HAUSA

PREFACES

&

EUCHARISTIC PRAYERS

 

Prepared by
Joseph Kenny, O.P., and Musa Ɗanjuma

 

The Hausa Translation Commission
of the Northern Dioceses of Nigeria
1976


INTRODUCTION

The Hausa Translation Commission of the northern Dioceses, under the chairmanship of Bishop Christopher Abba, issued a draft version of the Prefaces and the Eucharistic Prayers on 6 June 1975.

The translation was by Musa Ɗanjuma and Fr. Joseph Kenny, O.P., with considerable input from Fr. Malachy Cullen, O.S.A. Corrections were made with the help of (the late) Fr. Bruno Kowalkowski, O.P. (+ 10 Aug 1998), Fr. Ces Prazan, O.P. (+ 5 July 1998), Isiyaku Adamu, Gabriel Sabo, Siman Sani, and Bulus Barau. The texts were read by 35 students at the Malumfashi Catechetical Training Centre, for further input reflecting the widely different parts of the North.

The Eucharistic Prayers were then revised by the Commission and finalized in April 1976. I made two changes only: (1) I used the spelling "Ikiliziya" instead of "Ekiliziya", to be consistent with the Preface texts (and current usage). (2) I propose once again the phrase "Ɗan Ragon Allah", rather than "Ɗan tunkiya", simply because "ɗa" in this case does not mean "son", but is a diminutive. Ɗan tunkiya means "little female sheep". "Ɗan Rago" means "little male sheep". It would be an error to think that "rago" stands for a human father, while "tunkiya" represents Mary.

I am disappointed that an important proposal of the 1976 Commission has still not been effected in Hausa liturgical books. And that is the use of the word "yarjejeniya" (covenant) in the consecration of the wine, instead of "alkawari" (promise). A covenant is a two-way contract with obligations on both sides. That is in no way conveyed by the word "alkawari" (from Arabic القول —a "saying" or "statement").

I am not sure the 1976 texts were consulted in preparing the editions now in print, since I left the North and moved to Ibadan that year.

The Prefaces, untouched over the years, I went over this year (2009), consulting Fr. Cullen's detailed annotations as well as the Latin, and made a number of revisions.

The text here presented uses Unicode Hausa characters, which are readable on any platform.


SHIRIN KYAUTAYI

A ƙarshe

Mu yi addu'a a lokacin da za a miƙa hadaya ta dukan Ikiliziya.

Saboda ɗaukakar Allah da ceton duniya.

[Easy to say, brief form, after the French: "Pour la gloire de Dieu et le salut du monde".]


SU GABARTAWA

A farkon kownensu:

Ubangiji ya zama tare da ku.

Tare da kai ma.

Ku faranta zukatanku.

Mun far anta su a gaban Ubangiji.

Mu yi godiya wa Ubangijin Allah.

Kyakkyawan abu, daidai ne kuma.

 

1.  Zuwan Almasihu 1

Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Da ya fara zuwa wurinmu
sai ya ƙasƙantad da kansa,
ya kuwa ɗauki jiki irin namu.
Ta haka ya cika nufinka
wanda ka shirya tun dā,
ya kuwa buɗe mana hanyar ceto.
Yanzu muna zuba ido
ga ranar da zai sake zuwa da ɗaukaka,
don ya cika alkawarinsa
ya kuwa ba mu cikakken ceton da muke marmari.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

2.  Zuwan Almasihu 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Annabawa duka sun yi annabcin zai zo.
Mahaifiyarsa Mariya Budurwa ta yi cikinsa
da ƙauna mai yawan gaske.
Yohana mai yin babtisma ya yi shelar zai zo,
ya kuma nuna shi wa mutane da ya zo.
Yanzu Yesun nan yana so mu yi shiri
ga idin haifuwarsa da murna,
don sa'ad da ya zo ya same mu
muna addu'a, muna yabonsa.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

3.  Haifuwar Almasihu 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Domin yau ka haskaka zukatammu
da sabon hasken ɗaukakarka,
inda madawwamiyar Kalimarka ta zama mutum.
Gama a cikin Yesun nan mai ganuwa
mun gane Allah mara ganuwa,
ana kuwa ɗauke hankalimmu ga ƙaunarsa.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

4.  Haifuwar Almasihu 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Shi Allah ne wanda ba ya ganuwa,
amma yau ya bayyana kansa da kamannin mutum.
Tun fil'azal shi Ɗa ne a gare ka,
amma yau aka haife shi ga kabilar 'yan'adan
Ya zo domin ya ta da masu karaya,
ya shirya tsakanin masu ja-in-ja,
ya kuma kirawo ɓatattun mutane ga mulkin sama.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

5.  Haifuwar Almasihu 3
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Domin yau Yesu ya yi aiki mai ban mamaki don cetommu,
watau shi Kalmarka ya ɗauki kumamancin 'yan'adan,
mutum mai mutuwa kuwa ya ɗauki dawwamar Allah.
Gama cikin Yesu ne dukkanmu
muka shiga darajar Allah.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

6.  Bayyanuwar Ubangiji
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Gama asirin ceton da ka shirya mana dun dā
yau ne ka bayyan shi cikin Almasihu,
wanda ya ke haskaka al'umman duniya duka.
Da ma ya bayyana gare mu kamar mutum,
ka ɗaukaka mu da nasa madawwamin rai.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

7.  Babtismar Ubangiji
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ka nuna yardarka da babtisma
wanda aka yi wa Ɗanka cikin Kogin Urdun
ta yin wasu al'ajiban da suka shaida
sabuwar yarjejeniyar da ka yi da mu.
Muryarka da aka ji daga sama ta nuna
Kalmarka ya zama mutum a cikinmu.
Ruhunka kuwa wanda ya sauko da siffar kurciya
ya nuna yadda baranka Yesu
ka naɗa shi Almasihu,
ya yi wa matalauta Bishara ta farinciki.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

8.  Shirin Faska 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Kowace shekara kana kiran mu amintattunka
mu yi shiri domin idin Faska
da tsabtar zuciya da murna.
idan mun yi aikin ƙauna a gidajemmu da ko'ina,
idan kuma mun riƙa yin asirin hadayar Yesu
wadda ta mai da mu 'ya'yanka,
za ka kuwa kai mu ga cikakkiyar daraja ta 'ya'yanka.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

9.  Shirin Faska 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ka keɓe wa 'ya'yanka wannan lokaci
don a tsarkake zukatammu,
a kuma 'yanta mu daga muguwar sha'awa,
don mu yi zamammu a wannan duniya mai shuɗewa
muna ta neman abubuwan da ba za su shuɗe ba.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

10.  Shirin Faska 3
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ka zaɓar mana wata hanya ta yin godiya
ta rage wa kammu more wa arzikin duniya.
Ta haka kana horon son kammu,
kana ma sa mu mu kwaikwayi alherinka
ta ba matalauta abin da muka hana kammu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

11.  Shirin Faska 4
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ta hanyar azumimmu kana horon muguntammu,
kana ɗaga tunanimmu zuwa sama,
kana ƙarfafa mu domin mu yi ayyukan kirki,
mu kuma sami madawwamin lada
ta wurin Yesu Almasihu Ubangimimmu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

12.  Shirin Faska, Lahadi na 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ya yi azumin kwana arba'in,
yana nuna mana abin da ya kamata mu yi
a lokacin nan na shirin Faska.
Da ya dage wa kirsoshin Sheɗan,
ya koya mana yadda ya kamata
mu giji waswasin mugunta,
domin mu yi wannan bikin Faska
da hankali mai dacewa da asirinta,
mu ma kai madawwamin bikin Faska a sama.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

13.  Shirin Faska, Lahadi na 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Bayan ya gaya wa almajiransa yadda zai mutu,
ya tafi da su a kan wani tsauni,
ya nuna masu ɗaukakarsa.
Musa da Iliya sun shaida gaskiya ne
Yesu zai sha wahala, ya mutu,
kāna zai tashi daga mutuwa zuwa ɗaukakarsa.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

14.  Shirin Faska, Lahadi na 3, Shekara ta fari
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Da ya roƙi Basamariyar ta ba shi ruwan sha,
ya rigaya ya ba ta kyautar bangaskiya.
Da ya yi begen bangaskiyarta ta ƙaru,
sai kuma ya kunna ƙaunarka a zuciyarta.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

15.  Shirin Faska, Lahadi na 4, Shekara ta fari
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Lokacin da mu 'yan'adan mu ke zagawa cikin duhu,
ya zama mutum don ya ba mu hasken bangaskiya.
Haka ma mu da aka haife mu cikin bautar zunubi,
ya sake haifuwarmu da ruwan babtisma,
don mu zama 'ya'yan Allah.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

16. Shirin Faska, Lahadi na 5, Shekara ta fari
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Da ya ke shi mutum ne,
har kuka ya yi a kan rasuwar abokinsa Li'azaru.
Da ya ke shi madawwamin Allah ne kuma,
ya ta da Li'azaru daga kabari.
Saboda tausayinsa ga 'yan'adam dukka ma,
ta hanyar babtisma da cimarsa
ya raya mu da raywa ta Allah.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

17. Azabar Yesu 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Azabar da Ɗanka ya sha
ta kawo ceton dukkan 'yan'adan,
ta kuwa sa kowanemmu ya yabi ɗaukakarka.
Gama ta mafificin ikon gicciye
ka hukunta duniya,
ka ma sa Yesu ya yi sarautar dukkan 'yan'adan.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

18.  Azabar Yesu, Lahadi
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ko da ya ke ba shi da laifi,
ya yarda ya sha wahala domimmu masu laifi.
Sai ta mutuwarsa ya shafe zunubammu,
ta tashinsa kuwa daga mutuwa
ya sulhunta mu da kai.

19. Azabar Yesu 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Yanzu muna kusa da ranakun
da ya sha wahala domin cetommu,
ya kuma tashi daga mutuwa zuwa ɗaukakarsa.
Muna tare da shi a lokacin nan
da ya yi nasara a kan alfaharin Sheɗan
ya ma yi aikin cetommu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

20.  Alhamis mai tsarki, na kirisim
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ta man nan na Ruhu Mai Tsarki
ka shafa makaɗaicin Ɗanka,
ka naɗa shi babban limami.
Ta hikimarka da ƙaunarka ga Ikiliziyarka kuma
ka sa makaɗaicin limancin Yesu
ya riƙa zama a wurimmu.
Gama ya ba dukan jama'arsa darajar nan
ta limancinsa na kusantar Allah Sarki.
Da ƙaunarsa gare mu dukka kuma
ya zaɓi wasu daga cikimmu
don a sa masu hannuwa,
su yi wa jama'arka hidima da jagoranci.
Limaman nan, da ikon sunanka,
su kan sa hadayar nan ta Yesu a gabanka,
wadda ta kawo ceton mutane.
Su kan kuma sa cimar nan ta Yesu a gabammu,
inda su ke nuna mana ƙaunarsa mai girma.
Su kan koya mana maganarka;
su kan ƙarfafa mana rai kuma
ta sakiramentu iri iri.
Limaman nan kuma su kan ba da ransu
saboda kai da kuma ceton 'yan'uwanswu,
suna kwaikwayon Yesu har su zama masu kama da shi.
Wannan amana tasu da kai
ta nuna zurfin ganbaskiyarsu d ƙaunarsu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

21.  Cimar Ubangiji 1 (Alhamis mai tsarki)
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Shi madawwamin limami ne na gaske
wanda ya kafa hadaya irin wada ba za ta ƙare ba.
Ya fara miƙa maka hadayar kansa don cetommu,
ya ma umurce mu mu dinga miƙa wannan hadaya
domin tunawa da shi.
Jikinsa wanda aka bayas domimmu,
in mun ci shi, yana ƙarfafa mu.
Jininsa kuma wnada aka zubas domimmu,
in mun sha shi, yana wanke mu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

22.  Faska 1 (Satin Faska na fari)
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
tum ba a /daren nan/ ranar nan/ lokacin nan ba
da aka yanka hadayarmu ta Faska,
watau Yesu Almasihu.
Shi Ɗan Rago ne na gaske
wanda ya ɗauki zunuban duniya.
Ta mutuwarsa ya shafe tamu mutwa;
ta tashinsa daga kabari kuma ya ba mu sabon rai.
Saboda haka, Ikiliziyarka a dukan duniya tana murna,
tana yabon ka saboda aiki mai girma
wanda ka yi mana ta Faskar Almasihu.
Dukkan mala'iku da tsarkakan sama kuma
suna shelar darajarka, suna rerawa:

23.  Faska 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
tum ba a lokacin nan ba
da aka yanka hadayarmu ta Faska,
watau Yesu Almasihu.
Ta wurinsa a ke haifuwar 'ya'yan haske
ga madawwamin rai,
ana kuma buɗe ƙofofin sama
don masu imani su shiga.
Gama mutuwar Yesu ta fanshe mu daga mutuwa,
tashinsa daga kabari kuwa
ya ta da mu duka zuwa ga rai.
Saboda haka, Ikiliziyarka a dukan duniya tana murna,
tana yabon ka saboda aiki mai girma
wanda ka yi mana ta Faskar Almasihu.
Dukkan mala'iku da tsarkakan sama kuma
suna shelar darajarka, suna rerawa:

24.  Faska 3
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
tum ba a lokacin nan ba
da aka yanka hadayarmu ta Faska,
watau Yesu Almasihu.
Ba ya dena miƙa hadayar kansa gare ka domimmu;
kullum ma yana tsaya mana a wurinka.
Domin ko da ya ke an taɓa kashe shi, yana raye;
ko da ya ke an yanka shi, ba zai sake mutuwa ba.
Saboda haka, Ikiliziyarka a dukan duniya tana murna,
tana yabon ka saboda aiki mai girma
wanda ka yi mana ta Faskar Almasihu.
Dukkan mala'iku da tsarkakan sama kuma
suna shelar darajarka, suna rerawa:

25.  Faska 4
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
tum ba a lokacin nan ba
da aka yanka hadayarmu ta Faska,
watau Yesu Almasihu.
Gama an rushe tsohon mulkin zunubi,
an ta da masu sunkwiyawa da baƙinciki,
an ba mu kuma cikakken rai cikin Almasihu.
Saboda haka, Ikiliziyarka a dukan duniya tana murna,
tana yabon ka saboda aiki mai girma
wanda ka yi mana ta Faskar Almasihu.
Dukkan mala'iku da tsarkakan sama kuma
suna shelar darajarka, suna rerawa:

26.  Faska 5
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
tum ba a lokacin nan ba
da aka yanka hadayarmu ta Faska,
watau Yesu Almasihu.
Da ya miƙa maka hadayar jikinsa a kan gicciye,
ya cika dukan hadayun tsohuwar yarjejeniya.
Da ya sanya kansa a hannunka domin cetommu,
an gane yadda ya ɗauki matsayin limami
da na bagadi da na rago duk gaba ɗaya.
Saboda haka, Ikiliziyarka a dukan duniya tana murna,
tana yabon ka saboda aiki mai girma
wanda ka yi mana ta Faskar Almasihu.
Dukkan mala'iku da tsarkakan sama kuma
suna shelar darajarka, suna rerawa:

27.  Hawan Yesu sama 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Gama shi Ubangijimmu Yesu, Sarkin ɗaukaka,
wanda ya ci nasarar zunubi da mutuwa,
(yau) ya hau birbishin sama,
dukan mala'iku kuwa suna ta kallon shi.
Yana zaune can gidan sama
a Matsakaicin mutane da Allah,
Alkalin duniya, da kum Sarkin sarakuna.
Bai nufi ya bar mu nan a halin ƙasƙanci ba,
amma ya ba mu sa-zuciya
za mu bi shi wurin da ya tafi,
domin mu, da mu ke gaɓoɓin jikinsa,
mu haɗu da wanda ya ke kammu,
asalin rayuwarmu kuma.
Saboda haka, Ikiliziyarka a dukan duniya tana murna,
tana yabon ka saboda aiki mai girma
wanda ka yi mana ta Faskar Almasihu.
Dukkan mala'iku da tsarkakan sama kuma
suna shelar darajarka, suna rerawa:

28.  Hawan Yesu sama 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Bayan ya tashi daga mutwa,
ya nuna kansa ga manzanninsa,
don su gani, su tabbata shi ne.
Suna cikin kallon shi, aka yi sama da shi,
don ya ba mu rabo cikin darajarsa ta Allah.
Saboda haka, Ikiliziyarka a dukan duniya tana murna,
tana yabon ka saboda aiki mai girma
wanda ka yi mana ta Faskar Almasihu.
Dukkan mala'iku da tsarkakan sama kuma
suna shelar darajarka, suna rerawa:

29.  Saukowar Ruhu Mai Tsarki
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Gama mutanen da ka maishe su 'ya'yanka
ta yin tarayya da makaɗaicin Ɗanka
yau ne ka ba su Ruhu Mai Tsarki;
ta haka kuwa idin Faska ya kai ƙarshensa.
Ruhun nan a farawar Ikiliziya
ya ba mutane na ko'ina ganewar Allah kansa,
ya ma haɗa kan mutane masu harshe dabam dabam
don su yabe ka da shelar bangaskiya ɗaya.
Saboda haka, Ikiliziyarka a dukan duniya tana murna,
tana yabon ka saboda aiki mai girma
wanda ka yi mana ta Faskar Almasihu.
Dukkan mala'iku da tsarkakan sama kuma
suna shelar darajarka, suna rerawa:

30.  Tiriniti
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Gama ka bayyana mana asirin zamanka,
watau kai da makaɗaicin Ɗanka da Ruhu Mai Tsarki
ku abu uku ne, amma kun haɗu Allah ɗaya, Ubangiji ɗaya.
Mun dai gaskanta ɗaukakarka da ka bayyana mana
ita ɗaya ce ta Ɗanka da ta Ruhu Mai Tsarki,
ba wanda ya fi wani daraja.
Ta haka, mun yarda ku uku dabam dabam ne,
amma masu zati ɗaya da ɗaukaka ɗaya.
Kai ne mala'iku da manyan mala'iku,
da su Kerubim da Serafim,
ba su dena yabonka yau da gobe, suna rerawa:

31.  Cimar Ubangiji 2 (Corpus Christi)
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Da ya ke cin cimarsa ta ƙarshe
tare da manzanninsa,
sai ya miƙa maka kansa
kamar ɗan rago mara aibu,
hadaya ta cikakken yabo ke nan.
Ta haka ya bar mana ibadar tunawa
da azabarsa a kan giciye,
don ya kawo wa 'yan'adan ceto
har zuwa ƙarshen duniya.
Ta asirin wannan cimar Ubangiji
kana ƙosad da mu, kana kuma tsarkake mu,
domin 'yan'adan na dukan duniya,
bangaskiya ɗaya ta haskaka su,
ƙauna ɗaya kuma ta haɗa su.
Ga shi nan mun matso wannan sakiramenti mai girma
don ka shafe mu da mai na alherinka,
mu ma mu ɗau kamannin Yesu mai ɗaukaka.
Saboda haka, mazaunan sama da ƙasa
suna yabonka da sabuwar waƙa.
Mu ma mun haɗa baki da dukan mala'iku,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

32.  Zuciya mai tsarki ta Yesu
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Saboda yawan ƙaunad da ya yi mana
ya ba da kansa domimmu,
har aka ma ɗaga shi a kan gicciye.
Da soja ya soke shi da mashi a kwiɓi,
nan da nan sai ga gini da ruwa suka gudano.
Ta haka Yesu ya ba mu ruwan Babtisma
da kuma jininsa da za mu sha.
Gama zuciyarsa da aka buɗe
maɓuɓɓugar ceto ce,
tana jawo dukkan mutane
don dukammu mu riƙa sha ruwan rai da murna.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

33.  Almasihu Sarki
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ka shafe makaɗaicin Ɗanka
Yesu Almasihu Ubangijimmu
da man ƙanshi mai sa murna,
watau Ruhu Mai Tsarki,
don ka naɗa shi madawwamin limami
da sarkin 'yan'adan da dai dukan halitta.
Da ya miƙa hadayar kansa a kan gicciye,
hadaya mara aibi ke nan
wadda ke sulhunta mu da kai,
sai ya aikata ceton 'yan'adan,
ya ma mallaki dukkan halitta,
don ya mayar maka mulkin dukkan kome
wanda zai tabbata har abada.
A cikin mulkin nan sai ga gaskiya da rai,
ga tsarki da alheri,
ga kuma adalci da ƙauna da salama.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

34.  Lahadi 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ta gicciyensa da tashinsa daga mutuwa
ya fanshe mu daga zunubi da mutuwa.
Ya ma kira mu zuwa darajar nan
ta zama kabila zaɓaɓɓiya,
'ya'yan sarauta masu yin aikin limanci,
tsattsarkar al'umma,
da kuma jama'a mallakar Allah.
Ko'ina muna shelar aikinka mai girma,
gama ka kirawo mu daga cikin duhu,
muka shiga maɗaukakin haskenka.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

35.  Lahadi 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Domin yā ji ƙanmu masu bauɗewa,
ya zo duniya, haifaffe daga Budurwa Mariya.
Ta wahalar da ya sha a kan gicciye
ya fanshe mu daga mutuwa mara matuƙa.
Ta tashinsa kuma daga mutuwa
ya ba mu rai mara matuƙa.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

36.  Lahadi 3
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Kana nuna mana babbar ɗaukakarka
inda ka k yi mana agaji.
Amma ga hanyar agajin da ka zaɓa:
ka cece mu ta wurin wani ɗan'adan.
Kamar yadda Adamu kuwa ya ɓace gun wani ice,
haka ma Yesu ya cece mu a kan wani icen gicciye,
shi wanda ya ke Almasihu da Ubangijimmu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

37.  Lahadi 4
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ta wurin haifuwarsa a duniya
ya kau da kumamacimmu.
Ta wurin wahalarsa da mutuwa
ya shafe zunubammu.
Ta wurin tashinsa daga mutuwa
ya sa mu a kan hanyar madawwamin rai.
Ta hawansa kuma zuwa wurinka, ya Uba,
ya buɗe mana ƙofar gidan gaskiya.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

38.  Lahadi 5
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ka halicci dukan abubuwan duniya,
suna bin hanyar sauyin da ka ƙaddara masu.
Amma ka halicci mutum cikin kamanninka,
ka ma ba shi sarautar sauran halittarka,
don ya zama wakilinka a duniya,
ya kuma yabe ka koyaushe saboda al'ajibanka.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

39.  Lahadi 6
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ta gare ka ne mu ke rayuwa,
mu ke motse, muka kuma kasance.
Lokacin da mu ke a nan duniya
rahamarka tana kewaye da mu kullum,
gama kana ba mu abincin yini kowace rana,
har ma ka rigaya ka ba mu mafarin rai madawwami
ta zaman Ruhu Mai Tsarki a cikimmu.
Ruhun nan, wanda ya ta da Yesu daga mutuwa,
muna sa zuciya zai tashe mu kuma,
don mu rayu tare da Yesu har abada.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

40.  Lahadi 7
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Saboda ƙaunad da ka yi wa duniya,
har ka aiko mana da Macecin nan Yesu,
wanda ya zama kamar mu ta kowane hali,
sai dai bai ɗau zunubi ba.
Ta wajen yi maka biyayya kuwa
ya mayas mana baye-bayenka
waɗanda muka ɓata ta rashin biyayyarmu.
Ta dalilin kamarmu da shi ga kirki duk da jiki ne
ka ke ƙaunar mu da irin ƙaunar da ka ke yi masa.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

41.  Lahadi 8
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ko da ya ke ta yin zunubi ne
mu 'ya'yanka muka rabu da kai,
ka sake haɗa mu da kai
ta jinin Ɗanka da ikon Ruhu Mai Tsarki.
Ka ma tattara mu cikin Ekiliziya,
don mu mu zama ɗaya da juna
kamar yadda ka ke ɗaya, ya Uba,
da Ɗanka da Ruhu Mai Tsarki.
Ka maishe mu jikin Almasihu kuma
da mazaunin Ruhu Mai Tsarki.
Kash, ka yi aikin hikimarka mai dacewa da yabo!
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

42.  Ranukan sati 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ka nufi ka harhaɗa dukan abubuwa ta sarautarsa,
ka ma sa kowannemmu ya samu daga falala tasa.
Gama ko da ya ke da surar Allah ya ke,
ya mai da kansa baya matuƙa,
har ya zub da jininsa a kan gicciye
don ya kawo wa duniya salama.
Don haka an ɗaukaka shi bisa dukan kome,
ya ma zama tushen madawwamin ceto
ga dukan waɗanda ke yi masa biyayya.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

43.  Ranukan sati 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ta ƙaunarka ka halicci mutum,
ta adalcinka kuwa ka hukunta shi,
amma ta rahamarka ka cece shi,
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

44.  Ranukan sati 3
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ta wurin ƙaunataccen Ɗanka
ka halicce mu 'yan'adan,
ka ma ji ƙammu ta komad da mu ga kamanninka.
Don haka duk halitta tana bauta maka,
mu fansassu ma muna yabon ka,
tsarkakanka kuma na ɗaukaka ka baki ɗaya.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

45.  Ranukan sati 4
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ko da ya ke ba ka bukatar yabommu,
ta kyautarka ne mu ke iya yi maka godiya.
Ta yabon ka, ba wani abu mu ke ƙara maka ba,
sai ma mu ne mu ke cin gaba a kan hanyar ceto
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

46.  Ranukan sati 5
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Da ƙauna muna tunawa da mutuwarsa,
da ƙarfin bangaskiya muna shelar tashinsa,
ta tabbatacciyar sa-zuciya ma
muna jiran dawowarsa da ɗaukaka.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

47.  Ranukan sati 6
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin ƙaunataccen Ɗanka Yesu Almasihu.
Shi Kalmarka ne
wanda ka halicci duk komi ta wurinsa,
ka ma aiko mana da shi don ya cece mu.
Ta ikon Ruhu Mai Tsarki Budurwa Mariya ta haife shi;
ya ma yarda ya cika nufinka,
ya kuwa samo maka jama'a mai tsarki.
Saboda haka ya miƙa hannuwansa a kan gicciye,
yana shan azaba.
Ta haka ya ci nasara a kan mutuwa,
ya kuma nuna mana yadda za mu tashi zuwa rai.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

48.  Maryamu 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
mu kuma ɗaukaka ka da mafificin yabo

+  da mu ke tunawa da Budurwa Mariya mai tsarki

++  (a idin nan na: ......)

Ita ba ta taɓa haɗuwa da namiji ba,
amma ta ikon Ruhu Mai Tsarki
ta kawo wa duniya madawwamin hasken,
Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:


+   Ranukan sati, ran asabar, rukan tunawa:
Mai Lourdes, 11 Feb.
Mai Mount Carmel, 16 July
Tsarkakewar tata Basilica, 5 Aug.
Mai shan azaba, 15 Sept.
Miƙawa Mariyamu, 21 Nov.

++   Iduna masu girma:
Mariyamu Uwar Allah (1 Jan.)
ziyarar Mariyamu ga Alisabatu (31 May)
zuciya mai tsarki ta Mariyamu (Sat. after Sacred Heart)
Mariyamu Sarauniyar 'yan'adan (22 Aug.)
haifuwar Budurwa Mariyamu (8 Sept.)
Mariya Sarauniyar rosari (8 Oct.)


49. Maryamu 2
Lalle ya kamata mu yi maka godiya,
mu kuma yabe ka saboda darjar tsarkaka dukka,
amma da mu ke tunawa da Budurwa Mariya,
sai mu yi amfani da kalmomin waƙarta:
Ba shakka ka yi manyan al'amura har bangon duniya,
ka ma nuna tausayinka a dukan zamanai,
inda ka dubi ƙasƙancin baiwarka;
ta wurinta kuwa ka ba 'yan'adan Macecinsu
Ɗanka Yesu Almasihu Ubangijimmu.

50.  Mala'iku
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
mu kuma yabe ka saboda mala'ikunka.
Gama lokacin da mu ke girmama talikan nan
da ka same su cikin aminci,
hikimarka ce mu ke girmamawa ke nan.
Darajar da ka ba su kuma
ta nuna taka daraja mara iyaka,
mafiya dukan halitta girma.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

51.  Yusufu
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
mu kuma yabe ka da mafificin yabo
a wannan idi na tsattsarkan Yusufu.
Shi mai adalcin nan ne wanda ka zaɓa
ya zama mijin Budurwa Mariya Uwar Allah.
Shi kuma amintaccen wakilin nan mai hikima ne
da ka ba shi riƙon gidanka,
domin ya zama baban rukon makaɗaicin Ɗanka
wanda ta ikon Ruhu Mai Tsarki Mariya ta yi cikinsa,
shi Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

52.  Manzanni 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Kai madawwamin Makiyai ne
wanda ba ka yar da garkenka ba,
sai dai ta aikin tsarkakan manzanni
kana kula da su kullum.
Su wakilan Ɗanka ne
waɗanda ka sa su su yi kiwon garkenka,
su ma ja masu gora.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

53.  Manzanni 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Gama ka gina Ikiliziyarka bisa harsashin manzanni,
domin ta nuna wa duniya tsarkinka har ƙarshen zamanai,
ta kuma yi shelar bishararka ba fasawa ga dukan 'yan'adan.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

54.  Tsarkaka 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
A taron tsarkakanka ana yabonka,
a kan darajar da ka ba su.
Gama lokacin da ka ke ba su lada,
aikinka ne ka ke darajantawa a cikinsu.
Gama ka mai da su abin misali mu bi gurbinsu,
ka mai da su abokai masu sommu,
ka ma sa su su taimake mu da addu'o'insu.
Dubban shaidunka nan suna ƙarfafa mu
mu yi faman gaske a kan aikin da aka sa gabammu,
sai mun sami kambin ɗaukaka mara dusashewa,
tare da tsarkakan nan naka,
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

55.  Tsarkaka 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
A kowane zamani ka kan tayas tsarkakan mutane
don ka ba Ikiliziyarka sabon ƙarfi
da shaidarsu mai kyau,
ka ma nuna tabbatacciyar alama
ta ƙaunarka gare mu.
Mafificin misalin tsarkakan nan
yana tura mu mu bi gurbinsu;
addu'o'insu da ba fasawa kuma
suna taimakommu mu sami cikakken ceto.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

56.  Shaidu da jininsu
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Tsattsarkanka ....... ya nuna al'ajiban ikonka
inda ya bi misalin Almasihu,
ya ba da ransa domin shaidar sunanka.
Gama ka kan nuna cikar ikonka wurin marasa ƙarfi,
kana ƙarfafa su don su yi shaidarka da jininsu
ba kunya ba tsoro,
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

57.  Fastoci
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ka ba mu dama mu yi farinciki
da wannan rana ta tsattarkan ..........
Kana ƙarfafa mu ta misalin kirkinsa,
kana koya mana ta wa'azinsa mai hikima,
kana kuma tsare mu ta addu'o'in da ya ke yi mana.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

58.  Budurwai da masu keɓa kansu
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
amma yau mu yabi hikimar nufinka
saboda wasu tsarkaka
da suka keɓa kansu ga Ubangiji
don mulkin sama.
Ta haka ka tuna mana
da tsarkin Adamu kafin ya yi zunubi,
ka ma kira mu mu soma jin daɗin kyautayinka
yadda zamu ji daɗinsu a cikakke can gidan sama.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

59.  Mattatu 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Tun da ya ke shi ya tashi daga mutuwa,
mu kuma muna sa zuciya ga tashimmu.
Ba shakka kuwa za mu mutu,
amma baƙincikimmu ya koma farinciki
saboda rai na har abada da ka alkawarta mana.
Gama a ganin bangaskiyarmu, ya Ubangiji,
ba ɗaukar rammu a ke yi ba,
sai dai sauya mu a ke yi.
Watau, da muka gama da zamammu a nan duniya,
za mu sami wurin zama har abada a can sama.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

60.  Mattatu 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Gama shi ɗaya ne ya yarda ya mutu
domin kada mutuwa ta rinjayi jama'armu.
Shi ɗaya ne ma ya sha mutuwa
don jama'armu ta rayu a wurinka har abada.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

61.  Mattatu 3
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Shi macecin duniya ne,
mai raya 'yan'adan kuma,
mai ta da matattu ma.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

62.  Mattatu 4
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ta ikonka ka sa aka haife mu,
ta ƙaddararka kana lura da mu,
ta umurninka kuma
za a kwance mu daga ka'idar zunubi
wadda ke yaƙi da mu a nan duniya,
lokacin da za mu koma ƙasa,
wurin da aka samo mu.
Gama da ya ke Ɗanka ya fanshe mu ta mutuwarsa,
za ka tashe mu kuma zuwa ɗaukakar tashinsa
a ranar da ka sa.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

63.  Mattatu 5
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ko da ya ke hakkimmu ne mu mutu
saboda zunuban da muka yi,
da jinƙanka ka fanshe mu ta nasarar Yesu,
za ka kuwa kirawo mu mu rayu da shi har abada.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

64.  Tomas na Akwinas, 28 Jan.
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Gama ka sa malamin nan tsattsarkan Toma
ya zama kama a mala'ika
saboda halinsa mara aibu
da hazƙarsa mai yawan gaske.
Ta haka ka so ya ƙarfafa Ikiliziyarka,
ya kuma haskaka ta kamr rana
ta koyaswarsa mai gaskiy,
mai amfani ƙwarai kuma ga ceto.
A dukan duniy ana yabon hikimarsa,
gama tana da amfani ga kowa da kowa.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

65.  Miƙawar Ubangiji, 2 Feb.
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ɗanka, wanda ke zaune da kai fun fil'azal,
yau ne aka miƙa shi a haikali.
Aka ma yi masa kirarin nan:
"Ɗaukakar jama'ar Isra'ila"
da "Hasken al'ummai".
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

66.  Shelar haifuwar Ubangiji, 25 March
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Mala'ika Jibrilu ya gaya wa Mariya
za ta yi ciki ta ikon Ruhu Mai Tsarki,
za ta kuwa haifi mutumin
da zai ceci mutanen duniya.
Mariya ta gaskanta saƙon nan,
ta kuwa ɗauki Yesu a cikinta da ƙauna,
domin a cika alkawaran da ka yi wa Bani Isra'ila,
a kuma biya wa al'umman duniya begensu
fiye da yadda suka yi tsammani.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

67.  Yohana Maibabtisma
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Muna yabon ka saboda tsattsarkan Yohana,
wanda ya shirya wa Yesu hanya,
ya ma fi duk waɗanda mata suka haifa girma.
Tun yana a ciki, ya motsa da ƙarfi
saboda farinciki da zuwan Maceci.
Da aka haife shi kuwa,
sai duk garinsa suka yi murna.
Daga cikin dukkan annabawa
sai shi ya nuna wa mutane
Ɗan Ragon nan wanda ya fanshe su.
Ya kuma yi wa Yesu babtisma,
ko da ya ke Yesu ne ya ba ruwan iko
na tsarkake masu samun babtisma.
A ƙarshe kuwa ya ba da ransa
don ya yi wa Yesu mafificiyar shaidar gaskiya.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

68.  Bitrus da Bulus, 29 June
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ka sa idin nan na tsarkakan Bitrus da Bulus
ya kawo mana farinciki.
Gama Birus sarkin furtar bangaskiya ne,
Bulus kuwa malaminta ne mai bayaninta sosai.
Bitrus ya gina Ikiliziya wurin Yahudawa,
Bulus kuwa ya kirawo sauran al'ummai,
ya kuma koya masu bisharar Yesu.
Ta hanya dabam dabam ne
biyunsu suka tara jama'a ɗaya ta Yesu,
har suka zama tagwaye cikin ɗaukaka
sa'ad da suka ba da ransu domin Yesu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

69.  Sakewar kamanin Almasihu, 6 Aug.
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ya bayyana ɗaukakarsa
a gaban wasu zaɓaɓɓun almajirai masu shaida,
domin kada su fid da zuciya
da ganin mututuwarsa a kan gicciye.
Ya kuma sa ɗaukakarsa ta haskaka
cikin jiki irin namu,
domin ya nuna za a ɗaukaka jikinsa Ikiliziya
kamar yadda aka rigaya ɗaukaka shi,
wanda ya ke shi ne kan Ikiliziya.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

70.  Dominik, 8 August
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Domin kă ƙayyatar Ikiliziyarka mai tsarki
da wani muhimmin tsaro da ado,
ka sake kafa hanyar rayuwa irin ta manzannin Yesu
ta wurin tsattsarkan (kakammu) Dominik.
Gama da ya ke Uwar Ɗanka tan taimakon shi kullum,
sai ya yi wa'azin da ya dawo da ɓatattun mutane masu yawa,
ya ma kafa ƙungiyar masu wa'azi
masu yaƙi da makaman bangaskiya
saboda ceton al'ummai.
Ta haka ya jawo mutane mara iyaka ga Almasihu;
ko'ina kuwa a cikin duniya ana ta faɗin hikimarsa,
jama'ar Ikiliziya ma tana rera shelar yabonsa.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

71.  Ɗaukakawar Maryamu zuwa sama, 15 August
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri,
da mu ke tunawa da Budurwa Mariya mai tsarki.
Yau ne ka ɗauke ta zuwa wurinka a sama.
Ita ce mafarin Ikiliziya mai samaniya
da misalin sauranmu de ke fama a duniyar nan
yadda za mu zama mu ma nan gaba.
Gama ba sonka ba ne ta zauna a kabari ta ruɓe
bayan ta haifi Ɗanka,
wanda ya ke asalin rai duka.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

72.  Nasarar Giciye mai tsarki, 14 Sept.
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ka sa ceton 'yan'adan ya kasance ta icen gicciye,
domin wurin da mutuwa ta fito,
can ne a sake samun rai.
Gama bayan Sheɗan ya yi nasarar mutane
ta ruɗin Adamu game da wani ice,
sai Yesu ya yi nasarar Sheɗan
a kan itacen gicciye.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

73.  Firansis na Assisi, 4 October
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Da nagartakarka da ƙaunarka mara iyaka
ka sa baranka tsattsarkan Firansis
ya zama wani daga cikin manyan abokanka
waɗanda suka yi maka shaida mai kyau
ta mafificin halin kirkinsu.
Gama Ruhu Mai Tsarki ne ya sa
ƙaunar nan da Firansis ya yi maka
ta ci kamar wuta a cikinsa,
har ta alamta jikinsa da raunukan nan
irin waɗanda aka yi wa Yesu a kan gicciye.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

74.  Dukan tsarkaka, 1 November
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Yau ne ka faranta mana rai
saboda birnin nan mai tsarki Urushalima
wanda ya ke a sama.
Can ne marigayan 'yan'uwammu su ke,
suna ta yabon ka har abada.
Da mu ke taya Ikiliziya murna da su,
muna gaggauta da bangaskiya
cikin tafiyarmu zuwa wurinsu.
Kana sa su kuma su raka mu a hanya,
su taimake mu cikin buktarmu
da addu'o'insu da misalansu.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

75. Maryamu mara aibi, 8 Dec.
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ka tsare Budurwa Mariya tsattsarka
daga duk raunin laifi
tun lokacin da aka yi cikinta.
Ka kuma cika ta da baye-bayen Ruhunka
domin ta cancanci ta haifi Ɗanka,
domin kuma ta alamta farkon Ikiliziya,
wadda ta ke amaryar Ɗanka,
mai kyan ado, mara aibu, mara cikas.
Budurwar nan Mariya kuwa, mai mafificin tsarki,
ka sa ta haifi Ɗan Ragon nan mara aibi,
wanda ya shafe laifofin duniya.
Ka zaɓe ta a cikin mata kuma
domin ta zama misalin tsarki ga jama'arka,
ta kuma taimake mu mu sami alheri a wurinka.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

76.  Ruhu Mai Tsarki 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Da ya hau birbishin sama,
ya kuma zauna a hannunka na dama,
sai ya aiko Ruhu Mai Tsarki,
kamar yadda aka alkawarta,
don ya zauna a cikimmu 'ya'yanka.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

77.  Ruhu Mai Tsarki 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya.
Kana ja gorar Ikiliziyarka
ta ba ta baye-baye iri ir
masu dacewa da lokatai dabam dabam.
Gama da ikon Ruhu mai tsarki
kana ƙarfafa Ikiliziyarka kullum,
kana ma sa ta ta juya gare ka da dukan zuciya,
don kada ya dena yi maka roƙo lokacin tsanani,
kada ma ta fasa yi maka godiya lokacin murna.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

78.  Tsarkakewar ɗakin ibada 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ka ba mu dama mu gina wannan ɗaki,
wurin da ka kan yi mana albarka,
mu iyalinka masu tafiya gare ka.
A nan kana nuna mana
yadda ka ke zaune a cikimmu,
mu da mu ke haikalinka wanda ka ke ginawa.
Ta haka kana sa Ikiliziya ko'ina a duniya
ta yi girma, ta ma haɗa kai
kamar jiki ɗaya ne na Almasihu,
har ta kai darajar Urushaliman nan ta sama
wurin da salama cikakkiya ta ke.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

79.  Tsarkakewar ɗakin ibada 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Ta zamanka a ɗakin nan na addu'a
kullum kana yi mana albarka da taimako,
don ka cika gine-ginen haikalin Ruhu mai tsarki,
haikalin mutanen da ke haskaka da kirki.
Gama ɗakin nan alama ce
ta Ikiliziya amaryar Almasihu,
wadda kullum ka ke ta tsarkakewa
domin ta yi 'ya'ya masu yawa,
ta ma shiga wurin ɗaukakarka a sama.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

80.  Ɗaurin aure 1
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Irin auren da ka kafa
kana ɗaure shi da ƙauna da salama,
yadda ba damar kashewa.
Masu irin wannan aure kuwa
ka kan ba su albarkar 'ya'ya
waɗanda ka zaɓa su zama 'yan mulkinka.
Gama da ƙaddararka
aure ya ke ba duniya manyanta na gobe,
da kyautarka kuma
ya ke ba Ikiliziya tsarkakan mulkin sama.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

81.  Ɗaurin aure 2
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ta wurinsa ka yi sabuwar yarjejeniya da mu,
inda ka fanshe mu ta mutuwarsa da tashinsa,
domin mu zama 'ya'yanka,
mu kuma taya Yesu ɗaukaka a sama.
Ƙaunar nan da ka nuna mana cikin Yesu
tana kama da ƙaunar
da ke tsakanin miji da matarsa.
Ta haka ka ke jawo hankalimmu
ga ƙaunarka mara iyaka ga 'yan'adan.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

82.  Ɗaurin aure 3
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri.
Bayan ka halicci mutum,
ka ba shi babbar kyauta mai daraja
inda haɗuwar namiji da mace
ta zama kamannin gaske na ƙaunarka.
Gama ka halicci mutum da ƙauna,
kullum ma kana iza shi ya bi dokar ƙauna,
domin ya yi tarayya da madawwamiyar ƙaunarka.
Kana kuwa tsarkake ƙaunar namiji da mace
ta asirin aure mai tsarki
wanda ya ke alamar taka ƙauna.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

83.  Yin alkawalan keɓa kai
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Kamar fure mai tsabta ke tohowa daga saiwa,
haka Yesu ya fito daga Budurwa Mariya;
hi ma ya ce, "Albarka tatabbata
ga masu tsarkakakkiyar zuciya;"
ya kuwa ba da misalin barin aure saboda mulkin sama.
Cikin dukan kome ya yi wa nufinka biyayya,
har wadda ta kai shi ga mutuwa;
ta haka ya yi cikakkiyar hadayar kansa
irin wadda ka ji daɗinta.
Ya kuma ce, Wanda ya bar duk abin da ke nasa
domin ya yi hidima a cikin mulkinka,
zai sami lada mai yawa a wurinka.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

84.  Ɗayancin Ikiliziya
Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Ta wurinsa ka jawo mu ga sanin gaskiyarka,
domin bangaskiya ɗaya da babtisma ɗaya
su haɗa mu cikin jikinsa ɗaya.
Ta wurinsa kuma ka ba dukan al'ummai
baiwar Ruhu mai tsarki.
Ya kan rarraba masu baye-bayensa
dabam dabam masu ban mamaki,
ya kan sa 'ya'yanka kuma su haɗa kai,
yana kuma ja gorar Ikiliziyarka a ko'ina.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa:

 


ADDU'AR GODIYA TA FARI

Yabon Uba

Ya Uba, mai yawan alheri,
mun zo gare ka da zuciya ta godiya
ta wurin Ɗanka Yesu Almasihu Ubangijimmu:
Ta wurinsa muna roƙon ka, ka karɓa,
ka kum albarkaci waɗannan baye-baye
da mu ke miƙa maka hadaya.

Addu'a don Ikiliziya duka

Muna miƙa su don Ikiliziyarka mai tsarki
wadda ka kafa saboda 'yan'adan duka;
ka kula da ita, ka yi mata jagora,
ka ba ta salama da zuciya ɗaya ko'ina a duniya.
Ka kuma lura da shugabannimmu Papa ...... da Bishop ......
da sauran bishoshi da fadodi da malamai
waɗanda su ke koyas da addinin Katolika,
wanda muka karɓa daga gun manzanninka.

Addu'a don jama'armu

Ya Ubangiji, ka tuna (da bayinka ........ da)
mu jama'armu da muka taru a nan.
Kā san yadda mu ke ba da gaskiya gare ka
da yadda mu ke ba da kammu gare ka.
Muna roƙon ka, ka ba mu zaman lafiya da ceto,
mu da dukan 'yan'uwammu cikin Almasihu;
don haka ne mu ke miƙa wannan hadaya ta yabonka,
ya Allah rayayye mai gaskiya.

Tunawa ta tsarkaka

Mu da sauran Ikiliziya duka, muna girmama Maria,                                            Ga bambamcin a ƙasa
Uwar Yesu Almasihu Ubangijimju da Allahmmu,

+  wadda ba da taɓa sanin namiji ba,

ko da ya ke tana da miji Yusufu,
wanda mu ke girmamawa shi ma.
Muna kuma girmama manzanni Bitrus da Bulus da Andarawas,

[da Yakubu da Yohana da Toma da Yakubu da Filibus
da Bartalamawas da Matiyu da Siman da Tadawas
da Lainus da Kilitas da Kileman da Sistus
da Karniliyas da Sipiriyan da Lorans da Kirisagonas
da Yohana da Bulus da Kazmas da Demiyan]
da sauran waɗanda suka ba da ransu don Yesu,
da dai dukan tsarkaka.
Saboda addu'o'insu da halin kirkinsu ka taimake mu,
ka kuma kare mu yau da kullum.
[albarkacin Almasihu Ubangijimmu. Amin.]


Bambamci a kan wasu iduna

HAIFUWAR ALMASIHU
Mu da sauran Ikiliziya duka, muna yabon ka
a wannan rana (dare) wanda a cikinsa
Mariya ta haifa wa duniya Mai ceto,
Yesu Almasihu Ubangijimmu.
Muna girmama ta kamar Uwar Allah, +

BAYYANUWAR ALMASIHU
Mu da sauran Ikiliziya duka, muna yabon ka
a wannan rana da makaɗaicin Ɗanka,
wanda tun fil'azal ya ke da ɗaukaka ɗaya da kai,
ya bayyana kansa acikin siffar ɗan'adan.
Muna girmama Maria,
Uwar Yesu Almasihu Ubangijimju da Allahmmu, +

RAN ALHAMIS MAI TSARKI
Mu da sauran Ikiliziya duka, muna yabon ka
a wannan rana da Ubangijimmu Yesu Almasihu
ya yarda a bashe shi saboda mu.
Muna girmama Maria, Uwar Yesu Almasihu Ubangijimju da Allahmmu, +

FASKA, HAR ZUWA LAHADIN DA KE BAYANSA
Mu da sauran Ikiliziya duka, muna yabon ka
a wannan rana (dare) wanda a cikinsa
Yesu Almasihu Ubangijimmu ya tashi daga mutuwa.
Muna girmama Maria, Uwar Yesu Almasihu Ubangijimju da Allahmmu, +

HAWAN YESU ZUWA SAMANIYA
Mu da sauran Ikiliziya duka, muna yabon ka
a wannan rana da makaɗaicin Ɗanka Ubangijimmu
ya hau bisa da jikinsa irin namu,
ya kuma zauna a wurinka cikin ɗaukaka.
Muna girmama Maria, Uwar Yesu Almasihu Ubangijimju da Allahmmu, +

SAUKOWAR RUHU MAI TSARKI
Mu da sauran Ikiliziya duka, muna yabon ka
a wannan rana da Ruhu Mai Tsarki
ya bayyana kansa ga manzanni a cikin harsunan wuta.
Muna girmama Maria, Uwar Yesu Almasihu Ubangijimju da Allahmmu, +


Don hadayar ta amfane mu

Ya Uba, ka karɓi wannan baiko                                            Ga bambamcin a ƙasa.
da dukanmu iyalinka ke miƙawa:
Ka ba mu salama a zamammu na duniya,
a lahira kuma kada ka bari mu hallaka,
amma ka lissafta mu a cikin zaɓaɓɓun mutanenka.
[albarkacin Yesu Almasihu Ubangijimmu. Amin.]


Bambanci a kan wasu iduna

RAN ALHAMIS MAI TSARKI
Ya Uba, ka karɓi wannan baiko
da dukan iyalinka ke miƙawa
a ran da Ubangijimmu Yesu Almasihu
ya ba almajiransa asirin nan
na jikinsa da jininsa don su tuna da shi.
Ka ba mu salama a zamammu na duniya,
a lahira kuma kada ka bari mu hallaka,
amma ka lissafta mu a cikin zaɓaɓɓun mutanenka.

FASKA, HAR ZUWA LAHADIN DA KE BAYANSA
Ya Uba, ka karɓi wannan baiko
da dukan iyalinka ke miƙawa
musamman saboda waɗannan sabbin shiga
waɗanda suka sami sabon rai
ta ruwa da Ruhu Mai Tsarki,
suka kuma sami gafarar dukan zunubansu.
Ka ba mu salama a zamammu na duniya,
a lahira kuma kada ka bari mu hallaka,
amma ka lissafta mu a cikin zaɓaɓɓun mutanenka.


Don hadayar ta gamshi Allah

Don hadayar ta gamshe ka,
ka albarkaci baikommu,
ka sa mu miƙa shi da zuciya mai gaskiya,
don ya zama abu mai karɓuwa gare ka,
watau jiki da jinin majidaɗin Ɗanka
Yesu Almasihu Ubangijimmu.

Addu'ar Yesu ta godiya

Gabanin ran da zai sha wahala ne
ya ɗauki burodi da hannuwansa masu tsarki
ya ɗaga kai sama,
gare ka, Ubansa mai iko duka,
ya yi maka godiya,
ya albarkaci burodin, ya kakkarya,
ya ba almajiransa, yana cewa:

DUKANKU, KU KARƁA, KU CI:
WANNAN JIKINA NE,
WANDA ZA A BAYAR DOMINKU.

Haka kuma, bayan sun ci abinci,
ya ɗauki calis, ya yi maka godiya,
ya albarkace shi,
ya kuma ba almajiransa, yana cewa:

DUKANKU, KU KARƁA, KU SHA DAGA CIKINSA:
WANNAN CALIS NA JINANA NE,
JINI KUMA NA SABUWAR YARJEJENIYA MADAWWAMIYA;
ZA A ZUBAR DA SHI DOMINKU DA DUKAN MUTANE
DON GAFARAR ZUNUBAI.
KU RIƘA YIN HAKA DON TUNAWA DA NI.

Asirin bangaskiya da girma ya ke:

Shelar da jama'a ke yi

1.Yesu ya mutu.
 Yesu ya tashi.
 Yesu zai sake zuwa.
2.Ta mutwarka kā shafe mutwarmu.
 Ta tashinka kā sake raya mu.
 Ya Ubangiji Yesu, ka zo da ɗaukaka.
3.Duk sa'ad da mu ke cin wannan burodi,
 da mu ke sha daga wannan calis,
 muna shelar mutwarka, ya Ubangiji Yesu,
 sai ka zo da ɗaukaka.
4.Kā fanshe mu, ya Ubangiji
 ta gicciyenka da tashinka.
 Kai ne Mai ceton duniya.

Tunawa da aikin Yesu

Yanzu, ya Uba, muna tunawa da Almasuhu Ɗanka,
mu masu hidimarka da sauran jama'arka;
muna tunawa da azabarsa, da tashinsa daga mutuwa,
da hawansa zuwa sama cikin ɗaukaka.
Daga cikin kyautayi masu yawa kuma da ka ba mu,
ya Allah mai daraja, mai girma,
muna miƙa maka wannan cikakkiyar hadaya mai tsarki,
burodi na rai da calis na madawwamin ceto.

Don a karɓi hadayar

Ka dubi wannan hadaya da haƙuri,
ka karɓe ta kamar yadda ka karɓi kyautar adalinka Habila,
da hadayar Ibrahim, kakammu ta hanyar bangaskiya,
da kuma burodi da wain da limaminka Malkisadak ya miƙa maka.

Don a kyauta mana

Ya Allah mai iko duka, muna roƙon ka
ka sa mala'ikanka ya kai wannan hadaya
zuwa wurinka mai ɗaukaka:
[zuwa ga bagadin ɗaukakarka a sama:]
Sannan, lokacin da mu ke karɓar
jiki da jini mafi tsarki na Ɗanka a wannan bagadi,
ka cika mu da dukan alheri da albarka.
[albarkacin Yesu Almasihu Ubangijimmu. Amin.]

Addu'a don matattu

Ya Ubangiji, ka tuna ga 'yan'uwammu (......)
da suka riga mu gidan gaskiya,
suna ɗauke da hatimin bangaskiya:
Su da dukan masu hutawa cikin salamar Almasihu
ka sa su shiga haskenka
wurin da za su yi farinciki.
[albarkacin Yesu Almasihu Ubangijimmu. Amin.]

Addu'a don kammu

Mu kanmu kuma, muna roƙon wurin zama
a gun manzanninka da waɗanda suka ba da ransu don Yesu,
kamar su Yohana mai yin babtisma,
da Istifanus da Matiyas da Barnabas,

[da Igineshus, da Aligazanda
da Marsalinas da Bitrus
da Felisita da Parpetuwa
da Agata da Lusiya
da Aginas da Sisiliya da Anastasiya]
da kuma dukan tsarkakanka.
Ko da ya ke mu masu zunubi ne,
muna dogara ga jinƙanka da ƙaunarka.
Kada ka yi mana shari'a bisa ga laifofimmu,
amma ka yi mana gafara.

Albarkar baiko

Ta wurin Almasihu Ubangijimmu
ka ke ba mu dukan waɗannan abubwa,
kana cika su da rai da alheri,
kana albarkatar su, kana tsarkake su.

Ɗaukakawa

Ta wurinsa,
a cikinsa,
tare da shi kuma,
cikin ɗayancin Ruhu Mai Tsarki,
dukan ɗaukaka da dukan girma naka ne,
ya Uba mai iko duka,
har abada abadin.
Amin.

 


ADDU'AR GODIYA TA BIYU

Gabatarwa

Ya Uba, mai iko duka, Allah madawwami,
Lalle ya kamata mu yi maka godiya
a kowane lokaci da kowane wuri
ta wurin ƙaunataccen Ɗanka Yesu Almasihu.
Shi Kalmarka ne
wanda ka halicci duk komi ta wurinsa,
ka ma aiko mana da shi don ya cece mu.
Ta ikon Ruhu Mai Tsarki Budurwa Mariya ta haife shi;
ya ma yarda ya cika nufinka,
ya kuwa samo maka jama'a mai tsarki.
Saboda haka ya miƙa hannuwansa a kan gicciye,
yana shan azaba.
Ta haka ya ci nasara a kan mutuwa,
ya kuma nuna mana yadda za mu tashi zuwa rai.
Saboda haka, muna haɗa baki da dukan mala'iku da tsarkaka,
muna shelar darajarka, muna rerawa: MAI TSARKI...

Yabon Uba

Lalle kai ne Mai tsarki, ya Uba,
kai kaɗai ke mai da wani abu mai tsarki.

Roƙon albarkar Ruhu Mai Tsarki

Ka sa Ruhunka ya sauko a kan waɗannan baye-baye,
ya tsarkake su
don su zama mana jiki da jinin
Ubangijimmu Yesu Almasihu.

Addu'ar Yesu ta godiya

Kafin a bashe shi ga mutwar da ya yarda ya yi,
ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya,
ya kuma ba almajiransa, yana cewa:

DUKANKU, KU KARƁA, KU CI:
WANNAN JIKINA NE,
WANDA ZA A BAYAR DOMINKU.

Haka kuma, bayan sun ci abinci,
ya ɗauki calis, ya kuma yi godiya,
ya kuma ba almajiransa, yana cewa:

DUKANKU, KU KARƁA, KU SHA DAGA CIKINSA:
WANNAN CALIS NA JINANA NE,
JINI KUMA NA SABUWAR YARJEJENIYA MADAWWAMIYA;
ZA A ZUBAR DA SHI DOMINKU DA DUKAN MUTANE
DON GAFARAR ZUNUBAI.
KU RIƘA YIN HAKA DON TUNAWA DA NI.

Asirin bangaskiya da girma ya ke:

Shelar da jama'a ke yi

1.Yesu ya mutu.
 Yesu ya tashi.
 Yesu zai sake zuwa.
2.Ta mutwarka kā shafe mutwarmu.
 Ta tashinka kā sake raya mu.
 Ya Ubangiji Yesu, ka zo da ɗaukaka.
3.Duk sa'ad da mu ke cin wannan burodi,
 da mu ke sha daga wannan calis,
 muna shelar mutwarka, ya Ubangiji Yesu,
 sai ka zo da ɗaukaka.
4.Kā fanshe mu, ya Ubangiji
 ta gicciyenka da tashinka.
 Kai ne Mai ceton duniya.

Tunawa da aikin Yesu

Ya Uba, don tunawa da mutwar Ɗanka
da kuma tashinsa daga mutuwa,
muna miƙa maka jikinsa da jininsa
abinci na rai ke nan da abinsha na ceto.
Mun gode maka a kan ka yarda
mu taru a gabanka, mu yi maka hidima.

Roƙon Ruhu Mai Tsarki don haɗa kai

Muna kuma roƙon ka ka sa dukammu
da mu ke karɓar jiki da jinin Almasihu tare,
mu zama da zuciya ɗaya ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

Addu'a don Ikiliziya

Ya Ubangiji, ka lura da Ikiliziyarka ko'ina a duniya,
ka sa mu ƙaru da ƙaunar juna
tare da shugabannimmu Papa ...... da Bishop .......,
da dukan masu yin aikin Ikiliziya.

Addu'a don matattu

In an yi roƙo musamman don wani matacce, a fara da cewa:
Ka tuna da ......., wanda ka kira daga wannan duniya.
Ya mutu, an rufe shi, kamar yadda aka yi wa Yesu;
bari ya tashi kuma tare da Yesu.

Ka kuma tuna da'yan'uwammu da suka rasu
waɗanda su ke sa zuciya ga tashinsu.
Ka ba su haske su sami ganinka, su da sauran matattu.

Addu'a don kammu

Muna roƙon ka ka yi wa dukammu jinƙai,
yadda za mu sami rai madawwami,
mu da Budurwa Mariya mai tsarki, Uwar Allah,
da manzannin Yesu, da dukan tsarkaka,
waɗanda suka cika nufinka a nasu zamani,
tun farkon halittar duniya har zuwa yanzu.
Bari mu da su mu yabe ka,
mu kuma ɗaukaka ka ta wurin Ɗanka Yesu Almasihu.

Ɗaukakarwa

Ta wurinsa,
a cikinsa,
tare da si kuma,
cikin ɗayancin Ruhu Mai Tsarki,
dukan ɗaukaka da dukan girma naka ne,
ya Uba mai iko duka,
har abada abadin.
Amin.

 


ADDU'AR GODIYA TA UKU

Yabon Uba

Ya Uba, lalle kai ne Mai tsarki,
daidai ne kuma kukan halitta su yi yabonka:
Gama kai ne ke ba su rai, kana tsarkake su kuma
ta wurin Ɗanka Yesu Almasihu Ubangijimmu
da ikon Ruhu Mai Tsarki.
Tun zamanin dā har zuwa yanzu
kana ta tattara wa kanka jama'a,
domin daga gabas zuwa yamma
a miƙa maka hadaya mai tsarki.

Roƙon albarkar Ruhu Mai Tsarki

Saboda haka, ya Uba, mun kawo maka waɗannan baye-baye,
muna roƙon ka ka tsarkake su ta ikon Ruhunka,
domin su zama jiki da jinin Ɗanka
Ubangijimmu Yesu Almasihu,
wanda ya umurce mu
mu miƙa wanna hadaya ta godiya.

Addu'ar Yesu ta godiya

Cikin daren da aka bashe shi,
ya ɗauki burodi, ya yi maka godiya,
ya albarkace shi, ya kakkarya
ya kuma ba almajiransa, yana cewa:

DUKANKU, KU KARƁA, KU CI:
WANNAN JIKINA NE,
WANDA ZA A BAYAR DOMINKU.

Haka kuma, bayan sun ci abinci,
ya ɗauki calis, ya kuma yi godiya,
ya albarkace shi,
ya kuma ba almajiransa, yana cewa:

DUKANKU, KU KARƁA, KU SHA DAGA CIKINSA:
WANNAN CALIS NA JINANA NE,
JINI KUMA NA SABUWAR YARJEJENIYA MADAWWAMIYA;
ZA A ZUBAR DA SHI DOMINKU DA DUKAN MUTANE
DON GAFARAR ZUNUBAI.
KU RIƘA YIN HAKA DON TUNAWA DA NI.

Asirin bangaskiya da girma ya ke:

Shelar da jama'a ke yi

1.Yesu ya mutu.
 Yesu ya tashi.
 Yesu zai sake zuwa.
2.Ta mutwarka kā shafe mutwarmu.
 Ta tashinka kā sake raya mu.
 Ya Ubangiji Yesu, ka zo da ɗaukaka.
3.Duk sa'ad da mu ke cin wannan burodi,
 da mu ke sha daga wannan calis,
 muna shelar mutwarka, ya Ubangiji Yesu,
 sai ka zo da ɗaukaka.
4.Kā fanshe mu, ya Ubangiji
 ta gicciyenka da tashinka.
 Kai ne Mai ceton duniya.

Tunawa da aikin Yesu

Ya Uba, muna tunawa da mutuwar
da Ɗanka ya sha saboda cetommu,
da tashinsa mai ɗaukaka daga mutuwa,
da hawansa zuwa sama,
muna kuma jiran dawowarsa:
Don haka, muna miƙa wannan tsattsarkar hadaya mai rai
domin mu yi maka godiya.

Roƙon Ruhu Mai Tsarki don haɗa kai

Ka dubi hadayar nan ta Ikiliziyarka;
kă ga yadda Yesu ne mu ke miƙawa,
wanda ya sa da mu da kai ta mutwarsa:
Tun da ka ke sabunta rammu da jikinsa da jininsa,
sai ka cika mu da Ruhunsa mai tsarki,
don mu zama jiki ɗaya da ruhu ɗaya cikin Almasihu.

Addu'a don kammu

Bari Yesu ya mai da mu hadaya
ta yabonka yanzu da har abada,
yadda za mu ji daɗin zumuncinka,
mu da Budurwa Mariya mai mafificin tsarki, Uwar Allah,
da manzanni, da waɗanda suka ba da ransu don Yesu,
(da ...... mai tsarki,)
da kuma sauran tsarkaka duka:
Saboda roƙe-roƙensu ma muna sa zuciya
za ka taimake mu yau da kullum.

Addu'a don duniya duka

Ya Ubangiji, bari wannan hadaya,
wadda ta kawo salama tsakanimmu da kai,
ta yaɗa wa dukan duniya salama da ceto.

Addu'a don sauran mutane

Ya Uba mai rahama, ka kasa kunne ga roƙe-roƙen iyalinka,
mu da ka tara a nan gabanka:
Sauran 'ya'yanka kuma da suka warwatsu ko'ina a duniya
ka tattara su wurinka saboda jinƙansa.

Addu'a don mattatu*

'Yan'uwammu da suka rasu,
ka karɓe su cikin mulkinka,
su da duk waɗanda suka ƙaura daga duniya cikin amincinka:
Muna fata mu yi murna tare da su
ta ganin darjarka har abada,
ta wurin Almasihu Ubangijimmu;
albarkacinsa ne ka ke ba mu dukan abubuwan alheri.

Ɗaukakawa

Ta wurinsa,
a cikinsa,
tare da si kuma,
cikin ɗayancin Ruhu Mai Tsarki,
dukan ɗaukaka da dukan girma naka ne,
ya Uba mai iko duka,
har abada abadin.
Amin.


*In jana'iza ce, a sauya addu'ar da ke bisa da wannan:
Ka tuna da bawanka ....., wanda ka kira daga wannan duniya:
Ya mutu, an rufe shi, kamar yadda aka yi wa Yesu;
bari ya tashi kuma tare da Yesu
a lokacin da Almasihu zai ta da jikimmu mai mutuwa,
ya mai da shi kamar nasa jiki mai haske.
Sauran 'yan'uwammu da suka rasu,
ka karɓa su cikin mulkinka,
su da duk waɗanda suka ƙaura daga duniya cikin amincinka:
Muna fata mu yi murna tare da su
ta ganin darjarka har abada,
lokacin da za a shafe mana hawaye.
Ran nan za mu gan ka, ya Allah, kamar yadda ka ke;
za mu kuma zama kamar kai,
mu kuma yi yabonka har abada,
ta wurin Almasihu Ubangijimmu;
albarkacinsa ne ka ke ba mu dukan abubuwan alheri.


ADDU'AR GODIYA TA HUƊU

Gabatarwa

Ya Uba mai tsarki, lalle ya kamata mu ɗaukaka ka,
mu yi maka godiya,
gama kai ne Allah mai rai na gaskiya.
Kana nan tun fil'azal,
za ka kuma kasance har abada,
kana zaune cikin hasken da ba ya kusantuwa.
Kai kaɗai ne tushen rai;
kā yi dukan halittarka don ka cika su da albarka,
amma ka yi 'yan'adan don su sami ganinka.
Ga taron mala'iku marasa iyaka
suna tsaye a gabanka,
suna bauta maka dare da rana,
suna kallon darajar fuskarka,
suna ta yin yabonka ba fasawa.
Mu ma muna haɗuwa da su,
mu da dukan halittarka,
muna rera maka waƙa ta godiya: MAI TSARKI.....

Yabon Uba

Ya Uba mai tsarki, muna shaida girmanka;
dukan ayyukanka ma
suna bayyana hikimarka da ƙaunarka.

Labarin 'yan'adan

Kā sifanta mutane cikin kamannin kanka,
kā kuma ba su mulkin duniya duka,
don su yi maka bauta,
su kuma sarauci dukan sauran halitta.
Ko da ya ke sun ƙi yi maka biyayya,
har sun ɓata amincinka,
ba kabar su cikin mulkin mutuwa ba,
amma ka jawo su su neme ka,
su kuma same ka.
Sau da yawa ka ƙulla yarjejeniya da su,
ta bakin annabawa kuma kana koya masu
yadda za su sa zuciya ga cetonsu.

Labarin zuwan Yesu

Ya Uba mai tsarki,
saboda ƙaunar da ka ke yi wa 'yan'adan,
da lokaci ya cika,
har ka aiko da makaɗaicin Ɗanka don ya cece mu:
Aka yi cikinsa ta ikon Ruhu Mai Tsarki;
Budurwa Mariya ta haife shi.
Shi mutum ne kamarmu
ta kowane hali, banda zunubi:
Ya yi wa matalauta wa'azin bishara,
'yan kurkuku wa'azin 'yanci,
masu baƙinciki kuma wa'azin farinciki.
Don ya cika nufinka, ya ba da ransa ga mutuwa;
amma ta tashinsa daga kabari
ya shafe mutuwa, ya kuwa sabunta mana rai.

Labarin zuwan Ruhu Mai Tsarki

Domin kuma mu dena zaman kammu, sai nasa,
ya aiko mana Ruhu Mai Tsarki daga wurinka, ya Uba,
kyautarsa ta farko ga masu ba da gaskiya:
Ya aiko Ruhun domin ya cika aikinsa a duniya,
ya kuma tsarkake mu sarai.

Roƙon albarkar Ruhu Mai Tsarki

Ya Uba, bari wannan Ruhu Mai Tsarki
ya tsarkake baye-bayen nan,
ya sa su zama jiki da jinin Yesu Almasihu Ubangijimmu,
domin mu aikace wannan babban asiri na tunawa da shi,
madawwamiyar yarjejeniya ke nan wadda ya bar mana.

Addu'ar Yesu ta godiya

Da lokaci ya yi, ya Uba, da za ka girmama shi,
da ya ke ya ƙaunaci mutanensa da ke duniya,
sai y ƙaunace su har matuƙa.
Suna cikin cin abincin dare, sai ya ɗauki burodi,
ya albarkace shi, ya kakkarya,
ya ba almajiransa, yana cewa:

DUKANKU, KU KARƁA, KU CI:
WANNAN JIKINA NE,
WANDA ZA A BAYAR DOMINKU.

Haka kuma, ya ɗauki calis, cike da wain,
ya yi godiya, ya ba almajiransa, yana cewa:

DUKANKU, KU KARƁA, KU SHA DAGA CIKINSA:
WANNAN CALIS NA JINANA NE,
JINI KUMA NA SABUWAR YARJEJENIYA MADAWWAMIYA;
ZA A ZUBAR DA SHI DOMINKU DA DUKAN MUTANE
DON GAFARAR ZUNUBAI.
KU RIƘA YIN HAKA DON TUNAWA DA NI.

Asirin bangaskiya da girma ya ke:

Shelar da jama'a ke yi

1.Yesu ya mutu.
 Yesu ya tashi.
 Yesu zai sake zuwa.
2.Ta mutwarka kā shafe mutwarmu.
 Ta tashinka kā sake raya mu.
 Ya Ubangiji Yesu, ka zo da ɗaukaka.
3.Duk sa'ad da mu ke cin wannan burodi,
 da mu ke sha daga wannan calis,
 muna shelar mutwarka, ya Ubangiji Yesu,
 sai ka zo da ɗaukaka.
4.Kā fanshe mu, ya Ubangiji
 ta gicciyenka da tashinka.
 Kai ne Mai ceton duniya.

Tunawa da aikin Yesu

Ya Uba, da mu ke aikata wannan abin tunawa da fansarmu,
muna tunawa da mutuwar Almasihu,
da tafiyarsa wajen matattu,
da kuma tashinsa daga kabari,
da hawansa zuwa ga hannunka na dama,
muna kuma zuba ido ga komowarsa cikin ɗaukakarsa:
Don haka, muna miƙa maka jikinsa da jininsa,
hadaya mai karɓuwa,
wadda ke kawo wa duniya duka ceto.

Roƙon Ruhu Mai Tsarki don haɗa kai

Ya Ubangiji, ka dubi wannan hadaya
da ka ba Ikiliziyarka:
Bari Ruhunka mai tsarki ya tattara
dukan masu karɓar wannan abinci da abinsha,
ya mai da su jiki ɗaya na Almasihu,
hadaya mai rai ta yabonka.

Addu'a don Ikiliziya

Yanzu, ya Ubangiji, ka tuna da dukan
waɗanda mu ke miƙa wannan hadaya dominsu,
musamman bawanka Papa ........, da Bishop .........
da kuma dukan bishoshi da masu yin aikin Ikiliziya.
Ka kma tuna da waɗanda ke sa hannu cikin hadayar nan,
sauran jama'arka da ba su nan,
da dukan mutanen da ke nemanka da zuciya mai gaskiya.

Addu'a don mattatu

Ka kuma tuna da 'yan'uwammu da suka rasu
cikin imanin Almasihu,
da dai dukan matattu
waɗanda kai kaɗai ne ka san bangaskiyarsu.

Addu'a don kammu

Ya Uba mai rahama, mu da mu ke 'ya'yanka,
ka ba mu rabommu na mulkin sama,
tare da Budurwa Mariya, Uwar Allah,
da manzanninka da tsarkakanka:
Sannan a can cikin mulkinka
za mu zama 'yantattu daga ruɓa ta zunubi da mutuwa,
za mu kuwa yi waƙar darajarka tare da dukan halitta,
ta wurin Almasihu Ubangijimmu;
albarkacinsa ne ka ke ba mu dukan abubuwan alheri.

Ɗaukakawa

Ta wurinsa,
a cikinsa,
tare da si kuma,
cikin ɗayancin Ruhu Mai Tsarki,
dukan ɗaukaka da dukan girma naka ne,
ya Uba mai iko duka,
har abada abadin.
Amin.

 


CIMAR UBANGIJI

Da ƙarfin zuciya mu yi addu'a ga Uba
daidai yadda Ubangiji Yesu ya koya mana:

Ubammu wanda ke cikin samaniya,
a tsarkake sunanka,
mulkinka shi zo,
abin nufinka shi zama cikin duniya
kamar yadda a ke yinsa cikin sama.
Ka ba mu yau abincin yini.
Ka gafarta mana zunubammu,
kamar yadda mu ke gafarta wa masu yi mana laifi.
Kada ka kai mu cikin jaraba,
amma ka cece mu daga mugu.

Ya Ubangiji, muna roƙonka, ka cece mu daga dukan miyagu.
Ka ba mu salama a cikin kwanakimmu.
Ta tausayinka ka raba mu da zunubi da kowace irin damuwa,
lokacin da muke zuba ido ga zuwan mulkinka da dawowar Mai cetommu Yesu Almasihu.

Gama mulki, da iko, da girma naka ne har abada.

Ya Ubangiji Yesu Almasihu, kā ce da manzanninka,
"Na bar ku da salama; salamta na ke ba ku."
Kada ka kula da zunubammu, sai dai bangaskiya ta Ikiliziyarka.
Ta alherinka kuma ka sa mu zauna cikin salama da haɗa kai,
kai da ka ke raye, kana mulki har abada abadin.

Amin.

Salamar Ubangiji ta zama tare da ku har abada.

Tare da kai ma.

Mu yi wa juna gaisuwa ta salama da ƙauna.

Ya Ɗan Ragon Allah

Ya Ɗan Ragon Allah, kai da ka ke kawar da zunuban duniya:
Ka yi mana jinƙai.

Ya Ɗan Ragon Allah, kai da ka ke kawar da zunuban duniya:
Ka yi mana jinƙai.

Ya Ɗan Ragon Allah, kai da ka ke kawar da zunuban duniya:
Ka ba mu salama.

 

Ga Ɗan Ragon Allah. Ga shi wanda ke kawar da zunuban duniya.
Waɗanda aka gayyace su bikin Ɗan tunkiya, sun sami albarka.