zauna a hannun dama na Allah. 20 Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa’azi ko’ina, Ubangiji na taimakonsu, yana tabbatad da Maganar Allah ta mu’ujizan nan da ke tafe da ita. Hakika.


BISHARA TA HANNUN
LUKA

Tun da ya ke mutane da yawa sun ɗauki tsara tarihin waɗannan al’amura da suka tabbata a cikimmu, 2 daidai yadda waɗanda su ke shaidu tun farkon al’amari, masu hidimar Maganar Allah, suka rattaba mana; 3 kuma da ya ke na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya matifici Tiyofalas, 4 don kă san ingancin maganad da aka sanad da kai baka da baka.

Iyayen Yohana Maibabfisma

5 A zamanin Hirudus Sarkin Yahudiya, an yi wani malami mai suina Zakariya, na fannin Abiya. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu. 6 Dukkansu biyu kuwa masu gaskiya ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka cikin halin rashin zargi. 7 Amma ba su da ɗa, don Alisabatu juya ce, dukkansu biyu kuma sun tsufa.

Jibirilu ya Bayyana ga Zakariya

8 Ana nan, wata rana Zakariya na kan hidimatasa ta kusantar Allah, a sa’ad da hidimar ta kewayo kan fanninsu, 9 bisa al’adar hidimar kusantar Allah, sai ƙuri’a ta nuna shi ne mai shiga Wuri Tsattsarka na Ubangiji a Ɗakin Ibada, ya ƙona turaren wuta. 10 A lokacin ƙona turaren wuta kuwa duk taron jama’a na waje, suna addu’a, 11 sai wani mala’ikan Ubangiii ya bayyana gare shi, tsaye dama da Wurin ƙona turaren wutar. 12 Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro ya rufe shi. 13 Amma sai mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu’arka, matarka Alisabatu za ta haifar maka da, za ka kuma sa masa suna Yohana.

14 Za ka yi murna da farinciki,
Mutane da yawa kuma za su yi farinciki da haifuwatasa.
15 Don zai zama mai girma a wurin Ubangiji,
Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba.
Za a cika shi da Ruhu Tsattsarka
Tun yana cikin uwatasa.
16 Zai kuma juyo da Bani Isra’ila da yawa ga Ubangiji Allahnsu.
17 Zai riga shi gaba, yana mai ruhu da iko irin na Iliya.
Yi mai da hankalin iyaye kan ’yayansu,
Yd kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar masu gaskiya,
Ya tanada wa Ubangiji jama’a, ya same su a shirye.”

18 Sai Zakariya ya ce da mala’ikan, “Ƙaƙa zan san haka? Ga ni tsoho, maiɗakina kuma ta kwan biyu.” 19 Sai mala’ikan ya amsa masa ya ce, “Ni ne Jibirilu da ke tsaye a gaban Allah. Am aiko ni ne in yi maka magana, in kuma yi maka wannan albishir. 20 To, ga shi, za ka bebance, ba za ka iya magana ba sai ran da al’amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta.” 21 Jama’a na ta jiran Zakariya, suna mamakin jinkirinsa a Wuri Tsattsarka. 22 Da ya fito, sai ya ƙasa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Wuri Tsattsarka. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma har yanzu shiru. 23 Sa’ad da kuma kwanakin hidimarsa suka cika, sai ya koma gida.

24 Bayan kwanakin nan sai matatasa Alisabatu ta yi ciki. Sai ta riƙa ɓuya har wata biyar, tana cewa, 25 “Haka Ubangiji ya yi mini a kwanakin da ya dube ni da rabama, don yă kawar mini da wulakanci a cikin mutane.”

YIN FAƊI KAN HAIFUWAR YESU

Jibirilu ya Bayyana ga Maryamu

26 A wata na shida sai Allah ya aiko mala’ika Jibirilu wani gari a ƙasar Galili, wai shi Nazarat, 27 gun wata budurwa da aka bashe ta ga wani mutum mai suna Yusufu, na zuriyar Dawuda, sunan budurwar kuwa Maryamu. 28 Sai mala’ikan ya je wurinta, ya ce, “Ranki ya daɗe, ya ke zaɓaɓɓiya, Ubangiji na tare da ke!” 29 Amma sai ta damu ƙwarai da maganar, ta yi ta tunani ko wannan wace irin gaisuwa ce. 30 Mala’ikan kuma ya ce mata, “Kada ƙi ji tsoro, Maryamu, kin sami so wurin Allah. 31 Ga shi kuma za ƙi yi ciki, ƙi haifi da, ƙi kuma sa masa suna Yesu.

32 Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗam Maɗaukaki.
Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda,
33 Zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada;
Mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”

34 Sai Maryamu ta ce da mala’ikan, “Ƙaƙa wannan zai yiwu, tun da ya ke ba a kai ni Ɗaki ba?” 35 Mala’ikan ya amsa mata ya ce,

“Ruhu Tsattsarka zai sauko miki,
Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki.
Saboda baka Tsattsarkan nan da za a haifa za a kira shi Ɗan Allah.

36 Ga shi kuma ’yar’uwarki Alisabatu ma ta yi cikin da namiji da tsufanta, wannan kuwa shi ne watanta na shida, ita da a ke ce wa juya. 37 Ba wata faɗar Allah da za ta ƙasa cika.” 38 Sai Maryamu ta ce, “To, ga shi, ni baiwar Ubangiji ce, yă zamfe mini yadda ka faɗin.” Sai mala’ikan ya tafi daga gare ta.

Maryamu ta je gun Alisabatu

39 A kwanakin nan sai Maryamu ta tashi da hanzari, ta tafi wata ƙasa mai duwatsu, zuwa wani gari na. ƙasar Yahuda. 40 Ta shiga gidan Zakariya ta gai da Alisabatu. 41 Sai ya zamana da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai jariri ya motsa da ƙarfi a cikinta. Aka kuwa cika Alisabatu da Ruhu Tsattsarka, 42 har ta ta da murya da ƙarfi, ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata, ɗan cikinki kuma mai albarka ne! 43 Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da uwar Ubangijina za ta zo gare ni? 44 Don kuwa da jin muryarki ta gaisuwa a kunnena, sai jaririn ya motsa da ƙarfi a cikina don farinciki, 45 Albarka tā tabbata ga wadda ta gaskata, don za a cika abubuwan da Ubangiji ya aiko aka faɗa mata.” 46 Sai Maryamu. ta ce,

Wakar Maryamu

“Zuciyata na ɗaukaka shi Ubangiji,
47 Allah Macecina da shi ruhuna ke ta farinciki,
48 Domin fa shi ya dubi ƙasƙancinta ne baiwatasa.
Ai ga shi ma jamaa ta dukkan zamani,
Mubariƙa ce za su ce mini nan gaba.
49 Domin fa shi da ya ke yana Mai iko,
Ai manya manyan al’amurra yai mini,
Sunansa ko labudda tsattsarka ne.
50 Daga zamani har dai zuwa wani zamani,
Tausansa na ga waɗanda ke tsoronsa.
51 Al’amari babba da ƙarfinsa ya yi,
Ya watsa duk mutakabbirai sun watse.
52 Ya firfitad da sarakuna a sarauta,
Ya ɗaukaka mfasu zaman ƙaskanci.
53 Mayunwata ya yalwata da abubuwan alheri,
Ya sallame su da babu, masu wadata.
54 Ya taimaka wa baransa Isra’ila,
Domin yana tune dai da yin rahamarsa.
55 Ita ya yi alkawari ga kakannimmu,
Tutur ga Ibrahim da duk zuriyarsa.”

56 Maryamu kuma ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, sa’an nan ta koma gida.

Haifuwar Yohana Maibabtisma

57 To, sai lokacin Alisabatu na haifuwa ya yi, ta kuwa haifi da namiji. 58 Sai makwauta da ’yan’uwanta suka ji yadda Ubangiji ya ji tausayinta ƙwarai, har suka taya ta farinciki. 59 Sai ya zamana a rana ta takwas suka zo yi wa ɗan yaron kaciya. Dd za su sa masa sunan ubansa, Zakariya, 60 amma sai uwatasa ta ce, “A’a, Yohana za a sa masa.” 61 Sai suka ce mata, “Ai kuwa ba wani ɗan’uwanku mai suna haka. 62 Sai suka alamta wa ubansa, suna neman sunan da ya ke so a sa masa. 63 Sai ya nemfi a ba shi allo, sa’an nan ya rubuta, “Sunansa Yohana.” Duka aka yi mamaki. 64 Nandanan sai ya sami baki, kwaɗon harshensa ya saku, ya fara magana, yana yabon Allah. 65 Sai tsoro ya rufe dukkan makwautansu. Aka yi ta baza labarin duk waɗannan al’amura ko’ina a dukkan ƙasa mai duwatsu ta Yahudiya. 66 Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, “Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?” Gama ikon Ubangiji na tare da shi.

Waƙar Zakariya

67 Sai aka cika ubansa Zakariya da Ruhu Tsattsarka, ya yi faɗin Maganar Allah ya ce,

68 “Ubangiji Allahn Bani Isra’ila, A gare shi ne lalle yabo ke tabbata,
Don ya kula, ya fanshi ma jama’atasa.
69 Ya tasa ƙaƙƙarfan Maceci dom mu,
Daga zurriya ta baransa shi ne Dawuda.
70 Yadda a tun tunin shi ya faɗa fa ta bakunan
Su annabawan nasa tsarkakan nan.
71 Yă cece mu a gunsu abokanan gabammu,
Har ma a hannun dukkanin maƙiyammu.
72 Don nuna rahama ne ga kakannimmu,
Yă tuna da alkawarinsa tsattsarkan nan.
73 Shi ne rantsuwan nan wadda yai wa Ubammu lbrahimu,
74 Domin yana cetommu gunsu abokanan gabammu,
Yă ba mu baiwa don mu dai bauta masa,
A gabansa ba a cikin halin tsoro ba,
75 Sai dai cikin tsarki da halin gaskiya,
Dukkan iyakar kwanakin nan namu.
76 Ga yadda za a kira ka kai kuma yaro,
Ai annabi na Maɗaukaki ne haƙƙan.
Kai za ka je ka riga Ubangiji gaba,
Domin ka dai shisshirya hanyoyinsa,
77 Ka sanad da su cetonsu su jama’atasa,
Wato na samun gafarar zunubansu.
78 A saboda tsananin rahamar Allahmmu,
Albarkacin rahamar fa hasken alfijir,
Daga can cikin sama ne fa zai keto mana,
79 Har ma yă haskaka su na zaune cikin duhu,
Da waɗanda ke zaune a bakin halaka,
Har ma ya dai bishe mu hanyar lafiya.”

80 Sai ɗan yaron ya girma, ya ƙarfafa a ruhu. Ya kuwa zauna a jeji har ranar bayyanarsa ga Bani Isra’ila.

2

Haifuwar Yesu a Baitalami

A kwanakin nan sai Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da ke ƙarƙashin mulkinsa. 2 Wannan shi ne ƙirge na fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, gwamnan ƙasar Sham. 3 Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi. 4 Sai Yusufu ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da a ke kira Baitalami, (don shi zuriyar Dawuda ne kuma haulatasa), 5 don a rubuta shi, duk da Matyamu, wadda aka yi masa baiko, ta ke kuma da ciki. 6 Sa’ad da su ke can kuwa, sai lokacin haifuwarta ya yi. 7 Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantad da shi cikin wani komin dabbobi, don ba su sami Ɗaki ba a masauƙin.

Mala’iku da Makiyaya

8 A wannan yankin ƙasa kuwa wasu makiyaya na kwana a filin Allah, suna tsaron garken’ tumakinsu da dad dare. 9 Sai ga wani mala’ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskake kewayensu, har suka tsorata gaya. 10 Sai mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi albishir na kawo muku na farinciki mai yawa, wanda zai zame na dukkan mutane. 11 Domin yau an haifa muku Maceci a birnin Dawuda, wanda ya ke shi ne Almasihu, Ubangiji. 12 Ga alamad da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance cikin komin dabbobi.” 13 Kwaram! sai ga taron rundunar Sama tare da mala’ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa,

14 “Daukaka ga Allah ta tabbata, can cikin Sama mafi ɗaukaka.
A duniya amfinci ya tabbata, ga mutanen da ya ke murna da su matuƙa.”

15 Da mala’iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce da juna, “Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanad da mu.” 16 Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamn da Yusufu, da kuma jaririn kwance cikin komin. 17 Da suka gan shi, sai suka bayyana maganad da aka faɗa musu game da wannan ɗan yaro. 18 Duk waɗanda suka ji kuma, sai suka yi ta al’ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu. 19 Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci. 20 Sai makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

21 Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, sai aka sa masa suna Yesu, wato sunan da mala’ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.

22 Kuma da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa Shari’ar Musa, sai suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji, 23 (kamar dal yadda ya ke a rubuce a cikin Shari’ar Ubangiji, cewa, “Duk ɗam farin da aka haifa, za a kira shi keɓaɓɓe a tsarkake ga Ubangiii”), 24 su kuma yi hadaya bisa abin da aka faɗa a Shari’ar Ubangiji, cewa, “Kurciyoyi biyu, ko kuwa ’yan shila biyu.”

Waƙar Simiyan

25 To, akwai wani mutun a Urushalima, mai suna Simiyan, mutun ne mai gaskiya, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin Mai sanyaya wa Bani Isra’ila zuciya. Ruhu Tsattsarka kuwa na tare da shi. 26 Kuma Ruhu Tsattsarka ya riga ya bayyana masa, cewa ba zai mutu ba sai ya ga Almasihun Ubangiji. 27 Ruhu Tsattsarka na iza shi, sai ya shiga Ɗakin lbada. Kuma da iyayen suka shigo da ɗan yaron nan Yesu, su yi masa yadda ka’idar Shari’ar Musa ta ce, 28 sai Simiyan ya rungume shi, ya yi wa Allah godiya, ya ce,

29 “Yanzu kam ya Mamallaki,
Sai ka sallami bawanka lafiya,
Bisa faɗan nan da ka faɗa,
30 Don na ga cetonka zahiri,
31 Da ka shirya a gaban kabilu duka,
32 Haske mai yi wa sauran al’umma buɗi,
Abin kuma ɗaukaka jama’arka. Bani Isra’ila.”

33 Uwatasa da babansa kuwa suna mamakin abin da aka faɗa game da shi. 34 Sai Simiyan ya sa musu albarka, ya ce da Maryamu uwar Yesu,

“Kin ga, wannan yaron, shi aka ƙaddara ya zama sanadin faɗuwar wasu, kuma tashin wasu da yawa a cikin Bani Isra’ila,
Zai kuma zama alama wadda a ke kushenta,
35 Don tunanin zukata da yawa su bayyana.
Ke ma zai zamana kamar ana caka miki mashi.”

Hannatu ta yi maganar Yesu

36 Akwai kuma wata mai yin faɗin Maganar Allah, mai suna Hannatu, ’yar Fanu’ila, na kabilar Ashira. Ta kuwa tsufa ƙwarai, ta yi zaman aure shekara bakwai bayan ɗaukanta na budurci, 37 da mijinta ya mutu kuma ta yi zaman gwauranci har shekara tamanin da huɗu. Ba ta rabuwa da Ɗakin Ibada, tana bautar Allah dare da rana ta yin addu’a da hana kai abinci. 38 Nan take ita ma ta zo, ta yi wa Allah godiya, ta kuma yi maganar ɗan yaron nan ga dukkan masu sauraron fansar Urushalima.

39 Bayan kuma sun ƙare komai da komai bisa Shari’ar Ubangiji, sai suka koma ƙasar Galili suka tafi garinsu Nazarat. 40 Sai ɗan yaron ya girma, ya kawo ƙarfi, yana mai matuƙar hikima. Alherin Allah kuwa na tare da shi.

Yesu a Ɗakin Ibada

41 To, iyayensa su kan je Urushalima kowace shekara a lokacin Idin Ƙetarewa. 42 Da ya shekara goma sha biyu, sai suka tafi bisa al’adarsu a lokacin Idi. 43 Kuma da aka gama Idin, suna cikin komowa, sai yaron, wato Yesu, ya tsaya a Urushalima, ba da sanin iyayensa ba. 44 Su kuwa suka yi ta tafiya wuni guda, suna zaton yana cikin ayari. Sai suka yi cigiyarsa cikin ’yan’uwansu da idon sani. 45 Da ba su same shi ba, sai suka koma Urushalima, suna ta cigiyarsa. 46 Sai kuma a rana ta uku suka same shi cikin Ɗakin Ibada zaune cikin malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi. 47 Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al’ajibin fahintarsa da amsoshinsa. 48 Da suka gan shi sai suka yi mamaki, sai uwatasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk rammu a ɓace.” 49 Sai ya ce musu, “Me ya sa kuka yi ta nemana? Ashe ba ku san wajibi ne in yi sha’anin Ubana ba?” 50 Amma ba su fahinci maganad da ya yi musu ba. 51 Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwatasa kuwa na riƙe da dukkan abubuwan nan a ranta.

52 Yesu kuwa ya yi ta ƙaruwa da hikima, da tsayi, da kuma zama abin ƙauna ga Allah da mutane.

3

Wa’azin Yohana Maibabtisma

A shekara ta goma sha. biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus na gwamnan Yahudiya, Hirudus na sarautar Galili, cran’uwansa Filibus na sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma na sarautar Abilene, 2 a zamanin da Hanana da Kayafas ke Manyan Malamai, sai Maganar Allah ta zaike wa Yohana ɗan Zakariya a jeji. 3 Sai ya zaga duk lardin bakin Kogin Urdun, yana wa’azi mutane su tuba a yi musu babtisma, don a gafarta musu zunubansu. 4 Yadda ya ke a rubuce a Littafin maganar Annabi Ishaya, cewa,

“Muryar mai kira a jeji na cewa,
Ku shirya wa Ubangiji tafarki,
Ku miƙe hanyoyinsa.
5 Za a cike kowane kwari,
Kowane dutse da kowane tsauni za a baje su.
Za a mirce karkatattun wurare,
Za a bi da hanyoyin da ba su biyu ba.
6 Kuma dukkan ’yan’adan za su ga ceton Allah.”

7 Saboda haka, Yohana sai ya ce da taron jama’ad da ke zuwa don ya yi musu babtisma, “Ku macizan ƙaiƙayi! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa azaban nan mai zuwa? 8 Ku yi aikin da zai nuna tubanku, kada ko ma ku fara cewa a ranku Ibrahim ne ubanku. Ina dai gaya muku, Allah na iya halitta wa Ibrahim ’ya’ya da duwatsun nan. 9 Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyad da ba ta yi ’ya’ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.”

10 Sai taron suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi ke nan?” 11 Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, sai su raba da marar ita, mai abinci ma haka.” 12 Masu karɓar haraji ma suka zo a yi musu babtisma, sai suka ce masa, “Ya shugaba, me za mu yi?” 13 Ya ce musu, “Kada ku karɓi fiye da abin da aka umarce ku.” 14 Wasu soja ma suka tambaye shi, “To, mu fa, me za mu yi?” Sai ya ce musu, “Kada ku yi wa kowa ƙwace ko ƙazafi. Ku dai dangana da albashinku.”

15 Da ya ke mutane duk sun zafƙu, kowa na wuswasi a ransa game da Yohana ko watakila shi ne Almasihu, 16 sai Yohana ya amsa wa dukkansu ya ce, “Ni kam, da ruwa na ke muku babtisma, amma wani na zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa im ɓalle ba. Shi ne zai yi muku babtisma da Ruhu Tsattsarka, da kuma wuta. 17 Ƙwaryar shiƙarsa na harmunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai-sarai, ya taro alkama ya sa a taskarsa, amma ɓuntun sai ya ƙone shi a wuta marar kasuwa.”

18 Ta haka, da wasu gargaɗi masu yawa, Yohana ya yi wa jama’a Bishara. 19 Amma Sarki Hirudus, wanda Yohana ya tsawata wa a kan maganar Hirudiya, matar ɗan’uwansa, da kuma dukkan miyagun ayyukan da ya yi, 20 bugu da ƙari kuma har ya ƙulle Yohana a kurkuku.

Babtismar Yesu

21 To, da aka yi wa dukkan mutane babtisma, Yesu ma aka yi masa babtisma, yana cikin addu’a, sai Sama ta dare, 22 Ruhu Tsattsarka ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai no Ɗana Kaunataccena, ina farinciki da kai ƙwarai.”

23 Yesu kuwa sa’ad da ya fara koyarwa, yana da wajen shekara talatin. An ɗauke shi a kan wai shi ɗan Yusufu ne, wanda ya ke ɗan Heli, 24 Heli ɗam Matat, Matat ɗan Lawi, Lawi ɗam Malki, Malki ɗan Yanna, Yanna ɗan Yusufu, 25 Yusufu ɗam Matatiya, Matatiya ɗan Amos, Amos ɗan Nahum, Nahum ɗan Asali, Asali ɗan Najaya, 26 Najaya ɗam Ma’ata, Ma’ata ɗam Matatiya, Matatiya ɗan Shim’i, Shim’i ɗan Yuseka, Yuseka ɗan Yahuda, 27 Yahuda ɗan Yohana, Yohana ɗan Risa, Risa ɗan Zarubabila, Zarubabila ɗan Sha’altilu, Sha’altilu ɗan Niri, 28 Niri ɗam Malki, Malki ɗan Addi, Addi ɗan Kusama, Kusama ɗan Almadama, Almadama ɗan Ar, 29 Ar ɗan Yosi, Yosi ɗan Ali’azaru, Ali’azaru ɗan Yorima, Yorima ɗam Matat, Matat ɗan Lawi, 30 Lawi ɗan Simiyan, Simiyan ɗan Yahuda, Yahuda ɗan Yusufu, Yusufu ɗan Yonana, Yonana ɗan Aliyakimu, 31 Aliyakimu ɗam Malaya, Malaya ɗam Mainana, Mainana ɗam Matat, Matat ɗan Natana, Natana ɗan Dawuda, 32 Dawuda ɗan Yassa, Yassa ɗan Obida, Obida ɗam Bu’azu, Bu’azu ɗan Salmuna, Salmuna ɗan Nahashuna, 33 Nahashuna ɗan Aminadabu, Aminadabu ɗan Arama, Arama ɗan Hasarunu, Hasarurm ɗam Farisa, Farisa ɗan Yahuda, 34 Yahuda ɗan Yakubu, Yakubu ɗan Isiyaku, Isiyaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ɗan Taraha, Taraha ɗan Nahura, 35 Nahura ɗan Saruja, Saruja ɗan Ra’u, Ra’u ɗam Falaja, Falaja ɗan Abiru, Abiru ɗan Shela, 36 Shela ɗan Kan’ana, Kan’ana ɗan Arfakshaɗa, Arfakshaɗa ɗan Samu, Samu ɗan Nuhu, Nuhu ɗan Lamaka, 37 Lamaka ɗam Matushalaha, Matushalaha ɗan Anuhu, Anuhu ɗan Yarada, Yarada ɗam Mahala’ilu, Mahala’ilu cran Kan’ana, 38 Kan’ana ɗan Anosha, Anosha ɗan Shitu, Shitu ɗan Adamu, Adamu kuma na Allah.

4

Iblis ya Gwada Yesu

Yesu kuma cike da Ruhu Tsattsarka sai ya dawo daga Kogin Urdun. Ruhu na iza shi cikin jeji, 2 har kwana arba’in, Iblis na gwada shi. A kwanakin nan bai ci komai ba. Da suka ƙare kuwa sai ya ji yunwa. 3 Iblis ya ce masa, “In kai ɗan Allah ne, ka umarci dutsen nan ya zama burodi.” 4 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce ya ke, cewa, ’Ba da burodi kaɗai mutun zai rayu ba.’ 5 Sai Iblis ya kai shi wani wuri bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkin duniya a cikin kiftawar ido. 6 lbiis ya ce masa, “Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, kuma na kan bayar ga duk wanda na ga dama. 7 In kuwa za ka yi mini sujada, duk sai su zama naka.” 8 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce ya. ke, cewa, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ “

9 Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Ɗakin Ibada, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan. 10 Don a rubuce ya ke, cewa,

‘Zai Yi wa mala’ikunsa umarni game da kai, su kiyaye ka,’

11 kuma

‘Za su tallafe ka,
Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’

12 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ “ 13 Bayan Iblis ya gama irin dukkan gwaje gwajensa, sai ya rabu da shi sai lokacin da ya samu sarari.

Yesu ya fara Wa’azi a Galili

14 Sai Yesu ya koina ƙasar Galili, ikon Ruhu Tsattsarka na tafi da shi. Sai labarinsa ya bazu a dukkan kewayen. 15 Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, duk ana girmama shi.

16 Sai ya zo Nazarat inda aka rene shi. Ya shiga majami’a ran Asabar kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don ya yi karatu. 17 Sai aka miƙa masa Littafin Annabi Ishaya, ya buɗe littafin, ya sami inda aka rubuta, cewa,

18 “Ruhun Ubangiji na tare da ni,
Don ya shafa ni, tsattsarkar shafa,
In yi wa matalauta Bishara.
Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru,
Da kuma buɗe wa makafi ido,
In kuma ’yanta waɗanda ke danne,
19 In yi shela ta zamanin samun karɓuwa ga Ubangiii.”

20 Sai ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda ke cikin majami’a suka zuba masa ido. 21 Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.” 22 Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe wannan ba ɗan Yusufu ba ne?” 23 Yesu ya ce musu, “Lalle za ku tasa mini karin maganan nan, ‘Idan giji ba ta ƙoshi ba, ba ā ba daji ba. Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi a nan garinku. mana.’” 24 Kuma ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ba annabin da ke yardajje a garinsu. 25 Amma gaskiya na ke gaya muku, a zamanin Iliya akwai matan da mazansu suka mutu da yawa a cikin Bani Isra’ila, wato lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa’ad da babbar yunwa ta game dukkan ƙasar. 26 Duk da haka, ba a aiki Iliya gun ko ɗaya daga cikinsu ba, sai ga wata mace kaɗai a Zarifat ta ƙasar Saida, wadda mijinta ya mutu. 27 A zamanin Annabi Aliyasha kuma akwai kutare da yawa a cikin Bani Isra’ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Sham kaɗai.

Mutanen Garinsu sun so Kashe Shi

28 Da suka ji haka, duk waɗanda ke cikin majami’a sai suka fusata ƙwarai. 29 Sai suka tashi suka kora shi bayan gari, har suka kai shi goshin dutsen da aka gina garinsu a kai, don su jefa shi ƙas ta ka. 30 Amma sai ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa.

Yesu a Kafarnahum

31 Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a ƙasar Galili, yana koya musu ran Asabar. 32 Suka yi mamakin koyarwatasa don maganatasa a tabbace ta ke. 33 A cikin majami’ar kuwa akwai wani mutum mai baƙin aIjan. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce, 34 “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wanene kai, Tsattsarkan nan ne kai na Allah.” 35 Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” Bayan aljanin ya fyaɗa shi da ƙasa a tsakiyarsu, sai ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba. 36 Sai mamaki ya rufe su duka, suna ce da juna, “Wannan wace irin magana ce? Ga shi da tabbatarwa, kuma gabagaɗi ya ke umartar baƙaƙen aljannu, suna kuwa fita.” 37 Labarinsa duk ya bazu ko’ina a kewayen ƙasar.

Ya Warkad da Surukar Siman

38 Sai ya tashi daga majami’ar, ya shiga gidan Siman. Surukar Siman kuwa na fama da mugun zazzaɓi, sai suka roƙe shi saboda ita. 39 Sai ya tsaya a kanta, ya tsauta wa zazzaɓin, yu kuwa sake ta. Nan take ta tashi ta yi musu hidima.

40 Daidai faɗuwar rana, sai duk waɗanda ke da marasa lafiya masu cuta iri iri suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗadɗora wa kowarmensu hannu, ya warkad da shi. 41 Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai ɗan Allah ne!” Amma sai ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun san shi ne Almasihu.

42 Da gari ya waye sai ya fita, ya tall wani wuri inda ba kowa. Sai taro masu yawa suka yi ta nemansa, suka je wurinsa. Sonsu su tsaishe shi, kada ya tafi daga gare su; 43 amma sai ya ce musu, “Lalle ne in yi wa sauran garuruwa Bisharar Mulkin Allah. Don saboda wannan nufin ne aka aiko ni.” 44 Sai ya yi ta yin wa’azi a majami’un ƙasar Galili.

5

Almajiran Yesu na Farko

Wata rana taro na matsatasa don su ji Maganar Allah, shi kuwa yana tsaye a bakin Tafkin Janisarata, 2 sai ya hangi ƙananan jirage biyu a bakin tafkin, masuntan kuwa sun fita daga cikinsu, suna wankin tarunansu. 3 Sai ya shiga ɗaya jirgin, wanda ya ke na Siman, ya roƙe shi ya ɗan zakuda da jirgin daga bakin gaci. Sai ya zauna ya yi ta koya wa taro masu yawa daga cikin jirgin. 4 Da ya gama magana, sai ya ce da Siman, “Zakuda da jirgin zuwa wuri mai zurfi, ku saki tarunanku, ku janyo kifi.” 5 Siman ya amsa masa ya ce, “Ya Maigida, dare farai muna wahala, ba mu kama komai ba, amma da ka yi magana zan saki tarunan.” 6 Da suka yi haka kuwa, sai suka kamo kifi jingim, har rna tarunansu suka fara kecewa. 7 Sai suka yafato abokan aikinsu a ɗaya jirgin su zo su taimake su. Suka kuwa zo, suka ciccika jiragen nan duka biyu kamar sa nutse. 8 Da Siman Bitrus ya ga haka, sai ya faɗi a gaban Yesu ya ce, “Ya Ubangiji, wane ni ka tsaya kusa da ni, domin ni mutun ne mai zunubi.” 9 Don shi da waɗanda ke tare da shi duka, mamaki ya rufe su saboda kifin nan da suka janyo; 10 haka ma Yakubu da Yohana ’ya’yan Zabadi, abokan sabgar Siman. Sai Yesu ya ce da Siman, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa tsamowa.” 11 Da suka kawo jiragensu gaci, sai suka bar komai duka suka bi shi.

Yesu ya Warkad da Kuturu

12 Wata rana Yesu na ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutun wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu sai ya faɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda ka iya tsarkake ni.” 13 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take sai kuturtar ta rabu da shi. 14 Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, “sai dai ka je wurin malami ya gan ka, ka kuma yi baiwa saboda tsarkakewarka, don tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.” 15 Amma duk da haka labarinsa sai ƙara yaɗuwa ya ke yi, bar taro masu yawan gaske suka yi ta zuwa don su saurare shi, a kuma warkad da su daga rashin lafiyarsu. 16 Amma shi sai ya riƙa keɓanta a wuraren da ba kowa, yana addu’a.

Yesu ya Warkad da Shanyayye

17 Wata rana yana cikin koyarwa, wasu Farisiyawa kuwa da masana Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa na nan. 18 Sai ga wasu mutane ɗauke da wani shanyayye a kan gado, suna ƙoƙari su shiga da shi su ajiye shi a gaban Yesu. 19 Da suka kasa samun hanyar shiga da shi saboda taro, sai suka hau kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da gadonsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama’a a gaban Yesu. 20 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malan, an gafarta maka zunubanka.” 21 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasin cewa, “Wanene wannan ke maganar saɓo? Wa ke iya gafarta zunubi ban da Allah shi kaɗai?” 22 Da Yesu ya gane wuswasinsu, sai ya amsa musu ya ce, “Dom me ku ke wuswasi haka a zuciyarku? 23 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’? 24 Amma don ku sakankance Ɗam Mutun na da ikon gafarta zunubi a duniya”, sai ya ce da shanyayyen, “Na ce da kai, tashi, ka ɗauki gadonka, ka tafi gida.” 25 Nan take ya tashi a gaban idonsu, ya ɗauki abin kwanciyarsa, ya tafi gida, yana ɗaukaka Allah. 26 Sai suka yi mamaki gaya matuƙa su duka, suka yi ta ɗaukaka Allah, tsoro kuma ya rufe su, suka ce, “Kai, yau mun ga al’ajuba!”

Yesu ya Kira Lawi

27 Bayan haka sai ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi zaune, yana aiki a ofishin karɓar haraji. Sai ya ce masa, “Bi ni.” 28 Sai ya bar komai duka, ya tashi ya bi shi.

29 Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar dina a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da wasu mutane suna ci tare da su. 30 Sai Farisiyawa da malamansu na Attaura suka yi wa almajiransa gunaguni suka ce, “Dom me ku ke ci ku ke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?” 31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. 32 Ba don kiran masu gaskiya na zo ba, sai dai masu zunubi, su tuba.”

33 Sai suka ce masa, “Almajiran Yohana na hana kansu abinci a kai a kai, suna kuma addu’a, haka kuma almajiran Farisiyawa, amma naka suna ci suna sha.” 34 Sai Yesu ya ce musu, “Wato kwa iya sa abokan ango su hana kansu abinci tun angon na tare da su? 35 Ai lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su hana kansu abinci.” 36 Ya kuma kawo musu misali ya ce, “Ba mai tsage ƙyalle a jikin sabuwar tufa ya yi maho a tsohuwar tufa da shi. Im ma an yi, ai sai ya kece sabuwar tufar, kuma sabon ƙyallen ba zai dace da tsohuwar tufar ba. 37 Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofain salkuna. Im ma an ɗura, sai sabon ruwan inabin ya fasa salkunan, ya zube, salkunan kuma su lalace. 38 Sabon ruwan inabi ai sai sababbin salkuna. 39 Ba wanda zai so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon. Don sai ya ce, ‘Ai tsohon na da kyau.’”

6

Yesu da Farisiyawa

Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, sai almajiransa suka zagi alkamar, suna murtsukewa suna ci. 2 Sai wasu Farisiyawa suka ce, “Dom me ku ke yin abin da bai halatta a yi ba ran Asabar?” 3 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ashe ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa’ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa? 4 Yadda ya shiga Ɗakin Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodin nan ya ci, bar ma ya ba abokan tafiyarsa, wanda bai halatta kowa ya ci ba sai malamai kaɗai?” 5 Sai ya ce musu, “Ai Ɗam Mutun shi ne Ubangijin Asabar.

6 A wata Asabar sai ya shiga majami’a, yana koyarwa. Akwai wani mutun kuwa a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye. 7 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka yi haƙonsa su ga ko ya warkar ran Asabar, don su samu su zarge shi. 8 Shi kuwa ya san tunaninsu. Sai ya ce da mai shanyayyen hannun, “Taso, ka tsaya nan tsakiya.” Sai ya taso, ya tsaya a nan. 9 Yesu ya ce musu, “Ina yi muku tambaya. Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? a ceci rai, ko a hallaka shi?” 10 Sai ya duddube su duka, ya ce da mutumin, “Miƙe hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 11 Sai suka fusata ƙwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.

Ya Zaɓi Manzanni Sha Biyu

12 A kwanakin nan sai Yesu ya fita ya ban dutse don yin addu’a. Dare farai yana addu’a ga Allah. 13 Da gari ya waye sai ya kira almajiransa, ya zaɓi goma sha biyu a cikinsu, ya kira su Manzanni. 14 Su ne Siman, wanda ya sa wa suna Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, da Yakubu da Yohana, da Filibus, da Bartalamawas, 15 da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Alfayas, da Siman, wanda a ke ce da shi Zaloti, 16 da Yahuda ɗan Yakubu, da kuma Yahuda Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.

17 Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro na masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Sur da Saida da ke bakin bahar, waɗanda suka zo su saurare shi, a kuma warkad da cuce-cucensu. 18 Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu ke wahalshe su, aka warkad da su. 19 Duk taron suk a nemi taɓa shi, don iko na fitowa daga gare shi, ya kuwa warkad da su duka.

Yesu ya yi wa Almajiransa Jawabi

20 Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce,

“Albarka tā tabbata gare ku, ku matalauta, don Mulkin Allah naku ne.
21 “Albarka tā tabbata gare ku, ku da ke mayunwata a yanzu, don za a ƙosad da ku.
“Albarka tā tabbata gare ku, ku da ke kuka a yanzu, don za ku yi ɗariya.
22 “Albarka tā tabbata gare ku sa’ad da mutane suka ƙi ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗam Mutun. 23 Ku yi farinciki a wannan ranar, ku yi tsalle don murna, don ga shi sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.

24 “Amma kun shiga uku, ku masu arziki, don kun riga kun sami iya rabonku.
25 “Kun shiga uku, ku da ke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa.
“Kun shiga uku, ku masu ɗariya a yanzu, don za ku yi baƙinciki, ku yi kuka.
26 “Kun shiga uku in kowa na yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan karya.

Ku Ƙaunaci Magabtanku

27 “Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri. 28 Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu’a. 29 Wanda ya mare ka a ƙunci ɗaya, juya masa ɗaya ƙuncin kuma. Wanda ya ƙwace maka mayafi, kada ka hana masa taguwarka ma. 30 Duk wanda. ya roƙe ka, ka ba shi. Wanda kuma ya ƙwace maka kaya, kada ka neme su. 31 Yadda ku ke so mutane su yi muku, to, ku yi musu haka.

32 “In masoyanku kawai ku ke ƙauna, wane lada ne da ku? Ai ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu. 33 In kuma sai waɗanda ke muku alheri kawai ku ke yi wa alheri, wane lada ne da ku? Ai ko masu zunubi ma haka su ke yi. 34 In kuma sai ga waɗanda ku ke tsammani za su biya ku ne ku ke ba da rance, wane lada ne da ku? Ai ko masu zunubi ma, su kan ba masu zunubi rance, don a biya su daidai. 35 Amma ku dai ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammanci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama ’ya’yan Maɗaukaki. Don shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma miyagu. 36 Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku ke mai tausayi.

37 “Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku. 38 Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a ɗankare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”

39 Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho na iya yi wa makaho jagora? Ashe dukansu biyu ba sai su faɗa rami ba? 40 Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantad da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa. 41 Dom me ka ke duban ɗan hakin da ke idon ɗan’uwanka, amma gungumen da ke naka idon ba ka kula ba? 42 Ƙaƙa kuma za ka iya ce da ɗan’uwanka, ‘Ya ɗan’uwana, bari in cire maka ɗan hakin da ke idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da ke naka idon ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da ke idonka tukuna, sa’an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da ke idon ɗan’uwanka.

43 “Ba kyakkyawar bishiyad da ke haifar munanan ’ya’ya, ba kuma mummunar bishiyad da ke haifar kyawawan ’ya’ya. 44 Domin kowace bishiya da irin ’ya’yanta a ke saninta. Ai ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙiya. 45 Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciyatasa ya kan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyatasa ya kan yi mugun abu. Ai abin da ya ci rai, shi mutun kan faɗa.

46 “Dom me ku ke kirana ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ba kwa kuwa yin abin da na faɗa muku? 47 Duk mai zuwa wurina, ya ke jin maganata, ya ke kuma aikata ta, zan nuna muku kwatancinsa. 48 Kamar mutun ya ke mai gina gida, wanda ya yi haƙa mai zurfi har ya sa harsashin ginin a kan dutse. Da kogi ya cika ya bai daji, sai ya mangari gidan, amma bai iya girgiza shi ba, saboda an gina shi da aminci. 49 Amma wanda ya ji maganata, bai kuwa aikata ba, kamar mutun ya ke wanda ya gina gida a kan turbaya, ba harsashi. Kuma da kogi ya mangare shi, nandanan sai ya rushe. Kai, wannan gida ya yi mummunar rugurgujewa!”

7

Yesu ya Warkad da Bawan wani Kyaftin

Bayan Yesu ya ƙare jawabinsa duka a gaban jama’a, sai ya shiga Kafarnahum. 2 To, sai bawan wani kyaftin, wanda ubangijinsa ke ji da shi, ya yi rashin lafiya, har ya kai ga bakin mutuwa. 3 Da kyaftin ɗin ya ji labarin Yesu, sai ya aiki wasu shugabannin Yahudawa wurinsa su roƙe shi ya zo ya warkad da bawan nasa. 4 Da suka isa wurin Yesu sai suka roƙe shi ƙwarai suka ce, “Ai ya cancanci a yi masa haka, 5 don yana ƙaunar jama’armu, shi ne ma ya gina mana majami’armu.” 6 Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya matso kusa da gidan, sai kyaftin ɗin ya aiki aminansa wurinsa su ce masa, “Ya Ubangiji, kada ka wahal da kanka. Ban ma isa har ka zo gidana ba. 7 Shi ya sa ban ga ma na isa in zo wurinka ba, amma kă yi magana kawai, yarona kuwa sai ya warke. 8 Don ni ma a hannun wani na ke, da kuma soja a hannuna; sai in ce da wannan, ‘Je ka,’ sai ya je; wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo; in ce da bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.” 9 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce da taron da ke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Bani Isra’ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.” 10 Da waɗanda aka aikan suka koma gidan, sai suka sami bawan garau.

Yesu ya ta da Mataccen Yaro a Na’in

11 Ba da daɗewa ba, sai Yesu ya tafi wani gari wai shi Naim, almajiransa da kuma babban taro suka tafi tare da shi. 12 Ya kusanci ƙofar garin ke nan, sai ga wani mamaci ana ɗauke da shi, shi ke nan kaɗai wajen uwatasa, mijinta kuma ya mutu. Mutanen gari da yawa sun rako ta. 13 Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta, kuma ya ce mata, “Daina kuka.” 14 Sa’an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗaukan kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce da kai tashi.” 15 Mamacin sai ya tashi zaune, ya fara magana. Sai Yesu ya ba da shi ga uwatasa. 16 Sai tsoro ya rufe su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle wani annabi mai girma ya bayyana a cikinimu,” kuma, “Allah ya kula da jama’atasa.” 17 Wannan labari nasa kuwa ya bazu a dukkan ƙasar Yahudiya da dukkan kewayenta.

Yohana Maibabtisma ya yi Tambaya

18 Sai almajiran Yohana suka gaya masa dukkan abubuwan nan. 19 Sai Yohana ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, “Kai ne Maizuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?” 20 Da mutanen nan suka isa wurinsa, sai suka ce, “Yohana Maibabtisma ne ya aiko mu gare ka, yana tambaya, ‘Kai ne Maizuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?’ “ 21 Nan take Yesu ya warkad da mutane da yawa daga rashin lafiyarsu da cuce-cucensu da kuma baƙaƙen aljannu. Makafi da yawa kuma ya yi musu baiwar gani. 22 Sai ya amsa musu ya ce, Ku je ku gaya wa Yohana abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta Bishara. 23 Albarka tā tabbata ga wanda ba ya ƙosawa da ni.”

24 Bayan jakadun Yohana sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yohana, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska ke kadawa? 25 To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fada su ke. 26 To, wai kallon me kuka je yi? Annabi? Hakika, ina gaya muku, har ya fi annabi nesa. 27 Wannan shi ne wanda labarinsa ke rubuce, cewa,

‘Ga shi na aiko manzona ya riga ka gaba,
Wanda zai shirya maka hanya gabaninka.’

28 Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohana girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanci a cikin Mulkin Allah ya fi shi.” 29 Da duk jama’a da masu karɓar haraji suka ji haka, sai suka yarda da gaskiyar Allah, aka kuma yi musu babtisma ta Yohana. 30 Amma Farisiyawa da masana Attaura suka shure abin da Allah ke nufinsu da shi, da ya ke sun ƙi ya yi musu babtisma.

31 “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Waɗanne iri ne su? 32 Kamar yara su ke da ke zaune a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba;
Mun yi kukan mutuwa, ba ku koka ba.’

33 Ga shi, Yohana Maibabtisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, amma kuna cewa, ‘Ai yana da iska.’ 34 Ga Ɗam Mutun ya zo, yana ci yana sha, kuma kuna cewa, ‘Ga nan mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ 35 Duk da haka hikimar Allah, ta dukkan aikinta ne a ke tabbatad da gaskiyatata.”

Mace Mai Zunubi a Gidan Bafarisiye

36 Wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Sai ya shiga gidan Bafarisiyen, ya ƙishingiɗa wurin cin abincin. 37 Sai ga wata matar garin, mai zunubi; da ta ji Yesu na cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo wani ɗan tulu na man ƙanshi, 38 ta tsaya a bayansa wajen ƙafafunsa, tana kuka. Sai hawayenta ya fara zuba a ƙafafunsa, ta goge su da gashinta, ta yi ta sumbantarsu, ta shafa musu man ƙanshin. 39 To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san kowacece, kuma ko wace irin mace ce wannan da ke shafa shi, don mai zunubi ce.” 40 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Siman, ina da magana da kai.” Sai shi kuma ya ce, “Ai sai ka faɗa, ya Shugaba.” 41 Yesu ya ce, “Wani na bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. 42 Da suka gagara biya, sai ya yafe musu duka biyu. To, a cikinsu wa zai fi ƙaunarsa?” 43 Sai Siman ya amsa masa ya ce, “A ganina, wanda ya yafe wa mai yawan.” Sai ya ce masa, “Ka faɗi daidai.” 44 Da ya waiwaya wajen matar, sai ya ce da Siman, “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta. 45 Kai ba ka sumbance ni ba, ita kuwa, tun shigowata nan ba ta daina sumbantar kafafuna ba. 46 Ba ka shafa mini mai a ka ba, amma ita ta shafa man ƙanshi a ƙafafuna. 47 Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawan nan duk an gafarta mata; don ta yi ƙauna mai yawa. Wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, ƙauna kaɗan ya ke yi.” 48 Sai ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.” 49 Sai masu ci tare da shi suka fara ce da juna, “Wannan kuwa wanene wanda har ya ke gafarta zunubai?” 50 Sai Yesu ya ce da matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. ƙi sauka lafiya.”

8

Ba da daɗewa ba sai Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa’azi, yana yin Bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa na tare da shi, 2 da waɗansu mata da aka raba da baƙaƙen aljannu da kuma rashin lafiyarsu. Cikinsu da Maryamu mai suna Magadaliya, wadda aka fitar wa da aljannu bakwai, 3 da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzana, da kuma wasu da yawa da suka yi masa dawainiya da kayansu.

Misalin Mai Shuka

4 Da jama’a masu yawa suka taru, mutane na ta zuwa gare shi gari da gari, sai ya yi musu misali ya ce, 5 “Wani mai shuka ya tafi shuka. Yana cikin yafa iri sai waɗansu suka fantsama a kan hanya, aka tattake su, tsuntsaye suka tsince su. 6 Wasu kuma suka fantsama a kan dutse. Da suka tsiro sai suka bushe, don babu danshi. 7 Wasu kuma suka fantsama cikin ƙaya, suka tashi tare, har ƙayar ta sarƙe su. 8 Wasu kuma suka zuba a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi tsaba riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

9 Sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar misalin. 10 Sai ya ce, “Ku kam an yarje muku ku san zurfafan al’amuran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahinta ba. 11 To, misalin shi ne: Irin, Maganar Allah ce. 12 Waɗanda suka fantsama a kan hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa’an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyatasu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto. 13 Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farinciki. Su kam ba su da tushe. Su kan ba da gaskiya ’yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe. 14 Waɗanda suka fantsama cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani. 15 Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kankan da zuciya ɗaya kyakkyawa, har suka yi amfani game da jimirinsu.

16 “Ba mai kunna fitila ya rufe ta da masaki, ko ya ajiye ta ƙarƙashin gado. A’a, sai dai ya ɗora ta a kan maɗorinta, don masu shiga su ga hasken. 17 Ba abin da ke ɓoye da ba za a bayyana ba. Ba kuma asirin da ba zai tonu ya zama bayyananne ba. 18 Ku kula fa, ku iya ji. Don mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da, ya ke tsammani ya ke da shi ma, sai an karɓe masa.”

19 Sai uwatasa da ’yan’uwansa suka zo wurinsa, amma suka kasa isa gunsa saboda taro. 20 Sai aka ce masa, “Tsohuwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna son ganinka.” 21 Amma sai ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, su ke kuma aikatawa, ai su ne uwata, su ne kuma ’yan’uwana.”

Hadiri a Tafki

22 Wata rana ya shiga jirgi tare da almajiransa. Ya ce musu, “Mu haye wancan ƙetaren tafki.” Sai suka tashi. 23 Suna cikin tafiya sai barci ya kwashe shi. Sai hadiri mai iska ya taso a tafkin, jjrginsu ya tasam ma cika da ruwa, har suna cikin hatsari. 24 Sai suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, mun halaka!” Sai ya farka, ya tsauta wa iskar da kuma haukan ruwan. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit. 25 Ya ce musu, “Ina bangaskiyar taku?” Sai suka tsorata suka yi mamaki, suna ce da juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma ya ke yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”

Yesu ya fid da Aljannu

26 Sai suka iso ƙasar Garasinawa wadda ke hannun riga da ƙasar Galili. 27 Da saukarsa a gaci sai wani mai taɓin aljannu ya fito daga gari ya tare shi. Ya daɗe bai sa tufa ba, ba ya zama a gida kuwa, sai a makabarta. 28 Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.” 29 Don kuwa Yesu ya umarci baƙin aljanin ya rabu da mutumin ne. Gama sau da yawa aljanin kan buge shi, a kan kuma tsare shi, a ɗaure shi da sarka da mari, amma sai ya tsintsinka ɗaurin, aljanin ya kora shi jeji. 30 Sai Yesu ya tambaye shi, “Me sunanka?” Ya ce, “Tuli”. Don aljannu da yawa sun shige shi. 31 Sai suka yi ta roƙonsa kada ya umarce su su faɗa mahalaka.

32 To, wurin nan kuwa wani babban garken alade na kiwo a gangaren dutse, sai suka roƙe shi ya yardam musu su shige su. Ya kuwa yardam musu. 33 Sai aljannun suka rabu da mutumin, suka shigi aladen. Garken kuwa suka rungungunto ta gangaren, suka faɗa tafkin, suka halaka a cikin ruwa.

34 Da ’yan kiwon aladen nan suka a abin da ya faru, sai suka gudu, suka ba da labari birni da ƙauye. 35 Sai jama’a suka firfito su ga abin da ya auku. Suka zo wurin Yesu, suk a tarad da mutumin da aljannun suka rabu da shi, zaune gaban Yesu, saye da tufa, kuma cikin hankalinsa. Sai suka tsorata. 36 Waɗanda aka yi abin a kan idonsu kuwa, suka gaya musu yadda aka warkad da mai taɓin aljannun nan. 37 Sai dukkan mutanen kewayen ƙasar Garasinawa suka roƙi Yesu ya rabu da su, don tsoro mai yawa ya rufe su. Sai ya shiga cikin jirgi ya koma abinsa. 38 Mutumin da aIjannun suka rabu da shi kuwa, sai ya roƙe shi izinin tafiya tare da shi. Amma sai ya sallame shi ya ce, 39 “Koma gida, ka faɗi irin manyan abubuwan da Allah ya yi maka.” Sai ya tafi ko’ina cikin birni yana sanad da manyan abubuwan da Yesu ya yi masa.

Labarin ’Yar Yayinis

40 To, da Yesu ya komo, sai taron suka yi masa maraba don dā man duk suna jiransa ne. 41 Sai ga wani mutun mai suna Yayirus, wani shugaban majami’a, ya zo ya faɗi gaban Yesu, ya roƙe shi ya je gidansa. 42 Don yana da ’ya ɗaya tilo, mai shekara misalin sha biyu, tana kuma bakin mutuwa.

Yana cikin tafiya, taro masu yawa na matsatasa, 43 sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma ɓad da duk abin hannunta wajen masu magani, ba wanda kuwa ya iya warkad da ita. 44 Sai ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa. Nan take zubar-jininta ta tsaya. 45 Sai Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Da kowa ya yi musu, sai Bitrus da waɗanda ke tare da shi suka ce, “Maigida, ai taro masu yawa ne su ke tutturarka, suna matsarka.” 46 Amma Yesu ya ce, “An dai taɓa ni, don na ji iko ya fita daga gare ni.” 47 Da matar ta ga dai ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta faɗi a gabansa, ta bayyana a idon duk jama’a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take. 48 Sai ya ce mata, “’Yata, bangaskiyarki ta warkad da ke. ƙi sauka lafiya.”

49 Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami’ar, ya ce, “Ai ’yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahal da Malamin.” 50 Amma da Yesu ya ji haka, sai ya amsa ya ce da shugaban majami’ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.” 51 Da ya isa gidan bai yarda kowa ya shiga tare da shi ba, sai Bitrus da Yohana da Yakubu, da kuma uban yarinyar da uwatata. 52 Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai ba a mace ta ke ba, barci ta ke yi.” 53 Sai suka yi masa dariyar raini, don sun san ta mutu. 54 Shi kuwa da ya kama hannunta, sai yata da murya ya ce, “Yarinya, tashi.” 55 Sai ruhunta ya dawo, nan take ta tashi. Sai ya yi umarni a ba ta abinci. 56 Iyayenta suka yi mamaki. Amma sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.

9

Yesu ya Aiki Manzanninsa

Sai ya tar Sha biyun nan ya ba su ido da izini kan dukkan aljannu, da kuma warkad da cuce-cuce, 2 ya kuma aike su su yi wa’azin Mulkin Allah, su kuma warkad da marasa lafiya. 3 Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko da sanda, ko burgami, ko abinci, ko kuɗi. Kada kuma ku ɗauki taguwa biyu. 4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi. 5 Duk waɗanda ba su yi na’am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.” 6 Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin Bishara, suna warkarwa a ko’ina.

7 To, sai Sariki Hirudus ya ji duk abin da a ke yi, ya kuwa damu ƙwarai, don wasu na cewa Yohana ne aka tasa daga matattu. 8 Wasu kuwa suka ce wai Ilia ne ya bayyana. Wasu kuma suka ce ɗaya daga cijin annabawan dā ne ya tashi. 9 Sai Hirudus ya ce, “Yohana kam na fille masa kai. Wa ke nan kuma da na ke jin irin waɗannan abubuwa game da shi?” Sai ya nemi ganinsa.

Yesu ya Ci da Mutun Dubu Biyar

10 Da Manzanni suka dawo, sai suka gaya wa Yesu abin da suka yi. Sai ya tafi da su a keɓe zuwa wani gari wai shi Baitsaida. 11 Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkad da masu bukatar warkewa. 12 Da rana ta fara sunkuyawa, sai Sah biyun nan suka matso, suka ce masa, “Sai ka sallami taron, su shiga ƙauyuka da karkara na kurkusa, su sauka, su nemi abinci, don inda mu ke ba mutane.” 13 Amma sai ya ce musu, “Ku ku ba su abinci mana.” Suka ce, “Ai abin da mu ke da shi bai fi burodi biyar da kifi biyu ba, sai dai in mu je mu sayo wa dukkan jama’an nan abinci ne.” 14 Don maza sun yi wajen dubu biyar. Sai ya ce da almajiransa, Ku ce da su su zazzauna ƙungiya-ƙungiya, kowace ƙungiya misalin hamsin-hamsin.” 15 Haka kuwa suka yi, suka sa dukkaninsu suka zazzauna. 16 Da ya ɗauki burodi biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran suna kai wa jama’a. 17 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har aka kwashi ragowar gutattsrin, kwando goma sha biyu.

Babbar Bayyana Yarda ga Yesu

18 Wata rana yana addu’a shi kaɗai, almajiransa kuwa na tare da shi. Sai ya tambaye su, ya ce, “Wa mutane ke cewa na ke?” 19 Suka amsa suka ce, “Yohana Maibabtisma, wasu kuwa, Ilia, wasu kuma, ɗaya daga cikin annabawan dā ne ya tashi.” 20 Ya ce musu, “Amma ku fa, wa ku ke cewa na ke?” Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Almasihu na Allah.” 21 Sai ya kwaɓe su gaya matuƙa kada su gaya wa kowa wannan magana.

Yesu ya yi Faɗin Mutuwarsa da Tashinsa

22 Ya ce, “Lalle ne Ɗam Mutun yă sha wuya iri-iri, shugabanni da manyan malamai da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”

23 Sai ya ce da dukansu, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya shafa jini a wuyansa kowace rana, yă bi ni. 24 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, tattalinsa ya yi. 25 Me mutun ya amfana in ya sami duniya duka kan hasarar ransa, ko a bakin ransa? 26 Duk wanda zai guje mini, ya kuma guje wa maganata, Ɗam Mutun ma sai ya guje masa sa’ad da ya zo cikin ɗaukakarsa, da kuma ɗaukakar Uba, da ta mala’iku tsarkaka. 27 Amma hakika ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Mulkin Allah.”

Kamanninsa ya Sake a kan Dutse

28 Bayan misalin kwana takwas da yin maganan nan, sai Yesu ya ɗauki Bitrus da Yohana da Yakubu, ya hau wani dutse don yin addu’a. 29 Yana cikin yin addu’a, sai kamatasa ta sake, tufafinsa kuma suka yi fari fat, har suna ɗaukar ido. 30 Sai ga mutum biyu na magana da shi, Musa da Iliya. 31 Sun bayyana da ɗaukaka, suna zancen ƙauratasa ne, wadda ya ke gabannin yi a Urushalima. 32 Sai kuma Bitrus da waɗanda ke tare da shi, barci ya cika musu ido, arnma da suka farka sosai, sai suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da. shi. 33 Mutanen nan na rabuwa da shi ke nan, sai Bitrus ya ce da Yesu, “Maigida, ya kyautu da mu ke nan wurin. Mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta lliya.” Bai ma san abin da ya ke faɗa ba. 34 Yana cikin faɗar haka sai wani gajimare ya zo ya rufe su. Da kuma gajimaren ya lulluɓe su sai suka tsorata. 35 Sai aka ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana Zaɓaɓɓena. Ku saurare shi!” 36 Bayan muryar ta yi magana, sai aka ga Yesu shi kaɗai. Sai suka yi shiru. A kwanakin nan kuwa ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.

37 Washegari da suka gangaro daga kan dutsen, sai wani babban taro ya tarye shi. 38 Sai ga wani daga cikin taron ya ƙara, ya ce, “Ya Shugaba, ina roƙonka ka dubi ɗana da idon rahama, shi ke nan gare ni. 39 Ga shi aljani ya kan hau shi, ya kan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin kan buge shi, jikinsa na rawa, har bakinsa na kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi da kyau. 40 Na kuwa roƙi almajiranka su fid da shi, amma sun kasa.” 41 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan iya zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗan naka nan.” 42 Yana cikin zuwa sai aljanin ya buge shi da kyau, jikinsa na rawa. Amma sai Yesu ya tsauta wa baƙin aljanin, ya warkad da yaron, ya kuma mayar wa da ubansa shi. 43 Duk aka yi mamakin girman ikon Allah.

Tun dukkansu na mamakin duk abubuwan da ya ke yi, sai ya ce da almajiransa, 44 “Maganan nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗam Mutun ga mutane.” 45 Amma ba su fahinci maganan nan ba, an kuwa ɓoye musu ita ne don kada su gane, su kuwa suna tsoron tambayarsa wannan magana.

Gargadi kan Tawali’u

46 Sai musu ya tashi a tsakaninsu kan ko wanene babbansu. 47 Amma da Yesu ya gane tunanin zuciyarsu, sai ya kama hannun wani ƙaramin yaro ya ajiye shi kusa da shi. 48 Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai wanda ya ke mai ƙasƙanci a cikinku shi ne babba.”

49 Sai Yohana ya amsa ya ce, “Maigida, mun ga wani na fid da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya bimmu.” 50 Amma sai Yesu ya ce masa, “Kada ku hana shi. Ai duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

51 Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, sai ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima. 52 Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa su shisshirya masa. 53 Amma Samariyawa suka, ƙi karɓarsa, don niyyarsa duk a kan Urushalima ta ke. 54 Da almajiransa Yakubu da Yohana suka ga haka, sai suka ce, “Ya Ubangiji, ko kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama ta lashe su?” 55 Amma sai ya juya, ya tsawata musu. 56 Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauyen.

Masu Son Zama Almajiransa a kan wata Ka’ida

57 Suna cikin tafiya a kan hanya, sai wani mutun ya ce masa, “Zan bi ka duk inda za ka je.” 58 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramunansu, tsuntsaye kuma da wurin kwanansu, amma Ɗam Mutun ba shi da wurin shaƙatawa.” 59 Ya kuma ce da wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je im binne tsohona.” 60 Sai Yesu ya ce da shi, “Bari matattu su binne ’yan’uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanad da Mulkin Allah.” 61 Wani kuma ya ce, “Ya Ubangiji, zan bi ka, amma ka bar ni tukuna in yi wa mutanen gida bankwana.” 62 Yesu ya ce masa, “Ba mai huɗa da garmar shanu, ya ke kuma waiwaye, da zai dace da Mulkin Allah.”

10

Yesu ya Aiki Masu Bishara Saba’in

Bayan wannan sai Ubangiji ya zaɓi wasu mutun saba’in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane garin da kowane wurin da shi kansa za shi. 2 Ya ce musu, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbin ya turo masu girbi, su yi masa girbi. 3 To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar ’yan tumaki a cikin kuraye. 4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya. 5 Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, ‘Salama alaikum mutanen gidan nan!’ 6 In kuma da mai son aminci a gidan, to, fatanku na aminci zai tabbata a gare shi. In kuwa babu, sai ya komo muku. 7 Kuma ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, don ma’aikaci ya cancanci ladansa. Kada ku riƙa canjin masauƙi. 8 Duk garin da kuka shiga, in an yi na’am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku. 9 Ku warkad da marasa lafiyan da ke cikinsa, ku kuma ce da su, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’ 10 Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na’am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa, 11 ‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafummu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku san cewa Mulkin Allah ya kusato.’ 12 Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.

13 “Kin shiga uku Korasinu! Kin shiga uku Baitsaida! Da mu’ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Sur da Saida, da tuni sun tuba, sun zauna saye da tsumma, suna hurwa da toka. 14 Amma a Ranar Shari’a, za a fi haƙurce wa Sur da Saida a kanku. 15 Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaukaka ƙi Sama kuwa? La! ƙasƙantad da ke za a yi har Hades.

16 “Duk mai sauraronku, ni ya ke saurare. Mai ƙinku kuma, ni ya ke ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”

Saba’in ɗin sun Dawo

17 Sai kuma saba’in ɗin nan suka komo da farinciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aIjannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!” 18 Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walkiya. 19 Ga shi na ba ku ikon taka maciji da kunama, da kuma rinjaye kan dukkan ikon Makiyia, ba kuwa abin da zai cuce ku ko kaɗan. 20 Duk da haka, kada ku yi farincikin aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farincikin an rubuta sunayenku a Sama.”

Uba ya Mallaka Masa Kowane Abu

21 A wannan lokacin sai Ruhu Tsattsarka ya cika shi da farinciki matuƙa, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, don ka ɓoye waɗannan al’amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga sabon shiga. Hakika na gode maka ya Uba, don wannan shi ne nufinka na alheri. 22 Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wanene ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wanene Uban sai dai Ɗan , da kuma wanda Ɗan ya so ya buɗa wa.”

23 Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce da su a keɓance, “Albarka tā tabbata ga idanun da suka ga abin da kuka gani. 24 Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so ganin abin da ku ke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da ku ke ji, amma ba su ji ba.”

Basamariye na Kirki

25 Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Ya Shugaba, me zan yi in gaji rai madawwami?” 26 Yesu ya ce masa, “Me ke rubuce a cikin Attaura? Yaya ka ke karantawa?” 27 Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.” 28 Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka riƙa yin haka, sai ka rayu.”

29 Shi kuwa mutumin, don yana son gira, sai ya ce da Yesu, “To, wanene ɗan’uwan nawa?” 30 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutun ne ya tashi daga Urushalima za shi Yariko. Sai ’yam-fashi suka faɗa shi, suka tuɓe shi, suka yi masa mugun duka, suka tafi suka bar shi rai ga Allah. 31 Daganan sai ya zamana wani malami ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zage ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa. 32 Haka kuma wani Balawiye, da ya iso wurin ya gan shi, sai shi ma ya zage ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa. 33 Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda ya ke. Da ya gan shi, sai tausayi ya kama shi, 34 ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan inabi. Sa’an nan ya ɗora shi a kan dabbarsa, ya kai shi masauƙi, ya yi ta jiyyarsa. 35 Washegari sai ya ɗebo dinari biyu ya ba maigidan, ya ce, ‘Ka yi jiyyarsa, duk kuma abin da ka ɓatar bayan wannan, in na dawo sai im biya ka.’ 36 To, a cikin ukun nan, wa ka ke tsammani ya zama ɗan’uwa ga wanda ’yam-fashin suka faɗa wa?” 37 Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa tausayin.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma ka je ka riƙa yin haka.”

Labarin Marta da Maryamu

38 Suna cikin tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta sauke shi a gidanta. 39 Tana kuwa da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron maganatasa. 40 Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ka kula ba, ’yar’uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana. 41 Amma sai Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, haba Marta hankalinki a tashe ya ke, kina kuma damuwa kan abu da yawa. 42 Ai abu ɗaya ne ya wadatar. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”

11

Ya Koya wa Almajiransa Yin Addu’a

Wata rana Yesu na addu’a a wani wuri. Bayan ya gama sai wani a cikin almajiransa ya ce masa, “Ya Ubangiji, koya mana addu’a mana, kamar yadda Yohana ya koya wa almajifansa.” 2 Sai ya ce musu, “In kuna addu’a, ku ce,

“Ya Uba, a keɓe sunanka a tsarkake. Mulkinka yi bayyana. 3 Ka ba mu abincin yau da kullum. 4 Ka yafe mana zunubammu, don mu ma muna yafe wa duk mai yi mana laifi. Kada ka kai mu ga gwaji.”

5 Kuma ya ce musu, “Misali, wanenenku in yana da amini, in ya je wurinsa da tsakad dare ya ce masa, ‘Wāne, ranta mini burodi uku mana, 6 ga shi wani abokina matafiyi ya sauka a wurina yanzu, ba ni kuwa da abincin da zan ba shi’, 7 sa’an nan aminin yă amsa masa daga ciki yă ce, ‘Kada ka dame ni, ai an ƙulle ƙofa, da ni da ’ya’yana duk mun kwanta, ba zan iya tashi im ba ka wani abu ba’? 8 Ina gaya muku, ko da ya ke ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa ya ke bukata. 9 Ina dai gaya muku, Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta buga ƙofa, za a kuwa buɗe muku. 10 Duk wanda ya roƙa, a kan ba shi, mai nema na tare da samu, wanda ya buga ƙofa kuma za a buɗe masa. 11 Wane uba ne a cikinku, da ɗansa zai roƙe shi burodi, ya ba shi dutse? Ko ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji? 12 Ko kuwa ya roƙe shi kwai, ya ba shi kunama? 13 To, ku da ku ke miyagu ma kuka san yadda za ku ba ’ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da Ruhu Tsattsarka ga masu roƙonsa?”

Fid da Aljannu da Ikon Allah

14 Wata rana Yesu na fid da beben aljani, da aIjanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki. 15 Amma wasunsu suka ce, “Ai da ikon Ba’alzabul sarkin aIjamm ya ke fid da aljannu”. 16 Wasu kuwa, don su gwada shi, sai suka nemi ya nuna musu wata alama daga Sama. 17 Shi kuwa da ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu kan gāba, zai lalace. Haka kuma in gida ya rabu kan gāba, zai baje. 18 In kuma Shaiɗan ya rabu kan gaba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi kun ce da ikon Ba’alzabul na ke fid da aljannu. 19 In kuwa da ikon Ba’alzabul na ke fid da aljannu, to, ’ya’yanku fa da ikon wa su ke fitarwa? Saboda haka su ne za su zama alkalanku. 20 Ni kuwa in da ikon Allah na ke fid da aljannu, ashe Mulkin Allah ya aukam muku ke nan. 21 In ƙato ya yi ɗamara sosai, yana tsaron gidansa, kayansa sun tsira. 22 In kuwa wanda ya fi shi ƙarfi ya fāɗa masa, kuma ya rinjaye shi, sai ya ƙwace duk makamansa da ya dogara da su, ya kuma rarraba gammar. 23 Wanda ba nawa ba ne, gāba ya ke yi da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa ya ke yi.

24 “Baƙin aljan, in ya rabu da mutun, sai ya bi ta wurare marasa ruwa, neman hutu. In ya rasa, sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ 25 Sa’ad da kuwa ya koma gidan sai ya tarad da shi shararre, kawatacce. 26 Daganan sai ya je ya ɗebo wasu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutun ya kasa kasau ke nan.”

27 Yana faɗar haka sai wata mace a cikin taron ta daga murya ta ce masa, “Albarka tā tabbata ga wadda ta haife ka, wadda ka sha mamanta.” 28 Amma sai ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda ke jin Maganar Allah, su ke kuma kiyaye ta.”

29 Da taro ya riƙa karuwa wurinsa, sai ya fara cewa, “Wannan zamani mugun zamani ne. Suna neman ganin wata alama, amma ba wata alamad da za a nuna musu sai dai ta Yunusa. 30 Wato kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Ninawi, haka kuma Ɗam Mutun zai zame wa zamanin nan. 31 A Ranar Shari’a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta kā da su. Don ta zo ne daga bangon duniya tă ga hikimar Sulaimanu. Ga kuma wanda ya fi Sulaimanu a nan. 32 A Ranar Shari’a mutanen Ninawi za su tashi tare da mutanen zamanin rian su kā da su. Don sun tuba saboda wa’azin Yunusa. To, ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.

33 “Ba mai kunna fitila ya ɓoye ta a rami, ko ya rufe ta da masaki.

A’a, sai dai ya ɗora ta a kan madorinta, don masu shiga su ga hasken. 34 Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka sai ya cika da haske. In kuwa idonka da lahani, sai jikinka ya cika da duhu. 35 Saboda haka sai ka lura ko hasken da ke gare ka duhu ne. 36 In kuwa duk jikinka ya cika da haske, ba inda ke da duhu, ai duk sai ya haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila ke haskaka ka.”

Yesu a Gidan Bafarisiye

37 Yesu na cikin magana, sai wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Sai ya shiga ya zauna cin abincin. 38 Sai Bafarisiyen ya yi mamakin ganin Yesu zai ci abinci ba da fara wanke hannu ba. 39 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, ku kan wanke bayan kwarya da akushi, amma ta ciki sai zalunci da mugunta. 40 Ku marasa azanci! Ashe wanda ya yi bayan, ba shi ya yi cikin ba? 41 Gara ku tsarkake cikin, sa’an nan ne komai zai tsarkaka a gare ku.

42 “Kun shiga uku Farisiyawa! Ga shi kuna fid da zakkar na’a-na’a da ƙarƙashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da ya da waɗancan ba. 43 Kun shiga uku Farisiyawa! Ga shi kuna son mafifitan mazaunai a majami’u, da kuma gaisuwa a kasuwa. 44 Kun shiga uku! Kuna kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane ke takawa kan rashin sani.”

45 Sai wani a cikin masana Attaura ya amsa masa ya ce, “Malan, fadar haka fa mu ma ai ka ci mutuncinunu.” 46 Sai Yesu ya ce, “Ku ma masana Attaura, kun shiga uku! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku kuwa ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu! 47 Kun shiga uku! Don kuna gina gubbobin annabawan da kakanninku suka kashe. 48 Wato, ku shaidu ne a kan kun yarda da ayyukan kakanninku; ga shi su ne fa suka kashe su, ku kuwa wai har kuka gina musu gubbobin! 49 Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da masu yin faɗin Maganar Allah da manzanni, su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa wasu,’ 50 don alhakin jinin dukkan annabawa da aka zubar tun farkon duniya, a bi shi kan mutanen wannan zamani, 51 wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin Wurin Baiko da Wuri Tsattsarka. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi kan mutanen wannan zamani. 52 Kun shiga uku masana Attaura! Don kun ɗauke mabuɗin ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, kun kuma hana. masu son shiga shiga.”

53 Da ya fito daga wurin, sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara matsa masa ƙwarai, suna tsokanarsa ya yi maganar abubuwa da yawa, 54 suna haƙonsa su burma shi cikin maganarsa.

12

Ya yi wa Almajiransa Gargadi iri iri

Sa’an nan kuwa da dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, da farko sai ya yi magana da almajiransa ya fara cewa, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato makirci 2 Ba abin da ke rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da ke ɓoye da ba za a bayyana ba. 3 Don haka komai kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a turaka, za a yi shelarsa daga kan soraye.

4 “Ya ku masoyana, ina dai gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan mutun, kuma bayan sun kashe, ba abin da za su iya yi. 5 Amma zan gaya muku wanda za ku ji tsoro. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, ya ke da ikon jefawa Jahannama. Hakika, ina gaya muku, shi za ku tsorata! 6 Ashe ba gwara biyar ne kwabo biyu ba? Ko ɗayarsu kuwa Allah bai manta da ita ba. 7 Kai! ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye ya ke. Kada ku ji tsoro. Ai martabarku ta fi ta gwara masu yawa.

8 “Ina kuma gaya muku, kowa ya bayyana yarda gare ni a gaban mutane, Ɗam Mutun ma zai bayyana yarda gare shi a gaban mala’ikun Allah. 9 Wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musun saninsa a gaban mala’ikun Allah. 10 Kowa ya kushe wa Ɗam Mutun, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Tsattsarka, ba za a gafarta masa ba. 11 Sa’ad da suka kai ku gaban majami’u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi; ko kuwa abin da za ku faɗa. 12 Don Ruhu Tsattsarka zai koya muku abin da. ya kamata ku faɗa a lokacin.”

13 Sai wani a cikin taron ya ce da shi, “Ya Shugaba, kă ce da ɗan’uwana a raba gadon da ni.” 14 Amma sai Yesu ya ce masa, “Haba kai kuwa, wa ya sa ni in zame muku alkali, ko in raba muku gado?” 15 Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne mutum ba.” 16 Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka ƙwarai. 17 Sai ya ce a ransa, ‘To, ƙaƙa zan yi? Don ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’ 18 Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe taskokina, in gina wasu manya manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki. 19 Zan kuma ce a raina, Kai, lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. In sau jiki, in yi ta ci, in yi ta sha ina shagali.’ 20 Amma sai Allah ya ce da shi, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada na wa za su zama?’ 21 Haka wanda ya tanadar wa kansa dukiya ya ke, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”

Misalai da Hankaki da Furanni

22 Sai ya ce da almajiransa, “Don haka ina gaya muku, kada ku damu batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura. 23 Don rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 Ku dubi dai hankaki! Ai ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah na cishe su. San nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye! 25 Wanene a cikinku don damuwatasa zai iya ƙara ko da taki ga tsawon rayuwatasa? 26 To, im ba za ku iya yin ƙaramin abu ya wannan ba, dom me ku ke damuwa da sauran? 27 Ku dubi dai furanai yadda su ke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka ina gaya muku, ko Sulaimanu ma shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba. 28 To, ga shi Allah na kawata tsire tsiren jeji ma haka, waɗanda yau su ke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29 Ku ma kada ku damu kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi taraddadi. 30 Ai al’umman dunya na ta neman duk irin waɗannan abubuwa, ku kuwa Ubanku ya san kuna bukatarsu. 31 Sai dai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, sai a ƙara muku da waɗannan abubuwan kuma.

lnda Dukiyarka ta ke nan Ranka ma ya ke

32 “Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, don Ubanku na jin daɗin ba ku rabo cikin Mulkin. 33 Ku sai da mallakarku, ku bayar taimako. Ku sama wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato dukiya marar yankewa ke nan a Sama, inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓata 34 Don kuwa inda dukiyarka ta ke, a nan ranka ma ya ke.

35 “Ku yi ɗamara, fitilunku na kunne. 36 Ku dai zama kamar mutane masu jiran ubangijinsu ya dawo daga gidan biki, da zarar ya buga ƙofa su buɗe masa. 37 Albarka tā tabbata ga bayin nan waɗanda ubangijin nan da zuwansa zai same su a faɗake. Hakika, ina gaya muku, zai yi ɗamara, ya ce su zauna cin abinci, sannan ya bi kan kowannensu yana yi masa hidima. 38 In kuwa ya zo da tsakad dare ne, ko kuwa bayan tsakad dare, ya same su a faɗake, bayin nan masu albarka ne. 39 Amma dai ku san cewa, da maigida zai san lokacin da ɓarawo zai zo, da sai ya zauna a faɗake, ya hana a shigam masa gida. 40 Ku ma sai ku zauna a kan shiri, don a lokacin da ba ku zata ba Ɗam Mutun zai zo.”

41 Sai Bitrus ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne ka ke faɗa wa wannan misali, ko kuwa na kowa da kowa ne?” 42 Ubangiji ya ce, “Wanene amintaccen wakilin nan mai hikima, da ubangijinsa zai ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari? 43 Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangiiinsa ya dawo zai samu yana yin haka. 44 Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukkan mauakatasa. 45 In kuwa bawan nan ya ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ sa’an nan ya soma dukan barorin, maza da mata, ya shiga ci da sha bar yana buguwa, 46 ai ubangijin wannan bawan zai zo a ranad da bai zata ba, kuma a lokacin da bai sani ba, yă farfasa masa jiki da bulala, ya haɗa shi da marasa amana. 47 Bawan nan kuma wanda ya san nufin ubangijinsa, bai yi shiri ba, bai kuma bi nufinsa ba, za a yi masa matsanancin duka. 48 Wanda kuwa bai san nufin ubangiiinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa duka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka ɗanka wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.

49 “Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru! 50 Ina da babtismad da za a yi mini, na kuwa dokanta ƙwarai bar a yi mini ita! 51 Kuna tsammani na zo ne in kawo aminci duniya? A’a, ina gaya muku, sai dai rabuwa. 52 Nan gaba a gida guda mutum biyar za su kasu biyu, uku na gāba da biyu, biyu kuma na gāba. da uku. 53 Ta baka za su rabu. Uba na gāba da ɗansa, ɗan kuma na gāba da ubansa, uwa na gāba da ’yatata, ’yar kuma na gāba da uwatata, suruka na gāba da matar danta, matar ɗan kuma na gāba da surukatata.

54 Ya kuma ce da taron, “In kun ga girgije na tasowa daga yamma, nandanan ku kan ce, ‘Za a yi ruwa’. Sai kuwa a yin. 55 In kuwa kun ga iskar kudu na busowa, ku kan ce, ‘Za a yi matsanancin zafi’. Sai kuwa a yin. 56 Munafukai! Kuna iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma me ya sa ba ku iya gane alamomin zamanin nan ba? 57 Me ya sa ku da kanku ma ba kwa iya rarrabewa da abin da ke daidai? 58 Misali, in kuna tafiya gaban shari’a da mai ƙararka, sai ka yi ƙoƙari ku yi jiyayya da shi tun a kan hanya, don kada ya ja ka gaban alkali, alkali kuma ya miƙa wa ɗandoka, ɗandoka kuma ya jefa ka kurkuku. 59 Ina gaya maka, lalle ba za ka fita daga nan ba, sai ka biya duka, ba sauran ko anini.”

13

Nan take sai waɗansu da ke wurin suka ba shi labarin Galalawan da Bilatus ya sa aka kashe, har jininsu ya gauraya da na yankan da suka yi. 2 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galilawan sun fi duk sauran GaIiIawa zunubi ne don sun sha wannan azaba? 3 Ina gaya muku, ba haka ba ne! In kuwa ba kun tuba ba, duk za ku halaka kamarsu. 4 Ko kuwa sha takwas ɗin nan da hasumiya ta fado a kansu a Siluwam ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne? 5 Ina gaya muku, ba haka ba ne! In kuwa ba kun tuba ba, duk za ku halaka kamarsu.”

Ɓaure Marar ’ya’ya

6 Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutun na da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman ’ya’ya, amma bai samu ba. 7 Sai ya ce da mai kula da garkar, ‘Ka ga, yau shekara uku ke nan na ke zuwa neman ’ya’yan wannan ɓaure, amma ba na samu. A sare shi. Ƙaƙa zai tsare wuri a banza?’ 8 Sai ya amsa masa ya ce, ‘Ubangijina, bar shi dai bana ma, in yi masa kaftu, in zuba masa taki. 9 In ya yi ’ya’ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’”

10 Wata rana yana koyarwa a wata majami’a ran Asabar, 11 sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa. 12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce da ita, “Uwargida, an raba ƙi da rashin lafiyarki.” 13 Sai ya ɗora mata hannu, nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah. 14 Amma sai shugaban majami’a ya ji haushi wai don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce da jama’a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkad da ku, ba ran Asabar ba. 15 Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe kowannenku ba ya kwance takarkarinsa ko jakinsa a turke, ya kai shi ban ruwa ran Asabar? 16 Ashe bai kamata matan nan ’yar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure yau shekara goma sha takwas, a kwance ta daga wannan ƙuƙumi a ran Asabar ba?” 17 Da ya faɗi haka sai duk abokan adawarsa suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farinciki da abubuwan al’ajabin da ya ke yi.

18 Sai Yesu ya ce, “Da me Mulkin Allah ke kama? Da me kuma zan kwatanta shi? 19 Kamar ƙwayar mastad ya ke, wadda wani mutun ya je ya shuka a lambunsa, kuma ta girma ta zama bishiya, har tsuntsaye suka kwana a rassanta.”

20 Ya kuma sake cewa, “Da me zan kwatanta Mulkin Allah? 21 Kamar yisti ya ke wanda wata mace ta ɗauka ta cuda da mudu uku na garin alkama, bar duk garin ya game da yistin.”

Shiga ta Kunkuntar Ƙofa

22 Sai ya ɗauki hanyarsa ta cikin birane da ƙauyuka, yana koyarwa, yana dosar Urushalima. 23 Sai wani ya ce masa, “Ya Ubangiji, waɗanda za su sami ceto kam kaɗan ne?” Sai ya ce musu, 24 “Ku yi faman shiga ta ƙunƙuntar ƙofa. Don ina gaya muku, mutane da yawa za su nemi shiga, amma ba za su iya ba. 25 In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje kuna buga ƙofar, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, buɗe mana mana,’ sai ya amsa muku ya ce, ‘Ku kam ban san daga inda ku ke ba.’ 26 Sa’an nan za ku fara cewa, ‘Ai mun ci mun sha a gabanka, har ka koyar a titi-titimmu.’ 27 Shi kuwa sai ya ce, ‘Ina dai gaya muku, ku kam ban san daga inda ku ke ba. Ku tafi daga wurina, dukkanku, ku masu aikin rashin gaskiya!’ 28 Sa’ad da kuka ga Ibrahim da Isiyaku, da Yakubu, da dukkan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da gama haƙora 29 Za a zo daga gabas da yamma, kudu da arewa, a zauna cin abinci a Mulkin Allah. 30 Ga shi fa, waɗansu da ke na ƙarshe za su zama na farko, wasu kuwa da ke na farko za su koma na ƙarshe.’

31 Nan take sai wasu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai sa ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus na son kashe ka.” 32 Sa ya ce musu, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, ‘Ka ga, yau ina fid da aliannu, ina warkarwa, gobe ma haka, a rana ta uku kuwa zan gama aikina. 33 Duk da haka lalle ne in ci gaba da tafiyata yau da gobe da kuma jibi, don kuwa bai dace a kashe annabi ba im ba a cikin Urushalima ba.’

Yesu ya yi wa Urushalima Jaje

34 “Wohoho mutanen Urushalima! Woho mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko gare ku! San nawa ne na so in tattaro ku kamar yadda kaza ke tattara ’yan tsakinta cikin fikafikanta, amma kun ƙi! 35 Ga shi, am bar muku gidanku a yashe! Ina kuwa gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba sai ran da kuka ce, ‘Yabo ya tabbata ga Maizuwa da sunan Ubangiji.’”

14

Ya Warkar ran Asabar

Wata ranar Asabar, sai ya shiga gidan wani shugaba na Farisiyawa cin abinci, mutane kuwa na haƙonsa. 2 Sal ga wani mai ciwon fara a gabansa. 3 Yesu ya amsa ya ce da masana Attaura da Farisiyawa, “Ya halatta a warkar ran Asabar ko kuwa?” 4 Sal suka yi shiru. Sal Yesu ya riƙe shi, ya warkad da shi, ya kuma sallame shi. 5 Sa’an nan ya ce musu, “Misali, wanene a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya faɗa rijiya ran Asabar, ba zai fid da shi nandanan ba?” 6 Sal suka kasa ba da amsa a kan waɗannan abubuwa.

7 To, ganin yadda waɗanda aka gayyato sun zaɓi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali ya ce, 8 “In an gayyace ka biki, kada ka zauna a mazaunin alfarma, kada ya zamana an gayyato wani wanda ya fi ka daraja, 9 wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce da kai, ‘Ba mutumin nan wuri.’ Sa’an nan ka tashi tsamo-tsamo ka koma mazauni mafi ƙasƙanci. 10 Amma in an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi ƙasƙanci, don in mai gayyar ya zo, sai ya ce da kai, ‘Aboki, hawo nan mana.’ Ka ga sai a girmama ka a gaban dukkan abokan cinka. 11 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantad da shi. Mai ƙasƙantad da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”

12 Ya kuma ce da mai gayyar, “In za ka kira mutun cin abinci ko dina, kada ka riƙa kiran abokanka kawai, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko maƙwautanka masu arziki, kada su ma su gayyace ka, su sāka maka. 13 Amma in za ka kira dina, sai ka gayyato gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi, 14 za ka kuwa sami albarka, da ya ke ba su da hanyar saka maka. Sal kuwa a saka maka ranar tashin masu gaskiya.”

Cin Abinci a Mulkin Allah

15 Da jin haka, sai ɗaya daga cikin abokan cinsa ya ce da shi, “Albarka tā tabbata ga wanda zai ci abinci a Mulkin Allah.” 16 Amma sai ya ce masa, “Wani mutun ne ya shirya babbar dina ya gayyaci mutane da yawa. 17 Da lokacin dina ya yi, sai ya aiki bawansa ya ce da waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, duk an shirya komai.’ 18 Sal dukkansu baki ɗaya suka fara kawo hanzari. Na farko ya ce masa, ‘Na sayi gona, lalle ne in je in gano ta. Ina roƙonka ka ɗauke mini.’ 19 Sai wani kuma ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma, za ni in gwada su. Ina roƙonka ka ɗauke mini.’ 20 Wani kuma ya ce, ‘Na yi aure, don haka, ba zan iya zuwa ba.’ 21 Sai bawan ya dawo ya ba ubangijinsa labari. Sai maigidan ya yi fushi, ya ce da bawansa, ‘Fita maza, ka bi titi-titin birni da kwararo kwararo, ka ɗebo gajiyayyu, da musakai, da makafi, da guragu.’ 22 Sai bawan ya ce, ‘Ya ubangiji, abin da ka umarta duk an gama, amma har yanzu da sauran wuri.’ 23 Sai ubangijin ya ce da bawan, ‘Fita, ka bi gwadabe-gwadabe da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana. 24 Ina gaya muku, ba ko ɗaya daga cikin mutanen da na gayyata a dā da zai ɗanɗana abincin dinata.’ “

Iya Zama Almajirin Yesu

25 To, taro masu yawan gaske kuwa na binsa. Sai ya juya ya ce musu, 26 “Duk mai zuwa wurina, im bai ƙaunata a kan ubansa, da uwatasa, da matatasa, da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa maza da mata, bar ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27 Duk wanda bai shafa jini a wuyansa, ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28 Misali, in wani daga cikinku na son gina soron bene, da fari ba sai ya zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba, ya ga ko yana da isassun kuɗin da za su ƙare shi? 29 Kada ya zamana bayan ya sa harsashin ginin, yă kasa gamawa, har duk waɗanda suka gani, su fara yi masa ba’a, 30 su riƙa cewa, ’A! Ka ga mutumin nan ya fara gini, amma ya kasa gamawa!’

31 “Ko kuwa wane sarki ne, in za shi yaƙi da wani sarki, da fari ba sai ya zauna ya yi shawara, ya ga ko shi mai mutun dubu goma zai iya ƙarawa da mai dubu ashirin ba? 32 In kuwa ba zai iya ba, to, tun wancan na nesa sai ya aiki jakadu su tambayo sharuɗan amana. 33 Haka ma kowannenku im bai saki duk abin da ya mallaka ba, ba zai iya zama almajirina ba.

34 “Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sane, da me za a daɗaɗa shi? 35 Ba shi da wani amfani a gona, ko a taki, sai dai a zubar kawai. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

15

To, sai duk masu karɓar haraji da masu zunubi suka yi ta matsowa wurinsa su saurare shi. 2 Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka riƙa gunaguni suna cewa, “Haba! Wannan mutun na karɓar masu zunubi, har ma tare su ke cin abinci!”

Ɓatattun Tumaki

3 Sai ya ba su wannan misali ya ce, 4 “In waninku na da tumaki ɗari, ɗayarsu ta ɓace, to, ba sai ya bar casa’in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta ɓatan har ya same ta ba? 5 In kuwa ya same ta, sai ya saɓo ta a kafada, yana mai farinciki. 6 In ya dawo gida, sai ya tara abokansa da makwauta ya ce da su, ‘Ku taya ni farinciki, don na samo tinkiyata da ta ɓata 7 Ina dai gaya muku, haka kuma za a yi farinciki a Sama a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan masu gaskiya casa’in da tara waɗanda ba sai sun tuba ba.

Ɓataccen Kudi

8 “Ko kuwa wace mace ce in tana da kuɗin azurfa guda goma, in ta ya da ɗaya, ba sai ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nacin nemansa, har ta same shi? 9 In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da makwauta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farinciki, don na sami kuɗin nan da na yar. 10 Haka na ke gaya muku, abin farinciki ne ga mala’ikun Allah im mai zunubi guda ya tuba.”

Labarin Almubazzarin Ɗa

11 Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai ’ya’ya biyu maza. 12 Sai ƙaramin ya ce da ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gado.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa. 13 Bayan ’yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattaro duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa wata ƙasa mai nisa. A nan ya fallasad da kayansa wajen masha’a. 14 Da ya ɓad da komai kakat, sai aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara. 15 Sai ya je ya raɓu da wani ɗanƙasar, shi kuwa ya tura shi makiyaya kiwon alade. 16 Har ma ya so ya cika cikinsa da ’ya’yan gabaruwar gabas da alade ke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu. 17 Amma da ya taro hankalinsa sai ya ce, ‘Kaito! Nawa ne daga cikin barorin ubana da abinci ke kamar ƙasa a gare su! Ga ni nan kuwa yunwa na kisana! 18 Zan tashi, in tafi gun ubana, in ce da shi, “Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. 19 Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin barorinka.” ’ 20 Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana. daga nesa sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbantarsa. 21 Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’ 22 Amma uban sai ya ce da bayinsa, ‘Maza ku kawo ƙanƙararriyar riga mafi kyau, ku sa masa. Ku sa masa zobe da takalma, 23 a kuma kawo kiwataccen ɗam marakin nan, a yanka, mu ci, mu yi ta murna. 24 Don ɗan nan nawa dā ya mutu ne, amma yanzu ya komo; dā ya ɓata amma yanzu an same shi.’ Sai suka yi ta farinciki.

25 “A sa’an nan kuwa babban ɗansa na gona. Yana dawowa, ya yi kusa da gida ke nan, sai ya ji ana kaɗe-kaɗe da raye-raye. 26 Sai ya kira wani baran gidan, ya tambayi dalilin wannan abu. 17 Shi kuwa sai ya ce masa, ‘Ai ɗan’uwanka ne ya dawo, tsohonku ya yanka kiwataccen ɗam marakin nan saboda ya sadu da shi lafiya kalau.’ 28 Amma sai wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Ubansa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa. 29 Amma sai ya amsa wa Ubansa ya ce, ‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ƙetare umarninka ba. Duk da haka kuwa ba ka taɓa ba ni ko da ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina. 30 Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda kuwa ya fallasad da dukiyarka kan karuwai, ga shi ka ya masa kiwataccen ɗam marakin nan!’ 31 Sai uban ya ce masa, ‘Ya dana, ai kullum kana tare da ni, duk abin da ke nawa naka ne. 32 Ai kuwa daidai ne a yi ta murna da farinciki, don ɗan’uwan nan naka dā ya mutu, yanzu kuwa ya komo; dā ya ɓata amma yanzu an same shi.

16

Labarin Wakili Marar Gaskiya

Ya kuma ce da almgiiransa “An yi wani mai arziki da ke da wakili. Sai aka sari wakilin a wurinsa a kan yana fallasar masa da dukiya. 2 Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me na ke ji naka? Kawo littafinka na aiki, don ba sauran ka zama wakilina.’ 3 Sai wakilin ya ce a ransa, Ƙaƙa zan yi, da ya ke maigida zai karɓe wakilci daga hannuna? Ga shi ba ni da ƙarfin noma, ina kuwa jin kunyar raraka. 4 Yauwa! Na san abin da zan yi, don in an fisshe ni daga wakilcin, mutane su karɓe ni a gidajensu.’ 5 Sai ya kira mabartan maigidansa dai dai da dai dai, ya ce da na farko, ‘Nawa maigida ke binka? 6 Ya ce, ‘Garwa ɗari ta mai.’ Sai ya ce masa, ‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubuta hamsin.’ 7 Ya kuma ce da wani, ‘Kai fa, nawa a ke binka? Sai ya ce, ‘Buhu ɗari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.’ 8 Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don ’yan zamani cikin ma’amalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo. 9 Kuma ina gaya muku, ku yi abokai ta dukiya, har ɓacin nata, don sa’ad da ta ƙare su karɓe ku a gidaje masu dawwama.

10 “Wanda ya yi gaskiya a kan ƙaramin abu, mai gaskiya ne a kan babba ma. Wanda kuma ya yi rashin gaskiya a kan ƙaramin abu, marar gaskiya ne a kan babba ma. 11 Im ba ku yi gaskiya da dukiya ɓātacciya ba, wa zai amince muku dukiyar gaskiya? 12 In kuma ba ku yi gaskiya a kan kayan wani ba, wa zai ba ku naku hakkin? 13 Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku iya bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”

14 Farisiyawa kuwa da ya ke masu son kuɗi ne, da jin haka sai suka yi masa tsaki. 15 Sai ya ce musu, Ku ne masu tallan kanku a gaban mutane wai ku masu gaskiya ne. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane ke girmamawa ƙwarai, ai abin ƙyama ne a gun Allah.

16 “Attaura da Littattafan Annabawa na nan har ya zuwa kan Yohana: daga lokacin nan kuwa a ke yin Bisharar Mulkin Allah, kowa kuma na ƙoƙarin firmitsawa ya faɗa ciki. 17 Duk da haka zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, a kan ɗigo ɗaya na Attaura ya sarai.

18 “Kowa ya saki matatasa ya auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya ya yi zina.

Labarin Wani Mai arziki da Li’azaru

19 “Am yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu kawa, yana shan daularsa kowace rana. 20 An kuma ajiye wani miskini a ƙofarsa, mai suna Li’azaru, wanda duk jikinsa miki ne. 21 Shi kuwa na marmarin ya wadatu da sudin mai arzikin nan. Har ma karnuka su kan zo suna lasar miyakunsa. 22 Ana nan sai miskinin nan ya mutu, mala’iku kuma suka ɗauke shi suka kai shi Firdausi wurin Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi. 23 Yana cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li’azaru a Firdausi. 24 Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina mana, ka aiko Li’azaru ya tsoma kan yatsatasa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba na ke sha cikin wannan wuta.’ 25 Amma sai Ibrahim ya ce, Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li’azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu nan daɗi a ke ba shi, kai kuwa kana cikin azaba. 26 Ban da wannan ma duka, tsakanimmu da ku akwai wani gawurtaccen rami mai zurfi, zaunanne, don waɗanda ke son ƙetarewa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ƙetaro wurimmu daga can.’ 27 Sai mai arzikin ya ce, ‘To, ina roƙonka, Baba, ka aike shi gidan ubana, 28 don ina da ’yan’uwa biyar maza, ya je ya yi musu gargaɗi, kada su ma su zo wurin azaban nan.’ 29 Amma sai Ibrahim ya ce, ‘Ai suna da Littattafan Musa da na Annabawa, su saurare su mana.’ 30 Sai ya ce, ‘A’a, Baba Ibrahim, in dai wani daga cikin matattu ya je wurinsu sa tuba.’ 31 Ibrahim ya ce masa, ‘In dai har ba su saurari Littattafan Musa da na Annabawa ba, ko wani ya tashi daga cikin matattu ma, ba za su rinjayu ba.’ “

17

Ku Kula da Kanku

Sai ya ce da almajiransa, “Sanadin ɗaukan zunubi ba shi da makawa, duk da haka wanda shi ne sanadin ya shiga uku! 2 Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku. 3 Ku kula da kanku fa. In ɗan’uwank a ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi. 4 Ko ya yi maka laifi sau bakwai rana ɗaya, sa’an nan ya juyo wurinka sau bakwai ya tubar maka, sai ka yafe shi.

5 Sai Manzanni suka ce da Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya mana.” 6 Ubangiji kuwa ya ce, “In da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da sai ku ce da wannan durumi, ‘Ka ciru, ka dasu cikin teku,’ sai kuwa ya bi umarninku.

7 “Misali, wanene a cikinku in yana da bawa mai yi masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce masa, ‘Maza zo ka zauna, ka ci abinci’? 8 Ashe ba ce masa zai yi, ‘Shirya mini jibi, kuma ka yi ɗamara, ka yi mini hidima, har in gama ci da sha, daga baya kai kuma ka ci ka sha ba’? 9 Yă gode wa bawan nan ne don ya bi umarni? 10 Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da ke wajibimmu kurum.’”

Warkad da Kutare Goma

11 Wata rana, yana cikin tafiya Urushalima, sai ya bi ta kan iyakar ƙasar Samariya da Galili. 12 Yana shiga wani ƙauye ke nan, sai wasu kutare maza guda goma suka tarye shi, suna tsaye daga nesa. 13 Sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Maigida Yesu, ƙi ji tausayimmu.” 14 Da ya gan su, sai ya ce musu, “Ku je wurin malamai su gan ku.” Suna cikin tafiya ke nan sai suka tsarkaka. 15 Ɗayansu kuma ganin an warkad da shi, sai ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi; 16 sai ya faɗi gaban Yesu, yana gode masa. Shi kuwa Basamariye ne. 17 Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran? 18 Ashe ba wanda aka samu ya komo ya ɗaukaka Allah sai baƙon nan kaɗai?” 19 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi ka yi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkad da kai.”

Bayyanar Mulkin Allah

20 Da Farisiyawa suka tambaye shi lokacin bayyanar Mulkin Allah, sai ya amsa musu ya ce, “Ai bayyanar Mulkin Allah ba ganinta a ke yi da ido ba. 21 Ba kuwa za a ce, ‘A! Ga shi nan!’ ko kuwa, ‘Ga shi can!’ ba. Ai Mulkin Allah a tsakaninku ya ke.”

22 Ya kuma ce da almajiran, “Lokaci na zuwa da za ku yi begen ganin rana ɗaya daga cikin ranakun Ɗam Mutun, amma ba za ku gani ba. 23 Za su ce da ku, ‘A! Ga shi nan!’ ko kuwa ‘Ga shi can!’ Kada ku je, kada ku bi su. 24 Kamar yadda walƙiya ta ke wulgawa walai daga wannan bango zuwa wancan, haka ma Ɗam Mutun zai zama a ranar bayyanatasa. 25 Amma lalle sai ya sha wuya iri-iri tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ƙi shi. 26 Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Ɗam Mutun. 27 Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranad da Nuhu ya shiga jirgi, Ruwan Tsufana kuma ya zo, ya hallaka su duka. 28 Haka ma aka yi a zamanin Ludu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine, 29 amma a ranad da Ludu ya fita daga Saduma, sai aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, aka hallaka su duka. 30 Haka kuma zai zama a ranar bayyanar Ɗam Mutun. 31 A ran nan fa wanda ke kan soro, kayansa kuma na cikin gida, kada ya sauko garin ɗaukarsu. Haka kuma wanda ke gona, kada ya juyo. 32 Ku tuna fa da matar Ludu. 33 Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa, adana shi ya yi. 34 Ina gaya muku, a wannan daren za a ga mutum biyu a kan gado ɗaya, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 35 Za a ga mata biyu na niƙa tare, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 36 Za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.” 37 Sai suka amsa masa suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “Inda mushe ya ke, ai a nan ungulu kan taru.”

18

Alkali Marar Tsoron Allah

Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu’a, kada kuma su karai. 2 Ya ce, “A wani gari an yi wani alkali marar tsoron Allah, kuma marar kula da mutane. 3 A garin nan kuwa da wata wadda mijinta ya mutu, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, ‘Ka shiga tsakanina da abokin gabana mana.’ 4 Da fari sai ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, ‘Ko da ya ke ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane, 5 amma saboda gwauruwan nan ta dame ni, sai im bi bayanta, don kada ta gajishe ni da yawan zuwa.’ “ 6 Sai Ubangiji ya ce, Ku ji fa abin da alkalin nan marar gaskiya ya faɗa! 7 Ashe kuma Allah ba zai bi bayan zaɓaɓɓunsa ba, da ke masa kuka dare da rana, ko da ya yi jinkiri wajen bin bayansu? 8 Ina gaya muku, zai bi bayansu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa’ad da Ɗam Mutun ya zo, zai tarad da bangaskiya a duniya ne?”

9 Sai kuma ya ba da misalin nan ga wasu masu amince wa kansu kan su masu gaskiya ne, har suna raina sauran mutane, ya ce, 10 “Wasu mutum biyu suka shiga Ɗakin Ibada yin addu’a, ɗaya Bafarisiye, ɗaya kuma mai karɓar haraji. 11 Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu’a a ransa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka da ya ke ni ba kamar sauran mutane na ke ba, mazambata, marasa gaskiya, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan. 12 Duk mako ina hana kaina abinci sau biyu. Komai na samu na kan fid da zakka.’ 13 Mai karɓar haraji kuwa na tsaye can nesa, ba ya ma ɗaga kai sama, sai dai yana kama ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini rahama, ni mai zunubi!’ 14 Ina dai gaya muku, wannan mutun ya koma gidansa a gafarce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantad da shi. Mai ƙasƙantad da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”

Yesu ya Shafi Ƙananan Yara

15 To, har ma ’yan yaransu su ke kawo masa don ya shafa su. Ganin haka sai almajiransa suka kwaɓe su. 16 Amma sai Yesu ya kira ’yan yara wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai Mulkin Allah na irinsu ne. 17 Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na’am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro ke yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

Hadarin Arziki

18 Sai wani shugaban jama’a ya tambaye shi ya ce, “Ya Shugaba managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?” 19 Sai Yesu ya ce masa, “Dom me ka kira ni managarci? Ai ba wani managarci sai Allah kaɗai. 20 Kā dai san Umarnin nan, ‘Kada ka yi zina, Kada ka yi kisankai, Kada ka yi sata, Kada ka yi shaidar zur, Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ 21 Sai ya ce, “Ai duk na kiyaye waɗannan tun kuruciyata.” 22 Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sai da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, sai ka sami taskar dukiya a Sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.” 23 Da jin haka sai ya yi baƙinciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske. 24 Yesu kuwa da ya gan shi haka sai ya ce, “Kai! Ina ji wa masu dukiya wuyar shiga Mulkin Allah! 25 Ai zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta ƙofar allura, a kan mai arziki ya shiga Mulkin Allah.” 26 Waɗanda suka ji wannan magana, sai suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?” 27 Amma sai Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutun, mai yiwuwa ne a gun Allah.”

Bin Yesu Babbar Riba ce

28 Sai Bitrus ya ce, “To, ai ga shi mun bar mallakarmu, mun bi ka.” 29 Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko matatasa, ko ’yan’uwansa, ko iyayensa, ko kuma ’ya’yansa, saboda Mulkin Allah, 30 sa’an nan ya kasa samun ninkinsu mai yawa a yanzu, a Lahira kuma ya sami rai madawwami.”

Yesu ya Sake Yin Faɗin Mutuwarsa da Tashinsa

31 Sai ya keɓe Sha biyun nan, ya ce musu, “Ga shi za mu Urushalima, kuma duk abin da ke rubuce game da Ɗam Mutun ta hannun annabawa zai tabbata. 32 Gama za a bashe shi ga sauran al’umma, a yi masa ba’a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau. 33 Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.” 34 Amma ko ɗaya ba su fahinci waɗannan abubuwa ba, don zancen nan a ɓoye ya ke gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.

Yesu ya Warkad da Makaho

35 Da ya kusato Yariko, sai ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara. 36 Da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko menene. 37 Sai suka ce masa, “Ai Yesu Banazare ne ke wucewa.” 38 Sai ya daga murya ya ce, “Ya Yesu Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 39 Sai waɗanda ke gaba suka kwaɓe shi ya yi shiru. Amma sai ƙara daga murya ya ke yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya ɗan Dawuda, ka ji tausayina!” 40 Sai Yesu ya tsaya, ya yi umarni a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa kuwa, sai ya tambaye shi, 41 “Me ka ke so in yi maka?” Ya ce, “Ya Ubangiji, in sami gani mana!” 42 Yesu ya ce masa, “Ga nan idonka, bangaskiyarka ta warkad da kai.” 43 Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka sai duk jama’a suka yabi Allah.

19

Labarin Zakiyas

Yesu ya shiga Yariko. Yana ratsa garin, 2 sai wani mutum 19 mai suna Zakiyas, babba ne cikin masu karɓar haraji, mai arziki ne kuma, 3 ya nemi ganin ko wanene Yesu, amma ya kasa ganinsa saboda taro, don shi gajere ne. 4 Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi. 5 Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga kai ya ce masa, “Zakiyas, yi maza ka sauko, domin yau lalle a gidanka zan sauka.” 6 Sai ya yi hanzari ya sauko, ya karɓe shi da murna. 7 Da suka ga haka, duk sai suka yi ta gunaguni, suka ce, “A! A gidan mai zunubi dai ya sauka!” 8 Sai Zakiyas ya miƙe, ya ce da Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.” 9 Yesu ya ce masa, “Yau kam, ceto ya sauka a gidan nan, tun da ya ke shi ma ɗan Ibrahim ne. 10 Don Ɗam Mutun ya zo ne musamman neman abin da ya ɓăta, yd cece shi kuma.”

Bawan Kirki da Mugun Bawa

11 Da suka ji abubuwan nan, kuma da ya ke yana kusa da Urushalima, kuma suna tsammani Mulkin Allah zai bayyana nandanan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, 12 ya ce, “Wani mutum mai asali ya tafi wata ƙasa mai nisa neman sarauta yă dawo. 13 Sai ya kira bayinsa goma, ya ba su fam guda-guda, ya kuma ce musu, ‘Ku yi ta jujjuya su har in dawo.’ 14 Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu bayansa cewa ba sa so ya yi mulki a kansu. 15 Ana nan, da ya samo sarautar ya dawo, sai ya yi umarni a kirawo bayin nan da ya bai wa kuɗin, ya ga ribad da suka ci wajen jujjuyawar. 16 Sai na farko ya zo gabansa, ya ce, ‘Ya ubangiji, fam ɗinka ya jawo fam goma.’ 17 Sai shi kuma ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya kan ƙaramin abu, to, na ba ka mulkin gari goma.’ 18 Sai na biyun ya zo, ya ce, ‘Ya ubangiji, fam ɗinka ya jawo fam biyar.’ 19 Shi kuma ya ce masa, ‘Kai ma na ba ka mulkin gari biyar.’ 20 Wani kuma ya zo, ya ce, ‘Ya ubingiji, ga fam ɗinka nan! Dā ma a mayani na ƙulle shi, na ajiye. 21 Domin ina tsoronka, don kai mutun ne mai tsanani, son banza gare ka, ka kan girbi abin da ba kai ka shuka ba.’ 22 Sai ya ce masa, ‘Kai mugun bawa! Zan maka shari’a bisa abin da ka faɗa da bakinka. Ashe ka san cewa ni mutun ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba? 23 To, in haka ne, dom me ba ka ajiye kuɗin nawa a banki ba, da da dawowata sai in karɓa, har da riba?’ 24 Sai ya ce da na tsaitsaye a wurin, ‘Ku karɓe fam ɗin daga gunsa, ku bai wa mai goman nar.’ 25 Suka ce masa, ‘Ya ubangiji, ai yana da fam goma.’ 26 ‘Ina dai gaya muku, duk mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da ya ke da shi ma, sai an karɓe masa. 27 Waɗannan maƙiyan nawa kuwa da ba sa son in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ “

Yesu ya Shiga Urushalima a kan Aholaki

28 Da Yesu ya faɗi haka, sai ya yi gaba zuwa Urushalima. 29 Kuma da ya kusato Baitafaji da Baitanya, wajen dutsen da a ke kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa biyu, 30 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da ke gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi. 31 Kowa ya tambaye ku, ‘Dom me ku ke kwance shi?’ ku ce, ‘Ubangiji ne ke bukatarsa.’ “ 32 Sai waɗanda aka aikan suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu. 33 Suna cikin kwance aholakin, sai masu shi suka ce musu, “Dom me ku ke kwance aholakin nan?” 34 Sai suka ce, “Ubangiji ne ke bukatarsa.” 35 Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, sai suka ɗora Yesu. 36 Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a kan hanya. 37 Da ya zo dab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu’ujizan da suka gani. 38 Suka ce, “Yabo ya tabbata ga Sarkin nan Maizuwa da sunan Ubangiji! Aminci yā tabbata a Sama, ɗaukaka, kuma tā tabbata can cikin Sama mafi ɗaukaka!” 39 Sai wasu Farisiyawa a cikin taron suka ce masa, “Ya Shugaba, ka kwaɓi almajiranka mana!” 40 Ya amsa ya ce, “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, ko duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”

Yesu ya Koka wa Urushalinia

41 Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya koka masa, 42 ya ce, “Da mana a ce ko da yanzu ma kun san abubuwan da ke kawo aminci! Amma ga shi yanzu am ɓoye muku su. 43 Don lokaci zai taske muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe, 44 su fyaɗa ku da ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan’uwansa ba a birninku, don ba ku fahinci lokacin da a ke sauko muku da alheri ba.”

45 Sai ya shiga Ɗakin Ibada ya fara korar masu saide-saide, 46 ya ce musu, “Ai a rubuce ya ke, cewa, Ɗakina zai kasance ɗakin addu’a’. Amma ku kun maishe shi kogon ’yam-fashi.”

47 Kowace rana sai ya yi ta koyarwa a Ɗakin lbada. Amma manyan malamai, da malaman Attaura, da ƙusoshin gari suka nemi hallaka shi. 48 Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama’a hankali.

20

Wata rana yana koyad da mutane a Ɗakin lbada, yana yi musu Bishara, sai ga manyan malamai, da malaman Attaura, da shugabanni suka matso, 2 suka ce masa, “Gaya mana da wane izini ka ke yin abubuwan nan, ko kuwa wa ya ba ka izinin?” 3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya min, 4 Babtismad da Yohana ya yi, daga Sama ta ke, ko kuwa ta mutun ce?” 5 Sai suka yi muhawara da juna suka ce, “Im muka ce, ‘Daga Sama ta ke,’ sai ya ce, ‘To, dom me ba ku gaskata shi ba?’ 6 In kuwa muka ce, ‘Ta mutun ce,’ sai duk jama’a su jajjefe mu, don sun tabbata Yohana annabi ne.” 7 Sai suka amsa masa suka ce ba su san daga inda ta ke ba. 8 Yesu ya ce da su, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini na ke yin abubuwan nan ba.”

Miyagun Masu Sufuri

9 Sai ya shiga ba jama’a misalin nan, ya ce, “Wani mutun ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma sufurinta, kuma ya tafi wata ƙasa, ya daɗe. 10 Da kakar inabi ta yi, sai ya aiki wani bawansa gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma sai manoman suka yi masa duka, suka kore shi hannu banza. 11 Sai kuma ya aiki wani bawan, shi ma sai suka yi masa duka, suka wulakanta shi, suka kore shi hannu banza. 12 Har wa yau dai ya aiki na uku, shi kuwa suka yi masa rauni, suka kore shi. 13 Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’ 14 Amma da manoman suka gan shi, sai suka yi shawara da juna suka ce, ‘Ai wannan shi ne magajin. Mu kashe shi mana, gadon ya zama namu.’ 15 Sai suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi. To, me ubangijin garkan nan zai yi da su? 16 Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.” Da suka ji haka sai suka ce, “Allah ya sawwake!” 17 Amma sai ya dube su, ya ce, “Wannan fa kuma da ke rubuce, cewa,

‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ya zama babban dutsen harsashin gini’?
18 Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya rugurguje.
Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.

Harajin Kaisar

19 Nan take malaman Attaura da manyan malamai suka nemi kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama’a. 20 Sai suka yi ta haƙonsa, suka aiki ’yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu gaskiya ne, da nufin su burma shi cikin maganatasa, su kuma ba da shi ga gwamna ya hukunta shi. 21 Suka tambaye shi suka ce, “Haba Malan, ai mun san maganarka da koyarwarka duk gaskiya ne. Ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyad da tafarkin Allah sosai ka ke yi. 22 Shin daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?” 23 Shi kuwa sai ya gane makircinsu, ya ce musu, 24 “Ku nuna min dinari. Surar wa da sunan wa ke jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.” 25 Sai ya ce musu, “To, ai sai ku mayar wa da Kaisar abin da ke na Kaisar, ku kuma mayar wa da Allah abin da ke na Allah.” 26 Sai suka kasa burma shi kan wannan magana gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsatasa, sai suka yi shiru.

Yesu ya Tuƙe Hanzarin Sadukiyawa

27 Sai wasu Sadukiyawa suka zo wurinsa, su da ke cewa wai ba Tashin Matattu, 28 suka tambaye shi suka ce, “Malan, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan’uwan mutun ya mutu, ya bar matatasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ’ya’ya. 29 To, an yi wasu ’yan’uwa maza guda bakwai. Na farko ya yi aure, ya mutu bai bar baya ba. 30 Na biyun, 31 da na ukun kuma suka aure ta. Haka dai duk bakwai ɗin suka aure ta suka mutu, ba wanda ya bar ɗa. 32 Daga baya kuma ita matar ta mutu. 33 To, a Tashin Matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”

34 Sai Yesu ya ce musu, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna aurarwa. 35 Amma waɗanda aka ga sun cancanci samun shiga wancan zamani da kuma tashin nan daga matattu, ba za su yi aure ko aurarwa ba. 36 Ba shi yiwuwa su sake mutuwa, don daidai su ke da mala’iku, ’ya’yan Allah ne kuwa da ya ke ’ya’yan Tashin Matattu ne. 37 Game da tashin matattu kuwa ai Musa ma ya faɗa, a Nassin Saiƙaƙiya, inda ya kira Ubangiji, Allahn Ibrahim, kuma Allahn Isiyaku, kuma Allahn Yakubu. 38 Ai waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Don a wurinsa duka rayayyu ne.” 39 Sai wasu malaman Attaura suka amsa suka ce, “Ya Shugaba, ka faɗi daidai.” 40 Daganan kuma. ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.

41 Amma sai ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne? 42 Don Dawuda da kansa a cikin Zabura ya ce,

‘Ubangiji ya ce da Ubangijina,
Zauna a hannuna na dama,
43 Sai na sa ka take maƙiyanka.’

44 Dawuda ya kira shi Ubangiji ne. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?”

45 Sai ya ce da ‘almajiransa a gaban duk jama’a, 46 “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo cikin manyan riguna, da son a gaishe su a kasuwa, da kuma son mafifitan mazaunai a majami’u, da mazaunan alfarma a wurin biki. 47 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, da yin doguwar addu’a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

21

Gwauruwa Matalauciya

Sai Yesu ya ɗaga kai ya ga wasu masu arziki na zuba baikonsu a baitalmalin Ɗakin lbada. 2 Sai ya ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta zuba sisin kwabo biyu a ciki. 3 Sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiyar gwauruwan nan ta zuba a ciki ya fi na sauran duka. 4 Don duk waɗannan sun bayar daga yalwatasu ne, amma ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk ma kuɗinta na abinci.”

Yesu ya yi Faɗi kan Rushewar Ɗakin lbada

5 Wasu suna zancen Ɗakin Ibada, da yadda aka ƙawata shi da duwatsun alfarma da keɓaɓɓun kayan baiko, sai ya ce, 6 “In don waɗannan abubuwan da ku ke kallo ne, ai lokaci na zuwa da ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan’uwansa ba a baje shi ba.” 7 Sai suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa’ad da su ke shirin aukuwa?” 8 Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo suna aron sunana, suna cewa su ne ni, kuma suna cewa, ‘Lokaci ya yi kusa.’ To, kada ku bi su. 9 In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da hargitsi, kada ku firgita. Lalle ne wannan ya fara aukuwa, amma ƙarshen tukuna.”

10 Sa’an nan ya ce musu, “Kabila za ta tasam ma kabila, mulki ya tasam ma mulki. 11 Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa da annoba a wurare daban daban. Za a kuma yi al’amura masu ban tsoro da manyan alamomi daga sama. 12 Amma kafin wannan duka za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku majami’u da kurkuku, su kuma kai ku gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana. 13 Wannan zai zame muku hanyar ba da shaida. 14 Saboda haka sai ku ƙudura a ranku kan ba za ku damu da yadda za ku mai da jawabi ba. 15 Don ni ne zan ba ku ikon furci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku ba za su iya shanyewa ko musawa ba. 16 Ko, da iyayenku ma, da ’yan’uwanku, da danginku, da abokanku sai sun bashe ku, su kuma sa a kashe wasunku. 17 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. 18 Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo. 19 Jurewarku ce za ta fisshe ku.

20 “Sa’ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa’an nan ku tabbata an yi kusan ribɗe ta. 21 Sa’an nan waɗanda ke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu, na cikin birni su fice, na ƙauye kuma kada su shiga birni. 22 Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da ke rubuce. 23 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukam ma ƙasar, da kuma azaba ga jama’an nan. 24 Za a kashe wasu da kaifin takobi, a kuma kakkama wasu a kai su bauta cikin duk sauran al’umma. Sauran al’umma kuma za su tattake Urushalima har ya zuwa cikar zamaninsu.

Alamomin Bayyanar Ɗam Mutun

25 Za a kuma ga alamu a rana da wata da taurari, a duniya kuma al’ummai su matsu ƙwarai, suna cikin damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa. 26 Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargabar al’amuran da ke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manya-manyan abubuwan da ke sararin sama. 27 A sa’an nan ne za su ga Ɗam Mutun na zuwa cikin gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa. 28 Sa’ad da waɗannan al’amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, don fansarku ta yi kusa.”

29 Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi icen ɓaure da dukkan itatuwa, 30 da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan. 31 Haka kuma sa’ad da kuka ga waɗannan al’amura na aukuwa, ku san cewa Mulkin Allah ya gabato. 32 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku. 33 Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.

34 “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har wuf ranan nan ta mamaye ku kamar tarko. 35 Don haka za ta aukam ma mazauna duniya duk, kowa da kowa. 36 Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu’a ku sami ikon tsere wa dukkan waɗannan al’amuran da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗam Mutun.”

37 Kullum da rana ya kan koyar a Ɗakin lbada, da dare kuma ya kan fita ya kwana a dutsen da a ke kire Dutsen Zaitun. 38 Da sassafe kuma dukkan mutane su kan zo wurinsa a Ɗakin lbada su saurare shi.

MUTUWAR YESU DA TASHINSA

22

Yahuda ya Ci Amanar Yesu

To, sai Idin Burodi Marar Yisti, wanda a ke kira Idin Ƙetarewa, ya gabato. 2 Sai manyan malamai da malaman Attaura suka yi ta neman yadda za su kashe shi, amma kuwa suna tsoron jama’a.

3 Sai Shaiɗan ya shigi Yahuda, wanda a ke kira Iskariyoti, ɗaya daga cikin Sha biyun nan. 4 Sai ya tafi ya yi shawara da manyan malamai da shugabannin ma’aikatan Ɗakin Ibada kan yadda zai bashe shi a gare su. 5 Sai suka yi murna, suka kuma yi alkawarin ba shi kuɗi. 6 Shi kuwa ya yarda, ya kuma nemi hanyar bashe shi a gare su bayan idon jama’a.

Sun Shirya Abin Ƙetarewa

7 Sai ranar Idin Burodi Marar Yisti ta zo, wato ranad da a ke yanka ɗan ragon Idin ƙetarewa. 8 Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohana, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.” 9 Suka ce masa, “Ina ka ke so mu shirya shi?” 10 Ya ce musu, “Ga shi, da shigarku gari, za ku gamu da wani mutun ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi har cikin gidan da ya shiga. 11 Ku ce da maigidan, ‘Shugaba ya ce, ina masauƙin da zai ci Jibin Ƙetarewa da almajiransa?’ 12 Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.” 13 Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

Kafa Jibin Ubangiji

14 Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, Manzanninsa kuma na tare da shi. 15 Ya ce da su, “Ina so ƙwarai dā ma in ci Jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya. 16 Gama ina gaya muku ba zan ƙara cinsa ba, sai an cika shi a Mulkin Allah.” 17 Sai ya karɓi ƙoƙo, kuma bayan ya yi godiya ga Allah, ya ce, ‘Ungo wannan, ku shassha. 18 Ina gaya muku, daga yanzu ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.” 19 Sai ya ɗauki burodi, kuma bayan ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.” 20 Haka kuma bayan jibi, sai ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a zubar dominku. 21 Amma ga shi mai bashe nin nan yana ci akushi ɗaya da ni. 22 Lalle Ɗam Mutun zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka mutumin nan da ke ba da shi ya shiga uku!” 23 Sai suka fara tambayar juna ko wanene a cikinsu zai yi haka.

24 Sai musu ya tashi tsakaninsu a kan ko wanene babbansu. 25 Sai ya ce musu, “Sarakunan sauran al’umma su kan nuna musu iko, mahukuntansu kuma su kan nemi a kira su Mataimakan Jama’a. 26 Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda ke babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima. 27 Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe ba wanda ya zauna ya ke cin abincin ba ne? Ga shi kuwa ina cikinku kamar mai hidima.

28 “Ku ne kuka tsaya gare ni cikin gwaje‑gwajen da na sha. 29 Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma na ke ba ku iko 30 ku ci ku sha tare da ni a cikin mulkina, ku kuma zauna a kan gadajen sarauta, kuna hukunta kabilun nan goma sha biyu na Bani Isra’ila.

31 “Siman, ya Siman, Shaiɗan ya nemi izinin sheke ku kamar alkama, ya kuwa samu. 32 Ni kuwa na yi maka addu’a, kada bangaskiyarka ta gushe. Kai kuma, bayan ka juyo, sai ka ƙarfafa ’yan’uwanka.” 33 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, a shirye na ke im bi ka kurkuku, ko kuma Lahira.” 34 Yesu ya ce, “Ina dai gaya maka Bitrus, a yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

35 Ya kuma ce musu, “Sa’ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.” 36 Ya ce musu, “Amma yanzu duk mai jakar kuɗi yă ɗauka, haka kuma mai burgami. Wanda kuwa ba shi da takobi, ya sai da mayafinsa ya saya. 37 Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina, cewa, ‘Am lasafta shi a cikin masu laifi’. Har ma duk abubuwan da suka shafe ni, tabbatarsu ta zo.” 38 Sai suka ce, “Ya Ubangiji, ai ga takuba biyu.” Ya ce musu, “A bar maganar hakanan.”

Yesu a Jatsamani

39 Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun kamar yadda ya saba. Almijiransa kuwa suka bi shi. 40 Da ya iso wurin, sai ya ce musu, “Ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji. 41 Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu’a. 42 Ya ce, “Ya Uba, in dai haka ka nufa, ka ɗauke mini shan wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi. 43 Sai wani mala’ika ya bayyana gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi. 44 Don kuma yana shan wahala gaya sai ya ƙara himmar addu’a, har jininsa na ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini. 45 Da ya tashi daga addu’a, sai ya komo wurin almajiran, ya samu suna barci saboda baƙinciki. 46 Sai ya ce da su, “Dom me ku ke barci? Ku tashi, ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji.”

Am ba da Yesu an Kama Shi

47 Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama’a suka zo, mutumin da a ke kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha biyun nan, shi ke musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbance shi. 48 Amma sai Yesu ya ce masa, “Yahuda, ashe da sumba za ka ba da Ɗam Mutun?” 49 Da na kusa da shi suka ga abin da za a yi, sai suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?’ 50 Sai ɗayansu ya kai wa bawan Babban Malamin sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. 51 Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkad da shi. 52 Kuma Yesu ya ce da waɗanda suka tasam masa, wato, manyan malamai da shugabannin ma’aikatan Ɗakin Ibada da shugabannin jama’a, “Kun fito ne da takuba da kulake kamar masu kama ɗam-fashi? 53 Sa’ad da na ke tare da ku kowace rana cikin Ɗakin Ibada, ba ku taɓa kai mini cafka ba. Amma wannan ne lokacinku da na ikon duhu.”

Bitrus ya yi Musun Sanin Yesu

54 Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi cikin gidan Babban Malamin. Bitrus kuwa na biye daga nesa-nesa. 55 Da suka hura wuta a tsakar gida suka zazzauna, sai Bitrus ma ya zauna a cikinsu. 56 Sai wata baranya ta gan shi zaune a hasken wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Ai mutumin nan ma tare da shi ya ke.” 57 Amma sai ya musa ya ce, “Ke, ban ma san shi ba.” 58 Bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, sai wani ya gan shi, ya ce, “Kai ma ai ɗayansu ne.” Amma sai Bitrus ya ce, “Haba, ba shi ba ne.” 59 Bayan wajen sa’a guda sai wani dai ya nace, ya ce, “Ba shakka mutumin nan ma tare da shi ya ke, don Bagalile ne.” 60 Amma sai Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da ka ke faɗa ba.” Nan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara. 61 Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganad da Ubangiji ya faɗa masa, cewa, “A yau ma kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku. 62 Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

63 Sai mutanen da ke riƙe da Yesu suka yi ta. masa ba’a, suna dukansa. 64 Suka kuma ɗaure masa idanu, suka tambaye shi, suka ce, “Yi annabci! Wa ya buge ka?” 65 Kuma suka yi ta masa baƙaƙen maganganu masu yawa, suna zaginsa.

Yesu a Gaban Majalisar Yahudawa

66 Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama’a ta haɗu, da manyan malamai da kuma malaman Attaura. Sai suka kai shi ɗakin majalisarsu, suka ce, 67 “To, in kai ne Almasihu, gaya mana.” Amma sai ya ce musu, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ba. 68 In kuma na yi muku tambaya, ba za ku mai da jawabi ba. 69 Amma nan gaba Ɗam Mutun zai zauna a hannun dama na Allah Mai iko.” 70 Duk sai suka ce, “Ashe kai ɗin nan ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗan, ni ne.” 71 Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nemo? Ai mun ji da kammu daga bakinsa.”

23

Yesu a Gaban Bilatus

Duk taronsu sai suka tashi suka kai shi gaban Bilatus. 2 Sai suka fara ɗora masa laifi, suna cewa, “Mun sami mutumin nan na ɓad da jama’armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa wai shi ne Almasihu, kuma sarki.” 3 Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ashe kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Yadda ka faɗan.” 4 Bilatus ya ce da manyan malamai da taro masu yawa, “Ban sami mutumin nan da wani laifi ba.” 5 Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama’a, yana koyarwa a dukkan ƙasar Yahudiya tun daga ƙasar Galili har nan.” 6 Da Bilatus ya ji haka, sai ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne.

Yesu a Gaban Hirudus

7 Kuma da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus ya ke, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a Iokacin. 8 Da Hiudus ya ga Yesu, sai ya yi murna kwarai, saboda tun da daɗewa ya ke son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa, yana kuma fata ya ga wata mu’ujizad da Yesu zai yi. 9 Sai ya yi ta masa tambayoyi da yawa, amma bai ce masa ƙala ba. 10 Manyan malamai da malaman Attaura na nan tsaitsaye, suna tsananta ɗora masa laifi da tsawa mai yawa. 11 Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba’a; kuma da suka sa masa tufafi masu kawa, sai suka mai da shi wurin Bilatus. 12 A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gaba ne.

Bilatus bai Sami Yesu da Laifi ba

13 Sai Bilatus ya tara manyan malamai da shugabanni da kuma jama’a, 14 ya ce musu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan wai yana ɓad da jama’a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi ba a cikin ƙararrakinsa da kuka kawo. 15 Hirudus ma bai samu ba, don ya komo mana da shi. Ga shi kuwa bai yi wani abin da ya cancanci kisa ba. 16 Saboda haka zan yi masa bulala in sake shi.” 17 A lokacin Idi kuwa lalle ne ya sakam musu fursuna guda.

Bilatus ya Yanke wa Yesu Hukuncin Kisa

18 Amma sai duk suka ɗauki ihu gaba-ɗaya, suna cewa, “A yi da wannan ɗin, a sakam mana Barabbas!” 19 wato wani mutun ne da aka jefa kurkuku, saboda wani tawayen da aka yi a birni, da kuma kisankai. 20 Sai Bilatus ya sake yi musu magana, don yana son ya saki Yesu. 21 Amma sai suka yi ta ƙwala ihu, suna cewa, “A giciye shi! A giciye shi!” 22 Ya sake faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi? Ai ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka zan yi masa bulala in sake shi. 23 Amma sai suka matsa lamba, suna cira murya wai a giciye shi, har surutunsu ya yi rinjaye. 24 Sai Bilatus ya zartad da hukunci a biya musu bukata. 25 Ya kuwa sakam musu wanda suka tambaya, wato wanda aka jefa kurkuku a kan laifin tawaye da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu su yi masa abin da su ke so.

26 Suna tafiya da Yesu ke nan, sai suka cafke wani, mai suna Siman Bakurane, yana zuwa daga ƙauye, suka ɗora masa giciye, yă ɗauka ya bi Yesu. 27 Sai taron mutane masu yawan gaske suka bi shi, da wasu mata da ke kuka, su ke kuma jaje saboda shi. 28 Amma, sai Yesu ya juya gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma ’ya’yanku. 29 Don lokaci na zuwa da za su ce, ‘Albarka ta tabbata ga matan da ke juya, waɗanda ba su taɓa haifuwa ba, kuma waɗanda ba a taɓa shan mamansu ba.’ 30 Sa’an nan ne za su fara ce da manyan duwatsu, ‘Ku faɗo a kammu mana’, su kuma ce da tsaunuka, ‘Ku binne mu mana.’ 31 Ai wuta ta ci danye, balle ƙeƙasasshe.”

An Giciye Yesu

32 Wasu mutum biyu kuma masu laifi, sai aka kai su a kashe su tare da shi. 33 Da suka isa wurin da a ke kira Ƙoƙwan Kai, nan suka giciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya ta dama, ɗaya ta hagun. 34 Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da su ke yi ba.” Sai suka rarraba tufafinsa, suna ƙuri’a a kansu. 35 Sai mutane suka tsaitsaya, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa tsaki, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah, zaɓaɓɓensa!” 36 Soja kuma suka yi masa ba’a, suka matso suka miƙa masa ruwan tsami, 37 suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ceci kanka mana!” 38 Kuma sama da shi aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”

Ɓarawon da ya Tuba a kan Giciye

39 Sai ɗaya daga cikin masu laifin da aka giciye ya yi masa baƙar magana ya ce, “Shin ba kai ne Almasihu ba? To, ceci kanka mana duk da mu!” 40 Amma sai ɗayan ya amsa, ya kwaɓe shi, ya ce, “Kai ko tsoron Allah ma ba ka yi, kai da ya ke hukuncinka daidai da nasa? 41 Mu kam daidai aka yi mana, don hakika sakamakon aikimmu muka samu, amma mutumin nan bai yi wani laifi ba.” 42 Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka zo cikin sarautarka.” 43 Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, yau ma za ka kasance tare da ni a cikin Firdausi.”

Yesu ya Mutu

44 To, wajen tsakar rana ne kuwa, sai duhu ya rufe ƙasa duka, bar zuwa ƙarfe uku na yamma. 45 Hasken rana, ya dushe. Sai Labulen Wuri Tsattsarka ya tsage gida biyu. 46 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sanya ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka kuwa sai ya cika. 47 Sa’ad da kyaftin ɗin ya ga abin da ya wakana, sai ya ɗaukaka Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!” 48 Da duk taro masu yawa waɗanda suka zo kallo suka ga abin da ya faru, sai suka koma, suna kama ƙirjinsu. 49 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka biyo shi tun daga ƙasar Galili, sai suka tsaya daga nesa, suna duban waɗannan abubuwa.

Jana’izar Yesu

50 To, akwai wani mutum mai suna Yusufu, mutumin Aramatiya, wani garin Yahudawa, shi ɗam-majalisa ne, mutun ne nagari, kuma mai gaskiya. 51 Shi kuwa dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba, yana kuwa sauraron bayyanar Mulkin Allah. 52 Shi ne ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 53 Sai ya sauko da shi, ya sa shi a likkafanin linen, ya kwantad da shi a wani kabarin da aka fafe dutse aka yi, wanda ba a taɓa sa kowa ba. 54 Ran nan kuwa Ranar Shiri ce, Asabar kuma ta doso. 55 Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, sai suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka kwantad da jikinsa. 56 Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa.

Ran Asabar kuwa sai suka huta bisa umarni.

24

Tashin Yesu daga Matattu

A ranar farko ta mako kuwa, da asussuba, sai suka je kabarin da kayan ƙanshin da suka shirya. 2 Sai suka tarar an mirgine dutsen daga kabarin. 3 Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji Yesu ba. 4 Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga wasu mutum biyu tsaye kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali. 5 Don kuma tsoro sai matan suka sunkuyad da kansu ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Dom me ku ke neman rayayye a cikin matattu? 6 Ai ba ya nan, ya tashi. Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana Galili, 7 cewa, ‘Lalle ne a ba da Ɗam Mutun ga mutane masu zunubi, a giciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi’.” 8 Sai suka tuna da maganatasa. 9 Kuma da suka dawo daga kabarin sai suka shaida wa Sha dayan nan, da kuma duk sauransu, dukkan waɗannan abubuwa. 10 To, Maryamu Magadaliya, da Yuwana, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma sauran matan da ke tare da su, su ne suka gaya wa Manzarmin waɗannan abubuwa. 11 Su kuwa sai maganan nan ta zame musu kamar zance ne kawai, suka ƙi gaskatawa. 12 Amma sai Bitrus ya tashi, ya doshi kabarin da gudu. Ya duƙa, ya leka ciki, ya ga likkafanin linen a ajiye waje ɗaya. Sai ya koma gida yana al’ajabin abin da ya auku.

Yesu da Almajirai Biyu a Hanyar Imayas

13 A ran nan kuma sai ga wasunsu biyu suna tafiya wani ƙauye, mai suna Imayas, nisansa daga Urushalima kuwa kusan mil bakwai ne. 14 Suna ta zance da juna a kan dukkan al’amuran da suka faru. 15 Sai ya zamana tun suna cikin magana, kowa na faɗar albarkacin bakinsa, sai Yesu da kansa ya matso, suka tafi tare. 16 Amma idanunsu ya rufe, don kada su gane shi. 17 Yesu ya ce musu, “Wace magana ce ku ke yi da juna a tafe?” Sai suka tsaya cik, suna masu baƙinciki. 18 Sai ɗayansu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa ya ce, “Ashe kai wararren baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can cikin ’yan kwanakin nan ba?” 19 Sai ya ce musu, “Waɗanne abubuwan?” Suka ce masa, “Game da Yesu Banazare ne, wanda ya ke annabi mai yin manyan ayyuka da ƙwaƙƙwarar magana gaban Allah da dukkan mutane, 20 da kuma yadda manyan malamai da shugabannimmu suka ba da shi don a yi masa hukuncin kisa, suka kuwa giciye shi. 21 Dā kuwa mun sa zuciya shi ne zai ceci Bani Isra’ila. Hakika kuma bayan wannan duka, yau kwana uku ke nan da aukuwar wannan abin. 22 Har wa yau kuma wasu mata na cikimmu sun ba mu al’ajabi. Don sun je kabarin da sassafe, 23 kuma da ba su sami jikinsa ba, sai suka komo, suka ce har ma an yi musu wahayi sun ga mala’ikun da suka ce yana da rai. 24 Kuma wasunsu da ke tare da mu suka je kabarin, suka tarar kamar yadda matan suka faɗa, amma shi ba su gan shi ba.” 25 Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahinta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka fada! 26 Ashe ba wajibi ne Almasihu ya sha wuyar waɗannan abubuwa ba, ya kuma shiga ɗaukakarsa?” 27 Sai ya fara ta kan Littattafan Musa da na dukkan Annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukkan Littattafai Tsarkaka.

28 Sai suka kusato ƙauyen da za su. Ya yi kamar zai ci gaba, 29 sai suka matsa masa suka ce, “Sauka a wurimmu mana, ai magariba ta doso, rana duk ta tafi.” Sai ya sauka a wurinsu. 30 Sa’ad da ya ke cin abinci tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su. 31 Sai idonsu ya buɗe, suka kuma gane shi. Sai ya ɓace musu. 32 Sai suka ce da juna, “Kai! Ashe rammu bai tohu ba sa’ad da ya ke magana da mu a hanya, yana bayyana mana Littattafai Tsarkaka?”

Sun dawo Urushalima

33 Nan take sai suka tashi suka koma Urushalima, suka sami Sha dayan nan a tare gu ɗaya, da kuma waɗanda ke tare da su, 34 suna cikin cewa, “Hakika Ubangiji ya tashi, har ya bayyana ga Siman!” 35 Su kuma suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane shi wajen gutsura burodi.

Salama Alaikum—in ji Yesu

36 Suna cikin faɗar waɗannan abubuwa, sai ga Yesu kansa tsaye a tsakiyarsu, ya ce musu, “Salama alaikum!” 37 Amma sai suka firgita, tsoro ya rufe su, suka zaci fatalwa suka gani. 38 Sai ya ce musu, “Dom me kuka firgita, ku ke kuma tantama a zuciyarku? 39 Ku dubi hannayena da ƙafafuwana, ai ni ne da kaina. Ku taɓa ni ku ji. Don fatalwa ba ta da tsoka da ƙashi, yadda ku ke gani na ke da su.” 40 Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannayensa da ƙafafuwansa. 41 Amma tun suna da sauran shakka saboda tsananin farinciki da mamaki, sai ya ce musu, “Kuna da wani abinci a nan?” 42 Sai suka ba shi wata tsokar gasasshen kifi 43, Ya kuwa karɓa ya ci a gabansu.

Yesu ya ce, “Ku ne Shaiduna”

44 Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da ke rubuce game da ni a cikin Attaura ta Musa, da Littattafan Annabawa, da kuma Zabura.” 45 Sa’an nan ya ba su buɗi a zukatansu na fahintar Littattafai Tsarkaka, 46 ya kuma ce musu, “Haka ya ke a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, kuma a rana ta uku ya tashi daga matattu, 47 a kuma yi wa dukkan al’ummai wa’azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa. 49 Ga shi zan aiko muku da baiwan nan da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a cikin birni tukuna, har sai an yi muku baiwar iko daga Sama.”

Yesu ya Hau Sama

50 Sai ya kai su waje har jikin Baitanya. Ya ɗaga hannayensa ya yi musu albarka. 51 Yana cikin yi musu albarka ke nan, sai ya tafi daga wurinsu, aka ɗauke shi zuwa Sama. 52 Su kuwa suka yi masa sujada, suka kuma koma Urushalima, suna masu matuƙar farinciki. 53 Koyaushe kuma suna Ɗakin Ibada suna yabon Allah.


BISHARA TA HANNUN
YOHANA

1

Tun fil’azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah ya ke, Kalman nan kuwa Allah ne. 2 Shi ne tun fil’azal ya ke tare da Allah. 3 Dukkan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance a cikin abubuwan da suka kasance sai ta game da shi. 4 Shi ne tushen rai madawwami, rai madawwamin nan kuwa shi ne hasken mutane. 5 Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.

6 Akwai wani mutun da Allah ya aiko, mai suna Yohana. 7 Shi fa ya zo shaida ne, don ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8 Ba shi ne hasken ba, ya zo ne don ya shaidi hasken.

9 Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da ke haskaka kowane mutun. 10 Dā yana duniya, duniyar ma ta kansa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11 Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama’atasa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12 Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama ’ya’yan Allah, 13 wato waɗanda haifuwatasu ba ta zuriyar ɗan’adam ba ce, ba kuwa ta niyyar tarawa ko nufin mutum ba, sai dai ta Allah.

14 Kalman nan kuwa ya zama mutun, ya zauna a cikimmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin ɗan da ke daga wurin Uba.

Shaidar Yohana Maibabtisma

15 Yohana ya shaide shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, don dā ma yana nan tun ba ni.’” 16Dukkammu kuwa daga falalatasa muka samu, alheri kan alheri. 17 Don Shari’a ta hannun Musa aka ba da ita; alheri da gaskiya kuwa ta kan Yesu Almasihu suka kasance. 18 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicinna da ke dawwame game da Uba, shi ne ya bayyana shi.

19 Wannan kuwa ita ce shaidar Yohana, wato sa’ad da Yahudawa suka alki malamai da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi shi wanene. 20 Sai ya faɗi gaskiya, bai yi musu ba, gaskiya ya fada ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.” 21 Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A’a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A’a.” 22 Sai suka ce da shi, “To wanene kai, don mu sami amsad da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me ka ke ce da kanka?” 23 Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”

24 Su kuwa Farisiyawa ne suka aiko su. 25 Sai suka tambaye shi suka ce, “To, dom me ka ke yin babtisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” 26 Sai Yohana ya amsa musu ya ce, “Ni kam da ruwa na ke babtisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba, 27 shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa im ɓalle ba.” 28 An yi wannan a Baitanya ne, a ƙetaren Kogin Urdun, inda Yohana ke yin babtisma.

GA ƊAN RAGON ALLAH

29 Washegari Yohana ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, Sa ɗan Ragon Allah, mai ɗauke zunubin duniya! 30 Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani mutun na zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, don da ma yana nan tun ba ni.’ 31 Da kam ban san shi ba, sai don a bayyana shi ga Bani Isra’ila ne na zo na ke babtisma da ruwa.” 32 Yohana ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu Tsattsarka na saukowa kamar kurciya daga Sama, ya kuma zauna a kansa. 33 Da kam ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi babtisma da ruwa shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhu Tsattsarka na sauko masa, yana kuma zama a kansa, shi ne mai yin babtisma da Ruhu Tsattsarka.’ 34 Na kuwa gani, na kuma yi shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”

Almajiran Yesu na Farko

35 Kashegari kuma Yohana na tsaye da almajiransa biyu. 36 Yana cikin duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Ragon Allah!” 37 Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu. 38 Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me ku ke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi,” (wato, ya Shugaba ke nan), “ina ka ke da zama?” 39 Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda ya ke da zama; suka kuwa wuni tare da shi. Wajen ƙarfe goma na safe ne kuwa. 40 Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yohana suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan’uwan Siman Bitrus. 41 Sai ya fara samo ɗan’uwansa Siman, ya ce da shi, “Mun sami Masihi,” (wato, Shafaffe). 42 Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Siman ɗan Yohana? Za a kira ka Kefas,” (wato, Bitrus).

43 Washegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce da shi, “Bi ni.” 44 Filibus kuwa mutumin Baitsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus. 45 Filibus ya sami Natana’ilu, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a cikin Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.” 46 Natana’ilu ya ce da shi, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai ka gani.” 47 Yesu ya ga Natana’ilu na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba’isra’ile na gaske wanda ba shi da ha’inci!” 48 Natana’ilu ya ce da shi, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa’ad da ka ke gindin ɓaure ma, na gan ka.” 49 Sai Natana’ilu ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai ɗan Allah ne! Kai Sarkin Bani Isra’ila ne!” 50 Yesu ya amsa. masa ya ce, “Wato don na ce da kai na gan ka a gindin ɓaure ne ka ke ba da gaskiya? Ai za ka ga al’amuran da suka fi haka ma.” 51 Kuma Yesu ya ce da shi, “Lalle, hakika, ina gaya muku, za ku ga Sama ta dare, mala’ikun Allah na hawa da sauka ga Ɗam Mutun. “

2

Mu’ujizar Yesu ta Farko

A rana ta uku sai aka yi biki a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa na nan, 2 aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa. 3 Da ruwan inabi ya gaza, sai uwar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” 4 Yesu ya ce mata, “Iya, ai wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.” 5 Sai uwatasa ta ce da barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.” 6 A wurin kuwa akwai randuna shida. na dutse a ajijiye, bisa al’adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce na cin wajen tulu shida-shida. 7 Sai Yesu ya ce da su, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal-fal. 8 Sa’an nan ya ce musu, “To, yanzu sai ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai. 9 Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba, (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), sai ya yi magana da ango, 10 ya ce, “Kowa ai kyakkyawan ruwan inabi ya kan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa’an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”

11 Wannan ce mu’ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.

12 Bayan haka sal ya tafi Kafarnahum, da shi da uwatasa, da ’yan’uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can ’yan kwanaki.

Yesu a Ɗakin lbada

13 Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima. 14 A cikin Ɗakin Ibada sai ya sami wasu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabaru, da kuma ’yan-canjin-kuɗi zaune wurin aikinsu. 15 Sai ya tuka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Ɗakin Ibada, har da tumakin da shanun, ya kuma watsad da kuɗin ’yan-canjin, ya birkice teburansu. 16 Ya ce da dillalan tattabaru, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Ɗakin Ubana kasuwa.” 17 Sai almajiransa suka tuna a rubuce ya ke, cewa, “Kishin Ɗakinka ya ci raina matuƙa.” 18 Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu’ujiza za ka nuna mana da ka ke haka?” 19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe tsattsarkan wurin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.” 20 Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin tsattsarkan wurin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?” 21 Amma abin da Yesu ke nufi da tsattsarkan wurin nan, jikinsa ne. 22 Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, sai almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganad da Yesu ya faɗa.

23 To, sa’ad da ya ke Urushalima lokacin Idin Ƙetarewa, sai mutane da yawa suka gaskata da sunansa, saboda ganin mu’ujizan da ya yi. 24 Amma Yesu bai amince da su ba, 25 don ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutun a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da ke zuciyar ’yan’adan.

3

Labarin Nikodimu

To, akwai wani Bafarisiye, wai shi Nikodimu, wani shugaban Yahudawa. 2 Wannan mutun ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun san kai malami ne da ya zo daga wurin Allah, don ba mai iya yin waɗannan mu’ujizan da ka ke yi, sai ko Allah na tare da shi.” 3 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle, hakika, ina gaya maka, im ba an sake haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.” 4 Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutun bayan ya tsufa? Wato ya iya komawa cikin uwatasa ta sake haifo shi?” 5 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle, hakika, ina gaya maka, im ba an haifi mutun ta ruwa da ta Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba. 6 Abin da mutun ya haifa mutun ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne. 7 Kada ka yi mamaki don na ce maka, ‘Lalle a sake haifarku.’ 8 Iska na busawa inda ta ga dama. Ka kan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito ba, da inda za ta. Haka fa ya ke ga duk wanda Ruhu ya haifa.” 9 Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?” 10 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe kai ma da ka ke malamin Bani Isra’ila, ba ka fahinci waɗannan al’amura ba? 11 Lalle, hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi mu ke faɗa, muna kuma shaidad da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu. 12 In na yi muku zancen al’amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al’amuran Sama? 13 Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga cikin Sama, wato Ɗam Mutun da ke cikin Sama. 14 Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma lalle ne a daga Ɗam Mutun, 15 don duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.

Samun Rai Madawwami

16 “Saboda ƙaunad da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, don duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya yi yanke mata hukunci ba, sai dai don duniya ta sami ceto ta hanyarsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, har ya zama hukuntacce ko, don bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Hukuncin kuwa shi ne, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu da hasken, don ayyukansu miyagu ne. 20 Duk mai yin rashin gaskiya ya kan ƙi hasken, ba ya kuma zuwa wajen hasken, don kada ayyukansa su tonu. 21 Mai aikata gaskiya kuwa ya kan zo wajen hasken, don a bayyana ayyukansa cewa da taimakon Allah ne aka yi su.”

22 Bayan haka sai Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin babtisma. 23 Yohana kuma na yin babtisma a Ainon kusa da Salim, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu babtisma. 24 Don a sa’an nan ba a sa Yohana a kurkuku ba tukuna.

25 Sai fa almajiran Yohana suka tasam ma wani Bayahude da muhawara a kan maganar tsarkakewa. 26 Kuma suka zo wurin Yohana, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda da ku ke tare a ƙetaren Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaide shi, to, ga shi yana yin babtisma, har kowa da kowa na zuwa wurinsa.” 27 Sai Yohana ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun komai sai ko am ba shi daga Sama. 28 Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne in riga shi gaba. 29 Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da ke tsaye, ya ke kuma sauraron maganatasa, ya kan yi farinciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farincikin nan nawa ya kai matuƙa. 30 Shi kam lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.

31 “Mai zuwa daga Sama na sama da kowa. Wanda ke ƙasa ce asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma ya ke yi. Mai zuwan nan daga Sama na sama da kowa. 32 Abin da ya ji, ya kuma gani, shi ya ke shaidarwa, duk da haka ba wanda ke yarda da shaidarsa. 33 Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe cewa Allah Mai gaskiya ne. 34 Domin wanda Allah ya aiko, Maganar Allah ya ke faɗa, gama Allah na ba da Ruhu Tsattsarka ba da iyakancewa ba. 35 Uban na ƙaunar Ɗan, ya kuma sa komai a hannunsa. 36 Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai madawwami ba, sai dai azabar Allah ta tabbata a gare shi.”

4

Basamariya—Ruwan Rai

To, da Ubangiji Yesu ya san dai Farisiyawa sun ji labarin yana samun almajirai, yana kuma yi musu babtisma fiye da Yohana, 2 (ko da ya ke dai ba Yesu kansa ke yin babtisma ba, almajiransa ne), 3 sai ya bar ƙasar Yahudiya, ya koma ƙasar Galili. 4 Lalle ne kuwa yă ratsa ƙasar Samariya. 5 Sai ya zo wani gari na ƙasar Samariya wai shi Saikar, kusa da yankin ƙasad da Yakubu ya ba ɗansa Yusufu. 6 Rijiyar Yakubu kuwa a nan ta ke. Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna hakanan a bakin rijiyar. Wajen ƙarfe shida na yamma ne kuwa.

7 Sai ga wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata, “Sam mini ruwa in sha.” 8 Almajiransa kuwa sun shiga gari sayen abinci. 9 Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka tambaye ni ruwan sha, ni da na ke Basamariya?” (Don Yahudawa ba sa cuɗanyada Samariyawa). 10 Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce da ke, ‘Sam mini ruwa in sha,’ ai da kin roƙe shi, shi kuwa da sai ya ba ƙi ruwan rai.” 11 Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, ina ka sami ruwan nan na rai? 12 Ashe ka fi ubammu Yakubu ne, wanda ya bar mana rijiyar, har shi da kansa, da ’ya’yansa, da dabbobinsa, suka sha ruwanta?” 13 Yesu ya amsa mata ya ce, “Duk mai shan ruwan nan zai sake jin ƙishirwa. 14 Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, Yana ɓuɓɓugowa bar ya zuwa rai madawwami.” 15 Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ba ni ruwan nan mana, don kada in ƙara jin ƙishirwa, kada kuma in riƙa zuwa har nan ɗiba.”

16 Sai Yesu ya ce mata, “Je ƙi ku zo da mijinki.” 17 Sai matar ta amsa ta ce, “Ai ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ƙi da miji, 18 don kin auri maza biyar, wanda ku ke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.” 19 Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, na dai gane kai annabi ne. 20 Kakannimmu sun yi sujada a kan dutsen nan. Ku kuwa kun ce a Urushalima ne wurin da ya wajaba a yi sujada ya ke.” 21 Sai Yesu ya ce mata, “Uwargida, ƙi gaskata ni, lokaci na zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ba, ko a kan dutsen nan, ko a Urushalima. 22 Ku kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada, mu kuwa muna yi wa abin da muka sani sujada, domin ceto ta hanyar Yahudawa ya ke. 23 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada ta ruhu, kuma cikin gaskiya. Lalle kuwa irin waɗannan masu yi masa sujada Uba ke nema. 24 Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada ta ruhu, kuma cikin gaskiya.” 25 Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi na zuwa, wanda a ke kira Almasihu. Sa’ad da ya zo kuwa, zai sanad da mu komai.” 26 Yesu ya ce mata, “Ni mai maganan nan da ke, shi ne.”

Macecin Duniya

27 Nan take almajiransa suka dawo, suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma kuwa ba wanda ya ce, “Me ƙi ke bukata?” ko, “Dom me ka ke magana da ita?” 28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, ta ce da mutane, 29 “Ku zo ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin ko wannan shi ne Almasihu?” 30 Sai suka fito daga garin suka nufo shi.

31 Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya Shugaba, ci abinci mana.” 32 Amma sai ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.” 33 Almajiran suka ce da juna, “Shin wani ya kawo masa abinci ne?” 34 Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. 35 Ba kuna cewa ƙaƙa saura wata huɗu ba? Ina gaya muku fa, ku ɗaga kai, ku hangi yadda gonaki har suka isa girbi. 36 Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani mai kaiwa ga rai madawwami, don mai shuka da mai girbi su yi farinciki tare. 37 A nan kam karin maganan nan ya gaskanta, cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’ 38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Wasu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.”

39 Samariyawa da yawa na wannan garin suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” 40 Da Samariyawa suka iso wurinsa sai suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan. 41 Wasu kuma da yawa fiye da na dā, suka ba da gaskiya saboda maganatasa. 42 Sa’an nan suka ce da matar, “Yanzu kam mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, don mu ma mun ji da kammu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Macecin duniya.”

43 Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili. 44 Don Yesu kansa ya yi shaidar cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu. 45 Da ya isa ƙasar Galili sai Galilawa suka yi na’am da shi, don sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Idi, domin su ma sun je Idin.

46 Sai ya sake zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. A Kafarnahum kuwa akwai wani bafada wanda ɗansa ba shi da lafiya. 47 Da jin cewa Yesu ya fito ƙasar Yahudiya ya komo ƙasar Galili, sai ya tafi wurinsa, ya roƙe shi ya je ya warkad da ɗansa, don yana bakin mutuwa. 48 Yesu sai ya ce masa, “Im ba mu’ujizai da abubuwan al’ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.” 49 Sai bafadan nan ya ce masa, “Ya Shugaba, ka zo mana tun ƙaramin ɗana bai mutu ba.” 50 Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye ya ke.” Mutumin kuwa ya gaskata maganad da Yesu ya fada masa, ya yi tafiyarsa. 51 Yana cikin tafiya sai ga bayinsa sun taryo shi, suka ce masa, “Ɗanka a raye ya ke.” 52 Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙi. Suka ce masa, “Jiya da ƙarfe bakwai na yamma zazzaɓin ya sake shi.” 53 Sai uban ya gane cewa daidai lokacin nan ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye ya ke.” Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama’ar gidansa duka. 54 Wannan kuwa ita ce mu’ujiza ta biyu da Yesu ya yi bayan komowarsa ƙasar Galili daga ƙasar Yahudiya.

5

Yesu ya Warkad da Marar Lafiya Ran Asabar

Bayan haka sai aka yi wani idi na Yahudawa, Yesu kuwa ya tafi Urushalima. 2 A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da a ke ce da shi Baitasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar. 3 A shirayin nan marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu, (suna jiran a motsa ruwan. 4 Don lokaci-lokaci wani mala’ika ya kan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga ciki bayan an motsa ruwan, sal ya warke duk irin cutad da ya ke da ita). 5 A nan kuwa akwai wani mutun da ya shekara talatin da takwas da rashin lafiya. 6 Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma san ya daɗe cikin wannan hali, sai ya ce masa, “Kana so a warkad da kai?” 7 Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai ba ni da wanda zai angaza ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Kuma lokacin da na doshi ruwan sai in ga wani ya sha gabana.” 8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka yi tafiya!” 9 Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiya.

To, ran nan kuwa Asabar ce. 10 Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.” 11 Sai ya amsa musu ya ce, “Ai wanda ya warkad da ni shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in yi tafiya.” 12 Suka tambaye shi, “Wane mutun ne ya ce da kai ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya?” 13 Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wanene ba, don Yesu ya riga ya janye jiki saboda taron da ke wurin. 14 Bayan haka sai Yesu ya same shi a Ɗakin lbada, ya ce masa, “Ka ga fa ka warke! To, kada ka ƙara ɗaukar zunubi, don kada wani abin da ya fi wannan muni ya same ka.” 15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkad da shi. 16 Saboda haka sai Yahudawa suka fara tsananta wa Yesu, wai don yana yin irin waɗannan abubuwa ran Asabar. 17 Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, “Ubana na aiki bar yanzu, ni ma ina yi.” 18 Don haka Yahudawa suka ƙara ɗokanta su kashe shi, ba wai don ya keta umarnin Asabar kaɗai ba, har ma don ya ce Allah Ubansa ne, wato yana daidaita kansa da Allah.

Dukkan Hukunci a Hannan Ɗan ya ke

19 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle, hakika, ina gaya muku, ‘Ɗan ba ya iya yin komai shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba na yi. Don duk abin da Uban ke yi, haka shi ɗan ma ke yi. 20 Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa ke yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, don ku yi al’ajabi. 21 Yadda Uba ke ta da matattu ya kuma raya su, haka ɗan ma ke rayad da wanda ya nufa. 22 Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yă danƙa dukkan hukunci a hannun Ɗan, 23 don kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda a ke girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan. 24 Lalle, hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, ya ke kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, don ya riga ya tsere wa halaka, ya kai ga rai madawwami.

25 “Lalle, hakika, ina gaya muku, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu. 26 Yadda Uba kansa ya ke tushen rai madawwami, haka ya ƙaddara wa ɗan shi ma kansa tushen rai madawwami ne. 27 Ya kuma ba shi ikon zartad da hukunci, saboda shi Ɗam Mutun ne. 28 Kada ku yi mamakin wannan, don lokaci na zuwa da duk waɗanda ke kaburbura za su ji muryatasa, 29 su kuma fito,waɗanda suka aikata nagarta su tashi, Tashin rai madawwami; waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, Tashin hukunci.

30 “Ba na iya yin komai ni kaɗai. Yadda aka umarce ni, haka na ke yin hukunci. Hukuncina kuwa na gaskiya ne, domin ba nufin kaina na ke bi ba, sai dai nufin wanda, ya aiko ni. 31 In na shaidi kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce. 32 Akwai wani mashaidina daban, na kuwa san shaidad da ya ke mini tabbatacciya ce. 33 Kun aika wajen Yohana, shi kuma ya shaidi gaskiya. 34 Duk da haka shaidad da na dogara da ita ba ta mutum ba ce. Na dai faɗi haka ne don ku sami ceto. 35 Shi fitila ne mai ci, kuma mai haske, kun kuwa yarda ku yi farinciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan. 36 Amma shaidad da ni na ke da ita ta fi ta Yohana ƙarfi. Domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da na ke yi, ai su ne shaidata a kan cewa Uba ne ya aiko ni. 37 Uban kuma da ya aiko ni shi kansa ya shaide ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ko ganin kamatasa. 38 Maganatasa kuwa ba ta zauna a zuciyarku ba, don ba ku gaskata. wanda ya aiko ba. 39 Kuna ta bincika Littattafai Tsarkaka, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne ke shaidata. 40 Duk da haka kun ƙi zuwa wurina ku sami rai madawwami. 41 Ba na karɓar girma wurin mutane. 42 Amma fa na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci. 43 Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, da shi za ku karɓa. 44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da ke karɓar girma a junanku, girman da ke daga Allah Makaɗaici kuwa ba kwa nemansa? 45 Kada ku zaci zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda ku ke dogaro da shi. 46 Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, don labarina ya rubuta. 47 In kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”

6

Mu’ujizar Ci da Mutun Dubu Biyar

Bayan haka sai Yesu ya haye Tafkin Galili, wato Tafkin Tibariya. 2 Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu’ujizan da ya ke yi ga marasa lafiya. 3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa. 4 To, Idin Ƙetarewa, wato idin Yahudawa, ya gabato. 5 Da Yesu ya ɗaga kai ya hango wani babban taro na doso shi, sai ya ce da Filibus, “Ina za mu sayo burodin da mutanen nan za su ci?” 6 Ya faɗi haka ne fa don ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi. 7 Filibus ya amsa masa ya ce, “Ai ko burodin dinari metan ma bai isa kowannensu ya sami kaɗan ba.” 8 Sai ɗaya daga cikin almajiransa, wai shi Andarawas, ɗan’uwan Siman Bitrus, ya ce masa, 9 “Ga wani ɗan yaro nan da burodi biyar na sha’ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?” 10 Yesu ya ce, “Ku ce da mutanen su zauna.” Wuri ne kuwa mai ciyawa. Sai mazaje suka zazzauna, su wajen dubu biyar. 11 Yesu ya ɗauki burodin, kuma bayan ya yi godiya ga Allah, sai ya rarraba wa waɗanda ke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su. 12 Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce da almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada komai ya ɓata 13 Sai suka tattara gutsattsarin burodin nan biyar na sha’ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu. 14 Da jama’a suka ga mu’ujizad da ya yi, sai suka ce, “Lalle wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya!”

15 Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su. ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sake janye jiki, ya koma kan dutsen shi kaɗai

Yesu ya yi Taftya Kan Ruwa

16 Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara tafkin. 17 Suka shiga jirgi, suka tasam ma haye tafkin zuwa Kafarnahum. A sa’an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna. 18 Sai tafkin ya fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da ke busawa. 19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu na tafiya kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita. 20 Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.” 21 Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nandanan sai ga jirgin a gaɓad da za su.

22 Washegari sai sauran taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka kiyaye ba wani jirgi a wurin, sai wani ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba sai almajiran ne kaɗai suka tafi. 23 Akwai kuwa wasu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da mutane suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi wa Allah godiya. 24 Sa’ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, sai su ma suka shiga ƙananan jiragen nan, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.

25 Da suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?” 26 Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle, hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu’ujizai ba, sai don kun ci burodin nan kun ƙoshi. 27 Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗam Mutun zai ba ku. Don shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.” 28 Sai suka ce masa, “Me za mu yi mu aikata ayyukan da Allah ke so?” 29 Yesu ya amsa musu ya ce, “Wannan shi ne aikin da Allah ke so, wato ku gaskata da wanda ya aiko.” 30 Sai suka ce masa, “To, wace mu’ujiza za ka yi mu gani mu gaskata ka? Me za ka iya yi? 31 Kakannin kakannimmu sun ci manna a jeji, yadda ya ke a rubuce, cewa, ‘Ya ba su burodi daga Sama su ci.’ 32 Sa’an nan Yesu ya ce musu, “Lalle, hakika, ina gaya muku, ba t Musa ne ya ba ku burodin nan daga Sama ba, Ubana ne ke ba ku hakikanin Burodi daga Sama. 33 Ai Burodin Allah shi ne mai saukowa daga Sama, mai ba duniya rai madawwami.” 34 Sai suka ce masa, “Ya Ubangiji, ka riƙa ba mu irin wannan burodi kullum mana!”

35 Yesu ya ce musu, “Ni ne Burodi mai ba da rai madawwami. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. 36 Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. 37 Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan. 38 Domin na sauko daga Sama, ba don im bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 39 Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in ya da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe. 40 Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda ke duban Ɗan, ya ke kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”

Burodi daga Sama

41 Sai fa Yahudawa suka yi masa gunaguni wai don ya ce, “Ni ne Burodin da ya sauko daga Sama.” 42 Suka ce, “Ashe wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda uwatasa da ubansa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga Sama’?” 43 Yesu ya amsa musu ya ce, “Kada ku yi gunaguni a junanku. 44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uba wanda ya aiko ni ne ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe. 45 A rubuce ya ke cikin Littattafan Annabawa, cewa, ‘Dukansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni. 46 Ba wai don wani ya taɓa ganin Uba ba, sai shi wanda ke daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban. 47 Lalle, hakika, ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwani. 48 Ni ne Burodi mai ba da rai madawwami. 49 Kakannin kakarminku sun ci manna a jeji, amma kuwa sun mutu. 50 Ga nan Burodi mai saukowa daga Sama, don kowa yă ci, ba kuwa zai mutu ba. 51 Ni ne Burodin rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Burodin nan, zai rayu har abada. Har ma Burodin da zan bayar naman jikina ne, don duniya ta sami rai madawwami.”

52 Sai Yahudawa suka ta da husuma a junansu, suna cewa, “Yaya mutumin nan zai iya ba mu naman jikinsa mu ci?” 53 Sai Yesu ya ce musu, “Lalle, hakika, ina gaya muku, im ba ku ci naman jikin Ɗam Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, babu rai madawwami a gare ku. 54 Duk wanda ke cin naman jikina, ya ke kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe. 55 Don naman jikina abinci ne na hakika, jinina kuma abin sha ne na hakika. 56 Duk wanda ke cin naman jikina, ya ke kuma shan jinina, yana dawwame game da ni, ni kuma game da shi. 57 Kamar yadda Rayayyen Uba ya aiko ni, na ke kuma rayuwa ta kan Uban, haka ma wanda ya ke ni ne abincinsa zai rayu ta kaina. 58 Wannan shi ne Burodin da ya sauko daga Sama, ba irin wanda kakannin kakanninku suka ci ba, duk da haka suka mutu. Duk mai cin Burodin nan zai rayu har abada.” 59 Wannan kuwa a cikin majami’a ya faɗa, sa’ad da ya ke koyarwa a Kafarnahum.

60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan magana mai makaki ce, wa zai iya jinta?” 61 Yesu kuwa, da ya ke ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato wannan ne ya zame muku abin takaici? 62 Yaya ke nan in kuka ga Ɗam Mutun na hawa inda ya ke dā? 63 Ai Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana koma!’. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai madawwanu. 64 Amma fa akwai wasunku da ba su ba da gaskiya ba.” Don tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi. 65 Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni sai ko Uba ya yarje masa.”

66 Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba. 67 Sai Yesu ya ce da Sha biyun, “Ku ma kuna so ku tafi ne?” 68 Siman Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai ke da maganar rai madawwami. 69 Mu kuwa mun gaskata, mun kuma tabbata kai ne Tsattsarkan nan na Allah.” 70 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, Ba ni na zaɓe ku ku Sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.” 71 Wato yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyoti, don shi ne zai bashe shi, ko da ya ke ɗaya daga cikin Sha biyun nan ne.

7

Yesu a Idin Bukkoki

Bayan haka sai Yesu ya riƙa zagawa a cikin ƙasar Galili, bai yarda ya zaga a ta Yahudiya ba, don Yahudawa na neman kashe shi. 2 Idin Bukkoki na Yahudawa kuwa ya gabato. 3 Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da ka ke yi. 4 Ai ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da ya ke kana yin waɗannan al’amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya.” 5 Domin ko da ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba. 6 Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacinku ne. 7 Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni tana ƙina, don na shaide ta a kan ayyukanta miyagu ne. 8 Ku dai ku tafi Idin. Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.” 9 Da ya faɗa musu haka, sai ya dakata a ƙasar Galili.

10 Bayan ’yan’uwansa sun tafi Idin kuwa, shi ma sai ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba. 11 Yahudawa na ta nemansa a wurin Idin suna cewa, “Ina ya ke ne?” 12 Taro kuma suka riƙa maganatasa ƙasa-ƙasa, wasu na cewa, “Mutun ne nagari.” Wasu kuma na cewa, “A’a, ai ɓad da jama’a yake.” 13 Amma ba wanda ya yi maganatasa a fili don tsoron Yahudawa.

14 Wajen tsakiyar Idin sai Yesu ya shiga Ɗakin lbada ya koyar. 15 Yahudawa suka yi mamakin abin, suka ce, “Yaya mutumin nan ya ke da karatu haka, ga shi kuwa bai taɓa koyo ba?” 16 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta wanda ya aiko ni ce. 17 Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwan nan ko ta Allah ce, ko don kaina na ke faɗa. 18 Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa ya ke yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi. 19 Ashe ba Musa ne ya ba ku Shari’a ba? Duk da haka ba mai kiyaye Shari’a a cikinku. Dom me ku ke neman kashe ni?” 20 Taron suka amsa suka ce, “Kana da iska! Wa ke neman kashe ka?” 21 Yesu ya amsa musu ya ce, “Aiki ɗaya kawai na yi, dukanku kuwa kuna mamakinsa. 22 Musa ya bar muku kaciya, (ba ko shi ya fara ba, tun kakannin kakanni ne), ga shi kuma ku kan yi wa mutun kaciya ko a ran Asabar ma. 23 To, in ana yi wa mutun kaciya ran Asabar don gudun keta Shari’ar Musa, kwa yi fushi da ni don na warkad da mutun sarai ran Asabar? 24 Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukuncin gaskiya.”

25 Sai wasu mutanen Urushalima suka ce, “Ashe ba wannan ne mutumin da su ke nema su kashe ba? 26 Ga shi nan kuwa yana magana a fili, ba su ce masa komai ba! Ya yiwu kuwa shugabanni sun san lalle wannan shi ne Almasihun? 27 Wannan kam mun san daga inda ya ke, amma sa’ad da Almasilum ya zo ba wanda zai san daga inda ya ke.” 28 Yesu na cikin koyarwa a Ɗakin Ibada, sai ya daga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda na ke. Ban fa zo don kaina ba. Wanda ya aiko ni na gaske ne, shi kuwa ba ku san shi ba. 29 Ni na san shi, don daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.” 30 Don haka suka nemi kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna. 31 Duk da haka mutane da yawa cikin taron sun gaskata da shi, suna cewa, “Sa’ad da Almasihu ma ya zo, zai yi mu’ujizai ne fiye da na mutumin nan?”

32 Farisiyawa suka ji taro na maganatasa ƙasa-ƙasa haka, sai manyan malamai da Farisiyawan suka aiki ma’aikatan Ɗakin Ibada su kamo shi. 33 Sai Yesu ya ce, “Saurana ɗan lokaci kaɗan tare da ku, sa’an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni. 34 Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba. Inda na ke kuwa ba za ku iya zuwa ba.” 35 Sai Yahudawa suka ce da juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin sauran al’umma ne, ya koya wa sauran al’umman? 36 Me kuma ya ke nufi da cewa, ‘Za ku neme ni amma ba za ku same ni ba?’ da kuma cewa, ‘Inda na ke ba za ku iya zuwa ba’?”

37 A ranar ƙarshe ta Idin, wato babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa yd zo gare ni yă sha. 38 Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda Nassi ya ce, ‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.’” 39 To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu Tsattsarka, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, don har yanzu ba a ba da Ruhu Tsattsarka ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.

40 Da jin maganan nan sai waɗansu daga cikin taron suka ce, “Hakika wannan annabin nan ne.” 41 Wasu kuwa suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma waɗansu suka ce, “Me? Ashe Almasihu daga ƙasar Galili zai fito? 42 Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami ya ke, ƙauyen da Dawuda ya zauna?” 43 Sai kuma rabuwa ta shiga tsakaninsu a kansa. 44 Wasunsu suka so kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi.

45 Daganan sai ma’aikatan Ɗakin Ibada suka koma wurin manyan malamai da Farisiyawa, su kuwa suka ce da su, “Dom me ba ku kawo shi ba?” 46 Sai ma’aikatan suka amsa suka ce, “A’a, ba muturnin da ya taɓa magana kamar wannan!” 47 Sai Farisiyawa suka amsa musu suka ce, “Af! Har ku ma am ɓad da ku ne? 48 Ashe akwai wani daga cikin shugabanni ko Farisiyawa da ya gaskata da shi? 49 Don waɗannan talakawan kam da ba su san Attaura ba, ai la’anannu. ne.” 50 Nikodimu kuwa da ya je wurinsa dā, yana kuwa ɗaya daga cikinsu, sai ya ce musu, 51 “Ashe Shari’armu ta kan hukunta mutun tun ba a ji daga bakinsa ba, an kuma san abin da ya ke ciki?” 52 Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalilen ne? Bincika mana ka gani, ai ba wani annabin da zai bayyana a ƙasar Galili.” 53 Sai kowa ya tafi gida.

8

Matar da aka Kama da Zina

Yesu kuwa sai ya hau Dutsen Zaitun. 2 Da sassafe kuma sai ya sake shiga Ɗakin Ibada. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu. 3 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka kawo wata mace da aka kama da zina. Da suka tsai da ita a tsaka, 4 sai suka ce masa, “Ya Shugaba, matan nan an kama ta ne suna cikin yin zina. 5 To, a cikin Attaura Musa ya umarce mu mu kashe irin waɗannan da jifa, kai kuwa me ka ce?” 6 Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar zarginsa. Amma sai Yesu ya sunkuya ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa. 7 Da suka dinga tambayatasa sai ya ɗaga, ya ce musu, “To, marar zunubi a cikinku ya fara jifanta da dutse.” 8 Sai ya sake sunkuyawa, ya yi ta rubutu a ƙasa. 9 Su kuwa da suka ji haka sai suka fita ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar tsaye a tsakiya. 10 Sai Yesu ya ɗaga, ya ce mata, “Uwargida, ina masu ƙarar taki? Ba wanda ya hukunta ki?” 11 Ta ce, “Babu, ya Ubangiji.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ƙi ba. Yi tafiyarki. Daga yau kada ƙi ƙara ɗaukar zunubi.”

Yesu Hasken Duniya

12 Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda ke bina ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma zai sami hasken rai madawwami.” 13 Saboda haka Farisiyawa suka ce masa, “Kanka ka ke wa shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.” 14 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai shaidata tabbatacciya ce, don na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni. 15 Ku kuna hukunci da son-zuciya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa. 16 Amma ko da zan yi hukunci, hukuncina na gaskiya ne, don ba ni kaɗai na ke ba, ni da Uba wanda ya aiko ni ne. 17 A cikin Attaurarku ma a rubuce ya ke, cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce. 18 Ni ne na ke shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.” 19 Saboda, haka sai suka ce masa, “Ina Uban naka ya ke?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko ni ko Ubana ba wanda kuka sani. Da kun san ni, da kun san Ubana ma.” 20 Ya faɗi wannan magana, ne a baitalmalin Ɗakin Ibada, lokacin da ya ke koyarwa a Ɗakin lbada. Duk da haka ba wanda ya kama shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.

21 Sai ya ƙara ce musu, “Zan yi tafiya, za ku kuwa neme ni, amma za ku mutu da zunubinku. Inda za ni kuwa ba za ku iya zuwa ba.” 22 Saboda haka sai Yahudawa suka ce, “Wato zai kashe kansa ke nan da ya ce, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba’?” 23 Sai ya ce musu, “Ku daga ƙasa ku ke, ni kuwa daga Sama na ke. Ku na duniyan nan ne, ni kuwa ba na duniyan nan ba ne. 24 Shi ya sa na ce muku za ku mutu da zunubanku. Don im ba kun gaskata cewa ni ne shi ba, za ku mutu da zunubanku.” 25 Sai suka ce da shi, “Kai wanene?” Yesu ya ce musu, “Me ya sa ma na ke magana da ku ne? 26 Akwai abubuwa da yawa da zan faɗa game da ku, in kuma hukunta. Amma shi wannan da ya aiko ni Mai gaskiya ne. Abin da na jiyo daga gare shi kuwa, shi na ke shaida wa duniya.” 27 Ba su gane cewa maganar Uba ya ke yi musu ba. 28 Sai Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka daga Ɗam Mutun, a sa’an nan ne za ku gane ni ne shi, kuma ba na yin komai ni kaɗai, sai dai yadda Uba ya koya mini haka na ke faɗa. 29 Wanda kuwa ya aiko ni na tare da ni, bai bar ni ni kaɗai ba, don koyaushe ina aikata abin da ya ke so.” 30 Sa’ad da Yesu ke faɗar haka, sai mutane da yawa suka gaskata da shi.

31 Sai Yesu ya ce da Yahudawan nan da suka gaskata shi, “In dai kun zauna kan maganata, hakika ku almajiraina ne. 32 Za ku san Gaskiya, Gaskiyar kuwa za ta ’yanta ku.” 33 Suka amsa masa suka ce, “Ai mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a ’yanta mu?”

34 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle, hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne. 35 Ai bawa ba ya ɗorewa a gida har abada, ɗa kuwa na ɗorewa. 36 In kuwa Ɗan ya ’yanta ku, za ku ’yantu, ’yantuwar gaske. 37 Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku. 38 Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana ne, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uban.”

39 Suka amsa masa suka ce, “Ai Ibrahim ne ubammu.” Yesu ya ce musu, “Da ku ’ya’yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi. 40 Ga shi yanzu kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyad da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba. 41 Ku kuna aikin da ubanku ke yi ne.” Suka ce masa, “Mu kam ba shegu ba ne, ubammu ɗaya ne, wato Allah.” 42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, don daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo don kaina ba, shi ne ya aiko ni. 43 Dom me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne. 44 Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa’ad da ya ke ƙarya, cinikinsa ya ke yi, don shi maƙaryaci ne, kuma uban ƙarairai. 45 Amma don ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni. 46 A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa ɗaukar zunubi? In kuwa gaskiya na ke faɗa, to, dom me ba kwa gaskata ni? 47 Na Allah ya kan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”

48 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kuma kana da iska.” 49 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana na ke girmamawa, ku kuwa wulakanta ni ku ke yi. 50 Ba ni na ke nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari’a. 51 Lalle, hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.” 52 Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam mun tabbata kana da iska. Ai Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada. 53 Wato ka fi ubammu Ibrahim ne, ya kuwa mutu? Annabawa ma sun mutu! Wa ka mai da kanka ne?” 54 Yesu ya amsa ya ce, “Im ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba a bakin komai ta ke ba. Ubana shi ne mai ɗaukaka ni, wanda ku ke cewa wai shi ne Allahnku. 55 Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da zan ce ban san shi ba, da sai in zama maƙaryaci kamar ku. Amma na san shi; ina kuma kiyaye maganatasa. 56 Ubanku Ibrahim ya yi farinciki matuƙa ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya yi murna.” 57 Sai Yahudawa suka ce masa, “Har yanzu ma ba ka kai shekara hamsin ba, wai kuwa har ka ga Ibrahim!” 58 Sai Yesu ya ce musu, “Lalle, hakika, ina gaya muku, tun kafin a haifi Ibrahim na ke.” 59 Don haka sai suka ɗebo duwatsu su jajjefe shi. Yesu kuwa ya ɓuya, ya fice daga Ɗakin Ibadar.

9

Wanda aka Haifa Makaho

Yesu na wucewa sai ya ga wani mutun da aka haifa makaho. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya ɗauki zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?” 3 Yesu ya amsa ya ce, “Ba wai don mutumin nan ko iyayensa sun ɗauki zunubi ba, sai don a nuna aikin Allah ne a kansa. 4 Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai dare zai yi sa’ad da ba mai iya aiki. 5 Muddar ina duniya ni ne hasken duniya.” 6 Da ya faɗi haka sai ya tofa yawu a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon, 7 ya ce masa, “Je ka ka wanke a Ruwan Siluwam,” (wato, Aikakke). Shi ke nan sai ya je ya wanke, ya komo yana gani. 8 Makwauta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, sai suka ce, “Ashe, ba wannan ne ya kan zauna yana bara ba?” 9 Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Wasu kuwa suka ce, “A’a, kai dai sun yi kama.” Shi kuwa sai ya ce, “Sosai ni ne!” 10 Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?” 11 Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da a ke kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke’. Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.” 12 Suka ce masa, “Ina ya ke?” Ya ce, “Ban sani ba.”

13 Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da ke makaho a da. 14 To, ran Asabar ne kuwa Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido. 15 Farisiyawa ma sai suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, sai na ke gani.” 16 Saboda haka waɗansu Farisiyawan suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah ya ke ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Wasu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu’ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu. 17 Sai suka sake ce da makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da ya ke kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai annabi ne.”

18 Yahudawa kam ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, kuma ya sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin, 19 suka tambaye su suka ce, “Wannan ɗanku ne da ku ke cewa an haife shi makaho? To, ta yaya ya ke iya gani yanzu?” 20 Sai iyayen nasa suka amsa suka ce, “Mun dai san wannan ɗammu ne, kuma makaho aka haife shi. 21 Amma ta yadda aka yi ya ke gani yanzu ba mu sani ba, ba mu ma san wanda ya buɗe masa idon ba. Ku tambaye shi, ai ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.” 22 Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla cewa kowa ya amsa cewa shi ne AImasihu, za a fisshe shi daga jama’a. 23 Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”

24 Sai suka sake kiran mutumin nan da ke makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam mun san mutumin nan mai zunubi ne.” 25 Sai ya amsa ya ce, “Ko mai zunubi ne, ni ban sani ba. Abu ɗaya kam na sani, dā ni makaho ne, yanzu kuwa ina gani.” 26 Sai suka ce masa, “Shin menene ya yi maka? Ta yaya ya buɗe maka ido?” 27 Ya amsa musu ya ce, “Haba! Na riga na faɗa muku, ba ku ji ba. Dom me ku ke son ku sake ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?” 28 Sai suka fāɗa shi da zagi suna cewa, “Kai ne dai almajirin wannan ɗin, mu kam almajiran Musa ne. 29 Mun dai sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan ba mu san ta inda ya fito ba.” 30 Sai mutumin ya amsa musu ya ce, “Kai, yau ga abin mamaki! Ashe ba ku san ta inda ya fito ba, ga shi kuwa ya buɗe mini ido! 31 Mun san Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda ke mai bautar Allah, ya ke kuma aikata nufinsa, Allah ya kan saurare shi. 32 Tun da aka fari duniya ba a taɓa jin wani ya buɗe idon wanda aka haifa makaho ba. 33 Da mutumin nan ba daga Allah ya fito ba, da babu abin da zai iya yi.” 34 Suka amsa masa suka ce, “Haba, kai da aka haifa a cikin bakin zunubi ne za ka koya mana?” Sai suka kore shi.

35 Yesu ya ji labari sun kore shi. Da ya same shi, sai ya ce, “Ka gaskata da ɗan Allah ko?” 36 Ya amsa ya ce, “Wanene shi, ya Shugaba, da zan gaskata da shi?” 37 Yesu ya ce masa, “Ai ka gan shi, shi ne ma mai magana da kai.” 38 Sai ya ce, “Ya Ubangiii, na ba da gaskiya”; ya kuma yi masa sujada. 39 Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, don waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda ke gani kuma su makance.” 40 Da Farisiyawan nan da ke tare da shi suka ii haka sai suka ce masa. “Wato mu ma makafin ne?” 41 Yesu ya ce musu, “Ai da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da ya ke kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.

10

Amintaccen Makiyayi

Lalle, hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken 10 tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu, to, shi ɓarawo ne, kuma dam-fashi ne. 2 Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne. 3 Mai tsaron ƙofar ya kan buɗe masa, tumakin kuma su kan saurari muryatasa, ya kan kama sunan nasa tumakin, ya kai su waje. 4 Bayan ya koro dukkan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye da shi, don sun san muryatasa. 5 Ba za su bi bako ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.” 6 Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.

7 Don haka Yesu ya sake ce da su, “Lalle, hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8 Duk waɗanda suka riga ni zuwa kan cewa su ne ni, ɓarayi ne, kuma ’yam-fashi ne, amma tumakin ba su kula da su ba. 9 Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta cikina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo. 10 Ɓarawo ya kan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne don su sami rai madawwami, su kuma same shi a yalwace. 11 Ni ne Amintaccen Makiyayi. Amintaccen Makiyayi kuwa shi ne mai ba da ransa maimakon tumakin. 12 Wanda ke ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso sai ya watsad da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure wasu, ya fasa sauran. 13 Ya gudu ne fa don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin. 14 Ni ne Amintaccen Makiyayi. Na san nawa, nawa kuma sun san ni, 15 kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina kuma ba da raina maimakon tumakin. 16 Ina kuma da waɗansu tumakin da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda. 17 Don wannan Uba ke ƙaunata, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma. 18 Ba mai karɓe mini rai, don kaina na ke ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarrni ne daga wurin Ubana.”

19 Saboda maganan nan fa sai rabuwa ta sake shiga tsakanin Yahudawa. 20 Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai mai iska ne, haukansa kawai ya ke yi. Dom me za ku saurare shi?” 21 Wasu kuwa suka ce, “A’a, wannan magana ai ba ta mai iska ba ce. Ashe iska ta iya buɗe wa makaho ido?”

Idin Tsarkakewa

22 Lokacin Idin Tsarkakewa ne kuwa a Urushalima, 23 kuma damuna ce, Yesu kuwa na zagawa a Shirayin Sulaimanu cikin Ɗakin Ibada, 24 sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu a cikin shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.” 25 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da na ke yi da sunan Ubana, su ke shaidata. 26 Amma ku ba ku gaskata ba, don ba kwa cikin tumakina. 27 Tumakin nan nawa su kan saurari muryata, na san su, suna kuma bina. 28 Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29 Ubana da ya ba ni su, shi ne mafificin komai, ba kuwa mai iya ƙwace su daga hannun Uban. 30 Ni da Uba ɗaya mu ke.”

31 Sai Yahudawa suka sake ɗebo duwatsu su jajjefe shi. 32 Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba; a kan wanne ne a cikinsu za ku jajjefe ni?” 33 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don saɓo, don kai, ga ka mutun, amma kana mai da kanka Allah.” 34 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce ya ke cikin Littattafanku Tsarkaka ba, cewa, ‘Na ce ku Allah ne?” 35 To, in waɗanda Maganar Allah ta zo musu ya ce da su Allah, (Nassi kuwa ba ya tashi), 36 kwa ce da wanda Uba ya keɓe a tsarkake, ya kuma aiko duniya, ‘Saɓo ka ke,’ don na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’? 37 Im ba ayyukan da Ubana ke yi na ke yi ba, to, kada ku gaskata ni. 38 Amma in su na ke yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane cewa Uba na game da ni, ni kuma ina game da. Uba.” 39 Sai suka sake ƙoƙarin kama shi, amma ya fice daga hannunsu.

40 Sa’an nan ya sake komawa ƙetaren Kogin Urdun, wurin da Yohana ya fara yin babtisma, ya zauna a can, 41 mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa; sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yohana bai yi wata mu’ujiza ba, amma duk abin da ya fada game da mutumin nan gaskiya ne.” 42 Nan fa mutane da yawa suka gaskata da shi.

11

Yesu ya Ta da Li’azaru daga Matattu

Wani mutun ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li’azaru na Baitanya, ƙauyen su Maryamu. da. ’yar’uwarta Marta. 2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Li’azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta. 3 To, sai ’yan’uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi wanda ka ke ƙaunan nan ba shi da lafiya.” 4 Da Yesu ya ji haka sai ya ce, “Wannan rashin lafiya ƙarshenta ba mutuwa ba ce, don a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka ɗan Allah ta kanta.”

5 Yesu kuwa na ƙaunar Marta da’yar’uwatata, da. kuma Li’azaru. 6 To, da ya ji Li’azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a wurin da ya ke. 7 Bayan haka sai ya ce da almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.” 8 Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa ke neman jifanka, za ka sake komawa can kuma?” 9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce wuni ɗaya ba? Kowa ke tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyan nan. 10 Amma kowa ke tafiya da dare ya kan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi.” 11 Ya faɗi haka, sa’an nan ya ƙara ce da su, “Aminimmu Li’azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.” 12 Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi ai zai warke.” 13 Alhali kuwa Yesu zancen mutuwar Li’azaru ya ke, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne. 14 Sai Yesu ya gaya musu a fili, “Li’azaru dai ya mutu. 15 Ina kuwa farinciki da ba na nan, saboda ku, don ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.” 16 Sai Toma, wanda a ke kira Ɗan Tagwaye, ya ce da ’yan’uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”

17 Da Yesu ya isa, sai ya tarar Li’azaru har ya kwana huɗu a kabari. 18 Baitanya kuwa kusa da Urushalima ta ke, misalin mil biyu. 19 Yahudawa da yawa sun zo yi wa Marta da Maryamu ta’aziyyar ɗan’uwansu. 20 Da jin Yesu na zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida. 21 Sai Marta ta ce da Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba. 22 Ko yanzu ma na san komai ka roƙi Allah, zai yi maka.” 23 Yesu ya ce mata, “Ɗan ‘uwanki zai tashi.” 24 Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a Tashin Matattu a ranar ƙarshe.” 25 Yesu ya ce mata, “Ai ni ne Tashin Matattu, ni ne kuma Rai madawwami. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu. 26 Wanda kuwa ke raye, ya ke kuma gaskatawa, da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?” 27 Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, shi wannan mai zuwa duniya.”

28 Da ta faɗi haka sai ta je ta kirawo ’yar’uwatata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Shugaban ya zo, yana kiranki.” 29 Ita kuwa da jin haka, sai ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa. 30 Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi. 31 Da Yahudawan da ke tare da ita cikin gida suna mata ta’aziyya suka ga Maryamu ta yi maza ta tashi ta fita, sai suka bi ta, suna zaton za ta kabarin ne ta yi kuka a can. 32 Da Maryamu ta iso inda Yesu ya ke ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.” 33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya. 34 Ya kuma ce, “Ina kuka kwantad da shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.” 35 Sai Yesu ya zub da hawaye. 36 Don haka Yahudawa suka ce, “Kai, dubi yadda ya ke ƙaunarsa!” 37 Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”

38 Sai Yesu ya sake nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin. 39 Yesu ya ce, “Ku kau da dutsen.” Sai Marta, ’yar’uwar mamacin, ta ce masa, “Ya Ubangiji, ai yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.” 40 Sai Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba ne, in kin ba da gaskiya za ƙi ga ɗaukakar Allah?” 41 Sai suka kau da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42 Ko dā ma na san koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama’ad da ke nan tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ne ka aiko ni.” 43 Da ya faɗi haka sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li’azaru, fito!” 44 Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu. a ɗaure da abin likkafani, fuskatasa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa ya tafi.”

Yahudawa sun Gaskata da Yesu

45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, sai suka gaskata da shi. 46 Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47 Don haka manyan malamai da Farisiyawa suka tara ’yam-majalisa, suka ce, “Shin me mu ke yi ne, har mutumin nan ya ke ta yin mu’ujizai da yawa haka? 48 Im fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama’armu.” 49 Amma ɗayansu, wai shi Kayafas, wanda ya ke shi ne Babban Malami a shekaran nan, sai ya ce musu, “Ku dai ba ku san komai ba. 50 Ba kwa lura, ai ya fiye muku mutun ɗaya ya mutu maimakon jama’a, da duk jama’a ta halaka.” 51 Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da ya ke shi ne Babban Malami a shekaran nan, ya yi faɗin cewa Yesu zai mutu maimakon jama’a, 52 ba ma maimakon jama’a kaɗai ba, har ma yi tattaro ’ya’yan Allah da ke warwatse ko’ina su zama ɗaya 53 Daga ran nan fa sai suka ƙulla su kashe shi.

54 Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba, amma sai ya tashi daga wurin, ya tafi ƙasar da ke bakin jeji, ya shiga wani gari wal shi Ifraimu. Nan ya zauna da almajiran.

55 Ana nan sai Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya gabato, mutane da yawa daga ƙauye suka tafi Urushalima su tsarkake kansu kafin Idin. 56 Suka yi ta neman Yesu, suna tsaitsaye a Ɗakin Ibada, suna ce da juna, “Me kuka gani? Zai zo Idin kuwa?” 57 Don dā ma manyan malamai da Farisiyawa sun yi umarni, cewa kowa ya san inda ya ke, ya zo ya faɗa su kama shi.

12

Maryamu ta Shafa wa Yesu Man Ƙanshi

Idin Ƙetarewa sauran kwana shida, sai Yesu ya zo Baitanya inda Li’azaru ya ke, wanda Yesu ya tasa daga matattu. 2 Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce ta yi hidima, Li’azaru kuwa na cikin masu ci tare da shi. 3 Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa’an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man. 4 Amma Yahuda Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato wanda zai bashe shi, ya ce, 5 “Me ya hana a sai da man nan dinari ɗari uku, a ba gajiyayyu kuɗin?” 6 Ya faɗi haka ne fa, ba wai don yana kula da gajiyayyu ba, a’a, sai dai don shi ɓarawo ne, kuma da ya ke jakar kuɗinsu na hannunsa ya kan riƙa taɓa abin da ke ciki. 7 Sai Yesu ya ce, “A ƙyale ta ta ajiye shi don tanadin ranar jana’izata. 8 Ai kullum. kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum ku ke tare da ni ba.”

9 Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari yana nan, sai suka zo, ba don Yesu kaɗai ba, har ma don su ga Li’azaru wanda ya tasa daga matattu. 10 Sai manyan malamai suka yi shawarar kashe Li’azaru, shi ma, 11 domin a dalilinsa Yahudawa da yawa su ke warewa, suna gaskatawa da Yesu.

12 Washegari babban taron da suka zo Idi, da suka ji Yesu na zuwa Urushalima, 13 sai suka ɗaɗɗauko tankar dabino suka firfita taryensa, suna ta da murya suna cewa, “Hosanna! Yabo ya tabbata ga Maizuwa da sunan Ubangiji, Sarkin Bani Isra’ila!” 14 Da Yesu ya sami wani ɗan jaki sai ya hau, yadda ya ke a rubuce, cewa,

15 “Kada ƙi ji tsoro, ya ke ’yar Sihiyona,
Ga Sarkinki na zuwa a kan aholakin jaki!”

16 Da fari almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan an ɗaukaka Yesu, sai suka tuna abin nan a rubuce ya ke game da shi, har ma an yi masa shi.

17 Taron da ke tare da shi sa’ad da ya kira Li’azaru yă fito daga kabari, ya tashe shi daga matattu, su suka riƙa shaidarwa da haka. 18 Shi ya sa taron suka fita taryensa, don sun ji ya yi mu’ujizan nan. 19 Sai Farisiyawa suka ce da juna, “Kun ga! Ba abin da muka iya! Ai duk duniya na bayansa.”

Yesu da wasu Helenawa

20 To, a cikin waɗanda suka zo Idin yin sujada akwai wasu Helenawa. 21 Sai suka zo wurin Filibus, mutumin Baitsaida ta ƙasar Galili, suka roƙe shi suka ce, “Maigida, muna bukatar mu gana da Yesu.” 22 Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawas, Andarawas kuma ya zo da Filibus, suka gaya wa Yesu. 23 Yesu ya amsa musu ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗam Mutun. 24 Lalle, hakika, ina gaya muku, im ba am binne ƙwayar alkama ta mutu ba, sai ta zauna ita kaɗai. Amma in ta mutu sai ta hayayyafa. 25 Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyan nan, ya kiyaye shi ke nan har ya zuwa rai madawwami. 26 Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda na ke kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa ke bauta mini, Uba zai girmama, shi.

27 “Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, ‘Ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci’? A’a, ai da ma na zo ne takanas don wannan lokacin. 28 Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.” 29 Da taron da ke tsaye a wurin suka ji muryar, sai suka ce, “An yi cida.” Wasu kuwa suka ce, “Wani mala’ika ne ya yi masa magana.” 30 Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi muryan nan ba, sai don ku. 31 Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan. 32 Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukkan mutane gare ni.” 33 Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwad da zai yi. 34 Sai taron suka amsa masa suka ce, “Mun gani a cikin Littattafai Tsarkaka cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗam Mutun? Wanene Ɗam Mutun ɗin?” 35 Sai Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan nan gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya cim muku. Mai tafiya cikin duhu bai san inda ya ke tafiya ba. 36 Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, don ku zama mutanen haske.”

Yesu ya faɗi haka, sa’an nan ya tafi ya ɓuyar musu.

Cikar faɗar Annabi Ishaya

37 Amma ko da ya ke ya sha yin mu’ujizai da yawa a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba; 38 don a cika faɗar Annabi Ishaya, cewa,

“Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabimmu?
Ga wa kuma aka bayyana ikon Ubangiji?”
39 Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba.
Don Ishaya ya sake cewa,
40 “Ya makantad da su, ya kuma taurarad da zuciyatasu,
Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci,
Har su juyo gare ni in warkad da su.”

41 Ishaya ya faɗi haka ne saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa. 42 Duk da haka da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama’a. 43 Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane a kan girmamawar Allah.

44 Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Wanda ke gaskatawa da ni, ba da ni ya ke gaskatawa ba, da wanda ya aiko ni ne. 45 Wanda kuma ke dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne. 46 Na zo duniya a kan ni haske ne, don duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu. 47 Kowa ya ji maganata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni ke hukunta shi ba. Gama ba don yi wa duniya hukunci na zo ba, sai dai don in ceci duniya. 48 Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi; maganad da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe. 49 Ba kuwa don kaina na yi magana. ba, Uban da ya aiko ni shi ne da kansa ya ba ni umarni kan abin da zan faɗa, da kuma maganad da zan yi. 50 Na kuma san umarnin nan nasa rai ne madawwami. Don haka abin da na ke faɗa ina faɗa ne daidai yadda Uba ya faɗa mini.”

13

Yesu ya Wanke Kafafun Almajiransa

Ana nan tun kafin Idin Ƙetare da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da ya ke ya ƙaunaci mutanensa da ke duniya, sai ya ƙaunace su har matuƙa. 2 Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sanya a zuciyar Yahuda Iskariyoti ɗan Siman yă bashe shi, 3 Yesu kuwa, da ya ke ya san Uba ya sanya komai a hannunsa, ya kuma san daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma, 4 sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko tawul ya yi ɗamara da shi. 5 Sa’an nan ya zuba ruwa a daro, ya fara wanke ƙafafun almajiran, yana shafe su da tawul ɗin da ya yi ɗamara da shi. 6 Sai ya zo kan Siman Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe kai ne za ka wanke mini ƙafa?” 7 Yesu ya amsa masa ya ce, “Yanzu kam ba ka san abin da na ke yi ba, amma daga baya za ka fahinta.” 8 Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai ba za ka wanke min ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “Im ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.” 9 Siman Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kadai ba, har ma da hannayena da kaina!” 10 Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke komai, sai ƙafafunsa kawai, don ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukkanku ba.” 11 Don ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukkanku ne tsarkakakku ba.”

12 Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sake kishingida, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku? 13 Kuna kirana Shugaba, kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka na ke. 14 Tun da ya ke ni Ubangijinku, kuma Shugabanku, har na wanke muku kafa, ashe ku ma ya kamata ku wanke wa juna. 15 Na yi muku ishara don ku ma ku yi yadda na yi muku. 16 Lalle, hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi. 17 In dai kun san wannan, kuna kuma aika tawa, ku masu farinciki ne. 18 Ba dukkanku na ke nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk don a cika Nassi ne, cewa, ‘Wanda mu ke ci akushi ɗaya ya haure ni.’ 19 Tun yanzu zan sanad da ku abu tun bai faru ba, don sa’ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi. 20 Lalle, hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na’am da duk wanda na aiko, ya yi na’am da ni ke nan. Wanda ya yi na’am da ni kuwa, to, ya yi na’am da wanda ya aiko ni.”

Yahuda Iskariyoti Maci Amana

21 Bayan Yesu ya faɗi haka sai ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle, hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 22 Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda ya ke. 23 Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu ke ƙauna, yana kishingiɗe gab da ƙirjin Yesu. 24 Sai Siman Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa ya ke?” 25 Shi kuwa da ke kishingiɗe haka gab da ƙirjin Yesu sai ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane? 26 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma ’yar loman nan im ba shi.” Da ya tsoma ’yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuda, ɗan Siman Iskariyoti. 27 Da karɓar ’yar loman nan sai Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi maza.” 28 Ammna cikin waɗanda ke cin abincin, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. 29 Har wasu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar Idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuda ne ke riƙe da jakar kuɗinsu. 30 Shi kuwa da karɓar ’yar lomar, sai ya fita; dare ne kuwa.

31 Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗam Mutun, aka kuma ɗaukaka Allah ta kansa. 32 Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga Zatinsa, nandanan kuwa zai ɗaukaka shi. 33 Ya ku ’ya’yana kanana, saurana ɗan lokaci kaɗan tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka na ke faɗa muku yanzu. 34 Sabon umarni na ke ba ku, shi ne, Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma ku ƙaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”

36 Siman Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina ne za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.” 37 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, dom me ba zan iya binka a yanzu ba? Ai zan ba da raina saboda kai.” 38 Yesu ya amsa ya ce, “Ashe za ka ba da ranka saboda ni? LaIle, hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka y imusun sanina sau uku.

14

Yesu Shi ne Hanya

Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A gidan Ubana akwai wurin zama da yawa. Da ba haka ne ba, da na faɗa muku, don zan tafi in shirya muku wuri. 3 In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, don inda na ke, ku ma ku zama kuna can. 4 Inda za ni kuwa kun san hanyar.” 5 Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ƙaƙa za mu san hanyar?” 6 Yesu ya ce masa, ni ne Hanya, ni ne Gaskiya, ni ne kuma Rai madawwami. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta kaina. 7 Da kun san ni, da kun san Uban ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.”

8 Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, nuna mana Uban bukatarmu ta biya ke nan.” 9 Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’ 10 Wato ba ka gaskata ba cewa ni game da Uba na ke, Uba kum game da ni? Maganad da na ke faɗa muku, ba don kaina na ke faɗa ba, Uba ne da ke game da ni ya ke yin ayyukansa. 11 Ku gaskata ni cewa ni game da Uba na ke, Uba kuma game da ni; ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan kansu.

12 “Lalle, hakika, ina gaya muku, duk wanda ke gaskatawa da ni, ayyukan da na ke yi shi ma haka zai yi. Har ma zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, don zan tafi wurin Uba. 13 Kuma duk ab da kuka roƙa da sunana zan yi, don a ɗaukaka Uban ta kan Ɗan. 14 Komai kuka roƙa da sunana, zan yi shi.

Ruhu Tsattsarka Mataimaki

15 “In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. 16 Ni ma za tambayi Uba, zai kuwa ba ku wani Mataimaki ya kasance tare d ku har abada. 17 Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iy samu, don ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam kun san shi, don yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.

18 “Ba zan bar ku da maraici ba, zan zo wurinku. 19 Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye na ke, ku ma za ku rayu. 20 A ran na ne fa za ku san cewa ni game da Uba na ke, ku kuma game da ni ni kuma game da ku. 21 Duk wanda ya san umarnina, ya ke kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa Ubana za ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, im bayyana kaina gare shi.” 22 Sai Yahuda (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangi, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?” 23 Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa ke ƙaunata, zai kiyaye maganata, Uban kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi 24 Wanda ba ya ƙaunata, ba ya kiyaye maganata. Maganad da ku ke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.

25 “Duk wannan na faɗa muku ne tun muna tare. 26 Amma Mataimaki, Ruhu Tsattsarka, wanda Uba zai aiko da sunana, shi ne zai koya muku komai, ya kuma tuna muku duk abin da n faɗa muku. 27 Na bar ku da aminci. Amincina na ke ba ku. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa ba na ke ba ku. Kada ku damu kada kuma ku ji tsoro. 28 Kun dai ji na ce muku zan tafi, kuma in dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, don kuwa Uban ya fi ni. 29 To, yanzu na faɗa muk tun bai faru ba, don sa’ad da ya faru ku ba da gaskiya. 30 Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, don mai mulkin duniyan nan na zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina; 31 sai dal don duniya tă san ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.

15

Icen Inabi na Hakika

Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne mai kula da itacen. 2 Kowane reshe a jikina da ba ya ’ya’ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin ’ya’ya kuwa ya kan tsarkake shi don ya ƙara haifuwa. 3 Ko yanzu ma ku tsarkakakku ne saboda maganad da na faɗa muku. 4 Ku zauna a jikina, ni kuma a jikinku. Kamar yadda reshen inabi ba ya iya ’ya’ya shi kaɗai, sai ko ya zauna a jikin itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a jikina. 5 Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a jikina, ni kuma a jikinsa, shi ne mai yin ’ya’ya da yawa. Don im ba game da ni ba, ba za ku iya yin komai ba. 6 Duk wanda bai zauna a jikina ba, sai a yad da shi kamar reshen can, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta a ƙone. 7 In kun zauna a jikina, maganata kuma ta zauna a zuciyarku, sai ku roƙi duk abin da ku ke so, za a kuwa yi muku. 8 Yadda a ke ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna ’ya’ya da yawa, ta haka kuma ku ke tabbata almajiraina. 9 Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunad da na ke muku. 10 In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunad da na ke muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunad da ya ke mini. 11 Na gaya muku haka don farincikina ya tabbata a zuciyarku, farincikinku kuma ya zama cikakke.

12 “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 Ba ƙaunad da ta fi haka ga mutane, wato mutun yd ba da ransa maimakon aminansa. 14 Ku aminaina ne in kuna yin abin da na urnarce ku. 15 Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangiiinsa ke yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, don na sanad da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana. 16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi ’ya’ya, ’ya’yanku kuma su tabbata; don komai kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku. 17 Na umarce ku haka don ku ƙaunaci juna.

18 “In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. 19 Da ku na duniya ne da duniya ta so abinta, amma saboda ku ba na duniya ba ne, kuma na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya ta ke ƙinku. 20 Ku tuna da maganad da na yi muku cewa, ‘Bawa ba ya fin ubangijinsa.’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. In da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma. 21 Duk wannan za su yi muku ne saboda sunana, don ba su san wanda ya aiko ni ba. 22 Ba don na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam ba su da wani hanzari a kan zunubinsu. 23 Wanda ya ƙi ni ya ƙi Ubana ma. 24 Ba don na yi ayyuka a cikinsu da ba, wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gan mu, kuma sun ƙi mu, ni da Ubana duka. 25 An yi wannan kuwa don a cika maganad da ke rubuce cikin Littattafansu Tsarkaka ne, cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’ 26 Amma sa’ad da Mataimaki ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, wato Ruhu na gaskiya, mai fitowa daga wurin Uba, shi ne zai shaide ni. 27 Ku ma shaidu ne, don tun farko ku ke tare da ni.

16

Ya Sanad da su Abubuwa iri-iri

Na faɗa muku duk wannan ne don in kawar muku da sanadin ƙosawa. 2 Za su fisshe ku daga jama’a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku sai ya zaci bautar Allah ya ke yi. 3 Za su yi haka ne kuwa don ba su san Uba ko ni ba. 4 Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, don in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.

“Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, don ina tare da ku. 5 Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ 6 Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙinciki ya cika zuciyarku. 7 Duk da haka ina gaya muku gaskiya, ya fiye muku in tafi, don im ban tafi ba, Mataimakin nan ba zai zo gare ku ba. In kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8 Sa’ad da kuwa ya zo zai faɗakad da duniya a kan zunubinta, da gaskiyar Allah, da kuma hukunci. 9 Wato, a kan zunubi, don ba su gaskata da ni ba; 10 a kan gaskiyar Allah, don za ni wurin Uba, ba kuwa za ku ƙara ganina ba; 11 kuma a kan hukunci, don an yanke wa mai mulkin duniyan nan hukunci.

12 “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba. 13 Sa’ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai nushe ku dukkan gaskiya; don ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanad da ku al’amuran da za su auku. 14 Zai ɗaukaka ni, don zai ɗauko daga cikin abin da ke nawa ya sanad da ku. 15 Duk abin da Uba ke da shi, nawa ne. Shi ya sa na ce zai ɗauko daga cikin abin da ke nawa ya sanad da ku.

16 “Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni.” 17 Sai waɗansu almajiransa suka ce da juna, “Me ya ke nufi da ce mana, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? da kuma cewa, ‘Don za ni wurin Uba’?” 18 Suka ce, “Me ya ke nufi da, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan’ din? Ai ba mu san abin da ya ke faɗa ba.” 19 Yesu kuwa ya san suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato, kuna tambayar juna ne abin da na ke nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’? 20 Lalle, hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma jaje, amma duniya za ta yi farinciki. Za ku yi baƙinciki, amma, baƙincikinku zai koma farinciki. 21 Idan mace na naƙuda ta kan sha wuya, don lokacin haifuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalad da ta sha, don murnar an sami baƙon duniya. 22 Haka ku ma yanzu ku ke tare da baƙinciki, amma zan sake ganinku, sa’an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farincikinku. 23 A ran nan ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle, hakika, ina gaya muku, komai kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana. 24 Har yanzu dai ba ku roƙi komai da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, don farincikinku ya zama cikakke.

25 “Duk wannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci na zuwa da ba zan kƙara faɗa muku da misalai ba, sai dai im ba ku labarin Uba a sarari. 26 A ran nan za ku yi roƙo da sunana. Ban kuwa ce muku zan tambayar muku Uba ba, 27 don shi Uban kansa na ƙaunarku, don kun ƙaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28 Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”

29 Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa ka ke magana a sarari, ba da misali ba! 30 Yanzu ne muka tabbata ka san komai, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.” 31 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe yanzu kun gaskata? 32 To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai na ke ba, don Uba. na tare da ni. 33 Na faɗa muku wannan ne don ku sami aminci game da ni. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku amince, ai na yi nasara da duniya.”

17

Addu’ar Yesu

Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya, Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka don Ɗan ya ɗaukaka ka, 2 tun da ka ba shi iko a kan dukkan ’yan’adan, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3 Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihun da ka aiko. 4 Na ɗaukaka ka a duniya da ya ke na cika aikin da ka ba ni in yi. 5 Yanzu kuma, ya Uba, ka ɗaukaka ni zuwa ga Zatinka da ɗaukakan nan da na ke da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasance.

6 “Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka. 7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abin da ka ba ni daga gare ka ya ke. 8 Don kuwa maganad da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni. 9 Su na ke tambayar wa. Ba duniya na ke tambayar wa ba, sai waɗanda ka ba ni, don su naka ne. 10 Dukkan nawa naka ne, duk naka kuma nawa ne, an kuma ɗaukaka ni a zukatansu. 11 Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya su ke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Tsattsarka, ka kiyaye su ta ƙarfin sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda mu ke. 12 Duk sa’ad da na ke tare da su, na kiyaye su ta ƙarfin sunanka da ka ba ni. Na kare su, ba kuwa waninsu da ya halaka, sai dai halakakken nan, don Nassi ya cika. 13 Amma yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, don farincikina ya zama cikakke a zukatansu. 14 Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15 Ba na tambayarka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kare su daga Mugun nan. 16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. 17 Ka keɓe su a tsarkake ta gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya. 18 Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya. 19 Saboda su ne na ke keɓe kaina a tsarkake, don su ma a keɓe su a tsarkake ta gaskiya.

20 “Ba kuwa waɗannan kaɗai na ke tambayar wa ba, bar ma masu gaskatawa da ni ta maganarsu, 21 don dukkansu su zama ɗaya; kamar yadda kai, ya Uba, ka ke game da ni, ni kuma na ke game da kai, haka su ma su kasance game da mu, don duniya ta gaskata cewa kai ne ka aiko ni. 22 Ɗaukakad da ka yi mini, ita na yi musu, don su zama ɗaya kamar yadda mu ke ɗaya, 23 ni game da su, kai kuma game da ni, don su zama ɗaya sosai da sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane cewa ka ƙaunace su kamar yadda ka ƙaunace ni. 24 Ya Uba, ina bukatar waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda na ke, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, don ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba. 25 Ya Uba mai gaskiya, duniya kam ba ta san ka ba, amma ni na san ka; waɗannan kuma sun san cewa kai ne ka aiko ni. 26 Na sanad da su sunanka, zan kuma sanar, don ƙaunad da ka yi mini tă kasance a zuciyatasu, ni ma in kasance game da su.”

18

An Kama Yesu

Bayan Yesu ya yi maganan nan, sai ya fita shi da almajiransa zuwa ƙetaren Rafin Kidurun, inda wani lambu ya ke, kuma ya shiga shi da almajiransa. 2 Yahuda ma wanda ya bashe shi ya san wurin, don Yesu ya saba haɗuwa da almajiransa a can. 3 Yahuda kuwa bayan ya ɗauko kamfanin soja, da wasu ma’aikatan Ɗakin lbada daga manyan malamai da Farisiyawa, sai suka zo wurin, riƙe da fitilu da jiniyoyi da makamai. 4 Yesu kuwa da ya san duk abin da zai same shi, sai ya yiwo gaba, ya ce musu, “Wa ku ke nema?” 5 Suka amsa masa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce musu, “Ni ne.” Yahuda kuwa da ya bashe shi na tsaye tare da su. 6 Da Yesu ya ce musu, “Ni ne,” sai suka ja da baya da baya, bar suka faɗi. 7 Sai ya sake tambayarsu, “Wa ku ke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.” 8 Yesu ya amsa ya ce, “Ai na gaya muku, ni ne. In kuwa ni ku ke nema, sai ku bar waɗannan su tafi.” 9 Wannan kuwa don a cika maganad da ya yi ne, cewa, “A cikin waɗanda ka ba ni ban ya da ko ɗaya ba.” 10 Siman Bitrus kuwa da ya ke yana da takobi, sai ya zaro ya kai wa bawan Babban Malamin sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. Sunan bawan Malkus. 11 Sai Yesu ya ce da Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha da ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”

Yesu a Gaban Hanana da Kayafas

12 Sai kamfanin soja da kwamandansu da ma’aikatan nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi, 13 suka tafi da shi wurin Hanana da fari, don shi surukin Kayafas ne, wanda ya ke shi ne Babban Malami a shekaran nan. 14 Kayafas kuwa shi ne ya yi wa Yahudawa shawarar cewa ya fiye musu mutun ɗaya ya mutu maimakon jama’a.

15 Sai Siman Bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajiri. Almajirin nan kuwa sananne ne ga Babban Malamin, sai ya shiga bar cikin gidan Babban Malamin tare da Yesu, 16 Bitrus kuwa ya tsaya a bakin ƙofa daga waje. Sai ɗaya almajirin da ke sananne ga Babban Malamin ya fita, ya yi magana da wadda ke jiran ƙofa, sa’an nan ya shigo da Bitrus. 17 Baranyad da ke jiran ƙofar kuwa ta ce da Bitrus, “Anya! Kai ma ba cikin almajiran mutumin nan ka ke ba?” Ya ce, “A’a, ba na ciki.” 18 To, bayi da ma’aikatan Ɗakin lbada kuwa sun hura wutar gawayi, don ana sanyi, suna tsaitsaye suna jin wutar. Bitrus ma na tsaye tare da su yana jin wutar.

19 Sai Babban Malamin ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwatasa. 20 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami’u da Ɗakin lbada inda Yahudawa duka kan taro. Ban faɗi komai a ɓoye ba. 21 Dom me ka ke tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai su sun san abin da na faɗa.” 22 Da ya faɗi haka, sai wani daga cikin ma’aikatan da ke tsaye kusa, ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa Babban Malamin?” 23 Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu, ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, dom me za ka mare ni?” 24 Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafas, Babban Malamin.

25 To, Siman Bitrus kuwa na tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?” Sai ya musa ya ce, “A’a, ba na ciki.” 26 Sai wani daga cikin bayin Babban Malamin, wato dangin wanda Bitrus ya ɗauke wa kunne, ya ce, “Ashe ban gan ka tare da shi a lambun ba?” 27 Sai Bitru ya sake yin musu. Nandanan kuwa sai zakara ya yi cara.

Yesu a Gabon Gwamna Bilatus

28 Daga wurin Kayafas kuma sai suka kai Yesu faɗar gwamna. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga faɗar ba, wai don kada su ƙazantu su kasa cin Jibin Ƙetarewa. 29 Saboda haka Bilatus ya fito wajensu, ya ce, “Wace ƙara kuka kawo ta mutumin nan?” 30 Sai suka amsa masa suka ce, “Yo, da wannan ba mai laifi ba ne, ai da ba mu bashe shi gare ka ba.” 31 Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa shari’arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai ba mu da ikon zartad da hukuncin kisa a kan kowa.” ’ 32 Wannan kuwa don a cika maganad da Yesu. ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwad da zai yi.

33 Sai Bilatus ya koma cikin faɗa, ya kira Yesu ya ce masa “Ashe kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” 34 Yesu ya amsa ya ce, “Wato wannan faɗarka ce, ko kuwa wasu ne suka ce da n haka a wurinka?” 35 Bilatus ya amsa ya ce, “Ahaf, ni Bayahude ne? Ai jama’arku da manyan malamai su ne suka bashe ka gare ni. Me ka yi?” 36 Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina sai su yi yaƙi kada a bashe ni ga Yahudawa. Amma hakika, mulkina ba daga nan ya ke ba.” 37 Sai Bilatus ya ce masa, “Wato ashe sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗan, ni sarki ne. Don haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, don in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya ya kan saurari muryata.” 38 Bilatus ya ce masa, “Wane abu ne wai shi gaskiya?”

Bayan ya faɗi haka, sai ya sake fitowa wurin Yahudawa, ya ce musu, “Ni kam ban same shi da wani laifi ba. 39 Amma dai kuna da wata al’ada, in Idin Ƙetarewa ya yi, na kan sakam muku mutun ɗaya. To, kuna so in sakam muku Sarkin Yahudawa?” 40 Sai suka sake ɗaukar kururuwa suna cewa, “A’a, ba wannan ba, sa dai Barabbas! Barabbas ɗin nan kuwa dam-fashi ne.

19

Soja sun yi Masa Kambi no Kaya

Sa’an nan Bilatus ya sa aka tafi da Yesu, aka yi masa bulala 2 Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a ka, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura. 3 Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!’ suna ta marinsa. 4 Sai Bilatus ya sake fitowa, ya ce da Yahudawa “Ga shi zan fito muku da shi, don ku san ban same shi da wani laifi ba.” 5 Sa’an nan Yesu ya fito, saye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan jar garurar. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin! “ 6 Da manyan malamai da ma’aikatan Ɗakin Ibada suka gan shi, sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “A giciye shi! A giciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku giciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba.” 7 Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai muna da Shari’a, bisa ga Shari’an nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.” 8 Da Bilatus ya ji maganan nan sai ya ƙara tsorata. 9 Ya sake shiga fada, ya ce da Yesu, “Daga ina ne ka ke?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10 Saboda haka Bilatus ya ce masa, “Ba za ka yi mini magana, ba? Ba ka san ni ne da ikon sakinka ko giciye ka ba?” 11 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina im ba am ba ka daga Sama ba; saboda haka wanda ya bashe ni gare ka ya fi ka zunubi.”

12 Kan wannan sai Bilatus ya nemi ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.” 13 Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna kan gadon shari’a, wurin da a ke kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata. 14 Ran nan kuwa Ranar Shirin Idin ƙetarewa ce, wajen ƙarfe shida na safe. Sai ya ce da Yahudawa, “Ga nan sarkinku!” 15 Sal suka ɗau kururuwa suna cewa, “A yi da shi! A yi da shi! A giciye shi!” Bilatus ya ce musu, “A! In giciye sarkinku?” Sai manyan malamai suka, amsa suka ce, “Mu ba mu da sarki sai Kaisar.” 16 Sa’an nan ya bashe shi gare su su giciye shi.

An Giciye Yesu

17 Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi da kansa ke ɗauke da giciyensa, har zuwa wurin da a ke kira Wurin Ƙoƙwan Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota. 18 Nan suka giciye shi, da kuma wasu mutum biyu tare da shi, ɗaya ta kowane gefe, Yesu kuwa na tsakiya. 19 Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan giciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.” 20 Yahudawa da yawa kuwa sun karanta wannan sanarwa, don wurin da aka giciye Yesu kusa da birni ne. An kuwa rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da kuma Helenanci. 21 Sai manyan malaman Yahudawa suka ce da Bilatus, “Kada ka rubuta Sarkin Yahudawa, sai dai ka rubuta, ‘A faɗatasa shi ne Sarkin Yahudawa.’” 22 Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta na rubuta ke nan.”

23 Bayan soja sun giciye Yesu, sai suka ɗebi tufafinsa, suka kasa kashi huɗu, kowane soja ya ɗauki kashi guda. Suka kuma ɗauki taguwatasa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta. 24 Sai suka ce da juna, “Kada mu tsaga ta, sai dai mu yi kuri’a a kanta, mu. ga wanda, zai ci.” Wannan kuwa don a cika Nassi ne, cewa,

“Sun raba tufafina a junansu,
Taguwata kuwa sai suka yi ƙuri’a a kanta.”

25 Haka fa sojan suka yi. To, kusa da giciyen Yesu kuwa da uwatasa, da ’yar’uwatata, da Maryamu matar Kilobas, da kuma Maryamu Magadaliya, suna tsaye. 26 Da Yesu ya ga uwatasa, da almajirin nan da ya ke ƙauna tsaye kusa, sai ya ce da uwatasa, “Iya, ga ɗanki nan!” 27 Sa’an nan ya ce da almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.

28 Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama komai, don a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” 29 To, akwai wani gora cike da ruwan tsami a titsiye a nan. Sai suka jiƙa soso da ruwan tsamin, suka soka a sandan izob, suka kai bakinsa. 30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan sai ya ce, “An gama!” Sa’an nan ya sunkuyad da kansa ya ba da ransa.

31 Da ya ke ran nan Ranar Shiri ce, kuma don kada a bar jikkuna a kan giciye ran Asabar (don wannan Asabar ɗin babbar rana ce), sai Yahudawa suka roƙi Bilatus a karya ƙafafunsu, a kuma ɗauke jikkunan. 32 Sai soja suka zo suka karya ƙafafun na farkon nan, da kuma na ɗayan da aka giciye tare da shi. 33 Amma da suka zo kan Yesu, suka kuma ga ya riga ya mutu, ba su ƙarya ƙafafunsa ba. 34 Sai dai ɗaya daga cikin sojan nan ya soke shi da mashi a kwiɓi, nandanan sai ga jini da ruwa suka gudano. 35 Wanda ya ganin nan kuwa ya ba da shaida kan haka, shaidatasa kuwa gaskiya ce, ya kuma san gaskiya ya ke faɗa, don ku ma ku ba da gaskiya. 36 Wannan kuwa don a cika Nassi ne, cewa, “Ba ƙashinsa ɗaya da za a karya.” 37 Wani Nassin kuma ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”

Jana’izar Yesu

38 Bayan haka sai Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda ya ke almajirin Yesu ne, amma a ɓoye don tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izinin ɗauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izini, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu. 39 Nikodimu kuma, wanda farkon zuwansa wurin Yesu da dad dare ne, sai ya zo da mur da al’ul a gauraye, wajen awo ɗari. 40 Sai suka ɗauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin linen game da kayan ƙanshin nan, bisa al’adar Yahudawa ta jana’iza. 41 A wurin da aka giciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma da wani sabon kabari wanda ba a taɓa kwantad da kowa ba. 42 Da ya ke Ranar Shiri ce ta Yahudawa, kuma kabarin na kusa, sai suka kwantad da Yesu a nan.

20

Taskin Yesu daga Matattu

To, a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya ta je kabarin da asuba, tun da sauran duhu, ta ga an kau da dutsen daga kabarin. 2 Sai ta yiwo gudu wurin Siman Bitrus da kuma ɗaya almajirin nan da Yesu ke ƙauna, ta ce musu, “An ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuwa san inda aka kwantad da shi ba.” 3 Sai Bitrus da ɗaya almajirin suka fita suka doshi kabarin. 4 Duka biyu sai suka ruga a guje, amma ɗaya almajirin sai ya tsere wa Bitrus, ya riga isa kabarin. 5 Yana dukawa yana leƙa ciki sai ya ga likkafanin linen a ajiye, amma fa bai shiga ba. 6 Sa’an nan Siman Bitrus ya zo a bayansa, sai kuwa ya shiga kabarin, ya ga likkafanin a ajiye, 7 mayanin kuma da ke kansa ba a ajiye tare da likkafanin ya ke ba, amma a naɗe shi kaɗai a waje ɗaya. 8 Sai ɗaya almajirin da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga, ya gani, ya kuma ba da gaskiya. 9 Don kafin lokacin nan ba su fahinci Nassin nan ba, cewa Ialle ne yă tashi daga matattu. 10 Sai almajiran suka koma gida.

11 Maryamu kuwa na tsaye a bakin kabarin daga waje, tana kuka. Tana cikin kuka sai ta duƙa ta leƙa kabarin, 12 sai ta ga mala’iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda da jikin Yesu ke kwance, ɗaya wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu. 13 Suka ce mata, “Uwargida, dom me ki ke kuka?” Ta ce musu, “Ai an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka kwantad da shi ba.” 14 Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ba ne. 15 Yesu ya ce mata, “Uwargida, dom me ki ke kuka? Wa ki ke nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, sai ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya min inda ka kwantad da shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.” 16 Yesu ya ce da ita. “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” (wato, “Ya Shugaba!”). 17 Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin ’Yan’uwana ki ce da su ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.” 18 Sai Maryamu Magadaliya ta je ta ce da almajiran, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma ce shi ya faɗa mata waɗannan abubuwa.

Ya Bayyana ga Almajiransa

19 A ran nan da magariba, ranar farko ta mako, kofofin ɗakin da almajiran ke ciki na ƙulle don tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce musu, “Salamu alaikum!” 20 Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da kwiɓinsa. Sai almajiran suka yi farinciki da ganin Ubangiji. 21 Sai Yesu ya sake ce da su, “Salamu alaikum! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma na aike ku.” 22 Da ya faɗi haka sai ya busa musu numfashinsa, ya ce musu, “Ku karɓi Ruhu Tsattsarka. 23 Duk waɗanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk waɗanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba su gafartu ba ke nan.” 24 Toma kuwa, ɗaya daga cikin Sha biyun nan, wanda a ke kira Ɗan Tagwaye, ba ya nan tare da su sa’ad da Yesu ya zo. 25 Sai sauran almajiran suka ce masa, “Mun ga Ubangiji.” Amma sai ya ce musu, “Im ban ga gurbin ƙusoshi a hannuwansa ba, na sa yatsana a gurbin ƙusoshin, na kuma sa hannuna a kwiɓinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.”

26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma na nan tare da su, kofofi na ƙulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salamu alaikum.” 27 Sa’an nan ya ce da Toma, “Sa yatsanka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.” 28 Toma ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangijina, kuma Allahna!” 29 Sai Yesu ya ce masa, “Wato saboda ka gan ni ka ba da gaskiya? Albarka tā tabbata ga waɗanda ba su gani ba, amma kuwa suka ba da gaskiya.”

Manufar Bishara

30 Yesu ya yi wasu mu’ujizai da yawa daban-daban a gaban almajiran, waɗanda ba a rubuta a littafin nan ba. 31 Amma an rubuta waɗannan ne, don ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta gaskatawa kuma ku sami rai madawwami albarkacin sunansa.

21

Yesu ya Sake Bayyana ga Almajiransa

Bayan haka sai Yesu ya sake bayyana kansa ga almajiran a bakin Tafkin Tibariya. Ga kuwa yadda ya bayyana kansa. 2 Siman Bitrus, da Toma wanda a ke kira ɗan Tagwaye, da Natana’ilu na Kana ta ƙasar Galili, da ’ya’yan nan na Zabadi, da kuma wasu almajiransa biyu, duk suna nan tare. 3 Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni su.” Suka ce masa, “Mu ma ma tafi tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi. Amma a daren nan ba su kama komai ba.

4 Gari na wayewa sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran ba su gane Yesu ba ne. 5 Sai Yesu ya ce da su, “Samari, kuna da kifi?” Suka amsa masa suka ce, “A’a.” 6 Ya ce musu, “Ku jefa taru dama da jirgin za ku samu.” Sai suka jefa, har suka ƙasa jawo shi don yawan kifin. 7 Sai almajirin nan da Yesu ke ƙauna ya ce da Bitrus, “Ubangiji ne dai!” Da Siman Bitrus ya ji ashe Ubangiji ne, sai ya yi ɗamara da taguwarsa, don a tuɓe ya ke, ya faɗa tafkin. 8 Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin ƙaramin jirgi, janye da tarun cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, kamar misalin yadi ɗari ne.

9 Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi a kai, da kuma burodi. 10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo wasu kifi a cikin waɗanda kuka kama yanzu.” 11 Sai Siman Bitrus ya hau jirgin, ya jawo tarun gaci, cike da manya-manyan kifaye, ɗari da hamsin da uku. amma duk da yawansu haka, tarun bai kece ba. 12 Sai Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Daga cikin almajiran kuwa ba wanda ya yi ƙarfin-halin tambayarsa ko shi wanene, don sun san Ubangiji ne. 13 Sai Yesu ya zo ya ɗauki burodin, ya ba su, haka kuma kifin. 14 Wannan ne fa zuwa na uku da Yesu ya bayyana ga almajiran bayan an tashe shi daga matattu.

Yesu da Siman Bitrus

15 Da suka karya kumallo sai Yesu ya ce da Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohana, ka fi waɗannan ƙaunata?” Ya ce masa, “I mana, ya Ubangiji, ka dai san ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon ’ya’yan tumakina.” 16 Ya sake faɗa masa, faɗa ta biyu, “Siman ɗan Yohana, kana ƙaunata?” Ya ce masa, “I mana, ya Ubangiji, ka dai san ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka kiyaye tumakina.” 17 Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Siman ɗan Yohana, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙinciki don a faɗan nan ta uku ya ce masa, “Kana, sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai ka san komai duka, ka kuwa san ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.” 18 Lalle, hakika, ina gaya maka, lokacin samartakarka ka kan yi wa kanka ɗamara ka tafi inda ka nufa; amma in ka tsufa, sai ka miƙe hannuwanka, wani ya yi maka ɗamara, ya kai ka inda ba ka nufa ba.” 19 (Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwad da Bitrus zai yi ya ɗaukaka, Allah). Bayan ya faɗi haka, sai ya ce masa, “Bi ni.”

20 Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu ke ƙauna na biye da su, wato wanda ya karkata a kishingiɗe gab da ƙirjin Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wanene zai bashe ka?” 21 Da Bitrus ya gan shi, sai ya ce da Yesu, “Ya Ubangiji, wannan fa?” 22 Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, menene naka a ciki? Kai dai bi ni!” 23 Saboda haka maganan nan ta bazu cikin ’Yan’uwa, cewa almajirin nan ba zai mutu ba. Alhali kuwa Yesu bai ce da shi ba zai mutu ba, ya dai ce, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, menene naka a ciki?”

24 Wannan shi ne almajirin da ke ba da shaida kan waɗannan al’amura, ya kuma rubuta su, mun kuwa san shaidatasa tabbatacciya ce.

25 Akwai wasu al’amura kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta kowannensu dai-dai da dai-dai, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.


AYYUKAN MANZANNI

1

Yesu na Bayyane gare su Kwana Arba’in

Ya Tiyofalas, tarihin nan na farko wanda na rubuta, ya shafi dukkan abubuwan da Yesu ya fara yi, da kuma waɗanda ya fara koyarwa, 2 har ya zuwa ranad da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta Ruhu Tsattsarka ga Manzannin da ya zaɓa. 3 Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuyatasa, tare da tabbatarwa masu yawa, kuma masu ƙarfi, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba’in, yana zancen al’amuran Mulkin Allah. 4 Sa’ad da ya ke tare da su, ya umarce su kada su tashi daga Urushalima, amma su jira cikar alkawarin nan da Uba ya yi—“wanda kuka ji daga bakina, 5 don Yohana kam da ruwa ya yi babtisma, amma kafin ’yan kwanaki ku da Ruhu Tsattsarka za a yi muku babtisma,” in ji Yesu.

6 Saboda haka da suka taru, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sake kafa wa Bani Isra’ila mulki?” 7 Ya ce musu, “Sanin lokatai da zamanai, da Uba ya ƙaddara cikin ikonsa, ba naku ba ne. 8 Amma za ku sami iko sa’ad da Ruhu Tsattsarka ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”

An Dauke Almasihu Sama

9 Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba. 10 Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi. 11 Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, dom me ku ke tsaye kuna duban Sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa Sama.”

12 Sai suka koma Urushalima daga dutsen nan da a ke kira Dutsen Zaitun, wanda ke kusa da Urushalima, wajen mil ɗaya. 13 Da suka shiga birnin, sai suka hau soro inda su ke zama, wato Bitrus, da Yohana, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Alfayas, da Siman Zaloti, da kuma Yahuda na Yakubu. 14 Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu’a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma ’yan’uwansa.

Jawabin Bitrus ga ’Yan’uwa

15 To, a kwanakin nan sai Bitrus ya miƙe tsaye cikin ’Yan’uwa, (wajen mutun ɗari da ashirin ne a taron), ya ce, 16 “Ya ku ’Yan’uwana, lalle ne a cika Nassin nan da Ruhu Tsattsarka ya faɗa a dā ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya yi wa masu kama Yesu jagaba. 17 Don an lasafta shi cikimmu dā, an kuma ba shi tasa hidima cikin aikin nan. 18 (To, shi mutumin nan, da ladan rashin gaskiyarsa ya sayi wani fili; sai ya fāɗi da ka, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zubo. 19 Wannan abu fa ya zama sananne ga dukkan mazauna Urushalima, har a ke kiran filin Akaldama da bakinsu, wato, Filin Jini.) 20 Don a rubuce ya ke cikin Zabura, cewa,

‘Giɗansa yă zama yasasshe,
Kada kowa ya zauna a ciki’.

Kuma,

‘Matsayinsa wani yă gada.’

21 Don haka, lalle sai wani daga cikin mutanen nan da ke tare da mu, duk lokacin da Ubangiji Yesu ke cuɗanya da mu, 22 tun daga babtismad da Yohana ya yi, har ya zuwa ranad da aka ɗauke shi daga wurimmu aka kai shi Sama, wato ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaidar tashinsa daga matattu, tare da mu.” 23 Sai suka nuna mutum biyu, Yusufu mai suna Barsaba, wanda aka yi wa laƙabi da Yustus, da kuma Matiyas. 24 Sai suka yi addu’a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa, 25 yă karɓi matsayi cikin hidiman nan da manzancin nan da Yahuda ya bauɗe wa, don ya tafi matabbacinsa.” 26 Sai suka yi musu ƙuri’a. sai Matiyas ya ci, aka kuma sa shi cikin Manzannin nan goma sha ɗaya.

2

Ba da Ruhu Tsattsarka

Da ranar Fentikos ta yi, duk suna tare wuri ɗaya, 2 kwatsam sai aka ji wani diri daga sama, kamar na busowar gawurtacciyar iska, ya cika duk gidan da su ke zaune. 3 Sai waɗansu harsuna kamar na wuta suka bayyana a gare su, suna yayyankuwa, suna sassauka a kan kowannensu. 4 Sai duk aka cika su da Ruhu Tsattsarka, kuma suka fara magana da wasu harsuna daban-daban, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.

5 To, a Urushalima kuwa a lokacin, akwai wasu Yahudawa masu bautar Allah daga ko’ina cikin duniya. 6 Da jin dirin nan kuwa, sai taron ya haɗe, ya ruɗe, don kowarmensu ya ji suna magana da bakin garinsu. 7 Sai suka yi hakun suka yi mamaki, suna cewa, “Ashe, duk masu maganan nan ba Galilawa ba ne? 8 Ƙaƙa kuwa kowannemmu ke ji da bakin garinsu a ke magana? 9 Ga mu kuwa Bartiyawa, da Madayanawa, da Ilamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya, 10 da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Turabus, har ma da baki daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, 11 da kuma Karitawa, da Larabawa, duk muna ji suna maganar manya-manyan al’amuran Allah da bakunan garuruwammu.” 12 Duk kuwa sai suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce da juna, “Me ke nan kuma?” 13 Amma sai wasu suka yi ba’a suka ce, “Giya suka sha suka yi tatul!”

Jawahin Bitrus a Ranar Fentikos

14 Amma sai Bitrus ya miƙe tare da Sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ya ku ’yan’uwana Yahudawa da dukkan mazauna Urushalima, ku kula da wannan, ku kuma saurari maganata. 15 Ai mutanen nan ba bugaggu ba ne yadda ku ke zato, tun da ya ke yauzu ƙarfe tara na safe ne kawai. 16 Wannan ai shi ne abin da Annabi Yo’ila ya faɗa, cewa,

17 ‘Allah ya ce,
A zamanin ƙarshe zai zamanto zan kwararo wa dukkan ’yan’adan Ruhuna.
’Ya’yanku maza da mata za su yi faɗin Maganar Allah,
Wahayi zai zo wa samarinku,
Dattawanku kuma za su yi mafarkai.
18 Hakika, har ma a kwanakin nan zan kwararo Ruhuna a kan bayina maza da mata,
Za su kuma yi faɗin Maganar Allah.
19 Zan nuna abubuwan al’ajabi a sararin sama,
Da mu’ujizai a nan ƙasa,
Wato, jini, da wuta, da kuma tunnuƙaƙƙen hayaƙi.
20 Za a mai da rana duhu,
Wata kuma jini,
Kafin Ranar Ubangiji ta zo,
Babbar ranan nan mai girma.
21 A sa’an nan ne zai zamanto kowa ya yi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto.’

Bayani kan Tashin Yesu daga Matattu

22 “Ya ku Bani Isra’ila, ku ii wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu’ujizai, da abubuwan al’ajabi, da alamomi waɗanda ya yi ta kansa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani— 23 shi Yesun nan fa, am ba da shi bisa ƙaddarar Allah da magabacin saninsa, ku kuwa kuka giciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi. 24 Amma Allah ya tashe shi bayan ya ɓalle masa ƙangin mutuwa, don ba shi yiwuwa mutuwa ta riƙe shi. 25 Don Dawuda ya yi faɗi game da shi ya ce,

‘Kullum hankalina na kan Ubangiji,
Yana hannuna na dama, don kada in jijjigu.
26 Saboda haka zuciyata ta yi fari, ina farinciki matuƙa.
Har ma raina zai kwanta ina amincewa,
27 Domin ba za ka ya da raina a Hades ba,
Ba kuwa za ka yarda Tsattsarkanka yo ruɓa ba.
28 Kā sanad da ni hanyoyin rai madawwami.
Za ka cika ni da farinciki ta zamana a Zatinka.’

29 Ya ’yan’uwa, na iya yi muku magana cikin amincewa game da kakammu Dawuda, cewa ya mutu, am binne shi, kuma kabarinsa na nan gare mu har ya zuwa yau. 30 To, da ya ke shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa cewa zai ɗora wani daga cikin zuriyatasa kan gadon sarautatasa, 31 sai ya hango, ya kuma yi faɗi kan tashin Almasihu daga matattu, cewa dai ba za a yashe shi a Hades ba, jikinsa kuwa ba zai ruɓa ba. 32 Yesun nan kam, Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga haka. 33 Da ya ke an ɗaukaka shi a hannun dama na Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Tsattsarka daga wurin Uba, sai ya kwararo abin nan da ku ke gani, ku ke kuma ji. 34 Ai ba Dawuda ne ya hau Sama ba, amma shi kansa ya ce,

‘Ubangiji ya ce da Ubangiiina,
Zauna a hannuna na dama,
35 Sai na sa ka take maƙiyanka.’

36 “Don haka sai duk Bani Isra’ila su sakankance, cewa shi Yesun nan da kuka giciye, Allah ya sanya shi Ubangiji, kuma Almasihu.”

Mutun Dubu Uku Sun Tuba

37 To, da suka ji haka, sai maganar ta soke su a zuci, suka ce da Bitrus da sauran Manzannin, “’Yan’uwa, me za mu yi?” 38 Sai Bitrus ya ce da su, “Sai ku tuba, a yi wa kowannenku babtisma, kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, don a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Tsattsarka. 39 Don alkawarin nan ku aka yi wa, ku da ’ya’yanku, da kuma dukkan manisanta, wato duk waɗanda Ubangiji Allahmmu ya kira.” 40 Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi, yana cewa, “Ku kuɓuta daga wannan karkataccen zamani.” 41 Waɗanda suka yi na’am da maganatasa kuwa aka yi musu babtisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutun wajen dubu uku. 42 Sai suka himmantu ga koyarwar Manzarmi, da tarayya da juna, da gutsuttsura burodi, da kuma yin addu’a.

43 Sai tsoro ya rufe kowa, aka kuma yi abubuwan al’ajabi da mu’ujizai da yawa ta kan Manzannin. 44 Dukkan masu ba da gaskiya suna tare, suna mallakar komai nasu gaba-ɗaya. 45 Suka sai da mallakatasu da kayansu, suka rarraba wa kowa kuɗin, gwargwadon bukatatasa. 46 Kowace rana kuma su kan riƙa zuwa Ɗakin Ibada da nufi ɗaya, suna gutsuttsura, burodi a gidajensu, suna cin abinci da farinciki ƙwarai, rai kwance, 47 suna yabon Allah, kowa na sonsu. Kowace rana kuma Ubangiji na ƙara musu waɗanda a ke ceto.

3

Bitrus ya Warkad da Gurgu

To, Bitrus da Yohana suna tafiya Ɗakin Ibada a lokacm addu’a, da ƙarfe uku na yamma, 2 sai ga wani mutun da aka haifa gurgu, ana ɗauke da shi. Kowace rana kuwa a kan ajiye shi a ƙofar ‘Ɗakin lbada, wadda a ke kira Kawatacciyar Ƙofa, don ya yi wa masu shiga Ɗakin Ibada bara. 3 Ganin Bitrus da Yohana suna shirin shiga Ɗakin lbada, sai ya yi musu bara. 4 Bitrus kuwa ya zuba masa ido, Yohana kuma haka, ya ce, “Dube mu.” 5 Sai kuwa duk hankalinsa ya koma kansu, da tsammanin samun wani abu a gunsu. 6 Amma sai Bitrus ya ce, “Kuɗi kam ba ni da su, amma abin da na ke da shi, shi zan ba ka. Albarkacin sunan Yesu Almasihu Banazare, yi tafiya.” 7 Sai Bitrus ya kama hannunsa na dama, ya tashe shi. Nan take ƙafafunsa da wuyan sawunsa suka yi ƙarfi. 8 Wuf, sai ya zabura, ya miƙe tsaye, ya fara tafiya, ya shiga Ɗakin Ibada tare da su, yana tafe, yana tsalle, yana kuma yabon Allah. 9 Duk mutane suka gan shi yana tafe yana yabon Allah. 10 Suka kuwa gane cewa shi ne mai zama a bakin Ƙawatacciyar Ƙofa ta Ɗakin Ibada yana bara. Sai mamaki ya rufe su, suna al’ajabi ƙwarai a kan abin da aka yi masa.

Sunan Yesu ne ya Warkad da Gurgun

11 Tun yana ɗafe da Bitrus da Yohana, sai duk jama’a suka dungumo wurinsu cikin shirayin da a ke kira Shirayin Sulaimanu, suka ruɗe don mamaki. 12 Da Bitrus ya ga haka, sai ya yi wa jama’a jawabi, ya ce, “Ya ku Bani Isra’ila, dom me ku ke mamakin wannan? Dom me kuma ku ke ta dubammu, sai ka ce da ikon kammu ne, ko kuwa don ibadarmu muka sa shi tafiya? 13 Allahn Ibrahim, da Isiyaku, da Yakubu, Allahn kakannimmu, shi ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi a gaban Bilatus, sa’ad da ya ƙudura zai sake shi. 14 Amma ku kuka ƙi Tsattsarkan nan, Mai gaskiya, kuka roƙa a sau muku mai kisankai, 15 kuka kuwa kashe Tushen Rai Madawwami, amma Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga haka. 16 To, sunansa ne, wato, albarkacin bangaskiya ga sunansa, shi ne ya ba mutumin nan da ku ke gani, kuka kuma sani, ƙarfi. Hakika, bangaskiyad da ke ta kan Yesu ita ta ba mutumin nan cikakkiyar lafiyan nan, a gaban idonku duka.

Faɗar Annabawa a kan Almasihu ta Cika

17 “To, yanzu ’yan’uwa, na san cewa cikin jahilci kuka yi haka, kamar yadda shugabanninku ma suka yi. 18 Amma ta haka Allah ya cika faɗar da ya riga ya yi ta bakin annabawa duka, cewa dai Almasihunsa zai sha wuya. 19 Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, don a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya rika wartsakad da ku, 20 ya kuma aiko da Almasihun da aka ƙaddara muku tun dā, wato Yesu, 21 wanda lalle ne ya zauna a Sama, har kafin lokacin nan na sabunta dukkan abubuwa, da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka. 22 Musa ma ya ce, ‘Ubangiji Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin ’yan’uwanku, kamar yadda ya tashe ni. Lalle ne ku saurari duk abin da ya faɗa muku. 23 Kuma zai zamana, duk wanda ya ƙi sauraron annabin nan, za a hallaka shi daga cikin jama’a.’ 24 Hakika dukkan annabawa da suka yi faɗin annabci, wato tun daga kan Samu’ila da waɗanda suka zo daga baya, duk sun yi faɗi a kan waɗannan kwanakin. 25 Ku ne tsatson annabawa, kuma ku ne magadan alkawarin da Allah ya yi wa kakanninku, da ya ce da Ibrahim, ‘Ta kan zuriyarka ne za a yi wa dukkan kabilun duniya albarka.’ 26 Da Allah ya taso da Baransa, gare ku ne ya fara aiko shi, don yi yi muku albarka ta juyo da kowarmenku ga barin muguntarsa.”

4

An Kama Bitrus da Yohana

Suna cikin yin magana da jama’a sai malamai da shugaban ma’aikatan Ɗakin Ibada da Sadukiyawa suka ji haushi ƙwarai, suka aukam musu, 2 wai don suna koya wa jama’a, suna tabbatad da tashi daga matattu, suna misali da Yesu. 3 Sai suka kama su, suka sa su a gidan waƙafi sai gobe, don magariba ta riga ta yi. 4 Amma da yawa cikin waɗanda suka ji wa’azin sun ba da gaskiya, har jimlarsu ta kai wajen mutun dubu biyar.

5 Washegari sai shugabanninsu da dattawansu da malamansu na Attaura suka taru a Urushalima, 6 tare da Hanana, Babban Malamin, da Kayafas, da Yohana, da Iskandari, da kuma duk waɗanda ke dangin Babban Malamin. 7 Da suka tsai da su a tsakiya, sai suka tuhume su, suka ce, “Da wane iko ne, ko kuwa da wane suna ne, kuka yi haka?” 8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Tsattsarka, ya ce musu, “Ya ku shugabannin jama’a, da dattawa, 9 in dai ana tuhumarmu ne yau a kan alherin da aka yi wa naƙastaccen mutumin nan, ta yadda aka warkad da shi, 10 to, sai ku sani ku duka, da kuma duk Bani Isra’ila, cewa da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka giciye, wanda kuma Allah ya tasa daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan ke tsaye a gabanku lafiyayye. 11 Wannan shi ne dutsen nan da ku magina kuka raina, shi ne kuwa ya zama babban dutsen harsashin gini. 12 Babu kuma samun ceto ga wani. Don ba wani suna duk duniyan nan da aka sako cikin mutane, wanda lalle ta kansa ne za mu sami ceto.”

An Sake Su

13 To, da suka ga ƙarfin-halin Bitrus da Yohana, suka kuma gane cewa marasa ilimi ne, talakawa, sai suka yi mamaki, suka kuwa shaida su kan dā suna tare da Yesu. 14 Amma da suka ga mutumin nan da aka warkar ɗin na tsaye tare da su, sai suka rasa hanyar yin musu. 15 Bayan sun umarce su su fita daga majalisa, sai suka yi shawara da juna, 16 suka ce, “Yaya za mu yi da mutanen nan? Don hakika sanannen abu ne ga dukkan mazauna Urushalima, cewa an yi wata tabbatacciyar mu’ujiza ta kansu, ba mu kuwa da halin musawa. 17 Amma don kada abin ya ƙara bazuwa a cikin mutane, sai mu yi musu togaciya, kada su kuskura su ƙara yi wa kowa magana, suna kama wannan sunan.” 18 Sai suka kirawo Manzannin, suka kwaɓe su kada su kuskura su yi wa kowa magana, ko su ƙara koyarwa suna kama sunan Yesu. 19 Amma sai Bitrus da Yohana suka mayar musu da jawabi suka ce, “To, in daidai ne a gun Allah mu fi jin taku da ta Allah, sai ku duba ku gani. 20 Don mu kam, ba yadda za a yi sai mun faɗi abin da muka ji, muka kuma gani.” 21 Da kuma suka daɗa yi musu togaciya, sai suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama’a, don dukkan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku. 22 Mutumin nan da aka yi wa mu’ujizan nan ta warkarwa kuwa ya ba shekara arba’in baya.

lkiliziya ta yi Addu’a ga Allah Gaba-ɗaya

23 Da aka sau su, sai suka tafi wurin mutanensu, suka ba su labarin duk abin da manyan malamai da shugabanni suka faɗa musu. 24 Su kuwa da jin haka, sai suka cira muryarsu ga Allah gaba-ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin Sama da ƙasa da. teku, da kuma dukkan abin da ke cikinsu, 25 wanda ta Ruhu Tsattsarka, ta bakin kakammu Dawuda baranka, ka ce,

‘Dom me sauran al’umma suka fusata?
Kabilu kuma suka riya al’amuran wofi?
26 Sarakunan duniya sun kafa daga,
Mahukunta kuma sun haɗa kai,
Suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’

27 Hakika a birnin nan Hirudus da Buntus Bilatus, da sauran al’umma da Bani Isra’ila, duk sun taru suna gāba da Baranka Tsattsarka Yesu, wanda ka shafa, tsattsarkar shafa, 28 don su yi dukkan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ikonka da nufinka. 29 Yanzu kuma ya Ubangiji, dubi wannan togaciyar tasu, ka yi wa bayinka baiwar yin Maganarka gabagaɗi ƙwarai da gaske, 30 kana kuma miƙo hannunka kana warkarwa, ana kuma yin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi albarkacin sunan Baranka Tsattsarka. Yesu.” 31 Bayan sun yi addu’a, sai wurin da su ke tattare ya raurawa. Sai duk aka cika su da Ruhu Tsattsarka, suka yi ta faɗar Maganar Allah gabagaɗi.

‘Yan Ikiliziya sun Riƙi Komai Nasu Baki-ɗaya

32 To, duk taron da suka ba da gaskiya kuwa mifinsu ɗaya ne, ra’ayinsu ɗaya, ba kuma waninsu da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, sai dai komai nasu ne baki-ɗaya. 33 Manzannin kuma suka yi shaida da tabbatarwa mai ƙarfi kan tashin Ubangiji Yesu daga matattu. Alheri mai yawa na tare da kowannensu, 34 har ba wani miskini cikinsu ko ɗaya, don duk masu gonaki ko gidaje sun sai da su, 35 sun kawo kuɗin sun ajiye gaban Manzarmi, an kuwa rarraba wa kowa gwargwadon bukatarsa. 36 Ana cikin haka sai Yusufu, wani Balawiye, asalinsa mutumin tsibirin Kubrus, wanda Manzannin ke kira Barnabas, (wato, Mai ƙarfafa gwiwa), 37 ya sai da wata gonatasa, ya kawo kuɗin ya ajiye a gaban Manzannin.

5

Munafuncin Hananiya da Safiratu

Amma wani mutum mai suna Hananiya, da matatasa Safiratu, ya sai da wata mallakatasa, 2 sai ya ɓoye wani abu daga cikin kuɗin, da sanin matatasa, ya kawo shashin kurum ya ajiye a gaban Manzanni. 3 Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Tsattsarka ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga cikin kuɗin gonar? 4 Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar kuma, kuɗin ba halalinka ba ne? Ta ƙaƙa ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai ba mutun ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa.” 5 Da jin wannan magana sai Hananiya ya faɗi ya mutu. Duk waɗanda suka ji kuwa, sai matsanancin tsoro ya rufe su. 6 Samari suka, taso, suka sa shi a likkafani, suka ɗauke shi suka fita da shi, suka je suka binne shi.

7 Bayan misalin sa’a uku sai matatasa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba. 8 Sai Bitrus ya ce mata, “Gaya min, shin kam haka kuka sai da gonan nan?” Sai ta ce, ‘I, haka ne.” 9 Amma sai Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ƙi su fita da ke.” 10 Nan take sai ta faɗi a gabansa, ta mutu. Da dai samarin suka shigo suka iske ta matacciya, sai suka ɗauke ta suka fita da ita, suka binne ta a jikin mijinta. 11 Sai matsanancin tsoro ya rufe dukkan ikiliziyar, da kuma dukkan waɗanda suka ji labarin wadannau abubuwa.

12 To, an yi mu’ujizai da abubuwan al’ajabi masu yawa cikin mutane ta hannun Manzarmi. Dukkansu kuwa su kan hallara gabaɗaya a Shirayin Sulaimanu. 13 Amma cikin sauran mutanen ba wanda ya yi ƙarfin-halin shiga cikinsu, duk da haka kuwa jama’a na girmama su. 14 Masu ba da gaskiya sai ƙaruwa su ke ta yi ga Ubangiji fiye da dā, jama’a masu yawan gaske maza da mata. 15 Har ma ya kai ga suna fito da marasa lafiya titi-titi, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi, don in Bitrus ya zo wucewa, ko da inuwatasa ma ta bi ta kan wasunsu. 16 Mutane kuwa suka yi ta taruwa daga garuruwan da ke kewayen Urushalima, suna ta kawo marasa lafiya da waɗanda baƙaƙen aljannu ke wahalshe su dukkansu kuwa aka warkad da su.

Mala’ika ya Ɓude Kofolin Kurkuku

17 Amma sai Babban Malamin ya taso, da duk waɗanda ke tare da shi, wato ɗariƙar Sadukiyawa, suna kishi gaya, 18 sai suka kama Manzannin, suka sa su kurkuku. 19 Amma da dad dare sai wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce, 20 “Ku tafi, ku tsaya cikin Ɗakin lbada, ku sanad da jama’a duk maganar wannan rai madawwami.” 21 Da suka ji haka sai suka shiga Ɗakin lbada da sassafe, suna koyarwa.

To, sai Babban Malamin ya fito, shi da waɗanda ke tare da shi, suka kira majalisa, da dukkan shugabannin Bani Isra’ila, suka aika kurkuku a kawo su. 22 Amma da ma’aikatan Ɗakin lbada suka je, ba su same su a kurkukun ba, sai suka dawo suka ba da labari, suka ce, 23 “Mun iske kurkukun a ƙulle sosai, masu gadi kuma na gadi a bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka tarar ba kowa a ciki.” 24 To, da shugaban ma’aikatan Ɗakin Ibada da manyan malaman suka ji haka, sai suka ruɗe ƙwarai game da su, suka rasa inda abin zai kai. 25 Sai wani ya zo ya ce musu, “Ai ga shi, mutanen nan da kuka sa a kurkuku suna nan tsaye a Ɗakin lbada suna koya wa jama’a.” 26 Sai shugaban ma’aikatan Ɗakin Ibada da ma’aikatan suka je suka kawo Manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama’a su jajjefe su da duwatsu.

Bitrus ya Sake yin Shaida a kan Tashin Yesu

27 Da suka kawo su, sai suka tsai da su gaban majalisar. Sai Babban Malamin ya tambaye su, 28 ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku dafa mana alhakin jinin mutumin nan.” 29 Amma sai Bitrus da Manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutun. 30 Allahn kakannimmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe ta kafe shi a jikin gungume. 31 Shi ne Allah ya ɗaukaka ga hannun damansa, Shugaba kuma Maceci, don ya buɗe wa Bani Isra’ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu. 32 Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al’amura, haka kuma Ruhu Tsattsarka, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”

33 Da suka ji haka, sai suka fusata ƙwarai da gaske, suka so su kashe su. 34 Amma sai wani Bafarisiye, wai shi Gamaliyal, masanin Attaura, wanda duk jama’a ke girmamawa, ya miƙe cikin majalisa, ya yi umarni a fid da mutanen nan waje tukuna. 35 Sa’an nan ya ce da su, “Ya ku Bani Isra’ila, ku kula fa da abin da ku ke niyyar yi wa mutanen nan. 36 Shekarun baya wani mutun ya ɓullo, wai shi Tudas, yana mai da kansa wani abu, wajen mutun arbaminya kuma suka bi shi; amma sai aka kashe shi, mabiyansa kuwa aka watsa su, suka lalace. 37 Bayansa kuma, lokacin ƙirgen mutane, wani wai shi Yahuda Bagalile ya ɓullo, ya zuga wasu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya halaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su. 38 To, yanzu ma. ina gaya muku, ku fita sha’anin mutanen nan, ku ƙyale su. Idan dai niyyatasu ko aikinsu na mutun ne, ai zai rushe, 39 amma in na Allah ne, ba dama ku iya rushe su. Sai ma a same ku kuna gāba da Allah.”

40 Sai suka bi shawaratasa, da kuma suka kirawo Manzannin, sai suka yi musu dūka, suka kwaɓe su kada su ƙara magana da sunan Yesu, sa’an nan suka sake su. 41 To, sai suka tashi daga gaban majalisar, suna farinciki a kan an ga sun isa su sha wulakanci saboda sunanYesu. 42 Kowace rana kuwa, ko a Ɗakin lbada ko a gida, ba su daina koyarwa da yin Bishara cewa Yesu shi ne Almasihu ba.

6

Zaɓen Mutum Bakwai don Aikin Ikiliziya

To, a kwanakin nan da yawan masu bi ke karuwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni, domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, wajen rabon gudummawa kowace rana. 2 Sai Sha biyun nan suka kirawo duk jama’ar masu bi, suka ce, “Ai bai kyautu ba mu mu bar wa’azin Maganar Allah, mu shagala a kan sha’anin abinci. 3 Saboda haka, ’Yan’uwa, sai ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku, waɗanda a ke yaba wa, cike da Ruhu Tsattsarka da kuma hikima, waɗanda za mu ɗanka wa wannan aiki. 4 Mu kuwa sai mu nace da yin addu’a da kuma koyad da Maganar Allah.” 5 Abin da suka faɗa kuwa ya kayatad da jama’a duka. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da ke cike da bangaskiya da Ruun Tsattsarka, da Filibus, da Burukoras, da Nikano, da Timan, da Barminas, da Nikolas mutumin Antakiya, wanda dā ya shiga Yahudanci. 6 Waɗannan ne aka gabatar gaban Manzannin. Bayan sun yi addu’a kuma, sai suka ɗora musu hannu.

7 Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka ta ke yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ƙaruwa ya ke yi ƙwarai da gaske, malamai masu yawan gaske kuma suka yi na’am da Bangaskiyan nan.

An Kama Ishfanus

8 To, Istifanus, cike da rahamar Allah da ikon Ruhu Tsattsarka, ya yi ta yin manya-manyan al’ajuba da mu’ujizai a cikin jama’a. 9 Sannan waɗansu na majami’ar da a ke kira majami’ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, sai suka tasam ma Istifanus da muhawara. 10 Amma ko kaɗan ba dama su iya yi masa musu, don ya yi magana bisa hikima, Ruhu na iza shi. 11 Sai suka zuga mutane a asirce, su kuwa suka ce, “Mun ji shi yana zagin Musa, yana saɓon Allah.” 12 Ta haka suka ta da hankalin jama’a, da shugabanni, da malaman Attaura, su kuma suka aukam masa, suka kama shi, suka kawo shi gaban majalisa. 13 Sai suka gabatad da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe Tsattsarkan Wurin nan, da kuma Shari’ar Musa, 14 don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al’adun da Musa ya bar mana.” 15 Da duk waɗanda ke zaune a majalisar suka zura masa ido, sai suka ga fuskatasa kamar ta mala’ika ta ke.

7

Istifanus Ya Ba Da Hujjojinsa

Sai Babban Malamin ya ce, “Ashe haka ne?” 2 Sai Istifanus ya ce, “Ya ku ’yan’uwa da shugabanni, ku saurare ni. Allah Maɗaukaki ya bayyana ga kakammu Ibrahim, sa’ad da ya ke ƙasar Bagadaza, tun bai zauna a Harana ba, 3 ya ce masa, ‘Tashi daga ƙasarku, daga kuma cikin ’yan’uwanka, ka je ƙasad da zan nuna maka.’ 4 Sai ya tashi daga ƙasar Kaldiyawa, ya zauna a Harana. Daga can kuma, bayan mutuwar tsohonsa, sai Allah ya kawo shi ƙasan nan da yanzu ku ke zaune. 5 Amma kuwa shi kansa bai ba shi gadonta ba, ko da taki ɗaya, sai dai ya yi masa alkawari zai mallakar masa ita, shi da zuriyar bayansa, ko da ya ke ba shi da ɗa a lokacin. 6 Abin da Allah ya faɗa kuwa shi ne, zuriyar Ibrahim za su yi baƙunci a wata ƙasa, mutanen ƙasar kuwa za su bautad da su, su kuma gwada musu tasku bar shekara arbaminya. 7 ‘Har wa yau kuma,’ Allah ya ce, ‘kabilad da za su bauta wa, ni zan hukunta ta, bayan haka kuma za su fito su bauta mini a wannan wurin.’ 8 Ya kuma yi masa alkawari game da kaciya. Ta haka, da Ibrahim ya haifi Isiyaku, sai ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Isiyaku kuma ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi kakannimmu sha biyun nan.

9 “Kakannin nan kuwa, da ya ke suna kishin Yusufu, sai suka sai da shi, aka kai shi Masar. Amma Allah na tare da shi, 10 ya kuma tsamo shi daga dukkan wahalatasa, ya ba shi farinjini da hikima a gun Fir’auna Sarkin Masar, shi kuwa ya naɗa shi gwamnan Masar, ya kuma ɗanka masa jama’ar gidansa duka. 11 To, sai wata yunwa ta auku a dukkan ƙasar Masar da ta Kan’ana, game da matsananciyar wahala, har kakannimmu suka rasa abinci. 12 Amma da Yakubu ya ji akwai alkama a Masar, sai ya aiki kakannimmu tafiyar farko. 13 A tafiyarsu ta biyu Yusufu ya sanad da kansa ga ’yan’uwansa, asalinsa kuma ya sanu ga Fir’auna. 14 Sai Yusufu ya aika wa ubansa Yakubu yă zo, da kuma dukkan ’yan’uwansa, mutun saba’in da biyar. 15 Sai Yakubu ya taho Masar. A can ma ya mutu, shi da kakannimmu. 16 Sai aka ɗebo su aka mai da su Shakima, aka sanya su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗin azurfa a wurin ’ya’yan Hamur a nan Shakima.

17 “Amma da lokacin cikar alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim ya gabato, sai jama’ar suka ƙaru, suka yawaita ƙwarai a ƙasar Masar, 18 har aka yi wani sarki a Masar, wanda bai san kowanene Yusufu ba. 19 Wannan sarki kuwa ya cuci kabilarmu, yana gwada wa kakannimmu tasku, yana sawa a ya da jariransu, don kada su rayu. 20 A lokacin nan ne aka haifi Musa, yaro kyakkyawan gaske. Sai aka rene shi wata uku a gidan ubansa. 21 Da aka ya da shi, sai ’yar Fir’auna ta ɗauke shi tallafinta, ta goya shi kamar ɗanta. 22 Sai aka karantad da Musa dukkan ilimin Misirawa, shi kuwa mutun ne mai ƙwaƙƙwarar magana, mai kuma kwazo.

23 “Yana gab da cika shekara arba’in ke nan, sai ya faɗo masa a rai yă je ya gano ’yan’uwansa Bani Isra’ila. 24 Da ya ga ana cutar ɗayansu, sai ya tare wa wanda a ke wulakantawa, ya rama masa, ya buge Bamisiren, ya mutu. 25 Ya zaci ’yan’uwansa sun gane cewa ta hannunsa ne Allah ke kuɓutad. da su. Amma ba su gane ba. 26 Washegari kuma waɗansu na faɗa, sai ga shi, ya nemi shirya su, ya ce, ‘Haba jama’a, ku ’yan’uwa ne fa, dom me ku ke cutar juna?’ 27 Amma sai mai cutar ɗan’uwan nasa ya ture Musa, ya ce, ‘Wa ya sa ka shugaba, kuma alkali a kammu? 28 Wato kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamisiren nan na jiya?’ 29 Da jin wannan magana sai Musa ya gudu ya yi baƙunci a ƙasar Maɗayana, inda ya haifi ’ya’ya biyu maza.

30 “To, bayan shekara arba’in, sai wani mala’ika ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a wata sarƙaƙiya a jejin Dutsen Sina. 31 Da Musa ya ga haka, sai ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya matso don ya duba, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce, 32 ‘Ni ne Allahn kakamunka, Allahn Ibrahim da Isiyaku da Yakubu.’ Sai jikin Musa ya ɗauki rawa, bai kuma iya ƙarfin-halin dubawa ba. 33 Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Tuɓe takalminka, don wurin da ka ke tsayen nan tsattsarkan wuri ne. 34 Hakika, na ga wulakancin da a ke yi wa mutanena da ke Masar, na ji nishinsu, na kuma sauko in cece su. To yanzu, sai ka zo in aike ka Masar.’

35 “To, shi Musan nan da suka ƙi, suna cewa, ‘Wa ya sa ka shugaba kuma alkali?’ shi ne Allah ya aiko shugaba, kuma mai ceto, ta kan mala’ikan nan da ya bayyana gare shi a sarƙaƙiyan nan. 36 Shi ne kuwa ya fito da su, bayan ya yi abubuwan al’ajabi da mu’ujizai a ƙasar Masar, da Bahar Maliya, da kuma cikin jeji, har shekara arba’in. 37 Wannan shi ne Musan da ya ce da Bani Isra’ila, ‘Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin ’yanuwanku, kamar yadda ya tashe ni.’ 38 Shi ne kuma wanda ke cikin ikiliziyan nan a jeji tare da mala’ikan da ya yi masa magana, a Dutsen Sina, kuma tare da kakannimmu. Shi ne kuma ya karɓo rayayyiyar magana don ya kawo mana. 39 Amma kakannimmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ture shi, zuciyatasu ta koma ƙasar Masar. 40 Suka ce da Haruna, ‘Ka yi mana gumakan da za su yi mana jagaba, don Musan nan kam da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya auku gare shi ba.’ 41 A lokacin nan sai suka ƙera ɗam maraki, suka yanka wa gunkin nan hadaya, suka riƙa farinciki da aikin da suka yi da hannunsu. 42 Saboda haka sai Allah ya juya musu baya, ya sallama su ga bautar taurari, yadda ya ke a rubuce a Littafin Annabawa, cewa,

‘Ya ku Bani Isra’ila,
Ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya,
Har shekara arba’in a cikin jeji?
43 Ai yawo kuka yi da alfarwar Moloka,
Da surar tauraron gunki Ramfan,
Wato surorin nan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.
Ni kuwa zan kau da ku can bayan Babila.’

44 “Dā kakannimmu suna da Alfarwar Shaida a jeji, irin wadda mai maganan nan da Musa ya umarta a yi, daidai fasalin da ya gani. 45 Alfarwan nan ita ce kakannimmu suka gada, suka kuma kawo ƙasan nan a zamanin Yusha’u, bayan sun maye ƙasar al’umman da Allah ya kora a gaban idonsu. Alfarwan nan kuwa tana nan har ya zuwa zamanin Dawuda, 46 wanda ya sami so wurin Allah, har ya nemi alfarmar yi wa Allahn Yakubu gida. 47 Amma Sulaimanu ne ya gina wa Allah Ɗaki. 48 Duk da haka Maɗaukaki ba ya zama a ɗaki ginin mutun. Yadda Annabi Ishaya ya ce

49 ‘Allah ya ce, Sama ita ce gadon sarautata,
Ƙasa kuwa matashin ƙafata.
Wane Ɗaki kuma za ku gina mini?
Ko kuwa wane wuri ne wurin hutuna?
50 Ba da hannuna na halicci dukkan waɗannan abubuwa ba?

51 “Ku kangararru, masu ɓatan basira, masu kunnen ƙashi, kullum kuna yi wa Ruhu Tsattsarka tsayayya. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma ku ke yi. 52 Cikin annabawa wanene kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai gaskiyan nan, wanda yanzu kuka zama maciya amanarsa, kuma makasansa, 53 ku ne kuwa kuka karɓi Shari’ar Musa ta kan mala’iku, amma ba ku kiyaye ta ba!”

An Kashe Istifanus da Jifa

54 Da suka ji haka, sai suka fusata ƙwarai da gaske, har suka ciji baki don jin haushinsa. 55 Amma Istifanus, cike da Ruhu Tsattsarka, sai ya zuba ido Sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu tsaye a hannun dama na Allah. 56 Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗam Mutun tsaye a hannun dama na Allah.” 57 Amma sai suka ɗauki ihu ƙwarai, suka tattoshe kunnuwansu, suka aukam masa gaba-ɗaya, 58 suka fid da shi bayan gari, suka yi ta jifansa da dutse. Shaidu kuwa suka ajiye tufafinsu wurin wani saurayi wai shi Shawulu. 59 Suna ta jifan Istifanus, shi kuwa yana ta addu’a, yana cewa, “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” 60 Sannan ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka ɗora musu wannan zunubi.” Da faɗar haka sai ya yi barci.

8

Babban Tsanani ya Aukam ma Ikiliziya

Shawulu kuwa na goyon bayan kisan Istifanus.

A ran nan kuwa sai wani babban tsanani ya auko wa ikiliziyad da ke Urushalima. Duk aka warwatsa su a duk lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai Manzarmin kawai. 2 Sai wasu mutane masu bautar Allah suka binne Istifanus, suka yi masa kuka ƙwarai. 3 Amma sai Shawulu ya yi ta yi wa ikiliziya ɓama ƙwarai da gaske, yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata, yana jefa su kurkuku.

4 To, waɗanda aka warwatsan nan kuwa, sai suka yi ta zazzagawa suna yin Bishara. 5 Filibus ya tafi birnin Samariya, yana ta yi musu wa’azin Almasihu. 6 Da taron suka ji, suka kuma ga mu’ujizan da Filibus ke yi, sai gaba-ɗaya suka mai da hankali ga abin da ya faɗa. 7 Domin da yawa masu baƙaƙen aIjannu suka rabu da su, aljannun kuwa na ta ihu. Shanyayyu da guragu da yawa kuma an warkad da su. 8 Saboda haka sai aka yi ta farinciki a garin ƙwarai da gaske.

Siman Mai Sihiri

9 Akwai wani mutun kuwa, mai suna Siman, wanda da ya ke sihiri a birnin, har yana ba Samariyawa mamaki, yana cewa shi wani muhimmi ne. 10 Duk jama’a kuwa suka mai da hankali gare shi, babba da yaro, suna cewa, “Mutumin nan ai ikon nan ne na Allah, da a ke kira Mai girma.” 11 Sai suka mai da hankali gare shi, don ya daɗe yana ta ba su al’ajabi da sihirinsa. 12 Amma da suka gaskata Bisharad da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, sai duka aka yi musu babtisma maza da mata. 13 Har Siman da kansa ma ya ba da gaskiya, kuma bayan an yi masa babtisma, sai ya ɗafe wa Filibus. Ganin kuma ana yin mu’ujizai da manya-manyan al’ajuba, sai ya yi mamaki ƙwarai.

14 To, da Manzarmin da ke Urushalima suka ji Samariyawa sun yi na’am da Maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohana. 15 Su kuwa da suka iso, sai suka yi musu addu’a su sami Ruhu Tsattsarka, 16 don bai sauko wa kowannensu ba tukuna, sai dai kawai an yi musu babtisma ne su zama mallakar Ubangiji Yesu. 17 Sai suka ɗora musu hannu, suka kuwa sami Ruhu Tsattsarka.

18 To, da Siman ya ga ashe ta ɗora hannun Manzanni ne a ke ba da Ruhu Tsattsarka, sai ya miƙa musu kuɗi, 19 ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan ikon, don kowa na ɗora wa hannu, yd sami Ruhu Tsattsarka.” 20 Amma sai Bitrus ya ce masa, “Ku halaka kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah! 21 Ba ruwanka da wannan al’amari sam-sam, don zuciyarka ba ɗaya ta ke ba a gaban Allah. 22 Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka. 23 Don na ga kana kishi tuƙurunsa, har rashin gaskiya ya yi maka kanta.” 24 Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku roƙam mini Ubangiji kada ko ɗaya daga cikin abin da kuka faɗa ya aukam mini.”

25 To, bayan Manzarmin sun tabbatad da Maganar Ubangiji, sun faɗe ta, sai suka koma Urushalima, suna yin Bishara a kauyukan Samariyawa da yawa.

Filibus da Mutumin Habasha

26 Amma sai wani mala’ikan Ubangiji ya ce da Filibus, “Tashi, ka yi kudu, ka bi hanyad da ta fito daga Urushalima zuwa Gaza,” wato, hanyar hamada. 27 Sai ya tashi ya tafi. Sai ga wani mutumin Habasha, wani baba, mai babban matsayi a mulkin Kandakatu, sarauniyar Habasha, shi ne kuwa ma’ajinta, ya zo Urushalima ne yin sujada, 28 yana komawa gida zaune a cikin keken-dokinsa, yana karatun Littafin Annabi Ishaya. 29 Sai Ruhu Tsattsarka ya ce da Filibus, “Matsa ka yi kusa da keken-dokin nan.” 30 Sai Filibus ya yi gudu wurinsa, ya ji shi yana karatun Littafin Annabi Ishaya. Ya ce, “Kana kuwa fahintar abin da ka ke karantawa?” 31 Sai ya ce, “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau su zauna tare. 32 Wannan kuwa shi ne Nassin da ya ke karantawa:

“An ja shi kamar tinkiya zuwa mayanka.
Kamar yadda ɗan rago ke shiru a hannun mai saisayensa,
Haka ko bakinsa bai buɗe ba.
33 An yi masa ƙasƙanci har an hana masa gaskiyatasa.
Tir! Wa ke iya ba da labarin zamaninsa?
Don an katse ransa daga duniya.”

Filibus ya yi masa Babtisma

34 Sai baban ya ce da Filibus, “Shin kam, annabin nan, maganar wa ya ke yi? Tasa ko ta wani?” 35 Sai Filibus ya buɗe baki ya fara da wannan Nassi, yana yi masa Bisharar Yesu. 36 Suna cikin tafiya, sai suka iso wani ruwa, sai baban ya ce, “Ka ga ruwa! Me zai hana a yi mini babtisma?” 37 Filibus ya ce, “In dai ka ba da gaskiya da zuciya ɗaya, ai sai a yi maka.” Baban ya amsa ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu ɗan Allah ne.” 38 Sai ya yi umarni a tsai da keken-dokin. Sai dukkansu biyu suka gangara cikin ruwan, Filibus da baban, ya yi masa babtisma. 39 Da suka fito daga ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, baban kuma bai ƙara ganinsa ba. Sai ya yi ta tafiyatasa yana farinciki. 40 Amma sai aka ga Filibus a Azotus. Sai ya zaga dukkan garuruwa, yana yin Bishara, har ya isa Kaisariya.

9

Shawulu ya Gaskata da Ubangiji Yesu

To, Shawulu kuwa yana tsaka da haukan tsoratad da masu bin Ubangiji da kuma kisansu, sai ya je wurin Babban Malamin, 2 ya roƙe shi ya yi masa wasiku zuwa majami’un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan Hanya, maza ko mata, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure. 3 Yana cikin tafiya ke nan, ya yi kusa da Dimashƙu, kwamfa sai ga wani haske daga Sama ya haskake kewaye da shi. 4 Sai ya faɗi, kuma ya ji wata murya tana ce masa, “Shawulu, Shawulu, dom me ka ke tsananta mini?” 5 Shi kuma ya ce, “Wanene kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda ka ke tsananta wa. 6 Amma tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.” 7 Abokan tafiyarsa kuwa suka rasa bakin magana, suna jin muryar, amma ba su ga kowa ba. 8 Sai Shawulu ya tashi, amma da ya buɗe ido sai ya kasa gani. Sai aka yi masa jagora, aka kai shi Dimashƙu. 9 Kwanansa uku ba ya gani, ba ya kuma ci, ba ya sha.

10 To, akwai wani mai bi a Dimashƙu, mai suna Hananiya. Ubangiji ya yi masa magana cikin wahayi ya ce, “Hananiya.” Shi kuwa ya ce, “Na’am, ya Ubangiji.” 11 Sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka tafi titin nan da a ke kira Miƙaƙƙe, ka tambaya a gidan Yahuda akwai wani mutumin Tarsus, mai suna Shawulu, ga shi nan yana addu’a, 12 har ma a cikin wahayi ya ga wani mutun, mai suna Hananiya, ya shigo ya ɗora masa hannu, don ganinsa ya komo.” 13 Amma sai Hananiya ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, na sha jin labarin mutumin nan gun mutane da yawa, kan yawan muguntad da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima. 14 Ga shi kuma manyan malamai sun ba shi izini ya ɗaure duk mai yin addu’a da sunanka a nan ma.” 15 Amma sai Ubangiji ya ce masa, “Kai dai je ka, don shi abin aikina ne zaɓaɓɓe, don yi sanad da sunana ga sauran al’umma, da sarakuna, da kuma Bani Isra’ila. 16 Don zan sanad da shi yawan wuyad da lalle zai sha saboda sunana.” 17 Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, sai ya ce, “Ya ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyad da ka biyo, don ganinka ya komo, a kuma cika ka da Ruhu Tsattsarka.” 18 Nan take sai wani abu kamar ɓawo ya faɗo daga idanunsa, sai ganinsa ya komo. Sa’an nan ya tashi, aka yi masa babtisma. 19 Sai ya ci abinci, ƙarfinsa kuma ya komo.

Shawulu ya Fara Wa’azin Yesu Ɗan Allah ne

Shawulu kuwa ya yi ’yan kwanaki tare da masu bi da ke Dimashƙu. 20 Nandanan sai ya fara wa’azin Yesu a majami’unsu, cewa shi ne Ɗan Allah. 21 Duk waɗanda suka ji shi, sai suka yi al’ajabi, suka ce, “Ashe ba wannan ne ya watsa masu yin addu’a da sunan nan a Urushalima ba? Ya zo nan ne ma da niyyar kai su gaban manyan malamai a ɗaure.” 22 Sai Shawulu ya ƙara ƙarfafa, yana ta dama hankalin Yahudawan da ke zaune a Dimashƙu, yana tabbatarwa cewa Yesu shi ne Almasihu.

23 Bayan wani lokaci mai tsawo sai Yahudawa suka kulla shawara su kashe shi. 24 Amma Shawulu ya sami labarin makircinsu. Dare da rana suna fako a ƙofofin gari don su kashe shi, 25 amma da dad dare sai almajiransa suka tafi da shi, suka zura shi ta wata ƙofa a jikin ganuwa cikin babban kwando.

Barnabas ya kai Shawulu gun Manzanni

26 Da ya zo Urushalima sai ya yi ƙoƙarin shiga cikin masu bi, amma duk sai suka ji tsoronsa, don ba su gaskata shi mai bi ba ne. 27 Amma Barnabas ya kama hannunsa ya kai shi wurin Manzannin, ya gaya musu yadda Shawulu ya ga Ubangiji a hanya, da yadda Ubangiji ya yi masa magana, da kuma yadda ya yi wa’azi gabagaɗi da sunan Yesu a Dimashƙu. 28 Daganan sai ya yi ta cuɗanya da su a Urushalima, 29 yana wa’azi gabagaɗi da sunan Ubangiji. Ya kuma riƙa magana da Yahudawa masu jin Helenanci, yana muhawara da su, amma sai suka yi ta neman kashe shi. 30 Da ’yan’uwa suka fahinci haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka aika da shi Tarsus.

31 Sa’an nan ne ikiliziyar duk ƙasar Yahudiya da ta Galili da ta Samariya ta sami lafiya, ta ingantu sosai, suna tafiyad da al’amuransu da tsoron Ubangiji, Ruhu Tsattsarka na ƙarfafa musu gwiwa, har suka yawaita.

Bitrus ya Warkad da Iniyas

32 To, da Bitrus ya zazzaga lardi duka, sai kuma ya je wurin tsarkakan nan da ke zaune a Lidda. 33 Nan ya tarad da wani mutun, mai suna Iniyas, wanda ke kwance kan gado shekara takwas, yana shanyayye. 34 Sai Bitrus ya ce da shi, “Iniyas, Yesu Almasihu ya warkad da kai. Tashi ka kintsa gadonka.” Nan take ya tashi. 35 Duk mutanen Lidda da na ƙasar Sarona kuwa suka gan shi, sai suka juyo ga Ubangiji.

Bitrus ya ta da Tabita

36 A Yafa kuwa akwai wata mai bi, mai suna Tabita, wato Barewa ke nan. Matan nan kuwa lazimar aiki nagari ce, da kuma gudummawa. 37 A lokacin nan sai ta yi rashin lafiya, ta mutu. Da suka yi mata wanka, sai suka shimfiɗe ta a kan bene. 38 Da ya ke Lidda kusa da Yafa ta ke, da masu bi suka ji Bitrus na can, sai suka aiki mutum biyu wurinsa, su roƙe shi ya zo wurinsu ba da jinkiri ba. 39 Sai Bitrus ya tashi ya tafi tare da su. Da ya iso sai suka kai shi benen. Sai duk mata waɗanda mazansu suka mutu suka tsaya kusa da shi, suna kuka, suna nunnuna riguna da tufafin da Barewa ta yi musu. tun suna tare. 40 Amma sai Bitrus ya fid da su waje duka, ya durƙusa, ya yi addu’a. Sai ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Sai ta buɗe ido, da kuma ta ga Bitrus sai ta tashi zaune. 41 Sai ya miƙa mata hannu ya tashe ta. Sai ya kira tsarkaka da matan nan waɗanda mazansu suka mutu, ya miƙa musu ita rayayyiya. 42 Sai labari ya bazu a dukkan Yafa, mutane da yawa kuwa suka gaskata da Ubangiji. 43 To, sai ya zauna kwanaki da yawa a Yafa a gidan wani majemi mai suna Siman.

10

Mala’ika ya Bayyana ga Karniliyas

An yi wani mutun a Kaisariya, mai suna Kamiliyas, wani to kyaftin ne na kamfartin soja da a ke kira Kamfanin Italiya. 2 Shi kuwa mutun ne mai ibada, yana tsoron Allah shi da iyalinsa duka, yana ba jama’a sadaka hannu sake, yana kuma roƙon Allah a kai a kai. 3 Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, sai ya ga wani mala’ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Kamƙiyas.” 4 Shi kuwa sai ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, menene?” Mala’ikan kuma ya ce masa, “Addu’arka da sadakarka sun kai har gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi. 5 To, yanzu sai ka aiki mutane Yafa su kirawo Siman, wanda a ke kira Bitrus; 6 ya sauka ne a gun Siman Majemi, wanda gidansa ke bakin bahar.” 7 Da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, sai ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda ke yi masa hidima kullun. 8 Da ya ba su labarin komai, sai ya aike su Yafa.

An yi wa Bitrus Wahayi

9 Washegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu’a, wajen rana tsaka. 10 Sai yunwa ta kama shi, har ya so ya ci wani abu. Ana cikin shirya abincin, sai wahayi ya zo masa, 11 ya ga sama ta dare, wani abu kuma na saukowa kamar babban mayafi, ana zuro shi ƙasa ta kusurwoyinsa huɗu. 12 Cikinsa akwai kowace irin dabba, da masu jan ciki, da tsuntsaye. 13 Sai ya ji wata murya ta ce da shi, “Bitrus, tashi ka yanka ka ci.” 14 Amma sai Bitrus ya ce, “A’a, ya Ubangiji, don ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta ba.” 15 Sai ya sake jin murya, ji na biyu, ta ce, “Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.” 16 An yi wannan sau uku, sai nandanan aka yi sama da abin.

17 Bitrus na cikin damuwa ƙwarai a kan komecece ma’anar wahayin da aka yi masa, sai ga mutanen da Karniliyas ya aiko tsaye a ƙofar zaure, sun riga sun tambayi gidan Siman, 18 suna sallama, suna tambaya ko Siman da a ke kira Bitrus a nan ya sauka. 19 Tun Bitrus na bibiya wahayin nan, sai Ruhu Tsattsarka ya ce masa, “Ga mutun uku nan na nemanka. 20 Tashi ka sauka, ku tafi tare, ba da wata shakka ba, don ni ne na aiko su.” 21 Sai Bitrus ya sauka wurin mutanen, ya ce musu, “Ga ni, ni ne ku ke nema. Wace magana ke tafe da ku?” 22 Sai suka ce, “Wani kyaftin ne, wai shi Karniliyas, mai gaskiya, mai tsoron Allah, wanda duk jama’ar Yahudawa ke yabo, shi ne wani tsattsarkan mala’ika ya umarce shi, ya aiko ka je gidansa, ya ji maganarka.” 23 Sai Bitrus ya shigo da su, ya sauke su.

Bitrus ya Sadu da Karnifiyas

Washegari sai ya tashi suka tafi tare, waɗansu ’yan’uwa kuma daga Yafa suka raka shi. 24 Washegari kuma sai suka shiga Kaisariya. Dā ma Karniliyas na tsammaninsu, har ya gayyato yan’uwansa da aminansa. 25 Bitrus na shiga gidan ke nan sai Karniliyas ya tarye shi, ya fāɗi a gabansa, ya yi masa sujada. 26 Amma sai Bitrus ya tashe shi, ya ce, “Tashi, ai ni ma ɗan’adan ne.” 27 Bitrus na zance da shi, sai ya shiga ya tarar mutane da yawa sun taru. 28 Ya ce musu, “Ku da kanku kun san bai halatta Bayahude ya cuɗanya, ko ya ziyarci wani na wata kabila dabam ba. Amma Allah ya nuna mini kada in ce da kowa marar tsarki, ko mai ƙazanta. 29 Saboda haka da aka neme ni, sai na zo, ban ce a’a ba. To, yanzu ina so in ji abin da ya sa kuka kira ni.”

30 Sai Karniliyas ya ce, “Yau kwana uku ke nan, wajen war haka, ina addu’ar ƙarfe uku na yamma a gidana, sai ga wani mutun tsaye a gabana, saye da tufafi masu ɗaukar ido, 31 ya ce, ‘Ya Karniliyas, an amsa addu’arka, sadakarka kuma ta zama abar tunawa ga Allah. 32 Saboda haka sai ka aika Yafa a kirawo Siman, wanda a ke kira Bitrus, ya sauka ne a gidan Siman Majemi a bakin bahar.’ 33 Nandanan kuwa sai na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara gaban Allah, don mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”

34 Sai Bitrus ya kā da baki ya ce, “Hakika na gane lalle Allah ba ya nuna zaɓe. 35 amma a kowace al’umma duk mai tsoronsa, mai kuma aikata gaskiya, abin karɓuwa ne a gare shi. 36 Allah ya aiko wa Bani Isra’ila maganarsa, ana yi musu Bisharar aminci ta kan Yesu Almasihu, shi ne kuwa Ubangijin kowa. 37 Kun dai san labarin nan da ya bazu a duk ƙasar Yahudiya, am fara shi ne tun daga ƙasar Galili, bayan babtismad da Yohana ya yi wa’azi, 38 wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya yi masa shafa, tsattsarkar shafa, da Ruhu Tsattsarka, da kuma iko, da yadda kuma ya riƙa zagawa yana aikin alheri, yana warkad da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, don Allah na tare da shi. 39 Mu kuwa shaidu ne ga duk abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da Urughalima. Shi ne kuma suka kashe ta kafe shi a jikin gungume. 40 Shi ne Allah ya tasa a rana ta uku, ya kuma yarda ya bayyana, 41 ba ga dukkan jama’a ba, sai dai ga shaidun nan da Allah ya zaɓa tun dā, wato mu ke nan, da muka ci muka sha tare da shi, bayan ya tashi daga matattu. 42 Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane wa’azi, mu kuma tabbatar cewa shi ne wanda Allah ya sanya mai hukunta rayayyu da matattu. 43 Shi ne duk annabawa suka yi wa shaida, cewa albarkacin sunansa duk mai gaskatawa da shi zai sami gafarar zunubai.”

Am ba Sauran Mumma Ruhu Tsattsarka

44 Bitrus na cikin wannan magana, sai Ruhu Tsattsarka ya sauko wa dukkan masu jinta. 45 Sai Yahudawa masu bi, ɗakwacin waɗanda suka zo tare da Bitrus, suka yi mamakin ganin har sauran al’umma ma an kwararo musu baiwar Ruhu Tsattsarka. 46 Don sun ji suna magana da wasu harsuna, suna ta ɗaukaka Allah. Sa’an nan Bitrus ya ce, 47 “Akwai mai iya hana ruwan da za a yi wa mutanen nan babtisma, waɗanda suka sami Ruhu Tsattsarka, kamar yadda mu ma muka sanI 48 Sai ya yi umarni a yi musu babtisma da sunan Yesu. Almasihu. Sannan suka roƙe shi ya ƙara ’yan kwanaki a gunsu.

11

Bitrus ya koma Urushalima

To, sai Manzanni da ’yan’uwa da ke ƙasar Yahudiya suka ji cewa sauran al’umma ma sun yi na’am da Maganar Allah. 2 Da Bitrus ya zo Urushalima, sai ’yan ɗariƙar masu kaciyan nan suka ci gyaransa, 3 suka ce, “Ga shi ka shiga cikin marasa kaciya, har ka ci abinci tare da su!” 4 Amma sai Bitrus ya fara, yana yi musu bayani bi da bi, cewa, 5 “Ni dai, ina birnin Yafa ina addu’a, sai wahayi ya zo mini, na ga wani abu na saukowa kamar babban mayafi, an zuro shi daga sama ta kusurwoyinsa huɗu, har ya zo wurina. 6 Da na zuba masa ido, sai na duba na ga dabbobi, da namun daji, da masu jan ciki, da kuma tsuntsaye a ciki. 7 Sai kuma na ji wata murya ta ce mini, ‘Bitrus, tashi ka yanka ka ci.’ 8 Amma sai na ce, Wa, ya Ubangiji, don ba wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta da ya taɓa shiga bakina.’ 9 Sai muryar ta amsa daga sama ta yi magana ta biyu, ta ce, ‘Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.’ 10 An yi wannan sau uku, sa’an nan duk sai aka janye abin sama. 11 Kwamfa sai ga mutun uku tsaye a ƙofar gidan da mu ke, an aiko su wurina ne daga Kaisariya. 12 Sai Ruhu Tsattsarka ya ce mini in tafi tare da su, ba tare da wata shakka ba. ’Yan’uwan nan shida kuma suka rako ni, har muka shiga gidan mutumin nan. 13 Sai ya gaya mana yadda ya ga mala’ika tsaye a gidansa, yana cewa, ‘Ka aika Yafa a kirawo Siman, wanda a ke kira Bitrus, 14 shi zai faɗa maka maganad da za ka sami ceto game da ita, kai da jama’ar gidanka duka.’ 15 Da fara maganata, sai Ruhu Tsattsarka ya sauko musu, daidai yadda ya sauko mana tun da farko. 16 Sai na tuna da Maganar Ubangiji, yadda ya ce, ‘Yohana kam da ruwa ya yi babtisma, amma ku da Ruhu Tsattsarka za a yi muku babtisma.’ 17 Tun da ya ke Allah ya yi musu baiwa daidai da wadda ya yi mana, sa’ad da muka gaskata da Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni in dage wa Allah!” 18 Da suka ji haka, sai suka rasa ta cewa, kuma suka ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe har sauran al’umma ma Allah ya yi musu balwar tuba mai kaiwa ga rai madawwami.”

An Sa wa Masu Bi Sunan Kirista a Antakiya

19 To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin nan da ya wakana kan sha’anin Istifanus, sun yi tafiya bar ƙasar Finikiya, da tsibirin Kubrus, da birnin Antakiya, ba sa wa’azin Maganar Allah ga kowa sai ga Yahudawa kaɗai. 20 Amma akwai wasunsu, mutanen Kubrus da na Kurane, waɗanda da isowarsu Antakiya sai suka yi wa Helenawa magana, suna yi musu Bisharar Ubangiji Yesu. 21 Ikon Ubangiji kuwa na tare da su, har mutane da yawa da suka ba da gaskiya suka juyo ga Ubangiji. 22 Sai labarin nan ya kai kunnen ikiliziyad da ke Urushalima, ikiliziyar kuma sai ta aiki Barnabas can Antakiya. 23 Da ya iso ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, sai ya yi farinciki, ya gargaɗe su duka su tsaya ga Ubangiji, tsaiwar daka, 24 don shi mutun ne nagari, cike da Ruhu Tsattsarka da bangaskiya. Sai mutane masu yawan gaske suka ƙaru ga Ubangiji. 25 Sai Barnabas ya tafi Tarsus neman Shawulu, 26 bayan ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara sur suna taruwa da ikiliziya, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bi da sunan Kirista.

27 To, a kwanakin nan sai wasu masu yin faɗin Maganar Allah suka zo Antakiya daga Urushalima. 28 Sai ɗaya daga cikinsu, mai suna Agabas, ya miƙe tsaye, ya yi faɗi da ikon Ruhu Tsattsarka, cewa za a yi wata babbar yunwa a duniya duka; an yi ta kuwa a zamanin Kalaudiyas. 29 Sai masu bi suka ɗaura niyya, kowa gwargwadon ƙarfinsa, su aika wa ’yan’uwan da ke ƙasar Yahudiya gudummawa. 30 Haka kuwa suka yi, suka aika wa dattawan ikiliziya ta hannun Barnabas da Shawulu.

12

Hirudus ya Fille wa Yakubu Kai

A lokacin nan kuwa sai Sarki Hirudus ya fara gwada wa wasu ’yan ikiliziya tasku, 2 har ma ya sare Yakubu ɗanuwan Yohana da takobi. 3 Da ya ga abin ya ƙayatad da Yahudawa, har wa yau kuma sai ya kama Bitrus shi ma. Kwanakin Idin Burodi Marar Yisti ne kuwa. 4 Da ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, su yi gadinsa, da niyyar kawo shi gaban jama’a bayan Idin. 5 Sai aka tsare Bitrus a kurkuku, ikiliziya kuwa ta himmantu ga rofron Allah saboda shi.

Mala’ika ya fid da Bitrus daga Kurkuku

6 A daren da in gari ya waye Hirudus ke niyyar fito da shi a yi masa hukunci, Bitrus kuwa na barci tsakanin soja biyu, ɗaure da sarƙa biyu, masu gadi kuma na bakin ƙofa suna gadin kurkukun, 7 sai ga wani mala’ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskake ɗakin, sa’an nan mala’ikan ya bugi Bitrus a kwiɓi, ya tashe shi, ya ce, “Maza tashi.” Sai kuwa sarƙar ta zube daga hannunsa. 8 Mala’ikan ya ce masa, “Yi ɗamara, ka sa takalminka.” Sai ya yi. Sai ya ce masa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.” 9 Sai ya fito ya bi shi, bai san cewa abin nan da mala’ikan nan ya yi hakika ne ba, cewa ya ke wahayi a ke yi masa. 10 Da suka wuce masu gadin farko da na biyu, sai suka isa ƙyauren ƙarfe na ƙofar shiga gari, ƙyaurem kuwa ya buɗe musu don kansa. Sai suka fita. Sun ƙure wani titi ke nan, nandanan sai mala’ikan ya bar shi. 11 Da Bitrus ya farfaɗo, sai ya ce, “Yanzu kam na tabbata Ubangiji ne ya aiko mala’ikansa, ya cece ni daga hannun Hirudus, da kuma dukkan mugun fatan Yahudawa.”

12 Da ya gane haka, sai ya je gidan Maryamu, uwar Yohana wanda a ke kira Markus, inda aka taru da yawa ana addu’a. 13 Da ya buga ƙofar zauren, sai wata baranya mai suna Roda ta zo ta ji ko wanene. 14 Da ta shaida muryar Bitrus, ba ta buɗe ƙofar ba don murna, sai ta koma ciki a guje, ta ce Bitrus na tsaye a ƙofar zaure. 15 Sai suka ce mata, “Ke dai akwai ruɗaɗɗiya.” Ita kuwa ta nace a kan shi ne. Su kuwa suka ce, “To, mala’ikansa ne!” 16 Bitrus dai ya yi ta bugawa, da kuwa suka buɗe suka gan shi, sai suka yi ta al’ajabi. 17 Shi kuwa sai ya ɗaga musu hannu su yi shiru, ya kuma bayyana musu yadda Ubangiji ya fito da shi daga kurkuku. Ya kuma ce, “Ku faɗa wa Yakubu da ’yan’uwa waɗannan abubuwa.” Sannan ya tashi ya tafi wani wuri.

18 Da gari ya waye kuwa ba. ƙaramin hargitsi ne ya tashi tsakanin sojan nan ba, kan me ya ci Bitrus. 19 Da Hirudus ya neme shi bai same shi ba, sai ya yi ta tuhumar durobobin, ya kuma yi umarni a kashe su. Sa’an nan ya tashi daga ƙasar Yahudiya ya tafi Kaisariya, ya yi ’yan kwanaki a can.

Hirudus ya yi Muguwar Mutuwa

20 To, sai Hirudus ya yi fushi ƙwarai da mutanen Sur da na Saida. Sai suka haɗa kai suka zo wurinsa. Bayan sun shawo kan Bilastas, sarkin fada, sai suka nemi sulhu, domin da ƙasar sarkin nan suka dogara saboda abincinsu. 21 Ana nan a wata rana da aka shirya, sai Hirudus ya yi shigar sarauta, ya zauna a kan gadon sarauta, ya yi musu jawabi. 22 Taron mutane kuwa suka ɗauki sowa, suna cewa, “Kai! ka ji muryar wani allah, ba ta mutum ba!” Nan take sai wani mala’ikan Ubangiii ya buge shi, don bai ɗaukaka Allah ba. Sai tsutsotsi suka yi ta cinsa har ya mutu.

24 Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka ta ke yi, tana yaɗuwa.

25 Sai Barnabas da Shawulu suka komo daga Urushalima, bayan sun cika aiken da aka yi musu, suka kuma zo da Yohana wanda a ke kira Markus.

13

An Keɓe Barnabas da Shawulu don Aikin Bishara

To, a ikiliziyad da ke Antakiya akwai wasu masu yin faɗin Maganar Allah, da masu koyad da Maganar Allah, wato Barnabas, da Simiyan wanda a ke kira Băƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da Sarki Hirudus, da kuma Shawulu. 2 Sa’ad da su ke yi wa Ubangiji ibada, suna kuma hana kansu abinci, sai Ruhu Tsattsarka ya ce, “Sai ku keɓe mini Barnabas da Shawulu don aikin da na kira su a kai.” 3 Bayan kuma sun hana kansu abinci, sun kuma yi addu’a, sai suka ɗora musu hannu, suka sallame su.

TAFIYAR BULUS TA FARKO YIN WA’AZI

4 Su kuwa, da Ruhu Tsattsarka ya aike su, sai suka tafi Salukiya, daga can kuma suka shiga jirgin ruwa sai tsibirin Kubrus. 5 Da suka kai Salamis, sai suka sanad da Maganar Allah a majami’un Yahudawa, ga kuma Yohana na taimakonsu. 6 Bayan sun zazzaga tsibirin duka har Bafas, sai suka iske wani mai sihiri, annabin ƙarya, Bayahude, mai suna Bar-Yesu, 7 wanda su ke tare da muƙaddas Sarjiyas Bulus, mutum mai basira. Sai muƙaddashin ya kira Barnabas da Shawulu ya nemi jin Maganar Allah. 8 Amma Alimas mai sihirin nan, (don wannan ita ce ma’anar sunansa), sai ya musa musu, yana neman bauɗad da muƙaddashin nan daga Bangaskiya. 9 Shawulu kuwa, shi ma Bulus, cike da Ruhu Tsattsarka, sai ya zuba masa ido, 10 ya ce, “Kai babban maha’inci, munafuki, ɗan Iblis, magabcin duk aikin gaskiya, ba za ka daina karkata miƙakƙun hanyoyin Ubangiji ba? 11 To, ga shi hukuncin Allah na kanka, za ka makance, ba za ka ga rana ba har wani lokaci.” Nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi, ya yi ta neman wanda zai yi masa jagora. 12 Da muƙaddashin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, yana mamaki da koyarwar Ubangiji.

Bulus ya yi wa Yahudawa Wa’azi a Antakiya

13 Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafas a jirgin ruwa, suka isa Barga ta ƙasar Bamfiliya. Yohana kuwa ya bar su, ya koma Urushalima. 14 Amma sai suka wuce gaba daga Barga, suka tafi Antakiya ta ƙasar Bisidiya. Ran Asabar kuma suka shiga majami’a suka zauna. 15 Bayan an yi karatun Attaura da Littattafan Annabawa, sai shugabannin majami’ar suka afka musu, suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama’a, ai sai ku yi.” 16 Sai Bulus ya miƙe, ya ɗaga hammu a yi shiru, ya ce:

“Ya ku Bani Isra’ila, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara! 17 Allahn jama’an nan, Bani Isra’ila, ya zaɓi kakannimmu, ya ɗaukaka jama’ar sa’ad da su ke baƙunci a ƙasar Masar, kuma da maɗaukakin iko ya fito da su daga cikinta. 18 Kuma wajen shekara arba’in ya ke haƙuri da su cikin jeji. 19 Kuma da ya hallaka kabilu bakwai a ƙasar Kan’ana, sai ya raba musu ƙasatasu gado, suka zauna har shekara arbaminya da hamsin. 20 Bayan haka kuma ya naɗa musu mahukunta har ya zuwa zamanin Annabi Samu’ila. 21 Sannan suka roƙa a naɗa musu sarki, sai Allah ya ba su Shawulu ɗan Kisi, mutumin kabilar Bunyamunu, har shekara arba’in. 22 Bayan ya kau da shi, sai ya gabatad da Dawuda ya zama sarkinsu, ya kuma shaide shi da cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yassa, mutun ne da na ke ƙauna ƙwarai, wanda kuma zai aikata dukkan nufina.’ 23 Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Bani Isra’ila Maceci, Yesu, kamar yadda ya yi alkawari. 24 Kafin ya bayyana a fili kuwa, Yohana ya yi wa duk Bani Isra’ila wa’azi su tuba a yi musu babtisma. 25 Yayin da Yohana ya kusa gama nasa zamanin, sai ya ce, ‘Wa ku ke tsammani na ke? Ba fa ni ne Shi ɗin nan ba. Amma ga shi, akwai wani Mai zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa im ɓalle ba.’

26 “Ya ku ’yan’uwa, zuriyar Ibrahim, da kuma sauran masu tsoron Allah a cikinku, mu fa aka aiko wa kalmar ceton nan. 27 Ga shi mazauna Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sauran kuma ba su fahinci maganar annabawa da a ke karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganan nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi. 28 Ko da ya ke ba su same shi da wani laifin kisa ba, duk da haka sai da suka roƙi Bilatus a kashe shi. 29 Da suka cikasa dukkan abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauko da shi daga kan gungumen, suka kwantad da shi a kabari. 30 Amma sai Allah ya tashe shi daga matattu. 31 Kwanaki da yawa kuwa yana bayyana ga waɗanda suka zo tare da shi Urushahma daga Galili, waɗanda yanzu su ne shaidunsa ga jama’a. 32 Mu ma mun kawo muku albishir, cewa alkawarin nan da Allah ya yi wa kakannimmu, 33 ya cika mana shi, mu zuriyarsu, da ya ta da Yesu daga matattu, yadda ya ke a rubuce a cikin Zabura fasali na biyu, cewa,

‘Kai Ɗana ne,
Na mai da kai Ɗana yau.’

34 Game da ta da shi daga matattu da Allah ya yi a kan cewa ba zai sake komawa cikin halin da a ke ruɓa ba kuwa, ga abin da ya ce,

‘Zan yi muku tsattsarkar albarkan nan da na tabbatar wa Dawuda.’
35 Don a wani fasalin Zabura ma ya ce,
‘Ba za ka yarda Tsattsarkanka ya ruɓa ba.’

36 Dawuda kam, bayan ya bauta wa mutanen zamaninsa bisa ga nufin Allah, sai ya yi barci, aka binne shi tare da kakanninsa, ya kuwa ruɓe. 37 Amma shi wannan da Allah ya tasa, bai ruɓa ba, 38 Saboda haka, ’yan’uwa, sai ku san cewa albarkacin mutumin nan ne a ke sanad da ku gafarar zunubanku. 39 Ta gare shi kuma duk masu ba da gaskiya suka kuɓuta daga dukkan abubuwan da ba dama Shari’ar Musa ta kuɓutad da ku. 40 Saboda haka sai ku mai da hankali, kada abin nan da Littattafan Annabawa ke faɗa ya aukam muku, wato,’

41 ‘Ga shi, ku masu rainin wayo,
Za ku ruɗe don mamaki!
Domin zan yi wani aiki a zamaninku,
Aikin da ba yadda za a yi ku gaskata,
Ko da wani ya gaya muku.’”

42 Suna fita majami’ar ke nan, sai mutane suka roƙe su su ƙara yi musu wannan magana a ran Asabar mai zuwa. 43 Da jama’a suka watse, sai Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnabas. Su kuma suka yi musu magana, suna yi musu gargaɗi su zauna a cikin alherin Allah.

Bulus ya Juya ga Sauran Al’umma

44 Da Asabar ta kewayo, kusan duk birnin sai suka hallara su ji Maganar Allah. 45 Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, sai suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa. 46 Sai Bulus da Barnabas suka yi magana gabagaɗi suka ce, “Ku ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da ya ke kun ture ta, kun nuna cewa ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, sai mu juya ga sauran al’umma. 47 Domin haka Ubangiji ya umarce mu, ya ce,

‘Na sanya ka haske ga sauran al’unima,
Don ka zama sanadin ceto har ya zuwa iyakar duniya.

48 Da sauran al’umma suka ji haka, sai suka yi farinciki, suka ɗaukaka Maganar Ubangiji, kuma ɗakwacin waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami suka ba da gaskiya. 49 Maganar Ubangiji kuwa sai ta yi ta yaɗuwa a duk ƙasar. 50 Amma sai Yahudawa suka zuga wasu mata masu ibada, masu daraja, da kuma wasu ƙusoshin gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga ƙasarsu. 51 Su kuwa sai suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kansu, suka tafi Ikoniya. 52 Amma kuwa masu bi suna cikin farinciki matuƙa, suna kuma cike da Ruhu Tsattsarka.

14

Bulus da Barnabas a Ikoniya

To, a Ikoniya sai suka shiga majami’ar Yahudawa tare, suka yi wa’azi, har mutane masu yawa, Yahudawa da Helenawa, suka ba da gaskiya. 2 Amma Yahudawan da suka ƙi bi, sai suka zuga sauran al’umma, suka ɓata tsakaninsu da ’yanuwa. 3 Sai Bulus da Barnabas suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa’azi gabagaɗi bisa ikon Ubangiji, shi da ya shaidi maganar alherinsa ta yarjin yin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi fa hannunsu. 4 Amma sai mutanen birni suka rarrabu, wasu suka koma bayan Yahudawa, wasu kuma bayan Manzannin. 5 Sa’ad da sauran al’umma da Yahudawa tare da shugabanninsu suka tasam ma auka wa Manzannin, su wulakanta su, su jajjefe su da duwatsu, 6 sai suka sami labari, suka gudu zuwa biranen Likoniya, wato, Listira da Darba, da kuma kewayensu. 7 Nan suka yi ta yin Bisharar.

Bulus ya Warkad da Gurgu a Listira

8 To, a Listira akwai wani mutun a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba. 9 Yana sauraron wa’azin Bidus, sai Bulus ya zuba masa ido, kuma da ya ga bangaskiyarsa ta isa a warkad da shi, 10 sai ya daga murya ya ce, “Tashi ka tsaya cir.” Sai wuf ya zabura, har ya yi tafiya. 11 Da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ɗiba gaba-ɗaya suna cewa da Likoniyanci, “Kai, alloli sun sauko mana da siffar mutane!” 12 Sai suka ce Barnabas shi ne Zafsa, Bulus kuwa don shi ne shugaban magana, wai. shi ne Hamis. 13 Sai sarkin tsafin Zafsa, wanda ɗakin gunkinsa ke ƙofar gari, ya kawo bajimai da tutocin furanni ƙofar gari, wai yana son yin yanka tare da jama’a. 14 Amma da Manzannin nan, Barnabas da Bulus, suka ji haka, sai suka kyakketa tufafinsu, suka ruga cikin taron, suna ɗaga murya suna cewa, 15 “Haba jama’a! Dom me ku ke haka? Ai mu ma ’yan’adan ne kamarku, mun dai kawo muku Bishara ne, don ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci Sama da ƙasa da teku, da kuma dukkan abin da ke cikinsu. 16 Shi ne a zamanin dā, ya bar dukkan al’ummai su yi yadda suka ga dama. 17 Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa ba shaida ba, don yana yin alheri, da ya ke yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosad da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.” 18 Duk da waɗannan maganganu da ƙyar suka hana jama’an nan yin yanka saboda sli.

An Jajjefi Bulus

19 Amma sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya, da suka rarrashi taron, sai suka jajjefi Bulus, suka ja shi bayan gari, suna zaton ya mutu. 20 Amma da masu bi suka taru a kansa, sai ya tashi ya koma cikin garin. Washegari kuma ya tafi Darba tare da Barnabas. 21 Bayan sun yi Bishara a wannan garin, sun kuma sami masu bi da yawa, sai suka koma Listira da Ikoniya da kuma Antakiya, 22 suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya ga Bangaskiya, suna cewa sai da shan wuya mai yawa za mu shiga Mulkin Allah. 23 Bayan kuma sun zaɓar musu dattawa a kowace ikiliziya, game da addu’a da hana kai abinci, sai suka danƙa su ga Ubangiji, wanda da man suka gaskata da shi.

24 Da suka zazzaga ƙasar Bisidiya, sai suka isa ƙasar Bamfiliya. 25 Da kuma suka faɗi Maganar Allah a Barga, sai suka tafi Ataliya. 26 Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa sai Antakiya, inda tun dā aka yi musu addu’a rahamar Allah ta kiyaye su cikin aikin nan da yanzu suka gama. 27 Da suka iso, sai suka tara jama’ar ikiliziya suka ba da labarin dukkan abin da Allah ya aikata ta kansu, da kuma yadda ya buɗe wa sauran al’umma ƙofar Bangaskiya. 28 Sun kuwa jima a can tare da masu bi.

15

An yi Mahawara a kan Maganar Kaciya

Sai kuma waɗansu mutane suka zo daga Yahudiya suna koya wa ’yan’uwa, suna cewa, “Im ba an yi muku kaciya kamar yadda al’adar Musa ta ke ba, ba dama ku sami ceto.” 2 A kan wannan magana kuwa ba ƙaramar gardama da muhawara Bulus da Barnabas suka sha yi da mutanen ba. Sai aka sanya Bulus da Barnabas da kuma wasunsu, su je Urushalima gun Manzanni da dattawan ikiliziya a kan wannan magana. 3 To, da ikiliziya ta raka su, sai suka zazzaga ƙasar Finikiya da ta Samariya, suna ba da labarin tuban sauran al’umma, sun kuwa ƙayatad da dukkan ’Yan’uwa ƙwarai. 4 Da suka isa Urushalima, sai ikiliziya da Manzanni da dattawan ikiliziya suka yi musu maraba, su kuma suka gaggaya musu dukkan abin da Allah ya yi ta kansu. 5 Amma sai wasu masu ba da gaskiya, ’yan ɗarikar Farisiyawa, suka miƙe, suka ce, “Wajibi ne a yi musu kaciya, a kuma umarce su su bi Shari’ar Musa.”

6 Sai Manzannin da dattawan ikiliziya suka taru su duba maganar. 7 Bayan an yi ta muhawara da gaske, sai Bitrus ya miƙe, ya ce musu, “Ya ’Yan’uwa, kun san tun farkon al’amari Allah ya yi zaɓe a cikinku, cewa dai ta bakina ne sauran al’umma: za su ji maganar Bishara, su ba da gaskiya. 8 Allah kuwa masanin zuciyar kowa ya yi musu shaida da ya ba su Ruhu Tsattsarka, kamar yadda ya ba mu. 9 Bai kuma nuna wani bambanci tsakanimmu da su ba, tun da ya ke ya tsarkake zukatansu saboda bangaskiyatasu. 10 Saboda haka, dom me ku ke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, ko kakannimmu, muka ƙasa ɗauka? 11 Amma mun gaskata cewa albarkacin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.” 12 Sai duk taron mutane suka yi tsit, suka saurari Barnabas da Bulus sa’ad da su ke ba da labarin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi da Allah ya yi ga sauran al’umma ta kansu.

Yakubu ya kawo Shawara

13 Bayan sun gama jawabi, sai Yakubu ya amsa ya ce, “Ya ku ’Yan’uwa, ku saurare ni. 14 Simiyan ya ba da labari yadda Allah ya fara kula da sauran al’umma, don yă keɓe wata jama’a daga cikinsu ta zama tasa. 15 Wannan kuwa daidai ya ke da maganar annabawa, yadda ya ke a rubuce, cewa,

16 ‘Bayan haka kuma zan komo,
In sake gina gidan Dawuda da ya rushe,
In sake ta da kangonsa,
In tsai da shi,
17 Don sauran mutane su nemi Ubangiji,
Wato sauran al’umman da ke nawa.’
18 ‘Haka Ubangiji ya ce, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin da.’

19 Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa sauran al’umma waɗanda ke juyowa ga Allah, 20 sai dai mu rubuta musu wasiƙa su guji abubuwan ƙazanta na game da gumaka, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin jini. 21 Don tun zamanin dā, a kowane gari akwai masu yin wa’azi da Littattafan Musa, ana kuma karanta su a majam’iu kowace Asabar.”

Wasika zuwa ga Ikiliziyan Sauran Al’umma

22 Sai Manzanni da dattawan ikiliziya, tare da dukkan ’yan ikiliziya, suka ga ya kyautu su zaɓi wasu daga cikinsu, su aike su Antakiya tare da Bulus da Barnabas. Sai suka aiki Yahuda, wanda a ke kira Barsaba, da kuma Silas, shugabanni ne cikin ’Yan’uwa, 23 da wannan takardar, cewa, “Daga ’Yan’uwanku, Manzanni da dattawan ikiliziya, zuwa ga ’Yan’uwammu na sauran al’umma a Antakiya da ƙasar Sham da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa. 24 Tun da muka sami labari, cewa waɗansu daga cikimmu sun ta da hankalinku da maganganu, suna ruɗa ku, ko da ya ke ba mu umarce su da haka ba, 25 sai muka ga ya kyautu, da ya ke bakimmu ya zo ɗaya, mu aiko muku wasu zaɓabɓun mutane, tare da ƙaunatattummu Barnabas da Bulus, 26 waɗanda suka sai da ransu saboda sunan Ubangijimmu Yesu Almasihu. 27 Don haka, ga shi mun aiko muku Yahuda da Silas, su ma za su gaya muku waɗannan abubuwa da bakinsu. 28 Don Ruhu Tsattsarka ya ga ya kyautu, mu ma mun gani, cewa kada a ɗora muku wani nauyi fiye da na waɗannan abubuwa da ke wajibi, wato, 29 ku guji abin da aka yanka wa gunki, da cin jini, da cin abin da aka maƙure, da kuma fasikanci. In kun tsare kanku daga waɗannan, za ku zauna lafiya. Wassalam.”

30 Su kuma da aka sallame su, sai suka tafi Antakiya; da suka tara jama’ar, sai suka ba da wasiƙar. 31 Da suka karanta ta, sai suka yi farinciki saboda ƙarfafa musu gwiwa da aka yi. 32 Yahuda da Silas kuma, da ya ke su masu yin faɗin Maganar Allah ne, sai suka gargaɗi ’Yan’uwa da maganganu masu yawa, suka kuma ƙarfafa su. 33 Bayan sun yi ’yan kwanaki a wurin, sai ’Yan’uwa suka sallame su lafiya, su koma wurin waɗanda suka aiko su. 34 Amma Silas sai ya ga ya kyautu shi ya zauna a nan. 35 Bulus da Barnabas kuwa sai suka dakata a Antakiya, suna koyarwa suna kuma yin Bisharar Maganar Ubangiji, tare da wasu ma da yawa.

TAFIYAR BULUS TA BIYU YIN WA’AZI

36 Bayan wani lokaci sai Bulus ya ce da Barnabas, “Bari yanzu kuma mu koma mu dubo ’Yan’uwa a kowane garin da muka sanad da Maganar Ubangiji, mu ga yadda su ke.” 37 Barnabas kuwa ya so su tafi da Yobana, wanda a ke kira Markus. 38 Amma Bulus bai ga ya kyautu su tati da wanda ya janye jiki daga gare su a ƙasar Bamfiliya, ya ƙi tafiya aiki tare da su ba. 39 Sai matsanancin sabanin ra’ayi ya auku, har ya kai su ga rabuwa. Barnabas ya ɗauki Markus, suka shiga jirgin ruwa zuwa tsibirin Kubrus, 40 amma Bulus sai ya zaɓi Silas, kuma bayan ’Yan’uwa sun yi masa addu’a rahamar Ubangiji ta kiyaye shi, sai ya tafi. 41 Bulus ya zazzaga ƙasar Sham da ta Kilikiya, yana ta ƙarfafa ikiliziyai.

16

Bulus ya Dauki Timolawas a Listira

Sai kuma Bulus ya zo Darba da Listira. Akwai kuma wani almajiri a Listira, mai suna Timotawas, ɗan wata Bayahudiya mai bi, ubansa kuwa Bahelene ne. 2 Shi kuwa ’Yan’uwa da ke Listira da Ikoniya na yabonsa. 3 Sai Bulus ya so Timotawas ya rako shi, har ya yi masa kaciya saboda Yahudawan da ke waɗannan wuraren, don duk sun san ubansa Bahelene ne. 4 Lokacin da su ke tafiya suna bin gari-gari, sai suka riƙa gaya wa jama’a ka’idodin da Manzanni da dattawan ikiliziya suka ƙulla a Urushalima, don su kiyaye su. 5 Ta haka ikiliziyai suka ƙarfafa cikin Bangaskiya, kowace rana suna ƙara yawa.

6 Sai suka zazzaga ƙasar Firijiya da ta Galatiya, saboda Ruhu Tsattsarka ya hana su yin Maganar Ubangiji a ƙasar Asiya. 7 Da suka zo kan iyakar ƙasar Misiya, sai suka yi ƙofcarin zuwa ƙasar Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yardam musu ba. 8 Sai kuwa suka ratsa ƙasar Misiya, suka gangara zuwa Taruwasa. 9 Wata rana da dad dare sai aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, Yana roƙonsa Yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya ka taimake mu mana.” 10 Da kuwa ya samu wahayin, nan take sai muka nemi tafiya Makidoniya, muka tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu Bishara.

11 Shi ke nan fa, sai muka tashi a jirgin ruwa daga Taruwasa, muka miƙe sosai har tsibirin Samutaraki, washegari kuma sai Niyabolis, 12 daga nan kuma sai Filibi ta ƙasar Makidoniya, wadda ta ke babbar alkarya ce a wannan wajen, barikin Romawa ce kuma. A nan birnin muka yi ’yan kwanaki.

Lidiya ta Ba da Gaskiya

13 Ran Asabar sai muka fita ƙofar gari, muka je bakin kogi, inda mu ke tsammanin akwai wurin yin addu’a. Nan muka zauna, muka yi wa matan da suka taru magana. 14 Ɗaya daga cikin masu saurarommu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sai da jar haja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ne ya yi mata buɗi, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa. 15 Da aka yi mata babtisma tare da jama’ar gidanta, sai ta roƙe mu ta ce, “Da ya ke kun amince ni mai ba da gaskiya ga Ubangiji ce, to, sai ku zo gidana ku sauka.” Sai ta ci garimmu.

16 Wata rana muna tafiya wurin yin addu’a, sai muka gamu da wata yarinya mai taɓin aljani mai duba, tana kuwa samo wa iyayengijinta amfani mai yawa ta duban. 17 Sai ta riƙa bimmu, mu da Bulus, tana ihu tana cewa, “Mutanen nan fa bayin Allah Maɗaukaki ne, suna kuwa sanad da ku hanyar ceto!” 18 Haka ta dinga yi kwana da kwanaki, har Bulus ya ji haushi ƙwarai, ya juya ya ce da aljanin, “Na umarce ka da sunan Yesu Almasihu, ka rabu da ita.” Nan take kuwa ya rabu da ita.

An Kama Bulus da Silas

19 Da iyayengijinta suka ga hanyar samunsu ta toshe, sai suka danƙe Bulus da Silas, suka ja su bar bakin kasuwa gaban mahukunta. 20 Da suka kai su gaban alkalai, sai suka ce, “Mutanen nan suna birkita garimmu ƙwarai da gaske, Yahudawa ne kuwa. 21 Suna kuma koyad da al’adun da bai halatta mu karɓa ko mu bi ba, da ya ke mu ’yan-ƙasa ne a Roma.” 22 Sai jama’a suka ɗungumo musu gaba-ɗaya, alkalan kuma suka yi kaca-kaca da tufafinsu, suka tuttuɓe su, suka yi umarni a yi ta shauɗa musu tsumagu. 23 Da aka shasshaude su da gaske, sai aka jefa su kurkuku, aka umarci yari ya tsare su da kyau. 24 Shi kuwa da ya karɓi wannan umarni, sai ya jefa su can cikin basikel a kurkuku, ya sa su a turu.

Yarin Filibi ya Gaskata da Ubangiji Yesu

25 Wajen tsakad dare Bulus da Silas suna addu’a suna waƙoƙin yabon Allah, fursuna kuwa na sauraronsu, 26 farat sai aka yi wata babbar rawar-ƙasa, har harsashin ginin kurkukun ya raurawa. Nandanan sai ƙofofin suka bubbuɗe, marin kowa kuma ya ɓalle. 27 Da yari ya farka daga barci ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, sai ya zaro takobinsa, yana shirin kashe kansa, cewa ya ke fursunan sun gudu. 28 Amma sai Bulus ya ɗaka masa tsawa ya ce, “Kar ka cuci kanka, ai duk muna nan!” 29 Sai yari ya ce a kawo fitilu, ya yi wuf ya ruga ciki, ya faɗi gaban Bulus da Silas, yana rawar jiki don tsoro. 30 Sa’an nan ya fito da su waje, ya ce, “Ya shugabanni, me zan yi in sami ceto?” 31 Su kuwa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, sai ka sami ceto, kai da iyalinka.” 32 Sa’an nan suka gaya masa Maganar Ubangiii, shi da iyalinsa duka. 33 Nan take a cikin daren ya ɗebe su, ya wanke musu raunukansu. Nandanan kuwa aka yi masa babtisma. da dukkan iyalinsa. 34 Sannan ya kawo su gidansa, ya kawo musu abinci, ya yi ta farinciki matuƙa, don shi da iyalinsa duka sun gaskata da Allah.

An Saki Manzannin

35 Amma da gari ya waye, sai alkalan suka aiko dogarai, suka ce, “Wai a saki mutanen nan.” 36 Yari kuwa ya shaida wa Bulus maganar, ya ce, “Alkalai sun aiko a sake ku, saboda haka yanzu sai ku fito, ku tafi abinku.” 37 Amma sai Bulus ya ce musu, “Ai a fili suka daddoke mu, ba ko bin ba’asi, mu ma da ke ’yan-ƙasa a Roma, suka jefa mu kurkuku, yanzu kuma sa fid da mu a ɓoye? Haba! Sai dai su zo da kansu su fito da mu.” 38 Sai dogarai suka shaida wa alkalan wannan magana. Su kuwa da suka ji Bulus da Silas ’yan-ƙasa ne a Roma, sai suka tsorata. 39 Sa’an nan suka zo suka tubar musu, bayan kuma sun fito da su, sai suka roƙe su su bar garin. 40 To, da suka fita daga kurkukun, sai suka tafi wurin Lidiya. Bayan sun ga ’Yan’uwa, sun kuma ƙarrafa musu gwiwa, sai suka tashi.

17

Bulus ya yi Wa’azin Yesu a Tasalonika

To, da suka bi ta Amfibolis da Aboloniya, sai suka isa Tasalonika inda wata majami’ar Yahudawa ta ke. 2 Sai Bulus ya shiga wurinsu kamar yadda ya saba, Asabar uku a jere yana ba su hujjoji a cikin Littattafai Tsarkaka, 3 yana yi musu bayani, yana kuma tabbatarwa cewa lalle ne Almasihu yă sha wuya, ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Yesun nan da na ke sanar muku, shi ne Almasihu.” 4 Sai wasunsu suka amince, suka koma wajen Bulus da Silas, haka kuma babban taron Helenawa masu ibada, da manyan mata ba kaɗan ba. 5 Amma Yahudawa saboda kishi, sai suka ɗebi wasu ashararai, ’yan-iska, suka tara jama’a suka hargitsa garin kaf, suka fāɗa wa gidan Yasan, suna nemansu don su fito da su gaban taron jama’a. 6 Da ba su same su ba, sai suka jawo Yasan da wasu ’Yan’uwa har gaban mahukuntan garin, suna ihu suna cewa, “Mutanen nan masu ta da duniya tsaye ga su sun zo nan ma, 7 har ma Yasan ya sauke su! Dukkansu kuwa suna saɓa dokokin Kaisar, suna cewa wai wani ne sarki, wai shi Yesu.” 8 Da mutanen gari da mahukunta suka ji wannan, sai hankalinsu ya tashi. 9 Ba su sake su ba sai da suka karɓi kuɗin lamuni a hannun Yasan da sauransu.

Bulus ya je Biriya

10 Nandanan kuwa da dare ya yi, sai ’Yan’uwa suka sallami Bulus da Silas su tafi Biriya. Da suka isa can kuma sai suka shiga majami’ar Yahudawa. 11 To, waɗannan Yahudawan kam sun fi na Tasalonika dattaku, don sun karɓi Maganar Allah hannu biyu-biyu, suna ta bincika Littattafai Tsarkaka kowace rana, su ga ko abin haka ya ke. 12 Saboda haka da yawa daga cikinsu suka ba da gaskiya, har da wasu Helenawa ba kaɗan ba, mata masu daraja, da kuma maza. 13 Amma da Yahudawan Tasalonika suka ji labari Bulus na sanad da Maganar Allah a Biriya ma, sai suka je suka zuga taro masu yawa a can ma, suna ta da hankalinsu. 14 Nandanan kuwa sai ’Yan’uwa suka tura Bulus bakin bahar, amma Silas da Timotawas suka dakata a nan. 15 Waɗanda suka rako Bulus kuwa sai da suka kai shi har Atina. Bayan kuma Bulus ya yi musu sakon umarni zuwa wurin Silas da Timotawas cewa su zo wurinsa da gaggawa, sai suka tafi.

Bulus a Tudun Arasa a Atina

16 To, sa’ad da Bulus ke dakonsu a Atina, sai ya ji haushi ƙwarai da ya ga ko’ina gumaka ne a birnin. 17 Kowace rana sai ya yi ta muhawara a cikin majami’a da Yahudawa, da wasu masu ibada, da kuma waɗanda ya ke tararwa a bakin kasuwa. 18 Har wa yau kuma sai wasu Abikuriyawa da Sitokiyawa masu ilimi suka ci karo da shi. Wasu suka ce, “Me wannan suda ke faɗa?” Wasu kuwa suka ce, “Ga alama, mai yin wa’azin wasu bāƙin aljannu ne” —don kawai yana yin Bisharar Yesu, da kuma tashi daga matattu. 19 Sai suka riƙe shi suka kai shi Tudun Arasa, suka ce, “Ko ka faɗa mana wace irin baƙuwar koyarwa ce wannan da ka ke yi? 20 Domin ka kawo mana abin da ke baƙo a gare mu, muna kuwa so mu san ma’anarsa.” 21 Alhali kuwa duk Atinawa da baƙinsu ba abin da su ke yi sai kashe zarafinsu wajen jin baƙon abu, ko kuma ɗorad da shi.

22 Sai Bulus ya miƙe a tsakiyar Tudun Arasa, ya ce, “Ya ku mutanen Atina, na dai lura cewa ku masoya ibada ne ƙwarai, ta kowane fanni. 23 Don sa’ad da na ke zagawa, na duba abubuwan da ku ke yi wa ibada, bar ma na tarad da wani wurin hadaya da wannan rubutu a sama da shi, cewa, ‘Saboda Allahn da ba a sani ba.’ To, shi wanda ku ke wa sujada ba tare da kun san shi ba, shi na ke sanar muku. 24 Allahn da ya halicci duniya da dukkan abin da ke cikinta, shi da ya ke Ubangijin Sama da ƙasa, ba ya zama a ɗakunan ibada ginin mutun, 25 Haka kuma ba ya neman wani taimako gun mutun, ka ce wani abu ya ke bukata, tun da ya ke shi kansa ne ke ba dukkan mutane rai, da numfashi, da dukkan abubuwa. 26 Shi ne kuma ya halicci dukkan al’umma daga tsatso ɗaya, don su zauna a dukkan sararin duniya, ya kuma ƙayyade zamanansu da iyakokin ƙasashensu, 27 wato nufinsa shi ne su neme shi, ko watakila sa laluba su same shi, alhali kuwa ba ya nesa da kowane ɗayammu. 28 Don

‘Ta gare shi ne mu ke rayuwa, mu ke motsi, muka kuma kasance’,
kamar yadda wasu mawaƙanku ma suka ce,
‘Hakika, mu ma zuriyatasa ce.’

29 To, da ya ke mu zuriyar Allah ne, ai bai kamata. mu tsammaci Allah na kama da wata surar zinariya, ko ta azurfa, ko ta dutse ba, wadda mutun ya ƙago ta dabararsa. 30 Dā kam Allah ya kau da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko’ina su tuba, 31 tun da ya ke ya tsai da ranad da zai yi wa duniya shari’a, shari’ar gaskiya, ta kan mutumin nan da ya sanya, wannan kuwa ya tabbatar wa da dukkan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”

32 Da dai suka ji maganar tashin matattu, sai wasu suka yi ba’a, amma wasu suka ce, “Game da wannan magana kam, ma sake jin abin da za ka faɗa.” 33 Sai Bulus ya fita daga cikinsu. 34 Amma sai wasu mutane suka koma wajensa suka ba da gaskiya, a cikinsu har da Diyonisiyas, ɗam-majalisar Tudun Arasa, da wata mace mai suna Damarisa, da wasu dai haka.

18

Bulus a Korinti

Bayan haka sai Bulus ya tashi daga Atina ya tafi Korinti. 2 Can ya tarad da wani Bayahude mai suna Akila, asalinsa kuwa mutumin Fantas ne, bai daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, tare da matatasa Biriskila, don wai Kalaudiyas ya umarci dukkan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu. 3 Da ya ke kuma sana’arsu ɗaya ce, maɗinkan alfarwa ne, sai ya sauka a wurinsu, suka yi ta aiki tare. 4 Ya kuma yi ta ba da hujjoji a majami’a kowace Asabar, yana ta rinjayar Yahudawa da Helenawa.

5 Sa’ad da Silas da Timotawas suka zo daga Makidoniya, Bulus na dukufe kan yin wa’azi ba ji ba gani, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Almasihu dai Yesu ne. 6 Da suka musa masa, suna ta zaginsa, sai ya karkaɗe tufafinsa ya ce musu, “Alhakinku a wuyanku! Ni kam na fita. Daga yau wurin sauran al’umma zan je.” 7 Sai ya tashi daga nan ya je gidan wani mutum mai suna Titiyus Yustus mai ibada, gidansa kuwa dab da majami’a ya ke. 8 Sai Kirisbus, shugaban majami’ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama’ar gidansa duka. Korintiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus sai suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu babtisma. 9 Wata rana da dad dare, sai Ubangiji ya yi wa Buius wahayi, ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, sai dai ka yi ta wa’azi, kada ka yi shiru, 10 domin ina tare da kai, kuma ba wanda zai fāɗa ka ya cuce ka, don ina da mutane da yawa a wannan birnin.” 11 Sai Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da wata shida, yana ta koyad da Maganar Allah a cikinsu.

12 Amma sa’ad da Galiyo ke muƙaddashin ƙasar Akaya, sat Yahudawa suka tasam ma Bulus gaba-ɗaya suka kawo shi gaban shari’a, 13 suka ce, “Mutumin nan na rarrashin mutane wai su bauta wa Allah ta hanyad da Shari’ar Musa ta hana.” 14 Bulus na shirin yin magana ke nan sai Galiyo ya ce da Yahudawan, “Wohoho, ku Yahudawa! Da ma wani laifi ya yi, ko munafunci, da sai in iya sauraronku. 15 Amma tun da ya ke gardama ce kawai a kan kalmomi da sunaye da kuma shari’arku, ai sai ku ji da ita, ku da kanku. Ni kam ba ni da niyyar yin shari’ar irin waɗannan abubuwa.” 16 Sai ya kore su daga ɗakin shari’ar. 17 Sai duk suka kama Sastanisu, shugaban majami’ar, suka yi masa duka a gaban gadon shari’ar. Amma Galiyo ko yă kula.

18 Bulus kuwa sai da ya ƙara kwanaki da yawa, kuma bayan ya saisaye kansa a Kankinya don cika wa’adin da ya ɗauka, sai ya yi bankwana da ’Yan’uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Sham, tare da Biriskila da Akila. 19 Sai suka isa Afisa, a can ne kuma ya bar su, shi kuwa ya shiga majami’a ya yi muhawara da Yahudawa. 20 Sai suka roƙe shi ya ƙara jimawa a wurinsu, amma bai yarda ba. 21 Sai dai ya yi bankwana da su, ya ce, “Zan dawo wurinku in Allah ya so.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.

22 Da ya sauka a Kaisariya, sai ya je Urushalima ya gaisa da ikiliziya, sa’an nan ya tafi Antakiya.

TAFIYAR BULUS TA UKU YIN WA’AZI

23 Bayan ya ɗan jima a nan, sai ya tashi ya zazzaga ƙasar Galatiya da ta Firijiya, yana bin gari-gari, yana ƙarfafa dukkan masu bi.

24 To, sai wani Bayahude mai suna Afalas ya zo Afisa. Shi kuwa asalinsa mutumin Iskandariya ne, masani kuwa, ya san Littattafai Tsarkaka ƙwarai da gaske. 25 An karamad da shi tafarkin Ubangiji, da ya ke kuma mahimmanci ne ƙwarai, ya kan yi ta magana kan al’amuran Yesu, yana kuma koyad da su sosai, amma fa babtismar Yohana kaɗai ya sani. 26 Sai ya fara wa’azi gabagaɗi a majami’a, amma da Biriskila da Akila suka ji maganarsa, sai suka ja shi a jika, suka ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai. 27 Da ya so ƙetarewa zuwa ƙasar Akaya, sai ’Yan’uwa suka ƙarfafa masa gwiwa, suka rubuta wa masu bi wasiƙa su karɓe shi hannu biyu-biyu. Da kuwa ya isa, sai ya yi matuƙar taimako ga waɗanda suka ba da gaskiya ta rahamar Ubangiji, 28 don yā tuƙe hanzarin Yahudawa da gaske a gaban jama’a, yana tabbatar musu ta Littattafai Tsarkaka cewa Almasihu dai Yesu ne.

19

Bulus a Afisa

To, lokacin da Afalas ke Korinti, sai Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afsa. A can ya tarad da wasu masu bi, 2 sai ya ce da su, “Kun sami Ruhu Tsattsarka sa’ad da kuka ba da gaskiya?” Suka ce masa, “Ba mu ma ji akwai Ruhu Tsattsarka ba.” 3 Sai ya ce, “To, wace babtisma ke nan aka yi muku?” Suka ce, “Irin ta Yohana ce.” 4 Bulus ya ce, “Ai Yohana babtisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da Mai zuwa bayansa, wato Yesu.” 5 Da suka ji haka, sai aka yi musu babtisma su zama mallakar Ubangiji Yesu. 6 Da Bulus ya ɗora musu hannu, sai Ruhu Tsattsarka ya sauko musu, suka kuwa yi magana da wasu harsuna, suna yin faɗin Maganar Allah. 7 Su wajen sha biyu ne duka duka.

8 Sai ya shiga majami’a yana wa’azi gabagaɗi, kuma ya yi wata uku yana kawo musu hujjoji, yana kuma rinjayarsu a kan al’amarin Mulkin Allah. 9 Amma da wasu suka taurare, suka ƙi ba da gaskiya, suna kushe wannan Hanya gaban jama’a, sai ya janye jiki daga gare su, ya keɓe masu bi, yana ta kawo musu hujjoji kowace rana a makarantar Tiranas. 10 Shekara biyu ana wannan, har sai da dukkan mazauna ƙasar Asiya suka ji Maganar Ubangiji, Yahudawa da Helenawa duka.

11 Ta hannun Bulus kuma Allah ya yi wasu mu’ujizan da ba a saba gani ba, 12 har a kan kai wa marasa lafiya hankicansa, ko tufafinsa da ya ke sawa yana aiki, sun kuwa warke daga cuce-cucensu, baƙaƙen aIjannu kuma sun rabu da su. 13 Sai wasu Yahudawa masu yawo gari-gari, masu girka, suka yi ƙoƙarin kama sunan Ubangiji Yesu ga masu baƙaƙen aljannu, suna cewa, “Mun umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus ke wa’azi.” 14 To, akwai ’ya’ya bakwai maza, na wani babban malamin Yahudawa, mai suna Siba, duk suna yin wannan abu. 15 Amma sai aljanin ya amsa musu ya ce, “Yesu dai na san shi, na kuma san Bulus, to, ku kuma su wanene?” 16 Mutumin nan mai taɓin aljanin sai ya daka tsalle, ya fāɗa musu, ya fi ƙarfinsu dukkansu, ya ci dunguminsu, har suka fita daga gidan a guje, a tuɓe, suna masu rauni. 17 Wannan abu fa sai ya sanu ga dukkan mazauna Afisa, Yahudawa da Helenawa duka, duka kuma tsoro ya rufe su; aka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu. 18 Da yawa kuma daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya suka zo, suna bayyana ayyukansu ba rufi. 19 Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri sai suka tattaro littattafansu suka ƙone a gaban jama’a duka. Da suka yi wa littattafan nan ƙima, sai suka ga sun kai kuɗin azurfa dubu hamsin. 20 Sai kuma Maganar Ubangiji ta ƙara haɓaka, ta kuma fifita ƙwarai.

21 Bayan waɗannan al’amura sai Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.” 22 Da ya aiki mataimakansa biyu Makidoniya, wato Timotawas da Arastas, shi kuwa sai ya ɗan dakata a ƙasar Asiya.

Hargitsi a Afisa

23 A lokacin nan kuwa ba ƙaramin hargitsi aka yi game da wannan Hanya ba. 24 Don akwai wani maƙerin farfaru, mai suna Dimitiriyas, mai ƙera surorin ɗakin Artamisa da azurfa, ba kuwa ƙaramar riba ya ke jawo wa masu yin wannan sana’a ba. 25 Sai ya tara su da duk ma’aikatan irin wannan sana’ar, ya ce, “Ya ku jama’a, kun san fa da sana’an nan mu ke arziki. 26 Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyad da su, yana cewa, wai allolin da mutun ya ƙera ba alloli ba ne. 27 Ga shi kuma akwai haɗari, ba wai cinikimmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma ɗakin ibadan nan na uwargijiya Artamisa Mai girma zai zama ba a bakin komai ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka ke bauta wa.”

28 Da suka ji haka sai suka hasala ƙwarai, suka kuma ɗiba gaba-ɗaya suna cewa, “Girma ya tabbata ga Artamisa ta Afisawa!” 29 Sai garin duk ya ruɗe, jama’a suka ruga zuwa dandali gaba-ɗaya, suna jan Gayas da Aristarkus, mutanen Makidoniya, abokan tafiyar Bulus. 30 Bulus ya so shiga taron nan, amma sai masu bi suka hana shi. 31 Wasu zaɓaɓɓun mutanen ƙasar Asiya, waɗanda ke abokansa, su ma sai suka aika masa, suka roƙe shi kada ya kuskura ya shiga dandalin nan. 32 Taron kuwa, wasu su ta da murya su ce kaza, wasu su ce kaza, don duk taron a ruɗe ya ke, yawancinsu ma ba su san dalilin da ya sa suka taru ba. 33 Da Yahudawa suka gabatad da Iskandari, sai wasu suka ɗauka a kan shi ne sanadin abin. Iskandari kuwa sai ya ɗaga hannu a yi shiru, don ya kawo musu hanzari, 34 amma da suka fahinci cewa shi Bayahude ne, sai suka ɗiba gaba-ɗaya har wajen awa biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artamisa ta Afisawa!”

35 To, da magatakardan garin ya kwantad da hankalin jama’a, sai ya ce, “Haba mutanen Afisa! Wane mahaluƙi ne bai san cewa musamman birnin Afisawa ne ke kula da ɗakin ibada na Mai girma Artamisa ba, da kuma dutsen nan da ya faɗo daga sama? 36 To, da ya ke ba dama a yi musun waɗannan abubuwa, ai ya kamata ku nutsu, kada ku yi komai da garaje. 37 Ga shi kun kawo waɗannan mutanen nan, su kuwa ba su yi sata a ɗakin uwargijiya ba, ba su kuma saɓi uwargijiyarmu ba. 38 To, in Dimitiriyas da abokan sana’arsa suna da wata magana game da wani, ai ga ɗakin shari’a a buɗe, ga kuma mahukunta, sai su kai ƙara. 39 Amma in wani abu ku ke nema daban, to, ai sai a daidaita a majalisa ke nan. 40 Hakika muna cikin haɗarin amsa ƙara a kan tawaye saboda al’amarin nan na yau, tun da ya ke ba za mu iya ba da wani hanzari game da taron hargitsin nan ba.” 41 Da ya faɗi haka sai ya sallami taron.

20

Bulus ya Koma Makidoniya da Ƙasar Helenawa

Bayan hargowan nan ta kwanta, sai Bulus ya kira masu bi, kuma bayan ya ƙarfafa musu gwiwa, sai ya yi bankwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya. 2 Da ya zazzaga lardin nan, ya kuma ƙarfafa musu gwiwa ƙwarai, sai ya zo ƙasar Giris, 3 ya yi wata uku a nan. Kuma da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa’ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Sham, sai ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya. 4 Subataras Babiriye, ɗam Burus, shi ya raka shi, tare da Aristarkus da Sakundus, mutanen Tasalonika, da Gayas Badarbe, da Timotawas; har ma da Tikikus da Tarufimas mutanen Asiya, 5 waɗanda suka riga tafiya suka jira mu a Taruwasa. 6 Mu kuwa muka tashi daga Filibi a jirgin ruwa bayan Idin Burodi Marar Yisti, muka iske su a Taruwasa bayan kwana biyar. Nan muka zauna kwana bakwai.

7 A ranar farko ta mako kuma, da muka taru don gutsuttsura, burodi, sai Bulus ya yi musu jawabi, don ya yi niyyar tashi washegari; sai ya yi ta jan jawabin nasa har tsakad dare. 8 Akwai kuwa fitilu da yawa a benen da muka taru. 9 Da wani saurayi a zaune a kan taga, mai suna Aftikos, sai barci ya ci ƙarfinsa sa’ad da Bulus ya ke ta tsawaita jawabi; kuma da barci mai nauyi ya kwashe shi, sai ya faɗo daga can hawa na uku, aka ɗauke shi a mace. 10 Amma sai BuIus ya sauka ƙasa, ya miƙe a kansa, ya rungume shi, ya ce, “Kada ku damu, ai ya yi rai.” 11 Kuma da Bulus ya koma sama, ya gutsuttsura burodi ya ci, sai ya yi ta magana da su lokaci mai tsawo har gari ya waye, sa’an nan ya tashi. 12 Sai suka ɗauki saurayin nan a raye, daɗin da suka ji kuwa ba kaɗan ba ne.

13 Mu kuwa muka yi gaba zuwa jirgin, sai muka miƙa sai Asus da nufin ɗaukar Bulus daga can, don dā ma haka ya shirya, shi kuwa ya yi niyyar bi ta ƙasa. 14 Da ya same mu a Asus, sai muka ɗauke shi a jirgin, muka zo Mitilini. 15 Daga nan kuma muna tafe a jirgin ruwan dai, washegari kuma sai ga mu ɗaura da tsibirin Kiyos. Kashegari kuma sai ga mu a tsibirin Samas, washegari kuma sai Militus. 16 Dā ma kuwa Bulus ya ƙudura zai wuce Aftsa cikin jirgin, don kada ya yi jinkiri a Asiya, domin yana sauri, im mai yiwuwa ne ma, ya kai Urushalima a ranar Fentikos.

Bulus ya yi Bankwana da Dattawan Ikiliziyar Afisa

17 Daga Militus ne ya aika Afisa a kira masa dattawan ikiliziya. 18 Da suka zo wurinsa sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san irin zaman da na yi a cikinku, tun ran da na sa ƙafata a ƙasar Asiya, 19 ina bauta wa Ubangiji da matuƙar ƙankan-da-kai, har da hawaye, da gwagwarmaya iri-iri da na sha game da makircin Yahudawa. 20 Kun kuma san yadda ban ji nauyin sanad da ku kowane abu mai amfani ba, ina koya muku a sarari, da kuma gida-gida, 21 ina tabbatar wa Yahudawa da Helenawa duka sosai da sosai wajabcin tuba ga Allah, da kuma gaskatawa da Ubangijimmu Yesu. 22 To, ga shi kuma yanzu zan tafi Urushalima, Ruhu na iza ni, ban kuwa san abin da zai same ni a can ba, 23 sai dai Ruhu Tsattsarka ya kan riƙa tabbatar mini a kowane gari, cewa ɗauri da shan-wuya na dakona. 24 Amma ni ban mai da raina a bakin komai ba, bai kuma tsone mini ido ba, muddar zan iya cikasa aikina da kuma hidimad da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in tabbatad da Bisharar alherin Allah. 25 To, ga shi yanzu na san dukkanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku Bisharar Mulkin Allah. 26 Saboda haka ina dai tabbatar muku a yau, cewa na kuɓuta daga hakkin kowa. 27 Don ban ji nauyin sanad da ku dukkan nufin Allah ba. 28 Ku kula da kanku da kuma duk garken da Ruhu Tsattsarka ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon ikiliziyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa. 29 Na san cewa bayan tashina wasu miyagun kuraye za su shigo cikinku, ba kuwa za su ji tausayin garken ba. 30 Har ma a cikinku wasu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su. 31 Saboda haka sai ku zauna a faɗake, ku tuna cewa shekara uku ke nan ba dare ba rana, ban fasa yi wa kowa gargaɗi ba, har da hawaye. 32 To, yanzu na danƙa ku ga Ubangiji, maganar alherinsa kuma tă kiyaye ku, wadda ita ke da ikon inganta ku, ta kuma ba ku gado cikin dukkan waɗanda aka keɓe a tsarkake. 33 Ban yi ƙyashin kuɗin kowa ba, ko kuwa tufafin wani. 34 Ku da kanku kun san cewa hannuwan nan nawa su suka biya mini bukace-bukacena, da na waɗanda ke tare da ni. 35 Na zame muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta rau da gaɓa haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ “

36 Da Bulus ya faɗi haka, sai ya durƙusa, duka suka yi addu’a tare. 37 Sai duk suka fashe da kuka, suka rungume Bulus, suna ta sumbantarsa, 38 suna baƙinciki tun ba ma saboda maganad da ya faɗa ba, cewa ba za su ƙara ganinsa ba. Daganan sai suka rako shi har bakin jirgi.

21

Bulus a Sur

Sa’ad da muka rabu da su da kyar, sai muka shiga jirgi muka miƙe sosai zuwa tsibirin Kos, washegari kuma sai Rodusa, daga nan kuma sai Batara. 2 Da muka sami jirgi mai ƙetarewa zuwa ƙasar Finikiya, sai muka shiga muka tafi. 3 Da muka tsinkayo tsibirin Kubrus, sai muka mai da shi hagu, muka ci gaba zuwa ƙasar Sham, muka sauka a Sur, don a nan ne jirgin zai sauke kayansa. 4 Da muka sami inda masu bi su ke, sai muka zauna a nan kwana bakwai. Sai Ruhu Tsattsarka ya iza su suka gaya wa Bulus kada ya je Urushalima. 5 Amma da lokacin tashimmu ya yi, sai muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukkansu kuma har da matansu da ’ya’yansu, suka raka mu bayan gari, sa’an nan muka durƙusa a kan gaba, muka yi addu’a, muka yi bankwana da juna. 6 Sai muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.

Bulus a Kaisariya

7 Da muka gama tafiyarmu daga Sur, sai muka isa Talamayas muka gaisa da ’Yan’uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu. 8 Washegari muka tashi muka zo Kaisariya, kuma muka shiga gidan Filibus mai yin Bishara, wanda ya ke ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa. 9 Shi kuwa yana da ’ya’ya huɗu ’yammata, masu yin faɗin Maganar Allah. 10 To, muna nan zaune ’yan kwanaki, sai wani mai yin faɗin Maganar Allah, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya. 11 Da ya zo gare mu, sai ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sau da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Tsattsarka ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga sauran al’umma.’” 12 Da muka ji haka, sai mu da waɗanda ke wurin muka roƙi Bulus kada ya je Urushalima. 13 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan ku ke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai ni a shirye na ke, ba wai a ɗaure ni kawai ba, bar ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.” 14 Da dai ya ƙi rarrasuwa, sai muka yi shiru, muka ce, “Ubangiji ya yi yadda ya so.”

Bulus ya iso Urushalima

15 Bayan ’yan kwanakin nan sai muka shirya muka tafi Urushalima. 16 Wasu masu bi daga Kaisariya suka rako mu, suka kawo mu wurin Minasan mutumin Kubrus, wani daɗaɗɗen mai bi, wanda za mu sauka a gunsa.

17 Da muka zo Urushalima, sai ’Yan’uwa suka karɓe mu da murna. 18 Washegari sai Bulus ya tafi tare da mu wurin Yakubu, dattawan ikiliziya kuwa duk suna nan. 19 Bayan ya gaisa da su, sai ya shiga bayyana musu filla-filla abubuwan da Allah ya yi a cikin sauran al’umma ta kan aikinsa. 20 Su kuwa da suka ji haka, sai suka ɗaukaka Allah. Suka ce da Bulus, “To, kā gani, Ɗan’uwa, dubban mutane sun ba ‘da gaskiya a cikin Yahudawa, dukkansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari’ar Musa. 21 An kuwa sha gaya musu labarinka, cewa kai ne ka ke koya wa dukkan Yahudawan da ke cikin sauran al’umma su ya da Shari’ar Musa, Wai kuma kana ce musu kada su yi wa ’ya’yansu kaciya, ko kuwa su bi al’adu. 22 To, ƙaƙa ke nan? Lalle za su ji labarin zuwanka. 23 Saboda haka sai ka yi abin da za mu faɗa maka. Muna da mutum huɗu da suka ɗau wa’adi. 24 Sai ka tafi da su ku tsarkaka gaba-ɗaya, ka kuma biya musu komai don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai san cewa duk abin da aka gaya musu game da kai ba wata gaskiya a ciki, kuma kai ma kana kiyaye Shari’ar. 25 Amma game da sauran al’umma da suka ba da gaskiya, mun aika da wasiƙa a kan mun hukunta cewa su guji cin abin da aka yanka wa gunki, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin jini.” 26 Sa’an nan Bulus ya ɗebi mutanen nan, washegari kuma da suka tsarkaka tare, sai ya shiga Ɗakin Ibada don ya sanad da ranar cikar tsarkakewatasu, wato ranad da za a ba da baiko saboda kowannensu.

An Kamo Bulus

27 Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, kuma Yahudawan ƙasar Asiya suka gan shi a Ɗakin Ibada, sai suka zuga taron duka, suka danƙe shi, 28 suna ihu suna cewa, “Ya ku Bani Isra’ila, kururururu! Ga mutumin da ke bi ko’ina yana koya wa mutane su raina jama’armu da Shari’ar Musa, da kuma wannan wuri. Ban da haka kuma har ma ya kawo Helenawa Ɗakin Ibada, ya ƙazantad da wurin nan tsattsarka.” 29 Don da ma can sun ga Tarufimas Ba’afise tare da shi a cikin gari, sun kuma zaci cewa Bulus ya kawo shi Ɗakin Ibada. 30 Sai duk garin ya ruɗe, jama’a suka dungumo a guje suka danƙe Bulus, suka ja shi waje daga Ɗakin Ibada, nandanan kuma aka rufe ƙofofin. 31 Suna neman kashe shi ke nan, sai labari ya kai ga kwamandan bataliya, wai Urushalima duk ta hargitse. 32 Nan take sai ya ɗebi soja da kyaftin-kyaftin, suka ruga wajensu. Su kuwa da ganin kwamandan da soja sai suka daina dukan Bulus. 33 Sai kwamandan ya matsa kusa ya kama Bulus, ya yi umarni a ɗaure shi da sarƙa biyu, sa’an nan ya tambaya ko shi wanene, da abin da kuma ya yi. 34 Taron kuwa sai suka ɗau kururuwa, wasu su ce kaza, wasu su ce kaza. Don tsananin hargowa ma har ya kasa samun ainihin tushen maganar, sai ya yi umarni a kai shi barikin soja. 35 Da Bulus ya zo bakin matakala, sai da soja suka kinkime shi saboda haukan taron, 36 don taron jama’a na dannowa bayansu, suna ihu suna cewa, “A yi da shi!”

37 An yi kusan shigad da Bulus barikin soja ke nan, sai ya ce da kwamandan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai kwamandan ya ce, “Ashe, ka iya Helenanci? 38 Shin ba kai ne Bamisiren nan da shekarun baya ya haddasa tawaye ba, har ya ja mutanen nan dubu huɗu masu kisankai jeji?” 39 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Ai ni Bayahude ne na Tarsus ta ƙasar Kilikiya, ɗan shahararriyar alkarya, ina roƙonka ka bar ni in yi wa mutane jawabi.” 40 Da ya ba shi izini, sai Bulus ya tsaya a kan matakala, ya ɗaga wa jama’a hannu su yi shiru. Da suka yi tsit, sai ya yi musu magana da Yahudanci, ya ce:

22

Bulus Ya Ba Da Hujiojinsa

“Ya ku ’yan’uwa da shugabanni, ku ji hanzarin da zan kawo muku yanzu.”

2 Da suka ji ya yi musu magana da Yahudanci, sai suka ƙara nutsuwa. Sannan ya ce,

3 “Ni Bayahude ne, haifaffen Tarsus, ƙasar Kilikiya, amma a nan garin na girma, aka kuma karantad da ni wurin Gamaliyal, bisa ga tsarin tsanantacciyar hanyan nan ta Shari’ar kakannimmu. Ina mai himmar bauta wa Allah, kamar yadda dukkanku ku ke a yau, 4 har na tsananta wa masu bin wannan Hanya, ina karkashe su, ina ɗaure mutane maza da mata, ina jefa su a kurkuku. 5 Babban Malami ma da dukkan majalisar shugabannin jama’a za su iya shaidata; daga gunsu ne kuma na karɓi wasiƙu zuwa ga ’yan’uwammu Yahudawa, na tafi Dimashƙu, don in ɗebo waɗanda ke can ma, in zo da su Urushalima a ɗaure, a azabta su.

6 “Ina cikin tafiya, da na yi kusa da Dimashƙu, wajen rana tsaka, kwamfa sai wani matsanancin haske ya bayyano daga Sama, ya haskake kewayena. 7 Sai na faɗi, na kuma ji wata murya tana ce mini, ‘Shawulu, Shawulu, dom me ka ke tsananta minii? 8 Ni kuma na amsa na ce, ‘Wanene kai, ya Ubangiji?’ Sai ya ce mini, ‘Ni ne Yesu Banazare wanda ka ke tsananta wa.’ 9 To, waɗanda ke tare da ni sun ga hasken, amma ba su ji kalmomin mai yi mini maganan nan ba. 10 Sai na ce, ‘To, me zan yi, ya Ubangiji?’ Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi ka shiga Dimashƙu, a can ne za a faɗa maka duk abin da aka ɗora maka ka yi.’ 11 Kuma da na kasa gani saboda tsananin hasken nan, sai waɗanda ke tare da ni suka yi mini jagora, bar na isa Dimashƙu.

12 “Sai kuma wani mai suna Hananiya, mai bautar Allah ne wajen bin Shari’ar Musa, wanda duk Yahudawan da ke zaune a can ke yabo, 13 ya zo ya tsaya a kusa da ni, ya ce mini, ‘Ya Ɗan’uwana Shawulu, ganinka yă komo maka.’ Nan take ganina, ya komo, na kuwa gan shi. 14 Sai ya ce, ‘Allahn kakannimmu ya zaɓe ka kă san nufinsa, ka ga Mai gaskiyan nan, ka kuma ji jawabi daga bakinsa. 15 Don za ka zama mashaidinsa ga dukkan mutane game da abin da ka gani, ka kuma ji. 16 To, yanzu me ka ke jira? Tashi, a yi maka babtisma a wanke zunubanka, kana addu’a da sunansa.’

17 “Kuma da na komo Urushalima, ina addu’a a Ɗakin lbada, sai wahayi ya zo mini. 18 Sai na gan shi, yana ce mini, ‘Yi sauri maza ka fita daga Urushalima, don ba za su yarda da shaidarka a kan al’amarina ba.’ 19 Ni kuma na ce, ‘Ya Ubangiji, ai su ma kansu sun san cewa a kowace majami’a na ɗaɗɗaure waɗanda suka gaskata da kai, na kuma daddoke su. 20 Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus, mashaidin nan naka, ni ma ina tsaye a gun, ina goyon bayan abin da aka yi, har ma ina tsare da tufafin masu kisansa.’ 21 Sai ya ce mini, ‘Tashi ka tafi, zan aike ka can nesa wurin sauran al’umma.’”

An Daure Bulus da Tsirkiya

22 Har ya iso kalman nan suna ta sauraronsa, sai suka ɗau ihu suka ce, “A kashe shi! A raba irin mutumin nan da duniya, bai kyautu ya rayu ba!” 23 Da suka dinga ihu suna kaɗa mayafansu suna ta tula ƙura, 24 sai kwamandan ya yi umarni a kai Bulus barikin soja a tuhume shi da bulala, don yă san abin da ya sa su ke masa ihu haka. 25 Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, sai Bulus ya ce da kyaftin ɗin da ke tsaye kusa, “Ashe ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da ke ɗan-ƙasa a Roma bulala, ba ko bin ba’asi?” 26 Da kyaftin ɗin ya ji haka, sai ya je ya shaida wa kwamandan, ya ce, “Me ka ke shirin yi ne? Mutumin nan fa ɗan-ƙasa ne a Roma.” 27 Sai kwamandan ya zo ya ce da Bulus, “Faɗa mini gaskiya, kai kuwa ɗan-fasa ne a Roma?” Sai ya ce, “I.” 28 Sai kwamandan ya amsa ya ce, “Kai, ni fa da kuɗi masu yawa na sami zama ɗan-ƙasa a Roma.” Bulus ya ce, “Ni kuwa ɗan-ƙasa ne a Roma na asali kuwa.” 29 Saboda haka waɗanda ke shirin tuhumarsa, sai suka ja jiki daga wurinsa nandanan. Shi ma kwamandan da ya fahinci cewa Bulus ɗan-ƙasa ne a Roma sai ya tsorata, ga shi kuwa ya ɗaure shi.

30 Washegari kuma da kwamandan ya so sanin ainihin laifin da Yahudawa ke ɗora wa Bulus, sai ya kwance shi, ya yi umarni manyan malamai da dukkan majalisa su taru, sannan ya sauko da Bulus ya tsai da shi a gabansu.

23

Bulus a gaban Shari’a

Sai Bulus ya zuba wa majalisar ido ya ce, “Ya ku ’yan’uwa, bautar Allah na ke yi da zuciya garau bar ya zuwa yau.” 2 Sai Hananiya Babban Malami ya umarci waɗanda ke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa. 3 Sai Bulus ya ce masa, “Kai munafuki, kai ma Allah zai buge ka! Ashe wato kana zaune kana hukunta ni bisa Shari’ar Musa ne, ga shi kuwa kana yin umarni a doke ni, saɓanin Shari’ar?” 4 Sai waɗanda ke tsaye a wurin suka ce masa, “Kai, Babban Malamin Allah za ka zaga?” 5 Sai Bulus ya ce, “Ai ban san shi ne Babban Malami ba ’yan’uwa, don a rubuce ya ke, cewa, ‘Kada ka munana shugaban jama’a.’”

6 Amma da Bulus ya ga shashi ɗaya Sadukiyawa ne, ɗayan kuma Farisiyawa, sai ya daga murya a majalisar ya ce, “Ya ’yan’uwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗam Farisiyawa. Ga shi kuwa saboda na sa zuciya ga Tashin Matattu ne a ke mini shari’a.” 7 Da ya faɗi haka sai gardama ta tashi a tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, har taron ya rabu biyu. 8 Don Sadukiyawa sun ce wai ba Tashin Matattu, ba kuma mala’iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan duk akwai. 9 Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, kuma wasu malamai na ɗarikar Farisiyawa suka miƙe tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala’ika ya yi masa magana fa?” 10 Da gardamar ta yi tsanani, don gudun kada su yi kaca-kaca da Bulus, sai kwamandan ya umarci sojan su sauka su ƙwato shi daga wurinsu ƙarfi da yaji, su kawo shi barikin soja.

11 A cikin daren sai Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus, ya ce, “Ka yi ƙarfin-hali, don kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lalle ne ka shaide ni a Roma.”

Makircin Yahudawa bai ci ba

12 Da gari ya waye sai Yahudawa suka gama baki suka yi rantsuwa, cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kar Bulus. 13 Waɗanda suka ƙulla wannan makirci kuwa sun fi mutun arba’in. 14 Sai suka je wurin manyan malamai da shugabanni, suka ce, “Mun yi wata babbar rantsuwa, cewa za mu zauna ba ci ba sha sai mun kar Bulus. 15 Saboda haka yanzu ku da majalisa sai ku shaida wa kwamanda ya kawo muku shi, kamar kuna so ne ku ƙara bincika maganarsa sosai, mu kuwa a shirye mu ke mu kashe shi kafin ya iso.”

16 To, sai ɗan ’yar’uwar Bulus ya ji labarin fakon da za su yi ya kuma je ya shiga barikin soja ya gaya wa Bulus. 17 Bulus kuwa ya kira wani kyaftin ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin kwamanda, yana da wata magana da zai faɗa masa.” 18 Sai kyaftin ya ɗauki saurayin ya kai shi gun kwamandan, ya ce, “Fursunan nan ne Bulus ya kira ni, ya roƙe ni in kawo saurayin nan wurinka, don yana da wata maganad da zai gaya maka.” 19 Sai kwamandan ya kama hannun saurayin, ya ja shi waje ɗaya, ya tambaye shi a keɓance, “Wace magana za ka gaya mini?” 20 Yaron ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kai musu Bulus majalisa gobe, kamar suna so su ƙara bincika maganarsa sosai. 21 Amma kada ka yardam musu, don fiye da mutun arba’in daga cikinsu suna fakonsa, sun kuma yi rantsuwa a kan ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe shi. Yanzu kuwa a shirye su ke, yardarka kawai su ke jira.” 22 Sai kwamandan ya sallami saurayin, ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa ka sanad da ni maganan nan.”

An Kai Bulus Kaisariya

23 Sannan ya kira kyaftin biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba’in, da ’yam-masu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.” 24 Ya kuma yi umarni su shirya wa Bulus dabbobin da zai ban, don su kai shi wurin Gwamna Filikus lafiya. 25 Ya kuma rubuta wasiƙa, cewa:

26 “Daga Kalaudiyas Lisiyas, zuwa ga mafifici Gwamna Filikus. Gaisuwa mai yawa. 27 Bayan haka mutumin nan Yahudawa sun kama shi, kuma suna gab da kashe shi, sai na yi farat na je da soja na ƙwato shi, saboda na ji shi ɗan-ƙasa ne a Roma. 28 Da na so jin laifin da su ke zarginsa a kai, sai na kai shi majalisarsu. 29 Na kuwa tarar suna zarginsa ne a kan maganar Shari’arsu, amma laifin da suka ɗora masa bai kai kisa ko ɗauri ba. 30 Kuma da aka buɗa mini cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, sai nandanan na aika da shi gare ka, na kuma umarci masu ƙararsa su faɗi ƙararsu a gabanka. Wassalam.”

31 Saboda haka sai sojan suka ɗauki Bulus, kamar yadda aka umarce su, suka kai shi Antibatiris da dad dare. 32 Washegari kuma sai suka bar barade su ci gaba da shi, su kuwa suka koma barikin soja. 33 Da baraden suka isa Kaisariya, sai suka ba gwamna wasiƙar, suka kuma kai Bulus gabansa. 34 Da ya karanta wasiƙar, sai ya tambayi Bulus ko shi mutumin wane lardi ne. Da ya ji daga Kilikiya ya ke, 35 sai ya ce, “Zan saurari maganarka duka, im masu ƙararka sun zo.” Sai kuma ya yi umarni a tsare shi a faɗar Hirudus.

24

Bulus a Gaban Gwamna Filikus

Bayan kwana biyar sai Babban Malamin nan Hananiya, ya zo tare da wasu shugabanni, da kuma wani lauya, mai suna Tartulus, suka yi ƙarar Bulus gaban gwamna. 2 Da aka kirawo Bulus, sai Tartulus ya shiga faɗar laifinsa, ya ce,

“Ya mafifici Filikus, tun da ya ke ta gare ka ne mu ke zaman aminci ƙwarai, ta tsinkayarka ne kuma a ke kyautata zaman jama’armu, 3 kullum muna yarda da haka ƙwarai a ko’ina, tare da godiya ba iyaka. 4 Amma don kada in gajishe ka, ina roƙonka a cikin nasiharka, ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabimmu. 5 Mun tarad da mutumin nan fitinanne ne, shi ke ta da hargitsi tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya, kuma shi ne turun ɗarikar Nazarawa. 6 Har ma yana nema ya tozarta Ɗakin lbada, amma sai muka kama shi, da niyyar mu hukunta shi bisa Shari’armu. 7 Amma sai kwamanda Lisiyas ya zo ya ƙwace shi daga hannummu ƙarfi da yaji, 8 ya yi umarni masu ƙararsa su zo gabanka. In kuwa ka tuhume shi da kanka, za ka iya tabbatarwa daga bakinsa duk ƙarad da mu ke yi tāsa.”

9 Yahudawa ma sai suka goyi bayan haka, suna tabbatarwa haka abin ya ke.

10 Da gwamna ya alamta wa Bulus ya yi magana, sai ya amsa ya ce,

“Tun da na san ka yi shekaru da yawa kana yi wa jama’an nan shari’a, zan kawo hanzarina cikin amincewa. 11 Ai ka iya tabbatarwa, cewa bai fi kwana goma sha biyu ba tun da na tafi Urushalima yin sujada. 12 Ba su kuwa taɓa samuna ina muhawara da kowa ba, ko kuwa ta da husuma har mutane su taru a Ɗakin Ibada, ko a majami’u, ko kuwa a cikin birni. 13 Ba kuma za su iya tabbatar maka abin da yanzu su ke ƙarata a kai ba. 14 Amma na yarda cewa bisa Hanyan nan da su ke kira ‘Ɗarika’ na ke bauta wa Allahn kakannimmu, na ke kuma gaskata duk abin da ke rubuce a cikin Attaura da kuma Littattafan Annabawa. 15 Ina sa zuciya ga Allah, yadda su waɗannan ma su ke sawa, cewa za a ta da matattu, masu gaskiya da marasa gaskiya duka. 16 Saboda haka kullum na ke himma in kasance da zuciya marar abin zargi wurin Allah da wurin mutane. 17 To, bayan ’yan shekaru sai na je don in kai gudummawa ga kabilarmu, in kuma yi baiko. 18 Ina cikin yin haka sai suka same ni a tsarkake a cikin Ɗakin Ibada, ba kuwa da wani taro ba, balle hargowa. Amma akwai wasu Yahudawa daga ƙasar Asiya— 19 su ne ma kuwa ya kamata su zo nan gabanka su yi ƙarata, im ma suna da wata magana game da ni. 20 Ko kuwa ma waɗannan mutane kansu su faɗi laifina da suka saran, sa’ad da na tsaya gaban majalisa, 21 sai ko maganan nan ɗaya tak da na ɗaga murya na faɗa, sa’ad da na ke tsaye a cikinsu, cewa, ‘Game da maganar Tashin Matattu a ke yi mini shari’a a gabanku yau.’”

22 Filikus kuwa da ya ke yana da sahihin ilimi game da wannan Hanya sai ya dakatad da su, ya ce, “In kwamanda Lisiyas ya iso, zan yanke muku shari’a.” 23 Ya kuma ba kyaftin umarni ya tsare Bulus, amma ya sassauta masa, kada kuwa ya hana mutanensa zuwa wurinsa su kula da shi.

24 Bayan ’yan kwanaki sai Filikus ya zo tare da matarsa Durusila, wata Bayahudiya, sai ya aika a zo da Bulus, ya kuwa saurare shi kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu. 25 Bulus na ba da hujjoji a kan aikin gaskiya, da kamun-kai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, sai Filikus ya kaɗu, ya ka da baki ya ce, “Yanzu kam sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.” 26 Don yana sa ran Bulus zai ba shi kuɗi, shi ya sa ya yi ta kiransa a kai a kai, yana zance da shi. 27 Amma bayan shekara biyu sai Burkiyas Fastas ya canji Filikus. Filikus kuwa don neman faranta wa Yahudawa, sai ya bar Bulus a ɗaure.

25

Bulus a Gaban Gwamna Fastas

To, da Fastas ya iso lardinsa, bayan kwana uku sai ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urusbalima. 2 Sai manyan malamai da manyan Yahudawa suka kai ƙarar Bulus gunsa, suka roƙe shi 3 ya kyauta musu ya aika a zo da shi Urushalima, alhali kuwa sun shirya ’yan-kwanto su kashe shi a hanya. 4 Amma sai Fastas ya amsa ya ce, “Bulus na tsare a Kaisariya, ni ma kuwa da kaina ina niyyar zuwa can kwanan nan.” 5 Kuma ya ce, “Saboda haka, sai wasu manya a cikinku su taho tare da ni, in kuwa mutumin nan na da wani laifi, su yi ƙararsa.”

Am mai da Shari’ar Bulus gaban Kaisar

6 Bai fi kwana takwas ko goma a cikinsu ba, sai ya tafi Kaisariya. Washegari kuma sai ya zauna kan gadon shari’a, ya yi umarni a zo da Bulus. 7 Da ya zo, sai Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka kewaye shi a tsaitsaye, suna ta kawo ƙararraki masu yawa masu tsanani game da shi, waɗanda ma suka kasa tabbatarwa. 8 Amma sai Bulus ya kawo hanzarinsa ya ce, “Ni ban yi wani laifi game da shari’ar Yahudawa, ko Ɗakin Ibada, ko game da Kaisar ba, ko kaɗan.” 9 Fastas kuwa don neman faranta wa Yahudawa, sai ya amsa ya ce da Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a kan waɗannan abubuwa a gabana?” 10 Amma sai Bulus ya ce, “Ai tsaye na ke a kotun Kaisar, inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wa Yahudawa wani laifi ba, kai kanka kuwa ka san da haka sarai. 11 To, in ni mai laifi ne, har na aikata abin da ya isa kisa, ai ba zan guji a kashe ni ba; amma im ba wata gaskiya cikin ƙarata da su ke yi, to, ba mai iya bashe ni gare su don faranta musu. Na nemi a mai da shari’ata gaban Kaisar.” 12 Bayan Fastas ya yi shawara da majalisa, sai ya amsa ya ce, “To, ka nemi a mai da shari’arka gaban Kaisar! Gun Kaisar kuwa za ka tafi.”

Fastas ya gaya wa Agaribas Labarin Bulus

13 Bayan ’yan kwanaki sai Sarki Agaribas da Barniki suka zo Kaisariya don su yi wa Fastas maraba. 14 Da ya ke kuma sun yi kwanaki da dama a can, sai Fastas ya rattaba wa sarki labarin Bulus, ya ce, “Akwai wani mutumin da Filikus ya bari a ɗaure, 15 wanda sa’ad da na ke Urushalima manyan malamai da shugabannin Yahudawa suka kawo mini ƙararsa, suka roƙe ni in yi masa hukunci. 16 Ni kuwa sai na amsa musu na ce ba al’adar Romawa ba ce a yi wa mutun hukunci don faranta wa wani, ba tare da masu ƙarar, da wanda aka ƙarata, sun kwanta a gaban shari’a ba, ya kuma sami damar kawo hanzarinsa game da ƙarad da aka yi tāsa. 17 Saboda haka da suka zo nan tare, ban yi wani jinkiri ba, sai kawai na hau gadon shari’a washegari, na kuma yi umarni a kawo mutumin. 18 Da masu ƙarar suka tashi tsaye, ba su kawo wata mummunar ƙara yadda na zata game da shi ba, 19 sai dai wasu maganganu da suka ɗora masa game da addininsu, da kuma wani wai shi Yesu, wanda ya mutu, amma Bulus ya tsaya a kan wai yana da rai. 20 Ni kuwa da na rasa yadda zan bincika waɗannan abubuwa, sai na tambayi Bulus ko ya yarda ya je Urushalima a yi masa shari’a a can a kan waɗannan abubuwa. 21 Amma da Bulus ya nemi a dakatad da maganarsa sai Augustas ya duba ta, sai na yi umarni a tsare shi har kafin in aika da shi gun Kaisar.” 22 Sai Agaribas ya ce da Fastas, “Ni ma dai na so in saurari mutumin nan da kaina.” Fastas ya ce, “Ka kuwa ji shi gobe.”

23 To, washegari sai Agaribas da Barniki suka zo cikin alfarma, suka shiga ɗakin majalisa tare da kwamandodi da kuma jigajigan garin. Sai aka shigo da Bulus da umarnin Fastas. 24 Sai Fastas ya ce, “Ya Sarki Agaribas da dukkan mutanen da ke nan tare da mu, kun ga mutumin nan da duk jama’ar Yahudawa suka kawo mini ƙararsa a Urushalima, da kuma nan, suna ihu wai bai kamata a bar shi da rai ba. 25 Amma ni ban ga ya yi wani abin da ya isa kisa ba. Tun da kuma shi kansa ya nemi a mai da shari’arsa gaban Augustas, sai na ƙudura in aika da shi wurinsa. 26 Amma ba ni da wata tabbatacciyar maganad da zan rubuta wa ubangijina game da shi. Saboda haka na kawo shi gabanku, musamman kuwa gabanka, ya Sarki Agaribas, don bayan an yi bincike, ko na sami abin da zan rubuta. 27 Don ni, a ganina, wauta ce a aika da fursuna, ba tare da an nuna laifuffukan da ya yi ba.”

26

BuIus ya Kawo Hanzarinsa a Gaban Agaribas

Daganan sai Agaribas ya ce da Bulus, “Am ba ka izinin yin magana.” Sannan fa Bulus ya ɗaga hannu, ya fara kawo hanzarinsa ya ce,

2 “Lalle na yi arziki, ya Sarki Agaribas, da ya ke a gabanka ne zan kawo hanzarina yau game da duk ƙarata da Yahudawa suka yi, 3 musamman da ya ke gwani ne kai ga sanin al’adun Yahudawa da maganganunsu. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.

4 “Irin zaman da na yi tun daga ƙuruciyata, wato tun da farko, a cikin jama’armu da kuma a Urushalima har ya zuwa yau, sananne ne ga dukkan Yahudawa. 5 Sun sani tun ainihi, in dai za su yarda su yi shaida, cewa lalle ni Bafarisiye ne bisa ɗarikan nan da ta fi tsanani cikin addinin nan namu. 6 Ai saboda na sa zuciya ga cikar alkawarin nan ne da Allah ya yi wa kakannimmu na ke nan tsaye a ke mini shari’a. 7 Alkawarin nan kuwa shi ne wanda kabilummu goma sha biyu ke himmantuwa ga bauta wa Allah dare da rana, suna sa zuciya su ga cikarsa. Kuma saboda sazuciyan nan ne fa Yahudawa ke ƙarata, ya sarki! 8 Yaya cewa Allah na ta da matattu ya ƙi gaskatuwa a gare ku?

9 “To, ni kaina ma a dā na ga kamar wajibi ne in yi abubuwa da yawa na gāba da sunan Yesu Banazare. 10 Na kuwa yi haka a Urushalima, har na sami izini daga manyan malamai, na ƙulle tsarkaka da yawa a kurkuku. Har ma lokacin da a ke kashe su ina goyon bayan haka. 11 Na kuma sha gwada musu azaba a dukkan majami’u, ina ƙoƙarin sa su yin saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har wasu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.

12 “Cikin haka ne, ina tafiya Dimashƙu da izinin manyan malamai da kuma saƙonsu, 13 da rana tsaka a kan hanya, ya sarki, sai na ga wani haske ya bayyano daga Sama, fiye da hasken rana, duk ya haskake kewayena da abokan tafiyata. 14 Da duk muka faɗi, sai na ji wata murya tana ce mini da. Yahudanci, ‘Shawulu, Shawulu, dom me ka ke tsananta mini? Ba alheri ba ne a gare ka ka harbad da maganad da Allah ke kimsa maka a zuci.’ 15 Ni kuwa na. ce, ‘Wanene kai, ya Ubangiji?’ Sai Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda ka ke tsananta wa. 16 Amma tashi ka miƙe tsaye, gama na bayyana a gare ka ne da wannan maƙasudi, wato in sanya ka mai hidima, kuma mashaidi, na abubuwan da ka gani, da kuma abubuwa waɗanda ta cikinsu ne zan bayyana a gare ka. 17 Zan kuɓutad da kai daga Jama’a da kuma sauran al’umma, waɗanda zan aike ka gare su, 18 don ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, don su sami gafarar zunubai, da kuma gādo cikin waɗanda aka keɓe a tsarkake saboda sun gaskata da ni.’

19 “Saboda haka, ya Sarki Agaribas, ban ƙi biyayya ga wahayin nan da ya zo mini daga Sama ba. 20 Da fari sai na yi wa mutanen Dimashƙu wa’azi, sannan na yi a Urushalima da dukkan kewayen ƙasar Yahudiya, sannan kuma na yi wa sauran al’umma, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubansu. 21 Saboda wannan dalilin ne Yahudawa suka kama ni a Ɗakin lbada, har suna neman kashe ni. 22 Da na sami taimakon Allah kuwa, ga ni nan har yanzu, ina shaidarwa ga babba da yaro, ba na faɗar komai sai abin da Annabawa da Musa suka ce zai auku, 23 cewa dai lalle ne Almasihu yă sha wuya, kuma shi ne zai fara tashi daga matattu, ya sanad da Jama’a da sauran al’umma Maganar haske.”

24 Bulus na cikin kawo hanzarinsa, sai Fastas ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Haba Bulus, kai dai akwai ruɗaɗɗe, yawan karatunka shi ke juye maka kai.” 25 Amma sai Bulus ya ce, “Ya mafifici Fastas, ai ban ruɗe ba, gaskiya na ke faɗa, cikin nutsuwa kuwa. 26 Ai al’amarin nan sananne ne ga sarki, ina kuma masa magana gabagaɗi ne, gama na tabbata babu abin da ya kubce wa hankalinsa cikin al’amarin nan, don wannan abu ba a ɓoye aka yi shi ba. 27 Ya Sarki Agaribas, ka gaskata Littattafan Annabawa? Na dai sani ka gaskata.” 28 Sai Agaribas ya ce da Bulus, “Wato da ɗan wannan ka ke nufin mai da ni Kirista?” 29 Bulus kuwa ya ce, “Ko da ɗan wannan dai, ko da mai yawa, ina fata ga Allah, ba kai kaɗai ba, har ma duk waɗanda ke saurarona a yau, su zama kamar yadda na ke, sai dai ban da sarƙan nan.”

An Tarar Bulus ba shi da Laifi

30 Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Barniki, da waɗanda ke zaune tare da su. 31 Bayan sun keɓe waje ɗaya, sai suka yi shawara, suka ce, “Ai mutumin nan bai yi wani abin da ya isa kisa ko dauri ba.” 32 Agaribas kuma ya ce da Fastas, “Ba don dai mutumin nan ya riga ya nerni a mai da shari’atasa gaban Kaisar ba, da sai ma a sake shi.”

27

Tafiyar Bulus Roma a Jirgin Ruwa

Da aka shirya mu tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da wasu fursuna a hannun wani kyaftin, mai suna Yuliyas, na bataliyar Augustas. 42 Da muka shiga wani jirgi na Adaramatiya, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da ke gaɓar Asiya, sai muka fara tafiya. Aristarkus kuwa, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, na tare da mu. 3 Washegari sai ga mu a Saida. Yuliyas kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya ba shi izini ya je ya gano abokansa, su yi masa taimako. 4 Da muka tashi daga nan a jirgin ruwa sai muka zaga ta bayan tsibirin Kubrus, saboda iska na mai da mu baya. 5 Bayan mun ƙetare bahar ɗin da ke kusa da ƙasar Kilikiya da ta Bamfiliya, sai muka isa Mira ta ƙasar Likiya. 6 A nan kyaftin ya sami wani jirgin Iskandariya mai zuwa ƙasar Italiya, ya sa mu a ciki. 7 Muka yi kwana da kwanaki muna tafiya kaɗan-kaɗan, har da kyar muka kai kusa da Nidas. Da dai iska ta hana mu cin gaba, sai muka zaga ta bayan tsibirin Karita kusa da Salmoni. 8 Muna bin gefen gaɓarsa da kyar, har muka isa wani wuri wai shi Amintacciyar Mafaka, wadda ta ke kusa da Birnin Lasiya.

9 Da ya ke am ɓata lokaci mai yawa, tafiyar ma ta riga ta zama mai hatsari, lokacin da Yahudawa ke hana kansu abinci kuwa ya wuce, sai Bulus ya gargaɗe su, 10 ya ce musu, “Ya ku jama’a, na dai ga tafiyan nan za ta zamanto da masifa da hasara mai yawa, ba wai ta kaya da jirgi kawai ba, har ma ta rayukammu.” 11 Amma kyaftin sai ya fi mai da hankali ga maganar kyaftin ɗin jirgin da kuma ta mai jirgin, a kan abin da Bulus ya faɗa. 12 Kuma da ya ke mafakan nan ba ta kamaci jirage su ci damuna a ciki ba, sai yawanci suka kawo shawara a tashi daga nan, ko ta ƙaƙa su iya kaiwa Finikas, wata mafakar tsibirin Karita, mai duban gabas-maso-arewa da kuma gabas-maso-kudu, su ci damuna a can.

Babban Hadiri a Bahar

13 Da iska ta buso daga kudu sannu-sannu, a tsammaninsu muradinsu ya biya, sai suka janye turke suka bi gefen tsibirin Karita, dab da gaci. 14 Ba da jimawa ba kuwa sai ga wata gawurtacciyar iska da a ke kira Yurokilidon ta bugo daga tsibirin. 15 Da iskar ta bugo jirgin, har ya kam fuskantarta, sai muka sallama mata, ta yi ta kora mu. 16 Da muka bi ta jikin wani ɗan tsibiri wai shi Kalauda, sai muka samu muka yi iko da ƙaramin jirgimmu da kyar. 17 Bayan sun jawo shi kan babban jirgi, sai suka yi dabara suka ɗaɗɗaura igiyoyi ta bayan babban jirgin, suka rage shi. Don kuma gudun kada a fyaɗa su yashin nan na Sirtis mai makakkafiya, sai suka sauke filafilai, aka kora jirgin haka. 18 Saboda hadiri na sa mu tangadi ƙwarai da gaske, washegari sai suka fara watsad da kayan da jirgin ya ɗauko, a ruwa. 19 A rana ta uku kuma, su da kansu suka jefad da kayan aikin jirgin. 20 Da dai muka yi kwana da kwanaki ba mu ga rana ko taurari ba, gawurtacciyar iskar hadiri kuma ta yi ta bugummu, sai muka fid da zuciya da tsira.

21 Da ya ke an daɗe ba cin abinci, sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyarsu, ya ce, “Ya ku jama’a, da kun ji maganata, da ba ku taso daga tsibirin Karita kun faɗa wannan masifa da hasara ba. 22 To, yanzu ina yi muku gargaɗi ku yi ƙarfin-hali, don ba wanda zai yi hasarar ransa a cikinku, sai dai a yi hasarar jirgin. 23 Don a daren jiya wani mala’ikan Allahn da ke ni nasa ne, na ke kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni, 24 ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle sai ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma Allah ya amsa ya yardam maka duk abokan tafiyarka su kuɓuta.’ 25 Saboda haka sai ku yi ƙarfin-hali, ya ku jama’a, don na gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka za a yi. 26 Amma fa lalle ne a fyaɗa mu wani tsibirin.”

27 A dare na goma sha huɗu, ana ta kora mu sakaka a bahar Adariya, wajen tsakad dare sai masu tuƙin suka zaci mun yi kusa da ƙasa. 28 Sai suka gwada zurfin ruwan, suka sami gaba ashirin; da muka ci gaba kaɗan, sai suka sake gwadawa, suka sami gaba goma sha biyar. 29 Don gudun kada a fyaɗa mu kan duwatsu, sai suka saki turaka huɗu na bayan jirgin, suka ƙagauta gari ya waye. 30 Masu tuƙin na neman gudu daga jirgin ke nan, har sun zura ƙaramin jirgi cikin ruwa, wai don a ga kamar za su ja turaka ne daga goshin jirgin su sake su, 31 sai Bulus ya ce da kyaftin ɗin da kuma sojan, “Im mutanen nan ba su tsaya cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.” 32 Sai sojan suka yayyanke igiyoyin ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.

33 Da gari ya yi kusan wayewa sai Bulus ya yi ta ba su magana, su taɓa ɗan abinci, ya ce, “Yau fa kwana goma sha huɗu ke nan ku ke zaune a faɗake, kuna fargaba, ba wani abin da kuka ci. 34 Saboda haka ku taɓa ɗan abinci mana, don lafiyarku, tun da ya ke ba wanda ko gashin kansa zai yi ciwo a cikinku.” 35 Da ya faɗi haka, sai ya ɗauki curin burodi, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sannan ya gutsuttsura shi ya fara ci. 36 Sai duk suka farfaɗo, su ma kansu suka ci abinci. 37 Mu duka a cikin jirgin kuwa mutum metan da saba’in da shida ne. 38 Da suka ci suka ƙoshi, sai suka riƙa rage wa jirgin nauyi, suka yi ta zub da alkama cikin ruwa.

Jirgin ya Rugurguje

39 Da gari ya waye ba su shaida ƙasar ba, amma dai sun lura da wani lungu mai gaɓar yashi, sai kuma suka yi shawara im mai yiwuwa ne su kai jirgin kan yashin. 40 Sai suka daddatse turakan duka, suka bar su a ruwa, suna kuma ɓalle maɗaurin sitiyari a lokacin, sannan kuma suka ta da filafilan goshin jirgin daidai iska, suka doshi gaɓar yashin. 41 Amma da muka isa wata mahaɗar ruwa, sai suka tura jirgin ya dunguri yashi, har goshinsa ya cije ya kasa motsi, ƙarshensa kuma ya fara rugurgujewa saboda haukan raƙuman-ruwa. 42 Sai sojan suka yi niyya su kashe fursuna, wai don kada wani ya yi ninƙaya ya tsira. 43 Amma kyaftin da ya so kuɓutad da Bulus, sai ya hana i da nufinsu, ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara faɗawa zuwa gaci, 44 sauran kuwa wasu su bi katako, wasu kuma su bi guntayen katakin jirgin. Da haka duk suka kai gaci lafiya.

28

Kububuwa ta Ɗafe wa Bulus a Hannu

Bayan mun tsira, sai muka ji ashe sunan tsibirin nan Malta ne. 2 Mutanen garin kuwa sun yi mana alheri matuƙar alheri, don sun hura wuta sun karɓe mu mu duka, saboda ana ruwa, ga kuma sanyi. 3 Sa’ad da Bulus ya tattaro wasu ƙirare rungume guda ya sa a wutar, sai ga wata kububuwa ta ɓullo saboda zafi, ta ɗafe masa a hannu. 4 Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan maƙale a hannun Bulus, sai suka ce da juna, “Kai, lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da ya ke ya kuɓuta daga bahar, duk da haka alhaki na binsa sai ya mutu.” 5 Bulus kuwa sai ya karkaɗe ƙwaron cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba. 6 Su kuwa suna zaton wurin zai kumbura, ko kuwa faraɗ-ɗaya ya faɗi matacce. Amma da aka daɗe suka ga ba abin da ya same shi, sai suka sake magana suka ce lalle shi wani allah ne.

Bulus ya Warkad da Uban Shugaban Malta

7 Nan kusa kuwa akwai wani fili, mallakar shugaban tsibirin nan, mai suna Babiliyas. Shi ne ya karɓe mu, ya sauke mu a cikin martaba har kwana uku. 8 Ashe uban Babiliyas na kwance, yana fama da zazzaɓi da atuni. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi addu’a, ya ɗora masa hannu ya warkad da shi. 9 Da aka yi haka sai duk sauran marasa lafiya a tsibirin suka riƙa zuwa ana warkad da su. 10 Suka yi mana kyauta mai yawa, da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, sai suka yi ta tara mana duk irin abubuwan da mu ke bukata.

11 Bayan wata uku sai muka tashi cikin wani jirgin Iskandariya wanda ya ci damuna a nan tsibirin. An kuwa yi masa alama da surar Tagwayen Maza. 12 Da muka zo Sirakusa sai muka kwana uku a nan. 13 Daga nan kuma muka zaga sai ga mu a Rigiyum. Da muka kwana sai iska ta taso daga kudu, washegari kuma muka kai Butiyoli. 14 Nan muka tarad da wasu ’Yan’uwa, suka roƙe mu mu kwana bakwai tare da su. Da haka dai har muka isa Roma. 15 Da ’Yan’uwa na can suka ji labarimmu, sai da suka zo taryemmu har Kasuwar Abiya, da kuma wurin nan da a ke kira Maciya Uku. Da kuwa Bulus ya sadu da su, sai ya yi godiya ga Allah, kuma jikinsa ya yi ƙarfi. 16 Da muka shiga Roma sai aka yarje wa Bulus ya je ya sauka abinsa tare da sojan da ke gadinsa.

Bulus a Birnin Roma

17 Bayan kwana uku sai ya kira manyan Yahudawan birnin. Da suka taru sai ya ce musu, “ Ya ku ’yan’uwa, ko da ya ke ban yi wa jama’armu wani laifi ba, ko laifi game da al’adun kakannimmu, duk da haka am bashe ni ɗaurarre ga Romawa tun daga Urushalima. 18 Su kuwa da suka tuhume ni, sai suka so su sake ni, don ban yi wani laifin da ya isa kisa ba. 19 Amma da Yahudawa suka ƙi yarda, sai ya zame mini dole in nemi a mai da shari’ata gaban Kaisar —ba wai don ina ƙarar jama’armu ba ne. 20 Shi ya sa na nemi in gana da ku, tun da ya ke dai saboda sazuciyan nan da Bani Isra’ila ke yi ne na ke ɗaure da sarƙan nan.” 21 Sai suka ce masa, “Mu kam, ba mu sami wata wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, ba kuwa wani ɗan’uwammu da ya zo nan ya kawo labarinka, ko ya faɗi wata mummunar magana game da kai. 22 Amma muna so mu ji daga bakinka abin da ke ra’ayinka, don in dai ta ɗariƙan nan ne, mun san ko’ina ana kushenta.”

Bulus ya fara Wa’azi a Roma

23 Da suka sa masa rana, sai suka zo masauƙinsa su da yawa. Sa’an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta tabbatar musu Maganar Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu kan al’amarin Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da Littattafan Annabawa. 24 Wasu sun ba da kai ga abin da ya faɗa, amma wasu sun ƙi gaskatawa. 25 Da suka kasa yarda a junansu, kafin su watse sai Bulus ya yi musu magana ɗaya ya ce, “Ashe kuwa Ruhu Tsattsarka daidai ya faɗa, da ya yi wa kakanninku magana ta bakin Annabi Ishaya, cewa,

26 ‘Je ka wurin jama’an nan, ka ce,
Za ku ji kam, amma ba za ku fahinta ba faufau,
Za kuma ku gani, amma ba za ku gane ba faufau.
27 Don zuciyar jama’an nan ta yi kanta,
Sun toshe kunnuwansu,
Sun kuma runtse idanunsu,
Wai don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu,
Su kuma fahinta a zuciyarsu,
Har su juyo gare ni in warkad da su.’
28 To, sai ku san cewa wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga sauran al’umma; su kam za su saurara.”

29 Da ya faɗi haka, sai Yahudawa suka tashi suna ta muhawara da juna.

30 Sai Bulus ya zauna nan a gidan da ya ke haya har shekara biyu cikakku, yana maraba da duk wanda ya je wurinsa 31 yana ta wa’azin Mulkin Allah, da koyad da al’amarin Ubangiji Yesu Almasihu gabagaɗi, ba tare da wani hani ba.


WASIƘAR BULUS
ZUWA GA
ROMAWA

1

Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, Manzo kirayayye, keɓaɓɓe don yin Bisharar Allah, 2 wadda Allah ya yi alkawari tun dā, ta bakin annabawansa cikin Littattafai Tsarkaka, 3 wato Bishara game da Ɗansa, wanda zamansa mutun ta zuriyar Dawuda ne, 4 amma ta Tsattsarkan Ruhunsa an ayyana shi Ɗan Allah ne ta kwakkwarar shaidan nan ta tashinsa daga matattu, wato Yesu Almasihu Ubangijimmu, 5 wanda ta kansa ne muka sami alheri da kuma manzanci, don jawo dukkan al’ummai su yi biyayya ga Bangaskiya, saboda sunansa, 6 cikinsu har da ku ma da ke kirayayyun Yesu Almasihu, 7 zuwa ga dukkan ƙaunatattun Allah da ke Roma, tsarkaka kirayayyu.

Alheri da aminci na Allah Ubammu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Bisharar Ceto

8 Da farko dai ina gode wa Allahna ta kan Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko’ina a cikin duniya. 9 Don kuwa Allah, wanda na ke bauta wa a ruhuna ta yin Bisharar Ɗansa, shi ne mashaidina a kan yadda kullum ba na fasa ambatonku a cikin addu’ata, 10 ina addu’a, ko ta ƙaƙa, da yardar Allah yanzu kam in sami arzikin zuwa wurinku. 11 Domin ina dokin ganinku, in ni’imta ku da wata baiwa daga Ruhu Tsattsarka, don ku ƙarfafa. 12 Wato ni da ku, mu ƙarfafa wa juna gwiwa ta bangaskiyarmu, tawa da taku. 13 Ina so ku sani, ’Yan’uwa, na sha ɗaura niyyar zuwa wurinku, ko da ya ke har yanzu ba a yardam mini ba, don ku ma in ga wani amfani a gare ku, kamar yadda na gani a cikin sauran al’umma. 14 Akwai hakkin Helenawa, da na bare, da na masu ilimi, da na jahilai duka a kaina. 15 Saboda haka, in don ta ni ne, ina da himmar ku ma in yi muku Bishara, ku da ke Roma.

BANGASKIYA CE RAGAMAR SAMUN KARƁUWA GA ALLAH

16 Ni ba na ƙyamar Bishara, don ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa’an nan kuma sauran al’umma. 17 Don a cikinta Allah ya bayyana hanyar samun karɓuwa gare shi, wadda gaba da baya duk bangaskiya ce ragamatata, yadda ya ke a rubuce, cewa, “Mai samun karɓuwa ga Allah ta bangaskiya, zai rayu.”

Azabar Allah a kan Marasa bin Allah

18 Ana bayyana azabar Allah daga Sama a kan dukkan rashin bin Allah, da aikin rashin gaskiya na mutanen da ke danne gaskiya ta aikin rashin gaskiyarsu. 19 Domin abin da za a iya sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su, don Allah ne ya bayyana musu shi. 20 Tun daga halittar duniya al’amuran Allah marasa ganuwa, wato ikonsa madawwami, da kasancewarsa Allah, sun fahintu sarai, kuma ta hanyar abubuwan da aka halitta ne a ke gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari. 21 Don kuwa ko da ya ke sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyatasu marar fahinta kuma ta duhunta. 22 Suna da’awar wai su masu hikima ne, sai suka zama wawaye. 23 Sun canza ɗaukakar Allah marar mutuwa da misalin siffar mutum mai mutuwa ko badaɗe, da ta tsuntsaye, da ta dabbobi, da kuma ta masu jan ciki. 24 Saboda haka Allah ya sallama su ga rashin tsarkaka ta miyagun sha’awace-sha’awacensu, har su wulakanta jikinsu a junansu, 25 saboda sun canza gaskiyar Allah da ƙarya, har sun yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi yi wa Mahalicci, wannan da yabo ya tabbata a gare shi har abada. Hakika.

26 Don haka Allah ya sallama su ga miyagun sha’awace-sha’awace masu ban-ƙyama, har matayensu suka canza dabi’atasu ta halal, da wadda ta ke haram. 27 Haka kuma mazan suka bar ma’amalarsu ta halal da mata, jarabar juna ta ɗebe su, maza da maza suna aikata rashin kunya, suna jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewatasu.

28 Tun da ya ke sun ƙi yarda su san Allah, sai Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya. 29 Su masu aikin rashin gaskiya ne na innanaha, da mugunta, da kwaɗayi, da keta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha’inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne, 30 masu yanke, maƙiya Allah, masu cim-mutunci, masu girmankai, masu ruba, masu haddasa mugunta, marasa bin iyaye, 31 marasa fahinta, masu ta da alkawari, marasa ƙauna, marasa tausayi. 32 Waɗannan kuwa ko da ya ke sun san ka’idar Allah ce, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa sun cancanci halaka, duk da haka ba aikata su kaɗai su ke yi ba, bar ma suna goyon bayan masu yinsu.

2

Duk ’Yan’adam Masu zunubi ne

2 Saboda haka ba ka da wani hanzari kai bil’adan, ko kai wanene da ka ke ganin laifin wani. Yayin da ka ke ganin laifin wani, ai kanka ka ke hukuntawa, don ga shi kai mai ganin laifin wani, kai ma haka ka ke yi. 2 Mun dai san hukuncin Allah kan masu yin haka daidai ne. 3 Ya kai bil’adan, kai da ka ke ganin laifin masu yin haka, alhali kuwa kai kanka kana yinsu, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne? 4 Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe ba ka san alherin Allah shi ke jawo ka ga tuba ba? 5 Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nemar wa kanka azabar Allah a ranar azaba, sa’ad da za a bayyana hukuncin Allah macancanci. 6 Don zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa, 7 sakamakon rai madawwami ga waɗanda ta nacewatasu ga aiki nagari su ke neman ɗaukaka, da girma, da kuma rashin mutuwa, 8 sakamakon azaba da fushi, da wahala da masifa kuwa ga masu sonkai, waɗanda ke ƙin bin gaskiya, sai rashin gaskiya su ke bi, 9 ga kuma kowane mutum mai aikata mugunta, Yahudawa da fari, sa’an nan sauran al’umma. 10 Amma ɗaukaka, da girma da aminci sai su tabbata ga kowane mai yin aiki nagari, Yahudawa da fari, sa’an nan kuma sauran al’umma. 11 Don kuwa Allah ba ya nuna wariya.

Za a yi wa Kowa Shari’a—Babu Wariya

12 Ɗakwacin waɗanda suka ɗau zunubi a kan jahilcin Shari’ar Musa, za su halaka ne ba ta hanyar Shari’ar ba. Ɗakwacin waɗanda suka ɗau zunubi a kan sanin Shari’ar kuwa, za a hukunta su ta hanyar Shari’ar. 13 Don ba ta jin Shari’ar Musa kawai mutun ke samun karɓuwa ga Allah ba, sai dai masu binta ne za su sami karɓuwa. 14 In sauran al’umma, su da ba su da Shari’ar Musa, jikinsu ya ba su suka bi umarnin Shari’ar, ko da ya ke ba su da Shari’ar, ashe kuwa suna da Shari’a ke nan a gare su, 15 da ya ke suna nuna cewa hakkokin Shari’a na rubuce a zuciyatasu, shinan ya kamatansu kuwa shi ke tabbatad da haka, wuswasinsu kuma wani zubin yana ba su gaskiya, wani zubin kuma yana ƙaryata su. 16 A wannan rana Allah zai yi wa ’yan’adan shari’a a kan asiransu, ta kan Yesu Almasihu, bisa Bisharata.

17 To, in ka ce kai Bayahude ne, wai kuma ka dogara da Shari’ar Musa, har kana taƙama da Allah, 18 ka san abin da ya ke so, kuma da ya ke ka karantu da Shari’ar, ka iya bambancewa da abubuwa mafifita, 19 har ka amince kai kanka jagoran makafi ne, haske ga waɗanda ke cikin duhu, 20 mai horon marasa azanci, mai koya wa farin-shiga, don a cikin Shari’ar Musa kana da ainihin sani da ainihin gaskiya. 21 To, kai mai koya wa wani, ba ka koya wa kanka? Kai mai wa’azin kada a yi sata, shin kai ba ka yi ne? 22 Kai mai cewa kada a yi zina, wai kai ba ka yi ne? Kai mai ƙyamar gumaka, ba ka sata a Ɗakin gunki ne? 23 Kai mai taƙama da Shari’a, ashe ba wulakanta Allah ka ke yi ba ta keta Shari’ar? 24 Yadda ya ke a rubuce, cewa, “A sanadinku ne sauran al’umma ke saɓon sunan Allah.”

Kaciyar Ainihi da ta Zahiri

25 Lalle yin kaciya na da amfani, in dai kana bin Shari’ar Musa. Amma in kai mai keta Shari’ar ne, kaciyarka ba a bakin komai ta ke ba. 26 In kuwa marar kaciya na kiyaye farillan Shari’ar, ashe ba sai a ɗauki rashin kaciyarsa a kan kaciya ba? 27 Ashe wanda rashin kaciya al’adatasa ce, ga shi kuwa yana bin Shari’a daidai, ba sai ya ga laifinka ba, kai da ka ke da Littafin Shari’a da kuma kaciya, amma kana keta Shari’ar? 28 Don ba siffar Bayahude ne zama Bayahude ba, haka kuma kaciyar zahira ba ita ce kaciya ba. 29 Wanda ya ke Bayahude a zuci, ai shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci ta ke, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutun Allah ne ke yaba masa, ba ɗan’adam ba.

3

Nassi ya Tabbatad da Laifin Kowa

To, ina fifikon Bayahude ke nan? Ko kuma ina fa’idar kaciya? 2 Ai kuwa akwai ƙwarai, ta kowace hanya. Da farko dai, cewa Yahudawa su ne aka amince wa Maganar Allah. 3 To, ƙaƙa ke nan in wasu sun ci amanan nan? Kuma sai cin amanarsu ya shafe cikar alkawarin Allah? 4 A’a, ko kusa! A dai tabbata Allah Mai gaskiya ne, sai dai kowane mutun ne mai ƙarya, yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Don maganarka tă tabbatad da gaskiyarka,
Ka kuma yi rinjaye in am binciki al’amarinka.”

5 In kuwa rashin gaskiyarmu ita ke nuna gaskiyar Allah a fili, me za mu ce? In Allah ya yi mana azaba, ya yi rashin gaskiya ke nan? (Misali na ke yi kawai.) 6 A’a, ko kusa! To, in da haka ne, ta ƙaƙa Allah zai yi wa duniya shari’a? 7 In kuwa a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har ta ƙara ɗaukaka shi, to, dom me har yanzu a ke hukunta ni a kan ni mai zunubi ne? 8 In haka ne, ba sai mu yi ta yin mugun aiki don ya zama sanadin nagarta ba? Kamar yadda dai wasu ke mana yanke, wai haka mu ke faɗa. Hukuncin da za a yi wa irin waɗannan kuwa daidai ne.

9 To, ƙaƙa mu Yahudawa mun fi sauran ne? A’a, ko kaɗan! Don dā ma mun ɗora wa Yahudawa da sauran al’umma laifin cewa dukkansu zunubi na iko da su. 10 Kamar yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Babu wani mai gaskiya, babu, ko ɗaya;
11 Babu wani mai fahinta, babu wani mai neman Allah.
12 Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki-ɗaya;
Babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya.”
13 “Su kura ne baki buɗe,
Maganarsu ta yaudara ce.”
“Masu ciwon baki ne.”
14 “Yawan zage-zage da ɗacin-baki gare su.
15 “Masu hanzarin zub da jini ne,
16 Ta ko’ina suka bi sai halaka da baƙinciki,
17 Ba su kuma san hanyar aminci ba.”
18 “Babu tsoron Allah a cikin sha’aninsu sam-sam.’

19 To, mun san cewa duk abin da Shari’ar Musa ta ce, ya shaf waɗanda ke ƙarƙashinta ne, don a tuke hanzarin kowa, duk duniya kuma ta san cewa ƙarƙashin hukuncin Allah ta ke. 20 Ai ba wan mahaluƙin da zai sami karɓuwa ga Allah ta bin Shari’ar Musa, tur da ya ke ta kan Shari’ar ne mutun ke ganin laifinsa.

Samun Karɓuwa ga Allah ta Bangaskiya

21 Amma yanzu, ba kuwa game da bin Shari’ar Musa ba, an bayyana hanyar samun karɓuwa ga Allah, wadda ma Attaura da Littattafan Annabawa ke yi wa shaida, 22 wato hanyan nan ta samun karɓuwa ga Allah, wadda bangaskiya ga Yesu Almasihu ce ragamatata, saboda dukkan masu ba da gaskiya. Ba kuwa wani bambanci, 23 saboda duk an ɗau zunubi, an kuma gaza samun yabo daga Allah. 24 Amma am mai da su ababan karɓuwa ga Allah a kyauta, ta alherinsa, ta kan fansan nan da ke ga Almasihu Yesu. 25 Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu abin kankarar zunubi ta jininsa, ita kankaran nan kuwa ta kan bangaskiya a ke samunta. Allah kuwa ya yi haka don ya nuna gaskiyatasa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar, 26 don a nuna gaskiyatasa a wannan zamani, wato a bayyana cewa shi kansa mai gaskiya ne, mai kuma mai da duk mai gaskatawa da Yesu abin karɓuwa gare shi.

27 To, ina kuma alfaharimmu ya shiga? Ina kuwa! Ta wace hanya aka kau da shi? Ta aikin lada? A’a, sai dai ta hanyar bangaskiya. 28 Don mun yarda cewa ta bangaskiya ne a ke mai da mutun abin karɓuwa ga Allah, ba ta bin Shari’ar Musa ba. 29 Wato Allah, Allahn Yahudawa ne kurum? Ashe ba na sauran al’umma ba ne kuma? Hakika na sauran al’umma ne ma, 30 tun da ya ke Allah ɗaya ne, zai kuwa mai da masu kaciya abin karɓuwa gare shi ta kan bangaskiya, marasa kaciya ma ta wannan bangaskiyar. 31 Wato, mun soke Shari’ar ke nan ta kan bangaskiyan nan? A’a, ko kusa! Sai ma tabbatad da ita muka yi.

4

Ibrahim ya sami Karɓuwa ga Allah

To, me ke nan za mu ce game da Ibrahim kakammu bisa ga salsala? 2 Don in Ibrahim ya sami karɓuwa ga Allah ta aikinsa na lada, ashe kuwa yana da abin yin taƙama ke nan, amma fa ba a gaban Allah ba. 3 To, me Nassi ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma aka ɗaukam masa ita a kan samun karɓuwa ga Allah.” 4 To, wanda ya yi aikin lada, ba a ɗaukan laɗansa a kan kyauta ne, sai dai a kan sakamakonsa. 5 Wanda kuwa bai yi ba, amma yana gaskatawa da Mai mai da marasa bin Allah ababan karɓuwa gare shi, sai a ɗaukam masa bangaskiyan nan tasa a kan samun karɓuwa ga Allah. 6 Haka kuma Dawuda ya yi maganar albarkad da aka yi wa mutumin da Allah ya mayar abin karɓuwa gare shi, ba tare da aikinsa na lada ba, 7 da ya ce,

“Albarka tā tabbata ga waɗanda aka yafe wa laifuffukansu,
Waɗanda kuma aka shafe zunubansu,
8 Albarka tā tabbata ga wanda faufau Ubangiji bai dube shi da zunubansa ba.”

Ba ta Hanyar Kaciya a ke samu ba

9 To, wannan albarka, masu kaciya ne kawai a ke yi wa, ko kuwa har da marasa kaciyar ma? Don mun ce, Ibrahim kam, an ɗaukam masa bangaskiyatasa a kan samun karɓuwa ga Allah. 10 To, cikin wane halin aka ɗaukam masa ita? Bayan an yi masa kaciya ne, ko kuwa tun ba a yi ba? Ai tun ba a yi ba ne, ba bayan an yi ba. 11 An kuwa yi masa kaciya ne don alama, wato tabbatacciyar shaida ce ta samun karɓuwa ga Allah, albarkacin bangaskiyad da ya ke da ita tun ba a yi masa kaciya ba. Wannan kuwa don yă zama uban dukkan masu ba da gaskiya ne, ba tare da an yi musu kaciya ba, don su ma a mai da su ababan karɓuwa ga Allah; 12 haka kuma yă zama uban masu kaciya, waɗanda ba kaciya kaɗai su ke da ita ba, har ma suna bin hanyar bangaskiyan nan ta kakammu Ibrahim, wadda shi ma ya bi, tun ba a yi masa kaciya ba.

Ba kuma ta bin Shari’ar Musa a ke samu ba

13 Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyatasa, cewa zai zama magajin duniya, ba ta kan Shari’ar Musa aka yi masa ba, sai dai ta samun karɓuwa ga Allah ta kan bangaskiyatasa. 14 In dai masu bin Shari’ar Musa su ne magada, ashe bangaskiya ta zama banza ke nan, alkawarin nan kuma ya wofinta. 15 Don Shari’ar Musa na jawo azabar Allah. Inda ba Shari’ar kuwa, ba keta umarni ke nan.

Ta Bangaskiya ne a ke Samun Karɓuwa ga Allah

16 Saboda haka al’amarin ya dogara ga bangaskiya don ya zama bisa rahama, don kuma a tabbatad da alkawarin nan ga dukkan zuriyar Ibrahim, ba ga masu bin Shari’a kaɗai a cikinsu ba, har ma ga waɗanda ke da bangaskiya irin ta Ibrahim, shi da ke ubammu duka, 17 kamar yadda ya ke a rubuce, cewa, “Na sanya ka uban al’ummai da yawa.” Shi ne kuwa ubammu a gaban Allah, wannan da ya gaskata, wato, mai raya matattu, shi ne kuma Kunfayakunu. 18 Ibrahim kuwa ko da ya ke ba halin sazuciya a gare shi, sai ya yi ta sawa, ya gaskata zai zama uban al’ummai da yawa, kamar yadda aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za ta yawaita.” 19 Bangaskiyatasa kuwa ba ta raunana ba, bai dubi ragwaggwaɓewar jikinsa ba, don yana da shekara wajen ɗari a lokacin, ko kuma cewa Saratu ta wuce haifuwa. 20 Ba kuwa wata rashin bangaskiyad da ta sa shi shakkar cikar alkawarin Allah, sai ma ƙara ƙarfafa ga bangaskiyatasa ya yi, yana ɗaukaka Allah, 21 yana haƙƙaƙewa cewa Allah na da ikon yin abin da ya yi alkawari. 22 Shi ya sa “aka ɗaukam masa bangaskiyatasa a kan samun karɓuwa ga Allah.” 23 To, “ɗaukam masa” ɗin nan da aka rubuta kuwa, ba saboda Ibrahim kaɗai aka rubuta ba, 24 har saboda mu ma, za a ɗaukam mana, wato, mu da ke gaskatawa da wannan da ya ta da Yesu Ubangijimmu daga matattu, 25 wanda aka bayar a kashe saboda laifofimmu, aka kuma tashe shi don mu sami karɓuwa ga Allah.

5

Samun Kwanciyar Rai a gun Allah

To, da ya ke am mai da mu ababan karɓuwa ga Allah saboda bangaskiya, ashe kuwa muna da kwanciyar rai ke nan a gun Allah ta kan Ubangijimmu Yesu Almasihu. 2 Ta kansa kuma muka sami shiga ni’iman nan da mu ke ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sazuciyarmu ga samun ɗaukakan nan ta Allah. 3 Ban da haka ma har muna taƙama da shan-wuyarmu, da ya ke mun san shan-wuya ita ke haddasa jimiri, 4 jimiri kuma shi ke haifar ingantaccen hali, ingantaccen hali kuma shi ke saka sazuciya, 5 ita sazuciyan nan kuwa ba ta săce iska faufau, domin ƙaunad da Allah ke yi mana tā kwarara a zukatammu, ta Ruhu Tsattsarka da aka ba mu.

An Sada mu da Allah ta Mutuwar Ɗansa

6 Tun ba yadda mu ke, Almasihu ya mutu a daidaitaccen lokaci domin marasa bin Allah. 7 Da kyar za a sami wanda zai ba da ransa saboda mai tsai da haddi kawai, ko da ya ke watakila saboda mutum mai nagarta wani ma sai ya yi ƙasai da ransa. 8 Amma kuwa Allah na tabbatar mana da ƙaunad da ya ke mana, wato, tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domimmu. 9 To, tun da ya ke yanzu am mai da mu ababan karɓuwa ga Allah ta jininsa, ashe kuwa ta kansa za mu fi samun ƙarewa daga azabar Allah ke nan. 10 In kuwa tun muna maƙiya Allah aka sada mu da shi ta mutuwar Ɗansa, to, da ya ke an sada mu, ashe kuwa za a fi kare mu ta rayuwatasa ke nan. 11 Ban da haka ma, har muna taƙama da Allah ta kan Ubangijimmu Yesu Almasihu, wanda ta kansa ne muka sami sadawan nan a yanzu.

12 To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutun ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gado ga kowa, don kowa ya ɗau zunubi. 13 Lalle fa zunubi na nan duniya tun ba a ba da Shari’ar Musa ba, sai dai inda ba Shari’a, ba a kama laifi. 14 Duk da haka kuwa mutuwa ta sarau tun daga kan Adamu har kawo kan Musa, har ma kan waɗanda ba su ɗau zunubi irin na keta umarnin da Adamu ya yi ba, wanda ya ke shi ne kwatancin Maizuwan nan.

15 Amma fa baiwan nan daban ta ke ƙwarai da laifin nan. Ai in Iaifin mutun ɗayan nan ya jawo wa duk ’yan’adam mutuwa, ashe ma alherin Allah, da kuma baiwan nan, albarkacin alherin Mutun ɗaya, Yesu Almasihu, sai su yalwata ga dukkan ’yan’adam fin haka ƙwarai. 16 Baiwan nan kuwa daban ta ke ƙwarai da hakkokin zunubin mutun ɗayan nan. Don kuwa hukuncin da aka yi kan laifin mutun ɗayan nan, shi ya jawo hukuncin halaka. Amma baiwan nan da aka yi a sanadin laifofi da yawa, ita ta ke sa karɓuwa ga Allah. 17 In kuwa saboda laifin mutun ɗayan nan ne mutuwa ta sarau ta kansa, ashe kuwa waɗanda ke samun alherin nan mayalwaci, da kuma baiwan nan ta samun karɓuwa ga Allah, sai su sarau fin haka ƙwarai cikin rai madawwami, ta kan ɗayan nan, wato Yesu. Almasihu.

18 To, kamar yadda laifin mutun ɗayan nan ya jawo wa dukkan mutane hukunci, haka kuma aikin gaskiya na Mutun ɗayan nan ya zame wa dukkan mutane sanadin karɓuwa ga Allah zuwa rai madawwami. 19 Kamar yadda duk ’yan’adan suka zama masu zunubi ta rashin biyayyar mutun ɗaya, haka kuma ta biyayyar Mutun ɗaya duk ’yan’adan sa zama ababan karɓuwa ga Allah. 20 Shari’ar Musa fa an shigo da ita ne kamar ƙāri, don laifi yă haɓaka. Amma inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske. 21 Wato, kamar yadda zunubi ya sarau ta mutuwa, haka alherin Allah ma yă sarau ta samun karɓuwa ga Allah zuwa rai madawwami, ta kan Yesu Almasihu Ubangijimmu.

6

Bin Almasihu Kuɓuta daga Kangin Zunubi ne

To, me kuma za mu ce? Ma ci gaba da ɗaukar zunubi ne don alherin Allah yă haɓaka? 2 A’a, ko kusa! Mu da muka kuɓuta daga ƙangin zunubi, ƙaƙa za mu sarƙafe a cikinsa har yanzu? 3 Ashe ba ku san cewa duk ɗakwacin mu da aka yi wa babtisma ga mallakar Almasihu Yesu, ga mutuwatasa aka yi mana babtismar ba? 4 Saboda haka am binne mu da shi ke nan ta babtisma ga mutuwatasa, don kamar yadda aka ta da Almasihu daga matattu ta ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwa rayuwa.

5 Tun da ya ke mun zama ɗaya da shi wajen kwatancin mutuwatasa, ashe kuwa za mu zama ɗaya ma wajen tashinsa. 6 Wato, mun san cewa an giciye halayemmu na dā tare da shi, don jikin nan namu mai zunubi a zāre masa laka, kada mu ƙara bauta wa zunubi. 7 Wanda ya yi irin wannan mutuwa kuwa, an kuɓutad da shi daga zunubi ke nan. 8 In kuwa mutuwar Almasihu tamu ce, ashe mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma. 9 Mun san cewa tun dai da ya ke an ta da Almasihu daga matattu, ba zai sake mutuwa ba ke nan, mutuwa ba ta da sauran wani iko a kansa. 10 Mutuwan nan da ya yi kuwa, ya mutu ne sau ɗaya tak ba ƙari saboda shafe zunubammu, amma rayuwad da ya ke yi, yana rayuwa ne, rayuwar Allah. 11 Haka ku ma sai ku ɗauki kanku kan ku kuɓutattu ne daga ƙangin zunubi, amma kuna raye, rayuwar Allah, ta kan Almasihu Yesu.

12 Saboda haka kada ku yarda zunubi ya mallaki jikin nan naku mai mutuwa, har da za ku biye wa muguwar sha’awatasa. 13 Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku kan kayan aikin rashin gaskiya don ɗaukar zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah kan waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kan kayan aikin gaskiya. 14 Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da ya ke ba Shari’ar Musa ke iko da ku ba, alherin Allah ne.

15 To, ƙaƙa? Wato, sai mu ɗau zunubi don Shari’ar Musa ba ta iko da mu, sai alherin Allah? A’a, ko kusa! 16 Ba ku sani ba ne cewa in kun miƙa kanku ga wani a kan ku bayi ne masu biyayya, to, lalle ku bayin wanda ku ke bin ne ba? ko dai kan bautar zunubi ne, mai kaiwa ga halaka, ko kuwa kan biyayya, mai kaiwa ga samun karɓuwa ga Allah. 17 Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da ya ke dā can ku bayin zunubi ne, yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwan nan da aka yi muku. 18 Kuma da aka ’yanta ku daga bautar zunubi, kun zama bayin aikin gaskiya. 19 Ina misali ne kawai, saboda rashin ganewarku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarkaka, da mugun aiki kan mugun aiki, haka kuma yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin gaskiya, don a keɓe ku a tsarkake.

20 Sa’ad da ku ke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin gaskiya. 21 To, wace fa’ida kuka samu a lokacin nan game da aikin da ku ke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarkon irin wannan aiki halaka. ne. 22 Amma yanzu da aka ’yanta ku daga bautar zunubi, kun zama bayin Allah, fa’idarku kuma ita ce keɓewa a tsarkake, ƙarkonta kuwa rai madawwami. 23 Don sakamakon zunubi halaka ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami ta kan Almasihu Yesu Ubangijimmu.

7

Am Ɓalle mana Dabaibayin Shari’ar Musa

Ya ’Yan’uwa, ko ba ku sani ba ne cewa Shari’ar Musa na iko da mutun muddar yana raye ne kawai? —da masana Shari’ar fa na ke. 2 Misali, mace mai aure Shari’ar Musa ta haɗa ta da mijinta muddar yana da rai. Amma im mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar auren ke nan. 3 Don haka muddar mijinta na da rai, in ta auri wani, sai a kira ta mazinaciya. Amma im mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar wannan auren, ko da ta auri wani kuwa, ita ba mazinaciya, ba ce.

4 Haka kuma ’Yan’uwana, albarkacin jikin Almasihu, ku ma an kuɓutad da ku daga ƙangin Shari’ar Musa, don ku zama mallakar wani, wato, wanda aka tasa daga matattu, don mu amfana wa Allah. 5 Ai da, sa’ad da mu ke zaman burin-zuciya, muguwar sha’awad da faɗakarwar Shari’a ke sa a yi, ita ke aiki a gaɓoɓimmu, tă ƙare da halaka. 6 Amma yanzu am ɓalle mana dabaibayin Shari’ar Musa, ba kuma sauran ruwammu da abin da ya ɗaure mu dā, har muna iya bauta wa Allah cikin sabuwar rayuwa ta Ruhu Tsattsarka, ba cikin tsofaffin rubutattun ka’idodi ba.

7 To, me kuma za mu ce? Shari’ar Musa zunubi ce? A’a, ko kusa! Amma kuwa duk da haka ba don Shari’ar ba, da ban san zunubi ba. Ba don kuma Shari’ar ta ce, “Kada ka yi ƙyashi” ba, da ban san ƙyashi ba. 8 Amma zunubi, da ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya haddasa ƙyashi iri-iri a zuciyata. Gama ba don Shari’ar Musa ba, da zunubi ba shi da wani tasiri. 9 Dā kam sa’ad da ban san Shari’ar ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya farfaɗo, ni kuma sai na mace. 10 Umarnin nan kuwa wanda manufarsa a gare ni rai madawwami ne, sai ya jawo mini halaka. 11 Don kuwa zunubi, ta samun ƙofa ta hanyar umarni, sai ya yaudare ni, ta kansa kuma ya hallaka ni. 12 Ashe kuwa Shari’ar tsattsarka ce, umarnin kuma tsattsarka ne, mai gaskiya, kuma sahihi.

Yaƙi da Zuciya

13 Wato sahihiyar aba ta jawo mini halaka ke nan? A’a, ko kusa! Zunubi ne dai ya ke haddasa mini halaka ta sahihiyar aba, don a gan shi zahirinsa shi zunubi ne, kuma ta dalilin umarnin nan a bayyana matuƙar muninsa. 14 Mun dai san Shari’ar Musa aba ce ta Ruhu Tsattsarka, ni kuwa mai burin-zuciya ne, bautar zunubi kawai na ke yi. 15 Ban ma fahinci abin da na ke yi ba. Don ba abin da na ke niyya shi na ke aikatawa ba, abin da na ke ƙi, shi na ke yi. 16 To, idan abin da ba na niyya, shi na ke yi, na yarda ke nan Shari’ar aba ce mai kyau. 17 Ashe kuwa ba ni na ke yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune min ne. 18 Don na san cewa babu wani abin kirki da ya zaune min, wato a jikina. Niyyar yin abin da ke daidai kam ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu. 19 Sahihin abin da na ke niyya kuwa, ba shi na ke yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi na ke aikatawa. 20 To, idan abin da ba na niyya shi na ke yi, ashe kuwa ba ni na ke yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune min ne.

21 Sai na ga ashe ya zame mini ka’ida, in na so yin abin da ke daidai, sai in ga mugunta raɓe da ni. 22 Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da Shari’ar Allah. 23 Amma ina ganin wata ka’ida daban a gaɓoɓina, wadda ke yaƙi da ka’idad da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ka’idan nan ta zunubi, wadda ke zaune a gaɓoɓina. 24 Kaitona! Wa zai kuɓutad da ni daga jikin nan halakakke? 25 Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta kan Yesu Almasihu Ubangijimmu! Ashe kuwa, in don ta ni ne, a hankalina, hakika Shari’ar Aliah na ke bauta wa, amma a jikina, ka’idar zunubi na ke bauta wa.

8

Almasihu ya ’Yanta ni

Saboda haka yanzu ba sauran wani hukunci ga waɗanda ke na Almasihu Yesu. 2 Ka’idan nan ta Ruhu mai ba da rai madawwami da ke ga Almasihu Yesu ta ’yanta ni daga ka’idar zunubi da ta halaka. 3 Abin da ba shi yiwuwa Shari’a ta yi don ta kasa yin tasiri saboda halin bil’adan, Allah ya yi shi, wato ya tuɓe zunubi daga mulkinsa na ɗan’adan, da ya aiko Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, don kau da zunubi. 4 Wannan kuwa don a cika hakkokin Shari’a ne a gare mu, mu da ba zaman burin-zuciya mu ke yi ba sai dai na Ruhu Tsattsarka. 5 Masu zaman burin-zuciya ai ƙwallafa ransu ga burin-zuciyatasu su ke yi, masu zaman Ruhu Tsattsarka kuwa ga al’amuran Ruhu. 6 Ƙwallafa rai ga al’amuran burin-zuciya ƙarkonsa halaka ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu Tsattsarka kuwa rai madawwami ne da kwanciyar rai. 7 Don ƙwallafa rai ga burin-zuciya gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari’ar Allah, ba kuwa zai iya ba. 8 Masu zaman burin-zuciya ba dama su iya faranta wa Allah.

Ruhun Allah ne ke Tafi da ’Ya’yan Allah

9 Amma ku kam ba masu zaman burin-zuciya ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah na zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne. 10 In kuwa Almasihu na zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu Tsattsarka kuwa na rayarwa don kun sami karɓuwa ga Allah. 11 In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu na zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattun kuma zai raya jikin nan naku mai mutuwa, ta Ruhunsa da ke zaune a zuciyarku.

12 To fa, ’Yan’uwa, kun ga burin-zuciya ba shi da wani hakki a kammu har da za mu yi zamansa. 13 In kuna zaman burin-zuciya, za ku halaka ke nan, amma in da ikon Ruhu Tsattsarka kuka daina ayyukan nan na burin-zuciya, sai ku rayu. 14 Duk waɗanda Ruhun Allah ke tafi da su, su ne ’ya’yan Allah. 15 Ai ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A’a, na zama ’ya’ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!” 16 Ruhu Tsattsarka kansa ma tare da namu ruhun suna yin shaida, cewa mu ’ya’yan Allah ne. 17 In kuwa ’ya’ya mu ke, ashe kuma magada ne, magadan Allah, kuma abokan gado da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi don a ɗaukaka mu tare.

Ɗaukakar ’Ya’yan Allah

18 Haba ai a ganina wuyad da mu ke sha a wannan zamani ba ta isa a kwatanta ta da ɗaukakad da za a bayyana mana ba. 19 Ga shi duk halitta na haba-haba, tana ɗokin ganin bayyanar ’ya’yan Allah. 20 Duk halitta an ɗora mata rashin ɗorewar biyan bukata, ba kuwa a sonta ba, a son wanda ya ɗora mata ne, 21 da nufin ita halittar kanta ma, a kuɓutad da ita daga ƙuƙumin lalacewa, ta rabanta da ’yancin nan na ɗaukaka na ’ya’yan Allah. 22 Mun dai san dukkan halitta na nishi, sun kuma ɗau wahala gaba-ɗaya har ya zuwa yanzu. 23 Ban da haka ma har mu kammu da muka riga muka sami tumun fari na Ruhu Tsattsarka, muna nishi ta ciki, muna ɗokin cikar zamammu ’ya’yan Allah, wato ceton jikin nan namu ke nan. 24 Sa’ad da aka cece mu ne muka yi wannan sazuciya. Amma kuwa ai sa zuciya ga abin da aka samu, ba sazuciya ba ce. Wa ke sa zuciya ga abin da ya samu? 25 In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, sai mu kan yi ɗokin samunsa da jimiri.

26 Haka kuma Ruhu Tsattsarka ke mana taimako a kan gajiyawarmu, don ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu kansa shi ke mana addu’a da nishi ta ciki. 27 Amma shi Mai fayyace zukatammu ya san abin da Ruhu ke niyya, don bisa nufin Allah ne Ruhu ke yi wa tsarkaka addu’a.

Ƙaunar Almasihu Marar Iyaka

28 Mun kuma san Allah na mai da komai alheri ga masu ƙaunarsa, wato waɗanda ke kirayayyu bisa nufinsa. 29 Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tunin, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, don shi Ɗan yā zama Na farko cikin ’Yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda ya ƙaddaran nan kuwa, su ne ya kira. Waɗanda ya kiran kuwa, su ne ya mayar ababan karɓuwa gare shi. Waɗanda ya mayar ababan karɓuwa gare shi ɗin kuwa, su ne ya ɗaukaka.

31 To, me kuma za mu ce game da haka? Da ya ke Allah na bayammu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe kuma ba sai ya ba mu komai tare da shi ba hannu sake? 33 Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah da ke mai da su ababan karɓuwa gare shi? 34 Wa zai hukunta su? Ko Almasihu Yesu ne wanda ya mutu, har ma hakika aka tashe shi daga matattu, wanda ma ya ke hannun dama na Allah, ya ke kuma yi mana addu’a? 35 Me zai iya raba mu da ƙaunad da Almasihu ke yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko haɗari? ko takobi? 36 Kamar yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Saboda kai ne mutuwa ke jewa a kammu wuni zubur,
An ɗauke mu kamar tumakin yanka.”

37 Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun wuce ma a ce mana masu nasara, ta kan wannan da ya ƙaunace mu. 38 Don na tabbata, ko mutua ce, ko rai, ko mala’iku, ko manyan mala’iku, ko al’amuran yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko, 39 ko tsawo, ko zurfi, kai ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da ƙaunad da Allah ke yi mana ba ta kan Almasihu Yesu Ubangijimmu.

9

Bulus ya yi wa Bani Isra’ila Jaje

Ina faɗar gaskiya ne tsakani da Almasihu, ba ƙarya na ke ba, zuciyata na amince mini ta ikon Ruhu Tsattsarka, 2 cewa ina da gayar baƙinciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata. 3 Ina ma a la’ance ni a raba ni da Almasihu saboda amfanin dangina, ’yan’uwana na kabila! 4 Su ne Bani Isra’ila, waɗanda zama ’ya’yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari’ar Musa, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk su ke nasu. 5 Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta zamansa mutun, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da ke bisa komai. Hakika.

Ta kan Isiyaku ne za a bi Salsalar Zuriyarka

6 Ba wai cewa Maganar Allah ta fāɗi ba, don ba duk zuriyar Isra’ila ne ke Bani Isra’ila na gaske ba. 7 Ba kuwa duk ne su ke ’ya’yan Ibrahim ba, wai don suna zuriyarsa. Amma an ce, “Ta kan Isiyaku ne za a bi salsalar zuriyarka.” 8 Wato zama zuriyar Ibrahim ba shi ne zama ’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta kan alkawarin nan su ne a ke ɗauka a kan zuriyar Ibrahim. 9 Alkawarin kuwa shi ne, cewa, “Baɗi war haka zan dawo, Saratu kuma za ta haifi ɗa.” 10 Ban da haka ma, sa’ad da Rifkatu ta yi cikin nan nata guda da kakammu Isiyaku, 11 tun ba ta haifi ’ya’yan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau—don ƙaddarar Allah bisa zaɓinsa ta tabbata ba ga aikin lada ba sai dai ga kiransa—12 sai aka ce da ita, “Wan zai bauta wa ƙanen.” 13 Kamar yadda ya ke a rubuce, cewa, “Yakubu na fi so a kan Isuwa.

14 To, me kuma za mu ce? Allah ya yi rashin gaskiya ke nan? A’a, ko kusa! 15 Don ya ce da Musa, “Wanda zan yi wa rahama, zan yi masa rahamar kuwa, wanda zan nuna wa tausayi kuwa, zan nuna masa tausayin.” 16 Ashe kuwa abin bai danganta ga nufin mutun ko himmatasa ba, sai dai ga rahamar Allah. 17 Don a Nassi an ce da Fir’auna, “Na girmama ka ne musamman don in nuna ikona a kanka, don kuma a sanad da sunana a duniya duka.” 18 Wato ke nan, yana nuna rahama ga wanda ya so, yana kuma taurara zuciyar wanda ya so.

Samun Rahama Zaɓi ne na Allah

19 Kila ka ce min, “To, dom me har yanzu ya ke ganin laifi? Wa zai iya tsayayya da ƙaddaratasa?” 20 Haba kai ɗan’adan! Wanene kai har da za ka yi jayayya da Allah? Ashe abin da aka gina zai iya ce da magininsa, “Dom me ka yi ni haka?” 21 Ashe maginin tukwane ba ya iko da yumɓu, ya gina wata don aiki mai martaba, wata kuma don kasasshen aiki, duk daga curi ɗaya? 22 To, ƙaƙa in Allah, kan yana son nuna azabatasa da kuma bayyana ikonsa, ya haƙura matuƙar haƙuri da waɗanda suka cancanci azabatasa, suka kuma isa halaka, 23 da nufin ya bayyana yalwar ɗaukakatasa ga waɗanda ya yi wa rahama, waɗanda da ma ya yi wa tanadin ɗaukaka? 24 Wato mu ke nan da ya kira, ba kuwa daga cikin Yahudawa kaɗai ba, har ma daga cikin sauran al’umma. 25 Kamar dai yadda ya faɗa a Littafin Hosiya, cewa,

“Waɗanda dā ba jama’ata ba,
Zan ce da su ‘jama’ata,’
Wadda da ba abar ƙaunata ba kuma,
Zan ce da ita ‘abar ƙaunata.’ “
26 “A daidai wurin da aka ce da su,
‘Ku ba jama’ata ba ne,’
Nan ne za a kira su ‘’ya’yan Allah Rayayye.’”

27 Game da Bani Isra’ila Ishaya ma ya ɗaga murya ya ce, “Ko da ya ke yawan Bani Isra’ila ya kai kamar yashin teku, duk da haka kaɗan ne za su sami ceto. 28 Don Ubangiji zai zartad da hukuncinsa a duniya, ya gama shi tashi-ɗaya. 29 Kamar yadda Ishaya ya yi faɗi, cewa,

“Ba don Ubangijin Runduna ya bar mana zuriya ba,
Da mun zama kamar Saduma,
An kuma maishe mu kamar Gamurata.”

30 To, me kuma za mu ce? Ga shi sauran al’umma da ba su nace da neman samun karɓuwa ga Allah ba, sun samu, wato, samun karɓuwan nan da ke daga bangaskiya. 31 Bani Isra’ila kuwa da suka nace da neman hanyar samun karɓuwa ga Allah, sai suka kasa samu. 32 Me ya sa? Don ba su neme ta ta hanyar bangaskiya ba, sai dai yadda suka zata ta aikin lada. Sai suka yi tuntuɓe da dutsen nan da a ke tuntuɓe da shi, 33 kamar yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Ga shi na sanya dutse a Sihiyona abin yin tuntuɓe,
Kuma abin sa takaici.
Duk mai gaskatawa da shi, ba zai kunyata ba.”

10

Almasihu ne Cikamakin Shari’ar Musa

Ya ’Yan’uwa, muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah 10 saboda Bani Isra’ila, shi ne su sami ceto. 2 Na dai shaide su kan suna da himmar bauta wa Allah, amma ba da cikakken sani ba. 3 Don saboda rashin fahintar hanyar samun karɓuwa ga Allah wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanyar, sai suka ƙi bin ita wannan hanyar ta samun karɓuwa ga Allah da Allah ya tanadar. 4 Don Almasihu shi ne cikamakin Shari’ar Musa, don kowane mai ba da gaskiya ya sami karɓuwa ga Allah. 5 Game da samun karɓuwa ga Allah ta bin Shari’a, Musa ya rubuta cewa duk wanda ya aikata ta zai rayu ta haka. 6 Amma samun karɓuwan nan ga Allah da ke daga bangaskiya ya ce, Kada ka ce a ranka, “Wa zai hau Sama?” wato, yă sauko da Almasihu. 7 Ko kuwa, “Wa zai gangara can ƙasa?” wato, yă taso Almasihu daga matattu. 8 Amma me Nassi ya ce? “Maganar ai tana kusa da kai, tana ma bakinka, a kuma zuciyarka.” Ita ce Maganar Bangaskiya da mu ke wa’azi. 9 Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Don da zuci a ke gaskatawa a sami karɓuwa ga Allah, a kuma bayyana yarda da baka a sami ceto. 11 Gama Nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da shi ba zai kunyata ba.” 12 Ai ba wani bambanci tsakanin Bayahude da na sauran al’umma. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu’a gare shi. 13 “Duk wanda kuwa ya yi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto.”

Gaskatawa sai ta Jin Bishara

14 Amma ta ƙaƙa za su yi addu’a ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta ƙaƙa kuma za su gaskata da wanda ba su taɓa ji ba? Ta ƙaƙa kuma za su ji, im babu mai wa’azi? 15 Ta ƙaƙa kuma za su yi wa’azi, im ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda ya ke a rubuce, cewa, “Kai, wa zai gane min irin babbar saukad da za a yi wa masu kawo albishir!” 16 Amma ba duka ne suka yi na’am da albishirin ba. Don Ishaya ma ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabimmu?” 17 Ashe kuwa bangaskiya ta jawabin da a ke ji ta ke samuwa, jawabin da a ke ji kuma ta Maganar Almasihu ya ke.

18 Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji.

“Muryatasu ta gama duniya duka,
Maganarsu kuma ta kai har bargon duniya.”
19 Har wa yau ina tambaya.
Shin Bani Isra’ila kam ba su fahinta ba ne?
Da farko dai Musa ya ce,
“Zan sa ku kishin waɗanda ba al’umma ba ne,
Zan kuma sa ku fushi da wata al’umma marar fahinta.”

20 Ishaya kuma ya fito gabagaɗi ƙwarai ya ce,

“Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni.
Na bayyana kuma ga waɗanda ba su taɓa neman sanina ba.”

21 Amma game da Bani Isra’ila, sai ya ce,
“Wuni zubur ina miƙa hannayena ga jama’a marasa biyayya, masu tsayayya.”

11

Faɗuwar Bani Isra’ila ce Tashin Sauran Al’umma

To, ina tambaya. Wato Allah ya juya wa jama’atasa baya ke nan? A’a, ko kusa! Ai ni ma kaina Ba’isra’ile ne, zuriyar Ibrahim, na kabilar Bunyamunu. 2 Ko kaɗan Allah bai juya wa jama’atasa da ya zaɓa tun da baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne game da lliya? Yadda ya kai kuka ga Allah a kan Bani Isra’ila, ya ce, 3 “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka, sun rurrushe wuraren yi maka baiko. Ni kaɗai ne na rage, suna kuwa neman raina.” 4 Amma me Allah ya amsa masa? Cewa ya yi, “Na keɓe wa kaina mutun dubu bakwai, waɗanda ba su taɓa durƙusa wa Ba’al ba.” 5 Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa, zaɓen rahama. 6 In kuwa na rahama ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. Im ba haka ba, ashe rahama ba rahama ce ba kuma.

7 To, yaya ke nan? Ashe abin da Bani Isra’ila ke nema, ba su samu ba ke nan, amma, zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare. 8 Yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Allah ya toshe musu basira,
Ya ba su ido, ba na gani ba,
Da kuma kunne, ba na ji ba,
Har ya zuwa yau.”

9 Dawuda kuma ya ce,

“Ina ma shagalinsu ya zame musu tarko, abin shammatarsu,
Kuma sanadin faɗuwatasu, har aniyatasu ta koma kansu.
10 Idonsu kuma yă shiga duhu bar su kasa gani,
Ka kuma tankwara bayansu bar abada.”

11 Ina kuma tambaya. Faɗuwad da suka yi, sun faɗi ƙurmus ba tashi ke nan? A’a, ko kusa! Sai ma faɗuwar tasu ta zama sanadin ceto ga sauran al’umma, don a sa Bani Isra’ila kishin-zuci. 12 To, in kuwa duniya ta arzuta da faɗuwatasu, sauran al’umma kuma sun arzuta da hasaratasu, wa ke gane min irin abin da zai faru in suka farfaɗo?

13 Da ku sauran al’umma fa na ke. Tun da ya ke ni manzo ne ga sauran al’umma, ina taƙama da aikina, 14 ko ta wane hali in sa kabilata kishin-zuci, har in ceci waɗansunsa. 15 Don in an sada duniya da Allah saboda ya da su da aka yi, to, in an karɓe su fa, ba sai rayuwa bayan mutuwa ba?

Zaitun ɗin Gida da na Daji

16 In curin farko tsattsarka ne, haka sauran burodin ma. In kuma saiwa tsattsarka ce, haka rassan ma. 17 Amma in aka sassare wasu rassan zaitun na gida, kuma kai da ke zaitun na daji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan, 18 kada ka yi wa sauran rassan alwashi. In kuwa ka yi, ka tuna fa, ba kai ke ɗauke da saiwar ba, saiwar ce ke ɗauke da kai. 19 Kila ka ce, “Ai an sare rassan nan ne, don a ɗaura aure da ni.” 20 Hakika haka ne, amma saboda, rashin bangaskiyatasu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka, ne ka ke kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah. 21 Da ya ke Allah bai bar rassan asalin ba, kai ma ba zai bar ka ba. 22 Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka faɗi, alherinsa kuwa gare ka, muddar ka ɗore cikin alherin. Im ba haka ba, kai ma sai a datse ka. 23 Ko su ma, in dai ba su nace wa rashin bangaskiyarsu ba, sai a ɗaura aure da su, don Allah na da ikon sake mai da su. 24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa ke na daji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?

25 Don kada ku yi ji-ji-da-kai ’Yan’uwa, ina so ku fahinci wannan zuzzurfan al’amari, cewa taurara ta aukam ma wani shashi na Bani Isra’ila, sai sauran al’umma sun farfaɗo. 26 Sa’an nan ne duk Bani Isra’ila za su sami ceto, kamar yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Maceci zai zo daga Sihiyona,
Zai kuma kau da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu”,
27 “Cikar alkawarina gare su ke nan,
Sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”

28 Game da Bishara kuma, maƙiyan Allah ne su, don amfaninku ne kuwa. Amma game da zaɓen Allah, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu. 29 Don baiwar Allah da kiransa ba sa tashi. 30 Kamar yadda kuka ƙi bin Allah a da, amma yanzu aka yi muku rahama saboda rashin biyayyarsu, 31 haka su ma da ke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu rahama kamar yadda aka yi muku. 32 Don Allah ya tarnaƙe kowa cikin rashin biyayya, don ya nuna rahama ga kowa.

33 Kai, zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka ya ke!
Ƙaddaratasa ta fi gaban bincike, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!
34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?
Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”
35 “Wa kyauta ta shiga tsakaninsu da Allah, ya fara bayarwa,
Har da za a sāka masa?”
36 Ai daga gare shi ne, kuma ta kansa ne, dukkan abubuwa su ke, shi ne kuma makomatasu.
Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada. Amin.

12

Ku Miƙa Jikanku ga Allah

Don haka ina. roƙonku ’Yan’uwa, saboda yawan rahamar Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, keɓaɓɓiya a tsarkake, abar karɓuwa ga Allah. Don wannan ita ce ibadarku fahintacciya. 2 Kada ku biye wa zamanin nan, sai dai ku sake hali ta sabuntawar zuciyarku, don ku tabbatad da abin da Allah ke so, wato, kyakkyawa, abin karɓuwa, kuma cikakke.

3 Albarkacin alherin da aka yi mini, ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa gwargwadon bangaskiyad da Allah ya ba shi. 4 Wato kamar yadda gaɓoɓi da yawa ke harhaɗe a jiki ɗaya, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya su ke yi ba, 5 haka mu ma, ko da ya ke muna da yawa, jiki ɗaya mu ke haɗe da Almasihu, kowannemmu kuma gaɓoɓin ɗan’uwansa ne. 6 Da ya ke muna da baiwa iri-iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta yin faɗin Maganar Allah ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu; 7 in ta hidima ce, wajen hidimarmu; mai koyad da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwatasa; 8 mai ƙarfafa gwiwa kuwa, wajen ƙarfafa gwiwa; mai yin gudummawa kuwa, ya bayar hannu sake; shugaba ya yi shugabancinsa da himma; mai yin aikin tausayi, ya yi shi da fara’a.

Ku Kaunaci Juna Gaya

9 Ƙauna ta kasance tsakani da Allah. Ku yi ƙyamar abin da ke mummuna, ku lazamci abin da ke nagari. 10 Game da ƙaunar ’Yan’uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. Wajen ba da girma, kowa ya riga ba ɗan’uwansa. 11 Kada ku sassauta wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji. 12 Sazuciyan nan taku ta sa ku farinciki, ku jure wa wahala, ku nace da addu’a. 13 Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.

14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, ba ku zage su ba. 15 Ku taya masu farinciki farinciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka. 16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa wuya ga al’amuran ƙasƙanci. Kada ku yi ji-ji-da-kai. 17 Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku himmantu ga yin aiki nagari a gaban kowa. 18 Im mai yiwuwa ne, in don ta ku ne, ku yi zaman lafiya da kowa. 19 Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Don a rubuce ya ke, cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.” 20 Har ma “im maƙiyinka na jin yunwa, sal ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayad da shi. Don ta haka ne za ka sa shi jin zafin abin da ya yi.” 21 Kada mugunta ta rinjaye ku. A’a, sai ma ku rinjayi mugunta da nagarta.

13

Hakkin Mahukunta da ke Kammu

Kowa yă yi biyayya ga mahukunta. Don ba wani ikon da ba a hannun Allah ya ke ba. Mahukuntan da ke nan kuwa naɗin Allah ne. 2 Saboda haka duk wanda ya yi wa mahukunta tsayayya, ya yi wa umarnin Allah ke nan, masu yin tsayayyan nan kuwa za a yi musu hukunci. 3 Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ba ne ga masu aiki nagari, sai dai ga masu mugun aiki. Kana so kada ka ji tsoron mahukunci? To, sai ka yi nagarta, sai kuwa ya yaba maka. 4 Domin shi bawan Allah ne don kyautata zamanka. Amma in kai mai mugun aiki ne, to, ka ji tsoro, don ba a banza ya ke riƙe da sanda ba. Ai shi bawa ne na Allah, mai saka wa mugu da horo. 5 Saboda haka wajibi ne ka yi biyayya, ba wai don gudun horo kaɗai ba, bar ma don shinan ya kamata. 6 Shi ne ma ya sa ku ke biyan haraji, don su mahukunta ma’aikata ne na Allah, suna kuma kan wannan aiki koyaushe. 7 Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu; masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito; waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi; waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa. 8 Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar ɗan’uwansa ya cika Shari’ar Musa ke nan. 9 Umarnin nan cewa, “Kada ka yi zina, Kada ka yi kisankai, Kada ka yi sata, Kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarni, an ƙunshe su ne a wannan ƙaulin cewa, “Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.” 10 Ƙauna ba ta cutar ɗan’uwa, saboda haka ƙauna cika Shari’ar Musa ne.

11 Ga shi kuma, kun dai san irin zamanin da mu ke ciki, ai lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci. Gama yanzu mun fi kusata da ceton nan namu a kan sa’ad da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsad da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske. 13 Mu tafi da al’amurammu warkan yadda ya dace a yi da rana, ba cikin shashanci da buguwa, ko masha’a da fajirci, ko jayayya da kishi ba. 14 Amma ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku yi wani tanadi na burin-zuciya don biye wa muguwar shalawatasa.

14

Zaman Ƙauna da Ɗan ‘uwa

Game da wanda bangaskiyatasa rarrauna ce kuwa, ku karɓe shi hannu biyu-biyu, amma ba game da cin băƙinsa wajen ra’ayinsa ba. 2 Wani bangaskiyatasa ta yarje masa cin komai, wanda bangaskiyatasa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai ya ke ci. 3 To, kada fa mai cin komai ɗin nan ya raina wanda ya ƙi cin, kada kuma wanda ya ƙi cin nan ya ga laifin mai cin, don Allah ya riga ya karɓe shi bannu biyu-biyu. 4 Kai wanene har da za ka ga laifin baran wani? Ko dai ya tsaya ko ya faɗi, ai ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, don Ubangiji na da ikon tsai da shi.

5 Wani ya kan ɗaukaka wata rana fiye da sauran ranaku, wani kuwa duk ɗaya ne a wurinsa. Kowa dai yă zauna cikin haƙƙaƙewa a kan ra’ayinsa. 6 Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma yana ci ne saboda Ubangiji, da ya ke yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah. 7 Duk a cikimmu ba wanda ya isam ma kansa cikin sha’anin rayuwarsa ko mutuwarsa. 8 Ko muna raye, zaman Ubangiji mu ke yi; ko mun mutu ma, zaman Ubangiji mu ke yi. Ashe ko muna raye, ko kuma a macen, na Ubangiji ne mu. 9 Saboda haka ne musamman Almasihu ya mutu, ya sake rayuwa, wato don ya zama shi ne Ubangijin matattu da rayayyu duka.

10 To, kai me ya sa ka ke ganin laifin Ɗan ‘uwanka? Kai kuma, me ya sa ka ke raina Ɗan ‘uwanka? Ai dukkammu za mu tsaya a gaban gadon shari’ar Allah. 11 Don a rubuce ya ke, cewa,

“Na rantse da Zatina, in ji Ubangiji, kowace gwiwa sai ta rusuna min,
Kowane harshe kuwa sai ya yabi Allah.”
12 Don haka kowannemmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.

13 Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura kada kowannemmu ya zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga Ɗan ‘uwansa. 14 Na sani, na kuma tabbata, tsakani da Ubangiji Yesu, ba abin da ke marar tsarki ga asalinsa, sai dai ga wanda ya ɗauke shi marar tsarki ne ya ke marar tsarki. 15 In kuwa cimarka na cutar Ɗan’uwanka, ashe ba zaman ƙauna ka ke yi ba. Kada fa cimarka ta hallaka wannan da Almasihu ya mutu dominsa. 16 Saboda haka kada abin da ka ɗauka kyakkyawa ya zama abin zargi ga wasu. 17 Ai Mulkin Allah ba ga al’amarin ci da sha ya ke ba. A’a, sai dai ga samun karɓuwa ga Allah, da kuma aminci da farinciki ta kan Ruhu Tsattsarka. 18 Wanda duk ke bauta wa Almasihu ta haka, abin karɓuwa ne ga Allah, kuma yardajje ne ga mutane. 19 Don haka sai mu himmantu ga yin abubuwan da ke haddasa aminci, da kuma inganta juna. 20 Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci kawai. Hakika dukkan abu mai tsarki ne, amma mugun abu ne mutun ya zama sanadin tuntuɓe ga wani, ta abin da ya ke ci. 21 Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa Ɗan ‘uwanka yin tuntuɓe. 22 Kana da bangaskiya? To, riƙe ta tsakaninku kai da Allah. Albarka tā tabbata ga wanda zuciyatasa ba ta ba shi laifi ba, game da abin da hankalinsa ya ga daidai ne. 23 Wanda ke shakka, amma kuwa ya ci, ya san ya yi laifi ke nan, don ba da bangaskiya ya ci ba. Duk abin da ba bangaskiya ce ta haddasa ba kuwa, zunubi ne.

15

Wajibi ne Kada mu yi Sonkai

To, mu da ke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai. 2 Kowannemmu yă faranta wa ɗan’uwansa don kyautata zamansa da kuma inganta shi. 3 Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda ya ke a rubuce, cewa, “Zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.” 4 Ai duk abin da aka rubuta tun dā an rubuta ne don a koya mana, don mu ɗore cikin sazuciyan nan tamu ta jimiri da ƙarfin-gwiwa da Littattafai Tsarkaka ke haddasawa. 5 Allah Mai haddasa jimiri da ƙarfin-gwiwa, yă ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu, 6 don ku ɗaukaka Allahn Ubangijimmu Yesu Almasihu, kuma Ubansa, nufinku ɗaya, bakinku ɗaya.

7 Saboda haka ku karɓi juna hannu biyu-biyu, kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu-biyu, don a ɗaukaka Allah. 8 Ina dai gaya muku Almasihu ya zama bara ga Bani Isra’ila don nuna gaskiyar Allah, don kuma tabbatad da alkawaran nan da Allah ya yi wa kakannin kakannimmu, 9 sauran al’umma kuma su ɗaukaka Allah saboda rahamatasa. Yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Don haka zan yabe ka a cikin sauran al’umma,
In kuma yi waƙar yabon sunanka.”
10 Har wa yau kuma an ce,
“Ya ku sauran al’umma, ku yi ta farinciki tare da jama’atasa.”
11 Kuma,
“Ku yabi Ubangiji, ya ku sauran al’umma duka,
Dukkan kabilu kuma su yabe shi.”

12 Kuma Ishaya ya ce,

“Tsatson Yassa zai bayyana,
Wanda zai tashi ya mallaki sauran al’umma,
Gare shi ne sauran al’umma za su sa zuciya.”

13 Allah Mai haddasa sazuciya yă cika ku da matuƙar farinciki da aminci saboda bangaskiyarku, don ku yi matuƙar sazuciya ta ikon Ruhu Tsattsarka.

Burin Bulus ya sanad da Sunan Almasihu

14 Ya ’Yan’uwana, ni ma kaina na amince da ku, cewa ku kanku masu nagarta ne ƙwarai da gaske, da kuma cikakken sani, kun kuma isa ku gargaɗi juna. 15 Duk da haka a kan waɗansu maganganun da na rubuto muku, na ƙara ƙarfafawa ƙwarai don tuni, saboda alherin da Allah ya yi mini 16 da ya sa ni bawan Almasihu Yesu ga sauran al’umma, ina hidimar Bisharar Allah, don im miƙa sauran al’umma gare shi a kan baiko, abin karɓuwa gare shi, keɓaɓɓe a tsarkake ta ikon Ruhu Tsattsarka. 17 Ashe kuwa ina da dalilin yin taƙama da Almasihu Yesu game da al’amarin Allah. 18 Ba zan kuskura im faɗi komai ba, sai abin da Almasihu ya aikata ta kaina, wajen sa sauran al’umma biyayya ta maganata da aikina, 19 ta ikon muujizai da abubuwan al’ajabi da kuma ta ikon Ruhu Tsattsarka, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi Bisharar Almasihu a ko’ina. 20 Har ya zame min abin buri in sanad da Bishara a inda ba a taɓa sanad da sunan Almasihu ba, don kada in ɗora ginina a kan harsashin wani, 21 sai dai kamar yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Waɗanda ba a taɓa faɗa wa labarinsa ba, za su gane,
Waɗanda ba su taɓa jin labarinsa ba ma, za su fahinta.”

22 Shi ya sa sau da yawa ban sami sukunin zuwa wurinku ba. 23 Yanzu kuwa tun da ya ke ba sauran wani wurin da ya rage mini a lardin nan, kuma shekaru da yawa ina dokin zuwa wurinku, 24 ina sa zuciya in gan ku in zan wuce zuwa ƙasar Fanya, har ma ku raka ni can, bayan na ɗan ɗebe kewa da ganinku. 25 Amma yanzu kam za ni Urushalima ne, don kai wa tsarkaka gudummawa. 26 Don mutanen Makidoniya da na Akaya sun ji daɗin yin gudummawar daidai gwargwado ga gajiyayyu cikin tsarkakan da ke Urushalima. 27 Sun kuwa ji daɗin yin haka, don hakika kamar bashi ne a kansu. Don tun da ya ke sauran al’umma sun yi tarayya da su a kan ni’imarsu ta Ruhu Tsattsarka, ashe kuwa ya kamata su sauran al’umma ma su taimake su da ni’imarsu ta zahiri. 28 In kuwa na gama wannan, na kuma ɗanka musu wannan baiko lafiya, sai im bi ta kanku zuwa ƙasar Fanya. 29 Na kuma san in na zo wurinku, zan zo ne cikin falalar albarkar Almasihu.

30 Amma, ina roƙonku ’Yan’uwa, saboda Ubangijimmu Yesu Almasihu, da kuma ƙaunan nan da Ruhu Tsattsarka ke haddasawa, ku taya ni faman yin addu’a ga Allah saboda, kaina, 31 don in kuɓuta daga maƙiya ba da gaskiya a Yahudiya, don kuma gudummawar da na ke kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka, 32 har in Allah ya yarda in iso wurinku cikin farinciki, mu wartsake tare. 33 Allah Mai haddasa aminci ya kasance tare da ku duka. Amin.

16

Ga nan ’Yar’uwarmu Fibi ina sada ku da ita, ita ma kuwa mai hidimar ikiliziya ce a Kankiriya. 2 Ku karɓe ta hannu biyu-biyu saboda Ubangiji, ta halin da ya dace da tsarkaka. Ku kuma taimake ta da duk irin abin da ta nemi taimako a gare ku, don ita ma tā taimaki mutane da yawa, har ni kaina ma.

Gaishe-gaishe

3 Ku gai da Biriska da Akila, abokan aikina cikin al’amarin Almasihu Yesu, 4 waɗanda suka sai da ransu saboda ni, ba kuwa ni kaɗai na ke gode musu ba, har ma da dukkan ikiliziyan sauran al’umma. 5 Ku kuma gai da ikiliziyad da ke taruwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccena Abainitas, wanda ya ke shi ne ya fara bin Almasihu a ƙasar Asiya. 6 Ku gai da Maryamu, wadda ta yi muku aiki ƙwarai da gaske. 7 Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, Iyan’uwana, abokan daurina, waɗanda su ke shahararru cikin manzanni, har ma sun riga ni bin Almasihu. 8 Ku gai da Amfiliyas, ƙaunataccena a cikin al’amarin Ubangiji. 9 Ku gai da Urbanas, abokin aikimmu cikin al’amarin Almasihu, da kuma ƙaunataccena Istakis. 10 Ku kuma gai da Abalis, amintaccen nan cikin al’amarin Almasihu. Ku gai da jama’ar Aristobulus. 11 Ku gai da ɗan’uwana Hirudiyan. Ku gai da waɗanda ke na Ubangiji cikin jama’ar Narkisas. 12 Ku gai da Tarafina da Tarafusa, masu aikin Ubangiji. Ku gai da Barsisa, ƙaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji ƙwarai da gaske. 13 Ku gai da Rufas, shahararre ga al’amarin Ubangiji, da kuma uwatasa, tawa kuma. 14 Ku gai da Asinkiritas, da Filiguna, da Hamis, da Baturobas, da Hamasa, da kuma ’Yan’uwan da ke tare da su. 15 Ku gai da Filulugusa, da Yuliya, da Niriyas, da ’yar’uwatasa, da Ulumfas da kuma dukkan tsarkakan da ke tare da su. 16 Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba. Dukkan ikiliziyan Almasihu na gaishe ku.

17 Ina roƙonku, ’Yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwad da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. 18 Ai irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijimmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki su ke yaudarar masu sauƙin-kai. 19 Amma ku kam ai kowa ya san biyayyarku, shi ya sa na ke farinciki da ku. Sai dai ina so ku gwanance da abin da ke nagari, amma ya zama ba ruwanku da mugunta. 20 Allah Mai haddasa aminci kuwa zai sa ku tattake Shaiɗan da hanzari. Alherin Ubangijimmu Yesu Almasihu ya tabbata a gare ku.

21 Timotawas, abokin aikina, yana gaishe ku, haka kuma Lukiyas da Yasan da kuma Susibataras, ’yan’uwana.

22 Ni Tartiyas, mai rubuta wasiƙan nan, ina gaishe ku saboda Ubangiji.

23 Gayas, mai masaukina, mai kuma saukar dukkan ’yan-ikiliziya, yana gaishe ku. Arastas, ma’ajin gari, da kuma Ɗan’uwammu Kawartas, suna gaishe ku. 24 Alherin Ubangijimmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka. Amin.

25 Ɗaukaka tă tabbata ga Mai ikon ƙarfafa ku bisa Bisharata, bisa wa’azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana zuzzurfan al’amarin nan da ke ɓoye tun fil’azal. 26 Zuzzurfan al’amarin nan kuwa yanzu am bayyana shi, an kuma sanad da shi ga dukkan al’ummai ta Littattafan Annabawa, bisa umarnin Allah madawwami, don jawo su yin biyayya ga Bangaskiya.

27 Ɗaukaka tă tabbata har abada ga Allah makaɗaicin hikima ta kan Yesu Almasihu! Amin.


WASIƘAR BULUS TA FARKO
ZUWA GA
KORINTIYAWA

1

Daga Bulus, Manzo kirayayye na Almasihu Yesu cikin yardar Allah, da kuma Ɗan’uwammu Sastanisu, 2 zuwa ga ikiliziyar Allah da ke Korinti, wato waɗanda aka keɓe a tsarkake ta kan Almasihu Yesu, kirayayyun tsarkaka, tare da dukkan waɗanda a ko’ina su ke addu’a da sunan Ubangijimmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da mu duka.

3 Alheri da aminci na Allah Ubammu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

4 Kullum na kan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta kan Almasihu Yesu, 5 har aka wadata ku ta kowace hanya da iya fassara Maganar Allah matuƙar iyawa, da kuma cikakken sani ta kansa— 6 don kuwa an tabbatad da shaida a kan Almasihu a cikinku. 7 Har ma ku ba ƙasassu ba ne wajen samun kowace baiwar Allah, kuna zuba ido ga bayyanar Ubangijimmu Yesu Almasihu, 8 wanda zai tabbatad da ku har ya zuwa ƙarshe, ku kasance marasa abin zargi a ranar Ubangijimmu Yesu Almasihu. 9 Allah mai alkawari ne, shi ne kuma ya kira ku ga tarayya da Ɗansa Yesu Almasihu Ubangijimmu.

Tsaguwa a Ikiliziya

10 Na roƙe ku ’Yan’uwa, saboda sunan Ubangijimmu Yesu Almasihu, cewa dukkanku bakinku yă zama ɗaya, kada wata tsaguwa ta shiga tsakaninku, sai dai ku haɗa kai, kuna masu nufi ɗaya, ra’ayi ɗaya. 11 Don kuwa, ya ’Yan’uwana, mutanen gidan Kuluwi sun ba ni labari cewa akwai jayayya a tsakaninku. 12 Abin da na ke nufi shi ne, kowannenku wani kan ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuwa, “Ni na Afalas ne,” wani kuwa, “Ni na Kefas ne,” ko kuwa, “Ni na Almasihu ne.” 13 Ashe Almasihu a rarrabe ya ke? Ko Bulus ne aka giciye dominku? Ko kuwa an yi muku babtisma ne ga mallakar Bulus? 14 Na gode Allah da ban yi wa waninku babtisma ba, ban da Kirisbus da Gayas; 15 kada wani ya ce an yi muku babtisma ne ga mallakata. 16 Ai kuwa lalle na yi wa jama’ar gidan Istifanas ma. Amma ban da waɗannan ban san ko na yi wa wani babtisma ba.

Maganar Giciyen Almasihu

17 Ai ba don in yi babtisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanad da Bishara, ba kuwa da zalaƙa ba, kada a wofinta ƙarfin giciyen Almasihu.

18 Maganar giciye ta wauta ce ga waɗanda su ke halaka, amma ƙarfin Allah ce a gare mu, mu da a ke ceto. 19 Don a rubuce ya ke, cewa,

“Zan rushe hikimar mai hikima,
Zan kuma shafe haziƙancin haziƙi.”

20 To, ina masu hikima su ke? Ina kuma masana? Ina masu muhawarar zamanin nan? Ashe Allah bai fallashi hikimar duniyan nan kan wauta ce ba? 21 Da ya ke bisa hikimar Allah duniya ba ta san Allah ta hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya ta wautar sanad da Bishara. 22 Yahudawa kam mu’ujiza su ke nema su gani, sauran al’umma kuma hikima su ke nema su samu, 23 mu kuwa muna wa’azin Almasihu a giciye, abin sa takaici ga Yahudawa, wauta kuma ga sauran al’umma, 24 amma ga wadarida su ke kirayayyu, ko Yahudawa ko sauran al’umma duka biyu, Almasihu ikon Allah ne, kuma hikimar Allah. 25 Don abin da aka ɗauka kan wauta ce ta Allah, ya fi hikimar ɗan’adam; abin da kuma aka ɗauka kan rauni ne na Allah, ya fi duk ƙarfin ɗan’adan.

26 Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku ’Yan’uwa, a cikinku ai ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, ƙusoshin gari kuma ba su da yawa, haka masu asali ma ba yawa. 27 Amma Allah ya zaɓi abin da ke wauta a duniya, don ya kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abin da ke rarrauna a duniya, don ya kunyata ƙaƙƙarfa. 28 Allah ya zaɓi abin da ke ƙasƙantacce kuma wulakantacce a duniya, kai, har ma abubuwan da ba su, don ya shafe abubuwan da ke akwai. 29 Wannan kuwa duk don kada wani ɗan’adan ya yi fariya gaban Allah ne, 30 domin shi ne tushen rayuwarku ta kan Almasihu Yesu, wanda Allah ya sanya shi ne hikima a gare mu, wato samun karɓuwa ga Allah, da tsarkaka, da kuma fansa. 31 Saboda haka, yadda ya ke a rubuce ke nan, cewa, “Duk mai yin taƙama, yă yi taƙama da Ubangiji.”

2

Sa’ad da na zo wurinku ’Yan’uwa, ban zo ina sanad da ku zurfafan al’amuran Allah ta iya magana ko gwada hikima ba. 2 Don na ƙudura a raina, sa’ad da na ke zaune da ku, ba zan so sanin komai ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa a giciye. 3 Kuma ina tare da ku ne cikin halin raunana, da bangirma ƙwarai tare da matsananciyar kula. 4 Jawabina da wa’azina ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu Tsattsarka, 5 kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai dai da ƙarfin Allah.

Hikimar Allah Zazzurfa

6 Duk da haka dai muna sanad da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan waɗanda su ke kan shuɗewa ba. 7 Amma muna sanad da hikimar Allah ne zuzzurfa, ɓoyayyiya, wadda Allah ya ƙaddara tun gaban farkon zamanai, don a ɗaukaka mu. 8 A cikin masu mulkin zamanin nan ba wanda ya gane hikiman nan, don da sun gane ta, da ba su giciye Ubangiji Maɗaukaki ba. 9 Amma kuwa yadda ya ke a rubuce ke nan, cewa,

“Abubuwan da ido bai taɓa gani ba, Kunne bai taɓa ji ba,
Zuciyar mutun kuma ba ta ko riya ba,
Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”

10 mu ne Allah ya bayyana wa, ta Ruhu Tsattsarka, don Ruhu Tsattsarka shi ya ke fayyace komai, har ma zurfafan al’amuran Allah. 11 Wanene a cikin mutane ya san tunanin wani mutun, im ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12 Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda ke daga Allah, don mu fahinci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake. 13 Su ne kuwa mu ke sanarwa ta maganad da ba hikimar ɗan’adan ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu Tsattsarka ya koyar, muna bayyana al’amuran Ruhu Tsattsarka ga waɗanda Ruhu Tsattsarka ke tafi da su.

14 mutumin da ba Ruhu Tsattsarka ke tafiya da shi ba ya kan ƙi yin na’am da al’amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahintarsu ba, don ta Ruhu Tsattsarka ne a ke rarrabewa da su. 15 Mutumin da Ruhu Tsattsarka ke tafi da shi kuwa ya kan rarrabe da komai, shi kansa kuma ba mai jarraba shi. 16 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji har da zai koya masa?” Mu kuwa zuciyarmu ta Almasihu ce.

3

Kishi da Jayayya Tabbatar Burin-zuciya ne

Amma ni, ’Yan’uwa, ban iya yi muku jawabi kan waɗanda ‘Ruhu Tsattsarka ke tafi da su ba, sai dai kan ku masu burin-zuciya ne, kamar jarirai cikin al’amarin Almasihu. 2 Nono ne na shayad da ku, ba abinci mai tauri na ba ku ba, don ba ku isa ci ba a lokacin, ko yanzun ma ba ku isa ba, 3 don har yanzu ku masu burin-zuciya ne. Muddar akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe ku ba masu burin-zuciya ba ne? kuna kuma bin hali irin na ɗan’adan? 4 Don in wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afalas ne,” ashe ba burin-zuciya ne ke tafi da ku ba?

5 To, Afalas wanene? Bulus kuma wanene? Ashe ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta kansu, kowannensu kuwa da gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi? 6 Ni na shuka, Afalas ya yi banruwa, amma Allah ne ya girmar. 7 Don haka da mai shukar da mai banruwan ba a bakin komai su ke ba, sai dai Allah kaɗai, shi da ya girmar. 8 Da mai shukar da mai banruwan daidai su ke, sai dai kowanne zai sami nasa ladan gwargwadon wahalarsa, 9 gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, kuma gini na Allah.

Irin Aikin da ya Wajaba ga Kirista

10 Kamar gwanin magini haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma na ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutun ya lura da irin ginin da ya ke ɗorawa a kai. 11 Harsashin kam, ba wanda ke iya sa wani daban da wanda aka riga aka sa, wato Yesu Almasihu. 12 To, kowa ya yi ɗori a kan harsashin nan da zinariya, ko da azurfa, ko da duwatsun alfarma, ko da itace, ko da shuci, ko da kara— 13 ai aikin kowane mutun zai bayyana, don Ranan nan za ta tona shi, gama za a bayyana ta da wuta ne, wutar kuwa za ta gwada aikin kowa a san irinsa. 14 In aikin da kowane mutun ya ɗora a kan harsashin nan ya tsira, to, zai sami sakamako. 15 In kuwa aikin wani ya ƙone, to, sai ya yi hasara, ko da ya ke shi kansa zai cetu, amma kamar ya bi ta wuta ne.

16 Ashe ba ku san ku tsattsarkan mazauni na Allah ne ba, kuma Rulum Allah na zaune a zuciyarku? 17 In wani ya ɓāta tsattsarkan mazaunin Allah, Allah zai ɓāta shi. Gama tsattsarkan mazaunin Allah tsattsarka ne, ku ne kuwa shi.

Hikimar Duniyan nan Wauta ce a gun Allah

18 Kada kowa ya ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai ya mai da kansa marar hikima, don ya sami zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyan nan wauta ce a gun Allah. Don a rubuce ya ke, cewa, “Ya kan kama masu hikima cikin makircinsu.” 20 Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.” 21 Saboda haka kada kowa ya yi alfahari da ’yan’adan. Don kuwa komai naku ne, 22 ko Bulus, ko Afalas, ko Kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwan yanzu, ko da na gaba, ai duk naku ne. 23 Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.

4

Ana Bukatar Riƙon Amana a Gare Mu

Ta haka ya kamata a san mu da zama bayin Almasihu, masu riƙon amanar zurfafan. al’amuran Allah. 2 Har wa yau dai abin da a ke bukata ga mai riƙon amana, a same shi amintacce. 3 A gare ni kam sassaukan abu ne a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a gaban kowace mahukunta ta mutane. Ni ba na ma gwada kaina. 4 Ban san ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai Ubangiji shi ne mai gwada ni. 5 Don haka kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al’amuran da ke ɓoye a cikin duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa’an nan ne Allah zai yaba wa kowa daidai gwargwado.

6 To, ’Yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina da kuma Afalas saboda ku, don ku yi koyi da mu, cewa kada ku zarce abin da ke rubuce, kada kuma waninku ya yi alfahari da wani a kan wani. 7 Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma ka ke da shi, wanda ba ba ka aka yi ba? To, da ya ke ba ka aka yi, dom me ka ke alfahari, kamar ba ba ka aka yi ba?

Manzanni sun Zama Kamar Tozarin Duniya

8 Mhm, wato har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku! 9 Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu Manzanni, koma-bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa ke jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala’iku duk da mutane. 10 An ɗauke mu kan marasa azanci saboda Almasihu, wato ku kuwa masu azanci cikin al’amarin Almasihu! Wato mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance! 11 Har yanzu yunwa mu ke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana nannaushimmu, kuma yawo mu ke haka ba mu da gida. 12 Da gaɓarmu mu ke wahala. In an zage mu, mu kan ce, “Sambarka.” In an tsananta mana, mu kan ɗaure. 13 In an ci mutuncimmu, mu kan ba da haƙuri. Mun zama, kuma har yanzu ma mu ne kamar tozarin duniya, jujin kowa.

14 Ba don in kunyata ku na rubuta wannan ba, sai dai don in gargaɗe ku kan ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu. 15 Ko da kuna da malamai masu dumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku cikin al’amarin Almasihu ta kan Bishara. 16 Don haka ina roƙonku ku yi koyi da ni. 17 Saboda haka na aika muku da Timotawas, wanda ya ke shi ne dana ƙaunatacce, amintacce kuma cikin al’amarin Ubangiji, zai kuwa tuna muku da ka’idodina na bin Almasihu, kamar yadda na ke koyarwa ko’ina a kowace ikiliziya. 18 Waɗansu har suna ɗaga kai, kamar ba zan zo wurinku ba. 19 Amma kuwa zan zo gare ku ba da daɗewa ba, in Ubangiji ya yarda, zan kuma bincika in ga ƙarfin mutane masu ɗaga kan nan, ba maganganunsu ba. 20 Don Mulkin Allah ba ga maganar baka ya ke ba, sai dai ga ƙarfi. 21 To, me kuka zaɓa, in zo muku da sanda, ko kuwa da fuskar ƙauna da lumana?

5

Tsawatarwa Mai Ƙarfi

Ana ta faɗa akwai fasikanci a tsakaninku, irin wanda ma ba a yi ko a cikin sauran al’umma, har wani na zama da matar ubansa. 2 A! wai kuwa har ku masu alfarma ne! Ashe ba gwamma ku yi baƙinciki ba, har a fid da wanda ya yi wannan aiki daga cikin jama’arku?

3 Ko da ya ke ba na nan ga zahiri, ai ruhuna na nan, kuma kamar ina nan ne, har ma na riga na yanke wa mutumin da ya yi abin nan hukunci da sunan Ubangijimmu Yesu. 4 Sa’ad da kuka hallara, kuma ruhuna na nan, da kuma ikon Ubangijimmu Yesu, 5 sai ku miƙa irin wannan mutun ga Shaiɗan, don ya lalata jikinsa, ruhunsa kuma ya kuɓuta a ranar Ubangiji Yesu.

6 Alfaharinku ba shi da kyau. Ashe ba ku san cewa ɗan yisti kaɗan ke game dukkan curin burodi ba? 7 Ku fid da tsohon yistin nan, don ku zama sabon curi, don hakika an raba ku da yistin, da ya ke an riga an yanka Ɗan Ragommu na Idin Ƙetarewa, wato Almasihu. 8 Saboda haka sai mu riƙa yin Idimmu, ba da burodi mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da burodi marar yisti na sahihanci da gaskiya.

Kada ku Cuɗanya da Fasikai

9 Na rubuta muku a cikin wasiƙata cewa kada ku cuɗanya da fasikai. 10 Ko kusa ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwadaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai ya zama dole ku fita daga duniya. 11 Sai dai na rubuta muku ne kada ku cuɗanya da duk wanda a ke kira Ɗan’uwa mai bi in yana fasiki, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ko ma ku ci abinci da irin waɗannan. 12 Ina ruwana da hukunta waɗanda ba namu ba? Ba waɗanda ke cikin ikiliziya za ku hukunta ba? 13 Allah ne ke hukunta waɗanda ba namu ba. Ku kori mugun nan daga cikinku.

6

In waninku na da wata ƙara game da Ɗan’uwansa, ashe zai yi ƙurun kai maganar gaban marasa gaskiya, ba gaban tsarkaka ba? 2 Ashe ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa ku ne za ku yi wa duniya shari’a, ashe ba za ku iya shari’ar ƙananan al’amura ba? 3 Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba, balle al’amuran da suka shafi zaman duniyan nan? 4 In kuwa kuna da irin waɗannan ƙararraki, dom me kuma ku ke kai su gaban waɗanda su ba komai ba ne game da ikiliziya? 5 Na faɗi wannan ne don ku kunyata. Ashe wato ba ko mutun ɗaya mai hikima a cikinku, da zai iya sasanta tsakanin ’Yan’uwa? 6 Sai dai kuma Ɗan’uwa ya kai ƙarar ‘Ɗan ‘uwa, gaban marasa ba da gaskiya kuwa?

Ƙarar Juna Hasara ce

7 Ku yi ƙarar juna ma ai hasara ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura a zambace ku? 8 Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna zamba, har ma ’Yan’uwanku ku ke yi wa!

9 Ashe ba ku san cewa marasa gaskiya ba za su sami gado a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba wasu fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo, 10 ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gado a cikin Mulkin Allah. 11 Waɗansunku ma dā haka su ke, amma an wanke ku, an keɓe ku a tsarkake, an kuma mai da ku ababan karɓuwa ga Allah, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahmmu.

12 “Dukkan abubuwa halal ne a gare ni,” amma ba dukkan abubuwa ne masu amfani ba. “Abu duka halal ne a gare ni,” amma ba zan zama bawan komai ba. 13 “Abinci don ciki aka yi shi, ciki kuma don abinci” —Allah kuma zai hallaka duka biyu, wannan da waccan. Jiki kam ba don fasikanci ya ke ba, sai dai don Ubangiji, Ubangiji kuma don jiki. 14 Allah ya ta da Ubangiji daga matattu, haka mu ma zai ta da mu ta ikonsa.

Fasikanci da Matukar Muni ya ke

15 Ashe ba ku san jikinku gaɓoɓin Almasihu ba ne? Ashe kuma sai in ɗauki gaɓoɓin Almasihu im mai da su gaɓoɓin karuwa? Har abada! 16 Ashe ba ku san duk wanda ya tara da karuwa sun zama jiki ɗaya ke nan ba? Don a rubuce ya ke, cewa, “Su biyun za su zama jiki ɗaya.” 17 Duk wanda kuwa ya ke haɗe da Ubangiji, sun zama Ruhu ɗaya ke nan. 18 Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutun ke yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci yana ɗaukar alhakin jikinsa ne. 19 Ashe ba ku san cewa jikinku tsattsarkan mazauni ne na Ruhu Tsattsarka wanda ke zuciyarku, wanda kuka samu a gun Allah ba? Ai ku ba mallakar kanku ba ne. 20 Fansarku aka yi, amma sai da aka ji jiki. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku.

7

Hakkin Aure

To, yanzu kuma game da abin da kuka rubuto, yana da kyau mutun ya zauna ba mace. 2 Amma, don gudun fasikanci sai kowane mutun ya kasance da matatasa, kowace mace kuma da mijinta. 3 Miji yă ba matatasa hakkinta na aure, haka kuma matar ga mijinta. 4 Matar kuwa ba ta da iko da jikinta, sai dai mijin; haka kuma mijin ba shi da iko da jikinsa, sai dai matar. 5 Kada ɗayanku ya ƙaurace wa ɗaya, sai ko da yardar juna zuwa lokaci kaza don ku himmantu ga addu’a, sa’an nan ku sake haɗuwa, kada Shaiɗan ya zuga ku wajen rashin kamewa. 6 Na faɗi wannan ne bisa shawara, ba bisa umarni ba. 7 Ina ma a ce kowa kamar ni ya ke mana! Sai dai kowa da irin baiwad da Allah ya yi masa, wani iri kaza, wani kuma iri kaza.

Gargadi ga Masu Aure da Marasa Aure

8 Abin da na gani ga waɗanda ba su yi aure ba, da kuma matan da mazansu suka mutu, ya kyautu gare su su zatina ba aure kamar yadda na ke. 9 In kuwa ba za su iya kamewa ba, to, sai su yi aure. Ai gwamma a yi aure da sha’awa ta ci rai.

10 Masu aure kuwa ina yi musu umarni, ba kuwa ni ba, Ubangiji ne, cewa, kada mace ta rabu da mijinta, 11 (in kuwa ta rabu da shi, sai ta zauna haka ba aure, ko kuwa ta sake shiryawa da mijinta); miji kuma kada ya saki matatasa.

12 Ga sauran, ni na ke faɗa, ba Ubangiji ba, in wani Ɗan’uwa na da mace marar ba da gaskiya, kuma ta yarda su zauna tare, to, kada ya rabu da ita. 13 Mace kuma mai miji marar ba da gaskiya, ya kuwa yarda su zauna tare, to, kada ta rabu da shi. 14 Don miji marar ba da gaskiya, a tsarkake ya ke albarkacin matatasa. Mace marar ba da gaskiya kuma, a tsarkake ta ke albarkacin mijinta. Im ba haka ba ’ya’yanku sai su zama marasa tsarki, amma ga hakika tsarkaka ne. 15 In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin na son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, Ɗan’uwa ko ’Yar’uwa mai bi, ba tilas a kansu, don Allah ya kira mu ga zaman lafiya. 16 Ke mace, ina kika sani ko ma za ƙi ceci mijinki? Kai miji, ina ka sani ko ma za ka ceci matarka?

Inda Allah ya Ajiye Ka, Ka Zauna

17 Sai dai kowa ya yi zaman da Ubangiji ya sanya masa, kuma wanda Allah ya kira shi a kai. Haka na ke umarni a dukkan ikiliziyai. 18 Duk wanda Allah ya kira, wanda dā ma ke da kaciya, to, kada ya nemi zama marar kaciya. Wanda kuwa ya kira yana marar kaciya, to, kada ya nemi a yi masa kaciya. 19 Don kaciya da rashin kaciya ba sa hassala komai, sai dai kiyaye umarnin Allah shi ke hassala wani abu. 20 Kowa yă zauna a kan mukamin da Allah ya kiraye shi. 21 In ya kira ka kana bawa, kada ka damu. In kuwa kana iya samun ’yanci, ai sai ka samu. 22 Wanda aka kiraye shi ga tafarkin Ubangiji yana bawa, ai ’yantaccen Ubangiji ne. Haka kuma wanda aka kira shi yana ɗa, bawa ne na Almasihu. 23 Fansarku aka yi, amma sai da aka ji jiki. Kada fa ku zama bayin mutane. 24 To, ’Yan’uwa, duk halin da aka kira mutun a ciki, sai ya zauna a kai, yana zama tare da Allah.

25 Game da matan da ba su yi aure ba kuwa, ba ni da wani umarnin Ubangiji, amma ina ba da ra’ayina ne a kan ni amintacce ne bisa rahamar Ubangiji. 26 Na dai ga ya yi kyau mutun ya zauna yadda ya ke, saboda ƙuncin nan da ke gabatowa. 27 In da igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi kuɓuta. In kuwa ba igiyar aure a wuyanka, to, kada ka nemi aure. 28 Amma kuwa in ka yi aure, ba ka ɗau zunubi ba, ko budurwa ma ta yi aure, ba ta ɗau zunubi ba. Duk da haka dai duk masu yin aure za su ji jiki, niyyata kuwa in sauƙaƙe muku. 29 Abin da na ke nufi ’Yan’uwa, lokacin da aka ƙayyade ya ƙure. Nan gaba masu mata su zauna kamar ba su da su, 30 masu kuka kamar ba kuka su ke yi ba, masu farinciki ma kamar ba farinciki su ke yi ba, masu saye kuma kamar ba su mallaka ba, 31 masu moron duniya kuma kada su ba da ƙarfi ga moronta. Don yayin duniyan nan mai shuɗewa ne.

32 Ina so ku huta da taraddadi. Mutum marar aure ya kan tsananta kula da sha’anin Ubangiji, yadda zai faranta wa Ubangiii. 33 Mutum mai aure kuwa ya kan tsananta kula da sha’anin duniya ne, yadda zai faranta wa matatasa. 34 Hankalinsa ya rabu biyu ke nan. Mace marar aure, ko budurwa, ta kan tsananta kula da sha’anin Ubangiji, yadda za ta kasance tsattsarka, a jika, da kuma rai. Mace mai aure kuwa ta kan tsananta kula da sha’anin duniya, yadda za ta faranta wa mijinta. 35 Na faɗi haka don kanku ne, ba don in ƙuntata muku ba, sai dai don in kyautata zamanku, da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

36 Ga zancen ’ya budurwa, wadda ta zarta lokacin aure, idan ubanta ya ga bai kyauta mata ba, in kuwa hali ya yi, sai ya yi abin da ya nufa, wato a yi mata aure, bai ɗau zunubi ba. 37 In kuwa ya zamana ba lalle ne ya yi wa ’yatasa budurwa aure ba, amma ya tsai da shawara bisa ga yadda ya nufa, ya kuma ƙudura sosai a ransa kan zai tsare ta, to, haka daidai ne. 38 Wato, wanda ya yi wa ’yatasa budurwa aure, ya yi daidai, amma wanda bai aurad da ita ba, ya fi shi.

39 Igiyar aure na wuyan mace muddar mijinta na da rai. In kuwa mijinta ya mutu, tana da dama ta auri wanda ta ke so, amma fa sai mai bin Ubangiji. 40 Amma a nawa ra’ayin, za ta fi farinciki in ta zauna yadda ta ke. A ganina kuwa ina da Ruhu Tsattsarka na Allah.

8

Munin Cin Abin da Aka Yanka wa Gunki

To, yanzu kuma game da abubuwan da aka yanka wa gumaka, mun san cewa “dukammu muna da ilimi.” Ilimi ya kan kumbura mutun, ƙauna kuwa ta kan inganta shi. 2 Duk mai ganin ya san wani abu, ai har yanzu bai san yadda ya kamata ya sani ba. 3 In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.

4 Game da cin abin da aka yanka wa gumaka kuwa, mun san cewa “duk duniyan nan ba wani hakikanin abin da gunki ke wakilta,” kuma “babu wani Allah sai ɗaya.” 5 Ko da ya ke wai akwai waɗanda a ke kira alloli a Sama ko a ƙasa—don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa— 6 duk da haka dai a gare mu kam Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa ke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa mu ke yi, Ubangiji kuma ɗaya ne, Yesu Almasihu, wanda ta gare shi ne dukkan abubuwa suka samu, mu kuma ta gare shi muka kasance.

7 Amma dai ba kowa ne ke da wannan sani ba. Amma wasu ta sabawarsu da al’amuran gunki bar yanzu, su kan ci naman da suka ɗauka kamar an yanka wa gunki ne. Saboda kuma rashin tsai da zuciyarsu, sai zuciyarsu ta ƙazantu. 8 Abinci ba zai kare mu game da Allah ba. Im mun ci, ba mu ƙaru ba, in kuma ba mu ci ba, ba mu ragu ba. 9 Sai dai ku lura kada ’yancin nan naku ya zama abin sa tuntuɓe ga waɗanda ba su tsai da zuciyarsu ba. 10 Don kuwa in wani ya gan ka, kai da ka san fari ka san baƙi, kana ci a ɗakin gunki, im bai tsai da zuciyatasa ba, ashe ba sai jikinsa ya yi ƙarfi, ya ci abin da aka yanka wa gunki ba? 11 Wato ta sanin nan naka, sai a hallaka marar tsai da zuciyan nan, Ɗan’uwa ne kuwa wanda Almasihu ya mutu dominsa! 12 Ta haka ne, wato ta ɗaukar alhakin ’Yan’uwanku, da kuma yi wa zuciyatasu marar tsaiwa illa, ku ke saɓon Almasihu. 13 Saboda haka in dai cin nama ya sa Ɗan’uwana laifi, har abada ba zan ƙara cin nama ba don kada in sa Ɗan’uwana laifi.

9

Ni ba ɗa ba ne? Ba kuma Manzo ba ne? Ban ga Yesu Ubangijimmu ba ne? Ku ba aikina ba ne a cikin al’amarin Ubangiji? 2 Ai ko waɗansu ba su ɗauke ni a kan Manzo ba, lalle ku kam ni Manzo ne gare ku, don kuwa ku ne tabbatar manzancina a cikin al’amarin Ubangiii.

Ma’aikaci ya Cancanci Ladansa

3 Wadarman su ne hujjojina ga masu son tuhumata. 4 Ashe ba mu da ikon a ba mu ci da sha? 5 Ba mu da ikon tafiya da matarmu mai bi, kamar yadda sauran Manzanni da ’yanuwan Ubangiji da kuma Kefas ke yi? 6 Ko kuwa dai ni da Barnabas ne kawai ba mu da ikon a ɗauke mana aikin ci da kai? 7 Wa ke aikin soja, sa’an nan ya ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, ya ƙasa cin ’ya’yan? Wa zai yi kiwon garke, ya ƙasa shan nonon?

8 Wato ina faɗar haka bisa ra’ayin mutun kawai ne? Ba haka ma Attaura ta faɗa ba? 9 Ai haka ya ke a rubuce a Shari’ar Musa, cewa, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi a sa’ad da ya ke sussuka.” Da shanu ne kawai Allah ke kula? 10 Ba saboda mu musamman ya ke magana ba? Hakika saboda mu ne aka rubuta. Ai ya kamata mai noma ya yi noma da sazuciya, mai sussuka kuma ya yi sussuka da sazuciya ga samun rabo daga amfanin gonar. 11 Da ya ke mun shuka iri na Ruhu Tsattsarka a zuciyarku, to, mun yi zara ne im mun mori amfaninku na zahiri? 12 Da ya ke wasu sun mori halaliyarsu game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba?

Duk da haka ba mu mori wannan halallyar ba, sai dai muna jure wa komai, don ta ko ƙaƙa kada mu hana Bisharar Almasihu yaɗuwa. 13 Ashe ba ku san cewa masu hidima a Ɗakin Ibada daga nan su ke samun abincinsu ba? Kuma masu hidima a Wurin Baiko, a nan su ke samun rabo daga hadayad da aka yanka? 14 Hakanan kuma Ubangiji ya yi umarni, cewa ya kamata masu sanad da Bishara, a cishe su albarkacin Bishara.

Burin Bulus ya yi Bishara a Kyauta

15 Amma ni kam ban mori ko ɗaya daga cikin halaliyan nan ba, ba kuma ina rubuta wannan ne don a yi mini haka ba. Ai gara im mutu a kan wani ya banzanta mini taƙamata. 16 Don ko da ya ke ina yin Bishara, ba na taƙama da haka, gama tilas ne a gare ni. Kaitona im ba na yin Bishara! 17 Da da ra’ina na ke yi, da sai a biya ni. Amma da ya ke ba da ra’ina ba ne, an danƙa mini amana ke nan. 18 Ina kuma hakkina? To, ga shi. Duk lokacin da na ke yin Bishara, sona in yi ta a kyauta, kada in ƙurashe halaliyata game da Bishara.

19 Ko da ya ke ni ba bawan kowa ba ne, na mai da kaina bawan kowa, don in ƙara shawo kan mutane. 20 Ga Yahudawa sai na zama kamar Bayahude, don in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda Shari’ar Musa ke iko da su, sai na zama kamar wanda Shari’ar ke iko da shi—ko da ya ke ba Shari’ar ke iko da ni ba—don in rinjayi waɗanda Shari’ar ke iko da su ne. 21 Ga marasa Shari’ar kuwa sai na zama kamar marar Shari’ar—ba wai cewa ba wata shari’ar Allah da ke iko da ni ba, a’a, shari’ar Almasihu na iko da ni—don in rinjayi marasa Shari’ar Musa ne. 22 Ga marasa tsai da zuciya sai na zama kamar marar tsai da zuciya, don in rinjayi marasa tsai da zuciya. Kai! na zama kowane irin abu ga kowaɗanne irin mutane, don ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu. 23 Na yi wannan ne duk albarkacin Bishara, don in sami rabo a cikin albarkatata.

24 Ashe ba ku sani ba ne, cewa a wajen tsere dukkan masu gudu suna ƙoƙarin tsere wa juna, amma ɗaya ne kaɗai ke samun kyautar cin? To, sai ku yi ta gudu hakanan, don ku same ta. 25 Duk masu wasan gasa su kan hori kansu ta kowane hali. Su kam suna yin haka ne, don su sami lada mai lalacewa, mu kuwa marar lalacewa. 26 To, ni ba gudu na ke yi ba wurin zuwa ba, dambena kuwa ba naushin iska na ke yi ba. 27 Amma ina azabta jikina ne, don im bautad da shi, kada bayan na yi wa wasu wa’azi, ni kaina a soke ni.

10

Gani ga Wane ya isa Wane Tsoron Allah

To, ina so ku sani, ’Yan’uwa, cewa dukkan kakannimmu an kare su ne ƙarƙashin gajimare, kuma dukkansu sun ratsa ta cikin bahar. 2 Dukkansu kuwa an yi musu babtisma ga bin Musa cikin gajimaren, da kuma bahar din. 3 Duka kuwa sun ci abincin nan na Allah, 4 duk kuma sun sha ruwan nan na Allah. Don sun sha ruwa daga Dutsen nan na Allah, wanda ya bi su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne. 5 Duk da haka, kuwa Allah bai yi murna da yawancinsu ba, bar aka karkashe su a jeji.

6 To, ai waɗannan abubuwa gargaɗi ne gare mu, kada mu yi marmarin miyagun abubuwa, kamar yadda suka yi. 7 Kada fa ku zama matsafa kamar yadda wasunsu su ke. A rubuce ya ke, cewa, “Jama’a sun shantake garin ci da sha, suka kuma tashi suka yi ta bidiri.” 8 Kada fa mu yi fasikanci yadda wasunsu suka yi, har mutun dubu ishirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak. 9 Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda wasu suka yi, har macizai suka hallaka su. 10 Kada kuma mu yi gunaguni yadda wasu suka yi, har Mai hallakarwa ya hallaka su. 11 To, duk wannan ya same su ne a kan misali, an kuma rubuta shi ne don a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12 Don haka duk wanda ke tsammanin ya kafu, ya mai da hankali kada ya faɗi. 13 Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan’adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.

Ku Guji Bautar Gumaka

14 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, ku guji bautar gumaka. 15 Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da na ke faɗa. 16 Kokon nan na yin godiya, wanda mu ke gode wa Allah saboda shi, ashe ba tarayya ne ga jinin Almasihu ba? Burodin nan da mu ke gutsuttsurawa kuma, ashe ba tarayya ne ga jikin Almasihu ba? 17 Da ya ke burodi ɗaya ne, ashe kuwa mu da mu ke da yawa, jiki ɗaya ne, don mu duk burodi ɗaya mu ke ci. 18 Ku dubi ɗabi’ar Bani Isra’ila. Ashe waɗanda ke cin abin hadaya, ba tarayya su ke yi da Wurin Baiko ba? 19 Me na ke nufi ke nan? Abin da aka yanka wa gumakan ne ainihin wani abu, ko kuwa gunkin ne ainihin wani abu? 20 A’a! Na nuna ne kawai cewa abin da sauran al’umma ke yankawa, aljannu su ke yanka wa, ba Allah ba. Ba na fa so ku zama abokan tarayya da aljannu. 21 Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu. 22 Ashe har ma tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?

23 “Dukkan abubuwa halal ne,” amma ba dukkan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukkan abubuwa halal ne,” amma ba dukkan abubuwa ne ke ingantawa ba. 24 Kada kowa ya nemi kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan’uwansa. 25 Ku ci kowane irin abin da a ke sayarwa a mahauta, ba tare da wani tsantsani ba 26 Don “duniya ta Ubangiji ce, da duk abin da ke cikinta.” 27 In wani a cikin marasa ba da gaskiya ya kira ku cin abinci, kuka kuwa yarda ku tafi, sai ku ci duk irin abin da aka sa a gabanku, ba tare da wani tsantsani ba. 28 In kuwa wani ya ce muku, “An yanka wannan saboda gunki ne fa,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan mai gaya mukun, da kuma gudun illar zuciyatasa, 29 illar zuciyatasa fa na ce, ba taku ba. Me zai sa im mori ’yancin nan nawa, har yadda wani zai zarge ni a zuci? 30 Haba! In nā ci abinci game da gode wa Allah, saboda me za a zarge ni kan abincin da na ci tare da gode wa Allah?

Komai Naku ya Zama na Bautar Allah

31 To, duk abin da ku ke yi, ko ci, ko sha, ku yi komai saboda ɗaukaka Allah. 32 Kada ku zama abin takaici ga Yahudawa ko sauran al’umma ko ikiliziyar Allah, 33 kamar dai yadda na ke ƙoƙarin kyautata wa dukkan mutane a cikin duk abin da na ke yi, ba wai nema wa kaina amfani na ke yi ba, sai dai in amfani mutane da yawa, don su sami ceto.

11

Ku yi koyi da ni kamar yadda na ke koyi da Almasihu 2 Ina yaba muku ne don kuna tunawa da ni cikin kowace harka, kuna kuma riƙe ka’idodin nan kankan daidai yadda na ba ku. 3 Amma fa ina so ku fahinci cewa Shugaban kowane mutun Almasihu ne, shugaban kowace mace kuwa mijinta ne, Shugaban Almasihu kuma Allah ne. 4 Duk mutumin da ya yi addu’a ko yin faɗin Maganar Allah kansa rufe, ya wulakanta Shugabansa ke nan. 5 Amma duk matar da ta yi addu’a, ko yin faɗin Maganar Allah kanta a buɗe, ta wulakanta shugabanta ke nan, duk ɗaya ne da an aske kanta ma. 6 Im mace ta ƙi rufe kanta, to, sai ta saisaye gashinta. In kuwa abin kunya ne a yi wa mace saisaye ko kundumi, to, sai ta rufe kanta. 7 Namiji kam bai kamata ya rufe kansa ba, tun da ya ke shi kamannin Allah ne, kuma abin taƙamar Allah. Amma mace abar taƙamar namiji ce. 8 (Don kuwa namiji ba daga jikin mace ya ke ba, amma matar daga jikin namiji ta ke. 9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.) 10 Shi ya sa ya kamata mace ta rufe kanta, wato alamar ikon namiji, saboda mala’iku. 11 (Duk da haka a cikin al’amarin Ubangiji, mace ba rabe ta ke da namiji ba, haka kuma namiji ba rabe ya ke da mace ba. 12 Wato, kamar yadda mace ta ke daga namiji, haka namiji kuma haifuwar mace ne. Amma, dukkan abubuwa daga Allah su ke.) 13 Ku kanku ku duba fa ku gani. Ya dace da mace ke nan ta yi addu’a ga Allah kanta buɗe? 14 Ashe ko dabi’a ma ba ta nuna muku cewa namiji ya yi gizo, abin kunya ne ba? 15 In kuwa mace tana da gashi, ba alfarmarta ne ba? Gama don rufin kai ne aka yi mata gashin. 16 In kuwa wani na da niyyar gardama, to, mu dai ba mu san wata al’ada ba, ikiliziyan Allah kuma haka.

Umarni game da Cin Jibin Ubangiji

17 Game da umarnin nan kuwa, ban yaba muku ba, don taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin kirki ce. 18 To, da farko dai sa’ad da kuka taru, taron ikiliziya, na ji wai akwai rarrabuwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. 19 Don lalle ne a sam tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda ke amintattu a cikinku. 20 Ashe kuwa in kuka taru gu ɗaya, ba jibin Ubangiji ku ke ci ba! 21 Domin a wajen cin abincin, kowa ya kan dukufa a kan akushinsa, ga wani na jin yunwa, ga wan kuwa ya sha ya bugu. 22 A! Ba ku da gidajen da za ku ci ku sha a ciki ne? Ko kuwa kuna raina ikiliziyar Allah ne, kuna kuma muzanta waɗanda ba su da komai? Kash! To, me zan ce da ku? Yaba muku zan yi a kan wannan matsala? A’a, ba zan yaba muku ba.

Asalin Cin Jibin Ubangiji

23 Abin nan kuwa da na karɓa a gun Ubangiji, shi ne na ba ku, cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi, 24 kuma bayan ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura ya ce, “Wannan jikina ne, wanda ya ke saboda ku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.” 25 Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “Ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da jinina. Ku yi haka duk sa’ad da ku ke sha, don tunawa da ni.” 26 Wato, duk sa’ad da ku ke cin burodin nan, ku ke kuma sha a ƙoƙon nan, kuna ayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har kafin ya dawo.

27 Saboda haka duk wanda ya ci burodin nan, ko ya sha a ƙoƙon nan na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa ke nan. 28 Sai dai kowa ya auna kansa, sa’an nan ya ci burodin, ya kuma sha a ƙoƙon. 29 Kowa ya ci, ya kuma sha, ba tare da faɗaka da jikin Ubangiji ba, ya jawo wa kansa hukunci ke nan, ta ci da sha da ya yi. 30 Shi ya sa da yawa daga cikinku su ke da rashin lafiya da rashin ƙarfi, har ma waɗansu da dama suka yi barci. 31 Amma in da za mu auna kammu sosai, da ba za a hukunta mu ba. 32 In kuwa Ubangiji ne ke hukunta mu, muna horuwa ke nan, don kada a yanke mana hukunci tare da sauran duniya.

33 Saboda haka, ya ’Yan’uwana, in kuka taru don cin abinci, sai ku jiraci juna. 34 In kuwa wani na jin yunwa, sai ya ci a gida, kada ya zamana taronku ya jawo muku hukunci. Batun sauran abubuwa kuwa, zan ba da umarni a kai sa’ad da na zo.

12

Bawa iri-iri ta Ruhu Tsattsarka

Yanzu kuma ’Yan’uwa, game da baye-bayen Ruhu Tsattsarka, ba na so ku rasa sani. 2 Kun sani fa a sa’ad da ku ke bin sauran al’umma, an juyad da ku ga bin gumakan nan marasa baki, yadda aka ga dama. 3 Don haka na ke sanad da ku, cewa ba mai magana ta ikon Ruhun Allah sannan ya ce, “Yesu la’ananne ne!” Haka kuma ba mai iya cewa, “Yesu Ubangiji ne,” sai ta ikon Ruhu Tsattsarka.

4 To, akwai baiwa iri-iri, amma Ruhu Tsattsarka ɗaya ne. 5 Kuma akwai fanni iri-iri na ibada, amma Ubangiji ɗaya ne. 6 Akwai kuma aiki iri-iri, amma Allah ɗaya shi ke iza kowa ga yin kowannensu. 7 An yi wa kowanne baiwa da wani buɗi na Ruhu Tsattsarka, don kyautata wa duka. 8 Wani an yi masa baiwa da koyad da hikima ta Ruhu Tsattsarka, wani kuma da koyad da sani ta wannan Ruhun. 9 Wani kuwa an yi masa baiwa da bangaskiya ta Ruhun nan, wani kuma baiwar warkarwa ta Ruhun nan, 10 wani kuma yin mu’ujizai, wani kuma baiwar yin faɗin Maganar Allah, wani kuma baiwar rarrabe ruhu da aljani, wani kuma iya harshe iri-iri, wani kuma fassara harsuna. 11 Duk waɗannan Ruhu ɗaya ne ke iza su, ya ke kuma rarraba wa kowannensu yadda ya nufa.

Dukkammu Gaɓoɓin Jiki Guda ne

12 Wato kamar yadda jiki ya ke guda, ya ke kuma da gaɓoɓi da yawa, su gaɓoɓin kuwa ko da ya ke suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ya ke ga Almasihu. 13 Dukkammu an yi mana babtisma ta Ruhu Tsattsarka guda, mu zama jiki guda—Yahudawa ko sauran al’umma, bayi ko ’ya’ya—dukkammu kuwa an shayad da mu Ruhu guda.

14 Jiki ba gaɓa ɗaya ba ne, gaɓoɓi ne da yawa. 15 Da ƙafa za ta ce, “Da ya ke ni ba hannu ba ce, ai ni ba gaɓar jiki ba ce.” Faɗar haka ba za ta raba ta da zama gaɓar jikin ba. 16 Da kuma kunne zai ce, “Da ya ke ni ba ido ba ne, ai ni ba gaɓar jiki ba ne.” Faɗar haka ba za ta raba shi da zama gaɓar jikin ba. 17 Da dukkan jiki ido ne, da da me za a ji? Da dukkan jiki kunne ne, da da me za a sansana? 18 Amma ga shi Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa. 19 Da dukkan jikin gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin? 20 Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya. 21 Ba dama ido ya ce da hannu, “Ba ruwana da kai,” ko kuwa kai ya ce da ƙafafuwa, “Ba ruwana da ku.” 22 Ba haka ya ke ba, sai ma gaɓoɓin da a ke gani kamar raunana, su ne wajibi, 23 kuma gaɓoɓin jiki da a ke gani kamar sun kasa sauran daraja, mu kan fi ba su martaba. Ta haka gaɓoɓimmu marasa kyan gani, a kan ƙara kyautata ganinsu. 24 Gaɓoɓimmu masu kyan gani kuwa ba sai an yi musu komai ba. Amma Allah ya harhaɗa jiki, yana ba da mafificiyar martaba ga ƙaskantacciyar gaɓa, 25 kada rashin haɗa-kai ya wakana ga jiki, sai dai gaɓoɓin su kula da juna, kula iri ɗaya. 26 Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare; in kuwa am martaba wata, duk sai su yi farinciki tare.

27 To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. 28 A cikin ikiliziya, Allah ya sanya waɗansu su zama, na farko Manzanni, na biyu masu yin faɗin Maganar Allah, na uku masu koyad da Maganar Allah, sa’an nan sai masu yin mu’ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafi da ikiliziya, da kuma masu magana da harsuna iri-iri. 29 Shin duka Manzanni ne? Wai duka masu yin faɗin Maganar Allah ne? Ko duk ne masu koyad da Maganar Allah? Su duka masu yin mu’ujizai ne? 30 Duka ne ke da baiwar warkarwa? Duka ne ke magana da wasu harsuna? Ko kuwa duka ne ke fassara? 31 Sai dai ku himmantu ga neman mafifitan baye-baye.

Har ma zan nuna muku wata hanya mafificiya nesa.

13

Kauna ta fi Komai a cikin Halaye

Ko da zan yi magana da harsunan mutane, har da na mala’iku, amma ya zamana ba ni da ƙauna, na zama kararrawa mai yawan kara ke nan, ko kuge mai amo. 2 Ko da zan yi faɗin Maganar Allah, ina kuma fahintar dukkan zurfafan al’amura da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya har yadda zan iya kau da duwatsu, muddar ba ni da ƙauna, to, ni ba komai ba ne. 3 Ko da zan saɗaukad da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a ƙone, in bar ba ni da ƙauna, to, ban amfana da komai ba.

4 Kauna tana sa haƙuri da kirki. Kauna ba ta sa kishi da ji-ji-da-kai. 5 Ƙauna ba ta sa ɗaga-kai ko rashin kara; ƙauna ba ta sa sonkai, ba ta kuwa haddasa saurin fushi ko riƙo. 6 Kauna ba ta sa yin farinciki da aikin rashin gaskiya, sai dai da aikin gaskiya 7 Kauna tana sa jinkirin fallasa cikin kowane hali, da bangaskiya cikin kowane hali, haka kuma sazuciya cikin kowane hali, da jimiri cikin kowane hali.

8 Kauna ba ta ƙarewa bar abada. Yin faɗin Maganar Allah kam zai shuɗe, harsuna kuma za su ɓace, ilimi kuma zai shafe. 9 Ai hakika ilimimmu kima ne, yin faɗimmu na Maganar Allah ma haka ya ke kima. 10 Sa’ad da kuwa cikakken ya zo, sai ɗan kiman nan ya shuɗe. 11 Sa’ad da na ke yaro, na kan yi magana irin ta ƙuruciya, na kan yi tunani irin na ƙuruciya, na kan ba da hujjojina irin na ƙuruciya. Da na isa mutun kuwa, sai na bar halin ƙuruciya. 12 Yanzu kam ganimmu dishi-dishi ne, kamar a madubi, a ranan nan kuwa za mu gani ido da ido. Yanzu sanina ɗan kima ne, a ranan nan kuwa zan fahinta sosai da sosai, kamar yadda aka fahince ni sosai da sosai. 13 To, yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya da sazuciya da kuma ƙauna; amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

14

Gargadi a kan Magana da Wasu Harsuna

Ku nace wa ƙauna, ku kuma himmantu ga neman baye-baye na Ruhu Tsattsarka, tun ba ma na yin faɗin Maganar Allah ba. 2 Duk wanda ke magana da wani harshe, ba da mutane ya ke magana ba, da Allah ya ke yi; ba kuwa wanda ke fahintarsa, don zurfafan al’amura ya ke ambato ta Ruhu Tsattsarka. 3 Wanda kuwa ke yin faɗin Maganar Allah, mutane ya ke yi wa magana saboda inganta su, da ƙarfafa musu gwiwa, da kuma sanyaya musu zuciya. 4 Duk wanda ke magana da wani harshe, kansa ya ke ingantawa. Mai yin faɗin Maganar Allah kuwa, ikiliziya ya ke ingantawa. 5 To, ina so dukkanku ku yi magana da wasu harsuna daban, amma na fi so ku yi faɗin Maganar Allah. Wanda ke yin faɗin Maganar Allah, ya fi mai magana da wasu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, don a inganta ikiliziya.

6 To, ’Yan’uwa, in na zo muku ina magana da wasu harsuna, amfanin me zan yi muku im ban zo muku da wani buɗi ko ilimi, ko yin faɗin Maganar Allah, ko koyad da Maganar Allah ba? 7 In abubuwan nan marasa rai, kamar su sarewa da molo, muryarsu ba ta fita sosai ba, yaya wani zai san abin da a ke busawa ko kaɗawa? 8 Im ba am busa bigila sosai ba, wa zai yi shirin dabur? 9 Haka ma ya ke a gare ku. In kun yi magana da wani harshe, wanda ba a fahinta ba, yaya wani zai san abin da a ke faɗa? Kun yi magana a banza ke nan! 10 Hakika akwai harsuna iri-iri a duniya, ba kuwa wanda ba shi da ma’ana. 11 In kuwa ba na jin harshen, sai in zama bare ga mai maganar, mai maganar kuma ya zama bare a gare ni. 12 Haka ma ya ke a gare ku. Tun da ya ke kun dokanta da samun baye-baye na Ruhu Tsattsarka, sai ku himmantu ku ba da ƙarfinku ga inganta ikiliziya.

13 Saboda haka duk mai magana da wani harshe, sai ya yi addu’a a yi masa baiwar fassara. 14 In na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne ke addu’a, amma tunanina bai amfani kowa ba. 15 To, ƙaƙa ke nan? Zan yi addu’a da ruhuna, zan kuma yi game da tunanina. Zan yi waƙar yabon Allah da ruhuna, zan kuma yi game da tunanina. 16 Im ba haka ba, in ka gode wa Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda ke jahili zai ce “Amin” kan godiyad da ka ke yi, im bai san abin da ka ke faɗa ba? 17 Ko da ya ke ka gode wa Allah sosai, ai ɗan’uwanka bai ƙaru da komai ba. 18 Na gode Allah ina magana da wasu harsuna fiye da ku duka. 19 Duk da haka dai a cikin taron ikiliziya na gwammace im faɗi kalmomi biyar game da tunanina, don in karantad da wasu, da im faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.

20 Ya ku’Yan’uwa, kada ku yi hankali irin na yara, sai dai wajen mugunta ku yi halin jarirai, amma wajen hankali ku yi dattako. 21 A rubuce ya ke cikin Littattafai Tsarkaka cewa, “Zan yi magana da jama’an nan ta kan mutane masu baƙin harsuna, da

kuma ta harshen baƙi, duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba, in ji Ubangiji.” 22 Wato ashe harsuna a kan alamomi su ke, ba ga masu ba da gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Yin faɗin Maganar Allah kuwa don masu ba da gaskiya ne, ba don marasa ba da gaskiya ba. 23 Saboda haka in dukkan ikiliziya ta taru, kuma kowa na magana da wani harshe daban, kuma wasu jahilai ko marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe ba sai su ce kun ruɗe ba? 24 In kuwa kowa na yin faɗin Maganar Allah, kuma wani marar ba da gaskiya ko jahili ya shigo, sai maganar kowa ta ratsa shi, ya kuma tsargu a ransa ta maganar kowa, 25 kuma asiran zuciyarsa su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.

26 To, ƙaƙa abin ya ke ’Yan’uwa? Duk sa’ad da kuka taru, wani kan riƙo waƙar yabon Allah, wani kuwa koyad da Maganar Allah, wani, wani buɗi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi komai don ingantawa. 27 In kuwa wasu za su yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku su ma kuwa bi da bi, wani kuma ya yi fassara. 28 In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu ya yi shiru cikin taron ikiliziya, ya yi wa Allah magana a zuci. 29 Masu yin faɗin Maganar Allah kuma sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar. 30 In kuwa an yi wa wani wanda ke zaune wani buɗi, sai na farkon nan mai maganar ya yi shiru. 31 Dukkanku kuna iya yin faɗin Maganar Allah dai-dai da dai-dai, bar kowa ya koya, ya kuma sami ƙarfin-gwiwa. 32 Ruhohin masu yin faɗin Maganar Allah na bin masu yin faɗin Maganar Allah, 33 domin Allah ba Allahn rudu ba ne, na lumana ne.

Haka ya ke kuwa a duk ikiliziyan tsarkaka. 34 Sai mata su yi shiru a taron ikiliziya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce. 35 In akwai wani abin da su ke so su sani, to, sai su tambayi mazansu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a taron ikiliziya. 36 Kai! Maganar Allah a kanku ne ta fara, ko kuwa gare ku kaɗai ta isa?

37 In wani ya ga shi mai yin faɗin Maganar Allah ne, ko kuwa Ruhu Tsattsarka ya yi masa wata baiwa, to, sai ya fahinci cewa abin nan da na ke rubuto muku umarni ne na Ubangiii. 38 In kuwa wani ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi. 39 Saboda haka, ’Yan’uwa, sai ku himmantu ga samun baiwar yin faɗin Maganar Allah, kuma kada ku hana yin magana da wasu harsuna. 40 Sai dai a yi komai ta hanyad da ta dace, kuma a shirye.

15

Yanzu kuma, ’Yan’uwa, zan tuna muku da Bisharad da na sanad da ku, wadda kuka karɓa, wadda ku ke bi, 2 wadda kuma a ke cetonku da ita, muddar kun riƙe maganad da na sanad da ku kankan im ba sama-sama ne kuka gaskata ba.

Jawabi Mafi Muhimmanci

3 Jawabi mafi muhimmanci da na sanad da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa Almasihu ya mutu domin zunubammu, kamar yadda Littattafai Tsarkaka suka faɗa, 4 kuma cewa am binne shi, kuma cewa an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai Tsarkaka suka faɗa, 5 kuma cewa ya bayyana ga Kefas, sa’an nan ga Sha biyun. 6 Sa’an nan ya bayyana ga ’Yan’uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda, yawancinsu kuwa suna nan har yanzu, amma wadansu sun yi barci. 7 Sa’an nan ya bayyana ga Yakubu, sa’an nan ga dukkan Manzanni. 8 Daga ƙarshe duka ya bayyana a gare ni, ni ma da na ke ƙasasshe, marar cancanta. 9 Don ni ne mafi ƙanƙanta cikin Manzanni, ban ma isa a ce da ni Manzo ba, saboda na tsananta wa ikiliziyar Allah. 10 Amma saboda rahamar Allah na zama yadda na ke, rahamad da ya yi mini kuwa ba a banza ta ke ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, rahamar Allah ce da ke zuciyata. 11 To, ko ni ne dai, ko kuma su ne, haka mu ke wa’azi, ta haka kuma kuka gaskata.

Harsashin Bangaskiyarmu

12 To, da ya ke ana wa’azin Almasihu kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa wasunku ke cewa babu tashin matattu? 13 In dai babu tashin matattu, ashe ba a ta da Almasihu ba ke nan. 14 In kuwa ba a ta da Almasihu ba, to, ashe wa’azimmu banza ne, bangaskiyarku kuma banza ce. 15 Sai ma ya zamana mun yi wa Allah shaidar zur ke nan, don mun shaidi Allah cewa ya ta da Almasihu, wanda kuwa bai tasa ba, in da gaskiya ne ba a ta da matattu. 16 Don kuwa im ba a ta da matattu, ashe Almasihu ma ba a ta da shi ba ke nan. 17 In kuwa ba a ta da Almasihu ba, ashe bangaskiyarku banza ce, kuma har yanzu kuna tare da zunubanku. 18 Ashe kuma waɗanda suka yi barci a kan suna na Almasihu, sun halaka ke nan. 19 Da kuwa dogararmu ga Almasihu duniyan nan kaɗai ta shafa, ai da duk cikin mutane mu ne muka fi kowa zama abin tausayi.

Tabbatar Tashin Almasihu daga Matattu

20 Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma tumun fari cikin waɗanda suka yi barci. 21 Tun da ya ke mutuwa ta kan mutun ta faru, haka kuma tashin matattu ta kan Mutun ya ke. 22 Kamar yadda duk a ke mutuwa saboda Adamu, haka duk za a rayad da kowa saboda Almasihu. 23 Amma kowanne bi da bi; Almasihu ne tumun fari, sa’an nan a ranar komowatasa, waɗanda ke na Almasihu. 24 Sa’an nan sai ƙarshen, sa’ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko. 25 Don kuwa lalle ne ya yi mulki, bar sai ya take dukkan maƙiyansa. 26 Magabciyar ƙarshe da za a shafe, ita ce mutuwa. 27 “Gama Allah ya kallafa komai ƙarƙashin ikonsa.” Amma da aka ce, “An kallafa komai ƙarƙashin ikonsa” ɗin, a fili ya ke cewa shi wannan da ya kallafa komai ƙarƙashin ikonsa, a keɓe ya ke. 28 Sa’ad da kuma aka kallafa komai ƙarƙashin ikonsa ɗin, sa’an nan ne ɗan da kansa shi ma zai kallafa kansa ga wannan da ya kallafa komai ƙarƙashin ikonsa, don Allah yd tabbata shi ne komai da komai.

29 Im ba haka ba, me nufin waɗanda a ke yi wa babtisma maimakon matattu? Im ba a ta da matattu sam, dom me a ke yi wa waɗansu babtisma maimakonsu? 30 Dom me kuma na ke cikin hatsari kowane lokaci? 31 Na haƙiƙance ’Yan’uwa, saboda taƙama da ku da na ke yi cikin al’amarin Almasihu Yesu Ubangijimmu, kowace rana sai na sallama raina ga mutuwa! 32 Idan bisa ga ra’ayin mutun ne, na yi kokawa da masu halin damisa a Afisa, mecece ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da ya ke gobe za mu mutu?” 33 Kada fa a yaudare ku! “Zama da maɗaukin kanwa shi kan kawo farin kai.” 34 Ku farka daga magagi, ku kama aikin gaskiya, ku daina ɗaukar zunubi. Wasu kam sun jahilci Allah. Na faɗi wannan ne don ku kunyata.

Kowace Halitta da irin Jikinta

35 Kila wani zai yi tambaya, “Ƙaƙa a ke ta da matattu? Da wace irin kama kuma su ke fitowa?” 36 Kai, marar azanci! Abin da ka shuka ai ba zai tsiro ba sai ya mutu. 37 Abin da ka shuka kuma, ba shi ne ainihin abin da zai kasance ba, ƙwaya ce kawai, ko ta alkama, ko wata irin ƙwaya daban. 38 Amma Allah ya kan ba ta kama, yadda ya nufa, kowace ƙwaya da irin tata kama. 39 Don ba dukkan tsoka ce iri ɗaya ba, mutane da irin tasu, dabbobi da irin tasu, tsuntsaye da irin tasu, kifaye kuma da irin tasu. 40 Akwai halitta irin ta sama, akwai kuwa irin ta ƙasa. Amma ɗaukakar irin ta sama daban, ɗaukakar irin ta ƙasa kuma daban. 41 Ɗaukakar rana daban, ta wata daban, ta taurari kuma daban. Wani tauraro kuwa ya kan bambanta da wani wajen ɗaukaka.

Jikin Tashi daban da na Mutuwa

42 Haka kuma ya ke ga tashin matattu. A kan shuka su cikin halin ruɓa, a kan kuma ta da su cikin halin rashin ruɓa. 43 A kan shuka cikin wulakanci, a kan tasa cikin ɗaukaka, a kan shuka cikin rashin ƙarfi, a kan tasa cikin ƙarfi. 44 A kan shuka da jikin mutuntaka, a kan tasa da jiki na ruhu. Da ya ke akwai jiki na mutuntaka, lalle kuma akwai jiki na ruhu. 45 Haka kuma ya ke a rubuce, “Mutumin farko, Adamu, ya zama rayayyen taliki”; Adamun ƙarshe kuwa Ruhu ne Mai rayarwa. 46 Amma ba shi na ruhun nan ne ya fara bayyana ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhun. 47 Mutumin farko daga ƙasa ya ke, kuma na turɓaya ne. Na biyun kuwa daga Sama ya ke. 48 Kamar yadda shi na turɓayan nan ya ke, haka kuma waɗanda ke na turɓaya su ke. Kamar yadda Shi na Saman nan ya ke, haka kuma waɗanda ke na Sama su ke. 49 Kamar yadda muka ɗauki siffar na turɓayan nan, haka kuma za mu ɗauki siffar na Saman nan. 50 Ina dai gaya muku wannan, ’Yan’uwa, ba shi yiwuwa jiki mai tsoka da jini ya sami gado a cikin Mulkin Allah, haka kuma mai ruɓa ba ya gadon marar ruɓa.

Ke Mutuwa ina Nasararki a Kammu?

51 Ga shi zan sanad da ku wani zuzzurfan al’amari! Ba dukkammu ne za mu yi barci ba, amma dukkammu za a sauya kamannimmu, 52 farad-ɗaya, cikin ƙiftawar ido, da jin busar ƙaho na ƙarshe. Don za a busa ƙaho, kuma za a ta da matattu cikin halin rashin ruɓa, za a kuma sauya kamannimmu. 53 Don lalle ne marar ruɓa ya maye mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwan nan. 54 Sa’ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwan nan, a sa’an nan ne fa Maganan nan da ke rubuce za a cika ta, cewa, “An shafe mutuwa da aka ci garinta.”

55 “Ke mutuwa, ina nasararki?
Ke mutuwa, ina karinki?”

56 Ai zunubi shi ne karin mutuwa, Shari’a kuwa ita ce sanadin ƙarfin zunubi. 57 Godiya tā tabbata ga Allah wanda ke ba mu nasara ta kan Ubangijimmu Yesu Almasihu.

58 Don haka ya ’Yan’uwana, kaunatattu, ku tsaya tsaiwar daka, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, don kuwa kun san faman da ku ke yi saboda Ubangiji ba a banza ya ke ba.

16

Ba da Gudummawa ga Gajiyayyun Tsarkaka

To, yanzu kuma batun ba da gudummawa ga tsarkaka, kamar yadda na umarci ikiliziyoyin Galatiya, haka ku ma za ku yi. 2 A kowace ranar farko ta mako, kowannenku ya riƙa tanada wani abu, yana ajiyewa gwargwadon samunsa, kada sai na zo tukuna a tara gudummawa. 3 Sa’ad da na iso, sai in aiki waɗanda kuka amince da su da wasiƙa, su kai baikonku Urushalima. 4 In ya kyautu ni ma in tafi, to, sai su raka ni.

5 Zan zo gare ku bayan na zazzaga ƙasar Makidoniya, don kuwa ta Makidoniya zan bi. 6 Watakila zan jima a wurinku, ko ma in ci damuna, don ku yi mini rakiya duk inda za ni. 7 Ba sona ne in gan ku yanzu in wuce kawai ba, a’a, ina sa zuciya ma in yi kwanaki gare ku, in Ubangiji ya yarda. 8 Amma zan dakata a Afisa har ranar Fentikos. 9 Don kuwa am buɗe mini wata hanya mai faɗi ta yin aikin kwazo, akwai kuma magabta da yawa.

10 In Timotawas ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji ya ke yi kamar yadda na ke yi. 11 Kada fa kowa ya raina shi. Ku raka shi lafiya, ya komo gare ni, don ina duban hanyarsa tare da ’Yan’uwa.

12 Batun Ɗan’uwammu Afalas kuwa, na roƙe shi ƙwarai ya zo wurinku tare da sauran ’Yan’uwa, amma ko kusa bai yi nufin zuwa yanzu ba. Zai zo dai sa’ad da ya ga ya dace.

13 Ku zauna a faɗake, ku tsaya tsaiwar daka ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi. 14 Duk abin da za ku yi, ku yi shi da ƙauna.

15 To, ’Yan’uwa, kun sani fa jama’ar gidan Istifanas su ne tumun fari a ƙasar Akaya, sun kuwa ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. 16 Ina roƙonku ku yi wa irin waɗannan mutane biyayya, har ma ga duk waɗanda ke abokan aikinunu da wahalarmu. 17 Na yi farinciki da zuwan Istifanas da Fartunatas da Akaikas, domin sun ɗebe mini kewarku. 18 Sun dai wartsakad da ni da kuma ku. Sai ku kula da irin waɗannan mutane.

19 Ikiliziyoyin ƙasar Asiya na gaishe ku. Akila da Biriska, tare da ikiliziyad da ke taruwa a gidansu, na gaishe ku da kyau da kyau saboda Ubangiji. 20 Dukkan ’Yan’uwa na gaishe ku. Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.

21 Ni Bulus, ni na ke rubuta gaisuwan nan da hannuna. 22 Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji yă zama la’ananne. Ubangijimmu fa na zuwa! 23 Alherin Ubangijimmu Yesu yă tabbata a gare ku. 24 Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙauna, albarkacin Almasihu Yesu. Hakika.


WASIƘAR BULUS TA BIYU
ZUWA GA
KORINTIYAWA

1

Daga Bulus, Manzon Almasihu Yesu cikin yardar Allah, da kuma Ɗan’uwammu Timotawas, zuwa ga ikiliziyar Allah da ke Korinti, tare da dukkan tsarkaka na duk ƙasar Akaya.

2 Alheri da aminci na Allah Ubammu, da na Ubangiji Yesu Al,nasihu su tabbata a gare ku.

Yabo ya Tabbata ga Allah

3 Yabo ya tabbata ga Allahn Ubangijimniu Yesu Almasihu, kuma Ubansa, Uba Mai yawan rahama, Allah Mai haddasa kowane irin ƙarfin-gwiwa, 4 shi da ke ƙarfafa mana gwiwa cikin dukkan wahalarmu, don mu ma mu iya ƙarfafa wa masu shan kowace irin wahala gwiwa, da ƙarfin-gwiwan nan da mu ma muka samu a gun Allah. 5 Don kuwa kamar yadda mu ke shan wuya da gaske irin wadda Almasihu ya sha, haka kumaa ke ƙarfafa mana gwiwa da gaske, ta kan Almasihu. 6 In ana wahalshe mu ma, ai saboda ƙarfafa muku gwiwa ne, da kuma lafiyarku. In kuwa ƙarfafa mana gwiwa a ke yi, ai saboda ƙarfafa muku gwiwa ne, wadda ta ke sa ku ku hakurce wa irin wuyan nan da mu ke sha. 7 Sazuciyarmu ga al’amarinku ƙaƙƙarfa ce, don mun san kamar yadda kuka yi tarayya da mu cikin shan-wuya, haka kuma za ku yi tarayya da mu cikin ƙarfin-gwiwa.

8 ’Yan’uwa, ba ma so ku jahilta da wahalad da muka sha a ƙasar Asiya, domin mun jikkata ƙwarai da gaske, har abin ya fi ƙarfimmu, har ma muka fid da tsammanin rayuwa. 9 Kai har ma muka ji kamar hukuncin kisa aka yi mana, wannan kuwa don kada mu dogara da kammu ne, sai dai da Allah, mai ta da matattu. 10 Shi ne ya kuɓutad da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutad da mu, kuma da shi mu ke dogara ya kuɓutad da mu har ila yau. 11 Ku ma sai ku taimake mu da. addu’a, don mutane da yawa su gode wa Allah a dalilimmu, saboda albarkad da aka yi mana ta amsa addu’o’i masu yawa.

Taƙamarmu game da Ku

12 Taƙamarmu ita ce, shaidan nan da zuciyarmu ke amince mana, cewa mun yi zaman tsarkaka a duniya da zuciya-ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa wayo irin na ɗan’adam ba, sai dai bisa alherin Allah. 13 Domin wasiƙarmu gare ku ba ta ƙunshe wani abu dabam ba, sai dai ainihin abin da kuka karanta kuka fahinta; ina kuwa fata ku fahinta sosal da sosai, 14 kamar yadda kuka riga kuka ɗan fahince mu, cewa kwa iya yin takama da mu, kamar yadda mu ma za mu iya yi da ku, a ranar Ubangijimmu Yesu.

15 Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, don ku ci riba biyu. 16 Wato niyyata im bi ta kanku in za ni Makidoniya, in kuma komo wurinku daga Makidoniya, sannan ku yi mini rakiya in zan tafi Yahudiya. 17 Ashe da na yi njyyar yin haka, wato na nuna rashin tsai da zuciya ke nan? Ko kuwa shiririta, na ke yi kamar ɗan’adan kawai, in ce ‘I’ in koma in ce ‘A’a’? 18 Yadda ba shakka Allah ya ke mai alkawari, haka ma maganad da muka yi muku, ba shiririta a ciki. 19 Don kuwa ɗan Allah, Yesu Almasihu, wanda ni da Silwanas da Timotawas muka yi muku wa’azi, ai ba shiririta game da shi, kullum a kan gaskiya ya ke. 20 Don dukkan alkawaran Allah cikarsu a gare shi ta ke, ta kansa ne kuma mu ke faɗar ‘Amin’, don a ɗaukaka Allah. 21 Don kuwa Allah shi ne mai tabbatad da mu da ku gaba-ɗaya ga Almasihu, mai kuma shafarmu, tsattsarkar shafa. 22 Ya tabbatad da mu nasa ne, ya kuma yi mana baiwa da Ruhunsa a zukatammu, saboda tabbatarwa.

23 Labudda Allah shi ne mashaidina a kan cewa musamman don in sauƙaƙe muku ne na fasa zuwa Korinti. 24 Ba wai muna nuna muku iko a kan al’amarin bangaskiyarku ba ne, a’a, muna aiki tare ne, don ku yi farinciki, domin game da al’amarin bangaskiyarku kam kuna tsaye kankan.

2

Na ƙudura a raina ba zan sake zuwa wurinku in sa ku baƙinciki ba. 2 To, in na sa ku baƙinciki, wa zai faranta mini rai im ba wanda na sa baƙincikin ba? 3 Na rubuto muku haka ne don kada in na zo, waɗanda ya kamata su faranta mini rai, ya zamana sun sa ni baƙinciki. Don na amince da ku duka cewa farincikina naku ne ku duka. 4 Na rubuto muku ne ina cikin wahala da baƙinciki gaya, har da hawaye mai yawa, ba wai don in sa ku baƙinciki ba sai dai don ku san irin tsananin ƙaunad da na ke yi muku.

A Sake Karbar Wanda ya Tuba

5 Amma in wani ya jawo baƙinciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba amma ga wani fanni sai in ce dukkanku ne ya jawo wa—ba wai tsanantawa na ke yi ba. 6 Irin mutumin nan, horon nan da galibin jama’a suka yi masa, ai ya isa haka. 7 Gara dai ku yafe masa, ku kuma ƙarfafa masa gwiwa, don kada gayar bafcinciki ya sha kansa. 8 Saboda haka ina roƙonku ku tabbatar masa da ƙaunarku. 9 Na rubuto muku wannan takanas don in jarraba ku, in ga ko kuna biyayya ta kowace hanya. 10 Wanda kuka yafe wa komai, ni ma na yafe masa. Abin da na yafe kuwa, in dai har ma akwai abin yafewan, saboda ku ne na yafe masa, albarkacin Almasihu, 11 don kada Shaiɗan ya ribace mu, gama mu ba jahilan kissoshinsa ba ne.

12 To, sa’ad da na zo Taruwasa in yi Bisharar Almasihu, ko da ya ke am buɗe mini hanya cikin al’amarin Ubangiji, 13 duk da haka dai hankalina bai kwanta ba, don ban tarad da Ɗan’uwana Titus a can ba, saboda haka sai na yi bankwana, da su, na zarce na tafi Makidoniya.

14 Amma godiya ta tabbata ga Allah, shi da kullum ya ke yi mana jagaba mu ci nasara albarkacin Almasihu, ta kammu kuma ya ke baza ƙanshin nan na sanin Almasihu a ko’ina. 15 Don kuwa a gun Allah mu ne ƙanshin Almasihu a cikin waɗanda a ke ceto, da waɗanda ke hanyar halaka. 16 Ga na yayyau ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne mai kaiwa ga halaka; ga na farkon kuwa, ƙanshin rai madawwami ne mai kaiwa ga rai madawwami. To, wa zai iya ɗaukan nauyin waɗannan abubuwa? 17 Don mu ba kamar mutane da yawa mu ke ba, masu yi wa Maganar Allah algus; mu kaifi ɗaya ne, kamar yadda Allah ya umarce mu, haka mu ke magana tsakani da Allah, muna na Almasihu.

3

Wato har ila yau yabon kammu za mu fara yi kuma? Ko kuwa muna bukatar wasikokin yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda wasu ke yi? 2 Ai ku kanku ku ne wasiƙarmu ta yabo, wadda aka rubuta a zukatanku, don kowa yă san ta, ya kuma karanta ta. 3 A fili ya ke ku wasiƙa ce ta Almasihu, ta hannummu, ba kuwa rubutun tawada ba ne, na Ruhun Allah Ravayye ne, ba kuwa a kan allunan dutse aka rubuta ta ba, sai dai a zuci.

Iyawarmu daga Allah ta ke

4 Wannan ita ce irin amincewarmu ga Allah ta kan Almasihu. 5 Ba wai mun isam ma kammu ba ne, har da za mu ce mu ne mu ke ƙudura wani abu, a’a, iyawarmu daga Allah ta ke, 6 don shi ne ya iyam mana muka zama masu hidima na Sabon Alkawari, ba alkawarin rubutacciyar ka’ida ba, sai dai na Ruhu Tsattsarka. Don kuwa rubutacciyar ka’ida, kisa ta ke yi; Ruhu Tsattsarka kuwa, rayarwa ya ke yi.

Saunn Ɗaukaka Marar Dusashewa

7 To, im baiwar ka’idodin nan masu kaiwa ga halaka ma, waɗanda aka zana a jikin dutse, am bayyana ta da babbar ɗaukaka haka, har Bani Isra’ila suka kasa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ga ta kuwa mai shuɗewa ce, 8 me zai hana baiwar Ruhu Tsattsarka ta kasance da mafificiyar ɗaukaka? 9 Tun da ya ke akwai ɗaukaka game da baiwar ka’idan nan mai sa hukunci, ashe lalle ne ka’idan nan ta samun karɓuwa ga Allah tă fi ta ɗaukaka nesa. 10 Hakika a wannan hali, abin da dā ke da ɗaukaka ya rasa ɗaukaka sam, saboda mafificiyar ɗaukakad da ta jice ta. 11 Don in aba mai shuɗewa am bayyana ta da ɗaukaka, ashe abin da ke dawwamamme lalle ne ya kasance da ɗaukakad da ta fi haka nesa.

12 Tun da ya ke muna da sazuciya irin wannan, to, muna magana ne gabammu gaɗi ƙwarai. 13 Ba kamar Musa mu ke ba, wanda ya rufe fuskatasa da mayafi, don kada Bani Isra’ila su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa. 14 Amma sai hankalinsu ya dushe, domin har ya zuwa yau in ana karatun Tsohon Alkawari, mayafin nan har yanzu ba a yaye ya ke ba, domin ba ya yayuwa sai ta kan Almasihu kaɗai. 15 Hakika har ya zuwa yau, duk lokacin da a ke karatun Littattafan Musa, sai mayafin nan ya kan rufe zukatansu. 16 Amma da zarar mutun ya juyo ga Ubangiji, sai a kan yaye masa mayafin. 17 To, Ubangiji fa shi ne Ruhu, kuma inda Ruhun Ubangiji ya ke, a nan ’yanci ya ke. 18 Mu dukkammu kuma fuska buɗe mu ke nuna ɗaukakar Ubangiji kamar madubi, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji kuwa wanda ya ke shi ne Ruhu, shi ke zartad da haka.

4

Hasken Ɗaukakar Almasihu

Saboda haka, da ya ke muna da wannan hidima bisa rahamar Allah, ba za mu karai ba. 2 Ba ruwammu da ɓoye-ɓoye na munafunci, ko makirci, ko yi wa Maganar Allah algus, amma ta bayyana Maganar Gaskiya a fili, sai kowane mutun ya shaidi gaskiyarmu a zuciyatasa a gaban Allah. 3 Kuma ko da Bishararmu a rufe ta ke, ai ga waɗanda su ke hanyar halaka kaɗai ta ke a rufe 4 Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantad da hankalinsu, don kada hasken Bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da ke surar Allah, ya haskaka su. 5 Don ba wa’azin kammu mu ke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu. 6 Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatammu don haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.

7 Wannan arziki da mu ke da shi kuwa, a jiki na yumɓu ya ke, don a nuna cewa mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba. 8 Ana wahalshe mu ta kowace hanya, duk da haka ba a ci ɗungumimmu ba. Ana ruɗa mu, duk da haka ba mu karai ba. 9 Ana tsananta mana, duk da haka ba mu zama yasassu ba. Ana ta fyaɗa mu da ƙasa, duk da haka ba a hallaka mu ba. 10 Kullum muna cikin haɗarin kisa, irin kisan da aka yi wa Yesu, don a bayyana ran Yesu ta gare mu. 11 Wato muddar muna raye, kullun zaman mutuwa mu ke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta jikin nan namu mai mutuwa. 12 Ta haka mutuwa ke jewa a kammu, ku kuwa ta ke haddasa muku rai madawwami.

13 Tun da ya ke muna da ruhun bangaskiya iri ɗaya da na wanda ya rubuta wannan, “Na gaskata, saboda haka na yi magana,” to, mu ma mun gaskata, saboda haka kuma mu ke magana. 14 Mun san cewa shi wannan da ya ta da Ubangiji Yesu daga matattu, mu ma zai tashe mu albarkacin Yesu, yă kuma kawo mu gabansa tare da ku. 15 Duk wannan fa don amfaninku ne, don alherin Allah ya yaɗu ga mutane masu yawa, ta haka ya zama sanadin yawaita godiya ga Allah, don a ɗaukaka Allah.

16 Saboda haka ba mu karai ba, ko da ya ke jikimmu na mutuntaka na ta lalacewa, duk da haka ruhummu kowace rana sabunta shi a ke yi. 17 Don wannan ’yar wahala tamu mai saurin wucewa ita ke tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. 18 Domin ba abubuwan da ido ke gani mu ke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa; gama abubuwan da a ke gani, masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.

5

Muna Marmarin Zama a gun Allah

Don kuwa mun san cewa in an rushe ginin nan na yumɓu da mu ke ciki a nan duniya, muna da wani gini madawwami a Sama, ginin Allah kuwa, ba na mutum ba. 2 A wannan na duniya ne mu ke kuka, mu ke ɗokin shiga ginin nan namu na Sama, 3 don im mun shige shi, ba za mu zauna ba gida ba. 4 Ai muddar muna wannan gini na yumɓu, za mu yi ta kuka ne, muna marmatse, ba wai don muna so mu zauna ba gida ba, a’a, sai dai don a sake ba mu wani, wannan kuwa don rai madawwami ya maye abin nan mai mutuwa ne. 5 Allah kuwa shi ya tanadar mana wannan sākewa, shi da ya ba mu Ruhu Tsattsarka saboda tabbatarwa.

6 Saboda haka kullum mu ke da ƙarfin-gwiwa, mun kuma san cewa muddar muna tare da wannan jiki, rabe mu ke da Ubangiji, 7 domin zaman bangaskiya mu ke yi, ba na ganin ido ba. 8 Hakika muna da ƙarfin-gwiwa, mun kuma gwammaci mu rabu da jikin nan mu zauna a gun Ubangiji. 9 Saboda haka, ko muna gunsa, ko muna rabe da shi, burimmu shi ne mu faranta masa. 10 Don lalle ne dukkammu a ƙididdige mu a gaban gadon shari’ar Almasihu, don kowa ya sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko hairi ko sharri.

Kaunar Almasihu ce ke Tafi da Mu

11 Da ya ke mun san muna da tsoron Ubangiji, shi ya sa mu ke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda mu ke kuwa, ai sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin ya ke a zuciyarku. 12 Har wa yau kuma, ba wai yabon kammu mu ke yi a gare ku ba, sai dai muna ba ku hanyar yin taƙama da mu ne, don ku samu ku mai da jawabi ga waɗanda ke alfahari da muƙaminsu, ba da halinsu ba. 13 In hankalimmu ya fita, ai saboda Allah ne; in kuwa cikin hankalimmu mu ke, ai ribarku ce. 14 Kaunar Almasihu gare mu ita ke tafi da mu, saboda haka mun tabbata cewa da ya ke wani ya mutu a maimakon dukkan mutane, ashe kuwa mutuwar tasu ce dukkansu. 15 Ya kuwa mutu ne a maimakon dukkan mutane, don waɗanda ke raye, kada su yi zaman ganin dama nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu a maimakonsu, aka kuma tashe shi dominsu.

16 Saboda haka nan gaba ba ma ƙara duban kowane mutun a kan zahirinsa kawai, don ko da ya ke mun taɓa duban Almasihu kan yana mutun, yanzu ba ma ƙara dubansa haka. 17 Saboda haka, duk wanda ke na Almasihu, sabuwar halitta ne, tsohon al’amari duk ya shuɗe, ga shi komai ya zama sabo. 18 Duk wannan kuwa yin Allah ne, shi da ya sada mu da kansa ta kan Almasihu, ya kuma ba mu aikin shelar sadarwar, 19 wato, Allah ne ta kan Almasihu ya ke sada ’yan’adan da shi kansa, ba ya kuwa dubansu da laifuffukansu, ya kuma danƙa mana maganan nan ta sadarwar. 20 Saboda haka mu jakadu ne na Almasihu, wato Allah na neman mutane ta kammu. Muna roƙonku a madadin Almasihu, a sada ku da Allah. 21 Shi da bai ma san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, don mu zama ababan karɓuwa ga Allah ta kansa.

6

Ba Mu Zame wa Kowa Sanadin Tuntuɓe ba

Da ya ke kuma muna aiki tare da Allah, muna roƙonku kada ku yi na’am da alherin Allah a banza. 2 Don ya ce,

“Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa,
Na kuma taimake ka a ranar ceto.”

Ga shi yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma yau ranar ceto! 3 Ba ma zame wa kowa sanadin tuntuɓe, don kada a aibata aikimmu. 4 Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah mu ke, ta matuƙar jurewa, da shan wahala, da kuntata, da masifu, 5 da shan duka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da hana ido barci, da kuma hana kai abinci. 6 Muna kuma bayyana gaskiyarmu ta halin tsarkaka, da sani, da haƙuri, da kirki, da Ruhu Tsattsarka, da sahihiyar ƙauna, 7 da Maganar Gaskiya, da kuma ikon Allah. Muna riƙe da makaman aikin gaskiya dama da hauni. 8 Ana ɗaukaka mu, ana kuma wulakanta mu; ana yabommu, ana kuma kushemmu. An ɗauke mu a kan mayaudara, mu kuwa masu gaskiya ne. 9 Kamar ma ba a san mu ba, an kuwa san mu sarai; kamar a bakin mutuwa mu ke, ga shi kuwa muna raye; ana ta horommu, duk da haka ba a kashe mu ba; 10 kamar muna baƙinciki, kullum kuwa farinciki mu ke yi; kan matalauta mu ke, duk da haka kuwa muna arzuta mutane da yawa; kamar ba mu da komai alhali kuwa komai namu ne.

11 Ya ku Korintiyawa, ba mu ɓoye muku komai ba, mun saki zuciya da ku ƙwarai. 12 Ai ba wata rashin yarda a zuciyarmu sai dai a taku. 13 Ina roƙonku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.

Kada Ku Cuɗanya da Marasa Ba Da Gaskiya

14 Kada ku yi cuɗanya marar dacewa da marasa ba da gaskiya. To, me ya haɗa aikin gaskiya da na saɓo? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? 15 Ina kuma jiyayyar Almasihu da Beliyala? Me kuma ya haɗa mai ba da gaskiya da marar ba da gaskiya? 16 Wace yarjejjeniya ce ke tsakanin tsattsarkan mazaunin Allah da gumaka? Don mu tsattsarkan mazauni ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce,

“Zan zauna a zukatansu, in tafi da al’amuransu;
Zan kuma kasance Allahnsu,
Su kuma su kasance jama’ata.
17 Saboda haka sai ku fito daga cikinsu,
Ku keɓe, in ji Ubangiji.
Kada ku ko taɓa wani abu marar tsarki;
Ni kuwa in yi na’am da ku,
18 In kasance Uba gare ku,
Ku kuma ku kasance ’ya’yana, maza da mata,
In ji Ubangiji Maɗaukaki.”

7

Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kammu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, mu yi tsarkaka. kamila saboda tsoron Allah.

2 Ku saki zuciya da mu; ai ba mu cuci kowa ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu kuwa zambaci kowa ba. 3 Ba don in sa muku laifi na faɗi haka ba, don dā ma na gaya muku a rammu ku ke, duniya da Lahira. 4 Na amince da ku ƙwarai, ina kuma taƙama da ku gaya. Gwiwata ta yi ƙarfi matuƙa. Duk da wahalcemmu dai ina farinciki ƙwarai da gaske.

Bulus ya yi Farinciki da Zuwan Titus

5 Ko lokacin da muka zo ƙasar Makidoniya ma, ba mu sami shaƙatawa ba, ana ta wahalshe mu ta kowace hanya, rana zafi, inuwa zafi. 6 Amma Allah, shi da ke ƙarfafa wa ƙasƙantattu gwiwa, sai ya ƙarfafa mana gwiwa da zuwan Titus, 7 ba kuwa da zuwan Titus kawai ba, har ma game da ƙarfin-gwiwan nan da ya samu a wurinku, yayin da ya gaya mana yadda ku ke begena, kuna nadama, kuna kuma himmantuwa ga goyuwa bayana, har ma na ƙara farinciki ƙwarai. 8 Ko da na ɓata muku rai game da wasiƙad da da na rubuto muku, ba na baƙinciki da haka, ko da ya ke dā kam na yi baƙinciki, don na lura wasiƙan nan ta ɓata muku rai, ko da ya ke dai zuwa ɗan lokaci kaɗan ne. 9 Amma yanzu kam, ina farinciki, ba wai don kun yi baƙinciki ba, sai dai don baƙincikinku ya sa ku tuba, don kun yi baƙinciki irin wanda Allah ke so. Saboda haka ba ku yi hasarar komai a sanadimmu ba. 10 Don baƙinciki irin wanda Allah ke so shi ke kaiwa ga tuba, da kuma samun ceto, ba ya kuma sa ɗan-da-na-sani. Amma baƙinciki kan al’amarin duniya shi ke jawo halaka. 11 Ku dubi fa irin himmad da baƙincikin nan da Allah ke so ya haddasa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al’amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmad da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. Game da wannan sha’ani kam lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi. 12 To, ko da ya ke na rubuto muku wasiƙa, ba wai musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutan ba, sai dai don a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da ku ke yi da zarafimmu. 13 Saboda haka ne gwiwarmu ta yi ƙarfi.

Ban da ƙarfin-gwiwar tamu kuma, har wa yau mun ƙara farinciki ƙwarai saboda farincikin Titus, don dukkanku kun wartsakad da shi. 14 Don ko da na gaya masa ina ’yar taƙama da ku, ban kunyata ba. Kamar yadda duk abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka kuma taƙamarmu da ku a idon Titus ma ta zama gaskiya. 15 Ransa kuma na gare ku fiye da dā ƙwarai, duk sa’ad da ya ke yi na’am tunawa da biyayyarku, ku duka, da kuma yadda kuka yi na’am da shi cikin halin bangirma tare da matsananciyar kula. Ina farinciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.

8

Ikiliziyan Makidoniya sun yi Gudummawa Kwarai

To, ’YanÙuwa, muna so mu sanad da ku alherin Allah da ya bayar a cikin ikiliziyan Makidoniya, 2 wato ko da ya ke an gwada su da matsananciyar wahala, kuma suna cikin bakin talauci, duk da haka yawan farincikinsu har ya kai su ga yin alheri ƙwarai da gaske. 3 Don na tabbata daidai ƙarfinsu suka bayar, har ma, fiye da ƙarfinsu ne, da ra’insu kuwa. 4 Sun roƙe mu ƙwarai da gaske a kan mu yi musu alheri su ma a sa su cikin masu yi wa tsarkaka gudummawa, 5 har ma suka bayar fiye da yadda muka zata, amma af-ta-fari sai suka miƙa kansu ga Ubangiji da kuma mu, bisa nufin Allah. 6 Ganin haka sai muka roƙi Titus, da ya ke shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai kuma yă ƙarasa shi. 7 To, da ya ke kun fifita a cikin kowane abu, wato, a cikin bangaskiya, da fassara Maganar Allah, da sani, da matuƙar himma, da kuma ƙaunad da ku ke yi mana, to, sai ku fifita cikin wannan aikin alheri ma.

8 Ba kallafa muku wannan na ke yi ba, sai dai ta nuna himmar wasu in tabbata cewa ƙaunarku ma sahihiya ce. 9 Domin kun san alherin Ubangijimmu Yesu Almasihu, ko da ya ke dā yana da komai, sai ya zama marar komai saboda ku, don ku zama masu komai albarkacin rashinsa. 10 A wannan al’amari, ga shawarata. Ai ya fiye muku yanzu ku ƙarasa abin da kuka fara yi bara, har kuka yi da ra’inku. 11 To, sai ku ƙarasa aikin da irin ra’in da kuka fara, gwargwadon ikonku. 12 Don im mutun na da niyyar bayarwa gwargwadon abin da ke hannunsa, wannan abin karɓuwa ne ga Allah, gama mutum ba yā ba da abin da ba shi da shi ba. 13 Ba wai nufi na ke yi a sauƙaƙe wa wasu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. 14 Amma don a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu, don wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari. 15 Yadda ya ke a rubuce, cewa, “Wanda ya tara mai yawa, bai saura da komai ba, wanda ya tara kaɗan kuwa, ba abin da ya gaza masa.”

16 Godiya tā tabbata ga Allah wanda ya sanya tsananin kula da ku a zuciyar Titus, kamar yadda na ke yi. 17 Ba kuwa na’am da roƙommu kaɗai ya yi ba, har ma saboda tsananin himmatasa yana zuwa wurinku da ra’in kansa. 18 Ga shi mun aiko Ɗan’uwan nan tare da shi, wanda ya yi suna wajen yin Bishara a dukkan ikiliziyai; 19 ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikiliziyai sun zaɓe shi ya riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da mu ke yi saboda ɗaukaka Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu. 20 Wato muna gudun kada kowa ya zarge mu a kan kyautan nan da a ke yi hannu sake, wadda mu ke kasaftawa. 21 Niyyarmu ce mu yi komai warkan, ba wai a gaban Ubangiji kaɗai ba, har ma a gaban mutane. 22 Muna kuma aiko da Ɗan’uwammu tare da su, wanda sau da yawa muka tabbatad da himmatasa ta hanya iri-iri, yanzu kuma ya fi koyaushe himma, don amincewa da ku da ya ke yi ƙwarai da gaske. 23 Titus kuwa ai abokin tarayyata ne, kuma abokin aikina game da al’amuranku. ’Yan’uwan nan namu kuwa ai manzanni ne na ikƙiziyai, kuma ababan ɗaukaka Almasihu. 24 Saboda haka sai ku tabbatar wa waɗannan mutane a gaban ikiliziyai irin ƙaunarku, da kuma cewa taƙama da ku da mu ke yi gaskiya ce.

9

Bulas ya ce a Shirya Guduinmawa Kafin ya Je

Ba sai lalle na rubuto muku batun ba da gudummawa ga tsarkaka ba, 2 don na san niyyarku, har ma ina taƙama da ku gun mutanen Makidoniya a kan haka, ina ce musu ikiliziyar Akaya ta yi shiri tun bara, himmarku kuwa ta ta da yawancinsu a tsimi. 3 Amma na aiko da ’Yan’uwan nan, don kada taƙamad da mu ke yi da ku a cikin wannan al’amari ta zama ta banza, don ku zauna a kan shiri, kamar yadda dā na ce za ku zauna. 4 Don kada ya zamana in wasu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba ku shirya ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da mu ke yi da ku. 5 Saboda haka na dai ga lalle ne in roƙi ’Yan’uwan nan su riga ni zuwa gare ku, su tanada baikon nan da kuka yi alkawari kafin in zo, don a same shi a shirye, ba tare da matsawa ba, sai dai kyautar sa kai.

Allah na Son Mai Bayarwa a cikin Daɗin-rai

6 Abin la’akari fa shi ne: wanda ya yi ƙwauron yafa iri, gonatasa za ta yi masa ƙwauron amfani, wanda kuwa ya yafa a yalwace, sai ya girba a yalwace. 7 Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin-rai ko tilastawa ba, don Allah na son mai bayarwa a cikin daɗin-rai. 8 Allah kuwa na iya yi muku falala da kowace irin ni’ima, don kullum ku wadata da komai ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake saboda kowane irin kyakkyawan aiki. 9 Kamar yadda ya ke a rubuce, cewa,

“Ya warwatsa hannu sake,
Ya ba gajiyayyu,
Karamcinsa dawwamamme ne.”

10 Shi da ke ba mai shuka iri, ya ke kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku arziki, ya ribanya shi, ya kuma yawaita albarkar karamcinku. 11 Za a wadata ku ta kowace hanya, don ku riƙa bayarwa a yalwace, bayarwan nan kuwa da za ku yi ta kammu, za ta zama sanadin godiya ga Allah. 12 Don aikin nan na alberi, ba biyan bukatar tsarkaka kaɗai ya ke yi ba, har ma yana ƙara yawaita godiya ga Allah ƙwarai da gaske. 13 Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda cewa kun yi na’am da Bisharar Almasihu, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka hannu sake. 14 Su kuwa za su yi muku addu’a, su yi ɗokin ganinku saboda alherin Allah marar misaltuwa da ya yi muku. 15 Godiya tă tabbata ga Allah saboda baiwatasa da ta fi gaban faɗi.

10

Bulus ba ya So ya Nuna Ikonsa

Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da 10 sanyin-hali na Almasihu, ni da ke ‘wulaka-wulaka a cikinku, amma na ke da ƙarfin-hali sa’ad da na ke rabe da ku’, 2 ina roƙonku kada ya zame mini dole in na zo in nuna ƙarfin-hali, in yi magana ƙiri da muzu, yadda na yi niyyar yi game da waɗansu masu zargimmu a kan wai muna bin halin mutuntaka. 3 Ko da ya ke zaman mutuntaka mu ke yi, famammu ba na mutuntaka ba ne. 4 Don kuwa makamammu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe mukamai masu ƙarfi. 5 Muna ka da masu hujjoji cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu. 6 A shirye mu ke kuma mu hori kowane marar biyayya, muddar biyayyarku ta tabbata.

7 Ku dubi abin da ke bayyane mana! In dai wani ya amince shi na Almasihu ne, to, ya ƙara tunawa, wato kamar yadda ya ke shi na Almasihu ne, mu ma haka mu ke. 8 Ko da zan yi taƙama fiye da kima game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba zan kunyata ba. 9 Kada fa a ga kamar ina tsorata ku da wasiƙu ne. 10 Don wasu na cewa, “Wasiƙunsa masu ratsa jiki ne, masu ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi ba shi da kwarjini, maganarsa kuma ba ta da wani tasiri.” 11 Irin mutanen nan dai su fahinci cewa, abin da mu ke faɗa a cikin wasiƙa sa’ad da ba ma nan, shi mu ke aikatawa sa’ad da mu ke nan. 12 Wane mu mu daidaita kammu, ko mu gwada kammu da waɗansu masu yabon kansu! Ashe waɗannan mutane masu auna kansu da juna, su ke kuma neman bambancin tsakaninsu da juna, ba su da basira.

13 Amma dai ba za mu yi taƙama fiye da yadda ya kamata ba, sai dai mu tsaya kan iyakad da Allah ya yanke mana, wadda ta game har da ku. 14 Ai ba mu wuce gona da iri ba, kamar ba a hannummu ku ke ba, domin mu ne muka fara shan nisa, muka je gare ku da Bisharar Almasihu. 15 Taƙamarmu ba fiye da yadda ya kamata ta ke ba, ba ta kuma shafi aikin wasu ba. Amma muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa karuwa, ta haka kuma fagen aikimmu a cikinku ya riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske, 16 har ma mu samu mu yi Bishara a ƙasashen da ke gaba da ku, ba tare da wata taƙama da aikin da wani ya riga ya yi a fagensa ba. 17 Amma “Duk mai yin taƙama, ya yi taƙama da Ubangiji.” 18 Ai ba mai yabon kansa a ke yarda da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.

11

Ku Mai da Hankali da Makircin Shaiɗan

Da ma a ce ku jure ’yar wautata. Ku dai yi haƙuri da ni! 2 Ina kishi a kanku saboda Allah. Gama na bashe ku ga Almasihu, don im miƙa ku kamar amarya tsattsarka ga makaɗaicin mijinta. 3 Amma ina tsoro kada ya zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗad da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu. 4 Don in wani ya zo yana wa’azin wani Yesu daban da wanda muka yi wa’azi, ko kuma in kun sami wani ruhu daban da Ruhun da kuka samu, ko wata bishara daban da wadda kuka yi na’am da ita, ashe har kuna saurin miƙa wuya ga irinsu ke nan! 5 A ganina ban kasa mafifitan manzarmin nan da komai ba. 6 Ko da ya ke ni bami ne wajen yin magana, wajen sani kam ba haka ba ne, mun kuwa bayyana wannan sarai ta kowace hanya cikin dukkan sha’animmu da ku.

7 Ashe laifi na yi da na kankan da kaina don a ɗaukaka ku, wato saboda na yi muku Bisharar Allah a kyauta? 8 Wasu ikiliziyai sun mammatsa sun ba ni kuɗi don in samu in yi muku aiki. 9 Kuma sa’ad da na ke wurinku na ke zaman rashi, ban nauyaya wa kowa ba, domin ’Yan’uwan da suka zo daga Makidoniya su ne suka biya mini bukata. Saboda haka na ƙi nauyaya muku ta kowace hanya, ba kuwa zan nauyaya muku ba. 10 Albarkacin gaskiyar Almasihu da ke tare da ni, ba mai hana ni taƙaman nan tawa a lardin Akaya. 11 To dom me? Don ba na ƙauharku ne? Allah dai ya san ina ƙaunarku.

12 Abin da kuwa na ke yi, shi zan riƙa yi, don in yashe gindin mutanen nan da ke alwashi, suna nema mu daidaita da su. 13 Irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, mayaudaran ma’aikata, suna da’awar cewa su manzannin Almasihu ne. 14 Ba abin mamaki ba ne kuwa, domin ko Shaiɗan ma da kansa ya kan yi da’awar cewa shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka ba abin mamaki ba ne im bayinsa ma sun yi da’awar cewa su bayi ne ua aikin gaskiya. Abin da suka shuka, shi za su girba.

16 Ina sake faɗa, kada wani ya zaci ni wawa ne. In kuwa kun zaci haka na ke, to, ku je ni wawan ne, don ni ma in samu in taɓa ’yar taƙama kaɗan. 17 Abin nan da na ke faɗa fa, ba bisa umarnin Ubangiji na ke faɗa ba, sai dai magana ce irin ta wawa, wadda ya ke yi gabagaɗi, yana alwashi; 18 da ya ke mutane da yawa suna alwashi a kan al’amarin duniya kawai, ni ma zan yi. 19 Ai ku kam hikimarku bar ta kai ga jure wa wawaye da murna! 20 Don in wani ya sa ku bauta, ku kan jure masa, ko ya yi muku ƙwace, ko ya more ku, ko ya nuna muka isa, ko kuwa ya mare ku. 21 Mu kam saboda raunimmu, wane mu da yin haka!

Bulus ya Ambaci Wahalolin da ya Sha

Amma ta ko yaya wani ke ƙarfin-halin yin alwashi—ina magana a kan ni wawa ne fa! —to, ni ma sai in yi. 22 In su lbramiyawa ne, ni ma haka. In su Bani Isra’ila ne, ni ma haka. In su zunyar Ibrahim ne, ni ma haka. 23 In su bayin Almasihu ne, ni na fi su ma—ina magana kamar ruɗaɗde ne fa! —ai na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan ɗauri; na sha duka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. 24 Sau biyar Yahudawa ke mini bulala arba’in ɗaya babu-babu. 25 San uku a ke shauɗa min tsumagu, sau ɗaya bar an jajjefe ni da dutse. San uku jirgi na rugurgujewa ina ciki, na kwana na wuni ruwan bahar na tafiya da ni. 26 Na yi tafifiya da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yam-fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun sauran al’umma, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a bahar, na kuma sha hatsarin ’Yan’uwa na ƙarya. 27 Na sha fama, na sha wuya, na sha hana idona barci, na sha yunwa da ƙishirwa, sau da yawa na ke hana kaina abinci, na sha sanyi da huntanci. 28 Ban da wasu abubuwa daban kuma, kowace rana ina matse da matsananciyar kula saboda dukkan ikiliziyai. 29 Wanene ya raunana, ban ji abin a jika ba? Wanene laifi ya kama, ban ji zafin abin ba?

30 Im ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da ke nuna raunanata. 31 Allahn Ubangiji Yesu, kuma Ubansa, wanda yabo ya tabbata a gare shi bar abada, ya san ba ƙarya na ke yi ba. 32 A Dimashƙu gwamnan da ke ƙarƙashhin Sarki Aritas ya tsare ƙofofin birnin Dimashƙu don ya kama ni, 33 amma sai aka zura ni a cikin babban kwando ta tagar ganuwa, na kuɓuce masa.

12

An yi wa Bulus Wahayi iri-iri

An tilasta mini ne in yi taƙama, ko da ya ke ba za ta amfane ni da komai ba. Amma zan ci gaba da batun wahayi da buɗi iri-iri da Ubangiji ya. yi mini. 2 Na san wani mutun wanda yau shekara goma sha huɗu ke nan, aka fyauce shi zuwa Sama ta uku bisa ikon Almasihu—ko ta jika, ko ba ta jika ba, ban sani ba, Allah ne masani. 3 Na kuma san mutumin nan an fyauce shi zuwa Firdausi—ko ta jika, ko ba ta jika ba, ban sani ba, Allah ne masani— 4 ya kuma ji wasu maganganu, waɗanda ba dama a faɗa, irin ma waɗanda bil’adam ba shi da izinin faɗa. 5 Zan yi taƙama da mutumin nan kam, amma ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai ko da raunanata. 6 Ko da zan so yin taƙama ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda ya ke ganina, ko yadda ya ke jin maganata. 7 Kuma don kada kaina ya kumbura saboda mafifitan buɗi iri-iri da aka yi mini, sai aka gama ni da wata azaba a jika, wadda ta zame mini kaya, jakaɗan Shaiɗan, don ya riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura. 8 Sau uku na ke roƙon Ubangiji kan wannan abu ya rabu da ni, 9 amma sai ya ce da ni, “Alherina yā isam maka, don ƙarfina ta raunana a ke ganin kammalatasa.” Saboda haka sai ma in ƙara yin taƙama da raunanata, don ƙarfin Almasihu ya zauna tattare da ni. 10 Saboda haka ina murna da raunanata, da cim-mutuncin da a ke mini, da shan-wuya, da shan-tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa’ad da na ke rarrauna, a sa’an nan ne na ke da ƙarfi.

11 Na yi wauta kam, amma ku ne kuka tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini. Don ba inda na kasa waɗannan mafifitan manzanni, ko da ya ke ni ba komai ba ne. 12 An gudanad da tabbatattun alamomin Manzo a cikinku ta matuƙar jimiri, da alamomi da abubuwan al’ajabi da mu’ujizai. 13 Ta wace hanya aka rage muku a kan sauran ikiliziyai? Ko kuwa don dai ni ban nauyaya muku ba? To, ku yafe mini wannan laifi!

Bulus da Titus sun Nuna Rashin Sonkai

14 Ga shi na yi shirin zuwa wurinku, zuwa na uku, ba kuwa zan nauyaya muku ba, don ba abinku na ke nema ba, ku na ke nema. Don ba yara ne da ɗaukan nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukan nauyin yaran. 15 Ni kam zan kashe dukkan abin hannuna da dukkan zarafina da matuƙar farinciki saboda ranku. In na ƙara ƙaunarku, ashe sai a rage ƙaunata? 16 To, a ce ban nauyaya muku ba ɗin, ashe sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara! 17 Na cuce ku ne ta kan wani daga cikin waɗanda na aiko gare ku? 18 Na roƙi Titus ya je, na kuma aiko Ɗan’uwan nan tare da shi. To, Titus ya cuce ku ne? Ashe ba Ruhu ɗaya ke tafi da mu ba, ni da shi? Ba kuma hanya ɗaya mu ke bi ba?

19 Ashe tun dā tsammani ku ke yi muna kawo hanzarimmu gare ku ne? A’a, tsakani da Allah mu ke magana, muna na Almasihu, wannan kuwa duk don inganta ku ne, ya ku ƙaunatattu. 20 Ina tsoro kada watakila in na zo in same ku ba yadda na ke so ba, ku kuma ku gan ni ba yadda ku ke so ba, ko ma a tarad da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da yanke, da sara, da girmankai, da tashin-hankali. 21 Ina tsoro kada in na sake zuwa, Allahna ya ƙasƙanta ni a gabanku, in kuma yi baƙinciki saboda waɗansu da yawa da suka ɗau zunubi dā ba su kuwa tuba da aikinsu na lalata ba, da fasikancinsu, da fajircinsu da suka aikata.

13

Wannan shi ne zai zama zuwana na uku gare ku. Lalle ne kuwa a tabbatad da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku. 2 Na gargaɗi waɗanda suka ɗau zunubi dā, da kuma saura duka, yanzu kuma da ba na nan ina yi musu gargaɗi, kamar yadda na yi sa’ad da na ke nan a zuwana na biyu, cewa in na sake zuwa ba zan sauƙake musu ba. 3 In dai nema ku ke yi ku tabbata cewa da izinin Almasihu na ke magana, to, ai shi ba mai lakolako da ku ba ne, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku. 4 Ko da ya ke an gicjye shi ne yana rarrauna, duk da haka a raye ya ke ta ikon Allah. Mu ma raunana ne kamarsa, amma game da al’amuranku da za mu zartar, a raye mu ke tare da shi, ta ikon Allah.

Ku Riƙa Gwada Kanku

5 Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna riƙe da Bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe ba ku tabbata cewa Almasihu na game da ku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin! 6 Muna fata ku gane cewa mu ba mu kasa ba. 7 Amma muna roƙon Allah kada ku yi wani mugun abu, ba wai don mu mu zama kamar mun ci gwajin kawai ba, sai dai don ku yi abin da ke daidai, ko da ya ke za ku ga kamar mun kasa. 8 Domin ba dama mu saɓa wa Gaskiya, sai dai mu bi bayan Gaskiyar. 9 Don farinciki mu ke yi im muna raunana, ku kuwa kuna ƙarfafa. Addu’armu ita ce ku kammala. 10 Ina rubuta wannan ne sa’ad da ba na tare da ku, don sa’ad da na zo, kada ya zame mini tilas in yi muku tsanani game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.

11 Daga ƙarshe kuma, ’Yan’uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, kuna zaman amana, Allah Mai haddasa ƙauna da aminci kuwa zai kasance tare da ku. 12 Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba. 13 Dukkan tsarkaka na gaishe ku.

14 Alherin Ubangiji Yesu Almasjhu, da ƙaunar Allah, da tarayya da Ruhu Tsattsarka su tabbata a gare ku duka.


WASIƘAR BULUS
ZUWA GA
GALATIYAWA

1

Daga Bulus, Manzo, ba kuwa manzon mutum ba, ba kuma ta kan wani mutum ba sai dai ta kan Yesu Almasihu, da Allah Uba, wanda ya tashe shi daga matattu, 2 da kuma dukkan ’Yan’uwa da ke tare da ni, zuwa ga ikiliziyan ƙasar Galatiya.

3 Alheri da aminci na Allah Uba su tabbata a gare ku, da na Ubangijimmu Yesu Almasihu, 4 wanda ya ba da kansa saboda zunubammu, don ya cece mu daga mugun zamanin nan, bisa nufin Allahmmu, kuma Ubammu. 5 Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.

Kowa ya yi Wata Bishara Daban yă Zama La’ananne

6 Na yi mamaki yadda nandanan ku ke ƙaurace wa wanda ya kira ku bisa alherin Almasihu, har kuna komawa wata baƙuwar bishara, 7 alhali kuwa babu wata bishara daban, sai dai akwai wasu da ke ta da hankalinku, suna son jirkitad da Bisharar Almasihu. 8 Amma ko mu, ko kuma wani mala’ika daga Sama, wani zai yi muku wata bishara daban da wadda muka yi muku, to, yă zama la’ananne! 9 Kamar yadda muka faɗa da, haka yanzu ma na ke sake faɗa, cewa kowa ya yi muku wata bishara daban da wadda kuka karɓa, to, yă zama la’ananne!

10 To, wato ni son mutane na ke nema ne, ko kuwa na Allah? Ko kuwa ƙoƙari na ke yi im faranta wa mutane? Da har yanzu mutane na ke faranta wa, ai da ban zama bawan Almasihu ba.

Daga Bakin Yesu, Bulus ya Karɓi Bishara

11 Ina so in sanad da ku. ’Yan’uwa, cewa Bisharan nan da na sanar ba ta ɗan’adam ba ce. 12 Don ba daga wurin mutun na samo ta ba, ba kuma koya mini ita aka yi ba, sai dai ta bayyanar Yesu Almasihu a gare ni ne na same ta. 13 Kun dai ji irin zamana na dā cikin addinin Yahudanci, yadda na riƙa tsananta wa ikiliziyar Allah ƙwarai da gaske, har ina ta watsa ta; 14 yadda kuma cikin addinin Yahudanci har na tsere wa yawancin tsararrakina cikin mutanemmu, na himmantu ƙwarai da gaske ga bin al’adun kakannimmu. 15 Amma sa’ad da shi wannan da ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa rahamarsa, 16 ya ji daɗin bayyana Ɗansa a gare ni, don in sanad da shi ga sauran al’umma, ban yi shawara da ɗan’adam ba, 17 ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama Manzanni ba, sai nandanan na je ƙasar Larabawa, sa’an nan na komo Dimashƙu.

18 Bayan shekara uku kuma sai na tafi Urushalima ganin Kefas, na kuwa kwana goma sha biyar a gunsa. 19 Amma ban ga ko ɗaya a dkin sauran Manzannin ba, sai dai Yakubu ɗan’uwan Ubangiji. 20 Abin nan da na ke rubuto muku fa, ba ƙarya na ke yi ba, tsakani da Allah na ke faɗa. 21 Daga baya kuma sai na tafi ƙasar Sham da ta Kilikiya. 22 Amma kuwa ikiliziyan Almasihu da ke ƙasar Yahudiya, ba su san ni ido da ido ba tukuna 23 Sai dai kawai sun ji an ce, “Wanda dā ya ke tsananta mana, ga shi yanzu yana sanad da Bangaskiyan nan da dā ya ke ta watsarwa!” 24 Sai suka ɗaukaka Allah saboda ni.

2

Bulus ya Je Urushalima da Barnabas

Kuma bayan shekara goma sha huɗu sai na sake komawa Urushalima tare da Barnabas, na kuma ɗauki Titus. 2 Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu Bisharad da na ke yi a cikin sauran al’umma, amma a keɓance a gaban wasu ƙusoshin ikiliziya, kada himmad da na ke yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce. 3 Kai, ko da Titus ma da ke tare da ni, ba a tilasta masa yin kaciya ba, ko da ya ke shi Bahelene ne. 4 Maganan nan ta tashi saboda ’Yan’uwan ƙaryan nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka sadado su yi ganganen ’yancimmu da mu ke da shi ta kan Almasihu Yesu, wai don su sa mu bauta. 5 Amma ko kaɗan ba mu sakam musu ba, ko da taƙi, don gaskiyar Bishara tă zaune muku. 6 Waɗanda kuma aka ɗauka a dā kan su wani abu ne (ko su wanene, ai duk ɗaya ne a guna, don Allah ba ya nuna wariya), ina dai gaya muku waɗannan da su ke wani abu ne a dā ba su ƙare ni da komai ba. 7 Amma da suka ga an amince min yi wa marasa kaciya Bishara, kamar yadda aka amince wa Bitrus ya yi wa masu kaciya Bishara, 8 (don shi da ya yi aiki a zuciyar Bitrus ya sa shi Manzo ga masu kaciya, shi ne kuma ya yi aiki a zuciyata, ya sa ni Manzo ga sauran al’umma), 9 sai Yakubu da Kefas da Yohana, su da ke shahararrun ginshiƙan ikiliziya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnabas, hannu biyu-biyu, don mu mu je wurin sauran al’umma, su kuwa gun masu kaciya. 10 Sai dai kuma suna so mu tuna da gajiyayyu, wannan kuwa dā ma ina da himmar yi ƙwarai.

Bulus ya Tsawata wa Bitrus a Sarari

11 Amma da Kefas ya zo Antakiya, sai na musa masa a idonsa don laifinsa a fili ya ke. 12 Don kafin wasu su zo daga wurin Yakubu, ya kan ci abinci da sauran al’umma. Amma da suka zo, sai ya janye jiki ya ware kansa, yana tsoron ɗarikar masu kaciyan nan. 13 Haka ma sauran Yahudawa masu bi suka nuna fuska biyu kamarsa, ko da Barnabas ma sai da suka ciwo kansa da munafuncinsu. 14 Amma da na ga dai ba sa bin gaskiyar Bishara sosai, sai na ce da Kefas a gaban idon kowa, “Kai da ka ke Bayahude, in ka bi al’adar sauran al’umma ba ta Yahudawa ba, yaya za ka tilasta wa sauran al’umma su bi al’adar Yahudawa?

Samun Karɓuwa ga Allah sai ta Bin Yesu Kadai

15 “Mu da aka haifa Yahudawa, ba sauran al’umma masu zunubi ba, 16 da ya ke mun san cewa mutum ba ya samun karɓuwa ga Allah ta bin Shari’ar Musa, sai dai ta gaskatawa da Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, don mu sami karɓuwa ga Allah ta bangaskiya ga Almasihu, ba ta bin Shari’ar Musa ba, don ba ɗan’adan ɗin da zai sami karɓuwa ga Allah ta bin Shari’ar Musa. 17 In kuwa ya zamana, sa’ad da mu ke neman karɓuwa ga Allah ta kan Almasihu, an tarar har mu kammu ma masu zunubi ne, wato ashe Almasihu ke sa mu ɗaukar zunubi ke nan? A’a, ko kusa! 18 Amma in na sake ginin abin da dā na rushe, na tabbata mai laifi ke nan. 19 Don ni, ta kan Shari’ar Musa na samu na rabu da ita, don in yi zaman Allah. 20 An giciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma ke raye ba, Almasihu ne ke raye a jikina. Rayuwan nan kuma da na ke yi ta mutuntaka, rayuwa ce ta bangaskiya ga ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, bar ya ba da kansa domina. 21 Ba na tozarta rahamar Allah. Don da ta bin Shari’ar Musa a ke samun kar6uwa ga Allah, ashe da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”

3

Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ɗauke hankalinku? Ku da aka bayyana muku Yesu Almasihu giciyayye sosai da sosai a gaban idanunku. 2 Abu ɗaya kaɗai zan tambaye ku. Kun sami Ruhu Tsattsarka saboda bin Shari’ar Musa ne, ko kuwa saboda gaskatawa da maganad da kuka ji? 3 Ashe rashin azancinku bar ya kai haka? Da kuka fara da Rulm Tsattsarka, ashe yanzu kuma da al’amarin burin-zuciya za ku ƙarasa? 4 Ashe a banza kuka sha wuya iri-iri? In dai har a banzan ne? 5 Wato, shi da ke yi muku baiwar Ruhu Tsattsarka, ya ke kuma yin mu’ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari’ar Musa ne ya ke yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganad da kuka ji?

Bangaskiya ita ce Hanyar Samun Karɓuwa ga Allah

6 Haka ma Ibrahim “ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma aka ɗaukam masa ita a kan samun karɓuwa ga Allah.” 7 Wato kun ga ashe masu bangaskiya su ne ’ya’yan Ibrahim. 8 A cikin Nassi kuwa an hango cewa Allah zai karɓi sauran al’umma ta bangaskiya, wato dā ma can an yi wa Ibrahim Bishara cewa, “Ta kanka za a yi wa dukkan al’ummai albarka.” 9 To, ashe masu bangaskiya su ne aka yi wa albarka, game da Ibrahim mai bangaskiyan nan.

10 Gama duk waɗanda ke dogara da bin Shari’ar Musa la’anannu ne, don a rubuce ya ke, cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da ke rubuce a cikin Littattafan Shari’a ba, la’ananne ne.” 11 To, a fili ya ke, cewa ba mai samun karɓuwa ga Allah ta bin Shari’ar Musa, don “Mai samun karɓuwa ga Allah ta bangaskiya, zai rayu.” 12 Shari’ar Musa kuwa ba ta dangana ga bangaskiya ba, don ta ce, “Wanda ya aikata ta, ta gare ta ne zai rayu.” 13 Almasihu ya fanso mu daga la’anan nan ta Shari’ar Musa, da ya zama abin la’ana saboda mu. Don a rubuce ya ke, cewa, “Duk wanda aka kafe a jin itace, la’ananne ne.” 14 An yi wannan kuwa don albarkan nan da aka yi wa Ibrahim ta saukam ma sauran al’umma ta kan Almasihu Yesu, mu kuma ta bangaskiya mu sami Ruhu Tsattsarkan nan da aka yi alkawari :

15 To, ’Yan’uwa, bari in yi muku misali. Ko alkawari na mutun ne kawai, in dai an riga an tabbatad da shi, ba mai soke shi, ba kuma mai ƙara wani abu a kai. 16 To, alkawaran nan an yi wa Ibrahim ne, da kuma wani a cikin zuriyatasa. Ba a ce, “Da zuriya” ba, kamar suna da yawa. A’a, sai dai ɗaya kawai, aka ce, “Wani a cikin zuriyarka,” wato Almasihu. 17 Ga abin da na ke nufi. Shari’an nan ta Musa, wadda ta zo shekara arbaminya da talatin daga baya, ba ta shafe alkawarin nan da Allah ya tabbatar tun tuni ba, har da za ta wofinta shi. 18 Don da gadon nan ta hanyar Shari’ar Musa ya ke samuwa, ashe da ba sauran ya zama na alkawarin ke nan. Amma Allah ya bai wa Ibrahim ta alkawari ne

Manufar Shari’ar Musa

19 To, mecece manufar Shari’ar Musa ke nan? Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyan nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin; an kuma ba da ita ta kan mala’iku ne, kuma ta hannun mai sadarwa. 20 To, ai duk inda mai sadarwa ya ke, ya mma fiye da sashi guda. Amma Allah ɗaya ya ke.

21 Wato Shari’ar Musa ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A’a, ko kusa! Don da am ba da wata shari’a mai iya ba da rai madawwami, da sai a sami karɓuwa ga Allah ta bin shari’an nan. 22 Amma Nassi ya tamake kowa cikin zunubi, don albarkad da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.

23 Tun kafin bangaskiya ta zo, cikin ƙuƙumin Shari’ar Musa mu ke a tarnaƙe, sai lokacin da bangaskiya ta bayyana. 24 Ashe kuwa Shari’ar Musa ita ce makabuliyarmu, tā kai mu ga Almasihu, don mu sami karɓuwa ga Allah ta bangaskiya. 25 Yanzu kuwa da bangaskiyar ta zo, ba sauran zamammu a hannun wata makabuliya. 26 Don dukkanku ’ya’yan Allah ne, ta bangaskiya ga Almasihu Yesu. 27 Duk ɗakwacin ku da aka yi wa babtisma ga mallakar Almasihu, kun ɗau halin Almasihu ke nan. 28 Ba sauran cewa Bayahude ko na sauran al’umma, ko da ko bawa, ko mace ko namiji. Ai dukkanku ɗaya ku ke, na Almasihu Yesu. 29 In kuwa ku na Almasihu ne, ashe ku zuriyar Ibrahim ne, kuma magada ne bisa alkawarin nan.

4

Yadda a ke Zama ’Ya’yan Allah

Ina nufin cewa, magaji, muddin yana yaro, bai fi bawa ba, ko da ya ke shi ke da mallakar dukkan komai. 2 A hannun makabuli da wakili ya ke har zuwa ranad da ubansa ya sanya. 3 Haka ya ke gare mu, wato, sa’ad da mu ke kamar yara, a cikin ƙuƙumin ka’idodin farko na dabi’a mu ke. 4 Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, kuma haifaffe cikin tafarkin Shari’ar Musa, 5 don ya fanso waɗanda ke ƙarƙashin Shari’ar Musa, a mai da mu matsayin ’ya’yan Allah. 6 Tun da ya ke ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko Ruhun Ɗansa cikin zukatammu, yana kira, “Ya Abba! Uba!” 7 Don haka, kai ba bawa ba ne kuma, da ne. Da ya ke da ne kuma, to, magaji ne ta ikon Allah.

8 Dā da ba ku san Allah ba, kuna bauta wa waɗansu gumaka, waɗanda ga ainihi ba a bakin komai su ke ba. 9 Amma yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sake komawa kan raunanan ka’idodin farko marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu? 10 Ga shi al’adun ranaku da watanni da lokatai da shekaru ba sa wuce ku! 11 Kai, amma kun ba ni tsoro, kada ya zamana na yi wahala a kanku a banza!

12 Ina roƙonku, ya ku ’Yan’uwana, ku zama kamar yadda na ke, don ni ma na zama kamar yadda ku ke. Ba ku taɓa yi mini wani laifi ba. 13 Kun dai sani a dalilin rashin lafiyata ne na yi muku Bishara a zuwana na fari. 14 Kuma ko da ya ke rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna min raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na’am da ni kamar wani mala’ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa. 15 To, ina daɗin nan da kuka ji game da ni? Don na shaide ku a kan lalle da mai yiwuwa ne da kun ƙwaƙule idanunku kun ba ni! 16 Ashe wato na zama abokin gabanku ne don na gaya muku gaskiya? 17 Wadannan suna habahaba da ku, amma ba da kyakkyawar niyya ba. Niyyarsu su farraƙa ku da mu, don su ina ku yi habahaba da su. 18 Ai in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutun, ba wai sai ina tare da ku kaɗai ba. 19 Ya ku ’ya’yana ƙanana, ina sake shan wahalar naƙudarku har Almasihu ya siffantu a zuciyarku! 20 Ina ma a ce ina tare da ku yanzu in karya harshe! Gama na ruɗe kan sha’aninku.

’Ya’yan Ibrahim—Ɗan Kuyanga da Ɗan ’Ya

21 Ku gaya mini, ku da ke son Shari’ar Musa ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Shari’ar ne? 22 Don a rubuce ya ke, cewa Ibrahim na da ’ya’ya biyu maza, ɗaya ɗan kuyanga, ɗaya kuma ɗan ’ya. 23 ɗan kuyangan nan an haife shi ne ta nufin mutun, ɗan ’yar kuwa ta hanyar alkawari. 24 Wannan kuwa duk don ishara ne, wato matan nan a kan alkawarai biyu su ke. Ɗaya tushensa Dutsen Sina, mai haifuwar bayi, wato Hajaratu ke nan. 25 To ai Hajaratu Dutsen Sina ne a ƙasar Larabawa. Ita ce kwatancin Urushalima ta yanzu, don ita da ’ya’yanta duk a cikin bauta su ke. 26 Amma Urushalima ta Sama ai ’ya ce, ita ce kuma uwarmu, 27 Don a rubuce ya ke, cewa,

“Ki yi farinciki, ya ke juya da ba kya haifuwa,
Ki ɗauki sowa, ke da ba kya naƙuda,
Don yasasshiya ta fi mai miji yawan ’ya’ya.”

28 To, ’Yan’uwa, mu ma ’ya’yan alkawari ne kamar Isiyaku. 29 Kamar yadda dā shi da aka haifa ta nufin mutun ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu Tsattsarka, haka yanzu ma ya ke. 30 Amma me Nassi ya cc? “Ka kori kuyangar da danta, don ko kaɗan ɗan kuyangar ba zai ci gado tare da ɗan ’ya ba.” 31 Saboda haka ’Yan’uwa, mu ba ’ya’yan kuyanga ba ne, na ’ya ne.

5

Kaciya ba a Bakin Komai ta ke ba

Almasihu ya ’yanta mu, ’yantawar gaske. Don haka sai ku tsaya tsaiwar daka, kada ku sake sarkafewa cikin ƙuƙumin bauta.

2 To, ni Bulus, ina gaya muku, in kuna yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba zai amfane ku da komai ba ke nan. 3 Ina sake tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari’ar Musa. 4 Ku da ke neman karɓuwa ga Allah ta bin Shari’ar Musa, kun katse daga Almasihu ke nan, kun taɓe daga rahamar Allah. 5 Gama albarkacin Ruhu Tsattsarka mu ke dokin cikar sazuciyan nan tamu ta samun karɓuwa ga Allah saboda bangaskiya. 6 In ana na Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin komai su ke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.

7 Da ai kuna cin gaba sosai. Wanene ya hana ku bin Gaskiya? 8 Wannan rarrashin da a ke muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. 9 Ai ɗan yisti kaɗan shi ke game dukkan curin burodi. 10 Na dai amince da ku game da al’amarin Ubangiji, ba za ku bi wani ra’ayi daban da nawa ba. Wannan da ke ta da hankalinku kuwa zai sha hukunci, ko shi wanene. 11 Amma ’Yan’uwa, in da har yanzu wa’azin yin kaciya na ke yi, to, dom me har yanzu a ke tsananta mini? In da haka ne, ashe an kau da takaicin da giciyen Almasihu ke sawa ke nan! 12 Ina ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su fiɗiye kansu!

Ka Ƙaunaci Ɗan’uwanka Kamar Kanka

13 Ya ku ’Yan’uwa, don ’yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da ’yancin nan naku hujjar biye wa burin-zuciya, sai dai ku bauta wa juna cikin ƙauna. 14 Don duk Shari’ar Musa an ƙunshe ta ne a ƙauli guda, wato, “Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.” 15 Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.

16 Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu Tsattsarka, kuma ba za ku biye wa burin-zuciya ba. 17 Don burin-zuciya gāba ya ke yi da Ruhu Tsattsarka, Ruhu Tsattsarka kuma na gāba da burin-zuciya. Waɗannan biyu gāba su ke yi da juna, bar ba kwa iya yin abin da ku ke so. 18 In Ruhu Tsattsarka ne ke tafi da ku, ashe Shari’ar Musa ba ta iko da ku ke nan.

Aikin Burin-zuciya

19 Aikin burin-zuciya a fili ya ke, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci, 20 da bautar gumaka, da sihiri, da gaba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya, 21 da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakad da ku kamar yadda na faɗakad da ku a dā cewa masu yin irin waɗannan abubuwa ba za su sami gddo a cikin Mulkin Allah ba.

Albarkar Ruhu Tsattsarka

22 Albarkar Ruhu Tsattsarka kuwa ita ce ƙauna, da farinciki, da aminci, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da amana, 23 da sanyin-hali da kuma kamun-kai. Masu yin irin waɗannan abubuwa ba dama shari’a ta kama su. 24 Waɗanda kuwa su ke su na Almasihu Yesu ne sun giciye burin-zuciya da miyagun sha’awace-sha’awace iri-iri.

25 In dai rayuwar tamu ta Ruhu Tsattsarka ce, to, sai mu tafi da al’amurammu da ikon Ruhu Tsattsarka. 26 Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.

6

Ku Komo da Mai Laifi Hanya

Ya ku ’Yan’uwa, in an kama mutun farat yana cikin yin laifi, ku da Ruhu Tsattsarka ke tafi da ku, sai ku komo da shi hanya cikin sanyin-hali, kowa na kula da kansa kada shi ma ya burmu. 2 Ku ɗau wahalar juna, ta haka za ku cika umarnin Almasihu. 3 Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba komai ba ne, ya ruɗi kansa ke nan. 4 Kowa yā auna aikinsa ya gani, sannan ne zai iya takama da mukaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba, 5 Lalle kowa ya ji da kayansa.

6 Duk wanda aka koya wa Maganar Allah, su ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwan. 7 Kada fa a yaudare ku, ai ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutun ya shuka, shi zai girba. 8 Wanda ya yi shuka a gonar burin-zuciya, ta burin-zuciyatasa zai girbi halaka. Wanda ya yi shuka a gonar Ruhu Tsattsarka kuwa, rai madawwami zai girba, albarkacin Ruhu Tsattsarka. 9 Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, im ba mu karai ba. 10 To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda ke jama’ar masu ba da gaskiya ba.

Taƙamata ta Giciyen Almasihu Kaɗai

11 Ku dubi irin rubutu gwada-gwada da na ke muku da hannuna! 12 To, mutanen nan masu son tilasta muku yin kaciya, masu so a ga kamar ibada su ke yi, suna yi ne kawai don kada su sha wuya saboda giciyen Almasihu. 13 Ai ko waɗanda aka yi wa kaciya ma ba sa kiyaye Shari’ar Musa. Sonsu ne a yi muku kaciya, don su yi alwashi da ku a kan an yi muku kaciya. 14 Amma ni ko kusa ba zan yi taƙama ba, sai dai game da giciyen Ubangijimmu Yesu Almasihu, wanda albarkacin mutuwarsa a kan giciye ne na ya da sha’anin duniya, duniya kuma ta ya da sha’anina. 15 Kaciya da rashin kaciya ba a bakin komai su ke ba, sai dai sabuwar halitta ita ce wani abu. 16 Aminci da rahama su tabbata ga duk masu bin ka’idan nan, wato Bani Israilan gaske na Allah.

17 Nan gaba kada kowa ya ƙara damuna, domin a jikina ina da tabbai masu nuna cewa ni bawan Ubangiji Yesu ne.

18 Alherin Ubangijimmu Yesu Almasihu yd tabbata a zukatanku, ’Yan’uwa. Amin.


WASIƘAR BULUS
ZUWA GA
AFISAWA

1

Daga Bulus, Manzon Almasihn Yesu cikin yardar Allah, zuwa ga tsarkakan da ke Afisa, amintattu cikin al’amarin Almasihu Yesu.

2 Alheri da aminci na Allah Ubammu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Allah Ya Zaɓe mu Tun Fil’azal

3 Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijimmu Yesu Almasihu, kuma Ubansa, wanda ya yi mana albarka da kowace albarkar Ruhu Tsattsarka a mukaman Sama ta kan Almasihu, 4 don kuwa ya zaɓe mu ta kan Almasihu tun ba a halicci duniya ba, mu zama tsarkaka, marasa aibu a gabansa. 5 Ya ƙaddara mu ga zama ’ya’yansa cikin ƙauna ta kan Yesu Almasihu, bisa nufinsa na alheri, 6 don mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake ta kan Ƙaunataccensa. 7 Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifuffukammu, bisa yalwar alherin Allah, 8 wanda ya yi mana falala da matuƙar hikima da basira. 9 Don har ya sanasshe mu zuzzurfan al’amarin nufinsa bisa kyakkyawan nufinsa da ya bayyana game da Almasihu. 10 Duk wannan kuwa shiri ne, don a cikar lokaci a harhaɗa dukkan abubuwa ta kan Almasihu, wato, abubuwan da ke Sama da abubuwan da ke ƙasa.

Sannin Ruhu Tsattsarka Tabbatar Ɗaukaka ne

11 Ta kansa ne aka maishe mu abin gadon Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa nufin wannan da ke zartad da dukkan abubuwa bisa ƙudura da irada, 12 don mu da muka fara sa zuciya ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa. 13 Ta kansa ne ku kuma da kuka ji Maganar Gaskiya, wato Bisharar cetonku, kuka kuma ba da gaskiya gare shi, aka tabbatad da ku nasa ne da Ruhu Tsattsarka da aka yi alkawari. 14 Shi ne kuwa tabbatarwar gadommu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma don yabon ɗaukakarsa ne.

15 Saboda haka da ya ke na ji labarin bangaskiyarku ga Ubangiji Yesu, da kuma ƙaunarku ga dukkan tsarkaka, 16 ban fasa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa’ad da na ke muku addu’a, 17 da nufin cewa Allah na Ubangijimmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku ruhu mai hikima da buɗi ga saninsa, 18 a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, don ku san ko mecece sazuciyan nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mecece yalwar gadonsa mai ɗaukaka game da tsarkaka, 19 da kuma ko menene girman ikonsa marar misaltuwa da ya ke zartarwa a gare mu, mu masu ba da gaskiya, wato zartarwar ƙarfin ikon nan nasa, 20 wanda ya zartar ga Almasihu sa’ad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama a hannunsa na dama a muƙaman Sama, 21 can birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, kuma birbishin kowane sunan da za a sa, ba wai a duniyan nan kawai ba, har a Lahira ma. 22 Kuma Allah ya kallafa komai ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba shi shugabancin dukkan sha’anin ikiliziya, 23 wadda ita ce jikinsa da ya cika da falalarsa, shi wannan da ke cika dukkan abubuwa da falalarsa.

2

Ta Alheri aka Cece mu

Ku kuma yā raya ku sa’ad da ku ke matattu ta laifuffukanku da zunubanku, 2 waɗanda dā ku ke ciki, kuna biye wa alamarin duniyan nan, kuna bin Sarkin masu iko a sararin sama, wato iskan nan da ke zuga zuciyar kangararru a yanzu. 3 Dukkammu da mun zauna a cikinsu, muna biye wa son-zuciya, muna aikata abin da jiki da zuciya ke buri, har ma muna zaman ababan azabar Allah ga ɗabi’a kamar sauran ’yan’adan. 4 Amma Allah da ya ke mai yalwar rahama ne, saboda matsananciyar ƙaunad da ya ke mana, 5 ko a sa’ad da mu ke matattu ma ta laifuffukammu, sai ya rayad da mu tare da Almasihu, (ta alheri an cece ku), 6 ya kuma tashe mu tare da shi, har ya ba mu wurin zama tare da shi a muƙaman Sama ta kan Almasihu Yesu. 7 Allah ya yi wannan kuwa don a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa maras misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta kan Almasihu. Yesu. 8 Don ta alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya; wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah, 9 ba kuwa saboda aikin lada ba, kada wani ya yi alfahari. 10 Ai mu aikin hannunsa ne, an sake halittarmu ta kan Almasihu Yesu musamman don mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar irana tun da fari mu yi.

Almasihii ya Mai da mu Iyali Ɗaya

11 Saboda haka ku tuna da kam ku sauran al’umma ne bisa dabi’a, waɗanda a ke ce da su masu kaciyan nan kuwa, su kan ce da ku marasa kaciya, ga shi kuwa yin hannu ce; 12 ku kuma tuna a lokacin nan rabe ku ke da Almasihu, bare ne kuma ga Bani Isra’ila, kuma baki ne ga alkawaran nan da Allah ya yi, marasa sa zuciya, kuma marasa Allah a duniya. 13 Amma yanzu, haɗe da Almasihu, ku da dā ku ke can nesa, an kawo ku kusa ta jinin Almasihu. 14 Don Almasihu shi ne amincimmu, shi wandi ya mai da Yahudawa da sauran al’umma abu ɗaya, wato ya rushe katangan nan da ta raba su kan gāba. 15 Har ya soke Shari’an nan mai umarni da dokoki, ta ba da jikinsa, don ta gare shi yă halicci sabon mutun guda daga mutanen nan biyu, ta haka yă ƙulla aminci, 16 yă kuma sada su duka biyu da Allah, suna jiki ɗaya ta giciye, ta haka yă kashe gābar. 17 Ya kuma zo ya yi muku albishirin aminci, ku da ke nesa, ya kuma yi wa waɗanda ke kusa. 18 Don ta gare shi ne dukammu biyu muka sami isa gun Uba ta Ruhu Tsattsarka guda. 19 Wato ashe ku ba baƙi ba ne kuma, ko kawa bare, ai ku zumai ne na tsarkaka, kuma iyalin Allah, 20 waɗanda aka gina bisa harsashin. Manzanni da masu yin faɗin Maganar Allah, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne babban dutsen harsashin, 21 wanda aka haɗa dukkan tsarin ginin ta kansa, yana kuma tashi ya zama mazauni tsattsarka, keɓaɓɓe ga Ubangiji. 22 Cikinsa ne ku kuma aka gine ku, ku zama mazaunin Allah ta Ruhu Tsattsarka.

3

An Sanad da Bulus Zuzzurfan Al’amari

Don haka ni Bulus, fursuna saboda Almasihu Yesu don amfanin ku sauran al’umma, 2 a ce kun ji labarin mai da ni mai hidimar alherin Allah da aka yi mini baiwa saboda ku, 3 wato, yadda aka sanad da ni zuzzurfan al’amarin Ubangiji ta wahayi, kamar yadda na riga na rubuta a takaice. 4 Yayin da kuka karanta wannan, za ku iya gane basirata kan zuzzurfan al’amarin Almasihu, 5 wanda a zamanin dā ba a sanad da ’yan’adam ba, kamar yadda yanzu aka bayyana wa Manzanninsa tsarkaka da masu yin faɗin Maganar Allah, ta Ruhu Tsattsarka, 6 wato, yadda ta Bishara sauran al’umma ke abokan gado da mu, gaɓoɓin jiki guda, kuma abokan tarayya ga alkawaran nan ta kan Almasihu Yesu.

7 An kuwa sa ni mai hidima a wannan Bishara, bisa baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa. 8 Ko da ya ke ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa sauran al’umma Bishara kan yalwar Almasihu maras ƙididdiguwa, 9 in kuma bayyana wa dukkan mutane tsarin zuzzurfan al’amarin nan da shekara da shekaru ke ɓoye gun Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa. 10 An yi wannan ne kuwa don a yanzu a sanad da hikimar Allah iri-iri ga manyan mala’iku da masu iko a muƙaman Sama, ta hanyar ikiliziya. 11 Wannan kuwa bisa dawwamammen nufin nan ne da Allah ya zartar ta kan Almasihu Yesu Ubangijimmu. 12 Ta gare shi mu ke da amincewa da ƙarfin-gwiwar isa ga Allah, ta bangaskiyarmu gare shi. 13 Saboda haka ina roƙonku kada ku karai ganin wahalad da na ke sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

14 Saboda haka na ke durƙusa wa Uban, 15 shi da ke sa wa kowace kabila suna a Sama da ƙasa, 16 ina addu’a ya yi muku baiwa bisa yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta Ruhunsa Tsattsarka, 17 har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta bangaskiyarku, don ƙauna ta kafu da gindinta sosai a zukatanku, 18 har ku sami kaifin basira tare da dukkan tsarkaka, ku fahinci ko menene fāɗin ƙaunar Almasihu, da tsawonta, da zacinta, da kuma zurfinta, 19 ku kuma san ƙaunad da Almasihu ke yi mana, wadda ta fi gaban sani, don a cika ku da dukkan falala ta Allah.

20 Daukaka tā tabbata ga wannan da ke iya aikatawa fiye da dukkan abin da za mu roƙa, ko za mu zata nesa, wato aikatawa ta ƙarfin ikonsa da ke aiki a zuciyarmu. 21 Ɗaukaka tā tabbata a gare shi a cikin ikiliziya ta kan Almasihu Yesu, har ya zuwa dukkan zamanai bar abada abadin. Amin.

4

Ku Cancanci Kiran da aka yi muku

Don haka, ni fursuna saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku, 2 da matuƙar ƙanƙan-da-kai, da sanyin-hali, da haƙuri, kuna jure wa juna saboda ƙauna, 3 kuna himmantuwa ga riƙon haɗa-kai na Ruhu Tsattsarka wajen ƙulla aminci da juna. 4 Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku kan sazuciyan nan guda, wadda ta ke game da kiran nan. 5 Ubangiji guda ne, bangaskiya guda, kuma babtisma guda. 6 Allah ɗaya, kuma Ubammu duka, wanda ya ke bisa kowa, ke ratsa kowa, kuma ke cikin kowa. 7 Amma am ba kowannemmu alheri gwargwadon baiwar Almasihu. 8 Saboda haka Nassi ya ce,

“Sa’ad da ya hau Sama ya ja rundunar kamammu,
Ya kuma yi wa’yan’adam baiwa.”

9 (Wato, da aka ce “ya hau” ɗin, me aka fahinta, im ba cewa dā ya sauka can ƙasa ba? 10 Shi wanda ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau can birbishin dukkan sammai, don ya cika komai da Zatinsa.) 11 Ya kuma yi wa wasu baiwa su zama manzanni, wasu masu yin faɗin Maganar Allah, wasu masu yin Bishara, wasu makiyaya masu koyad da Maganar Allah, 12 don tsarkaka su samu su iya aikin hidimar ikiliziya don inganta jikin Almasihu, 13 har mu duka mu riski haɗa-kan nan na bangaskiya ga Ɗan Allah, da kuma saninsa, mu kai muƙamin cikakken mutun, mu kuma kai ga munzilin nan na falalar Almasihu. 14 An yi wannan kuwa don kada mu sake zama kamar yara, waɗanda a ke jujjuyawa, iskar kowace ibada tana ɗaukar hankalinsu bisa wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu. 15 Maimakon haka sai mu faɗi gaskiya cikin ƙauna, muna girma ta kansa ta kowace hanya, wato Almasihu, shi da ya ke Shugabammu. 16 Don ta gare shi ne dukkan jiki ke game, kuma ke ƙulle, ta kowace gaɓar da ke tafarkin rayuwarsa, ya ke kuma girma game da aikin kowace gaɓa sosai, yana kuma ƙara girma, yana ingantuwa cikin halin ƙauna.

17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma gargaɗi tsakani da Ubangiji, cewa kada ku sake zama irin na sauran al’umma, masu azancin banza da wofi. 18 Duhun zuciya gare su, rabe su ke da rai madawwami na Allah, sabili da jahilcin da ke gare su, saboda taurin-kansu. 19 Zuciyatasu ta yi kanta, sun dulmuya cikin fajirci, sun ɗokanta ido rufe ga yin kowane irin aikin lalata. 20 Ba haka kuka koyi al’amarin Almasihn ba, 21 in da a ce kun saurare shi, kuma an koya muku ta gare shi ne, wato yadda gaskiya ta ke ta Yesu ce. 22 Ku ya da halinku na dā wanda dā ku ke ciki, wanda ya ke kuma ɓatacce saboda jarabar zamba, 23 ku kuma sabunta ra’ayin hankalinku, 24 ku ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa yanayin Allah cikin haƙiƙanin gaskiya da tsarkaka.

Ku Watsad da Miyagun Ayyuka

25 Saboda haka sai ku watsad da ƙarya, kowa yă riƙa faɗin gaskiya ga ɗan’uwansa, gama mu gaɓoɓin juna ne. 26 In kun fusata, kada ku ɗau zunubi, kada ma fushinku ya kai faɗuwar rana, 27 kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa. 28 Kada ɓarawo ya ƙara yin sata, maimakon haka sai ya ran da gaba yana aikin gaskiya da hannunsa, har da zai sami abin da zai ba gajiyayyu. 29 Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganad da ta kyautu don ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, don ta sanya alheri ga masu jinta. 30 Kuma ku kula, kada fa ku ɓata wa Ruhu Tsattsarka na Allah rai, wanda ta kansa ne aka tabbatad da ku nasa ne bar ya zuwa ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin-rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da yanke da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta kan Almasihu.

5

Ku yi Zaman Ƙauna

Saboda haka sai ku zama masu koyi da Allah, kan ku ƙaunatattun ’ya’yansa ne. 2 Ku yi zaman ƙauna yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa domimmu, baiko mai ƙanshi, kuma hadaya ga Allah.

3 Kada ma a ko ambaci fasikanci da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, don kuwa bai dace da tsarkaka ba. 4 Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don ba su kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah. 5 Kun dai tabbata cewa ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da ke da gado cikin mulkin Almasihu, kuma na Allah. 6 Kada wani ya hilace ku da maganar wofi, gama sabili da waɗannan zunubai ne azabar Allah ke sauka kan kangararru. 7 Saboda haka kada ku cuɗanya da su, 8 domin dā ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne ta kan Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske, 9 don haske shi ke haifar duk abin da ke nagari, ke daidai, kuma ke na gaske. 10 Ku dai tabbata abin da zai faranta wa Ubangiji. 11 Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su. 12 Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da su ke yi a asirce. 13 Abin da duk haske ya tona sai ya ganu, abin da duk ya ganu kuwa, ya haskaka. 14 Saboda haka aka ce,

“Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu,
Almasihu kuwa zai haskaka ka.”

15 Saboda haka sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima. 16 Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne. 17 Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahinci abin da ke nufin Ubangiji. 18 Kuma kada ku bugu da giya, hanyar masha’a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu Tsattsarka, 19 kuna yi wa juna waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna waƙar ɗaukaka Ubangij zuciya-ɗaya. 20 Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijimmu Yesu Almasihu kan komenene.

Hakkin Aure

21 Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu. 22 Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazajenku, Ubangiji ke nan ku ke yi wa. 23 Don miji shi ne shugaban matatasa, kamar yadda Almasihu ke Shugaban ikiliziya, wato jikinsa, shi kansa kuma shi ne macecin jikin. 24 Kamar yadda ikiliziya ke bin Almasihu, haka kuma mata su bi mazansu ta kowane hali. 25 Ku maza, ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci ikiliziya, bar ya ba da kansa dominta, 26 don ya keɓe ta a tsarkake, bayan ya tsarkake ta da wankan babtisma ta Maganar Allah, 27 don shi da kansa yăba kansa ikiliziya cikin ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu. 28 Ta haka ya wajaba maza su ƙaunaci matansu, jikinsu ke nan su ke yi wa. Ai wanda ya ƙaunaci matatasa, ya ƙaunaci kansa ke nan. 29 Don ba wanda ya taɓa kin jikinsa, sai dai ya rene shi, ya yi tattalinsa, kamar yadda Almasihu ke yi wa ikiliziya, 30 don mu gaɓoɓin jikinsa ne. 31 “Saboda haka ne mutun sai ya bar uwatasa da ubansa, ya tsaya ga matatasa, su biyu su zama jiki guda.” 32 Wannan zuzzurfan al’amari muhimmi ne, ni kuwa ina nufin Almasihu ne da ikiliziya. 33 Duk da haka dai, sai kowane ɗayanku ya ƙaunaci matatasa, kamar kansa, ita matar kuwa ta ladabta wa mijinta.

6

Hakkin ’Ya’ya da na Iyayensu

Ku ’ya’ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, don wannan shi ne daidai. 2 Wannan shi ne umarnin farko mai alkawari, cewa, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don al’amarinka ya kyautatu, ka kuma yi tsawon rai a duniya.” 4 Ku ubanni, kada ku sa ’ya’yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya da kuma gargaɗi ta banyar Ubangiji.

Hakkin Bayi da na Iyayengijinsa

5 Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengiiinku na duniya, cikin halin bangirma tare da matsananciyar kula da zuciya-ɗaya, Almasihu ku ke yi wa ke nan; 6 ba aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane, sai dai kan bayin Almasihu masu aikata abin da Allah ke so, da zuciya-ɗaya, 7 kuna bauta da kyakkyawar niyya kan Ubangiji ku ke yi wa, ba mutane ba. 8 Kun san cewa kowane alherin da mutun ya yi, ko shi da ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi. 9 Ku iyayengiji, ku ma ku yi musu haka, ku bar tsorata su, ku san cewa shi wanda ke Ubangijinsu da ku duka yana Sama, shi kuwa ba ya zaɓe.

Kayan Ɗamara na Allah

10 A ƙarshe kuma ku ƙarfafa ga Ubangiji, kuma ga ƙarfin ikonsa. 11 Ku yi ɗamara da dukkan kayan ɗamara na Allah, don ku iya dage wa kissoshin Iblis. 12 Ai famammu ba da ’yanadam mu ke yi ba, da masarautu da masu iko na shaidanu ne, da masu ragamar mulkin duniya a wannan zamani mai duhu, da kuma rundunonin shaiɗanu a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku ɗauki dukkan kayan ɗamara na Allah, don ku iya dagewa a muguwar ranan nan, kuma bayan kun ga bayan komai duka, ku dage. 14 Saboda haka ku tsaya tsaiwar daka, gaskiya ta zama abar ɗamararku, kumakuminku kuma aikin gaskiya, 15 kuna kuma sāye da takalman na shirin nan da Bisharar aminci ke haddasawa. 16 Ban da waɗannan kuma ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kare dukkan kiban wutar Mugun nan, ku kashe. 17 Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu Tsattsarka, wato Maganar Allah, 18 kullun kullun kuna addu’a da roƙo ta ikon Ruhu Tsattsarka ba fasawa. Kan wannan manufa ku tsaya kan kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukkan tsarkaka addu’a. 19 Ni ma ku yi mini, don in sami baiwar yin furuci, in yi magana gabagaɗi, in sanad da zuzzurfan al’amarin Bishara, 20 wadda ni jakadanta ne, ɗaurarre. Ku dai yi mini addu’a, duk sa’ad da na ke yin Bisharar im bayyana ta gabagaɗi, kamar yadda ya kamata in yi.

21 Yanzu kuwa don ku ma ku san lafiyata, da kuma halin da na ke ciki, ga Tikikus, ƙaunataccen Ɗan’uwa, amintaccen mai hidima cikin al’amarin Ubangiji, zai sanad da ku komai. 22 Na aiko shi gare ku musamman don ku san yadda mu ke, ya kuma ƙarfafa muku gwiwa.

23 Amincin Allah Uba da na Ubangiii Yesu Almasihu su tabbata ga ’Yan’uwa, tare da ƙauna game da bangaskiya. 24 Alheri yl tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijimmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa.


WASIƘAR BULUS
ZUWA GA
FILIBIYAWA

Daga Bulus da Timotawas, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukkan tsarkaka cikin al’amarin Almasihu Yesu waɗanda ke Filibi, tare da masu kula da ikiliziya da kuma masu hidimarta.

2 Alheri da aminci na Allah Ubammu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Gode wa Allah saboda Filibiyawa

3 Ina gode Allahna duk sa’ad da na ke tunawa da ku, 4 kullum kuwa a kowace addu’a da na ke muku duka, da farinciki na ke yi. 5 Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa Bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu. 6 Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki gare ku, zai ƙarasa shi har ya zuwa ranar Yesu Almasihu. 7 Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, don kuna zuciyata, don dukkanku abokan tarayya ne da ni cikin alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da ba da hanzarina game da Bishara, da kuma tabbatad da ita. 8 Don Allah shi ne mashaidina a kan yadda na ke begenku duka, da irin ƙaunad da Almasihu Yesu ke yi. 9 Addu’ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka game da sani da matuƙar basira, 10 don ku zaɓi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu, 11 kuna da cikakken sakamakon aikin gaskiya da ke samuwa ta kan Yesu Almasihu, wannan kuwa duk don ɗaukakar Allah ne da yabonsa.

Daurin Bulas sanadin yaɗa Bishara ne

12 ’Yan’uwa, ina so ku san cewa abin nan da ya auku gare ni, sai ma ya yi amfani wajen yaɗa Bishara, 13 har dai ya zama sananne, ga dukkan sojan faɗa da sauran jama’a, cewa daurina saboda Almasihu ne. 14 Har ma yawancin ’Yan’uwa gwiwarsu ta ƙarfafa cikin al’amarin Ubangiji saboda ɗaurina, kuma sun ƙara fitowa gabagaɗi su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.

15 Lalle wasu suna wa’azin Almasihu saboda hassada da gasa, amma wasu kam saboda kyakkyawar niyya ne. 16 Na yayyau ɗin suna yi ne kan ƙauna, sun san cewa an sa ni nan ne don ba da hanzarina game da Bishara. 17 Na farkon kuwa suna sanad da Almasihu saboda sonkai ne, ba tsaf da rai ba, sonsu su wahal da ni cikin ɗaurina. 18 Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana sanad da Almasihu; na kuma yi farinciki da haka.

19 I, zan yi farinciki mana. Don na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, albarkacin addu’arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu. 20 Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, cewa ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin-hali matuƙa yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko, ta rayuwata, ko ta mutuwata. 21 Don ni, a gare ni, manufar rayuwata Almasihu ce, mutuwa kuwa riba ce. 22 In ya zamanto rayuwa zan yi, to, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa ta ɗauka. 23 Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, don wannan shi ne ya fi nesa. 24 Amma in wanzu, shi ya fi wajabci saboda ku. 25 Na tabbata haka ne, na kuwa san zan wanzu in zauna tare da ku duka, don ku ci gaba, bangaskiyarku na sa ku farinciki, 26 ku kuma sami ƙwaƙƙwaran dalilin yin taƙama da Almasihu ta kaina, saboda sake komowata gare ku.

Zaman da ya Cancanci Bishara

27 Sai dai ku yi zaman da ya cancanci Bisharar Almasihu, don ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku cewa kun tsaya tsaiwar daka, nufinku ɗaya, ra’ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyad da Bishara ke sawa, 28 ba kwa kuwa jin tsoron magabtanku sam-sam. Wannan kuwa ishara ce gare su ta halakarsu, ku kuwa ta kuɓutarku, isharar kuwa daga Allah ta ke. 29 Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa, 30 kuna shan fama irin nawa wanda kuka gani, wanda ku ke ji na ke sha har yanzu.

2

In akwai ƙarfafa gwiwa ta kan Almasihu, in dai da ƙarfin rinjaye na ƙauna, in har da tarayyarku ga Ruhu Tsattsarka, da soyayyarku da kuma tausayinku, 2 to, albarkacinsu ku cikasa farincikina da zamanku lafiya da juna, kuna ƙaunar juna, nufinku ɗaya, ra’ayinku ɗaya. 3 Kada ku yi komai da sonkai ko girmankai, sai dai da ƙanƙan-da-kai, kowa na mai da ɗan’uwansa fiye da shi. 4 Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ɗan’uwansa ma.

Ku Ɗauki Halin Almasihu Yesu

5 Ku ɗauki halin Almasihu Yesu, 6 wanda, ko da ya ke yanayin Allah ya ke, bai mai da daidaitakan nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba, 7 sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar yanayin bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan’adan. 8 Da ya bayyana da siffar mutun, sai ya ƙasƙantad da kansa ta yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta kan giciye. 9 Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, kuma ya yi masa baiwa da sunan nan da ke birbishin kowane suna, 10 don dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a Sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa, 11 kowane harshe kuma yă yarda cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, don ɗaukaka Allah Uba.

12 Saboda haka ya ƙaunatattuna, kamar yadda kullum ku ke biyayya, haka yanzu kuma, ku yi ta yin aikin ceton nan naku cikin halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba wai sai ina nan kawai ba, bar ma fiye da haka im ba na nan. 13 Don Allah shi ne mai aiki a zukatanku ku nufi abin da ke kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.

Gunaguni da Gardama ba su Dace da Kirista ba

14 Komai za ku yi kada ku yi shi da gunaguni ko gardama, 15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai, ’ya’yan Allah marasa aibu a cikin zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda ku ke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya, 16 kuna riƙe da maganar rai madawwami kankan har a ranar bayyanar Almasihu in yi taƙama kan cewa himmata da famana ba a banza su ke ba. 17 Ko da za a zub da jinina a ƙara kan baiko da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farinciki, in kuma taya ku farinciki ku duka. 18 Haka ku ma, ya kamata ku yi farinciki, ku kuma taya ni farinciki.

19 Ina sa zuciya ga Ubangiji Yesu in aika muku da Timotawas da wuri, don ni ma in ƙarfafa da samun labarinku. 20 Ba ni da wani kamarsa, wanda zai tsananta kula da zamanku lafiya tsaf da rai. 21 Dukkaninsu sha’anin gabansu kawai su ke yi, ba na Yesu Almasihu ba. 22 Amma ai kun san darajar Timotawas, yadda muka yi bautar Bishara tare, kamar da da ubansa. 23 Shi ne na ke fata in aiko, da zarar na ga yadda al’amarina ke gudana. 24 Na kuma amince ga Ubangiii ni ma kaina ina zuwa ba da daɗewa ba.

25 Kafin nan, na ga lalle ne in aiko muku da Abafaroditas Ɗan’uwana, abokin aikina, kuma abokin famana, wanda kuka aiko ya yi mini dawainiya. 26 Don yana begenku ku duka, har ma ya damu ƙwarai don kun ji ba shi da lafiya. 27 Lalle ya yi rashin lafiya, har ya yi kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayinsa, ba kuwa shi kaɗai ba, har ni ma, don kada in yi baƙinciki kan baƙinciki. 28 Saboda haka na ɗokanta ƙwarai in turo shi don ku yi farincikin sake ganinsa, ni kuma in rage baƙincikina. 29 Don haka sai ku karɓe shi da matuƙar farinciki saboda Ubangiji, kuma ku girmama irin waɗannan mutane, 30 don ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa don ya ciƙasa dawainiyarku gare ni.

3

A ƙarshe kuma ’Yan’uwa, ku yi farinciki da Ubangiji. Sake rubuto muku waɗannan abubuwa bai gundure ni ba, ga shi kuwa don lafiyarku ne.

2 Ku yi hankali da karnukan nan! Ku yi hankali da miyagun ma’aikatan nan! Ku yi hankali da masu yankan gaɓan nan! 3 Don mu ne masu kaciyar ainihi, masu bauta wa Allah ta Ruhu Tsattsarka, masu taƙama da Almasihu Yesu, ba ma kuma amincewa da halin mutuntaka, 4 ko da ya ke ni ina iya amincewa da halin mutuntaka, in da ina so. In kuma akwai wanda ke tsammanin yana iya amincewa da halin mutuntaka, to, ni na fi shi. 5 An yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Bani Isra’ila ne, na kabilar Bunyamunu, Ba’ibraniye ɗan Ibraniyawa, bisa Shari’ar Musa kuwa ni Bafarisiye ne, 6 wajen himma kuwa mai tsananta wa ikiliziya ne ni, wajen aikin gaskiya kuwa bisa tafarkin Shari’ar Musa, marar abin zargi na ke.

Burina Almasihu ya zama nawa

7 Amma dai kowace irin riba na taɓa ci, na ɗauka a kan hasara ce saboda Almasihu. 8 Dahir na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar shinan da na ke yi wa Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari don Almasihu yă zama nawa, 9 a kuma same ni a haɗe da shi, ba ina mai samun karɓuwa ta ƙoƙarin kaina, ba, wanda ya danganta da bin Shari’ar Musa, sai dai samun karɓuwan nan da ke tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato samun karɓuwan nan da ke samuwa daga Allah, albarkacin bangaskiya; 10 don in san shi da ikon nan da tashinsa ke da shi, in yi tarayya da shi cikin shan-wuyarsa, in kuma zama kamarsa wajen mutuwatasa, 11 don ta ko ƙaƙa in kai ga tashin nan daga matattu.

12 Ba wai na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa wai na zama kammalalle ba, a’a, sai dai ina nacewa ne in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi. 13 Ya ’Yan’uwa, ban ɗauka a kan cewa na riga na riƙi abin ba, amma abu guda kam ina yi, ina mantawa da abin da ke baya, abin da ke gaba kuwa kamar na yi fiffike in kamo. 14 Ina nacewa gaba-gaba zuwa manufan nan, don in sami ladan kiran nan zuwa Sama da Allah ya yi mini ta kan Almasihu Yesu. 15 Saboda haka ɗakwacin waɗanda suka kammala a cikimmu, sai su bi wannan ra’ayi. In kuwa game da wani abu ra’ayinku ya sha bamban, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma. 16 Sai dai duk mukamin da muka kai, mu ci gaba da haka.

Magabtan Giciyen Almasihu

17 Ya ku ’Yan’uwa, ku yi koyi da ni dukkanku baki-ɗaya, ku kuma dubi waɗanda zamansu ke daidai da misalin da muka yi muku. 18 Domin da yawa waɗanda na sha gaya muku, yanzu kuma na ke gaya muku har da hawaye, suna zaune a kan su magabtan giciyen Almasihu ne. 19 Ƙarshensu halaka ne, allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu kan al’amuran duniya. 20 Mu kuwa ’Yam Mulkin Sama ne, daga can ne kuma mu ke ɗokin zuwan Maceci, Ubangiji Yesu Almasihu, 21 wanda zai canza jikin nan namu na ƙasƙanci, ya mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka, da ikon nan mai sa har ya iya tankwasa dukkan abubuwa gare shi.

4

Saboda haka ya ’Yan’uwana, ƙaunatattuna, waɗanda na ke bege, ku da ke abin farincikina kuma abin taƙamata, ku tsaya haka ga Ubangiji tsaiwar daka, ya ku ƙaunatattuna.

2 Na gargaɗi Afodiya, na kuma gargaɗi Sintiki, su yi zaman lafiya da juna kan su na Ubangiji ne. 3 Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni kan al’amarin Bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu ke rubuce cikin Littafin Rai Madawwami.

Kullum ku yi Farinciki da Ubangiji

4 Kullum ku yi farinciki da Ubangiji; har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farinciki. 5 Bari kowa ya san sanyin-halinku. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu da komai, sai dai a cikin kowane hali ku sanad da Allah bukatunku, ta yin addu’a da roƙo tare da gode wa Allah. 7 Ta haka amincin Allah, wanda ya fi gaban dukkan fahinta, zai tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

8 Daga ƙarshe kuma, ’Yan’uwa, komenene ya ke na gaskiya, komenene abin girmamawa, komenene daidai, komenene tsattsarka, komenene abin ƙauna, komenene ɗaɗɗadar magana, fin ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani. 9 Abin da kuka koya, kuma kuka yi na’am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah Mai haddasa aminci zai kasance tare da ku.

Filibiyawa Sun Yi Gudummawa

10 Na yi farinciki da Ubangiji ƙwarai da ya ke yanzu kamkularku gare ni ta farfaɗo; ko dā ma kuna kula da ni, dama ce ba ku samu ba. 11 Ba wai ina kukan rashi ba ne, don na koyi yadda zan zauna da wadar zuci cikin kowane irin hali na ke. 12 Na san yadda zan yi in yi zaman ƙunci, na kuma san yadda zan yi in yi zaman yalwa. A cikin kowane irin hali duka na horu da ƙoshi da yunwa, yalwa da jikkata. 13 Zan iya yin komai albarkacin wannan da ke ƙarfafa ni.

14 Amma kuwa kun kyauta da kuka taya ni cikin ƙuntatata. 15 Ku kuma Filibiyawa, ku kanku kun sani tun da aka fara yin Bishara, sa’ad da na bar ƙasar Makidoniya, ba wata ikiliziyad da ta yi tarayya da ni wajen hidimar bayarwa da karɓa, sai dai ku kaɗai. 16 Ko sa’ad da na ke Tasalonika ma kun aiko mini da taimako ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. 17 Ba wai don ina neman kyautarku ba ne, a’a, nemar muku amfani na ke yi, a ƙara a kan ribarku. 18 Am biya ni sarai, har an yi rara. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautad da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiko mai ƙanshi, mai karɓuwa, kuma mai faranta wa Allah. 19 Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da ke ga Almasihu Yesu. 20 Ɗaukaka tă tabbata ga Allahmmu kuma Ubammu har abada abadin. Amin.

21 Ku gai da kowane tsattsarka cikin al’amarin Almasihu Yesu. ’Yan’uwan da ke tare da ni suna gaishe ku. 22 Dukkan tsarkaka na gaishe ku, tun ba ma na fadar Kaisar ba.

23 Alherin Ubangiji Yesu. Almasihn yd tabbata a zukatanku.


WASIƘAR BULUS
ZUWA GA
KOLOSIYAWA

1

Daga Bulus, Manzon Almasihu. Yesu cikin yardar Allah, tare da Timotawas, Ɗan’uwammu, 2 zuwa ga tsarkaka da amintattun ’Yan’uwa cikin al’amarin Almasihu da ke Kolosi.

Alheri da amincin Allah Ubammu. su tabbata a gare ku.

Gode wa Allah saboda Kolosiyawa

3 Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijimmu Yesu Almasihu, duk sa’ad da mu ke muku addu’a, 4 saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunad da ku ke yi wa dukkan tsarkaka, 5 saboda sa zuciya ga abin da aka tanadar muku a Sama. Kun riga kun ji labarin wannan a Maganar Gaskiya, 6 wato Bisharad da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda ta ke yi a tsakaninku tun daga ranad da kuka ji, kuka kuma fahinci alherin Allah na hakika. 7 Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi ammintaccen mai hidima ne na Almasihm a madadimmu, 8 ya kuma sanasshe mu ƙaunad da ku ke yi ta kan Ruhu Tsattsarka.

9 Shi ya sa tun ran da muka ji labarin, ba mu fasa yi muku addu’a ba, muma roƙon a cika ku da sanin nufin Allah ga matuƙar hikima da fahinta na Ruhu Tsattsarka, 10 don ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, sanin Allah na ƙara ku. 11 Allah yă dai ƙarfafa ku da matuƙar ƙarfi bisa ƙarfin ɗaukakarsa, don ku jure matuƙa game da haƙuri da farinciki, 12 kuna gode wa Uba, wanda ya maishe mu mu isa samun rabo cikin gadon tsarkakan da ke cikin haske. 13 Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa, 14 wanda ta gare shi ne muka sami fansa, wato gafarar zunubammu.

Almasihu ne Surar Allah Marar Ganuwa

15 Shi ne surar Allah marar ganuwa, Magaji ne tun ba a halicci komai ba, 16 don ta gare shi ne aka halicci dukkan komai, abubuwan da ke Sama da abubuwan da ke ƙasa, masu ganuwa da marasa ganuwa, ko manyan mala’iku, ko masu mulki, ko masarautu, ko masu iko, wato dukkan abubuwa an halicce su ne ta kansa, kuma shi ne makomatasu. 17 Shi ne Ƙadimi kan komai, dukkan abubuwa shi ke riƙe da. su. 18 Shi ne Kai ga jikin nan, wato ikiliziya. Shi ne Tushe, Na Farko cikin masu tashi daga matattu, don ta kowane abu ya zama shi ne mafifici. 19 A gare shi dukkan cikar Allah ta tabbata, don Allah na farinciki da haka, 20 da nufin ta kansa Allah yă sada dukkan abubuwa da shi kansa, na ƙasa ko na Sama, yana ƙulla aminci ta jininsa na giciye.

21 Ku kuma waɗanda dā ke rabe da Allah, maƙiyansa a zuci, masu mugun aiki, 22 yanzu kuwa ya sada ku ta hanyar jikinsa na mutuntaka, wato ta sanadin mutuwarsa, don miƙa ku a tsarkake, marasa aibu, kuma marasa abin zargi a gabansa, 23 muddin dai kun nace ga bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata raurawa daga sazuciyan nan ta Bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa ɗakwacin dukkan talikan da ke duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.

Shan-wuyar Manzanni da Ƙoƙarinsu

24 To, yanzu ina farinciki a tsakiyar wuyad da na ke sha saboda ku, kuma a jikina ina ciƙasa abin da ya saura ga wahalad da aka aza mini saboda Almasihu a kan jikinsa, wato ikiliziya, 25 wadda na zama mai hidimarta bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, don in sanad da Maganar Allah sosai da sosai, 26 wato zuzzurfan al’amarin nan da ke ɓoye tun zamanai masu yawa, amma yanzu am bayyana shi ga tsarkakansa. 27 Su ne Allah ya so sanad da yadda irin yalwar ɗaukakar zuzzurfan al’amarin nan ta ke a cikin sauran al’umma, zuzzurfan al’amarin nan kuwa shi ne Almasihu game da ku, tabbatar ɗaukakad da za a bayyana mana. 28 Shi ne kuwa mu ke sanarwa, muna yi wa kowane mutun gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutun da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutun cikakke a game da Almasihu. 29 Saboda wannan maƙasudi na ke shan wahala, na ke fama da matuƙar himma, wadda ya ke sanya mini ta ƙarfin ikonsa.

2

Sanin Zuzzurfan Al’amarin Allah

To, ina so ku san irin yawan shan faman da na ke yi dominku, da. waɗanda ke Lawudikiya, da kuma. duk waɗanda ba su taɓa ganina ba. 2 Sona a ƙarfafa musu gwiwa, ƙauna na haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahinta tabbatacciya, da sanin zuzzurfan al’amarin nan na Allah, wato Almasihu, 3 wanda shi ne taska maɓoyar dukkan mafifitan hikima da sani. 4 Na faɗi wannan ne don kada kowa ya hilace ku da maganar yaudara. 5 Don ko da ya ke ga zahiri ba na nan, ai ruhuna na nan tare da ku, ina kuwa farincikin ganin kyakkyawan tsarinku da dagewarku kan bangaskiyarku ga Almasihu.

6 Da ya ke kun yi na’am da Almasihu. Yesu Ubangiji, to, sai ku tsaya gare shi, 7 kuna kafaffu, kuna ƙaruwa gare shi, kuna tsaye kan Bangaskiya tsaiwar daka, daidai yadda aka koya muku, kuna masu gode wa Allah koyaushe.

Cikar Zatin Allah ga Almasihu ta ke Tabbace

8 Ku lura kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa al’adar mutane kawai, wato bisa al’adun duniyan nan, ba bisa koyarwar Almasihu ba. 9 Don a gare shi ne dukkan cikar Zatin Allah ke tabbata a gudan jiki muraran. 10 Kuma a gare shi ne aka kammala ku, wanda ya ke shi ne Shugaban dukkan sarauta da iko. 11 A gare shi ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, wadda Almasihu ya yi muku ce, ta ya da halinku na ɗaukar zunubi. 12 An kuma binne ku tare da shi wajen babtisma, inda kuma aka ta da ku tare da shi saboda bangaskiyarku ga ikon Allah, wanda ya ta da shi daga matattu.

Allah ya Yafe mana ta kan Almasihu

13 Ku kuma da ku ke matattu ta laifuffukanku da rashin kaciyar zuci, Allah ya raya ku tare da shi, ya yafe mana dukkan laifuffukammu, 14 ya kuma yanke igiyan nan ta Shari’a da ta ɗaure mu da dokokinta, ya ɗauke ta, ya buge ta da ƙusa jikin giciyensa. 15 Ya yarɓad da masarautu da masu iko na shaidanu, ya ƙwace makamansu, har ya kunyata su a fili, da ya yi nasara a kansu a kan giciyen.

16 Saboda haka kada ku damu in wani ya zarge ku kan abin da ku ke ci, ko abin da ku ke sha, ko kuwa kan rashin kiyayewar wani idi, ko tsayawar wata, ko Asabar. 17 Waɗannan kam isharori ne kawai na abin da zai auku, amma Almasihu shi ne ainihinsu. 18 Kada ku yarda wani ya kaɗar muku da ladanku, ta bin ra’ayinsa ga ladabta wa mala’iku, kuna musu sujada. Ai irin wannan mutun karambani ya ke yi, wai an yi masa wahayi, yana huruwar banza ta ra’ayinsa na burin-zuciya, 19 bai kuwa manne wa Kan ba, wanda shi ne tafarkin rayuwar dukkan jikin, ya ke kuma haɗa shi ta gaɓoɓinsa da jijiyoyinsa, ya ke kuma ƙara girmansa da girman da Allah ke bayarwa.

20 In lalle kun yā da al’adun duniyan nan a sanadin mutuwar Almasihu, me ya sa ku ke zama kamar har yanzu ku na duniya ne? Dom me ku ke ba da kai ga dokokin da aka yi bisa umarnin ’yan-adan da koyarwarsu, 21 kamar su “Kar ka kama,” “Kar ka ɗanɗana,” “Kar ka taɓa”? 22 (wato ana nufin abubuwan da in an ci su su kan ruɓa duka). 23 Irin waɗannan dokoki kam lalle suna da’awar hikima ta wajen yin ibadad da aka ƙago, da ƙanƙan-da-kai da kuma wahal da jiki, amma ko ɗaya ba su da wani tasiri ga sauƙake burin-zuciya.

3

Almasihu Shi ne Rammu

To, da ya ke an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da ke Sama, inda Almasihu ya ke, a zaune a hannun dama na Allah. 2 Ku ƙwallafa ranku kan abubuwan da ke Sama, ba kan abubuwan da ke ƙasa ba. 3 Domin kun mutu, ranku kuwa a ɓoye ya ke a gun Almasihu game da Allah. 4 Sa’ad da Almasihu wanda ya ke shi ne rammu ya bayyana, sai ku ma ku bayyana tare da shi a wurin ɗaukaka.

5 Saboda haka sai ku kashe zukatanku ga sha’awace-sha’awacen duniya, wato fasikanci, aikin lalata, muguwar sha’awa, mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne. 6 Saboda waɗannan abubuwa ne azabar Allah ke sauka. 7 Dā kuna bin waɗannan sa’ad da su ke jiki gare ku. 8 Amma yanzu sai ku yā da duk waɗannan ma, wato fushi, da hasala, da ƙeta, da yanke, da alfasha. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da ya ke kun yā da halinku na dā da ayyukansa, 10 kun ɗau sabon halin nan da a ke sabuntawa ga sani bisa yanayin Mahaliccinsa. 11 A nan kam ba banyar bambanci tsakanin na sauran al’umma da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare ko baubawa, ko da da bawa, sai dai Almasihu shi ne komai, kuma shi ke ratsa kowa.

Halin da ya Kamaci Kirista

12 Saboda haka sai ku ɗau halin tausayi, da kirki, da da-kai, da sanyin-hali, da haƙuri, kan ku zaɓaɓɓun Allah ne, tsarkaka, ƙaunatattu, 13 kuna jure wa juna, kuma in wani na da miki a zuci game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma ku yafe. 14 Kuma fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala ke ƙulluwa a jikinta. 15 Kuma amincin Almasihu yă mallaki zuciyarku, don lalle ga haka aka kira ku kan kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah. 16 Maganar Almasihu tă kafu da gindinta sosai a zuciyarku, kuna koya wa juna, kuna yi wa jutia gargaɗi da matuƙar hikima ta yin waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma yi wa Allah waƙa, kuna gode masa a zuci. 17 Komai ku ke yi, game da magana ko aikatawa, ku yi komai da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta kansa.

18 Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace cikin al’amarin Ubangiji. 19 Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kuma kada ku yi musu kaushin-hali. 20 Ku ’ya’ya, ku yi wa iyayenku biyayya ta kowane hali, don haka Ubangiji ke so. 21 Ku ubanni, kada ku ƙuntata wa iya’yanku, don kada su karai. 22 Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda ke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane, sai dai da zuciya-ɗaya, kuna tsoron Ubangiji. 23 Komai za ku yi, ku yi shi da himma kan kuna bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba, 24 da ya ke kun san cewa Ubangiji zai ba ku gado sakamakonku. Ubangiji Almasihu ku ke bauta wa fa! 25 Mai mugun aiki kuwa za a saka masa da mugun aikin da ya yi, kuma babu wariya.

4

Ku iyayengiji kuma, ku riƙi bayinku da gaskiya da daidaitawa, da ya ke kun san ku ma kuna da Ubangiji a Sama.

2 Ku lazamci yin addu’a, kuna tsai da zuciyarku a kanta sosai, tare da gode wa Allah; 3 mu ma ku yi mana addu’a Allah ya buɗe mana hanyar yin Maganarsa, mu sanad da zuzzurfan al’amarin Almasihu, wanda saboda shi ne na ke ɗaure, 4 don im bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata im faɗa.

Zaman Masu bi cikin Marasa Bi

5 Ku tafi da al’amuranku da hikima cikin zamanku da marasa bi, kuna matuƙar amfani da lokaci. 6 Kullum maganarku ta zama tattausa, mai ratsa jiki, don ku san irin amsad da ta dace ku ba kowa.

7 Tikikus zai sanad da ku duk abin da na ke ciki. Shi ƙaunataccen Ɗan’uwa ne, amintaccen mai hidima, kuma abokin bautarmu cikin al’amarin Ubangiji. 8 Na aiko shi gare ku musamman don ku san yadda mu ke, yă kuma ƙarfafa muku gwiwa. 9 Ga kuma Unisimus nan tare da shi, amintaccen Ɗan’uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku ya ke. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.

10 Aristarkus abokin daurina na gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnabas. Shi ne aka riga aka ba ku umarni game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe sbi. 11 Yasuwa kuma da a ke kira Yustus na gaishe ku. Wato cikin abokan aikina ga Mulkin Allah waɗannan su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi, sun kuwa sanyaya mini zuciya. 12 Abafaras wanda ke ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, kullum yana yi muku addu’a da himma a kan ku tsaya tsaiwar daka, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah. 13 Na shaide shi kan lalle ya yi muku aiki ƙwarai da gaske, da kuma waɗanda ke Lawudikiya da na Hirafolis. 14 Luka, ƙaunataccen likitan nan, da Dimas suna gaishe ku. 15 A gayar mini da ’Yan’uwa na Lawudikiya, da kuma Nimfa da ikiliziyad da ke taruwa a gidanta. 16 Sa’ad da aka karanta wasiƙan nan a gabanku, ku sa a karanta ta kuma a gaban ikiliziyad da ke Lawudikiya, ku kuma ku karanta tasu, wato ta Lawudikiyawa. 17 Ku kuma faɗa wa Arkibus ya mai da hankali ya cika hidimad da Ubangiji ya sa shi.

18 Ni Bulus, ni na ke rubuta gaisuwan nan da hannuna. Ku tuna da ɗaurina. Alheri yׁ tabbata a gare ku.


WASIƘAR BULUS TA FARKO
ZUWA GA
TASALONIKAWA

1

Daga Bulus, da Silwanas, da Timotawas, zuwa ga ikiliziyar Tasalonikawa, wadda ke ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu.

Alheri da aminci su tabbata a gare ku.

Ayyukansu na Bangaskiya

2 Kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, koyaushe muna ambatonku cikin addu’armu, 3 ba ma fasa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahmmu kuma Ubammu, da faman da ku ke yi don ƙauna, da kuma sazuciyarku marar gushewa ga Ubangijimmu Yesu Almasihu. 4 Domin mun sani ’Yan’uwa, ƙaunatattun Allah, shi ya zaɓe ku; 5 domin Bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, har ma da iko, da Ruhu Tsattsarka, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku don ku amfana, 6 har kuka zama masu koyi da mu, da kuma Ubangiji, kuka kuma karɓi Maganar Allah game da farincikin da Ruhu Tsattsarka ke sawa, ko da ya ke ta jawo muku tsananin wahala. 7 Ku ma har kuka zama abin koyi ga dukkan masu ba da gaskiya a ƙasar Makidoniya da ta Akaya. 8 Don ta kanku ne aka baza Maganar Ubangiji, ba ma a cikin ƙasar Makidoniya da ta Akaya kaɗai ba, har ma a ko’ina bangaskiyarku ga Allah ta shahara, har ma ya zamana ba sai lalle mun faɗa ba. 9 Domin su da kansu ke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, don ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya, 10 ku kuma saurari komowar Ɗansa daga Sama, wanda ya tasa daga matattu, wato, Yesu, mai kuɓutad da mu daga azaban nan mai zuwa.

2

Wa’azin Manzanni

Ai ku da kanku kun sani ’Yan’uwa, cewa ziyartarku da muka yi, ba a banza ta ke ba. 2 Amma ko da ya ke da ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahmmu muka sanad da ku Bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama. 3 Ai gargaɗin da mu ke yi muku babu bauɗewa ko munafunci a ciki, balle yaudara, 4 sai dai kamar yadda Allah ya yarda da mu ya amince mana Bishara, haka mu ke sanad da ita, ba don mu faranta wa mutane ba, sai dai don mu faranta wa Allah, shi da ke jarraba zukatammu. 5 Yadda kuka sani, ba mu taɓa yin daɗin baki ba, ko raragefen kwaɗayi. Allah kuwa shi ne shaida. 6 Ba mu kuwa taɓa neman girma ga mutane ba, ko a gare ku, ko ga wasu, ko da ya ke da mun so, da mun mori ikon nan namu na Manzannin Almasihu. 7 Amma mun nuna taushin-hali a cikinku, kamar yadda mai goyo ke kula da goyanta. 8 Saboda kuma muna ƙaunarku ƙwarai da gaske ne ya sa mu ke jin daɗin ba da har rayukammu ma saboda ku, ba yi muku Bisharar Allah kaɗai ba, don kun shiga rammu da gaske.

9 Ya ku ’Yan’uwa, kuna iya tunawa da wahala da faman da muka sha, har muna aiki dare da rana, don kada mu nauyaya wa kowane ɗayanku duk sa’ad da mu ke yi muku Bisharar Allah. 10 Ku shaidu ne, haka kuma Allah, a kan irin halin tsarkaka, da gaskiya, da kuma rashin aibu da muka nuna muku, ku masu ba da gaskiya. 11 Don kun san yadda muka yi wa kowannenku gargaɗi kamar uba da ’ya’yansa ne, muna ƙarfafa muku gwiwa, muna ƙarfafa muku umarnin cewa 12 ku yi zaman da ya cancanci bautar Allah, wanda ke kiranku ga mulkinsa da ɗaukakarsa.

Tasalonikawa sun Sha Wuya

13 Saboda wannan ne kuma mu ke gode wa Allah ba fasawa, don sa’ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakimmu, ba ku karɓe ta a kan maganar mutun ce ba, sai dai a kan ainihin yadda ta ke, wato Maganar Allah, wadda ta ke aiki a zuciyarku, ku masu ba da gaskiya. 14 ’Yan’uwa, ku ne kuka zama masu koyi da ikiliziyan Allah da ke na Almasihu Yesu, waɗanda ke ƙasar Yahudiya; don ku ma kun sha wuya a hannun mutanen ƙasarku, kamar yadda ikiliziyan nan ma suka sha a hannun Yahudawa, 15 waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa, suka kuma kore mu; ba sa yin aikin da Allah ke so, kuma masu gaba ne da dukkan mutane, 16 suna hana mu yi wa sauran al’umma wa’azi, don kada su sami ceto. Ta haka kullum su ke cika mudun zunubansu. Amma fa azabar Allah tā saukam musu, matuƙar sauka.

17 Ya ku ’Yan’uwa, ko da ya ke mun yi kewarku saboda an raba mu ɗan lokaci kaɗan, duk da haka kuna cikin zukatammu, mun kuwa ƙara ɗokanta mu gan ku ido da ido, matuƙar ɗoki. 18 Mun dai yi niyyar zuwa wurinku—ni Bulus, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba—amma Shaiɗan ya hana. 19 Suwanene abin sazuciyarmu, da abin farincikimmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowatasa, im ba ku ba? 20 Ai ku ne abin taƙamarmu, da abin farincikimmu.

3

Zuwan Timotawas gare su

Saboda haka da muka ƙasa ɗaurewa, sai muka ga ya kyautu a bar mu a Atina mu kaɗai, 2 muka kuma aiki Timotawas Ɗan’uwammu, kuma bawan Allah cikin al’amarin Bisharar Almasihu, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa muku gwiwa a kan al’amarin bangaskiyarku, 3 don kada kowa ya raurawa a cikin tsananin wahalan nan. Ai ku kanku kun san an ƙaddaro mana haka. 4 Don dā ma sa’ad da mu ke tare, mun gaya muku tun da wuri, cewa za mu sha wahala. Haka kuwa ya auku, kamar yadda kuka sani. 5 Saboda haka ni ma da na kasa ɗaurewa, sai na aika in sami labarin bangaskiyarku, da fatan kada ya zamana Mai ruɗin nan ya riga ya ruɗe ku, famammu kuma yă zama banza.

6 Amma ga shi yanzu da Timotawas ya dawo daga wurinku, ya yi mana albishir a kan bangaskiyarku da ƙaunarku, da kuma yadda ku ke tunawa da mu da alheri koyaushe, bar kuna begen ganimmu, kamar yadda mu ma mu ke yi. 7 Saboda haka ’Yan’uwa, cikin dukkan wahala da ƙuncin da muka sha, an sanyaya mana zuciya game da ku, albarkacin bangaskiyarku. 8 Yanzu kam a raye mu ke, in dai kun tsaya ga Ubangiji tsaiwar daka. 9 Kai! wace irin godiya za mu yi wa Allah saboda ku, kan matuƙar farincikin da mu ke yi a gaban Allahmmu a dalilinku! 10 Dare da rana muna nacin addu’a ƙwarai mu sami ganinku ido da ido, mu kuma cikasa abin da ya gaza cikin bangaskiyarku.

11 Muna fata dai Allahmmu, kuma Ubammu shi kansa, da kuma Ubangijimmu Yesu, ya kai mu gare ku. 12 Ku kuma, Ubangiji ya sa ku ƙaru, ku kuma yalwata da ƙaunar juna da dukkan mutane, kamar yadda mu ke muku, 13 har ya tsai da zukatanku ku zama marasa abin zargi cikin tsarkaka a gaban Allahmmu, kuma Ubammu, a ranar komowar Ubangijimmu Yesu tare da dukkan tsarkakansa.

4

Sabuwar Rayuwa

Daga ƙarshe kuma ’Yan’uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurimmu, irin zaman da ya dace da ku ku faranta wa Allah, kamar yadda yanzu ma ku ke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske. 2 Domin kun san umarnin nan da muka yi muku da izinin Ubangiji Yesu. 3 Gama wannan shi ne nufin Allah, wato a keɓe ku a tsarkake, ku guji fasikanci, 4 kowannenku kuma ya san yadda zai auro matatasa cikin tsarkaka da martaba, 5 ba ta muguwar sha’awa ba, yadda sauran al’umma ke yi, waɗanda ba su san Allah ba. 6 A cikin wannan al’amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan’uwansa, don Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri. 7 Ai ba ga zaman rashin tsarkaka ne Allah ya kira mu ba, sai dai ga zaman tsarkaka. 8 Saboda haka kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutun ya ƙi ba, Allah ya ƙi, shi da ke ba ku Ruhunsa Tsattsarka.

9 Game da ƙaunar ’Yan’uwa kuma, ba sai lalle wani ya rubuto muku ba. Ai ku kanku Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna. 10 Hakika kuwa kuna ƙaunar dukkan ’Yan’uwa a duk ƙasar Makidoniya. Sai dai muna muku gargaɗi ’Yan’uwa, ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske, 11 kuna himmantuwa ga zaman lafiya, kuna kula da sha’anin gabanku kawai, kuna kuma aiki da gaɓarku, kamar yadda muka umarce ku, 12 don ku zama masu mutunci ga waɗanda ba masu bi ba, kada kuma ku rataya a jikin kowa.

Komowar Ubangiji Yesu

13 Amma ’Yan’uwa, ba ma so ku jahilta game da waɗanda suka yi barci, don kada ku yi baƙinciki, kamar yadda sauran ke yi, marasa sazuciya. 14 Tun da muka gaskata cewa Yesu ya mutu, ya kuwa sake tashi, haka kuma albarkacin Yesu, Allah zai kawo waɗanda suka yi barci su zo tare da shi. 15 Muna kuwa shaida muku bisa faɗar Ubangiji, cewa mu da muka wanzu, mu ke raye bar ya zuwa komowar Ubangiji, ko kaɗan ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16 Don Ubangiji kansa ma zai sauko daga Sama da kira mai ƙarfi na umarni, da muryar babban mala’ika, da kuma busar ƙahon Allah. Waɗanda suka mutu suna na Almasihu su ne za su fara tashi, 17 sa’an nan sai mu da muka wanzu, mu ke raye, sai a fyauce mu tare da su ta cikin gajimare, mu sadu da Ubangiji a sararin sama, sai kuma kullum mu kasance tare da Ubangiji. 18 Saboda haka sai ku ƙarfafa wa juna gwiwa da wannan magana.

5

Ku Zauna a faɗake

Amma ga zancen ainihin lokaci ko rana, ’Yan’uwa, ba sai lalle an rubuto muku komai ba. 2 Don ku da kanku kun sani sarai, cewa ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo cikin dare. 3 Lokacin da mutane ke cewa, “Muna zaman aminci da zaman lafiya,” wuf, sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda ke kama mace mai ciki, babu kuwa hanyar tsira. 4 Amma ai ba a cikin duhu ku ke ba, ’Yan’uwa, har da ranan nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo. 5 Don duk mutanen haske ku ke, kuma na rana. Mu ba na dare ko na duhu ba ne. 6 Ashe kuwa saboda haka kada mu yi barci yadda wasu ke yi, sai dai mu zauna a faɗake, cikin nutsuwa. 7 Don masu barci dad dare su ke barci, masu sha su bugu ma dad dare su ke sha su bugu. 8 Amma da ya ke mu na rana ne, sai mu nutsu, muna saye da kumakumin bangaskiya da ƙauna, sazuciya ga samun ceto kuma. ita ce kwalkwalimmu. 9 Allah bai ƙaddara mana shan azaba ba, sai dai samun ceto ta kan Ubangijimmu Yesu Almasihu, 10 wanda ya mutu saboda mu, don ko muna raye, ko muna barci, mu zama muna tare da shi. 11 Saboda haka sai ku ƙarfafa wa juna gwiwa, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda ku ke yi.

Ku riƙa yi wa juna aiki nagari

12 Amma muna roƙonku ’Yan’uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda ke shugabanninku cikin al’amarin Ubangiji, su ke kuma yi muku gargaɗi. 13 Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna. 14 Muna kuma yi muku gargaɗi ’Yan’uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa wa masu rarraunar zuciya gwiwa, ku taimaki marasa tsai da zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa. 15 Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace da yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane. 16 Ku riƙa yin farinciki kullum. 17 Ku riƙa yin addu’a ba fasawa. 18 Ku yi godiya ga Allah a cikin kowane hali, don shi ne nufin Allah game da ku ta kan Almasihu Yesu. 19 Kada ku danne maganar Ruhu Tsattsarka. 20 Kada ku raina faɗin Maganar Allah, 21 sai dai ku jarraba komai, ku riƙi abin da ke nagari kankan 22 Ku yi nesa da kowace irin mugunta.

23 Allah kansa, Mai haddasa aminci, yd keɓe ku a tsarkake sarai-sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku Ralau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijimmu Yesu Almasihu. 24 Wanda ke kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.

25 Ya ku ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.

26 Ku gai da dukkan ’Yan’uwa da tsattsarkar sumba.

27 Na gama ku da Ubangiji, a karanta wa dukkan ’Yan’uwa wasiƙan nan.

28 Alherin Ubangijimmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.


WASIƘAR BULUS TA BIYU
ZUWA GA
TASALONIKAWA

1

Daga Bulus, da Silwanas, da Timotawas, zuwa ga ikiliziyar Tasalonikawa, wadda ke ta Allah Ubammu da Ubangiii Yesu Almasihu.

2 Alheri da aminci na Allah Uba, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

3 Lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’Yan’uwa, haka kuwa ya kyautu, da ya ke bangaskiyarku haɓaka ta ke yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna karuwa ta ke yi. 4 Saboda haka mu kammu ma taƙama mu ke yi da ku a cikin ikiliziyan Allah, saboda jimirinku, da bangaskiyarku cikin yawan tsananin da ku ke sha, da ƙuncin da ku ke ciki.

Bayyanar Ubangiji Yesu don Shari’a

5 Wannan kuwa ita ce tabbatar hukuncin gaskiya na Allah, don a lasafta ku a cikin waɗanda suka cancanci zama a Mulkin Allah, wanda ku ke shan wuya dominsa, 6 don kuwa Allah ya ga daidai ne ya yi sakamakon ƙunci ga waɗanda su ke kuntata muku, 7 ya kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da a ke ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga. Sama tare da manya-manyan mala’ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa, 8 yana ta zabga sakamako kan waɗanda suka ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin Bisharar Ubangijimmu Yesu. 9 Za su sha hukuncin madawwamiyar halaka, suna ware da Zatin Ubangiji, da kuma maɗaukakin ikonsa, 10 wato a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al’ajabinsa a ranan nan, don kun gaskata shaidad da muka yi muku. 11 Da wannan maƙasudi kullum mu ke muku addu’a, Allahmmu yă sa ku cancanci kiransa, ya biya muku duk muradinku na yin nagarta, da aikin bangaskiya ta ƙarfin ikonsa, 12 don a ɗaukaka sunan Ubangijimmu Yesu ta kanku, ku kuma ta kansa, bisa alherin Allahmmu da na Ubangiji Yesu Almasihu.

2

To, game da komowar Ubangijimmu Yesu Almasihu, da kuma taruwarmu mu sadu da shi, muna roƙonku ’Yan’uwa, 2 kada ku yi saurin jijjiguwa a zukatanku, ko kuwa hankalinku ya tashi saboda faɗar wani ruhu, ko wani jawabi, ko wata wasiƙa a kan cewa daga gare mu su ke, wai ranar Ubangiji ti zo.

Sarkin Tawaye da Halakatasa

3 Kada ku yarda kowa ya yaudare ku ko ta halin ƙaƙa domin wannan ranar ba za ta zo ba sai an yi fanɗarewan nan, Sarkin tawaye kuma ya bayyana, wato halakakken nan. 4 Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gaba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda a ke yi wa ibada. Har ma ya kan zauna a Wuri isattsarka na Allah, yana cewa wai shi ne Allah. 5 Ashe ba ku tuna ba cewa na kan gaya muku haka tun muna tare? 6 To, yanzu dai kun san abin da ke tare shi, don kada ya bayyana kafin lokacinsa. 7 Ko yanzu ma tawayen nan am fara yinsa a munafunce, amma fa har kafin a ɗauke mai tarewan nan a yanzu ne kawai. 8 Sa’an nan ne fa Sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiii Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanatasa a ranar komowatasa. 9 Mai tawayen nan kuwa zai zo ne bisa ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al’ajabi, da alamomi, da aikin dabo na ƙarya iri-iri, 10 yana kuma yaudarar waɗanda ke hanyar halaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar Gaskiya har yadda za su sami ceto. 11 Saboda haka Allah zai sauko musu da wata babbar ɓatan basira don su gaskata ƙarya, 12 don duk a hukunta waɗanda suka ƙi gaskata Gaskiya, su ke kuma jin daɗin rashin gaskiya.

13 Ya ku ’Yan’uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin tun fil’azal Allah ya zaɓe ku ku sami ceto, ta keɓe ku a tsarkake da Ruhu Tsattsarka, da kuma gaskata Gaskiya da kuka yi. 14 Don wannan maƙasudi ya kira ku, ta Bishararmu, don ku sami ɗaukakar Ubangijimmu Yesu Almasihu. 15 Saboda haka ’Yan’uwa, sai ku tsaya tsaiwar daka, kuma ku riƙi ka’idodin da muka koya muku, ko da baka ko ta wasiƙa, kankan.

16 To, Ubangijimmu Yesu Almasihu da kansa, da kuma Allah Ubammu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamin ƙarfin-gwiwa da kyakkyawar sazuciya ta rahamarsa, 17 yă ƙarfafa muku gwiwa, ya kuma ƙarfafa ku ga yin kowane kyakkyawan aiki da magana.

3

Addu’a don Yada Maganar Ubangiii

Daga ƙarshe kuma ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a Maganar Ubangiji ta yi saurin yaɗo, ta sami ɗaukaka, kamar yadda ta samu a gare ku, 2 a kuma kuɓutad da mu daga fanɗararrun mutane, miyagu. Don ba duka ne ke da bangaskiya ba. 3 Amma Ubangiji mai alkawari ne, zai kuwa kafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan. 4 Mun kuma amince da ku game da al’amarin Ubangiji, cewa kuna bin umarnin da muka yi muku, za ku kuma riƙa bi. 5 Ubangiji yă tattaro hankalinku a kan ƙaunan nan ta Allah, da kuma jimirin nan na Almasihu.

Kowa Ya yi Aiki

6 To, ’Yan’uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijimmu Yesu Almasihu, ku fita sha’anin kowane Ɗan’uwa malalaci, wanda ba ya bin ka’idodin da kuka samu a wurimmu. 7 Ai ku kanku kun san yadda ya kamata ku yi koyi da mu, domin sa’ad da mu ke tare, ba mu nuna muku lalaci ba, 8 ba mu kuwa ci abincin kowa a banza ba, sai dai mun sha wahala da fama, muna aiki dare da rana, don kada mu nauyaya wa kowane ɗayanku. 9 Ba wai don ba mu da halaliya a wurinku ba ne, a’a, sai dai don mu zama abin misali a gare ku kawai, don ku yi koyi da mu. 10 Ai ko dā ma, sa’ad da mu ke tare, mun yi muku wannan umarni cewa: Duk wanda ya ƙi aiki, kada a ba shi abinci. 11 Gama mun ji labari cewa waɗansunku malalata ne kawai, ba sa aikin komai, masu shisshigi ne kurum. 12 To, irin waɗannan mutane muna yi musu umarni, muna kuma gargaɗinsu da izinin Ubangiji Yesu Almasihu, su riƙa aiki cikin nutsuwa, suna ci da kansu. 13Amma ku ’Yan’uwa, kada ku gaji da yin aiki nagari.

14 In wani ya ƙi bin abin da muka faɗa a wasiƙan nan, sai fa ku lura da shi, kada ma ku cuɗanya da shi, don yi kunyata. 15 Amma kada ku ɗauke shi kan abokin gaba, sai dai ku gargacre shi kan Ɗan’uwa ne.

16 To, Ubangiji kansa, Mai haddasa aminci, yă ba ku aminci a koyaushe a cikin kowane hali. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.

17 Ni Bulus, ni na ke rubuto wannan gaisuwa da hannuna. Ita ce kuwa shaidar kowace wasiƙata. Rubutun hannuna ke nan. 18 Alherin Ubangijimmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka.


WASIKAR BULUS TA FARKO
ZUWA GA
TIMOTAWAS

Daga Bulus, Manzon Almasihu Yesu bisa umarnin Allah Macecimmu, da kuma na Almasihu Yesu abin sazuciyarmu, 2 zuwa ga Timotawas, ɗana na hakika ta wajen Bangaskiya.

Alheri da rahama da aminci na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijimmu su tabbata a gare ka.

Aikin Timotawas a Afisa

3 Kamar yadda na roƙe ka ka dakata a Afisa sa’ad da za ni ƙasar Makidoniya, ka gargaɗi wasu mutane kada su koyad da wata koyarwa daban, 4 kada kuma su kashe zarafinsu wajen almara da yawan ƙididdigar asali marar iyaka, waɗanda su kan haddasa gardandami, maimakon riƙon amanar al’amuran Allah cikin bangaskiya; to, yanzu ma haka. 5 Alhali kuwa manufar gargaɗimmu ƙauna ce, wadda ke ɓuɓɓugowa daga tsarkakakkiyar zuciya, wadda ta ke garau, da kuma bangaskiya tsakani da Allah. 6 Waɗansu sun kauce wa waɗannan al’amura; har sun bauɗe sun shiga zancen banza. 7 Suna burin zama masana Attaura, ba tare da fahintar abin da su ke faɗa ba, balle matsalad da su ke taƙamar haƙiƙicewa a kai.

8 To, mun san Shari’ar Musa aba ce mai kyau, im mutun ya yi aiki da ita yadda ya wajaba, 9 yana kuma tunawa cewa ita Shari’a ba a kafa ta don masu aikin gaskiya ba, sai don kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da iyaye mata, da masu kisankai, 10 da fasikai, da masu ludu, da masu sace mutane, da makaryata, da masu shaidar zur, da kuma duk sauran abin da ya saɓa sahihiyar koyarwan nan, 11 bisa Bishara mai ɗaukaka ta Allah abin yabo, wadda aka ɗanka mini.

Tabbatacciyar Magana

12 Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijimmu, wanda ya ƙarfafa ni, saboda ya amince da ni, bar ya sa ni aikinsa, 13 ko da ya ke dā can saɓo na ke yi ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka sai da aka yi mini rahama, domin na yi haka ne cikin jahilci saboda rashin bangaskiya. 14 Alherin Ubangijimmu kuma ya kwararo mini ƙwarai da gaske, game da bangaskiya da ƙaunad da ke ga Almasihu Yesu. 15 Maganan nan tabbatacciya ce, kuma ta cancanci a karɓe ta dungum, cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne don ceton masu zunubi”, ni ne kuwa babbansu. 16 Duk da haka an yi mini rahama musamman don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yă nuna cikakken haƙurinsa, in zama abin misali ga waɗanda nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami. 17 Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, bar abada abadin. Amin.

18 Ya ɗana Timotawas, na ɗanka maka wannan umarni bisa faɗin annabcin nan da ya ba da ishara a kanka, domin albarkacin faɗin annabcin nan ka yi fama, faman gaske, 19 kana riƙe da bangaskiya, zuciyarka garau. Gama waɗansu mutane saboda shure abin da hankalinsu ya ba su, sai suka kacancana bangaskiyatasu. 20 Cikinsu har da Himanayas da Iskandari, waɗanda na miƙa wa Shaiɗan, don su horu su bar yin saɓo.

2

Ikiliziya tă yi wa Duniya Duka Addu’a

Da farko dai ina gargaɗi, cewa a yi ta roƙon Allah, ana addu’a, ana gode wa Allah saboda dukkan mutane, 2 da sarakuna da kuma duk waɗanda ke manyan mukamai, don mu zauna lafiya, rai kwance, muna bin Allah sosai cikin nutsuwa. 3 Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓuwa ne a gun Allah Macecimmu, 4 wanda ke son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin Gaskiya. 5 Domin Allah ɗaya ne, mai sadarwa kuma ɗaya ne tsakanin Allah da mutane—Almasihu Yesu, mutun, 6 wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa. 7 Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, kuma Manzo, (gaskiya na ke faɗa, ba ƙarya ba), mai koya wa sauran al’umma al’amarin Bangaskiya da kuma na Gaskiya.

Halin da ya Dace da Mata Masu Bi

8 Saboda haka a kowane wuri ina so maza su yi addu’a, suna ɗaga hannaye tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba. 9 Mata kuma su riƙa sa tufafin da ya dace da su saboda kunya da kamun-kai; ba adon kitso, ko kayan gwal, ko lu’ulu’u, ko tufafi masu tsada ba, 10 sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibadatasu. 11 Mace ta riƙa koyo cikin kawaici da matuƙar biyayya. 12 Ban yarda mace ta koyar, ko kuma ta yi iko da maza ba, sai dai ta zauna shiru. 13 Ai Adamu aka fara halitta, sannan Hawwa’u. 14 Ba kuma Adamu aka yaudara ba, matar ce aka yaudara bar ta keta umarni. 15 Duk da baka kuwa, ta haifar ’ya’ya sai ta kai ga kammala, muddin ta nace wa bangaskiya, da ƙauna, da tsarkaka, da kuma kamun-kai.

3

Masu Aikin Kula da Ikiliziya

Maganan nan tabbatacciya ce, cewa duk mai burin aikin kula da ikiliziya, yana burin aiki mai kyau ke nan. 2 To, lalle ne mai kula da ikiliziya yă zama marar abin zargi, ya zama mai mace ɗaya, mai kamun-kai, nutsattse, kintsattse, mai yi wa baƙi alheri, kuma gwanin koyarwa. 3 Ba mashayi ba, ba mai saurin hannu ba, sai dai mai sanyin-hali, ba kuma mai husuma ba, ba kuwa mai son kuɗi ba. 4 Lalle ne yă iya sarrafa iyalinsa da kyau, yana kuma kula ’ya’yansa su yi biyayya da matuƙar ladabi. 5 Don kuwa im mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ƙaƙa zai iya kula da ikiliziyar Allah? 6 Lalle ne kuma kada ya zama farin-shiga, don kada ya ɗaga kai ya burmu cikin hukuncin da aka yi wa Iblis. 7 Ban da haka kuma lalle ne ya zama mai mutunci ga waɗanda ba sa cikimmu, don kada ya zama abin zargi, ya faɗa tarkon Iblis.

8 Haka kuma masu hidimar ikiliziya, lalle ne su zama nutsattsu, ba masu baki biyu ba, ko mashaya, ko masu kwaɗayin kazamar riba. 9 Lalle ne su riƙi zuzzurfan al’amarin Bangaskiya da zuciya tsarkakakkiya. 10 Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar. 11 Haka kuma matan, lalle su zama nutsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamun-kai, masu alkawari ta kowace hanya. 12 Masu hidima kuma su zama masu mata ɗai-ɗai, masu sarrafa ’ya’yansu da sauran iyalinsu da kyau. 13 Masu hidimad da ke aikinsu sosai, suna sama wa kansu kyakkyawan suna, da kuma ƙaƙƙarfar amincewa ga bangaskiyatasu ga Almasihu Yesu.

Ikiliziyar Allah Rayayye

14 Ina sa zuciya in zo wurinka ba da daɗewa ba, amma ina rubuto maka waɗannan abubuwa, 15 don in ya zamana na yi jinkiri, kă san irin zaman da ya kamata a yi a cikin jama’ar Allah, wadda ta ke ita ce ikiliziyar Allah Rayayye, jigon Gaskiya kuma ginshiƙinta. 16 Dahir, zuzzurfan al’amarin addinimmu babba ne ƙwarai:

Am bayyana shi da jikin mutun,
Ruhu Tsattsarka ya tabbatad da gaskiyatasa,
Mala’iku sun gan shi,
An yi wa al’ummai wa’azinsa,
An gaskata da shi a duniya,
An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.

4

Malaman Karya da Koyarwatasu

To, Ruhu Tsattsarka musamman ya ce, a can wani zamam wasu za su fanɗare wa Bangaskiya, su mai da hankali ga aIjannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu, 2 ta makircin wasu maƙaryata waɗanda zuciyatasu ta yi kanta. 3 Su ne masu hana aure da cin abinci iri-iri, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya, suka kuma san Gaskiya, su karɓa da godiya. 4 Domin duk abin da Allah ya halitta kyakkyawa ne, kada kuma a ƙi komai muddar an karɓe shi da godiya, 5 don Maganar Allah da addu’a sun keɓe shi a tsarkake.

Ka Hori Kanka ga Bin Allah

6 In kana tuna wa ’Yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar Bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwan nan da ka bi bar ya zuwa yau. 7 Ka ƙi tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi. Ka hori kanka ga bin Allah. 8 Horon jiki na da ɗan amfaninsa, amma bin Allah na da amfani ta kowace hanya, da ya ke shi ke da alkawarin rai madawwami a yanzu da kuma Ranar gobe. 9 Maganan nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta dungum. 10 Saboda wannan maƙasudi mu ke wahala, mu ke fama, don mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda ya ke shi ne Macecin dukkan mutane, musamman masu ba da gaskiya.

11 Ka yi umarni da waɗannan abubuwa, ka kuma koyad da su. 12 Kada ka yarda kowa ya raina kuruciyarka, sai dai ka zama abin misali ga masu ba da gaskiya ta magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka. 13 Kafin in zo ka lazamci karanta wa mutane Littattafai Tsarkaka, da yin gargaɗi, da kuma koyarwa. 14 Kada ka shagala da baiwad da aka yi maka, wadda aka ba ka ta faɗin annabci, sa’ad da dattawan ikiliziya suka ɗora maka hannu. 15 Ka himmantu ga waɗannan abubuwa, ka kuma lazamce su ƙwarai, don kowa yă ga ci gaban da ka ke yi. 16 Ka kula da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da haka, don ta yin haka za ka kuɓutad da kanka da masu sauraronka.

5

Kada ka tsauta wa dattijo, sai dai ka roƙe shi kamar mahaifinka. Samari kuma ka ɗauke su kamar ’yan’uwanka, 2 tsofaffi mata kuma kamar iyayenka, ’yammata kuwa kamar ’yan’uwanka, da matuƙar tsarkaka.

3 Ka taimaki matan da mazansu suka mutu, waɗanda ba su da mataimaka. 4 In wata matar da mijinta ya mutu tana da ’ya’ya ko jikoki, sai su koyi cewa danginsu ya wajaba su fara nuna wa bautar Allah da su ke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓuwa ne a gun Allah. 5 Matar da mijinta ya mutu marar mataimaki kuwa, mai zaman kaɗaitaka, tă dogara ga Allah ke nan, tana nacewa ga roƙon Allah, tana addu’a dare da rana. 6 Wadda kuwa ta ke zaman annashuwa, kamar matacciya ta ke, ko da tana raye. 7 Ka yi umarni game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi. 8 Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya musa wa Bangaskiya ke nan, kuma ya kasa marar ba da gaskiya.

9 Duk matar da mijinta ya mutu, wadda ta kasa shekara sittin, ko kuwa wadda ta yi aure fiye da ɗaya, kada a rubuta ta cikin gwauraye. 10 Sai dai wadda a ke yabo kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi ’ya’ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke kafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari. 11 Amma kada ka rubuta mata masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu, cikin gwaurayen, don in zuciyatasu ta kasa ɗaurewa game da wa’adin da suka yi da Almasihu, sai su so yin aure, 12 hukunci yā kama su ke nan, tun da ya ke sun ta da wa’adinsu na farko. 13 Ban da haka kuma su kan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shisshigi, suna faɗar abin da bai kamata ba. 14 Saboda haka ina so mata masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu su yi aure, su haifu, su tafi da al’amuran cikin gida, kada su ba magabci hanyar zargimmu. 15 Gama wasu ma har sun bauɗe sun bi Shaiɗan. 16 Duk mace mai bi da ke da dangi mata waɗanda mazansu suka mutu, sai ta taimake su, kada a nauyaya wa ikiliziya, don ikiliziyar ta samu ta taimaki gwauraye marasa mataimaka.

Ma’aikaci ya Cancanci Ladansa

17 Dattawan ikiliziya da ke riƙe da al’amura sosai, a girmama su ninkin ba ninkin, tun ba ma waɗanda ke fama da yin wa’azi da koyarwa ba. 18 Don Nassi ya ce, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi sa’ad da ya ke sussuka.” Ya kuma ce, “Ma’aikaci ya cancanci ladansa.” 19 Kada ka yarda in an kawo ƙarar wani dattijon ikiliziya, sai dai da shaidu biyu ko uku. 20 Masu ɗaukar zunubi kuwa, sai ka tsawata musu a gaban dukkan jama’a, don saura su tsorata. 21 Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ba sani ba sabo, kada ka yi komai da wariya. 22 Kada ka yi garajen ɗora wa kowa hannu, kada kuwa zunuban waɗansu su shafe ka. Ka tsare kanka a tsarkake.

23 Nan gaba ba ruwa kaɗai za ka sha ba, sai dal ka sha ruwan inabi kaɗan saboda cikinka, da kuma yawan laulayinka.

24 Zunuban wasu mutane a fili su ke, tun ba a kai gaban shari’a ba. Zunuban wasu kuwa sai daga baya su ke bayyana. 25 Haka kuma kyawawan ayyukan waɗansu a fili su ke, kuma ko ma ba a fili su ke ba, ba za su tabbata a ɓoye ba.

6

Hakkin Bayi game da lyayengijinsu

Duk ɗakwacin masu igiyar bauta a wuyansu su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci a girmama su matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwan nan. 2 Waɗanda ke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su wai don su ’Yan’uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da ya ke waɗanda ke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, kuma ƙaunatattu ne a gare su.

Ka koyad da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu. 3 Duk wanda ke wata koyarwa daban, bai kuwa yarda da sahihiyar Maganar Ubangijimmu Yesu Almasihu, da kuma koyarwad da ta dace da bautar Allah ba, 4 girmankai ya ciccika shi ke nan, bai san komai ba; yana da muguwar jarabar gardama da jayayya a kan maganganu kawai, waɗanda ke jawo hassada, da husuma, da yanke, da miyagun zace-zace, 5 da kuma yawan tankiya cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammanin bin Allah hanya ce ta samu. 6 Bin Allah game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa. 7 Don ba mu zo duniya da komai ba, ba kuwa za mu iya fita da komai ba. 8 To, im muna da abinci da sutura, ai sai mu dangana da su.

Togaciya a kan Kwaɗayi

9 Masu ɗokin yin arziki kuwa, su kan zarme da jaraba, su faɗa tarko, suna miyagun sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda ke dulmuyad da mutane su kai ga lalacewa da halaka. 10 Ai son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane har sun bauɗe wa Bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙinciki iri-iri masu sukan rai.

11 Amma ya kai bawan Allah, ka guji waɗannan abubuwa, ka dimanci aikin gaskiya, da bin Allah, da bangaskiya, da ƙauna, da jimiri, da kuma ƙanƙan-da-kai. 12 Ka yi fama, faman gaske saboda Bangaskiya; ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa’ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa. 13 Na gama ka da Allah mai raya komai, na kuma gama ka da Almasihu Yesu, wanda ya yi shaida, kyakkyawar shaidan nan, a gaban Buntus Bilatus, 14 ka bi umarninsa, ba tare da wani aibi ko zargi ba, har ya zuwa bayyanar Ubangijimmu Yesu Almasihu; 15 wannan kuwa Makaɗaicin Mamallaki abin yabo, Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji zai bayyana shi a lokacinsa. 16 Shi ne kaɗai mutuwa ta koru gare shi, ya ke kuma zaune cikin hasken da ba ya kusantuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata gare shi. Amin.

Gargaɗi ga Masu Dukiya

17 Masu dukiyar duniyan nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda ke ba mu komai a yalwace don mu ji daɗinsa. 18 Sai dai su yi nagarta da bajinta wajen aiki nagari, su kasance masu hannu sake, suna alheri. 19 Ta haka su ke kafa wa kansu kyakkyawan tushe don gaba, domin su riƙi rai madawwami wanda ya ke na hakika.

20 Ya Timotawas, ka kiyaye abin da aka ba ka amana. Ka yi nesa da masu maganganun saɓo na banza da wofi, da yawan musu da a ke ƙarya a ke ce da shi ilimi. 21 Waɗansu kuwa garin taƙama da haka har sun kauce wa Bangaskiya.

Alheri yd tabbata a gare ku.


WASIƘAR BULUS TA BIYU
ZUWA GA
TIMOTAWAS

Daga Bulus, Manzon Almasihu Yesu cikin yardar Allah, don sanad da alkawarin nan na rai madawwami da ke ga Almasihu Yesu, 2 zuwa ga. Timotawas ƙaunataccen ɗana.

Alheri da rahama da aminci na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijimmu su tabbata a gare ka.

3 Ina gode wa Allah, wanda na ke bauta wa da zuciya garau, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa’ad da na ke tunawa da kai cikin addu’ata ba fasawa. 4 Sa’ad da na ke tunawa da hawayenka na kan yi begen ganinka dare da rana, don in yi farinciki matuƙa 5 ina tunawa da bangaskiyarka ta tsakani da Allah, wadda da farko ke tare da kakarka Luwisa, da mahaifiyarka Afiniki, yanzu kuma na tabbata tana tare da kai. 6 Saboda haka ina so in faɗakad da kai, ka tayar da baiwan nan ta Allah, wadda ke tare da ka ta ɗora maka hannayena. 7 Ai Allah ba ragon ruhu ya ba mu ba ruhu mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamun-kai.

Ku Jure wa Shan Wuya saboda Bishara

8 Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijimmu da kuma tawa, ni da na ke fursuna saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare saboda Bishara, bisa ikon Allah, 9 wanda ya cece mu, ya kuma kira mu mu yi zaman tsarkaka, ba wai don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai don nufinsa da kuma rahamatasa da aka yi mana baiwa tun fil’azal, albarkacin Almasihu Yesu, 10 wadda. yanzu aka bayyana, ta bayyanar Macecimmu Almasihu Yesu wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai madawwami da rashin mutuwa, ta Bishara. 11 A wannan Bishara an sa ni mai wa’azi, kuma manzonta, kuma mai koyarwatata. 12 Saboda haka ne na ke shan wuya haka. Duk da haka ban kunyata ba, don na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa har ya zuwa waccan rana. 13 Ka yi koyi da sahihiyar maganad da ka ji daga gare ni, cikin bangaskiya da ƙauna da ke ga Almasihu Yesu. 14 Kyakkyawan abin nan da aka ba ka amana, ka kiyaye shi ta Ruhu Tsattsarka, wanda ke zaune a zuciyarmu.

15 Ka dai sani duk waɗanda ke ƙasar Asiya sun juya mini baya, cikinsu kuwa har da Fijalas da kuma Harmajanas. 16 Ubangiji yi yi wa iyalin Unasifaras rahama, don sau da yawa ya ke sanyaya mini zuciya, bai kuwa yi ƙyamar ɗaurina da aka yi ba. 17 Har ma da ya zo Roma, sai ya neme ni ido rufe, ya kuwa same ni. 18 Ubangiji ya rahamshe shi a waccan ranar. Ka dai sani sarai yadda ya yi dawainiya mai yawa a Afisa.

2

Amintaccen Sojan Almasihu Yesu

Saboda haka ya kai ɗana, sai ka ƙarfafa da alherin da ke ga Almasihu Yesu. 2 Abin da ka ji a guna a gaban shaidu masu yawa kuwa, sai ka ɗanka wa amintattun mutane, waɗanda za su iya koya wa waɗansu ma. 3 Kai ma ka jure wa shan wuya kana amintaccen sojan Almasihu Yesu. 4 Ai ba sojan da ke bakin daga da ransa zai sarƙafe da sha’anin duniya, tun da ya ke burinsa shi ne yă faranta wa wanda ya ɗauke shi soja. 5 Mai wasan guie-guje da tsalle-tsalle, ba zai sami ɗaukaka ba, sai ko ya bi dokokin wasan. 6 Ma’aikacin manomi, ai shi ya kamata ya fara cin amfanin gonar. 7 Ka yi tunani a kan abin da na ke faɗa, Ubangiji kuwa zai ba ka fahintar komai.

8 Ka tuna da Yesu Almasihu fa, shi da aka tasa daga matattu, na zuriyar Dawuda, bisa Bisharata, 9 wadda na ke shan wuya saboda ita, har na ke ɗaure kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure ta ke ba. 10 Don haka na ke jure komai saboda zaɓaɓɓu, don su ma su sami ceton nan da ke samuwa albarkacin Almasihu, game da madawwamiyar ɗaukaka.

Bayan Wuya sai Daɗi

11 Maganan nan tabbatacciya ce, cewa,

Im mun mutu tare da shi, za mu rayu ma tare da shi;
12 Im mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi;
Im mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun sanimmu;
13 Im ba mu da alkawari, shi kam ya tabbata mai alkawari,
Don ba zai iya musun kansa ba.

14 Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai ta ke yi. 15 Ka himmantu ka miƙa wuya ga Allah kana abin karɓuwa gare shi, ma’aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassara Maganar Gaskiya daidai wa daida. 16 Ka yi nesa da masu maganganun banza na saɓo. Sai daɗa jan mutane ga rashin bin Allah su ke yi, 17 maganatasu ta kan haɓaka kamar gyambo. Cikinsu har da Himanayas da Filitus, 18 waɗanda suka bauɗe wa Gaskiya, wai Tashin Matattu ya riga ya wuce, suna jirkitad da bangaskiyar wasu. 19 Duk da haka ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa, cewa, “Ubangiji ya san nasa”, kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikin rashin gaskiya”. 20 A babban gida, ba kayan zinariya da na azurfa ne kawai ba, har ma da na ice da na yumɓu, wasu don aikin ɗaukaka, wasu kuwa don ƙasƙantaccen aiki. 21 Kowa ya tsarkake kansa daga ayyukan nan ƙasƙantattu, zai aima abin ɗaukaka, keɓaɓɓe a tsarkake, mai amfani ga Ubangiji, shiryayye ga kowane kyakkyawan aiki.

Gargaɗi ga Timotawas

22 Don haka sai ka guje wa miyagun sha’awace-sha’awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin gaskiya, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma aminci, tare da waɗanda ke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya. 23 Ka ƙi gardandamin banza marasa ma’ana; ka san lalle suna jawo husuma. 24 Bawan Ubangiji kuwa lalle kada ya zama mai husuma, sai dai ya zama mai sanyin-hali ga kowa, gwanin koyarwa, mai haƙuri, 25 mai sa abokan hamayyarsa hanya cikin ƙanƙan-da-kai, ko Allah ya sa su tuba, su kai ga sanin Gaskiya, 26 su kuɓuce wa tarkon Iblis, su bi nufin Allah, bayan Iblis ya tsare su.

3

Ɓataccen Hankali na Zamanin Ƙarshe

Amma sai ka fahinci cewa a zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai. 2 Mutane za su zama masu sonkai, masu son kuɗi, masu ruba, masu girmankai, masu zage-zage, marasa bin iyayensu, masu butulci, marasa tsarkaka, 3 marasa ƙauna, masu riƙo a zuci, masu yanke, fajirai, maƙetata, maƙiya nagarta, 4 maciya amana, masu taurinkai, mutakabbirai, masu son annashuwa fiye da son Allah, 5 suna riƙe da siffofin ibada, amma suna saɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane. 6 A cikinsu kuwa akwai masu sadadawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha’awa iri-iri kuma ta ɗauke musu hankali, 7 kullum suna koyo, amma kullum sai su kasa kaiwa ga sanin Gaskiya. 8 Kamar yadda Yanisu da Yambarisu suka tayar wa Musa, haka mutanen nan kuma ke tayar wa Gaskiya, mutane ne masu ɓataccen hankali ƙwarai, bangaskiyarsu ta banza ce. 9 Amma ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.

10 Kai kam ka riga ka kiyaye da koyarwata, da halina, da niyyata, da bangaskiyata, da haƙurina, da ƙaunata, da jimirina, 11 da kuma yawan tsananin, da wuyad da na sha, da suka same ni a Antakiya, da Ikoniya, da Listira, wato irin tsanance-tsanancen da na jure. Amma Ubangiji ya kuɓutad da ni daga cikinsu duka. 12 Labudda duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Almasihu Yesu, za su sha tsanani. 13 Miyagun mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14 Amma kai kuwa ka zauna kan abin da ka koya, ka kuma haƙƙaƙe, gama ka san wurin waɗanda ka koye su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramin yaro ka san Littattafai Tsarkaka, waɗanda su ke iya koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Almasihu Yesu. 16 Duk Littattafai Tsarkaka faɗar Allah ne, masu amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin gaskiya, 17 don bawan Allah yă zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.

4

Ka yi Wa’azi ko da Yaushe

Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanda zai yi wa rayayyu da matattu shari’a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanatasa da kuma mulkinsa, 2 ka yi wa’azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa gwiwa, game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa. 3 Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu na ƙaiƙayi, sai su taro malaman da za su biya musu muradinsu. 4 Za su toshe kunnensu ga jin Gaskiya, su karkata ga jin tatsuniyoyi. 5 Kai kuwa sai ka nutsu cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai Bishara, ka cika hidimarka.

6 Don ni kam a yanzu gab na ke da a zub da jinina. Lokacin ƙaurata ya yi. 7 Na sha fama, faman gaske, na gama tseren, na riƙe Bangaskiya. 8 Santa kuwa sai sakamakon nan na aikin gaskiya da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, Mahukunci mai gaskiya, zai ba ni a ranan nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har duk waɗanda suka ƙaunaci su ga bayyanatasa.

9 Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo wurina da hanzari, 10 domin Dimas, saboda ƙaunar duniyan nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaskas ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya. 11 Luka ne kaɗai ke tare da ni. Ka ɗauko Markus ku zo tare, gama yana da amfani gare ni wajen yi mini hidima. 12 Tikikus kuwa na aike shi Afisa. 13 Sa’ad da za ka taho, ka zo da alkyabban nan da na bari a wurin Karbus a Taruwasa, da kuma littattafan nan, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba. 14 Iskandari maƙerin farfarun nan ya yi min mugunta ƙwarai. Ubangiji zai yi masa sakayyar aikinsa. 15 Kai ma ka mai da hankali da shi, gama ya hauri maganarmu, kyakkyawar haura. 16 A lokacin ba da hanzarina na farko, ba wanda ya goyi bayana, sai duk suka yashe ni. Ina fata kada wannan laifi ya ɗoru a kansu. 17 Amma sai Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanad da Bishara sosai da sosai, don duk sauran al’umma su ji; aka kuwa cece ni daga bakin zaki. 18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.

19 Ka gayar mini da Biriska da Akila, da mutanen gidan Unasifaras. 20 Arastas yā dakata a Korinti. Tarufimas kuwa na bar shi a Militus, ba shi da lafiya. 21 Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus na gaishe ka, da Budas, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan ’Yan’uwa.

22 Ubangiji yă kasance a zuciyarka. Alheri yd tabbata a gare ku.


WASIKAR BULUS
ZUWA GA
TITUS

Daga Bulus, bawan Allah kuma Manzon Yesu Almasihu, don tabbatad da bangaskiyar zaɓabɓun Allah, da kuma saninsu na Gaskiya mai haddasa bautar Allah; 2 duk wannan kuwa saboda sazuciyan nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil’azal, shi da karya ta koru gare shi, 3 ya kuwa bayyana maganatasa a lokacin da ya ƙayyade, ta wa’azin da shi Allah Macecimmu ya amince min bisa umarninsa; 4 zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen Bangaskiyamm mu duka.

Alheri da aminci na Allah Uba, da na Almasihu Yesu. Macecimmu su tabbata a gare ka.

Halin da ya Dace da Dattawan Ikiliziya

5 Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman don ka ƙarasa daidaita al’amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikiliziya a kowane gari, kamar yadda na nushe ka. 6 Amma sai wanda ya kasance marar abin zargi, mai mace ɗaya, wanda ’ya’yansa ke masu ba da gaskiya, waɗanda ba a zargi da aikin masha’a ko kangara. 7 Lalle ne kuwa kowane mai kula da ikiliziya, da ya ke shi mai riƙon amana saboda Allah ne, ya zama marar abin zargi, ba mai taurinkai ba, ko mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai saurin hannu, ko mai kwaɗayin ƙazamar riba. 8 Amma sai ya kasance mai yi wa baƙi alheri, mai son abu nagari, nutsattse, inai gaskiya, tsarkakakke, mai kamun-kai, 9 mai riƙe da tabbatacciyar maganan nan kankan, daidai yadda aka koya masa, don ya iya ƙarfafa wa wasu gwiwa da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta. 10 Don kuwa akwai kangararrun mutane da yawa, masu surutan banza, masu ruɗi, tun ba ma ɗariƙar masu kaciyan nan ba. 11 Lalle ne a kwaɓe su, tun da ya ke suna jirkitad da jama’a gida-gida, ta koyad da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riba. 12 Wani daga cikin Karitawa ma, mawakinsu, har ya ce, “Karitawa kullum maƙaryata ne, miyagun dabbobi, ragwaye haɗamammu.” 13 Shaidan nan tasa kuwa gaskiya ce. Saboda haka sai ka tsawata musu da gaske, don su zama sahihai wajen Bangaskiya, 14 a maimakon su mai da hankali ga almarar Yahudawa, ko kuwa dokokin mutane masu kin Gaskiya, 15 Ga masu tsarkin rai duk al’amarinsu mai tsarki ne; marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al’amarinsu da ke mai tsarki; da zuciyatasu da ra’ayinsu duka marasa tsarki ne. 16 Suna cewa sun san Allah, amma suna saɓa masa ta aikinsu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani wajen yin aiki nagari.

2

Halin da ya Dace da Dattawa Maza da Mata

Amma kai kam sai ka faɗi abin da ya dace da sahihiyar koyarwa. 2 Dattawa su kasance masu kamun-kai, nutsattsu, mahankalta, masu sahihiyar bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimiri. 3 Haka kuma manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyad da kyakkyawan abu, 4 ta haka su koya wa mata masu ƙuruciya su so mazansu da ’ya’yansu, 5 su kuma kasance nutsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah. 6 Haka kuma ka gargaɗi samari su yi kamun-kai. 7 Kai ma sai ka zama abin misali na aiki nagari ta kowace hanya, cikin koyarwarka kana nuna rashin jirkituwa, da nutsuwa, 8 da kuma sahihiyar maganad da ba za a kushe mata ba, don a kunyata abokan hamayya, su rasa hanyar zargimmu. 9 Bayi su yi biyayya ga iyayengijinsu, su kuma gamsad da su ta kowane hali. Kada su yi tsayayya, 10 ko taɓe-taɓe, sai dai su riƙi amana sosai tsakani da Allah, don su ƙawatad da koyarwar Allah Macecimmu ta kowane hali.

Ku yi Zaman Tsarkaka

11 Alherin Allah ya bayyana saboda ceton dukkan mutane, 12 yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da miyagun sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi zamammu a duniyan nan cikin nutsuwa, da gaskiya, da kuma bin Allah, 13 muna sauraron cikar sazuciyan nan mai albarka, wato, bayyanar ɗaukakar Allahmmu Mai girma, Macecimmu Yesu Almasihu, 14 wanda ya ba da kansa domimmu, don ya fanso mu daga dukkan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama’a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.

15 Ka yi ta sanad da waɗannan abubuwa, kana gargaɗi da su, kana tsawatarwa da kakkarfan umarni. Kada ka yarda kowa ya raina ka.

3

Girmama Mahukunta

Ka riƙa tuna musu su yi wa mahukunta da shugabarmi ladabi, suna yi musu biyayya, suna kuma zaune da shirinsu na yin kowane irin kyakkyaan aiki. 2 Kada su ci naman kowa, kada su yi husuma, sai dai su zama masu sanyin-hali, suna yi wa dukkan mutane matuƙar ƙanƙan-da-kai. 3 Mu kammu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, am ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha’awa da nishadi iri-iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi wasu. 4 Amma sa’ad da alherin Allah Macecimmu da ƙaunarsa ga ’yan’adan suka bayyana, 5 sai ya cece mu, ba wai don wani aikin gaskiya da mu muka yi ba, a’a, sai dai don rahaman nan tasa, albarkacin wankan nan na sake haifuwa, da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Tsattsarka, 6 wanda ya kwararo mana a yalwace ta kan Yesu Almasihu Macecimmu. 7 Wannan kuwa don a maishe mu abin karɓuwa ga Allah bisa alherinsa ne, mu kuma zama magada masu sa zuciya ga ra madawwami. 8 Maganan nan tabbatacciya ce.

Himmantuwa ga Aiki Nagari

Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari; waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, kuma masu amfani ga mutane 9 Amma ka yi nesa da gardandamin banza, da ƙididdigar asali, da husuma, da jayayya a kan Shari’ar Musa, domin ba su da wata riba, kuma aikin banza ne. 10 Fanɗararren mutun kuwa, in ya shanye gargaɗinka na farko da na biyu, to, sai ka fita sha’aninsa. 11 Ka dai san irinsa ɓatacce ne, mai ɗaukar zunubi, shi kansa ma ya san hakanan ya ke.

12 Sa’ad da na aiko Artimas ko Tikikus wurinka, sai ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo wurina a Nikafolis, don na yi niyyar cin damuna a can. 13 Ka yi himmar taimakon Zinas, masanin Attaura, da Afalas, su kamo hanya, ka kuma tabbata ba abin da ya gaza musu 14 Jama’armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.

15 Duk waɗanda ke tare da ni suna gaishe ka. Ka gayar mini da masoyammu kan al’amarin Bangaskiya.

Alheri yă tabbata a gare ku ku duka.


WASIKAR BULUS
ZUWA GA
FILIMAN

Daga Bulus, fursuna saboda Almasihii Yesu, da kuma Timotawas Ɗan’uwammu, zuwa ga Filiman ƙaunataccen abokin aikimmu, 2 da Aufiya ’Yar’uwarmu, da Arkibus abokin famammu, da kuma ikitiziyad da ke taruwa, a gidanka.

3 Alheri da aminci na Allah Ubammu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

4 Kullum ina gode wa Allahna duk sa’ad da na ke maka addu’a, 5 saboda na kan ji labarin ƙauna da bangaskiya da ka ke yi wa Ubangiji Yesu da dukkan tsarkaka. 6 Ina addu’a Bangaskiyan nan da ta haɗa ku tă kasance mai ƙwazo wajen ciyad da sanin dukkan kyawawan abubuwan da ke namu gaba, don ɗaukaka Almasihu. 7 Na yi farinciki ƙwarai, gwiwata kuma ta yi ƙarfi saboda ƙaunad da ka ke yi, ya kai Ɗan’uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta kanka.

8 Saboda haka, ko da ya ke game da al’amarin Almasihu ina iya umartarka gabagaɗi ka yi abin da ya wajaba, 9 duk da haka saboda ƙauna na fi so in roƙe ka—ni Bulus tsoho, yanzu kuma ga m fursuna saboda Almasihu Yesu— 10 ina roƙonka saboda ɗana

Unisimus, wanda na zama ubansa ina ɗaure. 11 Dā kam ba shi da wani amfani a wurinka, amma yanzu hakika yana da amfani gare mu, ni da kai. 12 Ga shi nan na komo maka da shi kamar gudan zuciyata. 13 Dā kam sona in riƙe shi a wurina, ya rika yi mini hidima a madadinka, muddar ina ɗaure saboda Bishara; 14 amma ba na son in yi komai ba tare da yardarka ba, don kada alherinka ya zamana na tilas ne, ba na ganin dama ba.

15 Watakila shi ya sa kuka ɗan rabu, don kă same shi har abada, 16 ba kuma a kan bawa ba, sai dai a kan abin da ya fi bawa, wato, Ɗan’uwa abin ƙauna, tun ba ma gare ni ba, balle gare ka, ta wajen zumunci da kuma wajen al’amarin Ubangiji. 17 Saboda haka in ka ɗauke ni a kan abokin tarayya, to, sai ka karɓe shi kamar yadda za ka karɓe ni. 18 Ko ma ya yi maka wani laifi, ko kuwa kana binsa wani abu, sai ka mai da shi kaina. 19 Ni Bulus, ni na ke rubuto wannan da hannuna, ni kuwa zan biya-kada ma a yi zancen ranka da na fanso maka! 20 Ya Ɗan’uwana, in sarmi wata fa’ida mana a gare ka saboda Ubangiji! Ka sanyaya mini zuciya saboda Almasihu.

21 Don na tabbata da biyayyarka shi ya sa na rubuto maka, don na san za ka yi har fiye da abin da na faɗa. 22 Har wa yau kuma ka shirya mini masauƙi, don ina sa zuciya a ba ni yarjin zuwa gare ku albarkacin addu’arku.

23 Abafaras, abokin ɗaurina saboda Almasihu Yesu, na gaishe ka, 24 haka kuma Markus, da Aristarkus, da Dimas, da Luka, abokan aikina, suna gaishe ka.

25 Alherin Ubangijimmu Yesu. Almasihu yă tabbata a zukatanku.


WASIƘA
ZUWA GA
IBRANIYAWA

1

Allah ya yi Magana ta kan Ɗansa

A zamanin dā Allah ya yi wa kakannin kakannimmu magana ta hanyoyi masu yawa iri-iri, ta bakin annabawa, 2 amma a zamanin nan na. ƙarshe sai ya yi mana magana ta kan Ɗansa, wanda ya sanya magajin komai, wanda ta kansa ne kuma ya halicci duniya. 3 Shi ne hasken ɗaukakar Allah, kuma ainihin yanayin Zatinsa, shi ke kuma riƙe da dukkan abubuwa ta ikon faɗatasa. Bayan ya tsarkake zunubammu, sai ya zauna a hannun dama na Maɗaukaki a can Sama.

Fifikon Almasihu a kan Mala’iku

4 Ta haka ya ke da fifiko a kan mala’iku, kamar yadda sunansa da ya gada ke da fifiko nesa a kan nasu.

5 Don kuwa wanene a cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa,

“Kai Ɗana ne,
Na mai da kai Ɗana yau”?

kuma,

“Zan kasance Uba gare shi,
Shi kuma zai kasance Ɗa gare ni”?
6 Amma da zai sake shigo da Magaji duniya, sai ya ce,
“Dukkan mala’ikun Allah su yi masa sujada.”

7 Game da mala’iku kuma sai ya ce,

“Ya kan mai da mala’ikunsa ruhohi,
Masu hidimarsa kuma harsunan wuta.”

8 Amma game da ɗan sai ya ce,

“Gadon sarautarka, ya Allah, na har abada abadin ne,
Sandan sarautarka sanda ne na tsantsar gaskiya.
9 Kā ƙaunaci aikin gaskiya, ka ƙi aikin sabo.
Saboda haka Allah, wato Allahnka, ya shafe ka, tsattsarkar shafa,
Da man farinciki, fiye da tsararrakinka.”

10 Kuma,

“Ya Ubangiji, kai ne ka fari duniya tun farko,
Sammai kuma aikin hannunka ne.
11 Su za su halaka, amma kai madawwami ne.
Duk za su tsufa kamar tufa,
12 Za ka nade su kamar mayafi,
Za su kuma canza,
Amma kai kana nan ba canjawa,
Har abada shekarunka, ba za su kare ba.”

13 Amma wanene a cikin mala’iku Allah ya taɓa ce wa,

“Zauna a hannuna na dama,
Sai na sa ka take maƙiyanka”?

14 Ashe dukkan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah ya kan aika su yi wa waɗanda za su gaji ceto hidima?

2

Mu Tsananta Kula da Maganar Ceto

Saboda haka lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana. 2 In kuwa maganan nan da aka faɗa ta bakin mala’iku ta zama tabbatacciya, har kowane keta umarni da rashin biyayya suka gamu. da sakamakonsu da ya kamace su, 3 to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, im mun ƙi kula da babban ceto haka? Domin Ubangiji da kansa shi ne ya fara sanad da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi, 4 sa’an nan kuma Allah ya haɗa shaidatasa da tasu a kan ceton, ta alamomi da abubuwan al’ajabi da mu’ujizai iri-iri, da kuma baiwar Ruhu Tsattsarka daban-daban da ya rarraba kamar yadda ya nufa.

An Naɗa Almasihu da Ɗaukaka da Girma

5 Ai ba ga mala’iku ba ne Allah ya sanya mulkin Ranar Gobe, wanda mu ke faɗa. 6 Amma wani ya tabbatar a wani wuri, cewa,

“Mutum ma menene, har da za ka tuna da shi?
Ko ɗam mutum ma, har da za ka kula da shi?
7 Kā sa shi ya gaza mala’iku a wani lokaci kaɗan,
Kā naɗa shi da ɗaukaka da girma,
Kā ɗora shi a kan dukkan halittarka,
8 Kā kallafa komai ƙarƙashin ikonsa.”

To, wajen kallafa dukkan abubuwa ƙarƙashinsa ɗin nan, Allah bai bar komai a keɓe ba. Amma kuwa har yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba. 9 Amma muna ganin Yesu, wanda a wani lokaci kaɗan aka sa shi ya gaza mala’iku, an naɗa shi da ɗaukaka da girma saboda shan-wuyatasa ta mutuwa. Wannan kuwa duk don bisa rahamar Allah yă mutu ne saboda kowa.

10 Saboda haka ya dace da Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance dominsa, kuma ta gare shi ne dukkan abubuwa suka samu, yă kammala shugaban cetonsu ta shan wuya, wajen kawo ’ya’ya masu yawa ga samun ɗaukaka. 11 Domin da shi Mai keɓewa a tsarkake, da kuma waɗanda aka keɓe a tsarkaken, duk tushensu ɗaya ne. Shi ya sa ba ya ƙyamar kiransu ’Yan’uwansa, 12 da ya ce,

“Zan sanad da sunanka ga ’Yan’uwana,
A tsakiyar ikiliziya zan yabe ka da waƙa.”

13 Har wa yau ya ce,

“Zan dogara gare shi.”

Kuma,

“Ga ni nan, ni da ’ya’yan da Allah ya ba ni.”

14 Wato tun da ya ke ’ya’yan duk suna da tsoka da jini, shi ma sai ya ɗauki yanayin haka, don ya zāre lakar mai ikon hallakarwa, wato Iblis, ta mutuwarsa, 15 yă kuma ’yanta duk waɗanda tun haifuwarsu su ke zaman bauta kan tsoron halaka. 16 Don hakika ba mala’iku ya ke kama hannu ya ke ceto ba, a’a, zuriyar Ibrahim ne ya ke kama hannu ya ke ceto. 17 Saboda haka lalle ne ya zama kamar ’Yan’uwansa ta kowane hali, don ya zama Shugaba ga kusantar Allah, mai rahama, kuma mai alkawari, cikin al’amarin Allah, yi kuma kankare zunuban jama’a. 18 Tun da ya ke shi ma ya sha wuya sa’ad da aka gwada shi, ashe zai iya taimakon waɗanda a ke wa gwaji.

3

Fiƙkon Almasihu a kan Musa

Saboda haka, ya ku ’Yan’uwa tsarkaka, ku da kuka rabanta da kiran Allah daga Sama, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo kuma Shugaba ga kusantar Allah kan addinimmu, 2 shi da ke riƙon amanar wannan da ya sanya shi, kamar yadda Musa ya yi ga duk jama’ar Allah. 3 Amma kuwa an ga Yesu ya cancanci ɗaukaka fiye da ta Musa nesa, kamar yadda mai gina gida ya fi gidan martaba. 4 Kowane gida ai da wanda ya gina shi, amma maginin dukkan abubuwa Allah ne. 5 To, shi Musa ya riƙi amanar dukkan jama’ar Allah a kan shi bara ne, don saboda shaida a kan al’amuran da za a yi maganarsu a gaba, 6 amma Almasihu ya riƙi amana, yana mulkin jama’ar Allah a kan shi Ɗa ne, mu ne kuwa jama’atasa, muddar mun tsaya gabanunu gaɗi, muna taƙama da sazuciyarmu Rvvarai.

Gargadi kan Rashin Bangaskiya

7 Saboda haka, kamar yadda Ruhu Tsattsarka ya ce,

“Yau in kun, ji muryarsa,
8 Kada ku taurare zukatanku kamar a lokacin tawayen nan,
Wato ranar gwaji a Jeji,
9 Inda kakanninku suka gwada ni, suka jarraba ni,
Suna ganin ayyukana har shekara arba’in.
10 Saboda haka ne na yi fushi da wannan zamani,
Har na ce, ‘Har abada a sangarce su ke,
Ba su kuwa bi hanyoyina ba.’
11 Sai na yi rantsuwa ina mai fushi, na ce,
‘Ba za su shiga inuwata ba sam.’ “

12 Ku kula fa, ’Yan’uwa, kada wata muguwar zuciya marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗad da ku daga wurin Allah Rayayye. 13 Sai dai kowace rana ku ƙarfafa wa juna gwiwa muddar kuna raye, don kada kowannenku ya taurare, ta yaudarar zunubi. 14 Don kuwa mun zama masu tarayya da Almasihu, muddar muna tsaye kan amincewan nan tamu. ta fari tsaiwar daka, har ya zuwa ƙarshe. 15 Don kuwa an ce,

“Yau in kun ji muryarsa,
Kada ku taurare zukatanku kamar a lokacin tawayen nan.”

16 To, suwanene suka ji, duk da haka suka yi tawaye? Ashe ba duk waɗanda suka fito daga ƙasar Masar ba ne, waɗanda Musa ya shugabanta? 17 Da suwa kuma ya yi fushi har shekara arba’in? Ashe ba da waɗanda suka ɗau zunubi ba ne, waɗanda gawawakinsu suka ruɓe a Jeji? 18 Suwa kuma ya rantse wa, cewa ba za su shiga inuwatasa ba, im ba marasa biyayyan nan ba? 19 Sai muka ga ashe, saboda rashin bangaskiyarsu ne suka kasa shiga.

4

Kada fa wani ya Kasa shiga Inuwar Allah

Saboda haka, tun alkawarin shiga inuwarsa na nan, sai mu yi tsananin kula kada ya zamana waninku ya kasa shiga. 2 Ai kuwa an yi mana albishir kamar yadda aka yi musu, sai dai Maganad da aka yi musu ba ta amfane su da komai ba, don kuwa ba ta gamu da bangaskiya ga majiyanta ba. 3 Mu kuwa, da muka ba da gaskiya, muna shiga inuwar, yadda ya ce,

“Sai na yi rantsuwa ina mai fushi, na ce,
‘Ba za su shiga inuwata ba sam’”,

ko da ya ke ayyukan Allah gamanunu ne tun daga farkon duniya. 4 Don a wani wuri ya yi maganar rana ta bakwai, cewa, “A rana ta bakwai sai Allah ya huta daga ayyukansa duka.” 5 Amma a wannan wurin kuwa sai ya ce,

“Ba za su shiga inuwata ba sam.”

6 Wato tun da ya ke har yanzu dai da sauran dama waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kasa shiga saboda rashin biyayya, 7 to, sai ya sake sa wata ranar, ya ce, “Yau”, yana magana ta bakin Dawuda bayan wani zamani mai tsawo, da kalmomin nan da aka ambata dazu, cewa,

“Yau in kun ji muryarsa,
Kada ku taurare zukatanku.”

8 Da dai Yusha’u ya kai su inuwar Allah, da Allah bai yi maganar wata ranar daga baya ba, 9 wato ke nan har yanzu dai akwai sauran wani hutun Asabar ga jama’ar Allah, 10 don kuwa duk wanda ya shiga inuwar Allah, ya huta ke nan daga ayyukansa, kamar yadda Allah ya huta daga nasa.

11 Saboda haka sai mu yi himmar shiga inuwan nan, kada wani ya kuskure shiga saboda irin wannan rashin biyayyar. 12 Don Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufatata. 13 Ba wata halittad da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili ya ke, a shanye sosai a gaban idon wannan da ya ke da mu.

Yesu Ɗan Allah Shugaba ga Kusantar Allah ne Maigirma

14 To, tun da mu ke da Shugaba ga kusantar Allah, Maigirma wanda ya ratsa Sammai, wato Yesu ɗan Allah, sai mu tsaya kan abin da muka bayyana yarda gare shi, tsaiwar daka. 15 Don kuwa ba Shugaba ga kusantar Allah wanda ba ya iya jin tausayimmu kan gajiyawarmu ne mu ke da shi ba, a’a, namun wanda ya sha gwaji ne ta kowane hali kamarmu, sai dai bai ɗan zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu kusanci gadon sarautar Allah na alheri cikin amincewa, don a yi mana rahama, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.

5

Fifikon Almasihu a kan Haruna

Kowane shugaba ga kusantar Allah, da ya ke an zaɓe shi ne daga cikin mutane, a kan sanya shi ne ya wakilci mutane ga al’amarin Allah, don ya miƙa baiko da kuma hadaya don kau da zunubai. 2 Ya kuma zamana wanda zai iya tafiya da jahilai da sangartattu cikin sanyin-hali, tun da ya ke raunana ta kewaye shi ta ko’ina. 3 Saboda haka lalle ne ya miƙa hadaya, ba saboda kau da zunuban jama’a kaɗai ba, bar ma don nasa. 4 Kuma ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ne ke kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.

5 Haka kuma Almasihu ba shi ya ɗaukaka kansa ya zama Shugaba ga kusantar Allah ba, sai dai wannan ne ya sanya shi, wanda ya ce da shi,

“Kai Ɗana ne,
Na mai da kai Ɗana yau.”
6 Kamar dai yadda a wani wuri ma ya ce,
“Kai mai kusantar Allah ne na bar abada,
Kwatankwacin Malkisadik.”

7 Almasihu, a lokacin zamansa na duniya, ya yi addu’a da roƙo, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da ke da ikon kuɓutad da shi daga ƙangin mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin mifra wuyansa. 8 Ko da ya ke shi ɗan Allah ne, ya koyi biyayya ta wuyad da ya sha, 9 kuma da ya kai ga kammala, sai ya zama tushen madawwamin ceto ga dukkan waɗanda su ke masa biyayya, 10 don Allah na kiransa Shugaba ga kusantar Allah, kwatankwacin Malkisadik.

11 Muna da abin faɗa mai yawa game da shi kuwa, amma zai yi wuyar bayani, da ya ke basirarku ta dushe. 12 Ko da ya ke kamar yanzu kam ai ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka ashe ba ku wuce wani ya sake koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, bar ya zamana sai am ba ku nono, ba abinci mai tauri ba. 13 Ai duk wanda ya ke nono ne abincinsa, bai kware da maganar aikin gaskiya ba, kamar jariri ya ke. 14 Amma abinci mai tauri ai na manya ne, wato, waɗanda hankalinsu ya horu. yau da kullum, su rarrabe kyakkyawa da mummuna.

6

Gargadi Mai Tsanani

Saboda haka sai mu ci gaba a kan ka’idodin farko na al’amarin Almasihu har ya zuwa kammala, ba wai mu sake koyad da jigajigan nan na tuba da ibada maras tasiri ba, da na gaskatawa da Allah, 2 da kuma na koyarwa kan wanke-wanke, da ɗora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukunci. 3 Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda. 4 Don ba mai yiwuwa ba ne waɗanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka ɗanɗana baiwan nan ta Sama, suka kuma zama masu tarayya da Ruhu Tsattsarka, 5 har suka ɗanɗana daɗin Maganar Allah da ikon zamani mai zuwa, 6 sa’an nan kuma suka ridda, ba mai yiwuwa ba ne a sake jawo su ga tuba, tun da ya ke sake giciye ɗan Allah su ke yi, su da kansu, su ke kuma wulakanta shi a sarari. 7 Ƙasa ma da ke shanye ruwan da a ke yi mata a kai a kai, ta ke kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda a ke noma ta dominsu, Allah ya kan yi mata albarka. 8 Amma in tsire-tsirenta ƙaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, kuma tana gab da la’antarwa, karkonta dai konewa ne.

9, Ko da ya ke mun faɗi haka, game da ku kam, ya ƙaunatattu, mun tabbata kuna kan abubuwa mafiya kyau na game da ceto, 10 Gama Allah ba marar gaskiya ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi wajen yi wa tsarkaka gudummawa, bar yanzu ma kuna yi. 11 Muna dai bukata ƙwarai kowannenku ya nuna irin wannan himma ga yin cikakkiyar sazuciya, tabbatacciya, har ya zuwa ƙarshe, 12 don kada ku kwanta da sirdi, sai dai ku yi koyi da waɗanda suka sami cikar alkawaran nan, ta bangaskiyatasu da haƙurinsu.

13 Sa’ad da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da ya ke babu wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa, 14 ya ce, “Hakika zan yi maka albarka, in kuma riɓanya zuriyarka.” 15 Ta haka Ibrahim, bayan ya jure da haƙuri, ya sami cikar alkawarin. 16 Hakika mutane su kan rantse da abin da ya fi su, kuma rantsuwa ita ce abar tabbatarwa a duk lokacin gardama. 17 Don haka sa’ad da Allah ke son ƙara tabbatar wa magadan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai canzuwa ba ne samsam, sai ya haɗa da rantsuwa, 18 don albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa canzuwa, masu nuna cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu sami ƙarfin-gwiwa ƙwarai mu riski abin da muka sa zuciya a kai. 19 Sazuciyan nan kuwa da mu ke da ita, kamar turke ta ke ga rai, kafaffiya, tabbatacciya, ita ce kuma ke shiga bar cikin Wuri Mafi Tsarkaka, can bayan Labule, 20 inda Yesu ya shiga saboda mu, yana mana jagaba, da ya ke ya zama Shugaba ga kusantar Allah na har abada, kwatankwacin Malkisadik.

7

An Canza Irin Hanyar Kusantar Allah

Shi wannan Malkisadik, Sarkin Shalima, mai kusantar Allah Maɗaukaki, ya gamu da Ibrahim a lokacin da Ibrahim ke dawowa daga kisan sarakuna, ya sa masa albarka. 2 Shi ne kuwa Ibrahim ya ba ushirin komai. Da farko dai, kamar yadda ma’anar sunansa ta ke, shi sarkin gaskiya ne, sa’an nan kuma Sarkin Shalima ne, wato sarkin aminci. 3 Shi ba shi da uwa ko uba, ba a kuma san asalinsa ba. Ba shi da ranar haifuwa balle ranar mutuwa, yana dai kama da Ɗan Allah, yana mai kusantar Allah na har abada.

4 Kai, ku dubi irin girmansa! Har kakammu Ibrahim ma ya ba shi ushirin gamma! 5 Ga shi kuma wasu daga cikin zuriyar Lawi, in sun karɓi hidimar kusantar Allah, a kan umarce su bisa Shari’ar Musa su karɓi ushiri a gun jama’a, wato a gun ’yan’uwansu, ko da ya ke su ma zuriyar Ibrahim ne. 6 Amma wannan, wanda ma ba a zuriyar Lawi ya ke ba, ya karɓi ushiri a gun Ibrahim, har ya sa masa albarka, shi ma da aka yi wa alkawarai. 7 Ai ba abin musu ba ne cewa na gaba shi ke sa wa na baya albarka. 8 Ga shi a nan masu karɓar ushiri, mutane ne masu mutuwa ko badaɗe, a can kuwa mai karɓan, wanda aka shaida a kan shi rayayye ne. 9 A ma iya cewa ko Lawi ma kansa, mai karɓar ushiri, ya ba da ushiri ta kan Ibrahim, 10 don shi Lawi na tsatson kakansa Ibrahim, sa’ad da Ibrahim ɗin ya gamu da Malkisadik.

11 To, in da mai yiwuwa ne a sami kammala ta kusantar Allah bisa hanyar Lawi, (don ta gare ta ne jama’a suka karɓi Shari’ar Musa), wace bukata kuma a ke da ita ta wani mai kusantar Allah daban ya bayyana kwatankwacin Malkisadik, wanda za a ambata ba kwatankwatin Haruna ba? 12 Don in an canza irin hanyar kusantar Allah, sai tilas a canza Shari’a kuma. 13 Don kuwa shi wannan da aka faɗi waɗannan abubuwa game da shi, ai na wata kabila ne daban, wadda ba waninta da ya taɓa hidima Wurin Baiko. 14 Tabbatacce ne cewa Ubangijimmu ya fito daga zuriyar Yahuda ne, Musa kuwa bai ce komai ba game da kabilan nan kan zancen masu kusantar Allah.

Yesu Mai Kusantar Allah ne na Har abada

15 Wannan kuma ya ƙara fitowa fili warkan, sa’ad da wani mai kusantar Allah daban ya bayyana kamar Malkisadik, 16 wanda kuwa ya zama mai kusantar Allah, ba ta wata salsala ta ka’idar Shari’a ba, sai dai ta ikon rai marar gushewa. 17 Don an shaide shi da cewa,

“Kai mai kusantar Allah ne na bar abada,
Kwatankwacin Malkisadik.”

18 Ta wani halin an soke wani umarni na dā saboda rauninsa da kuma rashin amfaninsa 19 —don Shari’ar Musa ba ta kammala komai ba—ta wani halin kuma an shigo da wata sazuciya wadda ta ke mafi kyau, ta kanta kuwa mu ke kusantar Allah.

20 Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. 21 Waɗancan sun zama masu kusantar Allah ba tare da an yi musu rantsuwa ba, amma wannan kam sai da aka yi masa rantsuwa, da Allah ya ce masa,

“Ubangiji ya rantse,
Ba kuwa zai ta da maganatasa ba, cewa,
‘Kai mai kusantar Allah ne na bar abada.’”

22 A sanadin wannan ne Yesu ya zama lamunin alkawarin da ya fi wancan nesa.

23 Waɗancan masu kusantar Allah an yi su da yawa, don mutuwa ta hana su tabbata a cikin aikin. 24 Amma shi da ya ke madawwami ne, yana da matsayinsa na kusantar Allah wanda ba ya komawa hannun wani. 25 Saboda haka yana iya ceton masu kusantowa ga Allah ta kansa, matuƙar ceto, tun da ya ke kullum a raye ya ke saboda yi musu addu’a.

26 Irin Shugaba ga kusantar Allah da mu ke bukata ke nan, tsattsarka, marar aibu, marar tabo, keɓaɓɓe daga masu zunubl, kuma ɗaukakakke birbishin Sammai. 27 Ba sai ya miƙa hadaya kowace rana kamar waɗancan shugabanni ga kusantar Allah ba, wato da farko saboda zunubansu, sa’an nan kuma. saboda na jama’a. Ta yayyau ɗin ya yi ta ne sau ɗaya tak ba sakewa, lokacin da ya miƙa kansa hadaya. 28 Wato Shari’a tana shugabantad da mutane ga kusantar Allah da rauninsu, amma maganan nan ta rantsuwa da ta sauko bayan Shari’a, ta sanya Ɗa wanda ya ke kammalalle ne har abada.

8

Sabon Wuri Mafi Tsarkaka da Sabon Alkawari

Wato, duk manufar maganarmu dai ita ce wannan. Shi ne irin Shugaba ga kusantar Allah da mu ke da shi, wato wanda ya zauna a hannun dama na gadon sarautar Maɗaukaki a can Sama, 2 mai hidima a Wuri Mail Tsarkaka, da kuma Alfarwa ta gaske, wadda Ubangiji ya kafa, ba mutum ba. 3 Kowane shugaba ga kusantar Allah a kan sanya shi ne don ya miƙa baiko da hadaya; saboda haka wajibi ne wannan shi ma ya zamanto yana da abin da zai miƙa. 4 To, ashe da har yanzu yana duniya, da bai zama mai kusantar Allah ba ke nan, tun da ya ke akwai masu kusantar Allah da ke miƙa baiko bisa Shari’ar Musa. 5 Suna bauta wa makamantan abubuwan Sama da kuma ishararsu, kamar yadda Allah ya gargaɗi Musa sa’ad da ya ke shirin kafa Alfarwan nan, da ya ce, “Ka lura fa ka shirya komai da komai daidai yadda aka nuna maka a kan Dutsen.” 6 Amma ga ainihi, Almasihu ya sami hidima wadda ta ke mafificiya, kamar yadda alkawarin nan da ya ke sadarwa ya ke da fifiko nesa, tun da ya ke an kafa shi ne a kan mafifitan alkawarai. 7 Don da wancan alkawari na farko bai gaza da komai ba, da ba sai an sake neman na biyu ba.

8 Gama ya ga laifinsu da ya ce,

“Lokaci na zuwa, in ji Ubangiji,
Da zan yi sabon alkawari da Bani Isra’ila
Da kuma zuriyar Yahuda.
9 Ba irin alkawarin da na yi da kakanninsu ba,
A ranad da na kama hannunsu
Don in fito da su daga ƙasar Masar.
Saboda ba su tsaya ga alkawarina ba,
Shi ya sa na ƙi kula da su, in ji Ubangiji,
10 Wannan shi ne alkawarin da zan yi da Bani Isra’ila,
Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji,
Wato zan sanya Shari’ata a birnin zuciyarsu,
In kuma rubuta ta a allon zuciyarsu.
Zan kasance Allahnsu,
Su kuma su kasance jama’ata.
11 Ba kuma sai sun koya wa juna ba,
Balle wani ya ce da ɗan’uwansa,
‘Kă san Ubangiji mana!’
Don kowa zai san ni,
Daga ƙaraminsu har ya zuwa babbansu.
12 Don zan yi musu rahama kan rashin gaskiyarsu,
Ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”

13 Da ya ce sabon alkawari, ashe kuwa ya mai da na farkon tsoho ke nan. Abin da kuwa ke tsufa, yana kuwa dada tsofewa, lalle ya yi kusan shuɗewa ke nan.

9

Fasalin Alfariyar Duniya

To, ko da alkawarin farko ma yana da ka’idodinsa na bautar Allah, da kuma Wuri Tsattsarka a duniya. 2 Wato an kafa Alfarwa wadda ta baryar farko ke da fitila, da tebur, da kuma. keɓaɓɓen burodi. Ana kiran wannan ɓarya Wuri Tsattsarka. 3 Bayan Labule na biyu kuma akwai ɓaryar Alfarwad da a ke kira Wuri Mafi Tsarkaka. 4 A cikinsa kuwa da Wurin ƙona turaren wuta na zinariya, da kuma Sunduƙin Alkawari da aka yi masa laffa da zinariya ta kowane gefe. A cikinsa kuwa akwai tasar zinariya, da manna a ciki, da sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutse na alkawarin nan. 5 A bisa Sunduƙin nan kuma akwai cerabobin nan na ɗaukakar Allah, waɗanda suka yi wa wurin nan na kankare zunubi laima. Ba za mu iya yin maganar waɗannan abubuwa filla-filla ba a yanzu.

6 In an gama waɗannan shirye-shirye haka, sai masu kusantar Allah kullum su riƙa shiga ɓaryar farko ta Alfarwar, suna hidimarsu ta ibada. 7 Amma ta biyun sai shugaba ga kusantar Allah kaɗai ke shiga, shi ma kuwa sai sau ɗaya a shekara, sai kuma da jini, wanda ya kan miƙa hadaya saboda kansa, da kuma kurakuran jama’a. 8 Ta haka Ruhu Tsattsarka ya ke yin ishara, cewa ba a buɗe hanyar shiga Wuri Mafi Tsarkaka ba tukuna, muddar ɓaryar farko ta Alfarwa na nan tsaye, 9 wadda ta ke ishara ce ga wannan zamani. Bisa ga wannan ishara a kan yi ta miƙa baiko da hadaya, amma ba sa iya kammala zuciyar mai ibadar, 10 sai al’amarin ci da sha da wanke-wanke iri-iri su ke shafa, ka’idodi game da jiki kurum, waɗanda aka sanya kafin a daidaita al’amari.

Almasihu Ya buɗe Hanyar Shiga Wuri Mafi Tsarkaka a Sama

11 Amma da Almasihu ya bayyana a kan shi Shugaba ga kusantar Allah ne, game da kyawawan abubuwan da ke hannu, sai ya shiga ta cikin Alfarwan nan mafi ɗaukaka, mafi kammala, (wadda ba mutun ne ya yi ba, wato, ba irin ta wannan halitta ba), 12 ya shiga Wuri Mafi Tsarkaka sau ɗaya tak ba kari, ba kuwa ta jinin awaki ko na ’yam maruka ya shiga ba, sai dai ta nasa jinin, ya samo mana madawwamiyar fansa. 13 To, jinin awaki ne fa da na bajimai, da kuma tokar karsana da a ke yayyafa wa waɗanda suka ƙazantu, su ke keɓe su a tsarkake, tsarki na zahiri, 14 ballantana jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake zukatanku daga barin ibada maras tasiri, don ku bauta wa Allah Rayayye.

15 Saboda haka shi ne mai sadad da sabon alkawari, don waɗanda aka kira su karɓi dawwamammen gadon da aka yi musu alkawari, tun da ya ke an yi wata mutuwa mai fansar waɗanda suka keta umarni game da alkawarin farko. 16 Game da al’amarin wasiyya, lalle ne a tabbatad da mutuwar wanda ya yi ta tukun. 17 Don ba a zartad da wasiyya sai bayan am mutu, tun da ya ke ba a yin aiki da ita muddar wanda ya yi ta na raye. 18 Ashe kuwa mun ga alkawarin nan Ɗa farko, ba a tabbatad da shi ba sai game da jini. 19 Don bayan Musa ya sanad da kowane umarnin Shari’a ga dukkan jama’a, sai ya ɗebi jinin ’yam maruka da na awaki, tare da ruwa, da jan ulu, da kuma ganyen izoba, ya yayyafa wa Littafin kansa, da kuma duk jama’a, 20 yana cewa, “Wannan shi ne jini na tabbatar alkawarin nan, da Allah ya yi umarni game da ku.” 21 Haka kuma ya yayyafa jinin ga Alfarwan nan, da dukkan kayanta na yin hidima. 22 Hakika, bisa Shari’ar Musa, kusan kowane abu da jini a ke tsarkake shi, im ba game da zub da jini ba kuwa, babu gafara.

Almasihu ya Shiga Sama Kanta saboda mu

23 Da waɗannan abubuwa ne ya wajaba a tsarkake makamantan abubuwan da ke Sama, sai dai ainihin abubuwan Saman za a tsarkake su ne da hadaya mafi waɗannan daraja. 24 Don Almasihu bai shiga cikin Wuri Tsattsarka da mutun ya yi ba, wanda ya ke sura ne kawai na gaskantaccen, a’a, Sama kanta ya shiga, don yi bayyana a gaban Zatin Allah a yanzu, saboda mu. 25 Ba kuwa don ya riƙa miƙa kansa hadaya a kai a kai ba ne, kamar yadda shugaba ga kusantar Allah ke shiga Wuri Mafi Tsarkaka a kowace shekara da jinin da ba nasa ba. 26 In da haka ne, ashe da sai lalle ya yi ta shan wuya a kai a kai ke nan, tun daga farkon duniya. Amma yanzu ga shi ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamani, don ya kau da zunubi ta miƙa kansa hadaya. 27 Kuma tun da ya ke an ƙaddara wa ɗan’adan ya mutu sau ɗaya ne, bayan haka kuma sai shari’a, 28 shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak ba ƙari, don ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sake bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kau da zunubi ba, sai dai don yd ceci waɗanda su ke dokin zuwansa.

10

Shari’ar Musa Ishara ce kawai

To, tun da ya ke Shari’ar Musa ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da ke gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe har abada ba za ta iya kammala waɗanda ke kusantar Allah ta waɗannan hadaya ba, waɗanda a ke yi a kai a kai a kowace shekara. 2 In haka ne kuwa, ashe ba sai a daina yin hadayar ba? Da an taɓa tsarkake masu ibadan nan sarai, ai da an ɗauke musu ilIar zunubansu ɗungum. 3 Amma game da irin waɗannan haɗayu, a kan tuna zunubai a kowace shekara. 4 Don ba mai yiwuwa ba ne jinin bajimai da na awaki ya ɗauke zunubi.

“Na zo in aikata nufinka, ya Allah”

5 Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce,

“Haɗaya da baiko kam ba ka so,
Amma kā tanadar mini jiki.
6 Ba ka farinciki da hadayar ƙone-ƙone, da kuma hadayar kau da zunubai.
7 Sa’an nan na ce, ‘Ga ni na zo in aikata nufinka, ya Allah’,
Kamar yadda ya ke rubuce game da ni a Littafi.”

8 Sa’ad da ɗazu ya ce, “Ba ka son hadaya, da baiko, da hadayar ƙone-ƙone, da hadayar kau da zunubai, ba ka kuwa jin daɗinsu”, wato irin waɗanda a ke miƙawa ta hanyar Shari’ar Musa, 9 sai kuma ya ƙara, da cewa, “Ga ni na zo in aikata nufinka.” Ya kau da na farkon ne, don yă kafa na biyun. 10 Kuma ta nufin nan ne aka keɓe mu a tsarkake, ta miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak ba ƙarl.

Almasihu ya Miƙa Kansa Haɗaya don Kau da Zunubi

11 Har wa yau kuma, kowane mai kusantar Allah ya kan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai, waɗanda har abada ba za su iya ɗauke zunubai ba. 12 Amma shi Almasihu da ya miƙa hadaya guda ta har abada don kau da zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah, 13 tun daga lokacin nan yana jira sai an sa ya take maƙiyansa. 14 Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka keɓe a tsarkake har abada. ’ 15 Ruhu Tsattsarka ma yana yi mana shaidar haka, don bayan ya ce,

16 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su,
Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji,
Zan sanya Shari’ata a birnin zuciyarsu,
In kuma rubuta ta a allon zuciyarsu”,

17 sai kuma ya ƙara da cewa,

“Ba kuma zan ƙara tunawa da zunubansu da laifuffukansu ba.”

18 To, inda aka sami gafarar waɗannan, ba sauran wata hadaya don kau da zunubi.

Muna da Amincewar Shiga Wuri Mafi Tsarkaka

19 Saboda haka ya ’Yan’uwa, tun da mu ke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarkaka, albarkacin jinin Yesu, 20 ta sabuwar hanya, rayayyiya, wadda ya buɗe mana ta Labulen nan, wato, jikinsa, 21 kuma da ya ke muna da mai kusantar Allah, Maigirma, mai mulkin jama’ar Allah, 22 sai mu matsa kusa da zuciya-ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatammu tsarkakakku daga illar zunubammu, jikimmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa. 23 Sai mu tsaya a kan bayyana yarda ga sazuciyan nan tamu, tsaiwar daka, don shi Mai yin alkawarin nan amintacce ne, 24 mu kuma riƙa kula da juna, ta yadda za mu ta da juna a tsimi bisa yin ƙauna da aiki nagari. 25 Kada mu bar yin tarommu, yadda wasu ke yi, sai dai mu ƙarfafa wa juna gwiwa, tum ba ma da kuka ga ranan nan tana kusatowa ba.

Matsanancin Gargaɗi

26 In kuwa mun ci gaba da ɗaukan zunubi da gangan, bayan mun yi na’am da sanin Gaskiya, to, ba fa sauran wata hadaya don kan da zunubai, 27 sai dai matsananciyar fargabar hukunci, da kuma wuta mai tsananin zafi wadda za ta cinye maƙiyan Allah. 28 Kowa ya ya da Shari’ar Musa, a kan kashe shi ba tausayi, a kan shaidu biyu ko uku. 29 To, mutumin da ya tirsasa Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka keɓe shi a tsarkake da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani ku ke tsammani ya cancanta fiye da wancan? 30 Don mun san shi, shi wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka.” Da kuma, “Ubangiji zai yi wa jama’atasa hukunci.” 31 Abu ne fa mai matuƙar ban tsoro a faɗa cikin hukuncin Allah Rayayye.

32 Amma dai ku tuna shekarun baya, bayan an haskaka zukatanku, kun jure tsananin fama da shan wuya, 33 wata rana ana zaginku, ana ta wahalshe ku, ana wulakanta ku a gaban jama’a, wata rana kuma kuna mai da kanku ɗaya da waɗanda aka yi wa haka. 34 Domin kun ji tausayin ɗaurarru, kun kuma yarda cikin daɗin-rai da wason da aka yi muku, tun da ya ke kun sakankance kuna da mallaka mafi kyau, mai tabbata kuwa. 35 Saboda haka kada ku ya da amincewan nan taku, don tana da sakamako mai yawa. 36 Gama yin jimiri ya kama ku, don bayan kun aikata nufin Allah, ku sami abin da aka yi muku alkawari.

37 “Sauran lokaci kaɗan,
Mai zuwan nan zai zo, ba kuwa zai yi jinkiri ba.
38 Amma mai samun karɓuwa gare ni, ta bangaskiya zai rayu.
Amma in ya ja da baya,
Ba zan yi farinciki da shi ba.”

39 Amma mu ba cikin waɗanda ke ja da baya su halaka mu ke ba; mu a cikin masu bangaskiya mu ke, mai kai mu ga ceton rayukammu.

Ƙarfin Bangaskiya

To, bangaskiya kuwa ita ce haƙƙaƙewar abubuwan da aka sa zuciya a kai, ita ce kuma tabbatarwar abubuwan da ba a gani ba. 2 Don ta gare ta ne shugabannin dā suka sami yardar Allah. 3 Ta bangaskiya muka fahinci cewa faɗar Allah ce ta halicci duniya, har ma abubuwan da a ke gani, daga abubuwan da ba a gani ne suka kasance.

4 Ta bangaskiya ne Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan ta Kayinu, ta wannan bangaskiyar ce kuma ya sami yardar Allah a kan shi mai aikin gaskiya ne, don Allah ma ya shaide shi, da ya karɓi abubuwan da ya bayar. Ya mutu kam, amma ta bangaskiyan nan tasa bar yanzu yana magana. 5 Saboda bangaskiya ne aka ɗauke Anuhu, shi ya sa bai mutu ba, ba a kuwa same shi ba, don Allah ya ɗauke shi. Tun kafin a ɗauke shi ma, an shaide shi a kan ya faranta wa Allah. 6 Im ba game da bangaskiya ba kuwa, ba shi yiwuwa a faranta masa. Don duk wanda zai kusanci Allah, lalle ne ya gaskata cewa akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa. 7 Ta bangaskiya ne Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al’amuran da ba a gani ba a lokacin, sai ya tsoraci Allah ya sassaka jirgi, don ceton iyalin gidansa; ta bangaskiyar ne kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, bar ya zama magajin karɓuwan nan ga Allah, wadda ke samuwa ta bangaskiya.

8 Ta bangaskiya ne Ibrahim ya yi biyayya, sa’ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasad da zai karɓa gado. Ya kuwa fita, bai ma san inda za shi ba. 9 Ta bangaskiya ne kuma ya yi baƙunci a ƙasar alkawari, kamar dai a ƙasar bare, suna zaune cikin alfarwoyi, shi da Isiyaku da Yakubu, abokan tarayya ga gadon alkawarin nan. 10 Yana ta jiran birnin nan mai tushe, wanda mai fasalta shi, kuma mai gina shi, Allah ne. 11 Ta bangaskiya ne Saratu kanta ta sami ikon yin ciki, ko da ya ke ta wuce lokacin haifuwa, tun da dai ta amince cewa shi Mai yin alkawarin nan amintacce ne. 12 Saboda haka, daga mutun ɗaya, wanda ma da shi da matacce kusan ɗaya ne, aka haifi zuriya masu yawa kamar taurari, kuma kamar yashi samama a bakin teku.

13 Waɗannan duka sun mutu kan bangaskiya, ba su kuwa samu abubuwan da aka yi musu alkawari ba, amma da suka tsinkayo su, sai suka yi ta murna da ganinsu, suna kuma yarda cewa su baƙi ne, bare a duniya. 14 Mutane masu irin wannan magana ai sun bayyana a fili cewa suna neman gijiya ne. 15 Da suna marmarin ƙasan nan da suka baro ne, da sun sami damar komawa. 16 Amma bisa hakika sun ɗokanta ne a kan wata ƙasa mafi kyau, wato ta Sama. Saboda haka ne Allah ba ya ƙyamar a kira shi Allahnsu, don kuwa ya shirya musu birni.

17 Ta bangaskiya ne Ibrahim, sa’ad da aka gwada shi, ya miƙa Isiyaku hadaya, wato, shi da ya yi na’am da alkawaran nan, ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa, 18 wanda a kansa aka yi faɗi, cewa, —“Ta kan Isiyaku ne za a bi salsalar zuriyarka.” 19 Ya amince cewa Allah har ma na iya ta da mutun daga matattu. Ai kuwa bisa misali sai a ce daga matattu ne ya sake samun Isiyaku. 20 Ta bangaskiya ne Isiyaku ya sa wa Yakubu da Isuwa albarka a kan al’amuran da za su zo. 21 Ta bangaskiya ne Yakubu, sa’ad da ya ke bakin mutuwa, ya sanya wa ’ya’yan Yusufu albarka dukkansu biyu, ya kuma yi sujada, yana sunkuye a kan sanɗansa. 22 Ta bangaskiya ne Yusufu, da ajalinsa ya yi, ya yi maganar ƙaurar Bani Isra’ila, har ya yi wasiyya game da ƙasusuwansa.

23 Ta bangaskiya ne, sa’ad da aka haifi Musa, iyayensa suka ɓoye shi bar wata uku, don sun ga yaron kyakkyawa ne, kuma ba su ji tsoron umarnin sarki ba. 24 Ta bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya girma, ya ƙi yarda a kira shi ɗan ’yar Fir’auna, 25 ya gwammaci ya jure shan wuya tare da jama’ar Allah, a kan ya mori romon zunubi, mai saurin wucewa. 26 Ya amince cewa wulakanci saboda Almasihu arziki ne a gare shi fiye da arzikin ƙasar Masar, don yana ƙura ido ne a kan sakamakon. 27 Ta bangaskiya ne ya bar Masar, bai ji tsoron fushin Sarki ba; ya kuwa jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa. 28 Ta bangaskiya ne ya ci Jibin Ƙetarewa, ya yayyafa jini, don kada Mai hallaka ’ya’yan fari ya taɓa Bani Isra’ila.

29 Ta bangaskiya ne suka ƙetare Bahar Maliya ta kan busasshiyar ƙasa, amma da Misirawa suka yi ƙoƙarin yin haka, sai aka dulmuyad da su. 30 Ta bangaskiya ne ganuwar Yariko ta rushe, bayan an yi ta kewaya ta bar kwana bakwai. 31 Ta bangaskiya ne Rahaba karuwan nan ba ta halaka tare da maƙiya biyayya ba, ta karɓi ’yan ganganen nan kamar ’yan’uwa.

32 Me kuma zan ƙara cewa? Ai lokaci zai ƙure min wajen ba da labarin su Gidiyan, da Baraka, da Shamsuna, da Yaftaha, da Dawuda, da Samu’ila, da kuma annabawa, 33 waɗanda ta bangaskiya suka ci masarautu, suka aikata gaskiya, suka sami cikar alkawura, suka rurrufe bakunan zakoki, 34 suka im ma ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar wasu ƙasashe. 35 Am mayar wa mata da mutanensu da aka tasa daga matattu. Wasu mutane kuma an azabta su har suka mutu, amma sun ƙi yarda da irin shikan da za a yi musu, don su sake rayuwa mafi kyau a gaba. 36 Har wa yau kuma waɗansu suka sha ba’a da bulala, bar ma da ɗauri da jefawa kurkuku. 37 An jajjefe su da duwatsu, an gwada su, an raba su biyu da zarto, an sare su da takobi. Sun yi yawo rataye da buzun tumaki da na awaki, suna zaman rashi, da ƙunci, da wulakanci. 38 Su kam duniya ba ta ma cancanci su zauna a cikinta ba. Sun yi yawo a dazuzuwa da kan duwatsu, suna kwana a cikin kogwanni da ramuka.

39 Waɗannan duka, ko da ya ke Allah ya shaide su saboda bangaskiyarsu, duk da haka ba su sami cikar alkawarin ba, 40 tun da Allah ya gine mana wani abu mafi kyau, sai kuwa tare da mu ne za a kammala su.

12

Yesu ne Shugaban Bangaskiyarmu

Saboda haka, tun da taron shaidu masu dumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu ya da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya dafe mana dadaf, mu kuma yi tseren nan da ke gabammu tare da jimiri, 2 muna zuba ido ga Yesu, shi da ya ke Shugaban bangaskiyarmu, kuma Cikamakinta, wanda don farincikin da ke gabansa ya ɗaure wa giclye, bai mai da shi wani abin kunya ba, yanzu kuma ya ke zaune a hannun dama na gadon sarautar Allah.

Wanda Allah Ke Ƙauna shi ya ke Horo

3 Ku fa dubi wannan da ya jure irin gāban nan da masu zunubi suka sha yi da shi, don kada ku gaji, ko kuwa ku karai. 4 Famanku da zunubi bai kai bar yadda za a kashe ku ba. 5 Kun kuma mance da gargaɗin nan da Allah ya yi muku a kan ku ’ya’yansa ne, wato,

“Ya ɗana, kada ka raina horon Ubangiji,
Kada kuma ka karai, in ya kwaɓe ka.
6 Don Ubangiji, wanda ya ke ƙauna, shi ya ke horo,
Ya kan kuma hori duk ɗan da ya karɓa.”

7 Shan-wuyad da ku ke jurewa ai duk don horo ne. Allah ya riƙe ku a kan ku ’ya’yansa ne. To, wane da ne ubansa ba ya horonsa? 8 In kuwa ba ku da horo, irin horon da a ke yi wa kowa, to ashe kun zama shegu ke nan, ba ’yan halal ba. 9 Har wa yau kuma ai muna da ubannimmu na duniya da suka hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe ba za mu fi miƙa wuya ga Uban ruhohimmu ƙwarai ba, mu rayu? 10 Su kam sun hore mu a ɗan lokaci kaɗan don ganin damansu, amma shi, don amfanin kammu ne ya ke horommu, don mu rabanta a cikin tsarkakarsa. 11 Ai kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙinciki, ba na farinciki ba, amma kuwa daga baya ya kan sa kwanciyar-rai wadda aikin gaskiya ke haddasawa, ga waɗanda suka horu ta haka.

Ku Farfaɗa, Ku Tashi Tsaye

12 Don haka sai ku farfaɗo, ku tashi tsaye. 13 Ku bi miƙaƙƙun hanyoyi totar, don kada mai dingishi ya gulle, maimakon ya warke. 14 Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, da kuma samun tsarkakad da im ba game da ita ba, ba wanda zai ga Ubangiji. 15 Ku kula fa, kada kowa ya kasa samun alherin Allah, kada kuma wani ɗacin-rai ya wakana, ya haddasa ɓarna, bar ya ɓata mutane masu yawa ta haka; 16 kada kuma wani ya zama fasiki, ko mai saɓon Allah, kamar Isuwa, wanda ya sai da hakkinsa na dam-fari kan cimaka ɗaya tak. 17 Kun dai san daga baya, da ya so ya gaji albarkan nan, sai aka ƙi shi, don bai sami hanyar gyara al’amarin ba, ko da ya ke ya yi ta nemanta har da hawaye.

18 Ai ba abin da za a taɓa ne kuka iso ba, ko wuta mai ruruwa, ko baƙin duhu, duhun ƙirin, ko hadiri, 19 ko karar kakaki, ko wata murya, wadda har masu jin maganarta suka yi roƙo kada su ƙara jin aiken, 20 don ba su iya jure umarnin da aka yi musu ba, cewa, “Ko da dabba ce ta taɓa Dutsen, sai a kat ta da jifa.” 21 Kai, amma ganin wannan abu da matuƙar ban tsoro ya ke! bar ma Musa ya ce, “Ina rawar jiki don matuƙar tsoro.” 22 Amma ku kun iso Dutsen Sihjyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala’iku, 23 da masu taron murna, da kuma wurin taron magada, waɗanda sunayensu ke rubuce a Sama, da kuma wurin Allah, wanda ya ke shi ne Mai yi wa kowa shari’a, da, kuma wurin ruhohin mutane masu gaskiya, waɗanda aka kammala, 24 da kuma wurin Yesu, mai sadad da sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda ya ke mafificiyar magana a kan na Habila.

25 Ku kula fa kada ku ƙi Mai maganan nan. Don in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, im mun ƙi jin wannan da ke mana gargaɗi ma daga Sama? 26 A lokacin nan muryarsa ta girgiza ƙasa, amma yanzu ya yi alkawari, cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak, ba ƙasa kaɗai zan girgiza ba, har sama ma.” 27 To, wannan ƙauli cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak”, ya nuna kau da abubuwan da aka girgiza, wato, abubuwan da aka halitta, don abubuwan da ba sa girgizuwa su wanzu. 28 Saboda haka sai mu yi godiya don mun rabanta cikin mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah bauta mai karɓuwa, tare da tsoro da tsananin miƙa wuya, 29 don Allahmmu wuta ne mai cinyewa.

13

Ku Nace da Ƙaunar ’Yan’uwa da yin Aiki Nagari

Sai ku nace da ƙaunar ’Yan’uwa. 2 Kada ku yi sake da yi wa baƙi alheri, gama ta haka ne wasu suka sauki mala’iku ba su san mala’iku ba ne. 3 Ku riƙa tunawa da waɗanda ke kurkuku, kamar tare ku ke ɗaure, da kuma waɗanda a ke gwada wa wuya, kamar ku a ke yi wa. 4 Kowa yd girmama aure. Gădon aure kuwa ya zauna marar dauda, don fasikai da mazinata Allah zai hukunta su. 5 Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da ku ke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” 6 Saboda haka ma iya fitowa gabagaɗi, mu ce,

“Ubangiji shi ne mataimakina,
Ba zan ji tsoro ba.
Me mutun zai iya yi mini?”

Mu Tsaya ga Almasihu

7 Ku tuna da shugabanninku na dā waɗanda suka faɗa muku Maganar Allah. Ku dubi ƙarkonsu, ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu. 8 Yesu Almasihu ba ya canzawa, shi ne a jiya, da yau, hakika har abada ma. 9 Kada baƙuwar koyarwa iri-iri ta bauɗad da ku, ai abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi ke ƙarfafa zuciya, ba abinci iri-iri na baiko ba, waɗanda ba sa amfani ga masu dogara da su. 10 Muna da Wurin da aka yi Hadaya, wanda masu ibada a Alfarwan nan ba su da izini su ci abincin wurin, 11 domin naman dabbobin da shugaba ga kusantar Allah ke ɗiban jininsu yă kai Wuri Mafi Tsarkaka don kau da zunubai, a kan ƙone shi ne a bayan sansani. 12 Haka ma Yesu ya sha wuya a bayan gari, don yă keɓe jama’a a tsarkake da nasa jinin. 13 Saboda haka sai mu fita mu je gare shi a bayan sansani, muna, shanye irin wulakancin da aka yi masa. 14 Don ba mu da wani dawwamammen birni a nan, bimin nan mai zuwa mu ke nema. 15 To, koyaushe sai mu yi ta yabon Allah ta kansa, baikon da mu ke miƙawa ke nan, wato, mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa 16 Kada kuwa ku yi sake da yin alheri da ba da gudummawa, don irin waɗannan baiko su ke faranta wa Allah.

17 Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku miƙa wuya gare su, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za a tambaya hakkinku, don su samu su yi haka da farinciki, ba da baƙinciki ba, don in sun yi da baƙinciki ba zai amfane ku ba.

18 Ku yi mana addu’a, don mun tabbata zuciyarmu garau ta ke, muna fa so mu tafi da al’amurammu da halin kirki ne. 19 Musamman na ke tsananta roƙonku ku yi haka, don a hanzarta komo da ni gare ku.

20 Allah Mai haddasa aminci, wanda ya taso Ubangijimmu Yesu, Makiyayin tumaki Maigirma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari, 21 yă kammala ku da kowane irin kyakkyawan abu don ku aikata nufinsa, ya kuma aikata abin da ke faranta masa a zukatanku, ta kan Yesu Almasihu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.

22 To, ina roƙonku, ’Yan’uwa, ku yi haƙuri da gargaɗina, don a taƙaice na rubuto muku. 23 Ku fahinci cewa an sau Ɗan’uwammu Timotawas, da shi ma za mu gan ku, in ya zo da wuri. 24 Ku gai da dukkan shugabarminku, da kuma dukkan tsarkaka. Waɗanda ke daga ƙasar Italiya na gaishe ku. 25 Alherin Ubangiji yă tabbata a gare ku, ku duka. Amin.


WASIKAR
YAKUBU

1

Daga Yakubu, bawan Allah, kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilun nan goma sha biyu da ke warwatse a duniya Gaisuwa mai yawa.

Jarrabawar Bangaskiya

2 Ya ku ’Yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje iri-iri suka same ku, ku mai da su abin farinciki ƙwarai. 3 Don kun san jarrabawar bangaskiyarku ta kan haifi jimiri. 4 Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, don ku zama kamilai, kuma cikakku, ba ku gaza da komai ba.

5 In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi. 6 Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman-ruwan teku ya ke, waɗanda iska ke korawa tana tuttunkuɗawa. 7-8 Kada irin mutumin nan mai ruwan ido, wanda bai tsai da zuciyarsa gu ɗaya cikin dukkan al’amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.

9 Ƙaskantaccen Ɗan’uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa. 10 Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa. 11 In rana ta tāke da ƙunanta, sai ciyawa ta bushe, hudarta kuma ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana tsaka da harkarsa.

Samun Kambin Rai Madawwami

12 Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, don in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai madawwami, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari. 13 Duk wanda a ke jarabta, kada ya ce Allah ne ke jarabtarsa, don ba ruwan Allah da yin mugunta, shi kansa kuwa ba ya jarabtar kowa. 14 Amma kowane mutun ya kan jarabtu im mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi. 15 Mugun buri kuma in ya yi ciki, sai ya kan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, sai ya kan jawo halaka.

16 Kada fa a yaudare ku, ya ’Yan’uwana ƙaunatattu. 17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama su ke, sun sauko ne daga wurin Mahaliccin hasassakin sararin sama, wanda ba canzawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau. 18 Bisa nufinsa ya haife mu ta Maganar Gaskiya, don mu zama kamar ’yam-fari na halittarsa.

19 Ya ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato kowa yă yi marmarin ƙasa kunne, da jinkirin jawabi, da kuma jinkirin fushi, 20 don fushin mutum ba ya aikata abin karɓuwa ga Allah. 21 Saboda haka sai ku ya da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri-iri, Maganan nan da aka dasa a zuciyarku ku yi na’am da ita cikin halin ƙanƙan-da-kai, don ita ce mai ikon ceton rayukanku.

22 Amma sai ku zama masu aikata Maganar Allah, ba masu ji kawai kuna yaudarar kanku ba. 23 Don duk wanda ya ke mai jin Maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutun ya ke mai duba idonsa a madubi, 24 don ya kan dubi idonsa ne kawai ya tafi, nandanan kuwa sai ya mance kamanninsa. 25 Amma duk mai duba cikakkiyar ka’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to, wannan shi za a yi wa albarka cikin abin da ya ke aikatawa.

Addini Sahihi marar Aibu

26 In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne. 27 Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubammu, shi ne, a kula da matan da mazansu suka mutu, da marayu, cikin kuntatarsu, a kuma keɓe kai daga duniya cikin halin rashin aibu.

2

Zartad da Hukunci da Miyagun Tunani

Ya ku ’Yan’uwana, kada ku nuna bambanci muddar kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijimmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki. 2 Misali, fin mutum mai zobban zinariya da tufafi masu ƙawa ya halarci taronku, wani gajiyayye kuma ya shigo saye da tsummokara, 3 sa’an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawan nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau nan, yallaɓai”, gajiyayyen nan kuwa kuka ce masa, “Kai, tsaya daga can”, ko kuwa, “Zauna nan ƙasa gabana”, 4 ashe ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartad da hukunci da miyagun tunani? 5 Ku saurara, ya ’Yan’uwana ƙaunatattu. Ashe Allah bai zaɓi gajiyayyun duniyan nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado cikin Mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? 6 Amma kun wulakanta gajiyayyu! Ashe ba masu arzikin ne ke matsa muku ba? Ba su ne kuwa ke janku gaban shari’a ba? 7 Ba kuma su ne ke saɓon Sunan nan mai girma. da a ke kiranku da shi ba?

8 Idan lalle kun cika mafificin umarnin nan yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka”, to, madalla. 9 Amma in kun nuna bambanci, kun ɗau zunubi ke nan, kuma Shari’ar Musa ta same ku da laifin keta umarni. 10 Duk wanda ke kiyaye dukkan Shari’ar, amma ya saɓa kan abu guda, ya saɓi Shari’ar gaba-ɗaya ke nan. 11 Don shi wannan da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” To, im ba ka yi zina ba, amma ka yi kisankai, ai ka zama mai keta Shari’ar ke nan. 12 Saboda haka maganarku da aikinku su kasance irin na mutanen da za a yi wa shari’a bisa ka’idar ’yanci. 13 Hukunci ba zai tausasa wa maras tausayi ba. Mai tausayi kuwa yana nasara wajen hukunci.

Bangaskiya ba Aikatawa Banza ce

14 Ya ku ’Yan’uwana, ina amfani mutun ya ce yana da bangaskiya, alhali kuwa ba ya aikin da zai nuna ta? Anya bangaskiyan nan tāsa ta iya cetonsa? 15 Misali, in wani Ɗan’uwa ko ’Yar’uwa na zaman huntanci, kuma kullum abinci bai wadace shi ba, 16 kuma waninku ya ce masa, “To, sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da tufatarwa” ba tare da kun biya masa bukata ba, ina amfanin haka? 17 Haka ma bangaskiya ita kaɗai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce.

18 To, amma wani zai ce, “Ai kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna min bangaskiyar taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata. 19 Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro. 20 Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka cewa bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce? 21 Ashe kakammu Ibrahim, ba saboda aikatawa ne ya sami karɓuwa ga Allah ba, sa’ad da ya miƙa ɗansa Isiyaku a kan wurin yin hadaya? 22 Ka gani ashe bangaskiyatasa da aikatawatasa ne suka yi aiki tare, har ta aikatawan nan bangaskiyatasa ta kammala. 23 Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma aka ɗaukam masa ita a kan samun karɓuwa ga Allah”, aka kuma kira shi badaɗin Allah. 24 Kun ga ashe Allah na karɓar mutun saboda aikatawarsa ne, ba saboda bangaskiya ita kaɗai ba. 25 Ashe ba haka kuma Rahaba karuwan nan ta sami karɓuwa ga Aliah saboda aikatawarta ba? Wato sa’ad da ta sauki jakadun nan, ta fid da su ta wata hanya daban? 26 To, kamar yadda jiki ba numfashi matacce ne, haka ma bangaskiya ba aikatawa matacciya ce.

3

Ɓarnar Harshe

Ya ku ’Yan’uwana, kada yawancinku su zarme da son koyad da Maganar Allah, don kun san mu da mu ke koyarwa za a yi mana shari’a da mafi tsananin ƙididdiga. 2 Don dukkammu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutun ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma. 3 Ga misali idan mun sa linzami a bakin doki don mu bi da shi, sai mu kan sarrafa dukkan jikinsa ma. 4 Ku dubi jiragen ruwa kuma, ko da ya ke suna da girma haka, kuma ƙaƙƙarfar iska na kora su, duk da haka da ɗan ƙaramin sitiyari ne matuƙi ke juya su duk inda ya nufa. 5 Haka ma harshe ya ke, ga shi ɗan ƙaramin alhaki, sai manya-manyan alfahari! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin alhaki sai manya-manyan alfahari! Ku dubi yadda ɗan ƙarmin ƙyastu ke kunna wa babban daji wuta!

6 Harshe ma wuta ne fa! Cikin duk gaboɓimmu, harshe shi ne kulliyar kowace irin mugunta, mai ɓata dukkan jiki, mai zuga zuciyar mutun ta tafasa, shi kuwa Jahannama ce ke zuga shi. 7 Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan’adan har yă sarrafa su ma, 8 amma ba bil’adan ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai mugunta ce da ba ta hanuwa, cike ya ke da dafi mai kashewa. 9 Da shi mu ke yabon Ubangiji kuma Uba, da shi kuma mu ke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah. 10 Da baki ɗaya a ke yabo, a ke kuma zagi. Haba ’Yan’uwana, ai wannan bai kamata ba! 11 Ashe marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda? 12 Ya ’Yan’uwana, ashe ɓaure na iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.

Hikima Mai Saukowa daga Sama

13 Ina mai hikima da fahinta a cikinku? To, ta kyakkyawan zamansa sai ya nuna aikinsa cikin halin tawali’u da hikima ke sawa. 14 Amma in kuna da matsanancin kishi da sonkai a zuciyarku, kada ku yi alwashi da haka, kuna saɓa wa Gaskiya. 15 Wannan hikima ba irin wadda ke saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son-zuciya, kuma ta Shaiɗan. 16 Duk inda kishi da sonkai su ke, nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma su ke. 17 Amma hikiman nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, kuma mai lumana ce, lafiyayyiya, mai sauƙin-kai, mai tsananin tausayi, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, kuma marar munafunci. 18 Aikin gaskiya a gonar lumana a ke shuka shi, albarkatasa kuwa ta masu yaɗa lumanar ce.

4

Ainihin abin da ke Haddasa Gaba da Husuma

Me ke haddasa gaba da husuma. tsakaninku? Ashe ba sha’awace-sha’awacenku ne ke yaƙi da juna a zukatanku ba? 2 Ku kan zarme da son abu ku rasa, sai ku yi kisankai. Ku kan yi kwaɗayi, ku ƙasa samu, sai ku yi husuma da gaba. Ku kan rasa don ba kwa addu’a ne. 3 Ku kan yi addu’a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.

Abuta da Duniya Gaba ce da Allah

4 Maciya amana! Ashe ba ku san abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan. 5 Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce, “Ruhu Tsattsarka da Allah ya sanya mana a zukatammu yana ƙaunarmu da kishi” 6 Allah shi ke yin mayalwacin alheri. Don haka Nassi ya ce, “Allah na gāba da mai girmankai, amma yana kyautata wa mai ƙanƙan-da-kai.” 7 Saboda haka ku miƙa wuya ga Allah, ku tirje wa Iblis, lalle kuwa zai guje ku. 8 Ku kusanci Allah, shi ma zai kusance ku. Ku tsarkake al’amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukatanku, ya ku masu fuska-biyu. 9 Ku muzanta, ku yi nadama, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙinciki, murnarku tă koma ɓacinzuciya. 10 Ku ƙasƙantad da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.

11 Ya ku ’Yan’uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa Ɗan’uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa Shari’a ke nam, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa, ka ɗora wa Shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. 12 Mai ba da Shari’a ɗaya ne, shi ne kuma mai yinta, shi ne kuwa mai ikon ceto da hallakarwa. To, kai wanene bar da za ka ɗora wa Ɗan’uwanka laifi?

Rai Kamar Raɓa ya ke

13 To, ina masu cewa, “Yau ko gobe za mu je gari kaza, mu shekara. a can, mu yi ta ciniki, mu ci riba”? 14 Alhali kuwa ba ku san abin da gobe za ta kawo ba. Ranku nawa ya ke? Ai kamar raɓa ya ke, in an jima sai ta kaɗe. 15 Sai dai ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, ya kai rai, ma yi kaza da kaza.” 16 Amma ga shi kuna alfahari ta alfarmar banza da ku ke yi. Duk irin wannan alfahari kuwa mugun abu ne. 17 Saboda haka duk wanda ya san ya kamata, ya kuwa kasa yi, ya ɗau zunubi ke nan.

5

Arzikin Haramun Mushe ne

To, ina masu arziki? Ku yi ta kuka da kururuwa saboda baƙinciki iri-iri da za su aukam muku. 2 Arzikinku mushe ne! Tufafinku kuma duk cin asu ne! 3 Zinariyarku da azurfarku sun ɓaci ƙwarai, ɓacin nan nasu kuwa zai zama shaida a kanku, ya ci naman jikinku kamar wuta! Kun dai jibga dukiya a zamanin ƙarshen nam! 4 Ga shi kuwa zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku na ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna. 5 Kun yi zaman duniya da annashuwa da almubazzaranci, ashe kiwata kanku kuka yj saboda yanka! 6 Kun hukunta mai gaskiya, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.

7 Don haka sai ku yi haƙuri ’Yan’uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi na sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka. 8 Ku ma sai ku yi haƙuri, ku tsai da zukatanku, don ranar komowar Ubangiji ta yi kusa. 9 ’Yan’uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga Mai shari’a a bakin kofa! 10 Kan misalin shan-wuya da haƙuri kuma ’Yan’uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji. 11 Ga shi mu kan yaba wa waɗanda suka jure. Kun dai ji irin jimirin da Ayuba ya yi, kun kuma ga irin ƙarkon da Ubangiji ya kawo, yadda Ubangiji ya ke mai yawan tausayi, kuma mai rahama.

12 Amma fiye da komai, ’Yan’uwana, kada ku rantse sam-sam, ko da da Sama, ko da da ƙasa, kai, ko da da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I”, ya tsaya kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A’a”, ya tsaya kan “A’a” ɗin kawai. Kada laifi ya hau ku.

Marar Lafiya yă Kira Dattawan Ikiliziya

13 In waninku na shan wuya, to, sai ya yi addu’a. In kuma waninku na murna, to, sai ya yi waƙar yabon Allah. 14 In waninku na rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan ikiliziya su yi masa addu’a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji. 15 Addu’ar bangaskiya kuwa za ta warkad da marar lafiya, Ubangiji kuma zai tashe shi; im ma ya ɗau zunubi, za a gafarta masa. 16 Saboda haka sai ku riƙa bayyana wa juna laifuffukanku, kuna yi wa juna addu’a, don a warkad da ku. Addu’ar mai gaskiya tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske. 17 Iliya bil’adan ne kamarmu, amma da ya nace da addu’a kada a yi ruwa, sai da aka shekara uku da wata shida ba a yi ruwa a ƙasar ba. 18 Da ya sake yin addu’a kuwa sai sama ta sako da ruwa, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.

19 Ya ku’Yan’uwana, in waninku ya bauɗe wa Gaskiya, kuma wani ya komo da shi, 20 to, yă dai tabbata, kowa ya komo da mai zunubi hanya daga bauɗewatasa, ya kuɓutad da ran mai zunubin nan ke nan daga halaka, ya kuma rufe dimbin zunubansa.


WASIƘA TA FARKO
TA
BITRUS

1

Daga Bitrus, Manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da ke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya, 2 su da ke zaɓaɓɓu bisa ƙaddarar Allah Uba, waɗanda kuma Ruhu Tsattsarka ya keɓe a tsarkake, don su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da aminci su yawaita a gare ku.

Rayayyiyar Sazuciya

3 Yabo ya tabbata ga Allahn Ubangijimmu Yesu Almasihu kuma Ubansa, wanda ta tsananin rahamarsa ya sake haifarmu, don mu yi rayayyiyar sazuciya, albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu, 4 mu kuma sami gado marar lalacewa, marar ɓaci, kuma marar ƙarewa, wanda aka keɓe muku a Sama, 5 wato ku da ikon Allah ke kiyayewa ta bangaskiyarku, don samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani. 6 Kan wannan ne ku ke da matuƙar farinciki, ko da ya ke daga yanzu zuwa wani ɗan lokaci kwa yi baƙinciki ta gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa don tabbatad da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa ko da ya ke mai ƙarewa ce, a kan jarraba ta da wuta, don bangaskiyan nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu. 8 Ko da ya ke ba ku taɓa ganinsa ba, amma kuna ƙaunarsa. Ko da ya ke ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farinciki gaya matuƙa, wanda ya fi gaban ambato, 9 kuna samun ceton rayukanku, sakamakon bangaskiyarku.

Annabawa sun yi Faɗi kan Almasihu

10 Annabawan da suka yi faɗin annabei kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi kan wannan ceton, 11 suna bincike ko wanene, ko kuma wane lokaci ne Ruhun Almasihu da ke zuciyarsu ke ishara, sa’ad da ya yi faɗi kan wuyad da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakad da ke biye. 12 An dai bayyana musu cewa ba kansu su ke bauta wa ba, ku su ke bauta wa, game da abubuwan da masu yi muku Bishara ta ikon Ruhu Tsattsarka wanda aka aiko daga Sama suka sanad da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala’iku ke dokin gani.

13 Don haka sai ku yi damara, ku nutsu, ku sa zuciyarku sosai kan alherin da zai zo muku a bayyanar Yesu Almasihu. 14 Ku yi zaman ’ya’ya masu biyayya. Kada ku biye wa muguwar sha’awarku ta dā ta lokacin jahilcinku. 15 Amma da ya ke wanda ya kira ku tsattsarka, ne, ku ma kanku sai ku zama tsarkaka cikin dukkan al’amuranku. 16 Don a rubuce ya ke, cewa, “Sai ku zama tsarkaka don ni tsattsarka ne.”

Am Fanshe mu da Jinin Almasihu Mai Daraja

17 Da ya ke kuna kiransa Uba wajen addu’a, shi da ke yi wa kowa shari’a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙare lokacin baƙuncinku kuna tsoronsa. 18 Don kun san am fanshe ku ne daga al’adunku na banza da wofi da kuka gada, ba da abubuwa masu lalacewa ba kamar azurfa da zinariya, 19 sai dai da jinin nan mai daraja na Almasihu, kamar na ɗan rago marar naƙasa, marar tabo. 20 An ƙaddara shi kan haka tun ba a halicci duniya ba, amma saboda ku ne aka bayyana shi a zamanin ƙarshe. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, har bangaskiyarku da sazuciyarku su ke ga Allah.

Bishara fa Haddasa Kaunar Juna

22 Da ya ke kun tsarkake ranku da yi wa Gaskiya biyayya kan ƙaunar ’Yan’uwa tsakani da Allah, sai ku himmantu ga ƙaunar juna gaya, da zuciya-ɗaya. 23 Gama sake haifarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato ta Maganar Allah rayayyiya, kuma dawwamammiya. 24 Don

“Duk bil’adan kamar ciyawa ya ke,
Duk darajarsa kamar furen ciyawa ta ke,
Ciyawar ta kan bushe, furen ya kan kade,
25 Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce.”
Ita ce maganar Bishara da aka yi muku.

2

Saboda haka sai ku ya da kowace irin ƙeta, da ha’inci, da munafunci, da hassada, da kuma kowane irin kushe. 2 Kamar jariri sabon haifuwa, ku yi marmarin shan nono marar gami na Ruhu Tsattsarka, don ku girma da shi har ya kai ku ga samun ceto, 3 in dai har kun ɗanɗana alherin Ubangiji.

Babban Dutsen Harsashin Gini

4 Ku zo gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah. 5 Ku ma kamar rayayyun duwatsu, ku samu a gina gidan Ruhu Tsattsarka da ku, ku zama tsarkakan masu kusantar Allah, don ku miƙa baiko irin na Ruhu, abin karɓuwa ga Allah ta kan Yesu Almasihu. 6 Don a tabbace ya ke a Nassi, cewa,

“Ga shi na sanya babban dutsen harsashin gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke,
Duk mai gaskatawa da shi kuwa ba zai kunyata ba.”
7 Gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne.
Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to,
“Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ya zama babban dutsen harsashin gini.

8 Kuma,

“Dutse abin yin tuntuɓe,
Kuma abin sa takaici.”

Sun yi tuntuɓe ne da Maganar Allah, don sun ƙi ba ta gaskiya. Haka kuwa aka ƙaddaro musu.

9 Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ’ya’yan sarauta masu kusantar Allah, tsattsarkar al’umma, jama’a mallakar Allah, don ku sanad da mafifitan al’amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu kuka shiga maɗaukakin haskensa. 10 Da ba jama’a ɗaya ku ke ba, amma yanzu ku jama’ar Allah ce. Da ba ku sadu da rahamarsa, ba, amma yanzu kun sadu da ita.

11 Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku kan ku baƙi ne, kuma bare, ku guji miyagun sha’awace-sha’awace na burin-zuciya waɗanda ke yaƙi da zuciyarku. 12 Ku yi halin yabo a cikin sauran al’umma, don duk sa’ad da su ke kushenku wai ku miyagu ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah ran da alheri ya sauko musu.

Biyayya ga Mahukunta Wajibi ne

13 Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, don shi ne shumagaba, 14 ko kuwa ga mahukunta, don su ne ya a’aika su hori miyagu, su kuma yabi masu kirki. 15 Don nufin Allah ne ku tuƙe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari. 16 Ku yi zaman ’yanci, sai dai kada ku fake a bayan ’yancin nan naku ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah. 17 Ku girmama kowa, ku ƙaunaci ’Yan’uwa, ku tsoraci Allah, ku girmama sarki.

Mutun ya Jure Wuya ba da Alhakinsa ba lbada ce

18 Ku barori, ku bi iyayengidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin-hali kaɗai ba, har ma miskilai. 19 Ai abin karɓuwa ne ga Allah, in saboda mutun yana faɗake da Allah, ya jure wa wuyad da ya ke sha ba da alhakinsa ba. 20 To, ina abin taƙama don kun ɗau haƙuri in an nannaushe ku kan laifin da kuka yi? Amma in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuma kuka haƙura, to, shi ne abin karɓuwa ga Allah.

Almasihu ya bar mana Misali

21 Don a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku misali ku bi hanyarsa. 22 Bai taɓa yin laifi ba faufau, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba. 23 Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuwa bai yi ƙwafa ba, sai dai ya dogara ga wannan Mai shari’ar gaskiya. 24 Shi da kansa ya ɗauke zunubammu a jika a kan gungume, don mu fita sha’anin zunubi dungum, mu yi zaman aikin gaskiya. Da raunukansa ne aka warkad da ku. 25 Dā kun sangarce kamar tumaki, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi, kuma Mai kula da rayukanku.

3

Hakkin Aure

Haka kuma ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko wasu ba su bi Maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu ba tare da wata magana ba, 2 don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku. 3 Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso, da kayan gwal, ko tufafi masu ƙawa, 4 sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dusashewa na sanyin-hali da nutsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah. 5 Don da ma haka tsarkakan mata masu dogara ga Allah suka yi ado, suka bi mazansu, 6 kamar yadda Saratu ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta. Ku kuma ’ya’yanta ne muddar kuna aiki nagari, kuma ba kwa yarda wani abu ya tsorata ku.

7 Haka kuma ku maza, ku yi zaman ɗa’a da matanku, kuna girmama su, da ya ke su ne raunana, tun da ya ke ku abokan tarayya ne ga gadon baiwar rai madawwami, don kada wani abu ya hana ku yin addu’a tare.

Gargaɗi ga Bin Allah

8 Daga ƙarshe kuma dukkanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar ’Yan’uwa, masu tausayi, kuma masu ƙanƙan-da-kai. 9 Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka sai ku sa albarka. Don a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka. 10 Don,

“Duk mai son zaman girma da arziki,
Da kuma zaman alheri,
Sai ya kame bakinsa daga ɓama,
Ya kuma hana shi maganar yaudara.
11 Ya rabu da sharran, ya kama hairan,
Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.
12 Don Ubangiji na duban masu aikin gaskiya da idon rahama,
Yana kuma sauraron roƙonsu.
Amma Ubangiji na gāba da masu aikata mugunta.”

Ku yi Aikin Gaskiya ko da za ku Sha Wuya

13 To, wa zai cuce ku in kun himmantu kan abin da ke nagari? 14 Amma ko da za ku sha wuya kan aikin gaskiya, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoronsu, kada kuma ku damu. 15 Sai dai ku keɓe Almasihu a tsarkake a zukatanku kan shi Ubangiji ne. Kullun ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin sazuciyan nan taku, amma fa sai cikin sanyin-hali da bangirma. 16 Kuma zuciyarku ta tabbata garau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata. 17 Zai fi kyau a sha wuya ga yin abin da ke nagari, in hakan nufin Allah ne, a kan a sha ga yin abin da ba daidai ba. 18 Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, don kau da zunubammu, mai gaskiya maimakon marasa gaskiya, don ya kai mu ga Allah. An kashe shi ta jika, amma an rayad da shi ta ruhu. 19 Ta ruhun ne kuma ya je ya yi wa ruhohin da ke kurkuku shela, 20 wato waɗanda dā ba su bi ba, sa’ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassakar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato mutun takwas suka kuɓuta ta ruwa. 21 Babtisma kuwa, wadda ita ce kwatankwacin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fid da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta roƙon Allah da zuciya garau, albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu, 22 wanda ya tafi Sama, kuma ya ke hannun dama na Allah, mala’iku da manyan mala’iku da masu iko suna binsa.

4

Bin Almasihu Sai da Shan-wuya

Tun da ya ke Almasihu ya sha wuya a jika domimmu, sai ku ma ku ɗauki irin wannan ra’ayi. Ai duk wanda ya sha wuya a jika, ya daina aikata zunubi ke nan, 2 don nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa a duniya: ba tare da biye wa muguwar sha’awar zuciya ba, sai dai nufin Allah. 3 Lalle zaman da kuka yi na dā irin wanda sauran al’umma ke son yi, ya isa hakanan, wato zaman fajirci, da miyagun sha’awace-sha’awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka abar ƙyama. 4 Suna mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, kuna zarmewa kuna aikata masha’a irin tasu, har suna zaginku. 5 Amma lalle su ba da hujjojinsu ga wannan da ke shirye ya yi wa rayayyu da matattu shari’a. 6 Shi ya sa aka yi Bishara har ga matattu ma, waɗanda ko da ya ke an yi musu hukunci a jika kamar mutane, su samu su rayu a ruhu kamar Allah.

7 Karshen dukkan abubuwa ya gabato. Saboda haka sai ku kame kanku, ku nutsu, don ku samu ku yi addu’a. 8 Fiye da koma, kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna gaya, don ƙauna ta kan yafe laifuffuka masu ɗimbin yawa. 9 Ku riƙa yi wa juna bakunta, ba tare da kunkuni ba. 10 Duk baiwad da mutun ya samu, yă yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan’uwansa, kan amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah iri-iri ne. 11 Duk mai wa’azi yă dai san faɗar Allah ya ke yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, don ta kowane hali a ɗaukaka Allah ta kan Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Hakika.

Shan-wuya saboda Almasihu Albarka ce

12 Ya ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalad da ta same ku kan gwaji, kamar wani bakon abu ne ya ke faruwa gare ku. 13 Amma muddar kuna tarayya da Almasihu wajen shan-wuyarsa sai ku yi farinciki, don sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa, ku yi farinciki da murna matuƙa. 14 Albarka ta tabbata a gare ku in ana zaginku saboda sunan Almasihu, don Ruhun ɗaukaka, wato Ruhun Allah ya tabbata a gare ku. 15 Sai dai kada shan-wuyar ko ɗaya cikinku ya zama na horon laifin kisankai ne, ko na sata, ko na mugun aiki, ko kuma na shisshigi. 16 Amma in wani ya sha wuya a kan shi Kirista ne, to, kada ya ji kunya, sai dai ya ɗaukaka Allah ta wannan sunan. 17 Don lokaci ya yi da za a fara shari’a ta kan jama’ar Allah. In kuwa ta kammu za a fara, to, me zai zama ƙarkon waɗanda ba su bi Bisharar Allah ba? 18 Kuma,

“Im mai aikin gaskiya da kyar ya kuɓuta,
Me zai auku ga marar bin Allah da mai zunubi?”

19 Saboda haka sai duk masu shan wuya bisa nufin Allah su ɗanka ransu ga Mahalicci mai alkawari, suna aikata abin da ke daidai.

5

Gargadi ga Masu Kula da Ikiliziya

Don haka, ku dattawan ikiliziya da ke cikinku, ni da ke dattijon ikiliziya ɗan’uwanku, mashaidin shan-wuyar Almasihu, kuma mai samun rabo cikin ɗaukakad da za a bayyana, ina muku gargaɗi, 2 ku yi kiwon garken Allah da ke tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai kan yarda, ba ma don ribar banza da wofi ba, sai dai da himma. 3 Kada ku nuna wa waɗanda ke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan. 4 Sa’ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa. 5 Hakanan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikiliziya. Dukanku ku lazamci ƙanƙan-da-kai kuna bautar juna, don “Allah na gāba da mai girmankai, amma yana kyautata wa mai ƙanƙan-da-kai.”

6 Don haka sai ku ƙasƙantad da kanku kuna miƙa wuya ga maɗaukakin ikon Allah, don ya ɗaukaka ku a kan kari. 7 Ku jibga masa duk kulliyar taraddadinku, don yana kula da ku. 8 Ku nutsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis na zazzagawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame. 9 Ku tirje masa, kuna dagewa kan bangaskiyarku, da ya ke kun san ’Yan’uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan-wuya. 10 Kuma bayan kun sha wuya ta ɗan lokaci kaɗan, Allah Mai yawan alheri, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa kuna game da Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku. 11 Mulki yā tabbata a gare shi har abada abadin. Hakika.

12 Na rubuto muku wasiƙan nan a takaice ta hannun Silwanas, Ɗan’uwa mai alkawari, a yadda na ɗauke shi, don in yi muku gargaɗi, in kuma sanad da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske; ku tsaya a gare shi tsaiwar daka. 13 Ita da ke Babila, wadda ita ma zaɓaɓɓiya ce, ta aiko muku da gaisuwa. Haka kuma ɗana Markus. 14 Ku gai da juna da sumbar ƙauna.

Aminci yă tabbata a gare, ku duka, ku na Almasihu.


WASIKA TA BIYU
TA
BITRUS

1

Daga Siman Bitrus, bawan Yesu Almasihu kuma Manzonsa, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja ɗaya da tamu, albarkacin gagkiyar Allahmmu kuma Macecimmu Yesu Almasihu. 2 Alheri da aminci su yawaita a gare ku, wajen sanin Allah da Yesu Ubangijimmu.

Rayuwa Madawwamiya da Bin Allah

3 Allah da ikonsa yā yi mana baiwa da dukkan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa madawwamiya da kuma binsa, ta sanin wannan da ya kira mu ga samun ɗaukakarsa da fifikonsa, 4 waɗanda kuma ta kansu ya yi mana baiwa da manya-manyan alkawaransa masu ɗaukaka ƙwarai, don ta kansu ku zama masu tarayya da Allah wajen yanayinsa, da ya ke kun tsira daga ɓacin nan da ke duniya da muguwar sha’awa ke haifa. 5 Saboda wannan dalili musamman sai ku yi matuƙar himma, ku ƙara bangaskiyarku da halin kirki, halin kirki kuma da shinan ya kamata, 6 shinan ya kamata kuma da kamun-kai, kamun-kai kuma da jimiri, jimiri kuma da bin Allah, 7 bin Allah kuma da son ’Yan’uwa, son ’Yan’uwa kuma da ƙauna. 8 In kuwa halayen nan sun zama naku ne har suna yalwata, za su tsarshe ku daga zamowa marasa tasiri, ko marasa amfani wajen sanin Ubangijimmu Yesu Almasihu. 9 Don duk wanda ya rasa halayen nan, to, makaho ne ko kuwa ganinsa dishi-dishi ne, ya kuma mance cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā. 10 Saboda haka, ya ku ’Yan’uwa, ku ƙara ba da himma ku tabbatad da kiranku da zaɓenku da aka yi. Don in kun bi waɗannan halaye, ba za ku faɗi ba bar abada. 11 Ta haka kuma za a shirya muku ingantaccen tarye wajen shiga madawwamin mulki na Ubangijimmu kuma Macecimmu Yesu Almasihu.

12 Don haka lalle kullum ba zan fasa yi muku tunin waɗannan abubuwa ba, ko da ya ke kun san su, kuma kun kafu a kan Gaskiyan nan da ku ke da ita. 13 A ganina daidai ne, muddar ina zaman yumɓun nan, in riƙa faɗakad da ku ta hanyar tuni. 14 da ya ke na san na yi kusan rabuwa da yumɓun nan nawa, kamar yadda Ubangijimmu Yesu Almasihu ya yi min ishara. 15 Kulata ce, a kowane lokaci ku iya tunawa da waɗannan abubuwa bayan kaurata.

Sun ga Ɗaukakarsa Muraran

16 Ai ba tatsuniyoyi da aka kaga da wayo muka bi ba, sa’ad da muka sanad da ku ikon Ubangijimmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanatasa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran. 17 Don sa’ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, Mafificiyar ɗaukaka kuma ta zo masa da murya ta ce, “Wannan shi ne Ɗana Kaunataccena wanda na ke farinciki da shi ƙwarai”, 18 mu ne muka ji muryan nan da aka sauko daga Sama, don muna tare da shi a kan tsattsarkan Dutsen nan. 19 Har wa yau kuma aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku ku mai da hankali gare ta, don kamar fitila ta ke mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin Ranan nan, Gamzaki kuma yă bayyana a zukatanku. 20 Da farko dai lalle ne ku fahinci wannan, cewa ba wani faɗin annabci na Littattafai Tsarkaka da za a iya fassarawa ta ra’ayin mutun. 21 Don ba wani faɗin annabcin da ya taɓa samuwa ta nufin mutun, sai dai mutane ne Ruhu Tsattsarka ke izawa, Allah na magana ta bakinsu.

2

Annabawan Ƙarya da Malaman Ƙarya

Amma fa annabawan karya sun bayyana a cikin jama’a kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓamaciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu halaka faraɗ-ɗaya. 2 Da yawa kuwa za su bi fajircinsu, har za a kushe Hanyar Gaskiya saboda su. 3 Saboda dulmiyarsu cikin kwaɗayi za su more ku da ƙarairayinsu. Ai tun dā ma can alhakinsu na binsu, halakarsu kuma ba ta da makawa.

4 Da ya ke Allah bai rangwanta wa mala’iku ba sa’ad da suka ɗau zunubi, sai ya jefa su Jahannama, ya tura su cikin ramummuka masu zurfi, masu bakin duhu, a tsare su har ya zuwa Ranar Hukunci; 5 kuma, tun da ya ke bai rangwanta wa mutanen tun can na aru-aru ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa’azin aikin gaskiya, da wasu mutum bakwai, sa’ad da ya aiko da Ruwan Tsufana duniyan nan ta marasa bin Allah; 6 kuma, da ya ke ya mai da biranen Saduma da Gamurata toka, ya yi musu hukuncin halaka, ya mai da su abin ishara ga marasa bin Allah; 7 kuma, da ya ke ya ceci Ludu mai aikin gaskiya, wanda fajircin kangararru ya baƙanta masa rai ƙwarai, 8 (don kuwa abin da mai gaskiyan nan ya ji, ya kuma gani, sa’ad da ya ke cikinsu, sai kowace rana ya kan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai gaskiya); 9 ashe kuwa Ubangiji ya san yadda zai kuɓutad da masu tsoronsa daga gwajegwaje, ya kuma tsare marasa gaskiya kan jiran hukunci har ya zuwa Ranar Shari’a, 10 tun ba ma waɗanda suka dulmuya cikin muguwar sha’awa mai ƙazantarwa ba, su ke kuma raina mulki.

Hukuncin Masu Ya da Hanyar Gaskiya

Masu tsaurin-ido ne su, kuma masu taurin-kai, ba sa jin tsoron zagin masu ɗaukaka. 11 Amma kuwa mala’iku, ko da ya ke sun fi su ƙarfi da iko, duk da haka ba sa ɗora musu laifi da zage-zage a gaban Ubangiji. 12 Amma waɗannan mutane, kamar dabbobi marasa hankali su ke, masu bin abin da jikinsu ya ba su kawai, waɗanda aka haifa don a kama a kashe, har suna kushen abubuwan da ba su ma fahinta ba, lalle kuwa za su halaka a sanadin ɓacin nan nasu, 13 suna shan sakamakon rashin gaskiyarsu. Sun ɗauka kan jin daɗi ne a yi annashuwa da rana kata. Sun bakanta, sun zama abin kunya. Sun dulmuya ga ciye-ciye da shaye-shaye, suna ta rushadi a cikinku. 14 Jarabar zina gare su, ba sa ƙoshi da ɗaukan zunubi. Suna wasa da hankalin marasa kintsuwa. Sun ƙware da kwaɗayi. La’anannun iri! 15 Sun ya da miƙakkiyar hanya, sun bauɗe, sun bi hanyar Bal’ama ɗam Ba’ura, wanda ya cika son yin samu ta hanyar rashin gaskiya. 16 Amma an tsawata masa a kan laifinsa, har dabba marar baki ma ta yi magana, kamar mutun, ta kwaɓi haukan annabin nan.

17 Mutanen nan ƙafaffun rijiyoyi ne, ƙasunsumi ne da iska ke kadawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu. 18 Ta surutun banza da wofi na ruba, su kan yaudari waɗanda yankuwarsu ke nan daga masu zaman ɓata ta hanyar miyagun sha’awace-sha’awacen fajirci, 19 suna yi musu alkawarin ’yanci, ga su kuwa su kansu bayin zamba ne. Don mutum bawan duk abin da ya rinjaye shi ne. 20 In kuwa bayan sun tsere wa ƙazantar duniya albarkacin sanin Ubangijimmu, kuma Macecimmu Yesu Almasihu, suka kuma sake sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, sun kasa kasau ke nan. 21 Da ma ba su taɓa sanin banyan nan ta samun karɓuwa ga Allah tun da fari ba, da ya fiye musu, a kan bayan sun san ta, su juya baya ga tsattsarkan umarnin nan da aka yi musu. 22 Ai kuwa karin maganar nan na gaskiya ya dace da su, cewa, Kare ya cinye amansa, kuma, Wane ya koma tirkensa mai caɓi.

3

Maganar Allah ba ta Tashi

Ya ƙaunatattuna, wannan ita ce wasiƙa ta biyu da na rubuto muku, a kowaccensu kuwa na faɗakad da sahihan zukatanku ta hanyar tuni. 2 Ina so ku tuna da faɗin annabawa tsarkaka, da kuma umarnin Ubangiji Maceci ta bakin Manzannin da suka zo muku. 3 Da farko dai lalle ne ku fahinci wannan, cewa can zamanin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna biye wa muguwar sha’awatasu, 4 suna cewa, “To, ina alkawarin dawowar tāsa? Ai tun da kakannin kakannimmu suka ƙaura, dukkan abubuwa suna tafe ne kamar dā tun farkon halitta.” 5 Da gangan su ke goce wa maganan nan, cewa tun aru-aru sammai sun kasance ta Maganar Allah, kuma cewa ta Maganar Allah aka siffanta ƙasa daga ruwa, kuma da ruwa. 6 Ta haka ne kuma duniyar wancan zamani ruwa ya sha kanta, ta halaka.

Sammai da Kassai za su Shuɗe

7 Ta Maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da ke nan yanzu aka tanada su ga wuta, ana ajiye da su har ya zuwa ranan nan da za a yi wa marasa bin Allah shari’a, a hallaka su. 8 Amma ya ku ƙaunatattuna, kada ku goce wa magana gudan nan, cewa ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekara dubu ne, shekara dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. 9 Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda wasu suka ɗauki ma’anar jinkiri, amma mai haƙuri ne gare ku, ba ya son kowa ya halaka, sai dai kowa ya kai ga tuba. 10 Duk da haka Ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sannan kuma sammai za su shuɗe da ruri mai tsanani, za a hallaka dukkan abin da ke cikinsu da wuta, ƙasa kuma da abubuwan da ke kanta duk za a kone su ƙurmus.

11 Tun da ya ke duk abubuwan nan za a hallaka su haka, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama wajen zaman tsarkaka da bin Allah, 12 kuna jira, kuna kuma ƙagauta da zuwan Ranar Allah! Da zuwanta kuwa za a kunna wa sammai wuta, su halaka, kuma dukkan abubuwan da ke cikinsu wuta za ta narkad da su. 13 Amma bisa alkawarinsa muna jiran sabuwar sama da sabuwar ƙasa, inda aikin gaskiya ke zaune.

Ku Himmantu ya same ku Marasa Tabo

14 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, tun da ku ke jiran waɗannan abubuwa, ku himmantu ya same ku marasa tabo, marasa aibu, kuma kuna zaman aminci. 15 Ku ɗauki haƙurin Ubangijimmu a kan hanyar ceto ne. Haka ma ƙaunataccen Ɗan’uwammu Bulus ya rubuto muku bisa ga hikimad da aka yi masa baiwa, 16 yana magana kan wannan, kamar yadda ya ke yi a dukkan wasiƙunsa; akwai wasu abubuwa a cikinsu masu wuyar fahinta, waɗanda jahilai da marasa kintsuwa ke juya ma’anarsu, kamar yadda su ke juya sauran Littattafai Tsarkaka, ta haka su ke jawo wa kansu halaka. 17 Don haka, ya ku ƙaunatattuna, da ya ke kun riga kun san haka, ku kula kada bauɗewar kangararru ta tafi da ku har ku kwanta da sirdi. 18 Amma ku ƙaru da alherin Ubangijimmu, Macecimmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, kuma har ya zuwa Ranar Dawwama. Amin.


WASIƘA TA FARKO
TA
YOHANA

1

Am Bayyana Rai Madawwami

Shi da ke tun fil’azal ke nan, wanda muka ji, muka gani da idommu, muka kuma duba, hannayemmu kuma suka shafa, game da Kalmar Rai madawwami— 2 Rai madawwamin nan kuwa am bayyana shi, mu kuwa mun gani, muna ba da shaida, muna kuma sanad da ku Rai madawwamin nan wanda tun da ke tare da Uba, aka kuwa bayyana shi gare mu— 3 to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai mu ke sanad da ku, don ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyan nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu. 4 Kuma muna rubuto muku. wannan ne don farincikimmu ya zama cikakke.

5 Wannan shi ne jawabin da muka ji a gunsa, mu ke kuma sanad da ku cewa Allah haske ne, kuma babu duhu gare shi ko kaɗan. 6 Im mun ce muna tarayya da shi, alhali kuwa muna zaune a cikin duhu, mun yi ƙarya ke nan, ba ma aikata gaskiya. 7 In kuwa muna zaune a cikin haske kamar yadda shi ya ke cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, kuma. jinin Yesu Ɗansa na tsarkake mu daga dukkan zunubi. 8 Im mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kammu mu ke yi, kuma gaskiya ba ta tare da mu. 9 In kuwa muka bayyana zunubammu, to, shi mai alkawari ne, kuma mai gaskiya ne, zai kuwa gafarta mana zunubammu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin gaskiya. 10 Im mun ce ba mu ɗau zunubi ba, mun ƙaryata shi ke nan, Maganatasa kuma ba ta tare da mu.

2

Yesu shi ne Kankarar Zunuban Duniya Duka

Ya ku ’ya’yana ƙanana, ina rubuto muku wannan ne don kada ku ɗau zunubi. In kuwa wani ya ɗau zunubi, muna da Mai tsaya mana a gun Uba, wato Yesu. Almasihu Mai gaskiya. 2 Shi kansa kuwa shi ne kankarar zunubammu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka. 3 Ta haka za mu tabbata mun san shi in dai muna bin umarninsa. 4 Kowa ya ce ya san shi, ba ya kuwa bin umarninsa, maƙaryaci ne, gaskiya kuma ba ta tare da shi. 5 Amma duk wanda ke kiyaye Maganatasa, wannan kam hakika yana ƙaunar Allah, cikakkiyar ƙauna. Ta haka muka tabbata muna game da shi. 6 Kowa ya ce yana zaune game da shi, ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da shi ya yi.

Mai Ƙin Ɗan’uwansa Zaman Duhu ya ke yi

7 Ya ku ƙaunatattuna, ba fa wani sabon umarni na ke rubuto muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne dai wanda ku ke da shi tun farko. Daɗaɗɗen umarnin nan kuwa, ai shi ne maganad da kuka ji. 8 Har wa yau sabon umarni na ke rubuto muku, wanda ke tabbace gare shi, kuma gare ku, domin duhu na shuɗewa, hakikanin haske kuma na haskakawa. 9 Kowa ya ce yana cikin haske, yana kuwa ƙin ɗan’uwansa, ashe a cikin duhu ya ke har yanzu. 10 Mai ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin haske ya ke zaune, ba kuma wani sanadin tuntuɓe a gare shi. 11 Mai kin ɗan’uwansa kuwa, a cikin duhu ya ke, kuma a cikin duhu ya ke tafe, bai san ma inda ya ke sa ƙafa ba, domin duhun ya makantad da shi.

12 Ya ku ’ya’yana kanana, ina rubuto muku ne don an gafarta muku zunubanku saboda sunansa. 13 Ya ku dattawa, ina rubuto muku ne don kun san shi, shi wanda ke tun fil’azal. Ya ku samari, ina rubuto muku ne don kun ci nasara a kan Mugun nan. Ya ku ’yan yara, ina rubuto muku ne don kun san Uba. 14 Ya ku dattawa, na rubuto muku ne don kun san shi, shi wanda ke tun fil’azal. Ya ku samari, na rubuto muku ne don kuna da ƙarfi, kuma Maganar Allah na zaune a zuciyarku, kun kuma ci nasara a kan Mugun nan.

Kada ku Kaunaci Duniya

15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da ke cikinta. Kowa ke ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam. 16 Don kuwa duk abin da ke duniya, kamar su burin-zuciya, da muguwar sha’awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne. 17 Duniyar kuwa tana shuɗewa da miyagun gure-gurenta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.

Magabcin Almasihu

18 Ya ku’yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji cewa Magabcin Almasihu na zuwa, ko yanzu ma magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka san zamanin ƙarshe ne. 19 Sun dai fita daga cikimmu, amma da ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana cewa dukkansu ba namu a ciki. 20 Ku kam, Tsattsarkan nan ya shafe ku, tsattsarkar shafa, kuma duk kun san Gaskiya. 21 Ina rubuto muku ba wai don ba ku san Gaskiya ba ne, a’a, sai don kun san ta, kun kuma san Gaskiya ba ta haifar ƙarya. 22 Wanene maƙaryacin nan, im ba wanda ya musa Yesu shi ne Almasihu ba? Irin wannan shi ne magabcin Almasihu, shi wanda ke ƙin Uban da Ɗan. 23 Ba mai kin Ɗan ya sami Uban. Kowa ya bayyana yarda ga Ɗan, ya sami Uban ke nan. 24 Ku kam, abin da kuka ji tun da farko, sai ya zauna a zuciyarku. In abin da kuka ji tun da farko ya zauna a zuciyarku, ku ma sai ku zauna game da Ɗan, da kuma Uban. 25 Wannan shi ne alkawarin da ya yi mana, wato rai madawwami.

26 Ina rubuto muku wannan ne a kan waɗanda ke ƙoƙarin ɓad da ku. 27 Ku kam, shafan nan da kuka samu daga wurinsa tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafan nan tasa ke koya muku komai, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna game da shi.

28 To yanzu, ya ku ’ya’yana ƙanana, sai ku zauna game da shi, don sa’ad da ya bayyana, mu kasance da amincewa, kada kunya ta rufe mu a gabansa a ranar komowatasa. 29 Da ya ke kun san shi Mai gaskiya ne, ku dai tabbata cewa duk mai aikin gaskiya haifaffensa ne.

3

Ku dubi irin ƙaunad da Uba ya nuna mana, har yana ce da mu ’ya’yan Allah, haka kuwa mu ke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne. 2 Ya ku ƙaunatattuna, yanzu mu ’ya’yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa ba a bayyana ba tukuna, amma mun san cewa sa’ad da ya bayyana za mu zama kamarsa, don za mu gan shi kamar yadda ya ke. 3 Duk mai ƙwallafa sazuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi ya ke tsattsarka.

Zunubi Tawaye ne

4 Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne. 5 Kun dai san am bayyana shi don yd ɗauke zunubai ne, a gare shi kuma babu zunubi. 6 Kowa ke zaune game da shi, ba ya aikata zunubi. Kowa ke aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba. 7 Ya ku ’ya’yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Duk mai aikin gaskiya, mai gaskiya ne, kamar yadda shi ya ke mai gaskiya. 8 Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne yă rushe aikin Iblis. 9 Duk wanda ke haifaffen Allah, ba ya aikata zunubi, don shukakken Ruhunsa na dawwame a zuciyatasa, ba kuwa zai iya aikata zunubi ba, tun da ya ke shi haifaffen Allah ne. 10 Ta haka sai a ga waɗanda ke ’ya’yan Allah, da kuma waɗanda ke ’ya’yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata gaskiya, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

Mu Kaunaci Juna

11 Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun da farko, cewa dai mu ƙaunaci juna, 12 kada mu zama kamar Kayinu, wanda ke na Mugun ne, har ma ya kashe ɗan’uwansa. To, dom me ya kashe shi? Don ayyukansa miyagu ne, na ɗan’uwansa kuwa na gaskiya ne. 13 Kada ku yi mamaki ’Yan’uwa da duniya ke ƙinku. 14 Mu kam mun san mun riga mun tsere wa halaka, mun kai ga rai madawwami, saboda muna ƙaunar ’Yan’uwa. Wanda ba shi da ƙauna, zaman halaka ya ke yi. 15 Kowa ke ƙin ɗan’uwansa, mai kisankai ne. Kun kuwa sani ba mai kisankan da ke da rai madawwami a zaune tare da shi. 16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta ba da ransa da ya yi a maimakommu. Mu kuma ya kamata mu ba da rammu saboda ’Yan’uwa. 17 Duk kuwa wanda ke da abin hannunsa, ya ke kuma ganin ɗan’uwansa cikin rashi, sannan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah za ta dawwama a gare shi? 18 Ya ku ’ya’yana ƙanana, kada mu nuna ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya. 19 Ta haka za mu tabbata mu na Gaskiya ne, har kuma mu amince wa kammu gaban Allah, 20 duk sa’ad da zuciyarmu ta ba mu laifi; saboda Allah shi ne maɗaukaki a kanta, ya kuma san komai. 21 Ya ku ƙaunatattuna, in zuciyarmu ba ta ba mu laifi ba, sai mu je gaban Allah da amincewa. 22 Mu kan kuwa sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da ya ke so. 23 Umarninsa kuwa shi ne mu gaskata da sunan Ɗansa Yesu Almasihu, mu kuma ƙaunaci juna, kamar yadda ya umarce mu. 24 Duk mai bin umarninsa kuwa a dawwame ya ke game da shi, shi kuma game da shi. Ta haka muka tabbata ya dawwama game da mu, saboda Ruhu Tsattsarka da ya ba mu.

4

Koyarwar Gaskiya da ta Ƙarya

Ya ku ƙaunatattuna, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku jarraba ku gani ko na Allah ne, don annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2 Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato duk ruhun da ya bayyana yarda cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jikin mutun, shi ne na Allah. 3 Duk ruhun kuwa da bai bayyana yarda ga Yesu ba, ba na Allah ba ne; wannan shi ne ruhun magabcin nan na Almasihu wanda kuka ji zai zo, yanzu ma har yana cikin duniya. 4 Ya ku ’ya’yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kuma kun ci nasara a kan waɗannan, don shi wanda ke zuciyarku ya fi wanda ke cikin duniya ƙarfi. 5 Su kuwa na duniya ne, shi ya sa su ke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu. 6 Mu kam na Allah ne. Duk wanda ya san Allah ya kan saurare mu, wanda ya ke ba na Allah ba kuwa, ba ya saurarommu. Ta haka muka san Ruhu na gaskiya da ruhu na karya.

Kaunar Juna Wajibi ne

7 Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, don ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, kuma ya san Allah. 8 Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna. 9 Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗici duniya, don mu sami rai madawwami ta kansa. 10 A wannan ƙauna ta ke, wato ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, abin kankarar zunubammu. 11 Ya ku ƙaunatattuna, tun da ya ke Allah ya ƙaunace mu haka, ai mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna. 12 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai, amma kuwa im muna ƙaunar juna sai Allah ya dawwama game da mu, ƙaunan nan tasa kuma tă cika a gare mu.

13 Ta haka muka san muna dawwame game da shi, shi kuma game da mu, saboda Ruhunsa Tsattsarka da ya ba mu. 14 Mun duba, muna kuma ba da shaida, cewa Uba ya aiko ɗan kan shi ne Macecin duniya. 15 Kowa ya bayyana yarda cewa Yesu ɗan Allah ne, sai Allah yă dawwama game da shi, shi kuma game da Allah. 16 Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunad da Allah ke yi mana. Allah shi ne ƙauna, kuma wanda ke dawwame game da ƙauna, ya dawwama game da Allah ke nan, Allah kuma game da shi. 17 Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu, har mu sami amincewa a Ranar Shari’a, domin kamar yadda ya ke, haka mu ma mu ke a duniyan nan. 18 Babu tsoro ga ƙauna, sai dai cikakkiyar ƙauna ta kan yaye tsoro. Don tsoro kansa ma azaba ne, mai jin tsoro kuwa ba shi da cikakkiyar ƙauna. 19 Muna ƙauna, don shi ne ya fara ƙaunarmu. 20 Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin ɗan’uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da ya ke gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai ma taɓa gani ba. 21 Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah sai ya ƙaunaci ɗan’uwansa ma.

5

Kaunar Allah ita ce Bin Umarninsa

Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa ke ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar da ma. 2 Ta haka muka san muna ƙaunar ’ya’yan Allah, wato im muna ƙaunar Allah, muna kuma bin umarninsa. 3 Don ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne. 4 Don duk wanda ke haifaffen Allah yana nasara da duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ikon da ya yi nasara da duniya. 5 Wanene ke nasara da duniya, im ba wanda ya gaskata cewa Yesu ɗan Allah ba ne?

6 Shi ne wanda ya bayyana ta ruwa da jini, Yesu Almasihu, ba fa ta ruwa kaɗai ba, amma ta ruwa da jini. 7 Ruhu kuma shi ne mai ba da shaida, domin Ruhun shi ne gaskiya. 8 Akwai shaidu uku, wato Ruhu Tsattsarka, da ruwa, da kuma jini, waɗannan ukun kuwa manufarsu ɗaya ce. 9 Tun da ya ke ma muna yarda da shaidar mutane, ai shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato ya shaidi Ɗansa. 10 Kowa ya gaskata da ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidad da Allah ya yi wa Ɗansa ba. 11 Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai madawwami kuwa yana ga Ɗansa. 12 Duk wanda ke da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ba shi da ɗan Allah kuwa, ba shi da rai madawwami.

Tabbatar Samun Rai Madawwami

13 Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan ɗan Allah, don ku tabbata kuna da rai madawwami. 14 Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, cewa im mun roƙi komai bisa nufinsa, sai ya saurare mu. 15 In kuwa muka san komai muka roƙa yana saurarommu, mun tabbata cewa mun sami abin da muka roƙa a gare shi ke nan. 16 Kowa ya ga ɗan’uwansa na ɗaukan zunubin da bai kai halaka ba, sai ya yi masa addu’a. Saboda mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai madawwami ga waɗanda suka ɗauki zunubin da bai kai halaka ba. Akwai zunubin da ke na halaka. Ban ce a yi addu’a kan wannan ba. 17 Duk aikin rashin gaskiya zunubi ne. Akwai kuma zunubin da ba na halaka ba.

18 Mun san cewa kowane haifaffen Allah ba ya ɗaukan zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita kan kare shi, Mugun nan kuwa ba ya taɓa shi.

19 Mun san mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.

20 Mun kuma san cewa ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahinta don mu san shi wanda ke Na gaskiya. Mu kuwa muna game da shi, shi da ke Na gaskiya, wato game da Ɗansa Yesu Almasihu Shi ne Allah Na gaskiya da kuma Rai madawwami. 21 Ya ku ’ya’yana ƙanana, ku yi nesa da gumaka.


WASIƘA TA BIYU
TA
YOHANA

1 Daga dattijon nan na ikiliziya zuwa ga Uwargida zaɓaɓɓya, da ’ya’yanta waɗanda na ke ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukkan waɗanda suka san Gaskiya, 2 wato muna ƙaunarku saboda Gaskiyad da ke dawwame a gare mu, za ta kuwa kasance tare de mu bar abada.

3 Alheri da rahama da aminci na Allah Uba, da kuma na Yesu Almasihu Ɗan Uba, za su tabbata a gare mu a cikin gaskiya da ƙauna.

4 Na yi farinciki ƙwarai da samun wasu ’ya’yanki suna bin Gaskiya, kamar yadda Uba ya ba mu umarni. 5 Yanzu kuma ina roƙonki, Uwargida, ba cewa wani sabon umarni na ke rubuto miki ba, sai dai wanda mu ke da shi tun farko ne, cewa mu ƙaunaci juna. 6 Ƙauna kuwa ita ce mu bi umarninsa. Umarnin kuwa shi ne kamar yadda kuka ji tun farko, cewa ku yi zaman ƙauna. 7 Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jikin mutun. Irin wannan shi ne mai ruɗi, kuma magabcin Almasihu. 8 Ku kula da kanku kada ku ya da aikin da muka yi, sai dai ku sami cikakken sakamako. 9 Kowa ya yi kari bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwan nan, shi ke da Uba da Ɗan. 10 Kowa ya zo gare ku bai kuwa zo da wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi a gidanku, ko maraba ma kada ku yi masa. 11 Don duk wanda ya yi masa maraba, mugun aikinsa sai yă shafe shi.

12 Ko da ya ke ina da abin da zan faɗa muku da yawa, na gwammace ba a wasiƙa ba, amma na sa zuciya in ziyarce ku, mu yi magana baka da baka, don farincikimmu ya zama cikakke.

13 ’Ya’yan ’yar’uwarki zaɓaɓɓiya na gaishe ki.


WASIKA TA UKU
TA
YOHANA

1 Daga dattijon nan na ikiliziya zuwa ga Gayas ƙaunatacce, wanda na ke ƙauna da gaskiya.

2 Ya ƙaunataccena, ina addu’a kă sami zama lafiya ta kowace hanya da kuma lafiyar jiki, kamar yadda ruhunka ke zaune lafiya. 3 Na yi farinciki ƙwarai sa’ad da waɗansu ’Yan’uwa suka zo suka shaidi gaskiyarka, yadda hakika ka ke bin Gaskiya. 4 Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar jin cewa ’ya’yana suna bin Gaskiya.

5 Ya ƙaunataccena, duk abin da ka ke yi wa ’Yan’uwa, aikin bangaskiya ka ke yi, tun ba ma ga baƙi ba. 6 Su ne suka shaidi ƙaunarka a gaban ikiliziya. Zai kyautu ka raka su da guzuri, kamar ya ya cancanci bautar Allah, 7 don saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa kuma karɓar komai daga sauran al’umma. 8 Don haka ya kamata mu karɓi irin mutanen nan, mu ɗau nauyinsu, don mu zama abokan aiki da su kan Gaskiya.

9 Na yi wa ikiliziya ’yar wasiƙa, amma shi Diyotarifis wanda ke son ya fi kowa a cikinsu, ya ƙi bin maganarmu. 10 Saboda haka in na zo zan tabbatar masa da abin da ya ke yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har ya ƙi yi wa ’Yan’uwa maraba, yana kuma hana masu so su marabce su, yana fid da su daga ikiliziya.

11 Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa ke aiki nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam. 12 Dimitiriyas na da kyakkyawar shaida gun kowa, har Gaskiya kanta ma tana yi masa shaida. Mu ma mun shaide shi, ka kuwa san shaidarmu tabbatacciya ce.

13 Da kam, ina da abin da zan rubuto maka da yawa, amma yanzu na gwammace kada in rubuto a wasiƙa. 14 Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa’an nan ma yi magana baka da baka.

15 Aminci yă tabbata gare ku. Aminammu na gaishe ka. Ka gai da aminammu kowa da kowa.


WASIKAR
YAHUDA

I Daga Yahuda bawan Yesu Almasihu, kuma ɗan’uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, ƙaunatattun Allah Uba, keɓaɓɓu ga Yesu Almasihu.

2 Rahama da aminci da ƙauna su yawaita a gare ku.

3 Ya ku ƙaunatattuna, da ya ke da ma ina ɗokin rubuto muku batun ceton nan namu mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan Bangaskiyan nan da aka ɗanka wa tsarkaka sau ɗaya tak ba kari. 4 Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin Makaɗaicin Mamallakimmu Ubangijimmu Yesu Almasihu.

5 Sai dai ina so in tuna muku, ko da ya ke kun riga kun san komai sosai da sosai, cewa Ubangiji ya ceto jama’a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba. 6 Har ma mala’ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a cikin baƙin duhu, har ya zuwa shari’ar babbar ranan nan. 7 Haka kuma Saduma da Gamurata, da biranen kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha’awa marar dacewa, an nuna su domin ishara, suna shan hukunci cikin madawwamiyar wuta.

8 Haka kuma masu mafarke-mafarken nan, su kan ɓata jikinsu, su ƙi bin mulki, su kuma zagi masu ɗaukaka. 9 Amma lokacin da babban mala’ika Mika’ilu ke fama da Iblis, suna musu kan gawar Musa, shi Mika’ilu bai yi garajen ɗora masa laifi da zage-zage ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka.” 10 Amma mutanen nan su kan kushe duk abin da ba su fahinta ba, kuma abubuwan da jikinsu kan ba su kamar dabbobi marasa hankali, su ne sanadin halakarsu. 11 Sun shiga uku! Don sun bi halin Kayinu, sun dunguma cikin bauɗewar Bal’ama don kwaɗayi, sun kuma halaka ta irin tawayen Kuraha. 12 Waɗannan mutane lumbu-lumbu ne, wutar ƙaiƙayi a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Holoƙon hadiri ne su, wanda iska ke korawa. Wofayen itatuwa ne, marasa ’ya’ya ko da ƙaƙa matattu murus, tumɓukakku. 13 Gagara-horo, masu taƙama da rashin kunyarsu, finjirarru, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.

14 Anuhu ma wanda ke na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi faɗin annabci a kan waɗannan mutane, cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa, 15 don ya zartad da hukunci kan kowa, yi kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukkan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.” 16 Waɗannan su ne masu gunaguni, masu ƙunƙuni, masu biye wa muguwar sha’awa, marubata, masu yi wa mutane bambaɗanci don samun wata fa’ida.

17 Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganad da Manzannin Ubangijimmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā 18 da suka ce da ku, “A zamanin ƙarshe za a yi waɗansu mutane masu ba’a, masu biye wa muguwar sha’awatasu ta rashin bin Allah.” 19 Waɗannan su ne masu raba tsakani, masu son zuciya, marasa Ruhu Tsattsarka. 20 Amma ya ku ƙaunatattuna, ku riƙa inganta kanku ga Bangaskiyarku mafi tsarkaka, kuna addu’a da ikon Ruhu Tsattsarka. 21 Ku tsaya a kan ƙaunad da Allah ke yi mana, kuna sauraron rahamar Ubangijimmu Yesu Almasihu mai kaiwa ga rai madawwami. 22 Ku ji tausayin waɗanda ke shakka, 23 kuna ceton waɗansu kuna fizgo su daga wuta. Wasu kuma ku ji tausayinsu, amma sai game da lura, kuna ƙyamar ko da tufafin da jikinsu ya ƙazantar.

24 Ɗaukaka, da maɗaukakiyar alfarma, da mulki, da iko su tabbata ga wannan da ke iya hana ku faɗuwa, ya kuma miƙa ku marasa aibi a gaban maɗaukakin Zatinsa da matuƙar farinciki, 25 ga Allah Makaɗaici Macecimmu, ta kan Yesu Almasihu Ubangijimmu, tun fil’azal, da yanzu, da kuma bar abada abadin. Amin.


WAHAYIN
da aka yi wa
YOHANA

1

Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya yardam masa ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne ya auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta aiko da mala’ikansa wurin bawansa Yohana, 2 wanda ya shaidi Maganar Allah, da kuma shaidar Yesu Almasihu, wato dukkan abin da ya gani. 3 Albarka tā tabbata ga mai karanta maganan nan ta annabci, ta kuma tabbata ga masu ji, waɗanda kuma ke kiyaye abin da ke rubuce a ciki, domin lokaci ya gabato.

4 Daga Yohana zuwa ga ikiliziyan nan bakwai da ke ƙasar Asiya.

Alheri da aminci su tabbata a gare ku daga wannan da ya ke shi ne a yanzu, shi ne a da, shi ne kuma nan gaba, da kuma Ruhohin nan bakwai da ke gaban gadon sarautarsa, 5 da kuma Yesu Almasihu amintaccen mashaidi, Na Farko cikin masu tashi daga matattu, kuma mai mulkin sarakunan duniya.

Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wannan da ke ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubammu ta jininsa, 6 ya mai da mu jama’a masu kusantar Allahnsa kuma Ubansa. Amin. 7 Ga shi zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har waɗanda suka soke shi, kuma duk kabilun duniya za su yi kuka a sanadin zuwansa. Wannan haka ya ke, hakika.

“Ni ne Alfa, Ni ne Omiga”

8 “Ni ne Alfa, ni ne Omiga’”, in ji Ubangiji Allah, wannan da ya ke shi ne a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma nan gaba, Maɗaukaki.

9 Ni Yohana, Ɗan’uwanku, abokin tarayyarku cikin tsanani, da mulkin Allah, da kuma jimiri a kan al’amarin Yesu, ina can tsibirin da a ke kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu. 10 A ranar Ubangiji sai ya zamana Ruhu Tsattsarka na iza ni, sai na ji wata murya mai ƙara a bayana kamar ta kakaki, 11 tana cewa, “Rubuta abin da ka gani a littafi, ka aika wa ikiliziyan nan bakwai, wato ta Afisa, da ta Simirna, da ta Bargamuma, da ta Tayatira, da ta Sardisu, da ta Filadalfiya, da kuma ta Lawudikiya.”

12 Sai na juya in ga wanda ke mini magana; da juyawata kuwa sai na ga fitilu bakwai na zinariya. 13 A tsakan fitilun nan kuwa sai na ga wani kamar Ɗam Mutun, saye da riga har idon sawu, ƙirjinsa kuma da ɗamarar zinariya. 14 Kansa da gashinsa farare fat kamar farin ulu, farare fat kamar alli, idanunsa kamar harshen wuta, 15 ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar wadda aka tace a maƙera, muryatasa kuma kamar ƙugin ruwaye masu gudu. 16 Yana riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama, da wani kakkaifan takobi kuma a bakinsa tsinin gaba, fuskarsa na haske kamar rana a tsakan haskenta.

17 Da na gan shi sai na faɗi a gabansa kamar na mutu. Amma sai ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Na Farko, ni ne Na Karshe, 18 ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi yanzu ina raye bar abada abadin, ina kuwa da mabuɗan Gun Matattu da kuma Hades. 19 To, sai ka rubuta abubuwan da ka gani, wato abubuwan da ke nan yanzu, da abubuwan da ke shirin aukuwa bayan wannan. 20 Ma’anar taurarin nan bakwai da ka gani a hannuna na dama kuwa, da kuma fitilun nan bakwai na zinariya, to, su taurarin nan bakwai mala’iku ne na ikiliziyan nan bakwai, fitilun nan bakwai kuwa ikiliziyai bakwai ɗin ne.

2

Saƙo zuwa ga Ikiliziyai Bakwai

“Sai ka rubuta wa mala’ikan ikiliziyad da ke Afisa haka, ‘Ga maganar shi wannan da ke riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wanda kuma ke tafiya a tsakan fitilun nan bakwai na zinariya:

2 “ ‘Na san ayyukanka, wato famanka, da jimirinka, da yadda ba ka iya hakurce wa miyagun mutane, ka kuma gwada waɗanda ke ce da kansu manzanni, alhali kuwa ba su ba ne, ka tarar na ƙarya ne. 3 Na san kana haƙuri, kana kuma jimiri saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba. 4 Amma ga laifinka gare ni, cewa ka ya da ƙaunad da ka yi tun farko. 5 Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba ka yi irin aikin da ka yi tun da farko. Im ba haka ba, zan zo gare ka in kau da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba. 6 Amma a wannan wajen kam ka kyauta, kā ƙi ayyukan Nikolatawa, ni ma kuwa na ƙi su. 7 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu Tsattsarka ke faɗa wa ikiliziyai. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin cin ’ya’yan bishiyar rai madawwami, wadda ke cikin Firdausin Allah.’

8 “Kuma ka rubuta wa mala’ikan ikiliziyad da ke Simirna haka, ‘Ga maganar wanda ya ke shi ne Na Farko, shi ne kuma Na Karshe, wanda ya mutu, ya kuma sake rayuwa:

9 “‘Na san tsananin da ka ke sha, da talaucinka (amma bisa hakika kai mawadaci ne), na kuma san yanken da waɗansu ke yi maka, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, jama’ar Shaiɗan ne. 10 Kada ka ji tsoron wuyad da za ka sha. Ga shi Iblis na shirin jefa wasunku kurkuku, don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai madawwami. 11 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu Tsattsarka ke faɗa wa ikiliziyai. Duk wanda ya ci nasara, ko kaɗan mutuwa ta biyu ba za ta cuce shi ba.’

12 “Kuma ka rubuta wa mala’ikan ikiliziyad da ke Bargamuma haka, ‘Ga maganar wannan mai kakkaifan takobi:

13 “‘Na san inda ka ke da zama, wato inda gadon sarautar Shaiɗan ya ke. Duk da haka kuwa ka tsaya gare ni, ba ka kuwa bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, inda Shaiɗan ke zaune. 14 Amma ga wasu laifuffukanka kaɗan a gare ni: akwai wasu a cikinku da su ke bin koyarwar Bal’ama, wanda ya koya wa Balaka sa Bani Isra’ila laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka baiko, su kuma yi fasikanci. 15 Haka kai ma ka ke da wasu masu bin koyarwar Nikolatawa. 16 Saboda haka sai ka tuba. Im ba haka ba kuwa, zan zo gare ka da wuri, in yaƙe su da takobin da ke bakina. 17 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu Tsattsarka ke faɗa wa ikiliziyai. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, kuma zan ba shi wani farin dutse, da wani sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan sai wanda ya karɓe shi.’

18 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikiliziyad da ke Tayatira haka, ‘Ga maganar ɗan Allah, mai idanu kamar harshen wuta, mai kafafuwa kamar gogaggiyar tagulla:

19 “‘Na san ayyukanka, wato ƙaunarka da bangaskiyarka. da ibadarka da jimirinka, da kuma cewa ayyukanka na yayyau sun fi na farkon. 20 Amma ga laifinka gare ni, cewa ka haƙurce wa matan nan Jazabila, wadda ta ke ce da kanta mai yin faɗin Maganar Allah, ta ke kuma koya wa bayina, tana yaudararsu su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka baiko. 21 Na ba ta damar tuba, amma ta ƙi tuba da fasikancinta. 22 To, ga shi zan ɗora mata rashin lafiya, masu yin fasikanci da ita kuma zan ɗora musu matsananciyar wahala, sai ko in sun tuba da irin aikinta. 23 Zan kashe ’ya’yanta tashi-ɗaya, dukkan ikiliziyai kuma za su san ni ne Mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa. 24 Amma game da sauranku, ku na Tayatira, da ba sa bin wannan koyarwa, ba su kuma koyi abin da wasu ke kira zurfafan al’amuran Shaiɗan ba, ina ce da ku, ban ɗora muku wani nauyi ba. 25 Sai dai ku riƙi abin da ku ke da shi kankan har in zo. 26 Duk wanda ya ci nasara, ya ke kuma kiyaye aikina har ƙarshe, shi zan bai wa iko a kan al’ummai, 27 zai kuwa mallake su da tsanani ƙwarai, mulki marar rangwame, kamar yadda ni ma kaina na sami iko a gun Ubana, 28 kuma zan ba shi Gamzaki. 29 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu Tsattsarka ke faɗa wa ikiliziyai.’

3

“Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikiliziyad da ke Sardisu haka, “Ga maganar wannan mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai:

‘Na san ayyukanka. Wai kai rayayye, alhali kuwa matacce ne kai. 2 Farka, ka ƙarfafa abin nan da ya saura, ya ke kuma bakin mutuwa, don ban ga aikinka cikakke ne ba a gaban Allahna. 3 Don haka sai ka tuna abin da ka karɓa ka kuma ji; ka kiyaye shi, sannan ka tuba. Im ba za ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan auko maka ba. 4 Amma dai har yanzu kana da wasu kaɗan a Sardisu da ba su ƙazantad da kansu ba, za su kuwa kasance tare da ni cikin fararen kaya, don sun cancanta. 5 Duk wanda ya ci nasara za a sa masa fararen tufafi, kuma ba zan soke sunansa daga Littafin Rai Madawwami ba; zan ce shi nawa ne a gaban Ubana, kuma a gaban mala’ikunsa. 6 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu Tsattsarka ke faɗa wa ikiliziyai.’

7 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikiliziyad da ke Filadalƙya haka, ‘Ga maganar Tsattsarkan nan, Na gaskiya, wanda ke da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa:

8 ‘Na san ayyukanka. Ka ga na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba. 9 To, ga shi zan sa na jama’ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya su ke, zan sa su su zo su kwanta a gabanka, su san dai na ƙaunace ka. 10 Tun da ya ke ka kiyaye maganad da na yi maka ta yin jimiri, ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai zaike wa dukkan duniya don gwada mazauna duniya. 11 Ina zuwa da wuri. Ka riƙi abin da ka ke da shi kankan kada wani ya karɓe maka kambinka. 12 Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Tsattsarkan Mazauni na Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon sunan. 13 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu Tsattsarka ke faɗa wa ikiliziyai.’

14 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikiliziyad da ke Lawudikiya haka, ‘Ga maganar Tabbataccen nan, amintaccen Mashaidi, mai gaskiya, wanda ta kansa dukkan halittar Allah ta kasance:

15 “‘Na san ayyukanka. Ba ka da sanyin-jiki, ba ka kuwa da zafin-nama. Da ma a ce kana da sanyin-jiki mana, ko kuwa kana da zafin-nama. 16 To, saboda kai tsakatsaki ne, ba ka da sanyin-jiki, ba ka kuwa da zafin-nama, don haka zan tofad da kai daga bakina. 17 Tun da ka ce, kai mai arziki ne, wai ka wadata ba ka bukatar komai, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, gajiyayye, makaho, kuma tsirara. 18 Saboda haka, ina maka shawara ka sayi zinariya a guna, wadda aka tace da wuta, don ka arzuta, da kuma firaren tufafi da za ka yi sutura, ka rufe tsiraicinka don kada ka ji kunya, da kuma man shafawa a ido don ka sami gani. 19 Waɗanda na ke ƙauna, su na ke tsawatar wa, na ke kuma horo. Saboda haka sai ka himmantu ka tuba. 20 Ga ni nan tsaye a bakin ƙofa, ina bugawa; kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi ma kuma tare da ni. 21 Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a gadon sarautata, kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a gadon sarautatasa. 22 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu Tsattsarka ke faɗa wa ikiliziyai.’ “

4

Gadon Sarautar Allah

Bayan wannan sai na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā mai kama da kakaki, sai ta ce da ni, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.” 2 Nandanan kuwa sai Ruhu Tsattsarka ya iza ni, sai ga wani gadon sarauta a girke a Sama, da wani a zaune a kai. 3 Na zaunen kuwa ya yi kama da jasfal da kamiliyan’. Kewaye da gadon sarautar kuma akwai wani bakangizo mai kama da emerala. 4 Kewaye da gadon sarautar kuwa akwai wasu gadajen sarauta ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, cikin fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu. 5 Sai walkiya ke ta fita daga gadon sarautar, da kararraki, da kuma tsawar aradu. A gaban gadon sarautar kuma fitilu bakwai na ci, waɗanda su ke su ne Ruhohin nan na Allah guda bakwai. 6 A gaban gadon sarautar kuwa akwai wani abu kamar bahar ɗin gilas, garau ya ke kamar karau.

Kewaye da gadon sarautar kuma, ta kowane gefensa, da waɗansu rayayyun halitta guda huɗu, masu idanduna ta ko’ina, gaba da baya. 7 Rayayyiyar halittar farko kamar zaki ta ke, ta biyu kuma kamar ɗam maraki, ta uku kuma da fuska kamar ta mutun, ta huɗu kuma kamar juhurma na jewa. 8 Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu na da fikafikai shida, ta ko’inansu idanduna ne kewaye da su, sama da ƙasa, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa,

“Tsattsarka, Tsattsarka, Tsattsarka, Ubangiji Allah Maɗaukaki, Shi ne a dā shi ne a yanzu, shi ne kuma nan gaba!”

9 Kuma duk lokacin da rayayyun halittan nan suka ɗaukaka wannan da ke zaune a kan gadon sarautar, ya ke kuma raye har abada abadin, suka girmama shi, suka kuma gode masa, 10 sai dattawan nan ashirin da huɗu su faɗi a gaban wannan da ke zaune a kan gadon sarautar, so yi masa sujada, shi da ke raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban gadon sarautar, suna waƙa, suna cewa,

11 “Macancanci ne kai, ya Ubangiji kuma Allahmmu,
Kă sami ɗaukaka da girma da iko,
Don kai ne ka halicci dukkan abubuwa,
Da nufinka ne suka kasance kuma aka halicce su.”

5

Yimƙaƙƙen Littafi Mai Hatimi Bakwai

A hannun dama na wannan da ke zaune a kan gadon sarautar kuma, sai na ga wani littafi rubutacce ciki da bai, an yimƙe shi da hatimi bakwai. 2 Na kuma ga wani ƙaƙƙarfan mala’ika, yana shela da murya mai ƙarfi, cewa, “Wa ya cancanta ya buɗe littafin nan, ya kuma ɓamɓare hatimansa?” 3 Ba kuwa wani a Sama ko a ƙasa, ko a ƙarƙashin ƙasa, da zai iya buɗe littafin, balle ya duba cikinsa. 4 Sai na yi ta kuka da ba a sami wanda ya cancanta ya buɗe littafin, ko ya duba cikinsa ba, ko ɗaya. 5 Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce da ni, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na Kabilar Yahuda, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yadda zai iya buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”

Ɗan Rago Macancanci ne

6 Tsakanin gadon sarautar da rayayyun halittan nan huɗu, kuma, a cikin dattawan nan, sai na ga wani ɗan Rago tsaye, kamar an yanka shi, yana da kaho bakwai da ido bakwai, waɗanda su ke su ne Ruhohin Allah guda bakwai, da aka aika duniya duka. 7 Sai ya je ya ɗauki littafin nan daga hannun dama na wannan da ke zaune a kan gadon sarautar. 8 Da ya ɗauki littafin sai rayayyun halittan nan guda huɗu, da dattawan nan ashirin da huɗu, suka faɗi a gaban ɗan Ragon, kowannensu na riƙe da molo, da tasar zinariya cike da turaren wuta, waɗanda su ke su ne addu’o’in tsarkaka. 9 Suna rera sabuwar waƙa, suna cewa,

“Macancanci ne, kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa,
Domin dā an kashe ka, kuma ka fanso wa Allah mutane ta jininka
Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama’a, da kowace al’umma,
10 Ka mai da su jama’a, kuma masu kusantar Allahmmu,
Suna kuwa mulki a duniya.”

11 Sarman na duba, sai na ji muryar mala’iku masu yawa kewaye da gadon sarautar, da rayayyun halittan nan, da kuma dattawan nan, yawansu zambar dubu har dubun dubata, 12 suna cewa da murya mai ƙarfi, “Macancanci ne ɗan Ragon nan da aka yanka yă sami iko, da wadata, da hikima, da ƙarfi, da girma, da ɗaukaka, da yabo!” 13 Kuma sai na ji kowace halittad da ke Sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa, da bisa teku, da kuma dukkan abin da ke cikinsu, suna cewa, “Yabo, da girma, da ɗaukaka, da mulki sun tabbata ga wannan da ke zaune a kan gadon sarauta, da Ɗan Ragon nan, har abada abadin!” 14 Sai rayayyun halittan nan huɗu suka ce, “Amin!” Dattawan nan kuma suka faɗi suka yi sujada.

6

Ɗan Ragon ya Ɓamɓare Hatiman Littafi

To, ina gani sa’ad da ɗan Ragon nan ya ɓamɓare ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai, sai na ji ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan huɗu ta yi magana kamar tsawar aradu, ta ce, “Zo.” 2 Da na duba sai ga wani farin doki, mahayinsa kuma, na da baka; sai aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara don ya ƙara cin nasara.

3 Da ya ɓamɓare hatimi na biyu, sai na ji rayayyiyar halittan nan ta biyu ta ce, “Zo.” 4 Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izini ya ɗauke aminci daga duniya, don mutane su kashe juna; aka kuma ba shi wani babban takobi.

5 Da ya ɓamɓare hatimi na uku, sai na ji rayayyiyar halittan nan ta uku ta ce, “Zo.” Da na duba sai ga wani bakin doki, mahayinsa kuwa da mizani a hannunsa. 6 Sai na ii kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittan nan huɗu, tana cewa, “Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha’ir dinari guda, sai dai kada ka ɓata mai da kuma ruwan inabi!”

7 Da ya ɓamɓare hatimi na huɗu, sai na ji muryar rayayyiyar halittan nan ta huɗu, ta ce, “Zo.” 8 Da na duba sai ga doki kili, sunan mahayinsa kuwa Mutuwa, Hades kuma na biye da shi. Sai aka ba su iko a kan rubu’in duniya, su yi kisa da takobi, da yunwa, da annoba, da kuma namun daji na duniya.

9 Da ya ɓamɓare hatimi na biyar, sai na ga rayukan waɗanda aka kashe saboda Maganar Allah, da shaidad da suka yi, a ƙarƙashin Wurin ƙona turaren wuta. 10 Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Tsattsarka, Mai gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jinimmu gun mazauna duniya?” 11 Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce da su su huta dai kaɗan, har sai an cika adadin abokan bautarsu, kuma ’Yan’uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.

12 Da ya ɓamɓare hatimi na shida, sai na duba, sai kuwa aka yi wata babbar rawar-ƙasa, sai rana ta yi baƙi ƙirin, gudan wata ya zama kamar jini, 13 taurari kuma suka faɗi ƙasa, kamar yadda ɓaure ke zub da ɗanyun ’ya’yansa, in ƙasaitacciyar iskar bazara ta kaɗa shi, 14 sararin sama sai ya dare ya naɗe kamar tabarma, sai aka kau da kowane dutse da kowane tsibiri daga mazauninsa. 15 Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma’arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwarmi, da kuma cikin duwatsu, 16 suna ce da duwatsun “Ku faɗo kammu, ku ɓoye mu daga idon wannan da ke zaune kan gadon sarautar, da kuma fushin ɗan Ragon nan, 17 don babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya jure mata?”

7

Keɓewar Bayin Allah

Bayan wannan sai na ga mala’iku huɗu, tsaye a kusurwa huɗu ta duniya, suna tsare da iskokin nan guda huɗu na duniya, don kada wata iska ta busa kan ƙasa, ko kan teku, ko kan wata bishiya. 2 Sai na ga wani mala’ika na hawa daga mafitar rana, riƙe da hatimin Allah Rayayye. Sai ya yi wa mala’ikun nan huɗu magana da murya mai ƙarfi, waɗanda aka bai wa ikon azabtad da ƙasa da teku, 3 yana cewa, “Kada ku azabtad da ƙasa ko teku ko bishiyoyi, sai mun buga wa bayin Allahmmu hatimi a goshinsu tukuna.” 4 Sai na ji adadin waɗanda aka buga wa hatimin, dubu ɗari da arba’in da huɗu ne, daga kowace kabilar Bani Isra’ila; 5 wato an yi wa dubu goma sha biyu hatimi daga kabilar Yahuda, dubu goma sha biyu daga kabilar Ruben, dubu goma sha biyu daga kabilar Jada, 6 dubu goma sha biyu daga kabilar Ashira, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa, 7 dubu goma sha biyu daga kabilar Simiyan, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Isakar, 8 dubu goma sha biyu daga kabilar Zebulun, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, dubu goma sha biyu kuma daga kabilar Bunyamunu, aka buga wa hatimin.

Ƙasaitaccen Taro Wanda ya Fi Gaban Ƙirge

9 Bayan wannan sai na duba, sai ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al’umma, da kabila, da jama’a, da harshe, suna tsaitsaye a gaban gadon sarautar, kuma a gaban ɗan Ragon, saye da fararen riguna, da tankar dabino a hannunsu, 10 suna ta da murya da ƙarfi, suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahmmu wanda ke zaune a kan gadon sarauta, da kuma ɗan Rago!” 11 Dukkan mala’iku kuwa na tsaitsaye kewaye da gadon sarautar, da dattawan nan, da kuma rayayyun halittan nan guda huɗu, sai suka faɗi a gaban gadon sarautar suka yi wa Allah sujada 12 suna cewa, “Hakika! Yabo, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da girma, da iko, da ƙarfi su tabbata ga Allahmmu har abada abadin! Amin.”

13 Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya yi mini magana, ya ce, “Suwanene waɗannan da ke saye da fararen riguna, daga ina kuma su ke?” 14 Sai na ce masa, “Ya shugaba, ai ka sani.” Sai ya ce da ni, “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.

15 Saboda haka ne su ke gaban gadon sarautar Allah,
Suna bauta masa dare da rana a Tsattsarkan Mazauninsa.
Na zaune kan gadon sarautan nan kuwa zai kare su da Zatinsa,
16 Ba za su ƙara jin yunwa ba, ba kuma za su ƙara jin ƙishirwa ba,
Ba za su ƙara jin zafin rana ko wani ƙuna ba sam.
17 Don ɗan Ragon nan da ke tsakiyar gadon sarauta, shi zai zama makiyayinsu,
Zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai,
Kuma Allah zai share musu dukkan hawaye.”

8

Mala’iku Bakwai Masu Kakaki Bakwai

Sa’ad da ɗan Ragon ya ɓamɓare hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a Sama kamar rabin sa’a. 2 Sannan sai na ga mala’ikun nan bakwai da ke tsaiwa gaban Allah, am ba su kakaki bakwai. 3 Sai kuma wani mala’ikan ya zo ya tsaya a gaban Wurin ƙona turaren wuta, riƙe da tasar zinariya ta ƙona turaren wuta. Sai aka ba shi turaren wuta mai yawa, don ya haɗa da addu’o’in tsarkaka duka a kan Wurin ƙona turaren wuta na zinariya a gaban gadon sarautar. 4 Sai hayaƙin turaren wutar ya tashi daga hannun mala’ikan tare da addu’o’in tsarkaka, ya isa gaban Allah. 5 Sai mala’ikan ya ɗauki tasan nan ta ƙona turaren wuta, ya cika ta da wuta daga Wurin ƙona turaren wutar, ya watsa a kan duniya; sai aka yi ta tsawar aradu, da kararraki masu tsanani, da walkiya, da kuma rawar ƙasa.

6 Sannan sai mala’ikun nan bakwai masu kakaki bakwai ɗin nan suka yi shirin busa su.

7 Mala’ikan farko ya busa kakakinsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini, aka zuba su duniya, sai sulusin duniya ya kone, sulusin bishiyoyi suka ƙone, kuma dukkan ɗanyar ciyawa ta ƙone.

8 Sai mala’ika na biyu ya busa kakakinsa, sai aka jefa wani abu a teku kamar wani babban dutse mai tsawo, mai cin wuta. 9 Sai sulusin teku ya zama jini, sulusin halittad da ke ruwa suka mutu, kuma sulusin jiragen ruwa suka halaka.

10 Sai mala’ika na uku ya busa kakakinsa, sai wani babban tauraro ya fado daga Sama, yana cin wuta, sai ya faɗa a sulusin koguna da maɓuɓɓugan ruwa. 11 Sunan tauraron kuwa Ɗaɗɗata. Sai sulusin ruwaye suka zama masu daci, sai mutane da yawa suka mutu saboda shan ruwan, don am mai da shi ɗaɗɗata.

12 Mala’ika na huɗu ya busa kakakinsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin wuni, haka kuma a sulusin dare.

13 Sannan da na duba, sai na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Bala’i Bala’i Bala’i a kanku, ku mazauna duniya, in an yi busan sauran kakakin da mala’ikun nan uku ke shirin busawa!”

9

Sai mala’ika na biyar ya busa kakakinsa, sai na ga wani tauraron da ya faɗa duniya daga sama, sai aka ba shi mabuɗin ramin mahalaka. 2 Ya kuwa buɗe ramin mahalakar, sai wani hayaƙi kamar na babbar matoya ya taso, har hayaƙin ramin nan ya duhunta rana da sararin sama. 3 Sai fari suka fito duniya daga cikin hayaƙin nan, sai aka ba su ikon harɓi irin na kunamin duniya. 4 Aka kuwa hana su cutar ciyayin duniya, ko tsiro, ko kowace bishiya, sai dai mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu. 5 Aka kuwa yarje musu su yi musu azaba har wata biyar, amma kada su kashe su; azabatasu kuwa kamar ta kunama ta ke, in ta harɓi mutun. 6 A waɗannan kwanaki kuwa mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba, za su ƙagauta su mutu, mutuwa kuwa sai ta guje musu.

7 Kamannin farin nan kuwa kamar dawaki ne da suka ja batar yaƙi, a kansu kuma da,wani abu kamar kambin zinariya, fuskatasu kuwa kamar ta mutun, 8 gashinsu kamar na mace, haƙorinsu kuma kamar na zaki. 9 Suna da ɓawo kamar kumakumai, dirin fikafikansu kuwa kamar dirin kekunan doki masu yawa ne suna rugawa fagyan yaƙi, 10 wutsiyatasu kamar ta kunama, ga kuma ƙari, ikonsu na ji wa mutane ciwo har wata biyar kuwa a wutsiyatasu ya ke. 11 Sarkinsu kuwa da ke iko da su shi ne mala’ikan mahalakar, sunansa da Yahudanci Abadan, da Helenanci kuwa Afaliyan.

12 Bala’in farko ya wuce, ga kuma bala’i biyu har wa yau tafe.

13 Sannan sai mala’ika na shida ya busa kakakinsa, sai na ji wata murya daga kahonin nan huɗu na Wurin ƙona turaren wuta na zinariya a gaban Allah, 14 tana ce da mala’ikan nan na shida mai kakaki, “Saki mala’iku huɗun nan da ke ɗaure a babban kogin nan Furatu.” 15 Sai aka saki mala’ikun nan huɗu, waɗanda aka tanada saboda wannan sa’a, da wannan rana, da wannan wata, da wannan shekara, su kashe sulusin ’yan’adan. 16 Yawan rundunonin sojan doki kuwa, na ji adadinsu zambar dubu metan ne. 17 Ga kuwa yadda na ga dawakin a wahayin da aka yi mini: Sojan doki na saye da kumakumai, launinsu ja kamar wuta, da shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta; kawunan dawakan kuma kamar na zaki, kuma wuta da hayaƙi da farar wuta na fita daga bakinsu. 18 Da waɗannan bala’i uku aka kashe sulusin ’yan’adan, wato da wuta, da hayaƙi, da farar wuta da ke fita daga bakinsu. 19 Domin ikon dawakan nan na bakinsu da wutsiyarsu, wutsiyoyinsu kamar macizai su ke, har da kawuna, da su ne su ke azabtarwa.

20 Sauran ’yan’adan waɗanda bala’in nan bai kashe ba kuwa, ba su tuba sun rabu da abubuwan da suka yi da hannunsu ba, ba su kuma daina yin sujada ga aljannu, da gumakan zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na dutse, da na itace ba, waɗanda ba sa iya gani, ko ji, ko tafiya; 21 ba su kuma tuba da kashe-kashen-kai da suka yi ba, ko sihirinsu, ko fasikancinsu, ko kuma sace-sacensu.

10

Ƙaƙƙarfan Mala’ika da Ƙaramin Littafi

Sannan sai na ga wani ƙaƙƙarfan mala’ika na saukowa daga Sama, lulluɓe da gajimare, da bakangizo bisa kansa, fuskatasa kamar rana, kafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta. 2 Da wani ɗan ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa, 3 ya yi kira da murya mai ƙarfi, kamar zaki na ruri. Da ya yi kiran sai aradun nan bakwai suka yi tsawa. 4 Sa’ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa, “Ƙyale abin da aradun nan bakwai suka ce, kada ka rubuta.” 5 Sai mala’ikan nan da na gani tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama, 6 ya rantse da wannan da ke raye har abada abadin, wanda ya halicci Sama da abin da ke cikinta, da ƙasa da abin da ke cikinta, da kuma teku da abin da ke cikinsa, cewa ba sauran wani jinkiri kuma, 7 sai dai a lokacin busa kakakin da mala’ika na bakwai zai busa ne, za a cika zuzzurfan al’amarin Allah, bisa bisharad da ya yi wa bayinsa annabawa.

8 Sannan sai muryan nan da na ji daga Sama ta sake yi mini magana, ta ce, “Je ka ka ɗauki littafin nan da ke buɗe a hannun mala’ikan da ke tsaye bisa teku da ƙasa.” 9 Sai na je wurin mala’ikan, na ce da shi ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce da ni, “Karɓi ka cinye, zai yi maka daci a ciki, amma a baka kamar zuma ya ke don zaƙi.” 10 Sai na karɓi ɗan ƙaramin littafin daga hannun mala’ikan, na cinye. Sai ya yi zaki kamar zuma a bakina, amma da na cinye, sai cikina ya ɗau daci. 11 Sai kuma aka ce mini, “Lalle ne ka sake yin annabci game da jama’a iri-iri, da al’ummai, da harsuna, da kuma sarakuna da yawa.”

11

Mashaida guda Biyu

Sannan sai aka ba ni wata gora kamar sanda, aka kuma ce da ni, “Tashi ka auna Wuri Tsattsarka na Allah, da Wurin Baiko, da kuma masu sujada a ciki, 2 amma kada ka auna harabar Wuri Tsattsarka, ka ƙyale ta, don am ba da ita ga sauran al’umma, kuma za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba’in da biyu. 3 Zan kuma yi wa mashaidana biyu baiwa su yi faɗin annabci kwana dubu da metan da sittin, suna saye da tsummoki.”

4 Waɗannan su ne bishiyoyin zaitun ɗin nan guda biyu, da fitilun nan biyu da ke tsaye gaban Ubangijin duniya. 5 In kuwa wani na niyyar cutarsu, sai wuta ta huro daga bakinsu, ta lashe maƙiyansu; duk mai niyyar cutarsu kuwa ta haka ne lalle za a kashe shi. 6 Suna da ikon hana ruwan sama, don kada a yi ruwa duk kwanakin da su ke yin maganar annabci; suna kuma da iko a kan ruwaye, su mai da su jini, su kuma ɗora wa duniya kowane irin bala’i, duk lokacin da su ke so. 7 Kuma bayan sun ƙare shaidarsu, sai muguwar dabba mai fitowa daga mahalaka tă yaƙe su, ta ci su, ta kuma kashe su, 8 a kuma bar gawawakinsu a kan titin babban birnin nan da a ke kira Saduma da Masar ga ma’ana, inda aka giciye Ubangijinsu. 9 Mutanen dukkan jama’a da kabila da harshe da al’umma za su riƙa kallon gawawakinsu har kwana uku da rabi, su kuwa ƙi yarda a binne su. 10 Kuma mazauna duniya sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagaIi, suna a’aika wa juna kyauta, domin annabawan nan biyu ɗin sun azabtad da mazauna duniya. 11 Amma bayan kwana uku da rabin nan, sai Ruhun rai madawwami daga wurin Allah ya shige su, suka tashi tsaye, matsanancin tsoro kuma ya rufe waɗanda suka gan su. 12 Sai suka ji wata murya mai ƙara daga Sama tana ce da su, “Ku hawo nan!” Sai suka tafi Sama a cikin gajimare, maƙiyansu na gani. 13 Nan take sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, kuma sai ushirin garin ya zube, mutun dubu bakwai aka kashe a rawar ƙasar, sauran kuwa suka tsorata, suka ɗaukaka Allah Mai Sama.

14 Bala’i na biyu ya wuce; ga kuma bala’i na uku na zuwa nandanan.

15 Sannan mala’ika na bakwai ya busa kakakinsa, sai aka ji wasu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijimmu da na Almasihunsa, kuma shi zai yi mulki har abada abadin.” 16 Kuma sai dattawan nan ashirin da huɗu da ke zaune a kan gadajensu na sarauta a gaban Allah suka faɗi suka yi wa Allah sujada, 17 suna cewa,

“Mun gode maka, ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
Wanda ya ke shi ne a yanzu, shi ne kuma a dā,
Saboda ka ɗauki ikonka mai girma, kana mulki.
18 Al’ummai sun fusata, fushinka kuwa ya sauko,
Lokaci ya yi da za a yi wa matattu shari’a,
A kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako,
Da masu jin tsoron sunanka, yaro da babba,
A kuma hallaka masu hallaka duniya.”

19 Sannan sai aka buɗe Tsattsarkan Mazaunin nan na Allah da ke Sama, kuma sai aka ga Sunduƙin Alkawarinsa a Mazauninsa Tsattsarka. Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da tsawar aradu masu yawa, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya-manya.

12

Mace Mai haifuwa

Kuma sai aka ga wata babbar alama a Sama, wata mace na lulluɓe da rana, tana tsaye a kan wata, da kuma kambi mai taurari goma sha biyu a kanta. 2 Tana da ciki, kuma sai ta yi ta ƙara ta ƙagauta ta haifu, saboda azabar naƙuda. 3 Sai kuma aka ga wata alama a Sama, sai ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa. 4 Sai wutsiyatasa ta sharo sulusin taurari, ta zuba su ƙasa. Sai macijin ya tsaya a gaban matan nan mai naƙuda, don ya lanƙwame ɗan nata in ta haife shi. 5 Sai kuwa ta haifi da namiji, wanda zai mallaki dukkan al’ummai da tsanani ƙwarai, amma sai aka fyauce ɗan nata, aka kai shi wurin Allah da gadon sarautarsa. 6 Matar kuwa sai ta gudu ta shiga jeji, inda Allah ya shirya mata wurin da za a cishe ta bar kwana dubu da metan da sittin.

Yaƙi ya Tashi a Sama

7 Sai yaƙi ya tashi a Sama, Mika’ilu. da mala’ikunsa suna yaƙi da macijin nan, macijin kuma da mala’ikunsa suka yi ta yaƙi, 8 amma sai aka ci su, har suka rasa wuri a Sama sam. 9 Sai aka jefa ƙaton macijin nan ƙasa, wato macijin nan na tun aru-aru, wanda a ke kira Iblis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi duniya, mala’ikunsa ma aka jefa su tare da shi. 10 Sai na ji wata murya mai ƙara a Sama tana cewa, “Yanzu fa ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahmmu, da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana, don an jefa mai saran ’Yan’uwammu ƙasa, shi da ke saransu dare da rana a gun Allahmmu. 11 Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin Maganad da suka shaida, don ba su yi tattalin ransu ba, har abin ya kai su ga kisa. 12 Saboda haka sai ku yi farinciki, ya ku Sammai, da ku mazauna ciki. Amma kun shiga uku, ke ƙasa da ke teku! Don Iblis ya sauko gare ku cikin matsanancin fushi, don ya san lokacinsa ya kure.”

13 Da macijin nan ya ga an jefa shi ƙasa, sai ya fafari matan nan da ta haifi da namiji, da tsanani. 14 Amma sai aka ba matar fikafikan nan biyu na babban juhurman nan, don ta tashi ta guje wa maciiin nan, ta shiga jeji, ta je wurin da za a cishe ta lokaci ɗaya, da lokatai, da rabin lokaci. 15 Sai macijin ya kwarara ruwa daga bakinsa kamar kogi daga bayan matar, wai don ya share ta da ambaliya. 16 Amma sai ƙasa ta taimaki matar; ita ƙasar ta buɗe bakinta ta hadiye kogin da macijin nan ya kwararo, daga bakinsa. 17 Sai macijin ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriyatata, wato waɗanda ke kiyaye urnarnin Allah, su ie kuma shaidar Yesu. Sai ya tsaya a kan yashin teku.

13

Wata Dabba daga Teku Kuma sai na ga wata muguwar dabba na fitowa daga cikin teku, mai kaho, goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta 2 Muguwar dabbad da na gani kuwa kamar damisa ta ke, ƙafafunta kamar na bear, bakinta kuma kamar na zaki. Macijin kuwa ya ba ta ƙarfinsa, da gadon sarautarsa, da ikonsa mai girma. 3 Ɗaya daga cikin kawunanta an yi masa rauni kamar na ajali, amma sai rauninsa mai kamar na ajalin nan ya warke. Sai muguwar dabbar ta ɗauke wa duk duniya hankali, suna mamaki, 4 har suka yi wa macijin nan sujada, don shi ne ya bai wa muguwar dabbar ikonsa, suka kuma yi wa dabbar sujada, suna cewa, “Wa yai ya dabban nan? Wa kuma zai iya yaƙi da ita?” 5 An kuwa ba muguwar dabban nan baki, tana fahari da maganganun saɓo, aka kuma yarje mata zartad da iko har wata arba’in da biyu. 6 Sai ta buɗe bakinta don ta saɓi Allah, ta yi ta saɓon sunansa, da Mazauninsa, wato mazauna a Sama. 7 Aka kuma yarje mata ta yaƙi tsarkaka, ta ci su. Aka kuma ba ta iko a kan kowace kabila, da jama’a, da kowane harshe, da kowace al’umma. 8 Duk mazauna duniya kuma za su yi mata sujada, wato duk wanda tun farkon duniya ba a rubuta sunansa ba a Littafin Rai Madawwami na Ɗan Ragon nan da ke yankakke. 9 Duk mai kunnen ji, yă ji.

10 Kowa aka ƙaddara wa bauta, sai ya je aikin bautar.
Kowa kuwa ya kashe da takobi, to, da takboi za a kashe shi lalle.
Wannan shi ke nuna jimiri da bangaskiya na tsarkaka.

Wata Dabba daga Ƙasa

11 Sannan sai na ga wata muguwar dabbar na fitowa daga cikin ƙasa. Tana da ƙaho biyu kamar ɗan rago, maganarta kuwa kamar ta macijin nan. 12 Tana zartad da duk ikon muguwar dabban nan ta farko a kan idonta, tana kuma sa duniya da duk mazauna cikinta su yi wa muguwar dabban nan ta farko sujada, wadda aka warkar mata da rauninta mai kamar na ajali. 13 Tana yin manya-manyan abubuwan al’ajabi, har ma tana sa wuta ta zuba ƙasa daga sama, a gaban idon mutane. 14 Kuma tana yaudarar mazauna duniya, da abubuwan al’ajabin nan da aka yarje mata yi a gaban muguwar dabban nan, tana umartarsu su yi wata sura saboda muguwar dabban nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu. 15 An kuma yarje mata ta busa wa surar muguwar dabban nan rai, har surar muguwar dabban nan ma ta iya yin magana, ta kuma sa a kashe waɗanda suka ƙi yi wa surar muguwar dabban nan sujada. 16 Har wa yau sai ta sa a yi wa kowa alama a hannun dama, ko a goshi, manya da yara. duka, mawadata da matalauta, ɗa da bawa, 17 har ba mai iya saye ko sayarwa sai ko yana da alaman nan, wato sunan muguwar dabban nan, ko kuma lambar sunanta. 18 Wannan abu sai game da hikima. Duk mai basira ya ƙididdige lambar muguwar dabban nan, don lamba ce ta wani mutun, lambar kuwa ɗari shida ce da sittin da shida.

14

Masu Bin ɗan Ragon Duk Inda ya je

Sannan sai Ina duba, sai ga ɗan Ragon nan tsaye a kan Dutsen Sihiyona, akwai kuma mutun dubu ɗari da arba’in da huɗu tare da shi, waɗanda aka rubuta sunan Ubansa, a goshinsu. 2 Sai na ji wata murya daga Sama, kamar ƙugin ruwaye masu gudu, kamar tsawar aradu mai ƙara, muryad da na ji kuwa kamar masu molo ne na kidan molo. 3 Kuma suna rera wata sabuwar waƙa a gaban gadon sarautar, kuma a gaban rayayyun halittan nan huɗu, kuma a gaban dattawan nan. Ba mai iya koyon waƙan nan sai mutun dubu ɗari da arba’in da huɗu ɗin nan, waɗanda aka fanso daga duniya. 4 Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma su ke bin ɗan Ragon duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane kan su ne tumun fari na Allah, kuma na ɗan Ragon nan, 5 babu wata ƙarya a bakinsu, don su marasa aibu ne.

6 Sannan sai na ga wani mala’ikan yana kadawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar Bishara don ya sanad da ita ga mazauna duniya, wato ga kowace al’umma, da kabila, da harshe, da jama’a. 7 Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, don lokacinsa na yin hukunci ya yi. Kuma ku yi masa sujada, shi da ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma maɓuɓɓugan ruwaye.”

8 Sai wani mala’ika na biyu ya biyo, yana cewa “Ta faɗi! Babila mai girma ta faɗi! Ita da ta zuga dukkan al’ummai su yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita.”

9 Sai kuma wani mala’ika na uku ya biyo, yana daga murya da ƙarfi, yana cewa, “Duk mai yi wa muguwar dabban nan da surarta sujada, wanda kuma ya yarda a yi masa alama a goshinsa, ko a hannunsa, 10 zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa; za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala’iku tsarkaka, da kuma, ɗan Ragon. 11 Kuma hayaƙin azaban nan tasu sai ya dinga tashi har abada abadin, ba su da wani rangwame dare da rana, wato waɗannan masu yi wa muguwar dabban nan da surarta sujada, da kuma duk wanda ya yarda aka yi masa alamar sunanta.”

12 Wannan shi ke nuna jimirin tsarkaka, masu kiyaye umarnin Allah da kuma bangaskiya ga Yesu.

13 Sai kuma na ji wata murya daga Sama, tana cewa, “Rubuta wannan: Albarka tā tabbata ga matattu, wato waɗanda za su mutu nan gaba kan su na Ubangiji ne.” Ruhu Tsattsarka ya ce, “Hakika, masu albarka ne, don su huta daga wahalarsu, gama aikinsu na biye da su!”

Dawowar Ɗam Mutun

14 Sannan sai na duba, sai ga wani farin gajimare, da wani kamar Ɗam Mutun zaune a kan gajimaren, da kambin zinariya a kansa, da kakkaifan lauje a hannunsa. 15 Sai wani mala’ika ya fito daga Tsattsarkan Mazaunin, yana magana da murya mai ƙarfi da wannan da ke zaune kan gajimaren, yana cewa, “Sa laujenka ka yanke, don lokacin yanka ya yi, amfanin duniya ya nuna sarai.” 16 Sai wannan da ke zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa duniya, amfanin duniya ya yanku.

17 Wani mala’ikan kuma ya fito daga Tsattsarkan Mazauni a Sama, shi ma kuwa yana da kakkaifan lauje. 18 Sai kuma wani mala’ikan ya fito daga Wurin ƙona turaren wuta, wato mala’ikan da ke iko da wutar, sai ya yi magana da murya mai ƙarfi da wannan mai kakkaifan laujen, ya ce, “Sa laujenka ka yanke nonnan inabin duniya, don inabin ya nuna.” 19 Sai mala’ikan ya wurga laujensa duniya, ya tattara inabin duniya, ya zuba cikin babbar mamatsar inabi ta azabar Allah. 20 An tattake mamatsar inabin kuwa a bayan gari ne, jini kuma ya yi ta gudana daga mamatsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil metan.

15

Mala’iku Bakwai Masu Bala’i Bakwai

Sai kuma na ga wata alamar a Sama, mai girma, mai ban mamaki, mala’iku bakwai masu bala’i bakwai, waɗanda su ke su ne bala’in ƙarshe, don su ne iyakacin azabar Allah.

2 Sai na ga wani abu kamar bahar ɗin gilas, gauraye da wuta, na kuma ga waɗanda suka yi nasara da muguwar dabban nan, da surarta, da kuma lambar sunanta, a tsaitsaye a bakin bahar ɗin gilas, da molayen yabon Allah a hannunsu. 3 Suna rera waƙad da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda a ke yi wa ɗan Ragon nan, suna cewa,

“Ayyukanka manya-manya ne, kuma masu ban mamaki,
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki!
Hanyoyinka na gaskiya ne, kuma daidai su ke,
Ya Sarkin al’ummai.
4 Wanene ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, ya kuma ɗaukaka sunanka?
Domin kai kaɗai ne tsattsarka.
Dukkan al’ummai za su zo su yi maka sujada,
Don hukuncinka na gaskiya yā bayyana.”

5 Bayan wannan sai na duba, sai aka buɗe Tsattsarkan Mazaunin Alfarwar Shaida a Sama, 6 sai mala’iku bakwai ɗin nan masu bala’i bakwai suka fito daga Tsattsarkan Mazaunin, saye da tufafin linen mai tsabta, mai ɗaukar ido, da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu. 7 Sai ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan guda huɗu, ta ba mala’ikun nan bakwai tasoshi bakwai na zinariya, cike da azabar Allah, shi da ke raye har abada abadin. 8 Sai Tsattsarkan Mazaunin ya cika da hayaƙi mai fitowa daga maɗaukakin Zatin Allah, da kuma ikonsa. Kuma ba mai iya shiga Tsattsarkan Mazaunin nan sai bayan bala’i bakwai na mala’ikun nan bakwai sun ƙare.

16

Sai na ji wata murya mai ƙara daga Tsattsarkan Mazauni, tana ce da mala’ikun nan bakwai, “Ku je ku juye tasoshin nan bakwai na azabar Allah a kan duniya.”

2 Daganan sai mala’ikan farko ya je ya juye tasatasa a kan duniya, sai kuwa wasu miyagun miyaku masu azabtarwa suka fito a jikin mutanen da su ke da alamar muguwar dabban nan, su ke kuma yi wa surarta sujada.

3 Mala’ika na biyu ya juye tasa tasar a cikin teku, sai duk ya zama kamar jinin mataccen mutun, kowane abu mai rai na cikm teku kuma ya mutu.

4 Mala’ika na uku ya juye tasa tasar a cikin koguna da maɓuɓɓugan ruwaye, sai suka zama jini. 5 Sai na ji mala’ikan ruwaye na cewa,

‘Kai mai gaskiya ne cikin hukuncin nan naka,
Ya kai Tsattsarka, wanda ka ke a yanzu, ka ke kuma a dā.
6 Don mutane sun zub da jinin tsarkaka da annabawa,
Ga shi kuwa ka ba su jini su sha.
Sakamakonsu ke nan!”
7 Sai na ji Wurin kona turaren wuta na ƙara, yana cewa,
“Hakika, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,
Hukuncinka daidai ya ke, kuma na gaskiya ne!”

8 Sai mala’ika na huɗu ya juye tasa tasar a kan rana, sai aka yarje mata ta ƙona mutane da wuta. 9 Sai matsanancin zafin ya kona mutane, har suka zagi sunan Allah, shi da ke iko da waɗannan bala’i, ba su kuwa tuba sun ɗaukaka shi ba.

10 Sai mala’ika na biyar ya juye tasa tasar a kan gadon sarautar muguwar dabban nan, sai mulkinta ya zama duhu, har mutane suka ciji harshensu don azaba, 11 sai suka zagi Allah Mai Sama saboda azabatasu da miyakunsu, ba su kuma tuba da ayyukansu ba.

12 Sai mala’ika na shida ya juye tasa tasar a cikin babban kogin nan Furatu, sai ruwansa ya kafe, don a shirya wa sarakuna, daga gabas tafarki. 13 Kuma na ga baƙaƙen aljannu masu kama da kwaɗi guda uku, suna fitowa daga bakin macijin nan, da bakin muguwar dabban nan, da kuma bakin annabin nan na ƙarya, 14 su iskoki ne, aIjannu masu yin abubuwan al’ajabi, masu zuwa wurin sarakunan duniya duka, don su tara su saboda yaƙi a Babbar Ranan nan ta Allah Maɗaukaki. 15 (“Ga ni nan tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda ke zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”) 16 Sai suka tattara su a wurin da a ke kira Armagadan da Yahudanci.

17 Sai mala’ika na bakwai ya juye tasa tasar a sararin sama, sai aka ji wata murya mai ƙara daga Tsattsarkan Mazauni, wato daga gadon sarautar, ta ce, “An gama!” 18 Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da tsawar aradu, da wata babbar rawar ƙasa irin wadda ba a taɓa yi ba, tun da ɗan’adan ke duniya, gawurtacciyar rawar ƙasa ƙwarai da gaske. 19 Sai babban birnin nan ya rabu gida uku, biranen al’ummai kuma suka faɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta ta sha azabatasa mai tsananin gaske. 20 Kowane tsibiri kuma ya ɓace, manyan duwatsu ma ba a ƙara ganinsu ba. 21 Wasu manya-manyan ƙanƙara kuma kamar kayan jaki suka fado kan mutane daga sama, har mutane suka zagi Allah saboda bala’in ƙanƙarar. Kai, bala’in nan da matuƙar ban tsoro ya ke!

17

Hukuncin Maƙiyan Almasihu

Sai ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu tasoshin nan bakwai, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka hukuncin da za a yi wa babbar karuwan nan, wadda ta ke zaune bisa ruwaye masu yawa, 2 wadda sarakunan duniya suka yi fasikanci da ita, wadda kuma mazauna duniya suka jaraba da yim fasikanci da ita.” 3 Sai ya ɗauke ni ya tafi da ni jeji, Ruhu Tsattsarka na iza ni, sai na ga wata mace a kan wata dabba ja wur, duk jikin dabbar sunayen saɓo ne, tana kuma da kawuna bakwai, da ƙaho goma. 4 Matar kuwa tana saye da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma ja wur; ta ci ado da kayan gwal, da duwatsun alfarma, da lu’ulu’u; tana riƙe da kofin zinariya a hannunta, cike da abubuwan ƙyama, da ƙazantar fasikancinta. 5 A goshinta kuma an rubuta wani sunan sirri, “Babila mai girma, uwar karuwai, kuma uwar abubuwa masu ban ƙyama na duniya.” 6 Sai na ga matar ta bugu da jinin tsarkaka, da kuma jinin mashaidan Yesu.

Da na gan ta sai na yi mamaki ƙwarai da gaske. 7 Amma sai mala’ikan ya ce da ni, “Dom me ka ke mamaki? Zan buɗa maka sirrin matan nan, da kuma na muguwar dabban nan mai kawuna bakwai, da ƙaho goma, da ke ɗauke da ita. 8 Muguwar dabban nan da ka gani, wadda dā ta ke nan, yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahalaka, ta je ta halaka; kuma mazauna duniya waɗanda tun farkon duniya ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai Madawwami ba, za su yi mamakin ganin muguwar dabbar, don da tana nan, yanzu ba ta, kuma za ta dawo. 9 Fahintar wannan abu kuwa sai game da hikima. Wato, kawuna bakwai ɗin nan tuddai ne guda bakwai, waɗanda matar ke zaune a kai. 10 Har wa yau kuma sarakuna ne guda bakwai, waɗanda biyar daga cikinsu aka tuɓe, ɗaya na nan, ɗayan kuwa bai zo ba tukuna, sa’ad da ya zo kuwa lalle zamaninsa na lokaci kaɗan ne kawai. 11 Muguwar dabbad da ke nan da, yanzu kuwa ba ta, ita ce ta takwas, kuma daga cikin bakwai ɗin nan ta fito, za ta kuwa halaka. 12 Ƙahonin nan goma kuwa da ka gani, sarakuna goma ne waɗanda ba a naɗa ba tukuna, amma sa’a ɗaya tak za a ba su ikon mulki tare da dabbar. 13 Waɗannan ra’ayinsu ɗaya ne, kuma za su bai wa muguwar dabban nan ikonsu da sarautarsu. 14 Za su yaki ɗan Ragon, kuma Ɗan Ragon zai ci su, shi da waɗanda ke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, kuma amintattu, don shi ne Ubangijin iyayengiji.”

15 Sai mala’ikan nan ya ce da ni, “Ruwayen nan da ka gani, inda karuwan nan ke zaune, jama’a ce iri-iri, da taro masu yawa, da al’ummai, da harsuna. 16 Kahonin nan goma kuma da ka gani, wato su da muguwar dabban nan za su ƙi kauwar, su washe ta, su tsiraita ta, su cinye moriyatata, sa’an nan su ƙone ta, 17 domin Allah ya nufe su da zartad da nufinsa, su zama masu ra’ayi ɗaya, su bai wa dabban nan mulkinsu, har sai an cika Maganar Allah. 18 Matan nan da ka gani kuwa, ita ce babban birnin da ke mulkin sarakunan duniya.”

18

Babila Mai girma ta Faɗi

Bayan haka sai na ga wani mala’ikan na saukowa daga Sama, mai iko mai yawa, sai aka haskaka duniya da ɗaukakarsa. 2 Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce,

“Ta faɗi! Babila mai girma ta faɗi!
Ta zama mazatmin aljannu,
Matattarar kowane baƙin aljani,
Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.
3 Dukkan al’ummai sun yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita,
Sarakunan duniya kuma sun yi fasikanci da ita,
Attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
4 Kuma sai na ji wata muryar daga Sama, tana cewa,
“Ku fito daga cikinta, ya ku jama’ata,
Kada zunubanta su shafe ku,
Kada bala’inta ya taɓa ku,
5 Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai bar sama,
Allah kuma ya tuna da laifuffukanta.
6 Ku yi mata abin da ita ma ta yi,
Ku biya ta ninkin ayyukanta,
Ku dama mata biyun abin da ta dama muku.
Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci,
Haka ku ma sai ku saka mata da azaba, da baƙinciki, gwargwadon haka.
Tun da ya ke a birnin zuciyatata ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a kan gadon sarauta na ke,
Ni ba matad da mijinta ya mutu ba ce,
Ni da baƙinciki kuma har abada!’
8 Saboda haka bala’inta zai aukam mata rana ɗaya,
Mutuwa, da baƙinciki, da yunwa.
Za a kuma ƙone ta,
Don Ubangiji Allah da ke hukunta ta mai ƙarfi ne.”

Kuma sarakunan duniya da suka yi fasikanci da zaman almubazzaranci da ita, za su yi mata kuka da kururuwa, in sun ga hayaƙin ƙunatata, 10 za su tsaya can nesa, don tsoron azabatata, su ce,

“Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni!
Ya kai birni mai ƙarfi, Babila!
Cikin sa’a ɗaya hukuncinka ya sauko.”

11 Attajiran duniya kuma suna yi mata kuka suna baƙinciki, tun da ya ke ba mai ƙara. sayen kayansu, 12 wato zinariya, da azurfa, da duwatsun alfarma, da lu’ulu’u, da lallausan linen, da haja mai ruwan jar garura, da siliki, da jan alharini, da icen ƙanshi iri-iri, da kayan hauren giwa iri-iri, da kayan da aka sassaka da ice mai tsada, da na tagulla, da na bakin ƙarfe, da na dutse mai sheƙi, 13 da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur, da lubban, da ruwan inabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawaki, da kekunan doki, da kuma bayi, wato rayukan ’yan’adan.

14 “Amfanin da kika ƙwallafa rai a kai, har ya kuɓuce miki,
Kayan annashuwarki da na adonki sun ɓace miki, ba kuwa za a ƙara samunsu ba har abada!”

15 Attajiran waɗannan hajoji da suka arzuta game da ita, za su tsaya can nesa don tsoron azabatata, suna kuka, suna baƙinciki, suna cewa,

16 “Kaito! Kaiton babban birnin nan!
Wanda dā ya sa lallausan linen, da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma jan alharini,
Wanda ya ci ado da kayan gwal, da duwatsun alfarma, da lu’ulu’u!
17 Domin a cikin sa’a ɗaya duk dumbun dukiyan nan ta halaka.”

Sai duk kyaftin-kyaftin ɗin jiragen ruwa, da fasinjoji, da masu tuƙi, da duk waɗanda cinikinsu ya gamu da bahar, suka tsaya can nesa, 18 suna kururuwa da suka ga hayaƙin ƙunatasa, suna cewa,

“Wane birni ne ya yi kama da babban birnin nan?”
19 Har suka tula wa kansu ƙasa suna ta kuka, suna baƙinciki, suna kururuwa, suna cewa,
“Kaito! Kaiton babban birnin nan!
Wanda duk masu jiragen ruwa a bahar suka arzuta da ɗumbun dukiyatasa,
Cikin sa’a ɗaya ya halaka.
20 Ku yi farinciki saboda an yi masa haka, ya ke Sama,
Da ku tsarkaka, da manzanni, da masu yin faɗin Maganar Allah,
Don Allah ya rama muku abin da ya yi muku.”
21 Sai wani ƙaƙƙarfan mala’ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen nika, ya jefa cikin teku, ya ce,
“Haka za a fyaɗa Babila babban birni da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.
22 Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba;
Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana’a a cikinki ba;
Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba;
23 Fitila ba za ta ƙara haskakawa a cikinki ba;
Ba kuma za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba;
Don attajiranki dā su ne ƙusoshin duniya,
An kuma yaudari dukkan al’ummai da sihirinki,
24 Har an tarar hakkin jinin annabawa da na tsarkaka na wuyanta, da kuma na duk waɗanda aka kashe a duniya.”

19

Waƙar Halleluyah a Sama

Bayan wannan sai na ji kamar wata sowa mai ƙarfi ta ƙasaitaccen taro a Sama, suna cewa,

“Halleluyaha! Yin ceto, da ɗaukaka, da iko, sun tabbata ga Allahmmu,
Don hukuncinsa daidai ya ke, kuma na gaskiya ne,
Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da fasikancinta,
Ya kuma ɗauki fansar jinin bayinsa a kanta.”

3 Sai suka sake yin sowa, suna cewa,

“Halleluyah! Hayaƙinta na tashi har abada abadin.”

4 Sai dattawan nan ashirin da huɗu, da rayayyun halittan nan huɗu, suka faɗi suka yi wa Allah sujada, shi da ke zaune a kan gadon sarauta, suna cewa, “Amin. Halleluyah!” 5 Sai aka ji wata murya daga gadon sarautar, tana cewa,

“Ku yabi Allahmmu, ya ku bayinsa,
Ku da ke jin tsoronsa, yaro da babba.”

6 Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwaye masu gudu, kamar tsawar aradu masu ƙara, suna cewa,

“Halleluyah! Gama Ubangiji Allahmmu Maɗaukaki shi ke mulki.
7 Mu yi ta murna da farinciki matuƙa, mu kuma ɗaukaka shi,
Don bikin Ɗan Ragon nan ya zo,
Amaryatasa kuma ta kintsa.
8 An yarje mata ta sa tufafin lallausan linen mai ɗaukar ido, mai tsabta”,

domin lallausan linen ɗin nan shi ne aikin gaskiya na tsarkaka.

9 Sai mala’ikan ya ce da ni, “Rubuta wannan: Albarka tā tabbata ga waɗanda, aka gayyata cin abincin bikin Ɗan Ragon nan. “ Kuma ya ce da ni, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.” 10 Sai na faɗi a gabansa in yi masa sujada, amma sai ya ce da ni, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’Yan’uwanka, waɗanda ke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Don yi wa Yesu shaida, shi ne ainihin faɗar annabci.

11 Sai na ga Sama ta dare, sai ga wani farin doki! Mahayinsa ana ce da shi Amintacce, Mai gaskiya, yana hukuncin gaskiya, yana kuma yaƙi. 12 Idanunsa kamar harshen wuta su ke, kansa kuma da kambi da yawa; yana kuma da wani suna a rubuce, wanda ba wanda ya sani sai shi. 13 Yana saye da riga wadda aka tsoma a jini, kuma sunan da a ke kiransa da shi, shi ne Kalmar Allah. 14 Kuma rundunonin Sama, saye da lallausan linen fari mai tsabta, suna biye da shi a kan fararen dawaki. 15 Da wani kakkaifan takobi a bakinsa tsinin gaba, wanda zai sare al’ummai da shi, zai kuwa mulke su da tsanani ƙwarai, zai tattake mamatsar inabi ta tsananin azabar Allah Maɗaukaki. 16 Da wani suna a rubuce a jikin rigatasa, har daidai cinyatasa, wato, Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.

17 Sannan sai na ga wani mala’ika tsaye a jikin rana. Sai kuma ya kira dukkan tsuntsaye da ke kaɗawa a tsakiyar sararin sama, da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ku zo, ku taru wurin babban bikin nan na Allah, 18 ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaƙi, da naman ƙarfafa, da naman dawaki, da na mahayansu, da naman kowa da kowa, wato na ɗa da na bawa, na yaro da na babba.” 19 Sai na ga muguwar dabban nan, da sarakunan duniya, da rundunoninsu, sun taru su yaƙi wannan da ke kan dokin, da kuma rundunatasa. 20 Sai aka kama muguwar dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al’ajuba a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda aka yi musu alamar muguwar dabban nan, da kuma waɗanda suka yi wa surarta sujada. Waɗannan biyun sai aka jefa su da ransu cikin tafkin wuta mai cin duwatsun wuta. 21 Sauran kuwa aka sare su da takobin wannan da ke kan doki, wato da takobin nan da ke bakinsa tsinin gaba. Dukkan tsuntsaye kuwa suka ci namansu har suka yi gamba.

20

An Ɗaure Shaiɗan Shekara Dubu

Sannan sai na ga wani mala’ika na saukowa daga Sama, yana riƙe da mabuɗin mahalaka, da kuma wata babbar sarƙa a hannunsa. 2 Sai ya kama macijin nan, wato macijin nan na tun aru-aru, wanda ya ke shi ne Iblis, kuma Shaiɗan, ya ɗaure shi har shekara dubu, 3 ya jefa shi mahalakar, ya rufe, ya kuma yimƙe ta da hatimi, don kada ya ƙara yaudarar al’ummai kuma, har dai shekarun nan dubu su ƙare. Bayan wannan lalle ne a sake shi ɗan lokaci kaɗan.

Tashin Matattu Na Farko

4 Sannan sai na ga gadajen sarauta, da waɗanda aka ba wa ikon hukunci zaune a kai. Har wa yau kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidad da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa muguwar dabban nan da surarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamatata a goshinsu ko a hannunsu ba; sun sake rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu. 5 Sauran matattu kuwa ba su sake rayuwa ba sai bayan da shekarun nan dubu suka cika. Wannan fa shi ne tashin matattu na farko. 6 Duk wanda ya rabanta da tashin nan na farko mai albarka ne, kuma tsattsarka ne. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kan irin waɗannan, amma za su zama masu kusantar Allah da Almasihu, su kuma yi mulki tare da shi har shekara dubu.

An Jefa Iblis Tafkin Wuta

7 Kuma bayan shekarun nan dubu sun ƙare, sai a sau Shaiɗan daga ɗaurinsa, 8 ya kuma fito ya yaudari al’ummai waɗanda ke kusurwoyin nan huɗu na duniya, wato Yajuju da Majuju, ya tattara su saboda yaƙi, yawansu kamar yashin teku. 9 Sai kuma su bazu su mamaye duk duniya, su yi wa sansanin tsarkaka da ƙaunataccen birni ƙawanya; amma sai wuta ta zubo daga sama ta lashe su. 10 Shi kuwa Iblis mayaudarinsu, sai aka jefa shi tafkin wuta na duwatsun wuta, inda muguwar dabban nan da annabin nan na ƙarya su ke, kuma za a gwada musu azaba dare da rana har abada abadin.

Ranar Hisabi

11 Sannan sai na ga wani babban gadon sarauta fari, da wanda ke zaune a kai; sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace. 12 Sai na ga matattu manya da yara, tsaitsaye a gaban gadon sarautar, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda ya ke shi ne Littafin Rai Madawwami.

Aka kuwa yi wa matattu shari’a bisa abin da ke rubuce cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi. 13 Sai teku ta ba da matattun da ke cikinta, Gun Matattu da Hades kuma suka ba da matattun da ke gare su, aka kuwa yi wa kowa shari’a gwargwadon aikin da ya yi. 14 Sannan aka jefa Mutuwa da Hades tafkin nan na wuta. Wannan ita ce mutuwa ta biyu, wato tafkin wuta. 15 Kuma duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai Madawwami ba, sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.

21

Sabuwar Sama da Sabuwar Ƙasa

Sannan sai na ga sabuwar sama da sabuwar ƙasa, don sama ta farko da ƙasa ta farko sun shuɗe, babu kuma sauran teku. 2 Kuma sai na ga tsattsarkan birni, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga cikin Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amarya ta yi ado saboda mijinta. 3 Sai kuma na ji wata murya mai ƙara daga gadon sarautar, tana cewa, “Kun ga, mazaunin Allah na cikin mutane. Zai zauna a cikinsu, za su kuma zama jama’atasa, Allah kuma shi kansa zai kasance tare da su, 4 zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙinciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”

5 Sai na zaune a kan gadon sarautar ya ce, “Kun ga, ina yin komai sabo.” Ya kuma ce, “Rubuta wannan, don maganan nan tabbatacciya ce, kuma ta gaskiya ce.” 6 Sai ya ce da ni, “An gama! Ni ne Alfa, ni ne Omiga, ni ne Azal, ni ne kuma Matuƙa. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai madawwami kyauta. 7 Duk wanda ya ci nasara, zai ci wannan gado, wato in zama Allahnsa, shi kuma ya zama da gare ni. 8 Amma matsorata, da marasa amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da duwatsun wuta, wanda ya ke shi ne mutuwa ta biyu.”

Amaryar ɗan Rago

9 Sai kuma ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu tasoshin nan bakwai cike da bala’i bakwai na ƙarshe, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka Amarya, matar ɗan Ragon.” 10 Sai ya ɗauke ni, Ruhu Tsattsarka na iza ni, ya kai ni wani babban dutse mai tsawo, ya nuna mini tsattsarkan birnin Urushalima yana saukowa daga cikin Sama daga wurin Allah, 11 yana tare da maɗaukakin Zatin Allah. Hasken birnin na ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutsen alfarma, kamar jasfa a, garau kamar ƙarau. 12 Yana da babbar ganuwa mai tsawo, da ƙofar gari goma sha biyu; a ƙofofin kuma da mala’iku goma sha biyu, a jikin ƙofofin kuma an rubuta sunayen kabilun nan goma sha biyu na Bani Isra’ila, 13 a gabas ƙofa uku, arewa ƙofa uku, kudu ƙofa uku, yamma kuma ƙofa uku. 14 Ganuwar birnin kuwa tana da dutsen harsashi goma sha biyu; a jikinsu kuma an rubuta sunayen Manzannin nan goma sha biyu na ɗan Ragon.

15 Shi wanda ya yi mini maganar kuwa yana da sandan awo na zinariya, don ya auna birnin, da ƙofofinsa, da ganuwatasa. 16 Birnin muraɓɓa’i ne, tsawonsa da faɗinsa duka ɗaya ne. Sai ya auna birnin da sanɗansa, mil dubu da ɗari biyar, tsawonsa da faɗinsa da zacinsa duka ɗaya su ke. 17 Ya kuma auna ganuwatasa, kamu ɗari da arba’in da huɗu ne na mutun, wato na mala’ika ke nan. 18 Ganuwar kuwa da jasfal aka gina ta, birnin kuma da zinariya zalla, garau kamar gilas. 19 An kuma ƙawata harsasan ganuwar birnin da kowane irin dutsen alfarma. Jasfa, shi ne na farko, na biyu safaya, na uku agata, na huɗu emerala, 20 na biyar onikis, na shida kamiliyan, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras , na sha ɗaya jasin, na sha biyu kuma amisisti. 21 Ƙofofin gari goma sha biyun nan kuwa lu’ulu’u ne goma sha biyu, kowace ƙofa da lu’ulu’u guda aka yi ta, titin birnin kuwa zinariya ce zalla, garau kamar gilas.

Ba Za a yi Dare a Can ba

22 Ban kuwa ga wani Ɗakin Ibada a birnin ba, don Ɗakin lbadatasa Ubangiji Allah Maɗaukaki ne, da kuma ɗan Ragon. 23 Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, don maɗaukakin Zatin Allah shi ne haskensa, ɗan Ragon kuma fitilarsa. 24 Da haskensa al’ummai za su yi tafiya. Sarakunan duniya za su kawo ɗaukakarsu gare shi. 25 Ƙofofinsa kuwa ba za a rufe su da rana ba har abada, ba kuwa za a yi dare a can ba. 26 Za a kuma kawo ɗaukakar al’ummai da girmansu gare shi. 27 Amma ko kaɗan ba wani abu marar tsarki da zai shiga cikinsa, ko wani mai aikata abin ƙyama ko ƙarya, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a Littafin Rai Madawwami na ɗan Ragon kaɗai.

22

Kogin Rai da Bishiyar Rai

Sannan sai ya nuna mini kogin ruwan rai madawwami, yana ƙyalli kamar ƙarau, yana gudana daga gadon sarautar Allah shi da ɗan Rago. 2 ta tsakiyar titin birnin; kuma ta kowane gefen kogin akwai bishiyoyin rai madawwami masu haifuwar ’ya’ya iri goma sha biyu, kowane wata suna haifuwa, ganyen bishiyoyin kuwa saboda lafiyar al’ummai ne. 3 Ba sauran wani abin la’antarwa, amma gadon sarautar Allah shi da ɗan Rago zai kasance a cikinsa. Bayinsa za su bauta masa, 4 za su kuma ga fuskatasa, sunansa kuwa zai kasance a goshinsu. 5 Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila ko na rana ba, don Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni’imar mulki har abada abadin.

6 Sai ya ce da ni, “Wannan magana tabbatacciya ce, kuma ta gaskiya ce. Kuma Ubangiji, Allahn ruhohin masu yin faɗin Maganar Allah, ya aiko mala’ikansa, ya nuna wa. bayinsa abin da lalle ne ya auku ba da daɗewa ba. 7 Ga shi kuwa ina zuwa da wuri.”

Albarka tā tabbata ga wanda ke kiyaye maganar annabcin littafin nan.

8 Ni Yohana, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa’ad da kuwa na ji su na kuma gan sun, sai na faɗi a gaban mala’ikan da ya nuna mini su, don in yi masa sujada. 9 Amma sai ya ce da ni, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’Yan’uwanka masu yin faɗin Maganar Allah, da kuma waɗanda ke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”

10 Kuma sai ya ce da ni, “Kada ka rufe maganar annabcin littafin nan, domin lokaci ya kusa. 11 Marar gaskiya yă yi ta rashin gaskiyatasa, fajiri yă yi ta fajircinsa, mai aikin gaskiya kuwa, yă yi ta aikin gaskiyatasa, wanda ke keɓe a tsarkake kuwa ya zauna a tsarkake.”

12 “Ga shi ina zuwa da wuri, tare da sakamakon da zan yi wa kowa gwargwadon abin da ya yi. 13 Ni ne Alfa, ni ne Omiga, ni ne Na Farko, ni ne Na Ƙarshe, ni ne Azal, ni ne kuma Matuƙa.”

14 Albarka tā tabbata ga masu wanke rigunansu, don su sami izinin ɗiba daga bishiyar rai madawwami, su kuma shiga birnin ta ƙofa. 15 Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda ke son ƙarya, ya ke kuma yinta.

16 “Ni Yesu, na aiko mala’ikana gare ka da wannan shaida saboda ikiliziyai. Ni ne tsatson Dawuda, kuma zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”

Duk mai jin Ƙishirwa ya zo

17 Ruhu Tsattsarka da Amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata yă ɗebi ruwan rai madawwami kyauta.

18 Ina yi wa duk mai jin maganar annabcin littafin nan kashedi, in wani ya yi wani ƙari a kanta, Allah zai ƙara masa bala’in da aka rubuta a littafin nan. 19 In kuma wani ya yi ragi a maganar littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na bishiyar rai madawwami, da na tsattsarkan birni, waɗanda aka rubuta a littafin nan.

20 Shi wanda ya shaidi abubuwan nan ya ce, “Hakika, ina zuwa da wuri.” Amin. Zo, ya Ubangiji Yesu.

21 Alherin Ubangiji Yesu yă tabbata ga dukkan tsarkaka. Amin.