HAUSA PSALMS
translated by
Malam Bawa, of Kano
under supervision of Cyril Sanderson,Note: I met Cyril Sanderson in Kano in the early 1970s. Born on 29 May 1905 [information from his grand-nephew, John Collis], for health reasons, he was leaving for South Africa. Having done the Linjila, he could do no more on the Psalms than this "rough draft" (as stated on the front page). He gave it to me, hoping that I could bring it to conclusion.
Eventually I did turn to the Psalms, but, working directly from the Hebrew, with close recourse to Michel Dahood work on the Psalms in the Anchor Bible, I could no longer follow Sanderson's dependence on RSV and ERV. So Musa Ɗan Juma and I did an entirely new translation.
Nevertheless, improvements are always possible, and it is important to be able to refer to the pioneering work of Sanderson. For this reason I present the draft he left.
In many places Sanderson typed alternate wordings above the normal text. I separate these by a slash: /. I keep his format of indentation, but where there is overflow I keep it on a single line. I omit the verse numbers, as well as the headers, the "selah"s, the book divisions, and Sanderson's notes with outdated questions about the meaning of a verse. Here and there I met and corrected typing mistakes.
Sometimes Sanderson put a question mark over a word (of Malam Bawa's draft). I keep this in brackets: [?]. It is apparent from the queries in Sanderson's notes, that this translation is basically Malam Bawa's draft. After going through it, I see that it is rich in vocabulary, but really "rough" in getting the meaning and in finish.
—Joseph Kenny, O.P.
1
Albarka ta tabbata ga wanda
ya bin al'adar mugu,
ba ya zama tare da masu zunubi,
ba ya kuma zama a gun masu nami/ashararai.
Sai dai farincikinsa na ga dokokin Ubangiji,
dare da rana tunaninsa game da dokokin Ubangiji ne.
Zai kasance kamar ice ne
da a ka dasa/suka a bakin ƙorama,
wanda ya ke haifuwa lokacin haifuwarsa,
wanda kuma ganyensa ba ya ƙaiƙashewa.
Duk abin da ya yi kuwa sai ya zama
mai albarka.
Miyagu ba haka su ke ba,
sai dai kamar ƙaiƙayi su ke,
da iska ke tafiya da shi.
Saboda haka miyagu ba za su kai ba a ranar shari'a,
haka kuma masu zunubi a cikin taron masu gaskiya.
Domin Ubangiji ya san hanyar masu gaskiya,
amma ta miyagu mai kaiwa ga halaka ce.
2
Me ya sa al'ummai ke ɗaura yaƙi?
Mutane kuma ke tunanin abubuwan banza?
Sarakunan duniya su kan shirya,
masu mulki kuma su kan gama kai,
su yi gaba da Ubangiji da shafaffensa, suna cewa,
"Bari mu warwatsa jama'arsu,
mu kwance igiyarsu daga wuyammu."
Shi wanda ke zauna a sama zai yi dariya,
Ubangiji zai mai da su abin dariya.
Sa'an nan ne zai yi musu magana a husace,
ya yi hushi da su matuƙar hushi, yă ce,
"Amma kuwa na sanya sarkina
a kan tsattsarkan dutsena na Sihiyona."
Zan yi magana daga cikin dokokin Ubangiji:
Ubangiji ya ce da ni, "Kai ne ɗana,
a yau ne na haife ka.
Ka roƙe ni, zan ba ka al'ummai ka gada,
har bangon duniya duka za ka mallaka.
Za ka ci su da sandan ƙarfe.
Za ka rugurguza su kamar tukinya."
Saboda haka sai ka zama masu hikima, ya ku sarakuna.
Ku yi sani, ya ku alkalan duniya.
Ku bauta wa Ubangiji game da tsoro
ku yi farinciki tare da tawa-jiki."
Ku yi na'am da ɗan, don kada ya yi hushi,
ku halaka a tsakani,
domin nandanan zai husata.
Albarka tatabbata ga dukkan waɗanda
su ke amince da shi/ dogara gare shi.
3
Ya Ubangiji, yaya magabtana suka ƙaru!
waɗanda su ka tasam mini suna da yawa.
Da yawa waɗanda su ka ce mini
"Ai ba wani taimakon da Allah zai yi masa."
Amma, ya Ubangiji, kai ne garkuwata,
kai ne ɗaukakata/ mai ɗaukaka ni.
Ina ɗaukaka muryata ga Ubangiji,
yana kuwa amsa mini daga kan tsattsarkan dutsensa.
Na kan kwanta, in yi barci,
na kan kuma farka, domin Allah na kiyaye ni/ riƙe da ni.
Ba zan ji tsoron mutum dubu goma ba
waɗanda su ke gaba da ni a kewaye da ni.
Ka tashi mana, ya Ubangiji,
ka kuɓutad da ni, ya Allahna!
Domin ka mammangare dukkan magabtana,
ka kakkarye haƙoran miyagu.
Ceto na Ubangiji ne.
Albarka tă tabbata ga jama'arka.
4
Ya Allah abin gaskatawa ta, ka amsa mini in na yi kira,
ka kuɓutad da ni a sa'ad da na ke cikin baƙinciki.
Ka ji tausayina, ka saurari addu'ata.
Ya ku bil'adam! Har yaushe ɗaukakata za ta koma wulakanci?
Har yaushe za ku zauna cikin ruɗin duniya,
kuna biye wa ƙarya?
Amma dai ku san cewa Ubangiji ya keɓe wa kansa mai bin Allah.
Ubangiji zai saurara sa'ad da na kira shi.
Ka zama mai tsoron Allah, kada ku ɗau zunubi,
ka yi shiru, ka yi shawara da zuciyarka a kan gadonka.
Ka ba da hadayoyin aikin gaskiya,
ka kuma amince wa Ubangiji/ dogara da Ubangiji.
Akwai mutane da yawa masu cewa,
"Wa zai yi mana wani alheri?
Ya Ubangiji, ka haskaka mu da hasken nan na fuskarka."
Kai ne ka sanya farinciki a cikin zuciyata,
fiye da wanda su ke da si
sa'ad da hatsinsu da inabinsu suka ƙaru.
Zan kwanta in yi barci a cikin aminci,
domin kai daɗai ne, Ya Ubangiji,
ka ke zaunad da ni a cikin aminci/ sa in yi zaman aminci.
5
Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga magnata,
ka dubi tunanina.
Ka saurari sautin kukana,
Sarkina, kuma Allahna,
domin gare ka na ke addu'a.
Ya Ubangiji, za ka ji muryata da safe,
da safe na zan yi addu'a gare ka, in kuma yi dako.
Domin kai ba Allah ne mai jin daɗin mugun abu ba.
Mugu ba zai zauna a gunka ba.
Masu girman kai ba za su tsaya a gaban idanunka ba,
ka ƙi dukkan masu mummunan aiki.
Za ka halaka maƙaryata.
Ubangiji ya ƙi mai son kisan kai, mazambaci.
Amma ni kam zan zo gare ka,
cikin yalwar alherinka na ƙauna.
Game da tsoronka
zan bauta maka, ina fuskantar tsattsarkan ɗakin sujada.
Ya Ubangiji, ka bi da ni ta kan gaskiyarka/ in shiga gaskiyarka
saboda magabtana.
Ka nuna mini tafarkinka sosai a gaban idanuna.
Domin babu bangaskiya a bakunansu/ bakinsu,
can cikinsu ma mugunta ce tsantsa.
Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne,
suna zuga da harshensu/ kirari daɗin baki
Ka dubi/ kula da/ laifinsu, ya Ubangiji.
Shawarwarinsu suka da su.
Ka jefa su cikin ɗumbun laifuffukansu,
domin su yi maka tawaye.
Amma ka sa duk waɗanda suka gaskata da kai su yi farinciki;
ka sa har abada su riƙa ɗaukaka murya don farinciki,
domin ka hore su.
Ka sa suma waɗanda suka ƙaunar sunanka su yi farinciki game da kai.
Domin kai ne mai yi wa maigaskiya albarka, ya Ubangiji.
Ya Ubangiji, kai ne mai kewaye shi da soyayya kamar da garkuwa.
Dukkan magabtana za su kunyata, su husata ƙwarai.
Za su juyo su ji kunya kamar ƙiftawar ido.
6
Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini a cikin hushinka,
kada kum ka hore ni a cikin zafin hushinka.
Ka ji tausayina, ya Ubangiji, domin na bushe.
Ka warkad da ni, ya Ubangiji, domin ƙasusuwana sun wahala/ yi tsami.
Raina ma ya wahala/ ɓaci/ ƙwarai.
Ya Ubangiji har yaushe za ka dube ni?
Ya Ubangiji ka dawo ka kuɓutad da raina.
Ka cece ni saboda rahamarka ta ƙauna.
Domin babu tunawa da kai in an halaka,
wa zai yi maka godiya a cikin Mahalaka?
Na gaji tikis da nishi.
Kowane dare sai na cika gadona da hawaye,
ina jiƙa shi saboda kukana.
Idanuna sun lalace saboda baƙinciki,
har sun tsufa saboda magabtana.
Ku rabu da ni, ku masu mugun aiki,
domin Ubangiji ya ji sautin kukana.
Ubangiji ya ji roƙona,
Ubangiji zai amsa addu'aka.
7
Ya Ubangiji Allahna, gare ka na ke dogara,
ka cece ni daga dukkan masu korata, ka kuɓutad da ni.
Kada ya kacancana/ yayyaga/ ni kamar zaki,
yă yi filla-filla da ni, ba kuwa mai ceto.
Ya Ubangiji Allahna, in dai na yi wannan abu,
in da mugun abu a game da ni,
in na cuci mai ba ni amana,
kai! ko na cuci magabcina ba tare da wani dalili ba,
to, magabcin yă bi ni, yă kama ni
har ma yă tattake ni a ƙasa,
ya tursasa ɗaukakata.
Ka tashi ya Ubangiji da hushinka,
ka tasam ma tsananin hushin magabtana.
Ka dubi mini, kai ne ka yi umarnin shari'a/ hukumci.
Ka sa jama'a duk su kewaye ka,
ka kuma ɗaukaka mazauninka can sama da su.
Ubangiji ne ka yi wa mutane hukumci/ shari'a.
Ya Ubangiji, ka hukunta ni gwargwadon aikin gaskiyana.
da kuma mutuncin da na ke da shi.
Ka sa muguntar miyagu ta ƙare,
amma ka kafa mai gaskiya.
Domin Allah mai gaskiya
ya kan jarraba zukata da hankula.
Garkuwata ga Allah ta ke,
ita ce mai kuɓutad da mutum nagari a zuci.
Allah alkali ne mai gaskiya.
Shi Allah ne da a ke yi wa abin haushi kullum.
Im mutum bai juyo hanya ba,
sai Allah ya wasa takobinsa,
ya ɗaura bakansa ya shirya.
Ya kuma shirya masa kayan mutuwa,
ya sa kibansa a wuta sun yi ja.
Ga shi, mugu na shan wahala saboda mugun aiki.
Ga shi ya ƙunsa fitina/ mutunta/ a cikinsa,
ya haifo ƙarya.
Ya yi rami, ha haƙa shi sosai,
ya kuwa faɗa cikin ramin da ya yi/ tona.
Muguntatasa za ta koma kansa.
Tunzurinsa ma zai koma kansa.
Zan gode wa Ubangiji bisa ga gaskiyatasa,
zan kuma yi waƙar yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.
8
Ya Ubangiji, Ubangijimmu,
sunanka shi ne mafi ɗaukaka a dukkan duniya!
Wanda ya sanya ɗaukakarsa cikin sammai.
Daga bakin jarirai da masu shan mama
ka kafa ƙarfinka, saboda magabtanka
domin ka tsai da magabta da masu hari/ tsokana.
Sa'ad da na dubi sammanka, aikin hannunka,
wato wata da taurari waɗanda ka ƙaddara,
menene mutum, har da za ka kula shi,
da kuma bil'adam/ ɗan mutum,/ har da za ka ziyarce shi?
Domin ka yi shi ya kasa Allah kaɗan,
ka kuma naɗa shi da ɗaukaka da girma.
Ka sanya shi yă yi iko da aikin hannunka;
ka sanya komai a hannunsa.
Tumaki da bajimai/ shanu/ duka,
kai, har da dabbobin sarari,
da tsuntsaye da kifaye,
da dukkan abin da ke cikin ruwa.
Ya Ubangiji, Ubangijimmu,
sunanka mafi ɗaukaka ne a duniya duka.
9
Zan yaba wa Ubangiji da dukkan zuciyata.
Zan nuna dukkan ayyukanka na al'ajabi.
Zan yi murna, in yi farinciki da kai.
Zan yi waƙar yabo da sunanka, ya kai mafi ɗaukaka.
Sa'ad da magabtana suka juya
za su yi tuntuɓe su halaka a gabanka.
Domin ka yi na'am da hakkina, da sha'anina.
Ka bayyana a kan gadon sarauta, kana shari'a da gaskiya.
Ka tsawata wa al'ummai, ka halaka miyagu.
Ka shafe sunansu har abada abadin.
Magabta sun iso ƙarshensu,
sun wofinta har abada.
Biranen da ka halaka kuma,
babu sauran tunawa da su.
Amma Ubangiji yana zauna,
shi ne sarki har abada.
Ya shirya gadonsa na sarauta
saboda shari'a.
Zai yi wa duniya shari'ar gaskiya.
Zai yi wa mutane shari'a ta tsai da gaskiya.
Ubangiji kuma zai kasance matsera ga waɗanda aka matsa wa,
Matsera a lokacin ƙuntata.
Waɗanda suka san sunanka za su amince maka,
domin kai, ya Ubangiji, ba ka ya da masu nemanka ba.
Ku yi waƙoƙin yabon Ubangiji, wanda ke zauna a Sihiyona.
Ku yi shelar aikinsa a cikin mutane.
Domin shi mai ɗaukan fansar jini yana tunawa da su,
ba ya mantawa da kukan gajiyayye.
Ka ji tausayina, ya Ubangiji.
Ka ga wahalata ta masu ƙi na,
kai da ka karɓe ne daga hannun mutuwa,
don im bayyana dukkan yabonka,
a ƙofofin 'yar Sihiyona
zan yi farinciki da cetonka.
Al'ummai sun dulmuya cikin ramin da suka yi;
ƙafafunsu sun kamu a cikin tarkon da suka ɗana.
Ubangiji ya bayyana kansa,
ya zartad da hukunci.
Mugu ya kamu a tarkon
da ya yi da hannunsa.
Mugu zai komo Mahalaka,
har al'umman da suka manta da Allah.
Domin ba za a manta da mabukaci kullum ba,
sazuciyar gajiyayye ma ba za ta lalace har abada ba.
Ka tashi, ya Ubangiji, kada mutum ya ci nasara,
ka yi wa al'ummai hukumci a gaban idanunka.
Ka sa tsoro a zukatansu, ya Ubangiji.
Ka sa al'ummai su san su mutane ne kawai.
10
Ya Ubangiji, me ya sa ka tsaya can nesa?
Me ya sa ka ɓuya mana a lokacin wahala?
Miyagu, ta alfarmarsu, suna fafarar gajiyayyu ƙwarai.
Ka sa su kamu a cikin dabarun da suka ƙuƙƙulla.
Domin mugu yana alfahari da nufin zuciyatasa.
Makwaɗaici ya kan yi baƙar magana, kuma ya kan zagi Ubangiji.
Mugu, a cikin alfarmarsa ya kan ce ba ruwansa da shi;
a dukan tunaninsa yana cewa babu Allah.
Hanyoyin Ubangiji koyaushe masu ƙarfi ne;
shari'arka can sama su ke inda ba ya gani;
magabtansa kuwa sai fure su.
Mugu a zuciyarsa sai ya ce, "Ba zan raurawa ba,
ba zan sami magabci ba a dukkan zamani."
Bakinsa cika ya ke da zagi, da zamba, da zalumci;
mugunta ce da mugwar magana a bakinsa.
Ya kan fake a maɓoya a ƙauyuka,
yana kisan marasa aibu daga ɓoye.
Idanusan na hararar rarrauna.
Yana ɓuya a maɓoya kamar zaki a kurfinsa.
Ya kan yi kwanto don ya kama gajiyayya,
in ya sarƙafe shi a cikin tarkonsa.
Ya kan tanƙwasa gajiyayye, ya sunkuyad da shi,
sai ya faɗi a gaban wanda ya fi shi ƙarfi.
A zuciyarsa sai yă ce, "Allah ya mance,
ya ɓuya, ba zai ƙara ganinsa ba."
Ka tashi, ya Ubangiji, ya Allah, ka ɗaga hannunka,
kada ka manta gajiyayye.
Ta yaya mugu zai ƙi Allah,
har ya ce a zuciyarsa, "Ba za ka so shi ba"?
Ai ka gan shi, domin ka ga fitina hushi,
har ka ɗauka a hannunka.
Gajiyayye ya miƙa kansa gare ka.
Kai ne ka ke taimakon maraya.
Ka karya hannun miyagu,
mugu kuwa ka nemi muguntatasa sai im ba ka samu ba.
Ubangiji shi ne sarki har abada abadin,
al'ummai sun halaka daga ƙasatasa.
Ya Ubangiji, kā dai ji bukatar masu tawali'u,
za ka shirya zukatansu,
ka ka kasa kunne ka ji.
Ka yi wa marayu da waɗanda aka matsa wa shari'a.
Saboda haka mutun, da ya ke na duniya ne,
kada ya ƙara zama abin tsoro.
11
Ya Ubangiji na sanya amanta, yaya za ku ce mini
"Gudu kamar tsuntsu zuwa dutsenka?
domin ga shi mugu ha ɗaura baka,
sun ɗana kibiyarsu a kan tsirkiya,
don su harbi mutumin gaskiya a ƙirji a cikin duhu.
In an halaka rafuka,
me mai gaskiya zai yi"?
Ubangiji yana tsattsarkan ɗakin sujadarsa;
gadon Ubangiji na sarauta a sama ya ke.
Idanunsa na ganin ɗan'adam, fatar idonsa na yi masa shari'a.
Ubangiji na yi wa mai gaskiya shari'a
amma ransa ya ƙi mugu da taƙadari.
Zai zubo tarkuna ga miyagu.
Za su sha wuta da farar wuta da iska mai ƙuna.
Domin Ubangiji mai gaskiya ne, yana son gaskiya;
mai gaskiya zai gan shi.
12
Ka yi taimako, ya Ubangiji, domin mai bin Allah ya ƙare;
domin mai bangaskiya sun kasa a cikin bil'adam.
Kowa zancen wofi ya ke yi da ɗan'uwansa,
da daɗin baki da zuciyar biyu su ke magana.
Ubangiji zai yanka dukkan bakuna masu daɗin baki,
da harshen da ke manya-manyan maganganu,
waɗanda suka ce, "Za mu ci nasara da harshemmu,
bakimmu namu ne; wanene ubangijimmu?
"Saboda munana wa gajiyayyu, saboda ajiyar zucin matsattsu,
yanzu zan tashi," in ji Ubangiji.
"Wada su ke hurewan zan kiyaye shi."
Maganar Ubangiji magana ce mai tsarki/ tsarkakakkiya
kamar azurfad da aka jarraba a maƙera
wadda aka tsarkake sau bakwai.
Kai ne mai tsare su, ya Ubangiji,
kai ne za ka kiyaye su daga zamanin nan har abada.
Miyagu suna bin ko'ina,
a sa'an nan a ke ɗaukaka mugunta a cikin bil'adam.
13
Ya Ubangiji, ina tsawon lokacin da za ka mance da ni har abada?
Har yaushe ina ɓoye fuskarka gare ni?
Har yaushe zan dinga shawar a raina,
ina baƙinciki a zuciyata wuni zubur?
Ina tsawon lokacin da magabtana za su ɗaukaka a kaina?
Ka duba dai, ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna;
ka buɗe mini idona, don kada in yi barcin mutuwa.
Kada magabcina ya ce, "Ai na ci nasara a kansa".
Kada magabtana su yi farinciki in an girgiza ni.
Amma na ba da gaskiya ga rahamarka,
zuciyata za ta yi farinciki da ceonka.
Zan yi wa Ubangiji waƙa
domin ya yalwata mini.
14
Wawa ya ce a zuciyarsa, "Babu Allah."
Su ɓatattu ne, sun yi aiki abin ƙyama.
Ba wani mai yin abu mai kyau.
Sai Ubangiji ya dubo daga sama, ya ga 'yan'adam,
don ya ga ko akwai waɗanda suka fahimta, suka nemi Allah.
Duk sun fanɗare, duk sun ƙazantu gaba ɗaya.
Ba masu yi kyakkyawan aiki, a'a, ko ɗaya.
Ashe masu miyagun ayyuka, ba su da sani?
Waɗanda ke/ Masu/ cin mutanena kamar yadda su ke cin abinci/ burodi/ ba sa kiran Ubangiji.
Suna cikin babban tsoro,
domin Allah na tare da zuriyar masu gaskiya.
Kuna kunyata (shawarar) gajiyayye,
domin Allah shi ne mafakatasa.
Allah ya sa ceton Bani Isra'ila ya fito daga Sihiyona!
Sa'ad da Ubangiji ya komo da bayinsa daga bauta,
a sa'an nan ne Yakubu zai yi farinciki
Bani Isra'ila kuma su yi farinciki.
15
Ya Ubangiji, wa zai zauna a majami'arka ta alfarwa?
Wa zai zauna a kan tsattarkan dutsenka?
Shi ne wanda ke bin hanyar gaskiya, ya ke kuma aikata gaskiya,
shi ne mai faɗar gaskiya daga zuciyatasa,
shi ne bakinsa ba ya yanke,
ba ya kuma cutar abokinsa,
ba ya zagin ɗan'uwansa;
wanda ke raina mai laifi,
amma yana ba da girma ga masu tsoron Ubangiji;
shi ne in ya yi rantsuwa a zuciyatasa, ba ya sakewa.
Shi ne wanda ba ya caca,
ba ya karɓar lada a wurin mai gaskiya.
Duk mai yin waɗannan abubuwa
ba zai jijjiga ba har abada.
16
Ka adana ni ya Allah,
domin a gare ka na ƙwallafa raina.
Na gaya wa Ubangiji, cewa,
"Kai ne Ubangijina.
Ba ni da Allah ban da kai."
Tsarkakan da ke duniya kuwa, su ne mafiya kyau,
waɗanda dukkan farincikina ke gare su.
Waɗanda ke musanya Ubangiji da wani gunki
za a riɓanya baƙincikinsu;
ni ba zan yi hadaya da hadayarsu ta sha ta jini ba,
ba kuwa zan ambaci sunansu da bakina ba.
Ubangiji shi ne rabona na gado,
shi ne kuma ƙoƙona;
kă adana mini sha'anina.
Al'amari duka ya yi mini daɗi,
kai, na yi kyakkyawan gado.
Zan yaba wa Ubangiji wanda ya ba ni shawara.
Zuciyata dad dare ma tana koya mini.
Na sa Ubangiji a gabana kullum
domin a hannuna na dama ya ke, ba zan gigiza ba.
Saboda haka zuciyata ke/ na/ farinciki,
ɗaukakata ma ta ke yi;
jikina ma zan zauna cikin aminci.
Domin ba za ka bar raina ga Mahalaka ba,
ba kuma za ka bar mai tsarkin/ tsattsarkan/ nan naka ya ruɓa ba.
Za ka nuna mini hanyar rai;
cikar farinciki a cikin zatinka ta ke;
akwai dawwamman farinciki a hannunka na dama.
17
Ka saurari gaskiya, ya Ubangiji,
ka kula da kukana.
Ka kasa kunne ga addu'ata
wadda ta ke fitowa daga bakin da ba ya yaudara.
Kuɓutata tă zo daga zatinka.
Idanunka su dubi kyakkyawan abu.
Ai ka tabbatad da zuciyata,
ka sadu da ni dad dare.
Ka gwada ni, ba ka sami komai ba.
Na yi niyya bakina ba zai keta umarni ba.
Game da ayyukan mutane kuwa,
na rantse da maganarka;
na yi nesa da hanyoyin masu son tunzuri.
Ban ratse daga kan hanyata ba,
ƙafata ba ta kauce ba.
Na yi kiranka, ya Allah,
domin za ka amsa mini;
ka kasa kunnenka gare ni,
ka ji maganata/ jawabina.
Ka nuna alherinka na ƙauna,
ya mai kuɓutad da masu amince maka
daga hannun waɗanda suka tasam musu
ta hannunsu/ ??/ na dama.
Ka adana ni kamar ƙwayar ido,
ka ɓoye ni cikin inuwar fukafukanka,
daga mugun da ke ɓata ni,
wato miyagun magabtana da ke kewaye da ni.
Zuciyarsu ta rufe musu ido,
suna magana da alfarma.
To, yanzu sun kewaye mu a kan hanyarmu,
suna hararan yadda za su ka da mu.
Kamar zaki ya ke, mai haɗamar kisan abincinsa,
kamar safen zaki ya ke, mai ɓuya a wuraren fako.
Ka tashi, ya Ubangiji, ka sha gabansa, ka kada shi.
Ka ceci raina da takobi, daga hannun mugu.
Ka cece ni da hannunka, ya Ubangiji, daga mutane,
mutanen duniya waɗanda rayuwan nan ne kaɗai rabonsu.
Waɗanda ka cika wa ciki da dukiyarka.
Sun wadata da 'ya'ya,
suna kuma barin sauran kayansu ga 'ya'yansu.
Ni kam zan riƙa ganin fuskarka da gaskiya.
In na farka raina zai kwanta saboda ganin kamanninka.
18
Ina ƙaunarka, ya Ubangiji ƙarfina.
Ubangiji shi ne dutsena, uwar yaƙina, kuma macecina.
Allahna, ƙaƙƙarfan dutsena,
gare shi zan ba da gaskiya,
garkuwata, macecina, hasumiyata.
Zan yi kiran Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
ta haka za a/ don a/ cece ni daga magabtana.
Igiyoyin mutwa sun kewaye ni,
tsananin rashin bin Allah ya tsorata ni
Igiyoyin Mahalaka suna kewaye da ni,
tarkokin mutuwa sun zo kaina.
Na yi kiran Ubangiji a cikin baƙincikina,
na yi kuka ga Allahna.
Ya ji muryata daga ɗaukinsa da aka masa sujada;
kukana da na yi a gabansa kuwa ya shiga kunnensa.
Sai ƙasa ta yi girgiza, ta raurawa,
gindin duwatsu ma ya motsa,
ya girgiza, domin Ubangiji ya husata.
Hayaƙi ya fita daga kafafen hancinsa,
wuta kuma daga bakinsa,
tana cin gawayi.
Ya kuma tanƙwaso sammai sun/ ya[?]/ sunkuyo,
matsanancin duhu kuma na ƙafafunsa.
Ya hau 'cherub' ya tashi sama.
Ya tashi, iska ta tafi da shi da sauri ƙwarai.
Ya sa duhu ya zama abin ɓuyarsa, mai kewaya shi,
duhun ruwaye da gajimare masu karuri.
Ta hasken da ke gabansa
kakkauran gajimaren nan ya wuce,
tare da ƙanƙara da garwashin wuta.
Ubangiji kuma ya daka tsawa daga sama,
mafi ɗaukaka ya furta maganatasa,
sai ga ƙanƙara da garwashin wuta.
Ya harbo kabawunsa ya watsa su;
walƙiya ta yi 'walak' [?] ta fatattaka su.
Sai hanyoyin ruwa suka bayyana,
gindin duniya duka aka wofinta shi
da tsawarka, ya Ubangiji,
da hucin hancinka.
Ya aiko daga can sama ya ɗauke ni,
ya tsamo ni daga ruwaye masu yawa.
Ya cece ni daga ƙaƙƙarfan magabcina,
da kuma waɗanda suka ƙi ni,
domin sun fi ni ƙarfi nesa.
Sun zo gare ni a kwanakin nahisata,
amma Ubangiji shi ne madogarata.
Shi ne kumaya kawo ni wani yalwataccen wuri;
ya cece ni, domin yana farinciki da ni.
Ubangiji ya biya ni bisa gaskiyata,
bisa tsarkin hannayena, haka ya rama mini.
Domin na kiyaye hanyoyin Ubangiji,
ban yi mugunta na guje wa Allahna ba.
Domin dukkan hucumcinsa na gabana,
ban kuwa ya da dokokinsa ba.
Ni kuma cikkakke ne a wurinsa,
na kuma tsare kaina daga mugun aiki.
Saboda haka ne Ubangiji ya rama mini bisa ga gaskiyata,
bisa ga tsarkin hannuwana a idonsa.
Za ka nuna wa mai tausayi
kai mai tausayi ne.
Za ka nuna wa kamilin mutum
kai kamili ne.
Za ka nuna wa mai tsarki
kai tsattsarka ne,
karkatacce kuwa za ka nuna masa
kai karkatacce ne.
Domin kai ne za ka ceci mutanen da a ke wahalarwa,
amma masu alfarma za katanƙwaso su.
Domin kai ne mai kunna fitilata;
Ubangiji Allahna zai haskaka duhuna.
Da ƙarfinka an fatattaka runduna,
da ikon Allahna kuma na ke tsallake katanga.
Allah kuwa, hanyatasa tabbatacciya ce,
Maganar Allah ana tabbatad da ita,
shi garkuwa ne
ga dukkan masu gaskatawa da shi.
Wanene Allah im ba Ubangiji ba?
Wanene kuwa dutse ban da Allahmmu?
Allahn da ke yi mini ɗamara da gaskiya,
ya ke kuma tabbatad da hanyata.
Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa,
ya ɗora ni kan manyan matsayina.
Ya koya mini yaƙi
har hannuna na tanƙwasa bakan farin ƙarfe/ tagulla.
Kai ne kuma ka ba ni garkuwar cetonka,
hannunka na dama kuma ya riƙe ni,
taimakonka ya girmama ni.
Ka yalwata mini hanyata,
ƙafafuna kuwa ba su goce ba.
Zan bi magabtana da kora har in same/ iso/ su,
ba kuwa zan sake juyawa ba sai an halaka su.
Zan marmashe su yadda ba za su iya tashi ba.
Za su faɗi in tattake su.
Domin ka yi mini ɗamara da ƙarfin yaƙi.
Ka biyar mini da waɗanda suka tasam mini.
Kai ne kuma ka sa na ga ƙeyar magabtana,
don in rinjayi waɗanda suka ƙi ni.
Sun yi kuka, amma ba mai ceto,
har ga Ubangiji ma, amma bai amsa musu ba.
Sa'an nan sai na niƙe su tulus
kamar ƙura a gaban /cikin/ iska.
Na jefad da su kamar taɓon kan kwararo.
Kā kuɓutad da ni daga faman mutane;
kā mai da ni shugaban al'ummai;
mutanen da ban taɓa sani ba za su bauta mini.
Da sun ji labarina za su yi mini biyayya;
baƙa za su yi mini caffa.
Baƙi za su shuɗe,
za su zo suna rawar jiki da sanɗa.
Ubangiji rayayye ne/ a raye ya ke;
albarka tă tabbata ga dutsena,
ɗaukaka kuma ta tabbata
ga Allah macecina,
wato Allahn da ke ɗaukam mini fansa
ya ke biyar mini mutane;
shi ne ke kuɓutad da ni daga magabtana,
kai ne ka ke ɗaukaka ni
a kan waɗanda su ke tasam mini;
kai ne a cece ni daga hannun mai tunzuri.
Saboda haka zan gode maka a cikin al'umma, ya Ubangiji,
in kuma yi waƙar yabon sunanka.
Ya yi wa sarkinsa babban ceto,
yana nuna alheri da ƙauna ga shafaffensa,
ga Dawuda da irinsa har abada.
19
Sammai suna shaidad da ɗaukakar Allah;
al'arshi yana nuna iakinsa na hannu.
Kowace rana yana furta magana,
kowane dare yana nuna sani.
Ba wata magana, ba wani harshe,
ba za a iya jim muryarsu ba.
Amma kuwa muryarsu tana bazuwa a dukkan duniya,
maganarsu kuma har zuwa bangon duniya.
A cikinsu ya sanya majami'a saboda rana,
wadda ta ke ita ce ango mai fitowa daga ɗakinsa,
yana farinciki ya yi zamaninsa,
kamar ƙaƙƙarfan mutum.
Fitarsa daga ƙarshen sama ne,
kewayensa kuwa iyakokinta,
ba wani abin da ke ɓoye a zuciyarsa.
Shari'ar Ubangiji kammalalliya ce,
tana sa rai toko.
Shaidar Ubangiji tabbatacciya ce,
tana sa mutum haka kawai ya zama mai hikima.
Ka'idodin Ubangiji daidaitattu ne,
suna faranta zuciya.
Umarnin Ubangiji tsattsarka ne,
suna haskaka idanu.
Tsoron Ubangiji mai tsafta ne,
yana jurewa har abada;
hukuncin Ubangiji na gaskiya ne,
kuma masu gaskiya ne duk gaba ɗaya.
Su aka fi so a kan zinariya,
kai, har ma zinariya mai kyau, mai yawa;
sun ma fi zuma
da saƙar zuma zaƙi.
Da su ne aka gargaɗi bawanka.
Wajen kiyaye su akwai lada mai girma.
Wa zai iya rarrabe kurakuransa?
Ka tsarkake ni daga laifuffukan da ke ɓoye.
Ka kuma tsare bawanka daga zunuban ganganci,
kada su mallake ni.
A sa'an nan ne zan zama kamili,
in kuma zama kuɓutacce daga babban zunubi.
Maganta da na furta,
da tunanin da na yi a zuci
su karɓu a gare ka,
ya Ubangiji, dutsena, kuma macecina.
20
Ubangiji ya amsa maka a kwanakin wahala.
Sunan Allahn Yakubu ya sanya ka a can sama.
Ka/ Ya/ aiko da taimako daga wuri tsattsarka,
ya ƙarfafa ka daga Sihiyona.
Ka tuna da dukkan baye-bayenka
ka yi na'am da hadayarka/ baikonka/ ta ƙonewa.
Ka ba da bukatar zuciyarka,
ka cika dukkan shawarwarinka.
Za mu ci nasara game da cetonka,
da sunan Allahmmu za mu kafa tutocimmu.
Ubaniji ka cika dukkan roƙonka da aka yi.
Yanzu na san Ubangiji na ceton shafaffensa,
zai amsa masa daga tsattsarkar samansa
da ƙarfin nan na kuɓutawa na hannunsa na dama.
Waɗansu suna ba da gaskiya da karusai,
waɗansu da dawaki;
amma mu sunan Ubangiji Allahmmu
za mu ambata.
Sun sunkuya, sun faɗi,
amma mu mun tashi, muna tsaye cir.
Ya Ubangiji, ka kuɓutar.
Sarki yă amsa in mun yi kira.
21
Sarkin zai yi farinciki da ƙarfinka, ya Ubangiji;
wane irin babban farinciki kuma zai yi game da cetonka!
Ka biya masa burin zuciyatasa,
ba ka ƙyale roƙonsa ba.
Domin ka hana samun kyawawan abubuwa/ abubuwan daɗi;
ka sanya kambin kyakkyawar zinariya a kansa.
Ya roƙe ka rai, ka kuwa ba shi,
har ma tsawon kwana, har abada abadin.
Ɗaukakatasa babba ce ga cetonka.
Ka sanya masa girma da sarauta.
Domin ka mai da shi mafi albarka har abada;
ka sa ya yi murna tare da farinciki a gaban zatinka.
Domin sarkin ya ba da gaskiya ga Ubangiji,
kuma ba zai girgiza ba saboda alherin ƙauna ta mafi ɗaukaka.
Hannunka zai iya samun dukkan magabtanka;
hannunka na dama zai binciko masu ƙin ka.
Za ka mai da su kamar wutar maƙera
a lokacin hushinka.
Ubangiji zai haɗiye su a cikin hushinsa;
wutar kuma za ta cinye su.
Za ka halaka zuriyarsu daga duniya,
da kuma 'ya'yansu daga cikin bil'adam.
Domin sun nufin mugunta ne gare ka,
sun ƙaga/ dabarta/ wata dabara wadda ba za su iya yi ba.
Domin za ka sa su juya ƙeya
za ka shirya, bakanka a ɗaure a kansu.
Ya Ubangiji, ɗaukaka ta tabbata gare ka a ƙarfinka.
Haka za mu yi ta waƙar yabonka.
22
Ya Allahna, ya Allahna, dom me ka yashe ni?
Me ya sa ka yi nesa da taimakona,
da kuma sautin kururuwata?
Ya Allah, ina kuka da rana,
amma ba ka amsa ba,
da dare ma ban yi kawai ba.
Amma kai tsattsarka ne,
ya kai da ke mallakar yabon Bani Isra'ila.
Kakannimmu sun gaskata da kai;
sun ba da gaskiya, ka kuwa kuɓutad da su.
Sun yi kuka gare ka, sun kuwa kuɓuta.
Sun ba da gaskiya gare ka,
ba su kuwa kunyata ba.
Amma ni tsutsa ce, ba mutum ba;
abin zagi ga mutane wanda mutane suka raina.
Dukkan waɗanda su ke ganina
suna yi mini dariyar raini.
Suna tsake, suna kaɗa kai, suna cewa,
"Ya dogara da Ubangiji,
bari ya kuɓutad da shi,
bari ya kuɓutad da shi,
mu gani in yana farinciki da shi."
Amma kai ne, ka fid da ni daga mahaifa;
kai ne ka sa na ba da gaskiya
a sa'ad da na ke ƙirjin mahaifiyata/ uwata.
An jefo ni kanka daga mahaifa.
Kai ne Allahna tun ina cikin uwata.
Kada ka yi nesa da ni,
domin wahala na kusa,
domin ba wani mai taimaklo.
Bajimai da yawa sun kewaye ni,
ƙarfafan bajiman Bashan sun sa ni tsaka;
suna kallona har da baki,
kamar zaki mai kashewa kuma mai ruri.
An zub da ni kamar ruwa
ƙasusuwana duka sun sukurkuce.
Zuciyata kamar kakin zuma ta ke,
ta narke a tsakiyar kayan cikina.
Ƙarfina ya bushe kamar tsingaro,
harshena kuma ya tsangare a muƙamuƙina
ka kawo ni cikin ƙurar mutuwa.
Karnuka sun kewaye ni;
taron masu mugun aiki su sa ni a tsaka;
sun huda hannayena da ƙafafuna.
Ina iya ƙirga dukkan ƙasusuwana,
sun duba ni, suna kallona;
sun raba tufafina a junansu,
rigata kuwa suka yi ƙuri'a a kanta.
Amma ya Ubangiji, kada ka yi nisa.
Ya kai mataimakina, ka yi sauri ka taimake ni.
Ka ceci raina daga takobi
da kuma ikon kare.
Ka cece ni daga bakin zaki
hakika ka amsa mini ina kan ƙahon ɓauna.
Zan bayyana sunanka ga 'yan'uwana,
zan yabe ka a tsakiyar jama'a.
Ku da ke tsoron Ubangiji, ku yabe shi,
ya ku 'ya'yan Yakubu, ku yabe shi;
ya ku Bani Isra'ila, ku tsorace shi.
Domin bai raina wahalar mai wahala
ko ya ƙi shi ba,
bai kuwa guje shi ba,
duk sa'ad da ya kira shi, ya saurare shi.
Ta gare ka yabona ya ke bayyana a cikin babbar jama'a.
Zan biya rantsutata/ kaffarata/ a gaban masu tsoronsa.
Masu tawalin za su ci, su ƙoshi;
masu neman Ubangiji za su yaba masa.
Allah ya sa zuciyarka ta rayu har abada.
Dukkan iyakokin duniya za su tuna
su juyo ga Ubangiji;
dukkan al'ummai kuwa
sai sun bauta maka.
Domin mulkin na Ubangiji ne,
shi ne kuwa mai mallakar al'ummai.
Dukkan manyan duniya za su ci, su yi bauta;
dukkan waɗanda aka binne za su durƙusa masa,
wato shi wannan da ba zai iya hana kansa mutuwa ba.
Wani a cikin zuriya zai bauta masa;
za a gaya wa zuriya mai zuwa labarin Ubangiji.
Za su zo suba da shaidar gaskiyatasa
ga mutanen da za a haifa,
cewa ya yi abin.
23
Ubangiji shi ne makiyayina,
ba zan yi rashi ba.
Ya kan sa ni in kwanta a kan ɗanyar ciyawa.
Yana bi da ni ta gefen ruwan da ke kwance.
Yana farfaɗo mini da raina.
Yana nushe ni hanyar gaskiya
saboda sunansa.
Kai, ko da ya ke ina bin hanyoyin mutuwa
ba zan ji tsoron mugun abu ba,
domin kana tare da ni;
sandanka na sanyaya mini zuciya.
Ka shirya mini abinci
a cikin abokan gabana.
Ka shafa mini mai a ka,
ƙoƙona ya cika har yana zuba.
Ba shakka alheri da rahama za su bi ni
har iya tsawon rayuwata;
zan kuma zauna a gidan Ubangiji
har abada.
24
Ƙasa da ta Ubangiji ce, duk da ni'imatata,
da duniya da mazaunanta.
domin a kan teku ya fara ta,
ya kafa ta a kan ruwa.
Wa zai hau kan duwatsun Ubangiji?
Wa kuma zai tsaya kan tsattsarkan wurinsa?
Sai shi mai tsattsakar zuciya
wanda bai riya ransa ga ruɗi ba,
bai kuwa rantse a kan yaudara ba.
Ubangiji zai ya (yi?) masa albarka,
Allah mai cetonsa, kuma zai mai da shi mai aikin gaskiya.
Wannan ita ce zuriyar masu nemansa,
waɗanda su ke nemana, ya Allah Yakubu!
Ya ku ƙofofi, ku ɗaga kanku,
ku ƙofofin na har abada, ku ɗagu,
Sarkin Ɗaukaka zai shigo.
Wanene Sarkin Ɗaukaka?
Ubangiji ne, me ƙarfi, mai girma.
Ubangiji mai girma a gun yaƙi.
Ku ɗaga kanku, ku ƙofofi,
ku ɗaga su ku ƙofofi na har abada,
Sarkin Ɗaukaka zai shigo.
Wanene Sarkin Ɗaukaka?
Ubangijin runduna ne,
shi ne Sarkin Ɗaukaka
25
Ya Ubangiji, gare ka na ke cira raina.
Ya Allahna, gare ka na ba da gaskiya;
kada ka sa ni ji kunya;
kada abokan gabana su yi nasara a kaina.
Hakika ba mai dogara da kai
sa'an nan ya ji kunya.
Su masu aikata mugunta ba dalili
za su ji kunya.
Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji,
ka koya mini tafarkinka.
Ka bi da ni cikin gaskiyarka,
ka kuma koya mini,
domin kai ne Allahn mai cetona,
gare ka na ke tsaye dare da rana.
Ya Ubangiji, ka tuna da daddaɗar rahamarka,
da alherinka na ƙauna,
domin tun fil'azal su ke.
Kada ka tuna da zunubaina na ƙuruciya
ko kuwa laifuffukana;
bisa ga alherinka na ƙauna
za ka tuna da ni
saboda alherinka, ya Ubangiji.
Ubangiji mai nagarta ne,
kuma mai gaskiya ne;
saboda haka ne zai koya wa
masu zunubi su bi hanya.
Zai sa masu sanyin hali
hanya wajen shari'a,
zai kuma koya musu ta wannan hanya.
Dukkan hanyoyin Ubangiji alheri ne
game da ƙauna da kuma gaskiya
ga waɗanda suka kiyaye alkawarinsa da shaidatasa.
Ya Ubangiji, albarkacin sunanka
ka gafarci mugun aikina domin babba ne.
Wane mutum ne ke tsoron Ubangiji?
Shi ne wanda ya koya wa hanyad da ya zaɓa.
Ransa zai zauna cikin aminci,
zuriyatasa kuma za ta gaji ƙasar.
Asirin Ubangiji na ga masu tsoronsa,
zai kuwa nuna musu alkawarinsa.
Idanuna har abada ga Ubangiji su ke,
domin zai kau da ƙafafuna daga tarko.
Ka juyo gare ni, ka ji tausayina,
domin ni yasasshe ne, mai shan azaba.
An yawaita wahalce-wahalcen zuciyata,
ka fid da ni daga baƙincikina.
Ka dubi wahalata da azabata,
ka gafarta dukkan zunubaina.
Ka dubi magabtana, domin suna da yawa.
Sun kuwa ƙi ni, mugun ƙi.
Ka kiyaye raina, ka cece ni;
kada ka sa in ji kunya,
domin na dogara gare ka.
Mutunci da gaskiya su kiyaye ni,
domin a kanka na ke tsaye.
Ka kuɓutad da/ ceci/ Bani Isra'ila, ya Allah,
daga dukkan wahalce-wahalcensu.
26
Ka bi kaduna [?] ya Ubangiji,
domin na zauna a cikin mutuncina;
na kuma ba da gaskiya ga Ubangiji
ba tare da wata inda inda [?] ba.
Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka tabbatad da ni,
ka jarraba raina da zuciyata.
Domin alherinka na ƙauna yana gaban idanuna,
na kuwa bi gaskiyarka.
Ban zauna da mutanen banza ba,
ba kuwa zan haɗu da masu wata mutane ba.
Na tsargi taron masu aikata mugunta,
ba kuwa zan zauna da miyagu ba.
Zan fid da hannuna in zama marar aibu;
ta haka zan zaga wurin yim baiko gare ka, ya Ubangiji,
don in cira muryar yabonka, a ji ta,
in faɗi dukkan ayyukanka na al'ajabi.
Ya Ubangiji, ina ƙaunar zama a gidanka,
da wurin da ɗaukakarka ke zama.
Kada ka haɗa raina da na masu zunubi,
ko kuwa raina da masu kisan kai,
waɗanda fitina ke gare su,
hannunsu na dama kuma ke cike da zalunci.
Amma ni kam zan zauna da mutunci,
ka cece ni, ka yi mini rahama.
Ƙafata tsaye ta ke a madaidaicin wuri,
zan yabi Ubangiji a cikin taron jama'a.
27
Ubangiji shi ne haskena, kuma cetona.
To, wa zan ji tsoro?
Ubangiji shi ne ƙarfin raina.
Tsoron wa zan ji?
Sa'ad da miyagu suka zo
su ci namana,
wato magabtana da maƙiyana
sai suka yi tuntuɓe, suka faɗi.
Kai ne maigida, ka zauna kare/ kusa/ da ni,
zuciyata ba za ta ji tsoro ba;
ko da yaƙi zai taso mini,
sa'an nan ma sai in ƙarfafa.
Abu guda na roƙi Ubangiji,
shi ne zan nema daga baya,
cewa in zauna a gidan Ubangiji
a dukkan rayuwata,
don in ga kyan Ubangiji,
in kuma yi roƙo a ɗakin yi masa sujada.
Domin a kwanakin wahala
zai ɓoye ni a cikin shigafarsa.
A tsariyar majami'arsa zai ɓoye ni,
zai ɗaga ni a kan dutse,
Yanzu kuma zai ɗaga kaina
bisa da magabtana da su ke kewaye da ni.
Zan yi hadayoyin murna
a cikin majami'arsa.
Zan yi waƙa, zan ma yi waƙoƙin yabo
ga Ubangiji.
Ka saurara, ya Ubangiji, in na yi kira da muryata.
Ka kuma ji tausayina, ka amsa mini.
Sa'ad da ka ce, "Nemi fuskata,"
sai zuciyata ta ce maka,
"Ya Ubangiji, zan nemi fuskarka."
Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni.
Kada ka kori bawanka da hushi,
kai ne, ka ke/ mai/ taimakona.
Kada ka jefad da ni, kada kuwa ka yashe ni,
ya Allah mai cetona.
Domin ubana da uwata sun yashe ni,
amma Ubangiji ya ɗauke ni.
Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji;
ka bi da ni hanya sosai
saboda magabtana.
Kada ka bashe ni ga nufin magabtana
domin masu shaidar zur sun tasam mini,
har suna faɗan mugun abu.
Na riga na suma, sai ko in na tabbata
ganin kyakkyawan aikin Ubangiji
a ƙasar rayayyu.
Ka dakata a gun Ubangiji;
ka ƙarfafa,zuciyarka ta yi ƙarfin hali/ daure;
ka dai dakata a gun Ubangiji.
28
Ya Ubangiji, kai zan kira;
ya dutsena, kada ka kurunce mini,
kada in ka ƙyale ni,
in zama kamar waɗanda suka gangara cikin rami.
Ka ji muryata wajen roƙona
lokacin da na yi kuka gare ka,
lokacin da na ɗaga hannayena
wajen tsattsarkan wurinka.
Kada ka haɗa ni da miyagu,
da masu aikin mugunta,
waɗanda ke yim maganar aminci da maƙwantasu,
amma mugun abu a zuciyarsu.
Ka ba su jaza'in aikinsu,
da jaza'in mugun aikinsu.
Ka ba su bisa ga aikin hannayensu,
ka ba su abin da suka cancanta.
Domin ba su mai da aikin Ubangiji wani abu ba/ ga girman aikin Ubangiji ba,
ko kuwa aikin hannunsa.
Zai karya su, ba zai inganta sua ba.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
domin ya saurari/ ji/ muryata ta roƙo.
Ubangiji shi ne ƙarfina,
shi ne kuma garkuwata;
zuciyata ta ba da gaskiya gare shi,
an kuwa taimake ni.
Saboda haka zuciyata tana farinciki ƙwarai,
zan kuwa yabe shi da waƙata.
Ubangiji shi ne ƙarfinsu,
shi ne kuwa ƙarfin ceto ga shafaffensa.
Ka ceci mutane, ka yi wa gādonka albarka;
ka ci da su kuma, ka tallafe su har abada.
29
Ya ku 'ya'yan ƙaƙƙarfa, ku yi wa Ubangiji baiko.
Ku bar wa Ubangiji ɗaukaka da ƙarfi.
Ku ba Ubangiji ɗaukakad da ke ga sunansa;
ku bauta wa Ubangiji cikin kyautatuwar tsarkaka.
Muryar Ubangiji na kan ruwa;
Allah maɗaukaki yana tsawa a kan ruwa da yawa.
Muryar Ubangiji ƙaƙƙarfa ce,
kuma cike ta ke da iko.
Muryar Ubangiji na tsaga cedar,
kai, Ubangiji yana tsaga cedar ta Libanon kaca-kaca.
Yana sa su kuma suna tsalle kamar ɗan maraƙi,
Wato Lebanon da Sirion kamar sau jeji.
Muryar Ubangiji tana ta da harshen wuta.
Muryar Ubangiji tana girgiza jeji,
Ubangiji yana girgiza jejin Kadesh.
Muryar Ubangiji tana sa bareyi haifu,
tana kuma zabge ganyen daji duka;
a ɗakin yi masa sujada kuwa
kowane abu na ce "Ɗaukaka".
Ubangiji ya zauna a wajen ruwan tsufana,
kan shi ne sarki.
Kai, Ubangiji ai yana zaman sarki ne har abada.
Ubangiji zai ba mutanensa ƙarfi.
Ubangiji zai yi wa mutanensa albarka,
ya basu aminci.
30
Zan tsananta yabonka, ya Ubangiji,
domin kai ne ka ta da ni,
ba ka kuwa sa magabtana sun yi farinciki a kaina ba.
Ya Ubangiji Allahna! na yi kuka gare ka,
ka kuwa warkad da ni.
Ya Ubangiji, ka fito da raina daga Mahalaka.
Ka kiyaye ni a raye, don kada in gangara rami.
Ka yi waƙar yabon Allah/ Ubangiji/, ya ku tsarkakansa,
ku kuma gode wa tsattsarkan sunansa.
Domin hushinsu na ɗan lokaci kaɗan ne,
rayuwa ganin damansa ne.
Kuka ya kasance daddare ne kawai,
amma farinciki zai zo da safe.
Ni kam, da zuciya ɗaya na ke faɗa,
"Har abada ba zan jijjiga ba.
Ya kai Ubangiji, saboda ƙaunarka ne
ka sa dutsena ya tsaya da ƙarfi.
Da ka ɓoye fuskarka
sai na damu.
Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji,
Ubangiji kuma na ke roƙo.
"Ina ribar da jikina ya samu
in na faɗa rami?
Ƙasa za ta yabe ka ne?
Za ta faɗi gaskiyarka ne?
Ka saurara, ya Ubnagiji, ka ji tausayina.
Ubangiji, ka zama mai taimako ne."
Kai ne ka mai da baƙincikina ya zama rawa.
Kai ne ka yaye tsummokina
ka yi mini ɗamara da farinciki,
domin ɗaukakata ta yi makawaƙar yabo,
kada ta yi shiru.
Ya Ubangiji, Allahna, zan gode maka har abada.
31
Ya Ubangiji, gare ka na sanya yardata,
kada ka sa in ji kunya har abada.
Ka cece ni ta gaskiyarka.
Ka sunkuyo mini da kunnenka,
ka cece ni da sauri.
Ka zame mini ƙaƙƙarfan dutse,
wato matari don cetona.
Domin kai ne dutsena, kuma gunguna/ matserata.
Saboda haka sai ka ja ni, ka nushe ni hanya
albarkacin sunanka.
Ka fid da ni daga cikin tarkon
da suka sanya mini a asirce,
domin kai ne madogarata.
Na sanya ruhuna a hannunka,
ka ta da/ fanse/ ni, ya Ubangiji,
Allahn mai gaskiya.
Na ƙi su, su masu ƙarairayin banza,
amma na ba da gaskiya ga Ubangiji.
Zan yi murna in yi farinciki a cikin rahamarka,
domin ka ga wahalata,
ka kuma san yadda raina ke cikin magabta.
Ka kuma ba ka bar ni a hannun magabta ba.
Ka sanya ƙafauna a wani babban wuri.
Ya Ubangiji, ka ji tausayina,
domin ina cikin baƙinciki;
idanuna suna lalacewa saboda baƙinciki
har ma raina da jikina.
Domin raina kullum a cikin baƙinciki ya ke,
shekaruna kuma na tafiya a cikin fargaba.
Ƙarfina na ƙarewa saboda laifina,
ƙasusuwana suna gajiya.
Na zama muzi saboda magabtana,
har ma ga maƙwautana ƙwarai,
na kuma zama mai tsoron abokan sabona.
Waɗanda suka gan ni da rashi sun guje mini.
An mance da ni kamar mataccen da aka mance da shi;
kamar fasasshiyar ƙwarya na ke.
Domin na ji labarin karya darajar mutane da yawa
ta ko'ina tsananin tsoro.
Sa'ad da suka yi shawara a kaina,
sai suka yanke shawara a kan za su kashe ni.
Amma sai na dogara gare ka, ya Ubangiji,
na ce, "Kai ne Allahna."
Lokacina na hannunka;
ka cece ni daga hannun magabtana,
da kuma masu tsananta mini.
Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka;
ka cece ni game da alherinka na ƙauna.
Ya Ubangji, kada ka bari in ji kunya,
domin na yi kiranka.
Ka sa munafukai su yi kunya,
ka bari su yi shiru a cikin Mahalaka.
Ka sa duk bakin da ke ƙarya yă bebanta,
wato mai yi wa mai gaskiya ba'a
tare da girman kai da raini.
Kai! Alherinka da ka sanya wa masu tsoronka da girma ya ke,
wato wanda ka ba waɗanda su ke amince da kai a gaban 'yan'adm.
A maɓoyon zatinka za ka ɓoye su
daga makircin mutane.
Sai ka ɓoye su a asirce a shigifa
daga yawan surutu.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
domin ya nuna mini alherinsa
na ƙauna mai bam mamaki
a cikin ƙaƙƙarfan birni.
Ni kam, a cikin garaje na ce,
"An raba ni a gabanka."
Duk da haka kuwa sai ka ji addu'ata
sa'ad da na yi kuka gare ka.
Ya ku tsarkaka, ku ƙaunaci Ubangiji,
Ubangiji na kiyaye mai bangaskiya,
yana yi wa mai alfarma sakamako ƙwarai.
Ku ƙarfafa, ku ɗaure,
ya ku da kuka sa zuciya ga Ubangiji.
32
Albarka ta tabbata ga wanda aka yafe masa laifuffukansa,
aka gafarta zunubansa.
Albarka ta tabbata ga mutumin
da Ubangiji bai sanya wa mugun abu ba,
wanda kuma ba zamba a ransa.
Sa'ad da na yi shiru,
sai ƙassusuwana su ke tsufa,
ta ihuna wuni zubut.
Dare da rana hannunka yana nauyaya mini;
ni'imata ta ƙafe, kamar lokacin fari.
Na sanad da zunubina gare ka,
ban kuwa ɓoye miyagun ayyukana ba.
Na ce, "Zan faɗa wa Ubangiji laifuffukana";
kai ne kuma ka yafe miyagun ayyukana na zunubi.
Saboda haka sai duk mai bin Allah ya yi addu'a gareka
a lokacin da za a same ka;
ba shakka sa'ada da ruwa yaba daji ba zai iso shi ba.
Kai ne mafakata,
kai ne za ka kiyashe ni daga wahala;
za ka kewaye ni da waƙoƙin kuɓuta.
Zan karantad da kai in koya maka hanyar da za ka bi;
zan ba ka shawara, idona a kanka.
Kada ku zama kamar doki ko kuwa alfadari
waɗanda ba su da fahinta,
waɗanda ragama da linzmi na tarkon riƙe su,
im ba haka ba kuma ba za su zo kusa da kai ba.
Munafuki zai sha baƙinciki mai yawa,
amma wanda ya amince da Ubangiji rahama za ta kewaye shi.
Ku yi farinciki da Ubangiji,
ku yi murna, ya ku masu gaskiya;
ku yi ihu don murna,
ya ku duka masu gaskiya a zuci.
33
Ku yi farinciki game da Ubangiji, ya ku masu gaskiya.
Yabo ya kamaci mai gaskiya.
Ku gode wa Ubangiji da molo;
ku yi waƙoƙin yabo gare shi
da kiɗan molo mai tsirkiya goma.
Ku waƙa masa sabuwar waƙa;
ku yi kiɗa da azanci da murya/ sauti/ mai ƙara.
Domin Maganar Ubangiji daidai ce,
dukkan aikinsa kuwa da bangaskiya a ke yinsa.
Yana ƙaunar aikin gaskiya da sakamako;
duniya cika ta ke da alherin ƙauna na Ubangiji.
An yi sammai da Maganar Allah/ Ubangiji/ ne,
dukkan mazauna cikin ma da numfashinsa aka yi.
Yas tara ruwan teku ga ɗaya kamar tudu;
ya tara ruwayen a taskoki.
Duk duniya tă tsoraci Ubangiji;
duk mazauna duniya su tsorace shi.
Domin ya yi magana, an kuwa aikata;
ya yi unarni, ya kuwa tabbata.
Ubangiji ya mai da shawwar al'ummai ta zama banza;
ya mai da tunanin mutane marar amfani/ tasiri.
Shawarar Ubangiji tana nan har abada,
wato shawarar zuciyatasa zuwa ga dukkan zamanai.
Albarka ta tabbata ga al'umma da Ubangiji ne Allahnta;
su ne mutanen da ya zaɓa saboda samun gado a gare shi.
Ubangiji yana gani daga sama,
yana ganin dukkan 'ya'yan mutane;
daga wurin zamansa ya ke duban
dukkan mazaunan duniya,
shi da ke zayyana zukatansu su duka,
ya ke kuma duba ayyukansu.
Ba sarkin da yawan runduna ta kuɓutar;
ƙato ba ƙarfinsa na ke kuɓutad da shi ba.
Doki abin banza ne wajen neman tsari,
ba kuma zai iya ceton kowa da ƙarfin nan nasa mai yawa ba.
Ga shi, idon Ubangiji na kan masu tsoronsa,
da waɗanda kuma sa zuciya ga rahamarsa,
don ya ceci rai daga halaka,
ya kuma kiyaye su a raye a zamanin yunwa.
Rammu ya jiraci Ubangiji;
shi ne mataimakimu, kuma garkuwarmu.
Domin zuciyarmu za ta yi farinciki da shi,
domin mun amince da tsattsarkan sunansa.
Ya Ubangiji, ka sa tausayinka ya kasance a gare mu
kamar yadda muka sa zuciya gare ka.
34
Zan yaba wa Ubangiji a dukkan lokaci;
yabonsa zai kasance a bakina koyaushe.
Raina zai yi alfahari game da Ubangiji;
mai tawali'u zai ji ya yi farinciki da shi.
Ya mai ƙarfi, Ubangiji da ke tare da ni,
bari mu ɗaukaka sunansa tare.
Na roƙi Ubangiji, ya kuwa amsa mini,
ya kuɓutad da ni daga dukkan tsorona.
Sun dube ni/ shi [?]/, sun haskaka;
fuskokinsu ba za su kunyata ba har abada.
Mutumin nan abin tausayi, ya yi kuka,
Ubangiji kuma ya saurare shi,
ya kuɓutad da shi daga dukkan wahalce-wahalcensa.
Mala'ikan Ubangiji ya kan kewaye
masu tsoron Ubangiji, yă cece su.
Ka duba mana, ka gani yadda Ubangiji ke da kirki.
Albarka ta tabbata ga wanda ya amince da shi.
Ya ku tsarkakan Ubangiji, ku tsorace shi,
domin ba sauran bukata ga masu tsoronsa.
Kwiyakwiyan zaki sun yi rashi, suna yi yunwa,
amma masu neman Ubangiji ba za su nemi wani kyakkyawan abu ba.
Ya ku 'ya'ya, ku zo, ku saurare ni,
zan koya muku tsoron Ubangiji.
Wane mutun na ke bukatar rai,
ya ke son tsawon kwana don ya ga kyawawan abubuwa?
Ka tsare bakinka daga mugunta,
kada ka yi miyagun/ yaudara/ maganganu
Ka rabu da mugun abu, ka yi kyakkyawa;
ka nemi aminci, ka kiyaye shi.
Idanun Ubangiji ga mai gaskiya su ke,
kunnuwansa kuwa a buɗe su ke ga kukansu.
Fuskar Ubangiji a juye ta ke ga masu aikata mugunta;
ya kan ƙi tunawa da su a duniya.
Mai gaskiya ya yi kuka, Ubangiji kuwa ya ji,
ya kuwa kuɓutad da su daga wahalce-wahalcensu.
Ubangiji na suka da masu fargaba,
yana kuwa kuɓuta da masu zunubi.
Wahalce-wahalcen masu gaskiya suna da yawa,
amma Allah/ Ubangiji [?]/ ya kuɓutad da shi daga gare su duka.
Yana kiyaye dukkan ƙasusuwansa;
ba waninsu da ya karye.
Muguta ce za ta kau mugu;
waɗanda suka ƙi mai gaskiya kuwa za a hukunta/ halaka/ su.
Ubangiji yana farfaɗowa da ranbayinsa;
ba waninsu da za a halaka kuwa
a cikin masu amince da shi.
35
Ya Ubangiji, ka yi fama mana da masu fama da ni;
ka yi faɗa da masu faɗa da ni.
Ka ɗauki garkuwa da warwaji,
ka tsaya don taimakona.
Ka kuma zaro mashi
ka tsare hanyar masu kora ta.
Ka ce da raina,
"Ni ne cetonka!"
Masu neman raina
su kunyata, su zama masu ƙanƙanci.
Masu makirci game da ni
su juya, su kunyata.
Su zama ƙaiƙayi a gaban iska,
mala'ikan Ubangiji yana kora su.
Hanyarsu tă zama mai duhu da santsi,
mala'ikan Ubangiji yana korarsu.
Domin ba gaira ba sabar suka kafa mini tarko,
ba gaira ba sabar suka tona mini rami.
Halaka tă zaike masa ba shiri,
tarkonsa da ya ɗana yă kama shi
ya faɗa, yă halaka.
Raina zai yi farinciki da Ubangiji,
zai yi farinciki a lokacin ceton da zai yi.
Dukkan ƙasusuwana za su ce,
"Ya Ubangiji, wa ke kama da kai?
kai da ke kuɓutad da gajiyayye
daga hannun wanda ya fi shi ƙarfi ƙwarai,
har ma gajiyayyu da marasa daga hannun mai zalumtarsu.
Tashi, kai shaida marar gaskiya;
sun tambaye ni abubuwan da ban sani ba.
Suna rama mini alherina da mugunta,
suna ɓata raina/ suna neman raina.
Ni kuwa, im ba su da lafiya,
na kan sa tsumma,
na wahal da kaina da ƙin cin abinci;
addu'ata ta komo gare ni.
Na yi kamar abokina ne
ko kuwa ɗan'uwana;
na sunkuya, ina nadama kamar wanda ke baƙincikin mutuwar uwatasa.
Amma da na tsaya sai suka yi farinciki,
suka taru gu ɗaya.
Wulakantattun nan suka taru, suka tasam mini,
ni kuwa ban sani ba.
Suka yi ta yi mini rotsi da dainawa.
Kamar masu ba'ar wulakanci a wurin biki
suka yi ta cizo na.
Ya Ubangiji, har yaushe za ka dinga gani?
Ka ceci raina daga halakatasa,
ka cece shi daga zakoki.
Zan gode maka ababban taron jama'a;
zan yaba maka a cikin mutane da yawa.
Kada magabtana su yi farinciki akaina a banza,
waɗanda kuma suka ƙi ni
ba dalili kada su samu su rumtsa ido.
Domin ba sa maganar aminci,
sai dai suna shirya maganganun makirci ne
ga masu zama lafiya a cikin ƙasa.
Har suna buɗe mini bakunansu ƙwarai,
suka ce, "Mhm, Mhm, ai mun gani."
Kai ka gani, ya Ubangiji; kada ka ƙyale.
Ya Ubangiji, kada ka yi nesa da ni.
Ka motsa kanka, ka farka saboda shari'ata,
wato saboda sha'anina, ya Allahna, kuma Ubangijina.
Ka yi mini shari'a bisa gaskiyata, ya Ubangiji Allahna,
kada ka bari su yi farinciki a kaina.
Kada su ce a zuciyarsu,
"Mhm, haka mu ke so."
Kada su ce, "Ai mun haɗiye shi."
Bari su kunyata, su muzanta gaba ɗaya,
su da su ke murna da kuttuna.
Ka sa kunya ta lulluɓe su da wulakanci
su ka ke kumbura kansu suna gaba da ni.
Waɗanda ke jin daɗin sha'anina kuwa
su yi sowa don farinciki, su yi murna,
bari dai maganan nan ta tabbata a bakinsu koyaushe, cewa,
"Ɗaukaka ta tabbata ga Ubangiji,
shi da ke murna da arzutar bawansa."
Bankina zai yi maganr gaskiyarka
da yabonka wuni zubu.
36
Laifin mugu na faɗa mini a cikin zuciyata, cewa
ba tsoron Allah a gaban idanunsa,
wai ba za a gane muguntarsa
a ƙi ta/ shi/ ba.
Maganar bakinsa ma mugunta ce da yaudara;
ya bar yin hikima da yin kyakkyawan abu.
Yana ƙaga mugunta a kan gasonsa;
ya kan sa kansa hanyar da ba ta da kyau;
ba ya ƙin aikin mugunta.
Ya Ubangiji, alherinka na ƙauna yana sama,
gaskiyarka ta kai har cikin sammai.
Gaskiyarka kamar duwatsun Allah su ke,
hukunce-hukumcenka kamar teku su ke mai yawa;
ya Ubangiji, kai ne ka adana mutum da dabba.
Ya Ubangiji, alherinka na ƙauna da kyau ya ke!
'Yan'adam kuwa na fakewa a ƙarƙashin fukafukanka.
Za su wadata ƙwarai
da yalwar abin da ke gidanka,
za ka kuma shayad da su
daga kogin farincikinka.
Domin kogin rai a gare ka ya ke;
a cikin haskenka za mu ga haske.
Ka ci gaba da ba da alherinka na ƙauna
ga waɗanda suka san ka,
gaskiyarka kuma ga masu gaskiya a zuci.
Kada ka bari mai alfarma ya tasam mini,
kada kuma mugu ya kore ni.
Ga nan masu aikin mugunta sun faɗi,
an kashe su, ba za su kuwa iya tashi ba.
37
Kada ranka ya ɓaci saboda miyagu,
kada kuwa ka ji ƙyashin masu aikata rashin gaskiya.
Domin nandanan za a yanke su kamar ciyawa,
su bushe kamar ɗanyen ganye.
Ka amince da Allah,
ka yi kyakkyawan aiki;
ka zauna a ƙasar, ka yi bangaskiya.
Ka kuma yi farinciki da Ubangiji,
zai kuwa biya maka bukatun ranka.
Ka miƙa wa Ubangiji hanyoyinka;
ka kuwa gaskata/ amince/ da shi,
sai ya biya maka bukata.
Zai mai da gaskiyarka ta ci gaba kamar haske,
hukuncinka kamar tsakar rana.
Ka jingine/ dogara/ ga Ubangiji,
ka jira shi da haƙuri;
kada ka ranka ya ɓaci
da wanda ya arzuta a cikin al'amarinsa,
saboda mutumin da ya aikata miyagun abubuwa.
Ka daina hushi, ka ya da harzuƙa.
Kada ranka ya riƙa ɓaci,
mugun abu kaɗai ya ke jawowa.
Domin za a ware masu mugun aiki,
amma masu tsayawa ga Ubangiji za su gaji ƙasa.
Saura ɗan lokaci kaɗan mugu zai kau;
ka dai dubi matsayinsa ba zai wanzu ba.
Amma masu tawali'u za su gaji ƙasar,
za su yi murna da tare da yalwataccen aminci.
Mugu yana haƙa wa mai gaskiya rami,
yana cizon bakinsa saboda shi.
Ubangiji zai yi masa dariya,
domin ya ga kwanakinsa na gabatowa.
Miyagu sun zare takobi, sun ɗaura baka,
domin su ka da gajiyayyu masu talauci,
su karkashe masu gaskiya a cikin tafarkin Allah.
Takobinsu zai shiga zuciyarsu/ ratsa su,
bakanninsu kuma za su karye.
Ɗan kaɗan ɗin da mai gaskiya ke da shi
ya fi mai yawan da miyagu da yawa ke da shi.
Domin za a karya hannayen miyagu;
amma Ubangiji yana kiyaye mai gaskiya.
Ubangiji ya san kwanakin kamilai,
gadonsu zai zama na har abada.
Ba za su ji kunya ba a mugun lokacin,
za a kuma wadata su a kwanakin yunwa.
Amma miyagu za su halaka,
magabtan Ubangiji kuma za su zama kamar kiwatattun 'yan raguna,
za su ƙone, a cikin hayaƙi ma za su ƙone.
Mugu ya kan yi bashi, amma ba ya biya;
amma mai gaskiya ya kan yi dattaku, ya kan bayan.
Kamar waɗanda ya yi wa albarka su za su gaji ƙasar,
waɗanda ya la'anta kuwa sai a yanke su.
Tafiyar mutum ta Ubangiji ce,
yana kuwa farinciki da hanyatasa.
Ko ya faɗi, ba zai faɗi ƙurmus ba,
domin Ubangiji na riƙe shi da hannunsa.
Dā na yi ƙuruciya, amma yanzu na tsufa,
amma har yanzu ban ga an ya da mai gaskiya ba
ban kuma ga 'ya'yansa na barar abinci ba.
Wuni zubut yana yin abubuwan alheri,
yana kuma ba da ramce,
ana kuma yi wa zuriyarsa albarka.
Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri,
ku zauna har abada.
Domin Ubangiji na son shari'a,
kuma ba ya ya da tsarkakansa.
Ana adana su har abada,
amma zuriyar mugu kam yanke/ ware/ su za a yi.
Mai gaskiya shi zai gaji ƙasar,
yă zauna a cikinta har abada.
Bakin mai gaskiya maganar hikima ya ke yi,
kalaminsa kuwa na hukunci ne.
Ka'idodin Allahnsa na zuciyastasa,
ƙafarsa ba za ta sulluƙe ba.
Mugu yana ganin/ kallon/ mai gaskiya,
yana so ya kashe shi.
Ubangiji ba zai bar shi a hannunsa ba,
ba kuma zai ba shi rashin gaskiya ba in an yi masa shari'a.
Ko tsaya ga Ubangiji, ka kiyaye hanyatasa,
zai kuwa ɗaukaka ka har ka gaji ƙasar;
sa'ad da aka ware mugu za ka gani.
Na ga mugu a cikin iko mai girma,
yana bazuwa kamar bishiyad da ta da gargaje a ƙasarsu ta asali.
Amma si wani ya wuce, ashe, ba shi ba ne;
na yi ta nemansa, amma ba a iya samunsa ba.
Ka kula da kamilin mutun,
ka kuma dubi mai gaskiya,
domin ƙarkon na yayyan ɗin nan aminci ne.
Masu laifi kam, gaba ɗaya za a hallaka su;
ƙarshen miyagu yankewa/ warewa/ ne.
Amma ceton masu gaskiya na Ubangiji ne;
shi ne madogara a lokacin wahala.
Ubangiji kuwa ya taimake su ya cece su;
ya cece su daga hannun miyagu, ya kuɓutad da su,
domin sun nemi mafaka a gunsa.
38
Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini a cikin hushinka,
kada kuma ka hore ni a cikin tsananin hushinka.
Domin kibanka sun kama ni gar gar,
hannunka kuwa ya damƙe ni raf!
Jikina ba shi da aminci saboda haushin da ka ke ji,
ƙasusuwana kuma ba su da lafiya saboda zunubina.
Domin miyagun ayyukana sun sha kaina
kamar dai kaya mai nauyi, sun danƙare ni.
Miyakuna suna wari, suna kumruce
saboda rashin azancina.
Ina jin ciwo, har na tanƙware ƙwarai,
wuni zubut baƙinciki na ke yi.
Duk kunkumina ƙuna ya ke yi,
naman jikina bai ji daɗi ba.
Na ligirce, na ji ciwo ƙwarai,
na yi kururuwa saboda rashin kwanciyar zuciyata.
Ya Ubangiji, dukkan bukatata na gare ka,
ban kuwa ɓoye maka nishina ba.
Zuciyata tana harbawa,
ƙarfina yana gazawa,
ganin idona ma yana ɓace mini.
Masu ƙaunata da abokaina sun kau daga bala'ina,
dangina kuma sun tsaya can nesa.
Masu neman kashe ni kuma sun kakkafa mini tarko;
masu neman a cuce ni suna maganganun ɓarna.
suna ƙaga makirci wuni zubut.
Amma ni sai na ƙi ji, kamar kurma,
sai na zama kamar beben da ba ya magana.
Ni mutun ne wanda ba ya ji
wanda babu shaida a bakinsa.
Domin a gare kana ke sa zuciya, ya Ubangiji;
za ka amsa, ya Ubangiji, Allahna.
Domin na ce, "Kada su yi farinciki a kaina.
Sa'ad da na yi 'yar sassarfa sai suka tasam mini."
A shirye na ke in tsaya cik,
baƙincikina kuwa koyaushe yana gaban idanuna.
Zan bayyana muguntata,
zan yi ɗau da na sani game da zunubina.
Amma magabtana a faɗadke su ke, kuma ƙarfafa ne,
waɗanda suka ƙi ni ba dalili kuwa yaɗuwa su ke yi.
Masu rama alheri da mugunta ma abokan gabana ne,
domin ina bin kyakyawan abu.
Kada ka yashe ni, ya Ubangiji,
Ya Allahna, kada ka yi nesa da ni.
Ka yi hamzari ka taimake ni,
Ya Ubangiji, Macecina.
39
Na ce, "Zan mai da hankali da sha'anina,
kada in yi zunubi da harshena;
zan yi wa bakina linzami
a sa'ad da mugu ke gabana."
Na yi shiru kamar bebe
na yi kawai, har ga kyawawan abubuwa ma.
Hankalina ya tashi don baƙinciki.
Zuciyata na ƙuna.
Ina cikin wuswasi
sai wutar ta huru;
sa'an nan na yi magana da bakina, na ce,
"Ya Ubangiji, ka sanasshe ni ƙarshena mana,
in san iya tsawon kwanana,
in san ajizancina.
Ga shi, ka mai da kwanakina a tafin hannu;
shekaruna a gare ka kamar babu ne.
Ba shakka kowane mutun banza ne
a kowane maƙamin ɗaukaka ya ke.
Ba shakka kowane mutum ɗabi'ar banza ya ke bi
Hakika a banza aka damuwa;
yana jibga dukiya, bai kuwa san mai ɗebe ta ba.
"To, yanzu kuma, ya Ubangiji,
me na ke dako ne?
Sazuciyata na gare ka.
Ka kuɓutad da ni daga dukkan laifuffukana.
Kada ka mai da ni abin ƙyamar wawaye.
Na bebanta, ban buɗe bakina ba,
domin kai ne ka yi haka.
Ka kawar mini da dukan nan naka;
marinka ya halaka ni.
Ga shi kuwa kana gyara mugun aikin mutun da tsawartarwa,
ka kan sa kayansa yă dushe kamar asu;
hakika kowne mutun banza ne.
"Ya Ubangiji, ka saurari maganata,
ka saurari kukana;
kada ka ji daɗin zub da hawayena,
domin ni baƙonka ne,
baƙo, kamar yadda kakannina su ke.
Ka adana ni, don in farfaɗo da ƙarfinka,
kafin in tafi can, in ƙaura."
40
Na jiraci Ubangiji a cikin haƙuri,
ya kuwa karkata gare ni, ya ji kukana.
Ya kuma fid da ni daga mummunan rami,
daga taɓo mai caɓi,
ya ɗora ƙafafuna a kan dutse,
ya ɗaddara tafiyata.
Ya sanya sabuwar waƙa a bakina,
wato yabon Allahmmu.
Da yawa za su ga ni, su ji tsoro,
su kuma gaskata da Ubangiji.
Albarka ta tabbata ga wanda ya mai da Ubangiji madogaratasa,
wanda ba ya mutunta mutakabbiri,
ko kuwa mai biye wa ƙarairayi.
Ya Ubangiji Allahna, ayyukan da ka yi suna da yawa;
tunaninka da suka yi a kammu,
ba dama a shirya maka su.
In har zan shaidar, in yi magana a kansu,
ai har za su fi gaban ƙidaya.
Ba ruwanka da hadaya da baiko;
ka buɗe mini kunnuwana.
Ba ka bukaci ƙonannen baiko
da na gafarar zunubi ba.
Sa'an nan sai na ce,
"Ga shi maganad/ abin; da aka rubuta a littafi game da ni ta zo.
Ina farincikin aikata nufinka, ya Allahna;
ai shari'arka tana zuciyata."
Na shaidad da gaskiya a cikin babban taron jama'a;
ga shi, ban/ ba zan/ yi shiru ba,
ya Ubangiji, ai ka sani.
Ban ɓoye gaskiyarka a zuciyta ba,
na sanad da gaskiyarka da cetonka;
ban ɓoye alherinka na ƙauna ba da gaskiyarka
ga taron jama'a.
Kada ka hana ni tattausan alherinka, ya Ubangiji;
alherinka na ƙauna da gaskiyarka su kiyaye ni a kowane lokaci.
Domin miyagun abubuwa ba iyaka sun kewaye ni;
muguntata ta cim mini,
har ba na iya ɗaga kai in dubi sama;
har sun fi gashin kaina yawa,
zuciyata kuma ta narke.
Ya Ubangiji, kă ji daɗin cetona,
ka hanzarta taimakona, ya Ubangiji.
Bari su kunyata, su muzanta gaba ɗaya
su masu neman raina su halaka ni.
A mai da su baya, a sa su cikin wulakanci
su waɗanda ke farinciki da cutuwata.
Bari su kaɗaita, saboda kunyatarsu,
su da ke ce da ni, "Yauwa, yauwa!"
Bari duk masu nemanka
su yi farinciki, su yi murna da kai;
bari masu son cetonka
su koyaushe riƙa cewa, "Ɗaukaka tā tabbata ga Ubangiji."
Amma ni, gajiyayye ne, mabukaci;
duk da haka kuwa Ubangiji na tunawa da ni.
Kai ne mataimakina, mai cetona;
kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji.
41
Albarka ta tabbata ga mai kula da gajiyayyu.
Ubangiji zai cece shi a muguwar rana.
Ubangiji zai adana shi,
ya bar shi a raye,
za a yi masa albarka a duniya;
kada ka ba da shi ga magabtansa.
Ubangiji zai riƙe shi a kan gadon jinya;
kai ne ka shirya masu gadonsa na jinya.
Na ce, "Ya Ubangiji,
kă ji tausayina;
ka warkad da ni,
domin na yi maka laifi."
Magabtana suna zagina, suna cewa,
"Yaushe ne zai mutu, sunansa ya ɓata?"
In kuwa ya zo ganina,
sai ya kan yi muguwar magana/ faɗi mummunan abu;
zuciyatasa tana tara miyagun abubuwa;
in ya tafi nisan duniya ya kan faɗi haka.
Duk masu ƙi na su kan taru su raɗe ni,
suna shawarar abin da zai cuce ni a zuci.
Suka ce "Wai wani mugun ciwo ne ya ke tare da shi,
yanzu kuwa da ya kwanta, ba zai ƙara tashi ba.
Ga shi, abokina na kaina
wanda na amince da shi
ya haure ni.
Amma kai, ya Ubangiji, ka ji tausayina,
ka tashe ni, don in toshe bakinsu.
Ta haka na san kana farinciki da ni,
domin magabtana ba su yi nasara da ni ba.
Ni kuwa ka ɗaukaka ni a cikin mutuncina,
ka ajiye ni a gabanka har abada.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahn Bani Isra'ila
tun fil'azal har ya zuwa matuƙar zamani.
Amin, summa amin.
42
Kamar yadda agaren barewa ke neman ruwa/ rafi/ ido rufe,
haka raina ke nemanka ido rufe, ya Ubangiji.
Raina na ƙishin Allah, Rayayyan Allah.
Yaushe zan zo in bayyana a gaban Allah?
Hawayena sun zama su ne abincina dare da rana,
suna kuwa ce da ni koyaushe,
"Ina Allahn naka ne?"
Waɗannan abubuwa na ke tunawa,
na ke zubad da raina;
yadda na tafi da babban taro,
na kai su gidan Allah,
tare da muryar farinciki da yabo,
taro mai kiyaye tsattsarkar rana.
Me ya sa ka faɗi, ya kai raina,
kuma, me ya sa ka yi shiru a cikina?
Ka sa zuciya ga Allah,
domin har yanzu zan yabe shi,
saboda kyan kyan kamanninsa.
Ya Allahna, raina ya ɓaci;
saboda haka ina tunawa da kai
tun daga Kogin Urdun, da kuma Harmona
daga Dutsen Mizar.
......
......
Duk da haka kuwa Ubangiji zai umarci alherinsa na ƙauna da rana,
daddare kuwa waƙarsa za ta kasance a bakina,
wato addu'a ga Allah mai raya ni.
Zan ce da Allahna, kuma dutsena,
"Me ya ka mance da ni?
Dom me na ke baƙinciki
saboda matsawar magabta?"
Kamar ana sara ni da takobi,
magabtana suna zagi na;
koyaushe suna ce mini,
"Ina Allahn naka?"
Me ya sa ka yi jirim, ya kai raina,
kuma, me ya sa ka yi shiru?
Ka sa zuciya ga Allah,
domin zan yabe shi har wa yau,
shi wanda ke lafiyata, kuma Allahna.
43
Ka bi kaduna, ya Allah,
ka taimake ni a kan al'umma marar ibada;
ka cece ni daga hannun mayaudari, marar gaskiya.
Domin kai ne Allah mai ƙarfafa ne,
dom me ka jefad da ni?'Dom me na ke tafe ina kuka
saboda matsawar magabta?
Ka aiko da haskenka, da gaskiyarka, su ja ni,
su kawo ni tsattarkan dutsenka, da majami'unka.
A sa'an nan ne zan je wurin yim baiko ga Allah,
gun Allah abin matuƙar farincikina;
zan yabe ka a cikin molo,
ya Allah, Allahna.
Dom me ka yi jirim, ya kai raina,
dom me kuma ka yi shiru?
Ka sa zuciya ga Allah,
domin zan yabe shi har wa yau,
shi wanda ke lafiyata, kuma Alahna.
44
Mun ji da kunnuwammu, ya Allah,
kakannimmu sun gaya mana,
irin aikin da ka yi a zaaninsu,
a zamanin dā.
Ka kori al'ummai da hannunka,
ka kafa su a nan;
ka wahal da mutanen,
ka warwatsa su.
Domin sun kasa samun ƙasar su gada da takubasnsu;
hannayensu kuma ba su cece su ba;
sai dai hannnka na damatsenka,
da hasken fuskarka,
domin ba ka so su ba.
Kai ne Sarkina, ya Allah.
Ka umarci kuɓuta ga Bani Isra'ila.
Za mu kori magabtammu ta kanka;
ta kan sunanka za mu tattake su,
su da suka tasam mana.
Domin ba zan dogara ga bakana ba,
takobina kuma ba zai cece ni ba.
Amma kai, ka cece mu daga magabtammu,
kā kuma kunyata maƙiyammu.
Alfaharimmu ga Allah ya ke wuni zubut,
za mu gode wa sunanka har abada.
Amma yanzu ka jefad da mu, ka wulakanta mu,
ba ka tafi tare da rundunarmu ba.
Ka sa mun ba maƙiya ƙeya,
maƙiyan namu kuma sun ɓata wa kansu.
Ka ba da mu kamar tumakin da za a yanka a ci,
ka kuma warwatsa mu a cikin al'ummai.
Ka sai da mutanenka ba biya,
ba ka ƙari aljihunka da kuɗinsu ba.
Ka sa mun zama abin tsargi ga maƙwautammu,
abin zagi, kuma abin ba'a ga waɗanda ke kewaye da mu.
Ka mai da mu abin zunɗe ga al'ummai
abin kaɗa kai ga mutane.
Wuni zubut ina tare da wulakanci,
kunya kuma ta rufe ni,
saboda muryar mai zagin nan da mai saɓon nan,
saboda magabci da mai neman ramuwa.
Wannan duk ya same mu,
amma kuwa ba mu mance da kai ba,
ba mu kuma saɓa alkawarinka ba.
Zukatammu ba su juya ba,
ƙafafummu kuma ba su goce daga hanya ba;
ka watsa mu ƙwarai kamar mu dila ne,
mutuwa na jewa a kammu.
Idan mun mance da sunan Alahmmu,
ko kuwa mun ɗaga hannu mun roƙi wanin Allah,
ashe, Allah ba zai binciko wannan ba?
Domin ya san asirin zuci.
Ga shi, saboda kai ne aka kashe mu wuni zubut,
an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka ne.
Ka farka, dom me ka ke barci, ya Ubangiji?
Ka tashi, kada ka jefad da mu har abada.
Me ya sa ka ke ɓoye fuskarka,
ka ke mancewa da wahalarmu da matsuwarmu?
Domin rammu ya sunkuya ƙasa,
cikimmu ya fashe, ya faɗi.
Ka tashi don taimakommu,
ka cece mu saboda alherinka na ƙauna.
45
Zuciyata tana gudana da abu mai kyau;
ina faɗan abubuwan da na yi ne waɗanda suka shafi sarki;
harshena alkalamin mai shirin yin rubutu ne.
Kai ka fi 'yan'adam kyau,
bakinka an cika shi da alheri;
saboda haka Allah yā yi maka albarka har abada.
Ka ɗora takobinka a kan cinyarka, ya mai iko,
tare da ɗaukakarka da ikonka.
Ka yi hawan arziki a cikin ikonka,
saboda gaskiya da tawali'u da aikin gaskiya;
hannunka na dama kuwa zai koya maka abubuwa masu ban tsoro.
Kibanka masu tsiri ne.
Mutane suna mutuwa in sun kara da kai.
A zuciyar magabtan sarki su ke.
Ya Allah, gadon sarautarka na har abada abadin ne.
Sandan sarautar gaskiya shi ne sanadanka na sarauta;
kā ƙaunaci aikin gaskiya,
ka ƙi aikin mugunta.
Saboda haka Allah, Allahnka, ya shafe ka
da man farinciki birbishin jama'arku;
duk tufafinka na ƙamshin mur, da al'ul, da cassia.
Molo ya sa ka farinciki a wuraren kaɗe-kaɗe;
'ya'yan sarakuna suna daga cikin matan da ka ke mutuntawa;
sarauniya tana tsaye a hannunka na dama
a cikin kayan zinariya da Ophir.
Ki saurara, ya ke yarinya,
ki duba, ki kasa kunne;
ki kuma manta da mutanenku da gidan ubanki;
haka sarki zai so kyanki.
Domin shi ne ubangijinki
shi kuwa za ki bauta wa.
'Yar Taya ma za ta kasance
a can tare da wata kyauta,
ko mai arziki ma a cikin mutane
zai roƙe ka wata alfarma.
Maryama a cikin fada ita ce mafi ɗaukaka.
Tufafinta a saƙe su ke da zinariya.
Za a kai ta wurin sarki da ado.
Ƙawayar amarya da za su bi ta,
za a kawo su gare ka.
Za a kai su da murna da farinciki
su da za su shiga fadar sarki.
A maimakon kakanninka, sai ka ga 'ya'yanka,
su ne za ka mayar sarakuna a duniya duka.
Zan sa a tuna da sunanka a dukkan zamanai;
saboda haka sai mutane su gode maka har abada abadin.
46
Allah shi ne matserarmu, kuma ƙarfimmu,
mataimaki nandanan a lokacin wahala.
Saboda haka ba za mu ji tsoro ba
ko duniya ta sauya,
ko an kau da duwatsu
an kai cikin bahar;
ko ruwan bahar ya yi ruri yana hauka,
ko duwatsun sun raurawa saboda haukar ruwan.
Akwai wani kogi wanda rafukansa
su ke faranta wa birnin Allah,
wato tsattarkan wuri
na majami'un Mafi Ɗaukaka.
Allah na tsakiyatata, ba za ta damu ba;
Allah zai taimake ka nandanan kuwa.
Al'ummai sun fusata,
sarautu sun jijjiga;
ya yi furuci, duniya ta narke.
Allah Ubangijin runduna na tare da mu,
Allahn Yakubu shi ne matserarmu.
Ku zo, ku ga aikin Ubangiji,
irin wofintawar da ya yi a duniya.
Ya sa an daina yaƙi a ƙarshen duniya;
ya karya baka, ya karya mashi gida biyu,
ya ƙone karusai a wuta.
"Ku yi kawai, ku san ni ne Allah.
Za a ɗaukaka ni a cikin al'ummai,
Za a ɗaukaka ni a duniya."
Allah Ubangijin runduna na tare da mu;
Allahn Yakubu shi ne matserarmu.
47
Ya ku mutane, dukkanku ku yi tafi.
Ku yabi Allah da muryar nasara.
Domin Ubangiji Mafi Ɗaukaka abin tsoro ne,
shi ne babban sarki ne a duniya duka.
Zai biyar mana da mutanen,
da al'ummai duka, su bi mu/ mu hau kansu.
Shi zai zaɓa mana magadammu,
wato mai fifiko na Yakubu da ya ƙaunata.
Allah ya hau sama da ta da murya,
Ubangiji da muryar kakaki.
Ku yi waƙoƙin yabon Allah,
ku yi waƙoƙin yabo.
Ku yi waƙoƙin yabon sarkimmu,
ku yi waƙoƙin yabo.
Domin Allah shi ne sarkin duniya duka;
ku yi waƙoƙin yabo game da fahinta.
Allah ne ka mulkin al'ummai,
Allah na zaune a kan gadon sarautarsa tsattarka.
An tara sarakunana mutane
don su zama mutanen Allahn Ibrahim
Domin garkuwar duniya duka ta Allah ce;
an ɗaukaka shi da gaske.
48
Allah mai girma ne,
ya kuma cancanci matuƙar yabo/ yabo ƙwarai,/ a birnin Allahmmu.
Mai kyan ɗaukaka,
abin murnar duniya,
shi ne Dutsen Sihiyona ta ɓaryar arewa,
birnin babban Sarki.
Allah ya sanad da kansa a cikin fadarta
kan shi matsera ne.
Domin ga shi sarakunan sun tara kansu,
sun wuce tare.
Sun ga al'amarin,
kuma sai suka yi mamaki,
sun firgita, sun gudu;
a can jikinsu ya ɗauki rawa,
da ciwo kamar mace mai naƙuda.
Ka kakkarya jiragen Tarshishi
da iskar gabas.
Kamar yadda muka ji,
haka muka gani
a birnin Ubangijin runduna,
a birnin Allahmu;
Allah zai kafa shi har abada.
Muna tunanin alherinka na ƙauna, ya Allah,
a tsakiyar ɗakin yi maka sujada.
Kamar yadda sunanka ya ke, ya Allah,
haka kuma yabonka ya ke har ƙarshen duniya.
Hannun dama cike ya ke da aikin gaskiya;
ka sa Dutsen Sihiyona ya yi farinciki.
Bari 'ya'yan Yahuda mata su yi farinciki
saboda hkumcinka.
Ka zaga Sihiyona, ka kewaye ta,
ka faɗi hasumiyoyinta.
Ka kula ga gimshiƙanta sosai,
ka dubi fadatata,
domin ka gaya wa zuriyar da ke zuwa
domin Allahn nan
Allahmmu na har abada abadin.
Shi ne zai zama mai kula da mu har kan mutuwa.
49
Ku ji wannan, ya ku dukkan mutane.
Ku saurara, ya ku dukkan mazauna duniya,
ƙasƙastattu da ɗaukakakku duka,
da mawadata da matalauta duka.
Zan yi maganar hikima;
tunanin zuciyata zai zama na fahinta.
Zan kasa kunnena ga misali,
zan bayyana maganata ta ɓoye a cikin molo.
Yaya zan ji tsoro a kwanakin mugunta,
sa'ad da aikin mugunta ya kewaye ni ta ko'ina?
Waɗanda suka dogara da dukiyarsu,
su ke alfahari da tarin dukiyarsu.
Ba waninsu da zai iya ceton ɗan'uwansa ta ko yaya/ ƙaƙa,
ba kuma zai iya fansarsa a wurin Allah ba.
(Domin fansar ransu mai tsada ce,
sai dai a bar ta kawai har abada.)
Zai zauna kowane lokaci,
ba zai ruɓa ba.
Domin ya ga mutane masu hikima sun mutu,
wawaye da marasa hankali sun halaka gaba ɗaya,
sun bar wa waɗansu dukiyarsu.
Tunaninsu na zuciyatasu kam
shi ne gidajensu su tabbata har abada,
mazaunansu kuma su tabbata
cikin dukkan zamanai.
Suna sa wa ƙasashensu sunayensu.
Amma mutum ba ya zama a cikin daraja,
kamar dabba mai halaka ya ke.
Wannan hanya tasu ita ce wautarsu
amma kuwa mutane su na yarda da maganganunsu.
An ƙaddara su ne kamar garken Mahalaka;
Mutuwa ce za ta zama mai kiwonsu.
Masu gaskiya su za su mallake su da safe.
Ƙyansu zai zama na Mahalaka ne don ta cinye su,
don kada su sami wurin zama.
Amma Allah zai ceci raina daga ikon Mahalaka,
domin zai karɓe ni.
Kada ka ji tsoro in an arzuta wani,
in an ƙara ɗaukakar gidansa.
Domin in ya mutu ba zai ɗauki komai ya tafi da shi ba.
Ɗaukakarsa ba za ta tafi kabari tare da shi ba.
Ko da ya ke sa'ad da ya ke raye ya sa wa kansa albarka,
mutane kuma sun yaba maka sa'ad da ka kyantata wa kanka,
zai je wurin kakanninsa,
ba za su ga haske ba har abada.
Mutumin da ke da daraja/ ɗaukaka/, amma bai gane ba,
kamar dabbobi masu halaka ya ke.
50
Allah, wato Ubangiji, ya yi magana, ya kirayi duniya
tun daga hudowar rana har ya zuwa faɗuwatata.
Tabbatar kyau, daga cikin Sihiyona,
Allah ya haskako.
Allahmmu zai zo, ba zai yi shiru ba.
Wuta za ta riƙa ci a gabansa,
za ta kuwa ruruta ƙwarai kewaye da shi.
Zai yi kiran sama da ƙasa,
don ya yi wa mutanensa shari'a.
"Ku tataro mini tsarkakena,
wato waɗanda suka yi mini alkawari ta hadaya."
Sarkin sama kuwa zai bayyana gaskiyatasa,
domin Allah shi da kansa alkali ne.
"Ku saurara, ya ku mutanena,
zan yi magana;
ya ku Bani Isra'ila,
zan yi shaida gare ku.
Ni ne Allah, wato Allahnku.
Ba zan tsawata muku ba saboda hadayoyinku;
ƙonannun baikonku koyaushe suna gabana.
Ba zan ɗauki sa a gidanku ba,
ko kuwa bunsuru a garkenku.
Domin kowace dabba ta jeji tawa ce,
da shanun da ke kan dubban duwatsu.
Na san dukkan tsuntsayen duwatsu,
dabbobin daji kuma duk nawa ne.
Da ina jin yunwa, da ba zan gaya maka ba,
domin duniya da kayanta duka nawa ne.
Zan ci naman bajimai ne,
ko kuwa in sha jinin awaki?
Ka miƙa wa Allah hadayar godiya gare shi,
ka yi kafararka ga Mafi Ɗaukaka.
Ka kira sunana a lokacin wahala;
zan cece ka, za ka kuma ɗaukaka ni.
Amma Allah ya kan ce da mugu,
"Me ka ke yi na shaidad da dokokina,
ka yi na'am da alkawarina kuwa?
Da na ga ka ƙi umarni,
ka jefad da maganata.
Sa'ad da ka ga ɓarawo,
ka yarda da shi,
ka kuma zama mai taimakon fasikanci/ shiga cikin fasikai.
Ka sallama bakinka ga faɗar mugunta,
harshenka/ bakinka/ kuwa na faɗar yaudara.
Ka kan zauna kana cin naman ɗan'uwanka,
kana zagin cikin umanka [?].
Ka yi waɗannan abubuwa, na yi shiru;
kana zaton ni ma kamarka na ke sosai da sosai.
Amma zan tsawata maka,
in sanya su a gaban idanunka.
To, yanzu ku dubi wannan,
ku da kuka mance da Allah,
kada in yayyage ku,
a rasa waɗanda za a kuɓutar.
Duk wanda ya ba da hadayar godiya gare ni
yā ɗaukaka ni ke nan.
Wanda kuwa ya yi magantasa dai dai
sai in nuna masa ceton Allah."
51
Ya Allah, ka ji tausayina
bisa ga alherinka na ƙauna,
bisa ga yawan tattausan alherinka,
ka shafe laifuffukana.
Ka wanke ni sarai daga miyagun ayyukana,
ka kuma tsarkake ni daga zunubina.
Domin na shaida ina da laifuffuka,
zunubina kuma har abada yana tare da ni.
Na yi maka zunubi, kai kaɗai,
na yi abin da ke mummuna a idonka,
don in ka yi magana,
magnarka ta zama gaskiya
in kuwa ka yi hukunci, hukuncinka ya zama daidai.
Ga shi, an siffanta ni a cikin mugun aiki;
a cikin zunubi ne ma uwata ta yi cikina.
Ga shi, kana son gaskiya ta ciki,
ta ciki kuma za ka sanad da ni hikima.
Ka wanke cikina da ruwan soso,
sai in tsarkaka;
ka wanke ni, sai in fi alli fari.
Ka sa in ji farinciki da murna,
don ƙasusuwan da ka karya su yi farinciki.
Ka kau da kanka daga zunubaina,
ka kuma shafe dukkan miyagun ayyukana.
Ka halitta mini zuciya mai tsafta, ya Allah,
ka sabunta ruhu madaidaici a gare ni.
Kada ka fid da ni daga cikin zatinka,
kada kuwa ka ɗauke ruhunka tsattsarka daga gare ni.
Ka mayar mini da murnar cetonka,
ka kuma tallafe ni da 'yantaccen ruhu.
A sa'an nan ne zan koya wa masu laifi hanyoyinka,
za a kuma juyo da masu zunubi gare ka.
Ka kuɓutad da ni daga laifin hakkin jini, ya Allah,
Allah macecina;
bakina zai yi waƙa da ƙarfi ta gaskiyarka.
Ya Ubangiji, ka buɗe mini bakina,
bakina zai faɗi yabonka.
Domin ba ka farinciki da hadaya,
dā sai in yi ta,
ba ka murna da ƙonannen baiko.
Hadayoyin Allah ruhohi ne karyayyu;
yankakkiyar zuciya, ɓatacciya, ya Allah,
kai, ba za ka raina ba.
Ka kyautata a cikin ganin damanka mai kyau ga Sihiyona;
kă kina ganuwar Urushalima,
a sa'an nan ne za ka yi murna da hadayoyin aikin gaskiya
da ƙonannun baiko da kuma ƙonannun hadayoyi.
A sa'an nan ne za su yi hadayar shanu a kan wurin yi maka baiko.
52
Dom me ka ke alfahari game ga fitina kai da kanka,
ya kai gawurtaccen mutum?
Ai rahamar Allah tana nan koyaushe.
Bakinka na ƙaga ainihin mugunta,
kamar kakkaifar aska, yana aikata a asirce.
Ka fi son mugunta a kan gaskiya,
da kuma yin ƙarya a kan gaskiya.
Kana son dukkan kalmomi na ɓarna
a bakinka na yaudara.
Haka Allah zai halaka ka har abada;
zai ɗauke ka, ya fid da kai/ cire ka/ daga gidanka;
ya tumɓuke ka daga ƙasar rayayyu.
Mai gaskiya ma zai gan shi,
ya kuma ji tsoro;
zai kuma yi masa dariya, yă ce,
"Ga shi wannan shi ne mutumin
da bai mai da Allah shi na ƙarfinsa ba,
sai dai ya ba da gaskiya ga yawan arzikinsa,
ya kuma ƙarfafa kansa da mugunta tasa.
Amma ni kam kamar ɗanyar bishiyar zaitun na ke a gidan Allah.
Na amince da rahamar Allah har abada abadin.
Zan gode maka har abada
domin ka yi shi.
Zan kuma yi dako da sunaka,
domin kyakkyawa ne, a gaban tarkakanka.
53
Wawa ya ce a zuciyatasa
"Babu Allah."
Waɗannan ɓatattu ne, sun kuwa yi mugun abin ƙyama;
ba wani mai yin kyakkyawan abu.
Allah ya dubo 'yan'adam daga sama
don yă ga ko akwai masu fahinta,
waɗanda suka nemi Allah.
Kowane ɗayansu ya koma da baya;
duk sun zama ƙazamai gaba ɗaya;
ba wani mai yin kyakkyawan abu,
a'a, ko ɗaya babu.
Masu aikata mugunta ba su da sani ne?
Masu cinye mutanena kamar suna cin burodi,
ba sa kuwa kiran Allah.
Ga su nan a cikin babban tsoro,
inda ma ba tsoro.
Domin Allah ya warwatsa ƙasusuwan wanda ya ke gaba da kai,
zai sa su kunya, domin Allah ya ƙi su.
Ina ma a ce ceton Bani Isra'ila daga Sihiyona zai fito?
Sa'ad da Allah ya maido da mutanensa daga bauta,
a sa'an nan ne Bani Isra'ila za su yi murna, su yi farinciki.
54
Ya Allah, ka cece ni da sunanka,
ka yi mini shari'a da ikonka.
Ka ji addu'ata, ya Allah,
ka kasa kunne ga maganata.
Domin baƙi sun tasam mini,
mafaɗata kuma sun nemi raina;
Ba su sa Allah a gabansu ba.
Ga shi, Allah shi ne mai taimakona;
Ubangiji na waɗanda suka tallafi raina ne.
Zai rama muguntar magabtana;
ka hallaka su ta hanyar gaskiya.
Zan yi maka hadaya da yarda zuciya ɗaya;
zan yi godiya ga sunanka, ya Ubangiji,
domin kyakkyawa ne.
Domin ya cece ni daga dukkan wahala,
idona kuma ya ga burina a kan magabtana.
55
Ka kasa kunne ga addu'ata, ya Allah;
kada ka kau da kai ga addu'ata.
Ka karkato gare ni, ka amsa mini;
ba na hutawa da ƙarata, da guranina.
Saboda muryar abokan gaba,
saboda tsananin miyago,
domin sun jefo min mugun abu,
suna kuma tsananta mini cikin hushi.
Zuciyata tana raɗaɗi ƙwarari a cikina,
abin tsoro na mutuwa ya faɗo mini.
Tsoro da rawar jiki sun sauko mini,
masifa ta tsorata ni.
Sai na ce, "Ina ma a ce ina da fukafukai kamar kurciya,
da sai in tashi in je in huta.
Ga shi, da sai in tafi nesa,
da sai in sauka a jeji.
Sai in hanzarta in ɓuya
daga iskar hadari.
Ya Ubangiji, ka hallaka harshensu,
ka raba shi,
domin na ga tashin hankali
da ruɗu cikin birnin.
Dare da rana suna ta zaga shi ta kan ganuwa;
mugunta da fitina ma suna tsakansa,
mugunta tana tsakansa;
zalumci da yaudara
ba su rabu da hanyoyinta ba.
Domin ba magabtan da suka zage ni ba ne,
da sai in daure.
Ba kuwa shi ne ya ƙi ni ba, wanda ya ɗaukaka kansa bisana;
da sai in ɓoyar masa.
Amma kai ne, mutumin da ke daidai da ni,
abokin harkata, abokina da muka saba.
Mun yi shawarwari masu kyau tare,
mun zazzaga a cikin gidan Allah tare da jama'a.
Bari mutuwa ta zaike musu gaba ɗaya,
su faɗa rami suna raye,
domin mugunta tana gidansu, a tsakansu.
Ni kam, Allah zan kira,
Ubangiji kuwa zai kuɓutad da ni.
Safe da yamma da kuma tsakar rana
zan yi ƙara, in yi gurnani,
zai kuwa ji muryata.
Ya ceci raina da aminci
daga yaƙin nan da aka ɗaura a kaina,
domin suna da yawa masu fama da ni.
Allah zai ji, ya amsa musu,
wato shi da ke nan tun zamanin da;
mutanen da ba su canza ba,
ba sa kuma tsoron Allah.
Ya miƙa hannayensa kan waɗanda suka amince masa.
Ya saɓa alkawarinsa.
Bakins melmel kamar gishiri,
amma zuciyatasa muguwa ce;
maganarsa ta fi mai laushi,
amma kuwa zararren takobi ne.
Ku jibga wa Ubangiji kayanku,
zai kuwa tallafe ku.
Har abada ba zai bar
mai gaskiya ya raurawa ba.
Amma kai, ya Allah,
za ka kai su ga ramin halaka;
masu son kisan kai da masu yaudara
ba za su rayu rabin kwanakinsu ba.
Amma ni zan amince da kai.
56
Ka j tausayi na, ya Allah,
domin mutum zai haɗiye ni;
wuni zubut yana faɗa yana matsa mini.
Magabtana za su haɗiye ni wuni zubut,
domin masu yin faɗa da ni a cikin halin alfarma suna da yawa.
Duk lokacin da na ke jin tsoro
zan amince da kai.
Game da Allah, zan yi yabon maganatasa,
da Allah na amince; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum/ ɗan'adam/ zai yi mini?
Wuni zubut suna juya maganata;
dukkan tunaninsu a kan su cuce ni ne.
Suna taruwa, suna ɓuya,
suna lura da inda na ke tafiya;
wato kamar yadda su ke jiran kisana.
Ta mugun aiki a su tsira?
Ka ka da mutanen nan da hushi, ya Allah.
Kai ne za ka faɗi yawace-yawacena;
ka zuba hawayena a cikin kwalbarka.
Ashe, ba a cikin littafinka su ke ba?
Sa'an nan magabtana za su juya
a ranad da na yi kira.
Ta haka na san Allah nawa ne.
Gama da Allah zan yabi maganarsa;
game da Allah zan yabi maganarsa.
Ga Allah na sanya yardata, ba an ji tsoro ba.
Me mutum mai iya yi mini?
Ƙafarka tana kaina, ya Allah;
zan ba da baikon godiya gare ka.
Domin ka ceci raina daga mutuwa;
ba kai ne ka hana ni faɗua ba
don in yi tafiya a gaban Allah/ don in bi hanyoyin Allah
a cikin hasken rayayye?
57
Ka ji tausayina, ya Ubangiji, ka ji tausayina,
domin gare ka na ka fakewa;
lalle a ƙarƙashin inuwar fukafukanka zan fake,
har bala'in nan ya wuce.
Zan yi wa Allah Mafi Ɗaukaka kuka,
ga Allah mai yi mini komai.
Zai aiko daga sama a cece ni,
sa'ad da mai haɗiye ni ya husata.
Allah zai aiko da rahamarsa da gaskiyatasa.
Raina na cikin zakoki.
Ina kwance a cikin waɗanda aka kunna wa wuta wato 'yan'adam,
waɗanda haƙoransu masu ne, kuma kiban ne,
harshensu kuma kakkaifan takobi.
Ɗaukaka tā tabbata gare ka
can birbishin sammai, ya Allah.
Ɗaukakarka ta kasance
a birbishin dukkan duniya.
Sun shirya mini tarko;
raina har ya sunkuya.
Sun tona mini rami;
su da kansu kuwa sun faɗa ciki.
Zuciyata ta kafu, ya Allah,
zuciyata ta kafu.
Zan yi waƙa, lalle zan yi waƙar yabo.
Farka ɗaukakata,
farka, garaya da molo.
Ni da kaina ma zan farka da wuri.
Zan gode maka a cikin mutane, ya Ubangiji;
zan yi maka waƙar yabo a cikin al'ummai.
Domin rahamarka ga sammai tana da yawa,
da gaskiyarka kuma ga sararin sama.
Ɗaukaka ta tabbata gare ka can birbishin sammai, ya Allah.
Ɗaukakarka ta tabbata a duniya duka.
58
Kuna kuwa yim maganar gaskiya cikin halin shiru?
Kuna hukuncin gaskiya kuwa, ya ku bil'adam?
Kai, a zuci dai aikin mugunta ku ke yi,
ku dubi dai mugun aikin da kuka yi a duniya.
Miyagu wararru ne tun daga mahaifa,
su kan bauɗe da zarar an haife su.
Dafinsu kamar dafin maciji ne,
kamar kurmar kububuwa su ke,
wadda ta ke toshe kunnenta,
wadda ba ta sauraron muryar masu magani,
magani ba ya mata komai.
Ya Allah, ka karya haƙoransu a cikin bakinsu;
Ya Ubangiji, ka karye manyan haƙoran kwikwiyon zaki.
Su narke, kamar ruwa mai gudana;
sa'ad da ya auna kibansa, su zama kamar an yanke su.
Su zama kamar dodon katantanwa
wanda ke narkewa, ya shuɗe;
kamar ɓarin mace, ɗan da bai ga rana ba.
Kafin tukwanenku su ji ƙayoyin,
zai ɗebe su da guguwa,
da ɗanya na mai cin wutar duka.
Mai gaskiya zai yi farinciki in ya ga ramuwar;
zai wanke ƙafafunsa da jinin mugu.
Har ma mutane za su ce,
"Hakika ga ladan mai gaskiya;
hakika ga Allahn da ke shari'a a duniya."
59
Ka cece ni daga abokan gabana, ya Ubangiji/ Allah[?],
ka ɗora ni a kan masu tasam mini.
Ka cece ni daga masu aikata mugunta,
ka kuɓutad da ni daga masu son kisan kai.
Domin ga shi suna fakona su kashe ni;
masu ƙarfi sun taru a kaina.
Ba don laifina ko zunubina ba, ya Ubangiji.
Suna gudu suna shiryawa, ba tare da laifina ba.
Ka tashi, ka taimake ni, ka kuma duba.
Wato kai, ya Ubangiji Allah mai runduna, Allahn Bani Isra'ila.
Ka tashi, ka ziyarci dukkan majusu;
kada ka ji tausayin kowane mugun mai laifi.
Sun dawo da yamma,
suna haushi kamar kare,
suna zazzaga birnin.
Ga shi, suna gatsa da bakinsu,
takuba na baikinsu,
domin sun ce, "Wa ke ji?"
Amma, ya Ubangiji, kai kam za ka yi musu dariya;
za ka sa a yi wa majusu ba'a.
Ya ƙarfina, zan dakata a gare ka;
domin Allah shi ne hasumayata.
Allah mai tausayina zai hana ni;
Allah zai sa in ga cikar burina a kan abokan gabana.
Kada ka kashe su,
don kada mutanenan su mance;
ka warwatsa su da ƙarfinka,
ka sauko da su,
ya Ubangiji garkuwarmu.
Saboda zunubin bakinsu da magnarsu,
bari alfarmarsu ta sa a tafi da su,
saboda kuma zage-zage da ƙarairayi da suka yi.
Ka hallaka su da hushi,
ka hallaka su, don kada su wanzu,
bari su san Allah ne da iko da gidan Yakubu
har ƙarshen duniya.
Da maraice kuma ka bari su dawo,
bari su yi ta haushi kamar kare,
su riƙa zazzagawa a cikin birni.
Za su riƙa kaiwa, suna kawowa don neman abinci,
har su kwana dare farai im ba su wadata ba.
Amma ni zan yi waƙar ƙarfinka ne;
lalle zan yi waƙar rahamarka da ƙarfi da safe.
Domin kai ne hasumayata
kuma matsera a ranar ɓacin raina.
Gare ka zan yi waƙoƙin yabo, ya ƙarfina,
domin Allah shi ne hasumyata,
Allah mai tausayina.
60
Ya Allah, kā jefad da mu,
kā ka da mu;
ka yi hushi;
ka mai da mu gurbimmu mana.
Ka sa ƙasa ta raurawa,
ka tsage ta;
ka warkad da miyakunta
domin tana girgiza.
Ka nuna wa mutanenka abubuwa masu wuya;
ka sa mun sha giya mai sa tamɓela/ magagi.
Ka ba masu tsoronka tuta,
don a kafa ta saboda gaskiya.
Don a kuɓutad da ƙaunataccenka,
ka yi ceto da hannunka na dama,
ka amsa mana.
Allah ya yi magana a cikin tsarkakatasa,
ya ce "Zan yi matuƙar farinciki, zan raba Shechem
in kuma raba iyakar kwarin Sakkwato.
Gilad nawa ne, Manassaha kuma nawa ne;
Afraimu ma karewata ce;
Yahuda sandan sarautata ne.
Muwaba tukunyata ce;
Iduma kuwa a kansa zan tuɓe takalma;
Filistia ki yi kururuwa saboda ni.
Wa zai kawo ni ƙaƙƙarfan gari?
Wa zai kai ni Iduma?
Ashe, ya Allah, ba ka yashe mu ba?
Ba ka ma'amala da rundunarmu, ya Allah.
Ka taimake mu a kan magabta,
domin taimakon mutum banza ne.
Game da Allah za mu yi jarumtaka,
domin shi ne zai tattake magabtammu.
61
Ka ji kukana, ya Allah,
ka kula da addu'ata.
Zan yi kiranka daga ƙarshen duniya,
in zuciyata ta firgita.
Ka kai ni
dutsen da ya fi ni tsawo.
Domin kai ne matserata,
ƙaƙƙarfar hasumaya ta tsere wa magabta.
Zan zauna cikin majami'arka har abada.
Zan fake a ƙarƙashin fukafukanka.
Domin ka ji kafarata, ya Allah.
Ka ba ni gadon masu jin tsoron sunanka.
Za ka tsawaita ran sarki;
shekarunsa za su zama kamar zamanai masu yawa.
Zai zauna a gaban Allah har abada;
ka shirya alherin ƙauna da gaskiya don su kiyaye shi.
Haka zan yi waƙar yabon suanaka hara abada,
don kullum in cika wa'adinka.
62
Raina ga Allah kaɗai ya ke;
daga gare shi cetona zai zo.
Shi ne kaɗai dutsena, kuma macecina;
shi ne hasumayata,
ba zan jijjiga ƙwarai ba.
Ina iya tsawon lokacin da za ku yi haƙon mutum
don ku kashe shi, dukkanku,
kamar kagon da ya karkata,
kamar shingar da ya kishingiɗa.
Suna shawar ka da shi ne daga fifikonsa kaɗai.
Suna jin daɗin yin ƙarairai.
Suna sa albarka/ Suna yabo/ a zahiri,
amma a baɗini zai/ la'anarwa/ su ke yi.
Ya kai raina, ga Allah kaɗai za ka tsaye,
domin sazuciyata a gare shi ta ke.
Shi ne kaɗai dutsena, kuma macecina;
shi ne hasumayata, ba zan jijjiga ba.
Kuɓutata da ɗaukakata suna ga Allah;
dutsen ƙarfina, matserata na ga Allah.
Ya ku mutane, kowane lokaci ku ba da gaskiya gare shi;
ku sa masa zuciyarku.
Allah matserarmu ne.
Hakika mutane ƙasƙantattu banza ne,
ɗaukakakku kuwa ƙarya ne;
za su hau a wurin awu da mizani;
dukansu sun kasa banza nauyi.
Kada ka ba da gaskiya ga zalumci,
kada kuma ka zama mutumin banza wajen fashi/ sata.
In dukiya ta ƙaru,
kada ka ɗora zuciyarka a kai.
Allah ya yi magana sau ɗaya;
sau biyu ke nan na ji wannan;
ikon nan na Allah ne.
Gare ka kuma, ya Ubangiji, rahama ta ke,
domin ka kan saka wa kowa
gwargwadon aikinsa.
63
Ya Allah, kai ne Allahna;
da wuri zan nem ka;
raina na nemanka,
jikina da ɗokin ganinka
a ƙaiƙassasshiyar ƙasa mai sa gajiya,
inda ba ruwa.
Saboda haka na zuba ido gare ka a tsattsarkan wuri
don in ga ikonka da ɗaukakarka.
Domin alherinka na ƙauna ya fi rai,
bakina zai yabe ka.
Saboda haka zan yabe ka muddar ina raye;
zan ɗaga hannayena da sunanka.
Raina zai ƙoshi kamar da ɓargo da kitse;
bakina kuwa zai yabe ka yana mai farinciki.
Idan na tuna ka a kan gadona,
ina tunaninka a cikin lokatan dare,
domin ka zama mataimakina,
zan kuwa yi farinciki a cikin inuwar fukafukanka.
Raina na binka ƙwarai;
hannunka na dama ne ya tallafe ni.
Amma masu neman raina su hallaka shi,
za su gangara can rami mafi zurfi na duniya.
Za a kallafa su ga ikon takobi,
za su zama rabon yanyawa.
Amma sarkin zai yi farinciki da Allah;
duk wanda ya rantse da shi zai sami ɗaukaka,
domin za a toshe bakin maƙaryata.
64
Ya Allah, ka ji muryata mana ta ƙarata;
ka kiyaye raina daga tsoron magabta.
Ka ɓoye ni daga shawar asiri ta miyagu,
da hargitsin masu aikata mugun abu;
waɗanda suka wasa harshensu kamar takobi,
suka kuma ɗana kibansu, wato ɗaɗɗatar magana,
don su harbi kamili daga wurin ɓuya;
farat ɗaya za su harbe shi,
ba sa jin tsoro.
Suna ƙarfafa wa kansu gwiwa don yin muguwar niyya;
suna shawarar ɗana tarko a asirce.
Suna cewa, "Wa zai ga tarkon?"
Suna neman mutunta, suna cewa,
"Mun gama nema ƙas da bis."
Tunanin kowa da zuciyatasa kuwa zuzzurfa ne.
Amma Allah zai harbe su;
za a yi musu rauni da kibiya farat ɗaya.
Ta haka za a sa su yi tuntuɓe,
bakinsu ma sai ya saɓa musu.
Duk waɗanda suka gan su
sai sun kaɗa ki.
Dukkan mutane kuwa za su ji tsoro;
za su bayyana ayyukan Allah,
za su lura da abin da ya ke yi, a cikin azanci.
Mai gaskiya zai yi farinciki ga Ubangiji,
yă kuma dogara gare shi.
Dukkan masu gaskiya a zuci kuwa
za su sami ɗaukaka.
65
Yabo na dakonka,
ya Allah na cikin Sihiyona;
gare ka wa'adi zai cika.
Ya kai mai jin addu'a,
gare ka duk halitta za ta zo.
Mugunta ta ci nasara da ni.
Laifuffukammu kam
za ka wanke su.
Albarka ta tabbata ga wanda ka zaɓa,
ka sa ya doshe ka,
don ya zauna a majalisarka.
Za mu wadatu da kyawawan abubuwan da ke gidanka,
tsattarkan wurin na ɗakin yi maka sujada.
Za ka amsa mana da gaskiya ta abubuwan ban tsoro,
ya Allah macecimmu,
kai da ka ke madogarar dukkan kusurwowin duniya,
da kuma waɗanda ke can nesa a cikin bahar,
wanda ka kakkafa duwatsu da ƙarfinka,
ka ɗamaru da ƙarfi;
kai da ka ke kwantad da haukar teku,
haukar igawun ruwa,
da kuma boren mutane.
Waɗanda ke zaune a wurare masu nisa ma
suna tsoron alamominka;
kai ka ke sa fitar safiya da ta maraice
su yi farinciki.
Ka ziyarci duniya, ka shayad da ita ruwa,
ka arzuta ta ƙwarai;
kogin Allah cike ya ke da ruwa;
ka wadata su da hatsi
sa'ad da ka shirya duniya.
Ka shayad da ƙunyakenta da gaske,
ka ta da kunyakenta,
ka tausasa su da ruwan sama,
ka yi wa ƙoramanta albarka.
Ka naɗa shekara da alherinka,
hanyoyinka kuma suna ba da amfani.
Suna faɗuwa kan ciyawar jeji;
duwatsu kuma ana lulluɓe su da murna/ farinciki.
Ana yi wa sararin kiwo ado da dabbobi,
kwarurruka kuma an rufe su da shuka,
suna tada murya don farinciki, su ma suna waƙa.
66
Ke duniya duka, ki ta da murya da farinciki ga Allah.
Ki yi waƙar ɗaukakar sunansa;
ki mai da yabonsa mai ɗaukaka.
Ki ce da Allah, "Kai! ayyukanka da bantsoro su ke!
Ta ƙarfin ikonka ne magabtanka za su miƙa wuya gare ka.
Dukkan duniya za ta bauta maka,
za ta kuma yi maka waƙa,
za su yi waƙar yabon sunanka."
Ku zo ku ga ayyukan Allah;
shi abin tsoro ne a cikin ayyukansa game da 'yan'adam.
Ya mai da teku busasshiyar ƙasa;
sun bi ta cikin kogi da ƙafa.
A nan ne muka yi farinciki da shi.
Yana sarauta da ƙarfin iko har abada;
idanunsa na ganin al'ummai.
Kada masu fitina su ɗaukaka kansu.
Ku yabi Allahmmu, ya ku mutane,
ku sa a ji muryar yabonsa,
wanda ya ke riƙe da rayukammu,
ba ya kuwa bari a kan da ƙafafuwammu.
Domin kai, ya Allah, ka gwada mu;
ka jarraba mu kamar yadda aka jarraba azurfa.
Ka ɗebo mu a cikin koma,
ku ɗora mana kaya mai nauyi a kunumimmu.
Ka sanya mutane su hau kammu,
mun bi ta cikin wuta da ruwa;
amma ka fid da mu wurin arziki.
Zan zo gidanka da ƙonannen baiko;
zan cika maka wa'adodina
waɗanda na faɗa da bakina,
sa'ad da na ke cikin ɓacin rai.
Zan yi maka ƙonannun hadaya na 'yan bana ɗaya,
da ƙamshin raguna;
zan yi hadayar bajimai da awaki.
Ku zo ku ji, ku da ku ke tsoron Allah,
zan faɗi abin da ya yi mini.
Na yi masa kuka da bakina,
na kuma yabe shi da harshena.
In na nufi mugunta a zuciyata,
Ubangiji ba zai ji ba.
Amma kuwa Allah ya ji sosai;
ya saurari muryata ta addu'a.
Yabo ya tabbata ga Allah,
wanda bai kore addu'ata ba
ko kuwa rahamarsa a gare ni.
67
Allah na jin tausayimu, yana yi mana albarka,
yana sa fuskarsa ta haskaka mu,
don a san hanyoyinka a duniya,
wato lafiyan nan taka ta ceto,
a cikin dukkan al'ummai.
Bari mutane su yabe ka, ya Allah;
bari mutane su yabe ka.
Bari al'ummai su yi farinciki,
su yi waƙa don murna;
domin za ka yi wa mutane shari'a da gaskiya,
ka kuma yi mulkin al'ummai a duniya.
Bari mutane su yabe ka, ya Allah;
bari mutane su yabe ka.
Ƙasa ta ba da amfaninta;
Allah, wato Allahmmu, zai yi mana albarka.
Allah zai yi mana albarka;
har ƙarshen duniya kuma za su tsorace shi.
68
Bari Allah ya tashi;
bari magabtansa su watse/ bari a watsa magabtansa;
bari maƙiyansa kuma su gudu/ su ba shi ƙeya.
Ka kore su kamar yadda aka korar hayaƙi,
kamar yadda kakin zuma ke narkewa a gaban wuta,
ta haka ka sa miyagu su halaka a gaban Zatin Allah.
Amma bari masu gaskiya su yi murna,
su ɗaukaka a gaban Allah;
kai, bari da su yi farinciki saboda jin daɗi/ murna.
Ku yi wa Allah waƙa,
ku yi wa sunansa waƙoƙin yabo;
ku shirya wa mai tafiya a cikin hamada babbar hanya;
sunansa YAH, ku sami ɗaukaka game da sunansa.
Shi ne uban marayu,
kuma alkalin matan da mazansu suka mutu,
Allah ne a tsattsarkan mazuninsa.
Allah ya kan sanya mai kaɗaitaka a cikin dangogi;
ya kan arzuta ɗaurarru;
amma masu tawaye su kan zauna a ƙonanniyar ƙasa.
Ya Allah, sa'ad da ka wuce gaban mutanenka,
sa'ad da ka bi ta cikin jeji,
sai ƙasa ta raurawa,
sama kuma ta faɗi a gaban Zatin Allah;
har dutsen Sinina ma ya raurawa
a gaban Zatin Allah, Allahn Bani Isra'ila.
Ya Allah, kai ne ka aiko da ruwa mai yawa;
kai ne ka tabbatad da gādonka
lokacin da ya tsananta.
Jama'arka suka zauna a nan.
Kai ne, ya Allah, ka shirya wa gajiyayyu kyawawan ayyukanka.
Ubangiji ya faɗi maganar;
matan da ke baza labaran babbar runduna ce.
Sarakuna masu runduna suna gudu; suna gudu.
Ita kuwa da ta ke zauna a gida tana cin ganimar.
Za ka zauna a cikin garken tumaki ne,
kamar fukafukan kurciya da aka rufe da azurfa,
ɗeshinsu kuma da zinarya?
Sa'ad da Mai Iko ya warwatsa sarakuna a can,
sai ya zamana kamar an yi ƙanƙara ne a Zalman.
Dutsen Allah shi ne dutsen Bashan;
dutsen Bashan kuwa dogo ne.
Ku dogayen duwatsu, don me ku ke hararan,
dutsen da Allah ya nufa ya zama gidansa?
Hakika Ubangiji zai zauna a cikinsa/ kansa/ har abada.
Karusan Allah dubu ishirin ne,
wato dubbai a kan dubbai,
Ubangiji na cikinsu kamar a Sinina a tsattsarkan wuri.
Ka hau sama,
kana jan kamammunka a kame;
ka karɓi kyauta iri iri a cikin mutane,
har ma a cikin masu tawaye,
don Ubangiji Allah ya zauna tare da su.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji
wanda ya ke ɗauke da nauyimmu kullum;
wato Allah macecimmu.
Allah, Allahn ceto ne a gare mu,
kuma ga Ubangiji Allah ne sha'anin mutuwa ya ke.
Amma Allah zai buge kan magabtansa,
da buzurwan kambin nan
da mai ci gaba da muguntatasa har yansu.
Ubangiji ya ce,
"Zan sake kawowa daga Bashan,
zan sake kawo su daga zurfin teku,
don ka tsoma ƙafarka a cikin jini,
don karnukanka su sami rabunsu a wurin abokan gabanka."
Sun ga hanyoyinka, ya Allah,
wato hanyoyin Allahna,
sarkina a wuri tsattsarka.
Mawaƙa sun wuce gaba,
masu bushe-bushe sun bi baya,
suna tsakan 'yam mata
suna kaɗa tambari.
"Yabo ya tabbata ga Allah a cikin jama'a,
wato Ubangiji, kai da ke daga cikin Bani Isra'ila."
Ƙaramin Bunyhamunu na nan, sarkinsu,
sarakunan Yahuda da majalisarsu,
da sarakunan Zebulun da na Naftali.
Allahnka shi ne ya ƙaddara ƙarfinka,
ya Allah, ka ƙarfafa abin nan da ka ƙaddaro mana.
Saboda ɗakin yi maka sujada na Urushalima
sarakuna za su kawo maka kyauta.
Ka tsawatawa dabbar jeji ta cikin yama,
da taron bajimai da maruƙan mutane.
Suna tattake azurfa;
ya warwatsa mutanen da ke farinciki da yin yaƙi.
Sarakuna za su fito daga ƙasar Masar;
ƙasar Habasha za ta yi hanzarin miƙe hannayenta ga Ubangiji.
Ku yi wa Allah waƙa, ya ku masarautun duniya;
ku yi waƙoƙin yabo ga Ubangiji.
Ga wanda ke hawa can birbishin sama, daɗaɗɗiya;
ga shi yana magana,
muryatasa kuwa babba ce.
Ku bar wa Allah ƙarfin iko,
fifikonsa na ga Bani Isra'ila,
ƙarfinsa kuma na kan sammai.
Ya Allah, kai abin tsoro ne
im ba a cikin tsarkakan wurarenka,
Allahn Bani Israila na ba mutanensa iko da ƙarfi.
Yabo ya tabata ga Allah.
69
Ya Allah, ka cece ni,
domin ruwa ya ci ni.
Na nutse cikin taɓo mai zurfi,
inda ba damar tsayawa;
na shiga ruwa mai zurfi,
inda ya sha kaina.
Na gaji da kukana;
maƙogwarona ya bushe.
Idanuna sun gaza
sa'ad da na ke dakon Allahna.
Masu ƙi na ba dalili
sun fi gashin kaina yawa;
masu son yanke ni, suna magabtana
a karin banza, masu ƙarfi ne.
Sai na mai da abin da ban ɗauka ba.
Ya Allah, ka san wautata;
zunubaina kuwa ba a ɓoye su ke gare ka ba.
Kada masu dakonka su ji kunya ta kaina,
Ya Allah Ubangiljin runduna;
kada masu nemanka su wulakantu ta kaina,
ya Allahn Bani Isra'ila.
Domin saboda kai na ɗauki zagi,
kunya ta rufe ni.
Na zama baƙo ga 'yan'uwana,
bare kuma ga cikin umomina.
Domin kishin ɗakinka ya ci raina;
mugun aikin masu nunana maka ya jibgu a kaina.
Sa'ad da na yi kuka
na tsarkake zuciyata da hana kaina abinci,
wannan mugun abu ne gare ni.
Sa'ad da na mai da tufafina tsummoki,
sai na zame musu karin magana.
Masu zama a bakin ƙofa suna maganata,
na kuma zama abin waƙar mashaya.
Amma ni kam, addu'ata ta ne gare ka, ya Ubangiji.
A lokaci mai karɓuwa, ya Allah,
a lokacin rahamarka,
ka mayar mini da jawabi
a gaskiyar cetonka.
Ka cece ni daga laka,
kada ka bar ni in nutse;
in kuɓuta daga maƙiyana
da kuma zuzzurfan ruwa.
Kada amalalo ya birkita ni,
kada kuma teku ya haɗiye ni,
kada kuma rami ya rufe da/ rubza/ ni.
Ka amsa mini, ya Ubangiji,
saboda alherinka na ƙauna mai kyau ne;
ka juyo bisa ga yawan tattausan alherinka.
Kada ka juya wa bawanka baya;
domin ina cikin baƙinciki, ka amsa mini da sauri.
Ka kusato ni, ka ceci raina,
ka cece ni saboda magabtana
Ka san wahalata,
da kunyata da wulakancina;
magabtana duka na gabanka.
Wahala ta karya mini gaba,
duk zuciyata ta yi nauyi.
Na nemi masu jin tausayi,
amma ban samu ba;
da kuma masu sanyaya zuciya,
amma ban samu ba.
Sun kuma ba ni ruwan ɗaci a kan abinci,
sun kuma ba ni ruwan tsami in sha, da na ji ƙishirwa.
Abincinsu yă zama musu tarko,
in suna zan (?) lafiya ma yă zama tarko.
Idonsu yă rufe don kada su gani;
kunkuminsu kullum yă riƙa rawa.
Ka jibga musu haushinka,
ka sa tsananin hushinka ya cim musu.
Gidajensu su zama ba kowa,
kada kowa ya zauna a gidajensu.
Domin suna tsananta wa wanda ka buge,
suna kuma ba da labarin waɗanda ka yi wa rauni.
Ka ƙara munana muguntarsu,
kada su sami gaskiyarka.
A soke su daga cikin littafin rai;
kada kuma a rubuta su tare da masu gaskiya.
Amma ni gajiyayye ne/ abin tausayi ne/ mai baƙinciki;
ya Allah, cetonka yă ɗora ni a sama.
Zan yabi sunan Allah da waƙa;
zan kuma ɗaukaka shi da godiya.
Zai farauta wa Ugangiji fiye da sa
ko takarkari mai ƙaho da kofato.
Masu tawali'u sun gan shi,
sun kuwa yi murna;
ku da ke neman Allah,
zuciyarku tă tofu.
Domin Ubangiji yana sauraron mabukata,
ba ya kuwa raina ɗaurarrunsa.
Bari sama da ƙasa su yabe shi,
da tekuna da dukkan abin da ke motsi a cikinsa.
Domin Allah zai ceci Sihiyona,
ya gina garuruwan Yahuda;
za su zauna a can su mallake su;
zuriyar bayinsa kuma za su gaje su,
masu ƙaunar sunansa kuma
za su zauna a nan.
70
Ya Allah, ka hanzarta ka cece ni,
ka hanzarta taimakona, ya Ubangiji.
Ka sa masu neman raina
su kunyata, su muzanta,
su juya ƙeya, su wulakanta,
su waɗanda ke murna da cutuwata.
Su juya saboda kunyarsu
su masu cewa "Yauwa, yauwa!"
Duk masu nemanka su yi murna,
su yi farinciki a cikin al'amarinka.
Masu ƙaunar cetonka kuwa
a kowane lokaci su riƙa cewa,
"Ɗaukaka tă tabbata ga Allah!"
Amma ni gajiyayye ne, mabukaci,
ka hamzarta mini, ya Allah.
Kai ne mataimakina, kuma mai macecina;
ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.
71
A gare ka ne, ya Ubangiji, na ke dogara;
kada in kunyata har abada.
Ka cece ni a cikin gaskiyarka,
ka kuɓutad da ni, ka cece ni.
Ka zame min dutsen da zan yi gida,
inda zan riƙa komawa in zauna koyaushe.
Ka ba da umarni don a cece ni,
domin kai ne dutsena, kuma matserata.
Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugu,
da kuma hannun marar gaskiya mugu.
Domin kai ne abin sazuciyata, ya Ubangiji Allah,
kai ne abin dogarona tun ina yaro.
Game da kai ne na zauna a cikin mahaifa;
kai ne ka fid da ni daga cikin uwata.
Yabon da zan yi a kowane lokaci naka ne.
Ni kamar abin mamaki ne ga mutane da yawa;
amma kai ne ƙaƙƙarfar madogarata.
Bakina zai cika da yabonka,
da kuma girmama ka wuni zubur.
Kada ka jefad da ni a tsufata;
kada ka yashe ni sa'ad da ƙarfina ya ƙare.
Domin magabtana suna magana game da ni;
masu duba yadda za su ɗauki raina kuwa suna shawara da juna,
suna cewa, "Ai Allah ya hashe shi;
ku farfare shi, ku kama shi,
domin ba mai ceto."
Ya Allah, kada ka yi nisa da ni;
ya Allahna, ka hanzarta taimakona.
Ka sa masu gāba da ni su kunyata, su halaka;
masu neman su ga na cutu
su muzanta su wulakantu.
Amma kowane lokaci zan sa zuciya,
zan kuma ƙara yabe ka a koyaushe.
Bakina zai ba da labarin gaskiyarka,
da kuma cetonka wuni zubur,
domin ban san yawansu ba.
Zan zo da manya manyan ayyukan Ubangiji Allah;
zan ambaci gaskiyarka, wato naka kaɗai.
Ya Allah, kai ne ka koya mini tun daga ƙuruciyata,
daga nan kuma na faɗi ayyukanka na al'ajabi.
Kai, ko sa'ad da na tsufa na yi furfura ma,
kada ka yashe ni, ya Allah,
sai na faɗa wa zamani mai zuwa batun ƙarfinka,
ƙarfinka ga kowane mai zuwa.
Gaskiyarka kuma, ya Allah, tana da girma.
Kai da ka yi manya manyan abubuwa,
ya Allah, wa ya yi kamarka?
Kai da ka nuna mana wahalu masu yawa, masu ɗaci,
kai ne za ka sake raya mu,
ka kuma fito da mu
daga zurfin ƙasa.
Ka ƙara girmama,
ka sake juyowa
ka sanyaya mini rai.
Zan kuma sake yabonka da garaya,
wato gaskiyarka, ya Allahna.
Kai zan yaba da molo,
ya kai tsattsarkan nan na Bani Isra'ila.
Zan yi murna da bakina ƙwarai
sa'ad da na yi waƙar yabonka;
da raina da ka fanso kuma.
Harshena ma zai yi maganar gaskiyarka wuni zubur;
domin masu neman cutuwata sun kunyata, sun muzanta.
72
Ka ba sarki hukumcinka, ya Allah,
gaskiyarka kuma ka ba ɗan sarki.
Zai hukumta mutanenka da gaskiya,
gajiyayyunka kuma da hukumci.
Duwatsu za su kawo wa mutane amana,
tuddai kuma gaskiya.
Zai yi wa gajiyayyu a cikin mutane shari'a,
zai ceci 'ya'yan matsattsu,
zai kuma kakkarya azzalumi.
Za su tsorace ka da rana,
da kuma dare a dukkan zamani.
Zai sauko kamar ruwan sama
a kan ciyawar da aka yi wa fitiki,
kamar ruwan saman da ke jiƙa ƙasa.
Masu gaskiya za su wadata a zamaninsa,
da yalwar aminci, sai wata ya faɗi.
Zai kuma sami ƙasa daga bahar zuwa bahar,
daga kuma kogi har ya zuwa ƙarshen duniya.
Masu zama a ckikin jeji za su musuna masa,
magabtansa kuma za su ciji ƙasa.
Sarakunan Tarshishi da na tsibirai
za su kakkawo kyauta;
sarakunan Shiba da na Saba
za su ba da kyauta.
Kai, sarakuna duka za su yi sujada a gabansa;
dukkan al'ummai za su bauta masa.
Domin zai ceci mabukaci in ya yi kuka,
da kuma gajiyayyen da ba shi da mataimaki.
Zai ji tausayin gajiyayyu da mabukata,
zai kuma ceci rayukkan mabukata.
Zai kuɓutad da su daga zalumci da tunzuri;
jininsu kuma zai zama mai kyau a gaban idanunsa.
Za su rayu,
kuma shi ne za a bai wa zinaryiyar Shiba.
Dukkan mutane za su yi masa addu'a a kowane lokaci;
za su yabe shi wuni zubur.
Hatsi zai yalwata a duniya a kan duwasu.
Amfaninta zai girgiza kamar ƙasar Libanon;
mutanen gari za su yalwata
kamar ciyawar jeji.
Sunansa zai wanzu har abada
sunansa zai wanzu kamar rana.
Za a yi wa mutane albarka game da shi,
dukkan al'ummai za su kira shi mai farinciki.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, AllahnBani Isra'ila,
wanda shi ne kaɗai mai yin abubuwan mamaki.
Yabo kuma ya tabbata ga maɗaukakin sunansa har abada;
duniya duka ta cika da ɗaukakarsa. Amin.
73
Hakika Allah ya kyauta wa Bani Isra'ila
wato ga masu tsarkakan zukata.
Amma ni kam, ƙafafuna kamar sun tafi ne;
ƙafata kamar ta goce ne.
Domin ina jin ƙyashin/ kashin/ mai girman kai,
a sa'ad da na ga arzikin mugu.
Domin babu dafi a gubarsu,
amma kuwa ƙarfinsu na nan tabbatacce.
Ba su shiga wahala ba kamar sauran mutane,
annoba kuma ba ta mamaye su kamar sauran mutane ba.
Saboda haka alfarma ta zama musu kamar sarƙa a wuyansu;
tarzoma ta rufe su kamar mayafi.
Abin da su ke da shi
har ya fi abin da zuciya za ta riya tana so.
Suna zagi, suna kuma faɗan mugunta saboda mugun halinsu.
Suna manyan maganganu.
Suna zagin sama,
harshensu kuwa na maganar ko'ina a duniya.
Saboda haka mutanensa suka komo nan,
suka kuma zub da ruwa cike da ƙoƙo.
Kuma su kan ce, "Yaya Allah ya sani?
Mafi ɗaukaka na da sani ne?"
Ga nan miyagun.Da ya ke kullum suna cikin săkewa,
sai su kan ƙaru da arziki.
Hakika a banza na tsarkake zuciyata
na kuma wanke hannuna saboda rashin laifi.
Wuni zubur ina tare da ciwo,
ana tsarkake ni kowace safiya.
Da na ce, "Haka zan yi magana,"
ai da na yi wa zuriyar 'ya'yanka ƙeta.
Da na yi tunanin yadda zan san wannan,
sai abin ya yi mini ciwo ƙwarai,
sai da na je tsattsarkan wuri na Allah
na duba ƙarshensu.
Hakika ka sanya su a wurare masu santsi,
ka jefad da su ƙasa, su halaka.
Yaya suka zama a wofince a cikin ƙiftawar ido?
Tsoro ya rufe su ɗungum.
Kamar mafarki in an farka,
haka ya Ubangiji, in ka tashi sai ka raina kamanninsu.
Domin zuciyata tana baƙinciki,
an kuwa kama ni a wuya,
na zama kamar dabba, kuma jahili,
kamar dabba na ke a gabanka.
Duk da haka kuwa koyaushe ina tare da kai;
ka kama hannuna na dama.
Kai ne za ka nushe ni gami da shawararka,
daga baya kuma ka karɓe ni ga ɗaukaka/ ka ɗaukaka ni.
Wa na ke da shi a sama in ban da kai?
Ba kuwa wani a duniya da na ke bukata im ban da kai.
Jikina da zuciyata suna gazawa,
amma Allah shi ne ƙarfin zuciyata,
da sh'anina har abada.
Domin ga shi waɗanda ke nesa da kai za su halaka;
ka halaka duk waɗanda suka bijire maka.
Amma kyakkyawan abu ne gare ni in kusanci Allah;
na mai da Ubangiji Allah matserata,
don in ba da labarin ayyukana.
74
Ya Allah, dom me ka ka yashe mu har abada?
Dom me hushinka ya jice tumakin makiyayarka?
Ka tuna da taron jama'arka
wadda ka saya tun zamanin da,
wadda ka fansa su zama kabilar gādonka,
da kuma Dutsen Sihiyona inda ka zauna.
Ka ɗaga ƙafafuwanka daga gini mai zuba kullum,
wato daga dukkan mugun abin da magabta suka yi a wuri tsattsarka.
Magabtanka sun yi ruri a tsakiyar mutanenka;
sun sanya alamominsu a kan alamoni.
Alamarsu kamar mutane ne
da suka cira gatura a kan duhun itatuwa.
Yanzu kuma suna sassare dukkan aikinsa
na sassaka da adda da guduma.
Sun kunna wa tsattsarkan wurinka wuta;
sun wulakanta mazaunin sunanka,
har sun ka da shi ƙasa.
Sun ce a zuciyarsu, "Bari mu ɓaɓɓata su gaba ɗaya";
sun ƙone dukkan majami'un Allah a ƙasar.
Ba ma ganin alamomimmu;
ba sauran wani annabi,
ba kuma wani a cikimmu wanda ya san iya tsawon lokaci.
Ina tsawon lokaci, ya Allah,
da magabta za su yi ta wulakantarna?
Magabta za su yi tasaɓon sunanka na har abada?
Dom me ka janye hannunka, wato hannunka na dama?
Ka ciro shi daga ƙirjinka, ka halaka su.
Amma kuwa Allah shi ne Sarkina na tun zamanin da,
yana ceto a tsakiyar duniya.
Kai ne ka raba teku da ƙarfinka;
kai ne ka fasa kan dodanni a cikin ruwa.
Kai ne ka fas kan dodo rugu rugu,
ka miƙa shi ya zama abincin mutanen da ke zaune a jeji.
Ka raba rafi da amalalo;
ka ƙaiƙasad da manyan koguna.
Rana taka ce, dare kuma naka ne;
kai ne ka shirya haske da kuma rana.
Kai ne ka kafa dukkan iyakokin duniya;
kai ne ka yi damana da ɗari.
Ka tuna da wannan, ya Ubangiji,
cewa magabta sun yi mugun aki,
kuma wawayen mutane sun saɓi sunanka.
Kada ka miƙa ran kurciyarka ga dabbobin jeji;
kada ka mance da ran gajiyayyenka har abada.
Ka girmama alkawari,
domin wurare masu duhu na duniya cike su ke da wuraren fitina.
Kada ka bar wanda aka zalumta ya kunyata;
bari gajiyayye da mabukaci su yabi sunanka.
Ka tashi, ya Allah, ka tsaya
kan sha'anin da ya shafe ka.
Ka tuna da yadda wawan mutum
ya ke munana maka wuni zubur.
Kada ka mance da muryar magabtanka;
hayagagar waɗanda suka tasam maka
tana haukawa a kowane lokaci.
75
Mun gode maka, ya Allah, muna godiya
domin sunanka a kusa ya ke.
Mutane suna ba da labarin aikinka mai ban mamaki.
Sa'ad da na sami ƙayyadadden lokci
sai in yi hukumcin gaskiya.
Duniya da mutanenta an narkad da su,
na kafa gimshiƙanta.
Na ce da mai girman kai,
"Kada ka yi girman kai;"
na kuma ce da mugu,
"Kada ka ɗaga sanda,
kada ka ɗaga sandanka sama;
kada ka yi magana da tsaurin ido."
Domin ɗagawa ba daga gabar ta ke zuwa ba,
ba daga yamma ba,
ba kuma daga kudu ba,
amma Allah shi ne alkali;
ya kan sauke wani, ya ɗaga wani.
Domin akwai ƙoƙo a hannun Ubangiji,
ruwan inabin kuwa na kumfa;
cike ya ke da gauraye,
ita kuwa yake zubawa;
hakika dukkan miyagun duniya
za su girgije tsakin nasa su shanye.
Amma ni zan sanar har abada.
Zan yi waƙoƙin yabo ga Allahn Yakubu.
Zan kakkarya dukkan sandunan mugu,
amma za a cira tutar mai gaskiya.
76
A cikin kabilar Yahuda aka san Allah,
sunansa babba ne a cikin Bani Isra'ila.
Majami'atasa kuwa a Salem ta ke,
mazauninsa kuwa a Sihiyona.
A can ya kakkarya kiban bakan,
da garkuwar, da takobin, da yaƙin.
Kai maɗaukaki ne, mafifici,
tun daga dutsen farauta.
Masu taurin zuciya sun ɓaci;
sun riga sun yi barcinsu;
ba waɗansu mutane masu ƙarfi
da suka sami hannunsu.
Ya Allahn Yakubu, da tsawarka kurum
sai doki da karusar duka
sai barci mai nauyi ya kwashe su.
Kai kuwa, wato kai, sai a ji tsoronka.
Wa kuwa zai iya tsayawa a gabanka
in ka yi hushi?
Kai ka ke sa wa a ji hukunci daga sama;
ƙasa ta ji tsoro, ta yi shiru
sa'ad da Allah ya tashi yin shari'a
don ya kuɓutad da masu tawali'u na duniya.
Hakika, hushin mutum zai yabe ka
....
Ka yi kafara, ka biya Ubangiji Allahnka;
kowa ke kewaye da shi yă kawo masa kyauta,
shi da ya kamata a ji tsoronsa.
Zai yanke zuciyar sarakuna,
shi abin tsoro ne ga sarakunan duniya.
77
Zan yi wa Allah kuka da muryata,
wato ga Allah da muryata,
zai kuwa kasa kunne gare ni.
Na nemi taimakon Ubangiji a kwanakin wahalata;
hannuna a miƙe ya ke dad dare,
bai kuwa yi kasala ba
raina ya ƙi a sanyaya shi.
Na kan tuna da Allah, na kan damu,
na kan yi ƙara, raina kuma ya kan firgita.
Ka sa idanuna suna dubawa;
na damu har yadda ba na iya magana.
Na duba zamanin da,
shekarun zamanin da.
Na tuna waƙoƙina na dare;
na yi shawara da zuciyata,
raina kuma ya yi tsananin bincike.
"Ubangiji zai jefan na har abada,
ba zai ƙara zama abin/ mai/ ƙauna ba ne?
Rahamansa ta tafi ke nan ne sham har abada?
Alkawarinsa ya tashi ke nan ne har abada?
Allah ya mance zama mai alheri ne?
Ya rufe tattansan tausayinsa ne saboda hushi?"
Kuma na ce, "Wannan shi ne rashin ƙarfina,
amma zan tuna da shekarun hannun dama na Mafi Ɗaukaka.
Zan ambaci ayyukan Ubangiji,
domin zan tuna da abubuwan mamaki na abubuwan dā.
Zan kuma riƙa riya dukkan ayyukanka,
in kuwa yi murna da abubuwan da ka ke yi.
Hanyarka, ya Allah, a Wuri Tsattsarka ta ke.
Wanene mai girma kamar Allah?
Kai ne Allahn da ke yin abubuwan mamaki;
ka sa mutane sun san ƙarinka.
Da hannunka ka ceto mutanenka,
'ya'yan Yakubu da Yusufu.
Ruwaye sun gan ka, ya Allah;
ruwa ya gan ka ya tsorata;
teku ma ya raurawa.
Gajimare sun saki/ zubo/ ruwa;
sammai sun ta da murya;
kibanka kuma sun tafi nesa.
Muryar ardunka na cikin guguwa;
haskokin sun haskaka duniya;
duniya ta raurawa, ta girgiza.
Hanyarka a cikin bahar ta ke,
hanyoyinka a cikin manyan tekuna su ke;
hanyar da ke bi kuwa ba a sami ba.
Kai ne ka je mutanenka kamar tumaki,
ta hannun Musa da Haruna.
78
Ka kasa kunne, ya ku mutane ga shari'ata;
ku karkata kunnuwanku ga maganar da zan faɗa.
Zan yi magana da misali,
zan faɗi maganganun da ke cikin duhu na zamanin da,
waɗanda muka ji, muka kuma sani,
kakannimmu kuma suka faɗa mana.
Ba za mu ɓoye wa 'ya'yammu su ba;
muna gaya wa zuriya su zo
su yabi Ubangiji, da ƙarfinsa,
da ayyukansa masu bam mamaki da ya yi.
Domin ya kafa alkawari a zuriyar Yakubu,
ya kuma kafa shari'a a cikin Bani Isra'ila,
wadda ya umarci kakannimmu
don su sa su, su sanad da 'ya'yansu;
don zuriya mai zuwa su san su,
har ma 'ya'yan da za a haifa,
waɗanda za su tashi, su faɗa wa 'ya'yansu.
Don su sa zuciyarsu ga Allah,
kada kuma su manta da ayyukan Allah,
sai dai su kiyaye dokokinsa/ umarninsa;
kada kuma su zama kamar kakanninsu
zuriya mai tsayayya, kuma mai ta da husuma;
zuriyad da ba sa gyara zutakansu,
waɗanda kuma zuciyarsu ba ta tsaya kankan ga Allah ba.
'Ya'yan Afraimu da suka ɗauki kwari
sun juya baya a kwanakin yaƙi.
Ba su kiyaye alkawuran Allah ba,
sun kuwa ƙin bin shari'arsa.
Sun mance da ayyukansa
da ayyukansa na bam mamaki da ya nuna musu.
Ya yi abubuwan mamaki a gaban kakanninsu
a ƙasar Masar da filin Zowan.
Ya raba bahar ya sa sun wuce ta cike/ tsaka,
ya kuma sa ruwan ya tsaya kamar tudu.
Da rana kuma ya ja su da gajimare,
dare farai kuma da hasken wuta.
Ya tsaga duwatsu a jeji,
ya ba su ruwa sun sha sun wadatu, kamar a cikin teku.
Ya kuma fid da ƙoramai daga cikin duwatsu,
ya sa ruwa na gudana kamar koguna.
Amma duk da haka sai da suka saɓa shi,
suka yi wa Mafi Ɗaukaka tawaye a cikin hamada.
Suka gwada Allah a zukatansu
ta roƙon abinci/ nama/ don su kwantad da kwaɗayinsu.
Kai, sun saɓa wa Allah ta magana, suka ce
"Allah na iya shirya abinci a jeji?"
Ga shi, ya buge dutse, ruwa ya ɓuɓɓugo
rafuna/ ƙoramai/ kuma suna gudo.
Ya iya ba da burodi/ abinci/ kuma?
Ya iya ba mutanensa nama kuma?"
Saboda haka da Ubangiji ya ji sai ya husata;
sai fura wa Yakubu wuta,
aka kuma yi wa Bani Isra'ila hushi,
domin ba su gaskata da Allah ba,
ba su kuma gaskata da cetonsa ba.
Duk da haka kuwa ya umarci sammai,
ya kuma buɗe ƙofofin sama,
sai ya sauko musu manna daga sama don su ci,
ya ba su abincin sama.
Ɗan'adam ya ci burodin ƙaƙƙarfa;
ya aiko musu abincin mawadaci.
Ya sa iskar gabas ta busa a sama,
da ƙarfinsa kuma ya bi da iskar kudu;
ya kuma sauko mausu da nama daga sama kamar ƙura,
da kaji kamar yashin teku.
Ya sa sun zuba a tsakiyar sansaninsu,
da kewayen zangonsu.
Ta haka suka ci, suka kuma ƙoshi.
Ya ba su har suka yi kwaɗayi daga baya.
Ba a fanshe su daga kwaɗayinsu ba,
namansu/ abincinsu/ har yanzu na cikin bakinsu,
sa'ad da hushin Allah ya tasam musu,
ya kashe manyansu,
ya kashe Bani Isra'ila samari.
Bayan wannan duka sai suka sake ɗaukan zunubi;
ba su gaskata da aikinsa mai ban mamaki ba.
Saboda haka ya lalata kwanakinsu game da mugun aiki,
shekarunsu kuma game da tsoro.
Da ya riƙa kashe su, sai suka tambaye shi,
suka dawo suka nemi Allah da wuri.
Kuma suka tuna Allah ne dutsensu,
Allah Mafi Ɗaukaka kuma macecinsu.
Amma sun yi masa zaƙin baki,
suka yi masa ƙarya.
Domin zukatansu ba daidai su ke game da shi ba,
su kuma ba su da bangaskiya a cikin alkawarinsa.
Amma shi da ya ke yana cike da tausayi
sai ya gafarta mugun aikinsu,
bai halaka su ba;
kai, sau dayawa ya juya hushinsa,
bai ta da hushinsa ba.
Sai ya tuna cewa su dai bil'adam ne kurum,
iska mai wucewa ba ta kuma dawowa.
Sau nawa suka tayar masa a jeji,
suka kuma baƙanta masa ciki a cikin hamada!
Suka kuma juyo suka gwada Allah,
suka tsokani tsattsarkan nana na Bani Isra'ila.
Ba su tuna da hannunsa ba,
balle ranan nan da ya cece su daga abokan gaba.
Yadda ya sanya alamominsa a Masar
da abubuwansa na mamaki a filin Zawan.
Ya mai da kogunansu jini,
da kuma rafunansu har ba sa iya shansu.
Ya aika musu da dumbun ƙudaji suka cinye su,
da kwaɗi da suka hallaka su.
Ya ba tsutsotsi amfaninsu na gonaki,
wahalarsu kuma ga fara.
Ya halaka gonakin inabinsu da ƙanƙara,
ɗorawinsu kuma da sanyi mai sandararwa.
Ya kuma bar wa ƙanƙara shanunsu,
tumakinsu da awakinsu kuwa ga araduwa mai zafi.
Ya zuba musu tsananin hushinsa,
hushi, da haushi, da wahala,
rundunar mala'iku daga sama.
Ya yi wa hushinsa hanya;
bai kara ransu daga mutuwa ba,
sai dai ya bar su ga tsananin masifa.
Ya kashe dukkan 'ya'yam farin Masar,
da sarkin ƙarfinsu a alfarwar Hamu.
Amma ya ja mutanensa kamar tumaki,
ya bi da su/ sa su hanya/ ta cikin jeji kamar garken tumaki.
Ya ja su cikin aminci, har ma ba su ji tsoro ba;
amma sai teku ya ɗimanta magabtansu.
Sai ya kawo su iyakar tsattsarkan wurinsa,
zuwa dutsen nan da hannunsa na dama ya saya.
Ya kuma kori al'ummai a gabansu;
ya shirya masu gado ta zuriya;
ya sa kabilun Bani Isra'ila su zauna a bukkokinsu.
Amma duk da haka sai suka gwada Allah Mafi Ɗaukaka,
suka kuma yi masa turu,
ba su kiyaye shaidatasa ba.
Amma sai suka juya, suka yi mugun aiki kamar kakanninsu;
aka kau da su gefe guda kamar baka.
Domin sun tsokane shi da wurarensu, ya yi hushi,
suka sa ya yi kishi saboda surorin da suka ƙera.
Da Allah ya ji wannan sai ya yi hushi,
ya tsargi Bani Isra'ila ƙwarai.
Saboda haka ma har ya ya da majami'ar Shiloha,
alfarwar da ya ajiye a gaban mutane,
ya kuma ba da ƙarfinsa wajen bautarwa/ kamu,
ɗaukakarsa kuma a hannun magabta.
Ya kuma ba da mutanensa a kashe su da takobi,
ya yi hushi da gadonsa.
Wuta ta ƙone samarinsu,
'yam matansu kuma ba su yi waƙar amarci ba.
Aka karkashe malamansu da takobi,
matan da mazansu suka mutu kuwa ba su yi takaba ba.
Sa'an nan sai sarki ya farka
kamar wanda ya tashi daga barci,
kamar ƙaton da ke surtuan giya.
Ya bubbuge magabtansa suka koma baya;
ya sanya su suna shan wahala a kowane lokaci.
Ban da haka kuma ya ƙi alfarwar Yusufi,
bai kuma zaɓi kabilar Afraimu ba;
amma sai ya zaɓi kabilar Yahuda,
Dutsen Sihiyona ya ƙaunata.
Sai ya gina tsattsarkan wurinsa kamar masu tsawo,
kamar ƙasad da kafa har abada.
Ya kuma zaɓi baransa Dawuda,
ya ɗauke shi daga garken/ gidimon [?]/ tumaki.
Ya kawo shi daga wurin bin tumaki masu shayad da mama,
don ya ciyad da Bani Yakubu mutanensa,
da kuma Bani Isra'ila abin gadonsa.
Haka ya ci da su bisa ga kyakkyawar zuciyarsa,
ya kuma bi da su da gwanintar hannunsa.
79
Ya Allah, saura ta zama abar gādonka;
kun ƙazantad da tsattsarkan ɗakin sujada;
sun mai da Urushalima tudun ƙasa.
Sun ba tsuntsaye gawawwakin bayinka su ci,
da naman tsarkakanka sum ba namun daji.
Sun zub da jini kamar ruwa kewaye da Urushalima,
ba kuwa mai binne su.
Mun zama abin zagi ga maƙwantammu,
abin zagi, abin ƙyama ga waɗanda ke kewaye da mu.
Sai yaushe, ya Ubangiji,
Za ka yi hushi na har abada?
Kishinka zai ci ne kamar wuta?
Ka kwararo hushinka kan majusu waɗanda ba su san ka ba,
da kuma masarautun da ba sa kama sunanka.
Domin sun cinye Yakubu,
sun mai da gidansa kufai.
Kada ka dube mu da miyagun abubuwan kakannimmu;
tattausan alherinka yă kare mu da hanzari,
domin an ƙasƙantad da mu ƙwarai.
Ka taimake mu, ya Allah Macecimmu,
saboda ɗaukakar sunanka;
ka cece mu, ka zub da zunubammu
saboda sunanka.
A sa'an nan ne majusawa za su ce,
"Ina Allahnsu?"
Bari fansar jinin bayinka da aka zubar
ya sanu ga majusawa a idommu.
Bari ajiyar zucin ɗaurarre ta zo gabanka;
bisa ga girman ikonka, ka tserad da waɗanda aka tanada kisansu.
Ka ba maƙwantammu riɓi bakwai;
mugun aikinsu da suka yi maka mugunta, ya Ubangiji.
Saboda haka mu mutanenka, kuma tumakin makiyayarka,
za mu gode maka har abada;
za mu nuna yabonka ga dukkan zamani.
80
Ka kasa kunne, ya kai Makiyayin Bani Isra'ila,
kai da ka ja Yusufu kamar garken tumaki.
Kai da ka zaune a kan 'cherubim', kă haskaka.
Ka farfaɗo da ƙarfinka
a gaban Afraimu, da Bunyamunu, da Manassaha,
kă zo kă cece mu.
Ka sake juyo da mu, ya Allah;
ka sa fuskarka ta haskaka, sai kuwa mu cetu.
Ya Allah mai runduna,
har yaushe za ka yi hushi da addu'ar mutanenka?
Ka ci da su da burodin hawaye,
ka kuma ba su hawaye da yawa su sha.
Ka sa mun zama ababan fama/ hargitsi/ da maƙwabtammu,
maƙiyammu kuma na ta dariya a junansu.
Ka sake juyo da mu, ya Allah mai runduna;
ka sa fuskarka ta haskaka, sai kuwa mu cetu.
Kai ne ka fito da inabi daga ƙasar Masar;
kai ne ka kori al'ummai, ka kuwa shuka su.
Kai ne ka shirya masu wuri,
ya kafa saiwa mai zurfi, ya cika ƙasar.
Inuwarsa ta rufe duwatsu,
rassansa kuma kamar rimin Alah su ke.
Ya baza rassansa har teku,
tohonsa kuma har kan koguna.
Dom me ka karya shingenta
har masu son wucewa ta hanyar suka tsigarta?
Alhanzir ɗin jeji na ɓarnata ta,
dabbobin jeji ma na cinye ta.
Mun roƙe ka, ka sake juyowa, ya Allah mai runduna.
ka dubo ƙasa daga sama, ka duba;
ka ziyarci inabin nan.
Tushen da ka dasa da kanka,
da reshen da kai da kanka ka ƙarfafa,
an ƙone shi da wuta, an sare shi;
sun halaka saboda tsawar fuskarka.
Hannunka yă kasance a mutumin da ke hannunka na dama;
a kan ɗan mutum wnada ka ƙarfafa saboda kanka.
Haka ba za mu tafi daga gare ka ba;
ka raya mu, mu kuwa sai mu kira sunanka.
Ka sake juyowa da mu, ya Ubangiji Allah mai runduna;
ka sa fuskarka ta yi haske, mu kuwa sai mu cetu.
81
Ku yi waƙa da ƙarfi ga Allahmmu mai ƙarfafa mu/ ƙarfimmu.
ku yi hananiyar murna ga Allahn Yakubu.
Ku ɗauki Zabura, ku kawo tambari nan;
molo mai daɗi da kuntigi.
Ku busa sabon kakaki a amaryar wata,
da tsakiyatasa, da kuma ranar muhimmin bikimmu.
Domin doka ce ta Bani Isra'ila
dokar Allahn Yakubu.
Ya sanya ta ga Yusufu saboda shaida
sa'ad da ya tafi ƙasar Masar
inda na ji harshen da ban sani ba.
"Na sauke kaya a kafaɗatasa,
an hutad da hannunsa daga ɗaukar kwando.
Ka yi kira sa'ad da ka ke cikin wahala,
na kuwa kuɓutad da kai;
na amsa maka a keɓaɓɓen wurin aradu;
na gwada ka a ruwan Maribaha.
Ya ku mutanena, ku saurara,
ya ku mutanena, zan yi muku shaida.
Ya ku Bani Isra'ila, idan ba za ku saurara mini ba,
ba wani baƙon gunkin da zai kasance a cikinku;
kada kuma ku bauta wa wani gunki.
Ni ne Ubnagiji Allah,
wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar.
Ku buɗe bakinku da faɗi, zan cika shi.
"Amma mutanena ba su saurari muryata ba;
Bani Isra'ila ma ba ko ɗayansu da ya ke nawa.
Saboda haka na bar su suka tafi bisa taurin zuciyarsu,
don su be shawarwarinsu.
Ina ma mutanena za su saurare ni,
Bani Isra'ila su bi hanyata!
Nandanan zan ci magabtansu,
in juyo kan magabtansu.
Maƙiya Ubangiji sai su miƙa kansu gare shi,
amma lokacinsu zai jure har abada.
Zai kuma ci da su; da alkama mafi kyau,
zan kuma wadata ka da zuma daga cikin dutse."
82
Allah na tsaye a cikin taron jama'ar Allah;
yana hukunci a cikin iyayengiji.
"Har yaushe za ka riƙa yin hukumci da rashin gaskiya
za ka yi wa mugu biyayya?
Ka hukunta gajiyayye da maraya;
ka yi wa cucecce da matalauci gaskiya.
Ka ceci gajiyayye da mai neman taimako;
ka cece su daga hannun mugu."
Ba su sani ba, ba su kuma fahimta ba;
suna kaiwa, suna kawowa a cikin duhu;
an girgiza dukkan harsashin duniya.
Na ce, "Ku iyayengiji ne,
ku kuwa duka 'ya'yan Mafi Ɗaukaka ne;
duk da haka kuwa za ku mutu kamar mutane,
] ku kuwa faɗi kamar ɗaya daga cikin sarakuna."
Ka tashi, ya Allah, ka hukunta duniya,
domin kai ne mai gādon dukkan al'ummai.
83
Ya Allah, kada ka yi shiru mana;
kada ka hana amincinka,
kada ka yi shiru, ya Allah.
Domin ga shi magabtanka sun tayar,
maƙiyanka kuma sun ɗaga kansu.
Sun yi shawara da makirci a kan mutanenka;
sun shawarci juna a kan ɓoyayyenka.
Sun ce, "Ku zo, mu yanke su daga zama al'umma,
don kada a ƙara tunawa da sunan Bani Isra'ila.
Domin sun haɗu baki sun yi shawara;
suna yin alkawarin da zai saɓa maka;
sansanin Iduma da na Isma'ilawa,
da na Muwaba da na Hajarawa,
wato Gebal da Ammon da Amaleka,
da Filistiya da mutanen Sur;
da Asiriya ita ma haɗa ta ke da su;
su ne ƙarfin 'ya'yan Luɗu.
Ka yi masu kamar yadda ka yi wa Midiyan,
da Siseriya da Jabin, a kogin Kishon,
waɗanda suka halaka a Indoru,
sun zama kamar kashin duniya.
Ka mai da dattawansu/ manyan mutanensu/ kamar Uriba da Ziba;
kai, dukkan sarakunansu ma kamar Zabita da Zamunna,
waɗanda suka ce, "Bari mu nema wa kammu mallakar gidan Allah."
Ya Allahna, ka mai da su kamar guguwa,
kamar bunun da iska ta ɗebo.
Kamar wuta mai ƙone daji/ wutar daji,
kamar wutad da ke ƙone kan duwatsu.
Saboda haka sai kakore su da hadirinka,
ka kuma tsoratad da su da hadirinka.
Ka cika fuskokinsu da ruɗewa/ Ka rurruɗa su,
don su nemi sunanka, ya Allah.
Bari su kunyata, su muzanta har abada,
kai, bari dai su ruɗe, su halaka.
Don dai su san kai kaɗai ne,
wanda sunanka ke Ubangiji,
ka ke Mafi Ɗauaka a dukkan duniya.
84
Majami'arka abar ƙauna ce,
ya Ubangiji runduna.
Raina na marmari, kai har ma yana suma
saboda majalisun Ubangiji;
zuciyata da jikina suna sowa
saboda rayayyen Allah.
Kai, gwara ta sama wa kanta gida,
tsattsewa/ alallaka/ bilbili/ ma ta sama wa kanta sheƙa,
inda za ta haifi 'ya'yanta,
kamar wuraren yi maka baiko, ya Ubangijin runduna,
sarkina kuma Allahna.
Albarka ta tabbata ga waɗanda ke zaune a gidanka;
har yanzu za su riƙa yabonka.
Albarka ta tabbata ga wanda ƙarfinka ke gare shi/ ka [?},
wanda manyan hanyoyin zuwa Sihiyona ke zuciyarsa.
Suna wucewa ta kogin Kuka,
suna mai da shi wurin ƙoramai;
ruwan farko ma ya lulluɓe shi da albarka.
Suna zuwa wurin mai ƙarfi
ɗayansu ma sai da ya bayyana
a gaban Allah a Sihiyona.
Ya Ubangiji Allah mai runduna, ka ji addu'ata;
ka kasa kunne, ya Allahn Yakubu.
Ka duba, ya Allah, garkuwarmu,
ka kuma duba fuskar shafaffenka.
Domin kwana ɗaya a ɗakunanka
ya fi kwana dubu.
Gara in zama mai tsaron ƙofa a ɗakin Allah
a kan in zauna a sansanin miyagu.
Domin Ubangiji Allah rana ne, kuma garkuwa ne.
Ubangiji zai ba da rahama da ɗaukaka.
Ba wani kyakkyawan abin da zai riƙe ya hana
masu bin hanyar gaskiya.
Ya Ubangijin runduna,
albarka tā tabbata ga wanda ya gaskata da kai.
85
Ya Ubangiji kā kyautata wa ƙasara;
ka maido kamammun gidan Yakubu.
Kā yafe laifin mutanenka;
kā rufe duk zunubansu.
Ka ɗauke duk hushinka;
ka juya daga tsananin hushinka.
Ka juyo da mu, ya Allah macecimmu,
ka daina jin haushimmu.
Za ka yi hushi da mu har abada ne?
Za ka yaɗa hushinka ne kan dukkan zamani?
Ashe, ba za ka sake raye mu ba,
don mutanenka su yi farinciki da kai?
Ka nuna mana tausayinka, ya Ubangiji,
ka kuma ba mu cetonka.
Zan ji abin da Ubangiji Allah zai ce,/ maganad da Ubangiji Allah zai yi,
domin maganar aminci zai yi wa mutanensa da kuma tsarkakansa;
amma kada ka bari su juyo kan wauta.
Hakika cetonsa na kusa da masu tsoronsa,
don ɗaukaka ta zauna a ƙasarmu.
An gama tausayi da gaskiya gu ɗaya;
aikin gaskiya da aminci sun sumbaci juna.
Gaskiya ta bullo daga duniya/ ƙasa,
aikin gaskiya kuma ya liƙo daga sama.
Kai, Ubangiji dai abin da ke kyakkyawa zai bayar,
ƙasarmu kuwa za ta ba da amfaninta.
Aikin gaskiya zai wuce gabansa,
zai kuma sa hanyoyinsa su zama abadan bi.
86
Ka karkato kunnnka, ya Ubangiji, ka amsa mini,
domin ni gajiyayye ne, kuma mabukaci.
Ka kiyaye raina, domin ni mai bin Allah/ ka/ ne;
ya kai Allahna, ka ceci bawanka wanda ya amince da kai.
Ka ji tausaina, ya Ubangiji,
domin gare ka na ke kuka wuni zubur.
Ka faranta cikin baranka,
domin gare ka ne, ya Ubangiji, na ke sa rai.
Domin kai kyakkyawa/ nagari/ ne, ya Allah,
kuma kana shirya ka yi gafara,
rahamarka kuwa mayalwaciya ce
ga duk masu son nemanka.
Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ga addu'ata,
ka kuma saurari muryata ta roƙo.
Zan kira ka a kwanakin wahalata,
domin za ka amsa mini.
Babu kamarka a cikin iyayengiji, ya Allah;
ba kuma ayyuka irin naka.
Dukkan al'umman da ka yi za su zo
su bauta maka, ya Ubangiji,
za su kuwa ɗaukaka sunanka.
Domin kai mai girma ne,
kana kuma yin abubuwan mamaki,
kai ne kaɗai Allah.
Ka koya mini tafarkinka, ya Ubangiji,
zan bi gaskiyarka;
ka haɗa zuciyata tă tsoraci sunanka.
Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna,
da dukkan zuciyata;
zan kuma ɗaukaka sunanka har abada.
Domin tausayinka gare ni mai yawa ne;
ka kuwa kuɓutad da raina daga rami mai zurfi.
Ya Allah, masu alfarma sun tasam mini,
kuma taron mafaɗata sun nemi raina,
ba su kuwa sa ka a gaba ba.
Amma kai, ya Allah, Allah ne mai yawan tausayi, kuma mai alheri,
marar hushi da sauri, mai yalwar tausayi da gaskiya.
Ka juyo gare ni, ka ji tausayina;
ka ba bawanka ƙarfinka,
ka ceci ɗan baiwarka.
Ka nuna mini alamar nagarta,
don maƙiyana su gani su kunyata
domin kai, ya Ubangiji, ka taimake ni,
ka kuma sanyaya mini zuciya.
87
Harsashinsa na tsarkakan duwatsu;
Ubangiji na ƙaunar ƙofofin Sihiyona
fiye da dukkan mazaunan Bani Yakubu.
Ana maganar abubuwan ɗaukaka game da ke,
ya ke birnin Allah.
Zan ambaci Rahaba da Babila a cikin waɗanda suka san ni;
ga Filistiya da Sur tare da Habasha.
"Wannan a can aka haife shi."
Game da Sihiyona za a ce,
"Wannan da wancan ita ce ta haife su";
Mafi Ɗaukaka da kansa zai kafa ta.
Ubangiji zai ƙirga sa'ad da ya ke rubuta mutanen;
"Wannan a can aka haife shi."
Masu waƙa da masu rawa za su ce,
"Dukkan ƙoramaina na gare ka."
88
Ya Ubangiji, Allah mai cetona,
na yi kuka a gabanka dare da rana.
Bari addu'ata ta kai ga zatinka,
ka kasa kunne ga kukana.
Domin raina kuma yana matsawa kusa da Mahalaka.
Ana lasafta ni tare da masu shiga rami;
ni mutun ne marar mataimaki,
wanda aka jefar a cikin matattu,
kamar matattun da ke cikin kabari
waɗanda ba ka ƙara tunawa da su,
an kuwa datse su daga hannunka/ gare ka.
Kā sanya ni a rami mafi zurfi,
a wurare masu duhu,
kuma wurare masu zurfi.
Hushinka ya danne ni da ƙarfi,
ka kuma tsananta mini da dukkan tsananinka.
Ka sanya abokaina nesa da ni;
ka mai da ni abin ƙyama gare su.
An rufe ni, ba zan iya fitowa ba;
idona na lalacewa saboda wahala.
Kullum na kan kira ka, ya Ubangiji;
na ɗaga hannuna gare ka.
Ka nuna wa matattu abin mamaki?
Waɗanda suka mutu sa tashi su yabe ka?
A faɗi alherinka na ƙauna a kabari,
ko kuwa gaskiyarka a wurin halaka?
A san abubuwanka na mamaki a cikin duhu,
ko kuma gaskyarka a ƙasar masu mantuwa?
Amma, ya Ubangiji, na yi kuka gare ka;
addu'ata kuwa za ta zo gabanka da safe.
Ya Ubangiji, dom me ka ya da raina?
Dom me ka ɓoye mini fuskarka?
An jarabce ni da cuta,
kuma na yi shirin mutuwa tun daga ƙuruciyata.
Sa'ad da na ke cikin shan wahalar abubuwanka na tsoro, na ji haushi.
Hushinka mai ban tsoro ya bi ta kaina;
abubuwanka na ban tsoro sun wuce ni.
Sun zo sun kewaye ni wuni zubur kamar ruwa;
sun haɗa kai sun kewaye ni.
Ka sanya mai ƙaunata da abokina nesa da ni;
abokaina kuwa ka sa su a cikin duhu.
89
Zan yi waƙar alherin Ubangiji mai yawa, har abada;
zan sanad da gaskiyarka ga dukkan zuriya da bakina.
Domin na ce, "Za a inganta tausayi har abada;
za a kafa gaskiyarka a sama sosai."
"Na yi alkawari da zaɓaɓɓena;
Na rantse wa barana Dawuda:
'Zan kafa zuriyarka har abada,
in inganta gadon sarautarka ga dukkan zamani.'"
Sammai kuma za su yabi abubuwanka na mamaki, ya Ubangiji,
da kuma gaskiyarka a taron tsarkaka.
Domin wanene za a iya gwadawa da Ubangiji a cikin sammai?
Wanene a cikin 'ya'yan manya ke kamar Ubangiji,
Allah mai ban tsor ƙwarai a cikin shawarar tsarkaka;
a kuma tsorace shi fiye da su duka,
su da ke kewaye da shi?
Ya Ubangiji Alah mai runduna,
wanene mai girma kamarka, ya Ubangiji;
gaskiyarka kuwa tana nan kewaye da kai?
Kai ne ka iko da alfarmar teku;
sa'ad da raƙuman ruwansa suka tashi,
kai ne ka ke kwantad da su.
Ka rugurguza Rahaba kamar wad da ka kashe,
ka warwatsa magabtanka da ƙarfin hannunka.
Sammai naka ne, ƙasa ma taka ce;
duniya da abin cikinta kai ne ka fare su.
Kai ne ka halicci kudu da arewa;
Taburu da Harmuna suna farinciki da sunanka.
Kana da babban hannu/ hannu mai ƙarfi;
Hannunka mai ƙarfi ne,
hannunka na dama kuwa ɗaukakke ne.
Aikin gaskiya da shari'a su ne harsashin gadon sarautarka;
tausayi da gaskiya su ke gabanka.
Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san muryar farinciki;
ya Ubangiji, suna bin/ zaune cikin/ hasken fuskarka ne;
a cikin sunanka su ke farinciki wuni zubur,
kuma a cikin gaskyarka ne aka ɗaukaka su.
Domin kai ne ɗaukakar ƙarfinsu;
kuma a game da ƙaunarka ne za a ɗaukaka ƙaƙƙarfammu.
Domin garkuwarmu ta Ubangiji ce,
da kuma sarkimmu na Tsattsarkan Bani Isra'ila.
Sa'an nan ka yi magan ta cikin wahayi ga tsarkakanka. Ka ce,
"Na taimaki wanda ke mai ƙarfi;
na ɗaukaka wanda aka zaɓa a cikin mutane.
Na sami barana Dawuda;
na shafe shi da tsattarkan maina/ man,
wanda za a kafa ikona game da shi,
hannuna ma zai ƙarfafa shi.
Magabta ba za su rinjaye shi ba;
mugun ɗa kuwa ba zai ba shi wahala ba.
Kuma zanbuge magabtansa a gabansa,
im buge maƙiyansa.
Amma bangaskiyata da tausayina
za su kasance tare da shi;
game da sunana ne kuma
za a ɗaukaka ƙarfinsa.
Zan kuma ɗora hannunsa a kan teku,
hannunsa na dama kuma a kan koguna.
Zai yi kuka gare ni, yă ce,
'Kai ne Ubana, Allahna, kuma dutsen cetona.'
Zan kuma sa shi yă zama ɗana na fari,
mafi ɗaukaka a kan sarakunan duniya.
Zan tsare masa tausayina/ rahamata/ har abada,
alkawarina kuwa zai zauna a gare shi da ƙarfi.
Zan kuma sa zuriyarsa tatabbata har abada,
gadon sarautarsa kuma kamar iya kwanakin sama.
In 'ya'yansa sun ya da shari'ata,
ba su bi shari'ata ba,
in sun karya dokokina,
ba su bi umarnina ba,
to, sai in hori laifuffukansu da sanda,
miyagun ayyukansu kuma da bulala.
Amma ba zan ɗauka tausayina gare shi sam-sam ba,
ba kuwa zan bar aikin gaskiyana ya wofinta ba.
Ba zan karya alkawarina ba,
ko kuwa in sake abin da na faɗa.
Na taɓa rantsewa da ɗaukakata
kan ba za ya da Dawuda ba.
Zuriyarsa za ta jre har abada,
gadon sarautarsa kuwa kamar rana a gabana.
Za a kafa shi har abada kamar wuta;
kuma kaman shaida mai gaskiya a sama."
Amma kai ka jefar, ka kuma ƙi,
ka yi hushi da shafaffenka.
Ka ƙi alkawarin baranka;
ka wulakanta kambinsa har ka tursasa shi.
Ka sassabe duk shingensa;
ka mai da ƙaƙƙarfan wurinsa kango.
Duk masu wucewa a kan hanya sun ɓata shi;
ya zama abin ƙyama ga 'yan'uwansa/ maƙwantansa.
Ka ɗaukaka hannun daman abokan gabarsa;
ka sa duk magabtansa sun yi farinciki.
Kai, har ma ka juya kaifin takobinsa,
ba ka sa ya jure yaƙin ba.
Ka sa haskensa ya daina;
ka ka da gadon sarautarsa har ƙasa.
Ka gajarta kwankin samartakatasa;
ka rufe shi da kunya.
Har yaushe, ya Ubangiji?
Za ka ɓoye fuskarka har abada?
Har yaushe fuskarka za ta ƙone kamar wuta?
Ka tuna mana da irin gajartar lokacina;
saboda wane mugun abu ne ka halicci ɗan'adan.
Wane mutun ne zai rayu, ba zai mutu ba?
Wanda zai kuɓutad da ransa daga Mahalaka?
Ya Ubangiji, ina tausayinka na dā
waɗanda ka rantse wa Dawuda
game da su a cikin halin gaskyarka?
Ya Ubangiji, ka tuna da muguntar bayinka;
yadda na ɗauki nauyin muguntar, dukkan manyam mutane,
waɗanda magabtanka suka yi wa mugunta, ya Ubangiji,
waɗanda suka yi wa hanyoyin shafaffenka mugunta.
Yabo yă tabbata ga Ubangiji har abada.
Amin, summa Amin.
90
Ya Ubangiji, kai ne mazaunimmu
a dukkan zamanai.
Kafin a fari duwatsu,
ko kuwa ma kafin ka fari ƙasa duniya,
wato tun daga fil'azal har ya zuwa har abada abadin,
Kai ne Allah.
Kai ne ka kai mutane ga halaka,
ka kuma ce, "Ku dawo, ya ku 'yan'adam."
Domin kwana dubu kamar kwana ɗaya ne a ganinka,
in sun wuce,
kuma kamar sa'a ce ta dare.
Ka ɗauke su kamar ruwa mai gudu, kamar barci suka yi;
da safe kuwa kamar ciyawa mai tsira su ke.
Da safe ta kan yi kyau tana girma;
da maraice kuwa a kan sare ta, ta bushe.
Domin muna halaka a cikin hushinka;
muna wahala a cikin tsananin hushinka.
Ka sanya miyagun abubuwanka a gabanka,
zunubammu na ɓoye suna cikin hasken fuskarka.
Domin duk kwanakimmu sun ƙare a cikin hushinka;
mun ƙare shekarammu kamar da tatsuniya.
Shekarummu saba'in ne,
ko kuwa im muna da ƙarfi mu yi tamanin;
duk da haka kuwa alfarmarsu wahala ce da baƙinciki;
domin nandanan za ta wuce, mu kuma mu shuɗe.
Wa ya san ƙarfin hushinka,
da tsananin hushinka bisa ga tsoronka da aka yi?
Saboda haka sai ka koya mana mu ƙirga kwanakimmu
don mu sami zuciyar hikima.
Ya Ubangiji, ka koma mana, yaya ka daɗe?
Bari a tuba maka saboda bayinka.
Ka wadata mu mana da rahamarka tun da safe,
don mu yi farinciki
mu yi murna a dukkan kwanakimmu.
Ka sa mu yi farinciki bisa ga kwanakin da ka shafe mu da wahala,
da shekarun da muka ga mugun abu.
Aikinka yă bayyana a kan bayinka,
da ɗaukakarka a kan 'ya'yansu.
Kyau Ubangilji Allahmmu ya kasance tare da mu;
ka kafa mana ayyukammu na hannummu,
kă dai kafa aikimmu na hannummu.
91
Shi wanda ke zauna a wuraren sirru na Mafi Ɗaukaka
zai zauna har abada a cikin inuwar Mafi Iko.
Gabe da Ubangiji zan ce, "Shi ne matserata, kuma mafakata/ madagarata;
Allahna, wanda na gaskata da shi."
Domin zai kuɓutad da kai daga tarkon mugun mutum,
da kuma tunzuri mai hayaniya.
Zai rufe ka da ɗeshin fuffukensa;
ƙarƙashin fukafukansa kuma za ka fake.
Gaskyarsa ita ce garkuwa da warwaji.
Kada ka ji tsoron abin tsoron cikin dare,
ko kuwa kibiyar da ke tafiya da rana,
saboda tunzurin da a ke yi a cikin dare,
ko kuma muguntar da ta ke bajewa da rana.
Mutum dubu za su faɗi a gabanka,
dubu goma kuma a hannunka na dama,
amma dare ba zai yi a can ba.
Da idonka kaɗai za ka gani
ka ga sakamakon mugu.
Domin ya Ubangiji, kai ne mafkata!
Ka sa wuri Mafi Ɗaukaka ya zama gidanka,
ba wani mugun abin da zai same ka,
ba kuma wani bala'in da zai zo ɗakinka/ alfarwarka.
Domin zai sa mala'ikunsa su kula da kai
don su kiyaye ka ta kowace hanya.
Za su tallafe ka da hanuunsu,
don kada ka yi tuntuɓe da dutse.
Za ka taka zaki da kāsā,
za ka taka kwikwiyon zaki da maciji.
Domin ya sanya mini ƙaunarsa,
saboda haka zan kuɓutad da shi;
zan ɗaukaka shi domin ya san sunana.
Zai kira ni, zan kuwa amsa masa;
zan kasance tare da shi a lokacin wahala;
zan kuɓutad da shi, in girmama shi.
Zan wadata shi da tsawon kwana,
in kuma nuna masa cetona.
92
Abu mai kyau ne a gode wa Ubangiji,
a kuma yi waƙar yabon sunanka, ya Mafi Ɗaukaka;
a nuna alherinka na ƙauna da safe,
da gaskiyarka dad dare,
da molo mai igiya goma
da kuma kuntigi,
da ƙaƙƙarfar murya a kan molon.
Domin ka faranta mini ciki ta aikinka, ya Ubangiji;
zan ci nasara ta ayyukan hannunka.
Ayyukanka da girma su ke, Ya Ubangiji.
Tuaninka suna da yawa ƙwarai.
Mutumin banza bai sani ba;
wawa ma bai fahimci wannan ba:
sa'ad da mugu ya fito kamar ciyawa,
sa'ad da kuma dukkan masu aikata mugunta suka arzuta/ wadata,
za a hallaka su ke nan har abada;
amma kai, ya Ubangiji, a sama ka ke har abada.
Domin, ga shi, magabtanka, ya Ubangiji,
ga shi magabtanka za su halaka;
masu aikata mugunta kuwa za a watse su.
Amma ka ɗaukaka ƙahona kamar ƙahon ɓauna;
an shafe ni da sabon mai.
Idona kuma ya ga biyan bukatata a kan magabtana,
kunnena ya ji bukata game da masu aikata mugunta
waɗanda suka tasam mini.
Masu gaskiya za su yi albarka kamar icen dibino;
zai tashi ya girma a ƙasar Libanon kamar rimi.
Waɗanda aka shuka a gidan Ubangiji,
za su yi albarka a ɗakunan Allahmmu.
Ko sun tsufa, za su haifu,
za su zama ɓulɓul da ruwa a jikinsu,
za su kuma zauna korra,
don a nuna cewa Ubangiji mai gaskiya ne;
shi ne dutsena, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.
93
Ubangiji shi ne mai sarauta,
ɗaukaka ta tabbata gare shi;
Ubangiji a ɗamare ya ke,
ya yi wa kansa ɗamara da ƙarfi.
Duniya ma an kafa ta don kada ta raurawa.
An kafa mulkinka tun zamanin da;
tun fil'azal ka ke.
Ya Ubangilji, ruwa ya janye,
ruwa ya yi shiru,
ruwa ya kwantad da raƙumansa.
Sama da dirin ruwaye masu yawa,
manya-manyan masu dama teku,
Ubangiji da ke sama ƙaƙƙarfa ne.
Shaidunka tabbatattu ne ƙwarai;
tsarkaka ta zama gidanka,
ya Ubangiji, har abada
94
Ya Ubangiji Allah, wanda ramuwa ke taka,
kai ne Allah da ramuwa ke taka kă haskaka.
Ka ɗaga kanka, kai alkalin duniya;
ka ba mutakabbirai hamadarsu.
Ya Ubangiji, har yaushe ne na miyagu
za su yi nasara?
Suna surutu, suna magana da alfarma;
dukkan masu mugun aiki suna ruba.
Suna lalata mutanenka, ya Ubangiji,
suna kuma wahal da magadanka.
Suna kashe gwawruwa da baƙo;
sun kuma kisan maraya;
kuma suna cewa, "Ubangiji, kai ba za ka gani ba;
Allahn Yakubu kuma ba zai yi la'akari ba.
Ku duba mana, ya ku mutane masu kama da dabbobi, a cikin mutane.
Ku kuma wawaye, yaushe za ku yi hikima?
Shi wanda ya dasa kunne,
ashe, ba zai ji ba?
Shi wanda ya yi ido,
ashe, ab zai gani ba?
Shi da ke tsarkake al'umma,
ashe, ba zai yi gyara ba?
Wato, shi da ke koya wa mutum sani?
Ubangiji ya san tunanin mutum,
cewa dai aikin banza ne.
Albarka tā tabbata ga mutumin
da ka tsarkake, ya Ubangiji,
ka ke kuma koyar masa ta shari'arka,
don ka hutad da shi daga kwanakin gaba,
sai an tona wa miyagu raji.
Domin Ubangji ba zai zub da mutanensa ba;
ba kuwa zai yada magadansa ba;
domin hukumci zai komo kan gaskiya,
duk masu gaskiya a zuci kuwa za su bi shi.
Wanene zai tsaya mini a kan miyagu?
Wa zai tsaya mini a kan masu aikata mugunta?
Im ba Ubangiji ne ya zama mataimakina ba,
sai raina ya zauna shiru nandana.
Sa'ad da na ce, "Santsi ya ɗauke ƙafata,"
sai ka taimake ni da alherinka in tashi, ya Ubangiji.
A cikin yawan tunanin zuciyata,
sai ka sanyaya mini zuciya in yi farinciki.
Ikon mugunta yā zauna tare dakai,
wanda ke ƙaga mutunga ta dokokinsa?
Sun taru suna gāba da mai gaskiya,
sun ƙi/ kashe/ marar laifi.
Amma Ubangilji ya zama doguwar hasumiyata,
Allahna kuma dutsen fakewata.
Ya kum saukam musu da muguntarsu a kansu
zai kuma ware/ yanke/ su tare da muguntarsu;
Ubangiji Allahmmu zai ware/ yanke/ su.
95
Ku zo mana, mu yi wa Ubangiji waƙa;
bari mu yi hayaniyar murna ga dutsen cetommu.
Mu zo Zatinsa muna godiya;
mu yi hayaniyar murna da waƙar Zabura.
Domin Ubangiji Allah ne babba,
kuma babban Sarki ne sama da dukkan alloli.
Zurfafan wuraren duniya a hannunsa su ke;
tsawon duwatsu ma nasa ne.
Teku nasa ne, shi ne ya yi shi;
hannunsa ne kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
Ku zo mana mu yi bauta, mu yi sujada;
mu durƙusa a gaban Ubangiji, mahaliccimmu.
Domin shi ne Allahmmu,
mu ne kuwa mutanen makiyayatasa,
kuma tumakinsa na kansa.
Da mana yau ku ji muryatasa!
Kada ku taurare zukatanku kamar Maribaha,
kamar a kwanakin Masaha a jeji,
sa'ad da kakanninku sauka gwada ni,
suka jarraba ni, suka kuma ga aikina.
Shekara arba'in ina baƙinciki da zamanin nan,
har na ce, "Mutane ne masu yin kuskure a zukatansu,
ba su san hanyoyina ba kuwa."
Ga shi kuwa na rantse a cikin hushina cewa
ba za su sai hutu gare ni ba.
96
Ku yi wa Ubangiji sabuwar waƙa;
dukkan duniya, ku yi wa Ubangiji waƙa.
Ku yi wa Ubangiji waƙa, ku yabi sunansa;
ku nuna cetonsa kullum.
Ku ba da labarin ɗaukakrsa a cikin al'ummai,
ayyukansa masu bam mamaki a cikin dukkan mutane.
Domin Ubangiji mai girma ne,
abin yabo ƙwarai ne kuma;
shi za a ji tsoro fiye da kowane alla/ dukkan alloli.
Domin dukkan allolin mutane gumaka ne,
amma Ubangiji shi ne ya halicci sammai.
Ɗaukaka da iko nasa ne;
ƙarfi da kyau a tsattsarkan wurinsa su ke.
Ku ba Ubangiji, ya ku dangin mutane,
ku bar wa Ubangiji ɗaukaka da ƙarfi.
Ku ba Ubangiji ɗaukakar da sunansa ya cancanta;
ku kawo baiko, ku kuma zo ɗakunansa.
Ku bauta wa Ubangiji mana da tsarkaka mai kyau;
duk duniya ku yi rawar jiki a gabansa.
Ku ce "Ubangiji ne mai iko," a cikin al'ummai.
"An kuma kafa duniya don kada ta jijjiga;
zai hukunta mutane da mugun abu."
Bari sammai su yi murna, duniya kuma ta yi farinciki;
bari teku ya yi ƙugi, shi da abin cikinsa duka.
Bari fili ya da abin da ke cikinsa su yi murna!
A sa'an nan ne dukkan bishiyoyin jeji za su yi waƙa don murna;
ku dubi Ubangiji, domin yana zuwa,
domin yana zuwa yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya da gaskiya,
da mutane kuma da gaskiyatasa.
97
Ubangiji ne mai iko; bari duniya ta yi farinciki;
bari tsibirai masu yawa su yi farinciki.
Gajimarai da duhu sun kewaye shi;
aikin gaskiya da hukunci
su ne harsashin/ tushen/ gadon sarautarsa.
Wuta na tafiya a gabansa,
tana ƙone magabtansa a kewaye da shi.
Walƙiyarsa ta haska duniya;
duniya ta gani, jikinta ya ɗauki rawa.
Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Zatin Ubangiji,
wato a gaban Zakin Ubangijin duniya duka.
Sammai sun faɗi gaskiyatasa;
kuma dukkan mutane sun ga ɗaukakatasa.
Duk masu bauta wa gumaka sun kunyata,
waɗanda ke ruban gumaka da kansu;
ku bauta masa ya ku alloli duka.
Sihiyona ta ji, ta kuwa yi farinciki;
'ya'yan Yahuda mata ma sun yi farinciki
saboda hukuncinka, ya Ubangiji.
Domin kai ne mafi ɗaukaka a duka duniya/ sama da dukan duniya/, ya Ubangiji;
kai ne ɗaukakakke nesa a kan dukkan alloli.
Ya ku waɗanda ku ke ƙaunar Ubangiji, ku ƙi mugun aiki;
ya kiyaye rayukan tsarkakansa;
ya kuɓutad da su daga hannun miyagu.
An shuka/ halicci/ haske ne saboda masu gaskiya,
farinciki kuma saboda masu gaskiya a zuci.
Ku yi farinciki da Ubangiji, ya ku masu gaskiya,
ku kuma yi wa tsattsarkan sunan nan nasa godiya!
98
Ku yi wa Ubangiji sabuwar waƙa mana,
domin ya yi abubuwan mamaki.
Hannunsa na dama da hannunsa tsattsarka
sun kawo masa ceto.
Ubangiji ya sanad da cetonsa,
ya nuna gaskiyatasa a gaban idon al'ummai.
Ya tuna da alkawarinsa da bangaskiyatasa
ga Bani Isra'ila.
Dukkan iyakokin duniya sun ga ceton Allahmmu.
Ku yi hayaniyar farinciki ga Ubangiji ku mutanen duniya duka;
ku yanku ku yi waƙa don farinciki;
kai, ku yi waƙoƙin yabo.
Ku yi wa Ubangiji waƙoƙin yabo da molo,
da molo da murya mai daɗi.
Da kakaki da bigila
ku yi hayaniyar farinciki a gaban Sarki, Ubangiji.
Bari teku ya yi ƙugi, duka da abin cikinsa;
har duniya da mazauna cikinta.
Bari ruwa ya yi tafi da kansa;
bari duwatsu su yi waƙa gaba ɗaya don murna
a gaban Ubangiji, domin yana zuwa yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya da gaskiya,
da kuma mutane da gaskiya.
99
Ubangiji ne ke mulki,
bari mutane su yi rawar jiki.
Yana zauna a kan 'cherubim',
bari ƙasa/ duniya/ ta girgiza.
Ubangiji babba ne a cikin Sihiyona;
shi ne kuwa maɗaukakai birbishin dukkan mutane
Bari su yabi sunan nan naka mai girma, mai ban tsoro!
Tsattsarka ne shi!
Ƙarfin Sarki ma, yana son hukunci,
kai ne ka kafa gaskiya;
kai ne ka zartad da shari'a
da gaskiya a gidan Yakubu.
Ku ɗaukaka Ubangiji Allahmmu;
ku yi bauta a matashin ƙafafunsa!
Tsattsarka ne shi!
Musa da Haruna a cikin malamansa,
da Samu'ila a cikinsu, masu kiran sunansa.
Sun kira Ubangiji, ya kuwa amsa musu.
Ya yi musu magana a gimshiƙin gajimare;
sun kiyaye alkawuransa,
da dokokin da ya ba su.
Ka amsa musu, ya Ubangiji Allahmmu;
kai ne Allah mai gafarta musu,
ko da ya ke ka rama abin da suka yi.
Ku ɗaukaka Ubangiji Allahmmu,
ku yi bauta a kan tsattsarkan dutsensa;
domin Ubangiji Allahmmu tsattsarka ne!
100
Ku yi hayaniyar farinciki ga Ubangiji, ya ku samari duka.
ku bauta wa Ubangiji da farinciki.
Ku zo cikin Zatinsa da waƙa.
Ku san dai Ubangiji Allah ne.
Shi ne ya halicce mu, mu kuma nasa ne;
mu mutanensa ne, kuma tumakin makiyayatasa.
Ku shiga ƙofofinsa da godiya,
da kuma ɗakunansa da yabo.
Ku gode masa, ku yabi sunansa.
Domin Ubangiji kyakkyawa ne;
tausayinsa na wanzuwa har abada,
gaskiyatasa kuma har ya zuwa dukkan zamani.
101
Zan yi waƙar tausayi da hukunci;
gare ka, ya Ubangiji, zan yi waƙar yabo.
Zan yi biyayya game da azanci ta hanya kammalalliya.
Yaushe ne za ka zo gare ni?
Zan kiyaye mutuncina
da cikakkiyar zuciya.
Ba zan dubi mummunan abu ba.
Na tsargi ayyukan masu kaucewa;
ba za su ɗafe mini ba.
Muguwar zuciya za ta rabu dani;
ba zan san wani mugun abu ba.
Duk wanda ya zagi ɗan'uwansa a asirce
sai in halaka shi.
Ba zan jure mai girman dia da mai alfarma ba.
Idona zai kasance a kan masu gaskiya na cikin ƙasa,
domin su zauna tare da ni;
wanda ke bin kyakkyawar hanya
zai yi mini hidima.
Wanda ke aikata yaudara
ba zai zauna a gidana ba;
maƙaryaci ba zai zauna
ina ganinsa ba.
Kullum safiya sai na halaka dukkan miyagun ƙasar,
in yanke dukkan masu aikata mutnta daga birnin Ubangiji.
102
Ka ji addu'ata, ya Ubangiji,
kukana yă zo gare ka!
Kada ka ɓiye mini fuskarka daga gare ka
a kwanakin wahalata.
Ka kasa kunne gare ni;
ka amsa mini da hanzari a kwanakin da zan yi kira.
Domin kwanakina suna ƙarewa kamar hayaƙi,
ƙasusuwana kuma suna ƙonewa kamar murhu.
An buge zuciyata kamar ciyawa, ta kuwa bushe;
domin na mance cin abincina/ burodina.
Saboda ƙarar nishina
ƙasusuwana sun manne a jikin tsokakina.
Kamar kwasakwasar daji na ke,
na zama mujiya ta cikin kangaye.
Ina dubawa,
na zama kamar gwara makaɗaiciya a kan ɗaki.
Magabtana suna zagina wuni zubur;
waɗanda ke yi mini tsananin ƙiyayya suna zagina.
Domin na ci toka kamar burodi,
na kuma garwaya abin da na ke sha da hawaye
saboda haushinka da hushinka;
domin ka ɗauke ni, ka jefad da ni.
Kwanakina sun zama kamar inuwa da ke ƙarewa;
na kuma ƙaiƙashe kamar ciyawa.
Amma kai, ya Ubangiji, za ka tabbata har abada;
tunawa da kai kuwa ai wanzu a dukkan zamani.
Za ka tashi ka ji tausayin Sihiyona;
domin lokacin a ji tausayinta ya yi;
kai, lokacin da aka ƙayyade ma dai ya yi.
Domin bayinka suna jin daɗin duwatsunta,
suna kuma jin juyayin turɓayatata.
Saboda haka al'ummai za su ji tsoron sunana Ubangiji;
dukkan sarakunana ƙasa kuma za su ji tsoron ɗaukakarka.
Domin Ubangiji ne ya gina Sihiyona;
ya bayyana a cikin ɗaukakatasa;
ya saurari addu'ar matalauta,
bai kuwa raina addu'arsu ba.
Za a rubuta wannan saboda zamani mai zuwa.
Mutanen da za a hilitta su za su yabi Ubangiji;
domin ya duba daga can bisan tsattsaran wurinsa;
daga sama ne Allah ya dubo ƙasa,
don yă ji waƙar ɗaurarre;
yă kwance waɗanda aka tanada wa kisa;
don mutane su faɗi sunan Ubangiji a Sihiyona,
da kuma yabonsa a Urushalima,
sa'ad da mutane suka taru,
masarautu kuma su bauta wa Ubangiji.
Ya raunana ƙarfina a kan hanya;
ya gajarta kwanana.
Na ce, "Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina/ yayina.
Shekarunka duk kowane zamani ne."
Tun da can ka sa harsashin duniya,
sammai kuma aikin hannunka ne.
Za su halaka, amma kai za ka wanzu;
kai, dukkan mutane za su tsufa kamar tufa.
Za ka sanya su kamar tufafi, za su kuwa sāke;
amma kai kana nan, ba ka da iyakar shekaru.
"Ya'yan baranka za su ci gaba;
za a kuma kafa zuriyarsu a gabanka.
103
Ka yabi Ubangiji, yā kai raina;
da dukkan waɗanda ku ke jikina,
ku yabi tsattsarkan sunansa.
Ka yabi Ubangiji, yā kai raina,
kada ka mance dadukkan amfanninsa;
shi ke gafarta dukkan miyagun ayyukanku;
shi ke warkad da dukkan cutukankau;
shi ke kuɓutad da rayukanku daga halaka;
shi ke naɗa ka da alherin ƙauna da tsananin tausayi;
shi ke ƙosad da kai da kyawawan abubuwa.
Saboda haka a ke sabunta ƙuruciyarka kamar gaggafa.
Ubangiji yana zartad da ayyukan gaskiya
da hukunci ga dukkan waɗanda ke matse.
Ya sanad da Musa hanyoyinsa,
ayyukansa kuma ga Bani Isra'ila.
Ubangiji mai tausayi ne ƙwarai, kuma mai alheri;
ba shi da saurin hushi, mai yalwar rahama ne kuwa.
Ba zai yi tankiya kullum ba,
ba kuwa zai tsare hushinsa har abada ba.
Bai yi komai da mu ba bisa ga zunubammu,
bai kuma saka mana bisa ga miyagun ayyukammu ba.
Domin kamar yadda sama ta ke birbishin duniya,
haka girman tausayinsa ya ke ga masu tsoronsa;
kamar yadda gabas ke nesa da yamma,
haka yă kau da laifuffukammu daga gare mu.
Kamar yadda uba ke tausayin 'ya'yansa,
haka Ubangilji ke jin tausayin masu jin tsoronsa.
Domin ya san ginimmu;
ya tuna mu turɓaya ne.
Mutun kam, kwanakinsa kamar ciyawa ne,
kamar furen jeji, haka zamansa ya ke;
domin iska ta kan kaɗa/ wuce/ ta kansa, sai ya kan shuɗe
wurin nasa kuwa ba zai ƙara tunawa da shi ba.
Amma alherin Ubangiji tun fil'azal ya ke, har abada kuma ya ke,
gare su su da ke tsoronsa;
gaskiyatasa kuma har kan jikanu ta ke,
ga waɗanda suka kiyaye alkawarinsa,
da kuma waɗanda ke tuna da ka'idodinsa su ke aikata su.
Ubangiji ya kafa gadonsa na sarauta a sama,
sarautarsa kuwa ita ke ido da komai.
Ya ku mala'ikun Ubangiji, ku yabe shi,
ku masu ƙarfi, masu cika maganatasa,
kuna sauraron muryatasa.
Ku yabi Ubangiji, ya ku rundunarsa,
ya ku masu yi masa hidima,
masu aikata abin da ya ke so.
Ku yabi Ubangiji, ya ku aikin hannunsa,
a dukkan wurare acikin mulkinsa.
Ka yabi Ubangiji,
ya kai raina.
104
Ku yabi Ubangiji, ya kai raina!
Ya Ubangiji Allahna, kai mai girma ne ƙwarai!
Mai ɗaukaka ne, mai iko,
ka lulluɓe jikinka da haske kamar da tufa,
ka miƙa sammai kamar labule,
ka kafa al'amudan ɗakunanka a cikin ruwa,
kana mai da gajimare karusanka,
kana tafiya a kan fukafukan iska,
kana sa iska ta zama manzonka,
masu yi maka hidima kuwa wuta mai ci.
Kai ne ka kafa harsashin duniya
don kada ta jijjiga har abada.
Kai ne ka rufe ta da teku, kamar da riga/ tufa;
ruwa ya tsaya a bisan duwatsu.
Sun gudu da jin tsawarka;
sun hanzarta sun tafi da jin aradunka.
Sun hau dutse sun tafi,
sun kuma bi kwari sun tafi wurin da ka tanada/ shirya/ musu.
Ka sa iyaka don kada su ƙetare,
don kada su sake juyowa su rufe duniya.
Yana aiko da idon ruwa a cikin kwarurruka;
suna gudu a jikin duwatsu,
suna shayad da kowace dabbar jeji;
jakunan jeji suna kau da ƙishirwarsu.
Tsuntsaye ma a kusa da su su ke yin sheƙarsu;
suna waƙa a cikin rassa.
Yana ba duwatsu ruwa daga ɗakunansa;
ƙasa ta wadatu da amfanin ayyukanka.
Shi ya ke sa ciyawa ta tsira saboda dabbobi,
da kuma ganyaye saboda amfani ga mutane,
don ya fid da abinci daga ƙasa,
da kuma ruwan inabi mai sa mutane farinciki,
da kuma mai don fuskarsa ta yi haske,
da abinci mai ƙarfafa zuciyar mutane.
An ƙosad da itatuwan Ubangiji,
rimayen Lebanon da ya dasa.
Inda tsuntsaye ke yin sheƙarsu;
shamuwa kam iccen fir ne gidanta.
Dogayen duwatsu na awakin daji ne;
duwatsu su ne mafakar zomaye/ agwada.
Ya sanya wata saboda lokatai;
rana ta san lokacin faɗuwa tata.
Kai ke yin duhu, sai dare yă yi,
a sa'an nan dukkan namun jeji ke fitowa.
Kwiyakwiyen zakoki su kan yi ruri saboda abincinsu,
suna neman abincinsu daga wurin Allah.
Rana ta kan fito, su kan gudu
su ɓuya a makwancinsu.
Mutum ya kan tafi wurin aikinsa,
yana kan aikinsa har la'asar.
Ya Ubangiji, yaya yawan aikinka ya ke!
Duka game da hikima ka yi su;
duniya cike ta ke da kayanka.
Can ga teku, mai girma, mai faɗi;
masu jan ciki a ciki ba sa ƙidayuwa;
manyan dabbobi da ƙanana duka biyu.
A can jirage ke tafiya;
akwai dodo wanda ka halitta don ya zauna a can.
Waɗannan duka suna jiranka,
don ka ba su abincinsu a kan kari.
Abin da ka ba su, shi za su tara;
ka kan buɗe hannunka;
su kan wadatu da kyakkyawan abu.
Ka kan ɓoye fuskarka, su wahala;
ka kan ɗauke numfashinka su mutu,
su koma, su zama ƙasa kamar dā.
Ka kan aikko da Ruhunka,
a kan halicce su;
ka kan sabuta fuskar ƙasa.
Ɗaukakar Ubangiji tă tabbata har abada,
Ubangiji yă yi murna da aikinsa.
Wanda ke duba duniya, ta ke raurawa,
ya kan taɓa duwatsu, sai su yi hayaƙi!
Zan yi wa Ubangiji waƙa muddar ina raye;
zan yi wa Allahn waƙar yabo tun ina nan.
Bari yabona ya yi masa daɗi;
zan yi farinciki game da Ubangiji.
Bari a halaka masu zunubi daga duniya,
bari miyagu su zama ba sauransu.
Ka yabi Ubangiji, ya kai raina!
Ku yabi Ubangiji!
105
Ku yi wa Ubangiji godiya, ku kira sunansa;
ku sanad da ayyukansa a cikin mutane.
Ku yi masa waƙa; ku yi masa waƙoƙin yabo;
ku faɗi dukkan abubuwansa na mamaki.
Ku ɗaukaka sunansa tsattsarka;
bari zukatan masu neman Ubangiji su yi farinciki!
Ku nemi Ubangiji da ƙarfinsa,
ku nemi fuskatasa har abada.
Ku tuna da ayyukansa masu bam mamaki waɗanda ya yi,
da abubuwansa na mamaki,
da hukuncin da ya yi da bakinsa,
ya ku 'ya'yan baransa Ibrahim,
ku 'ya'yan Yakubu, zaɓaɓɓunsa.
Shi ne fa Ubangiji Allahmmu;
hukuncinsa na kan duniya duka.
Yana tuna da alkawarinsa har abada,
maganad da ya umarci zamanai dubu,
alkawari da ya yi da Ibrahim,
da kuma rantsuwarsa ga Isiyaku,
ya kuma ƙara tabbatad da ita ga Yakubu a kan doka,
ga Bani Israila saboda alkawari na har abada,
yana cewa, "Kai zan ba ƙasar Kan'ana
wato kuka gadonka."
Sa'ad da su ke mutane kaɗan,
kai, su kaɗan ne ƙwarai,
kuma baƙi ne a cikinta,
suna yawo suna bin kan al'umma-al-umma,
daga wata masarauta zuwa wurin masu mutane,
bai bar wani mutum ya yi musu mugunta ba;
kai, har ma ya tsawata wa sarakuna saboda su,
yana cewa "Kada ku taɓa shafaffuna,
kada kuma ku yi wa annabawana wata mugunta."
Sai ya auko da yunwa ƙasar,
ya hana dukkan hatsi yi,
ya aiki mutum a gabansu,
an sai da Yusufu a kan bauta.
Sun yi wa ƙafafunsa ciwo da mari,
an ɗaure shi da sarƙa;
sai lokacin da maganarsa ta cika
Maganar Ubangiji ta jarraba shi.
Sarki ya aika an kwance shi,
har ma mai mulkin mutane,
she ne ya sau/ sake/ shi;
ya sanya shi sugaban gidansa,
kuma mai iko da dukkan kayansa,
yă ɗaure 'ya'yan/ 'yan/ sarki in ya ga dama
ya kuma koyawa fadawansa hikima.
Bani Isra'ila ma sun zo Masar;
Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Hamu.
Ya ƙara mutanensa ƙwarai,
ya sa suka fi abokan hamayyarsu ƙarfi.
Ya juyad da zukatansu su ƙi mutanensa,
su aikata mugunta ga bayinsa.
Ya aiki bawansa Musa,
da kuma Haruna da ya zaɓa.
Suna riƙe da alamominsa,
da abubuwan mamaki a ƙasar Hamu.
Ya aiko da duhu, ya sa duhu ya zauna,
ba su kuwa yi wa maganarsa tawaye ba.
Ya mai da ruwansu jini,
ya kuma kashe kifayensu.
Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,
har ɗakunana sarakunansu.
Ya yi magana, sai ga tarin ƙudaje,
da ƙarƙwata ta ko'ina.
Ya sauko masu da ƙanƙara a maimakon ruwa,
da wuta mai ruruwa a ƙasarsu.
Ya buge/ sharɓe/ inabinsu kuma da itatuwan ɓaurensu,
ya karya itatuwan iyakarsu.
Ya yi magana, fara ta sauko,
da kuma ɗango ba iyaka;
sun cinye kowane ganye a ƙasarsu,
sun kuma cinye amfanin ƙasarsu.
Ya kuma bubbuge dukkan 'ya'yam fari a ƙasarsu,
asalin dukkan ƙarfinsu.
Ya fito da su da azurfa da zinariya,
ba wani kumama a cikin kabilarsa.
Masar ta yi murna sa'ad da suka tafi,
domin tsoronsu ya kama su.
Ya baza gajimare saboda rufewa,
da kuma wuta tă ba da haske dad dare.
Sun tambaya/ roƙa/, ya aiko/ kawo/ da fakara,
ya kuma ƙosad da su burodin sama/ burodi daga sama.
Ya buɗe dutse, ruwa ya ɓuɓɓugo;
ya yi gudu kamar kogi a ƙaiƙasussun wurare.
Domin ya tuna ta tsattsarkar maganarsa,
da kuja baransa Ibrahim.
Ya fito da mutanensu da murna,
da zaɓaɓɓunsa game da waƙa.
Ya ba su ƙasashen al'ummai;
suka ɗebi kayan mutanen suka mallaka,
domin su kiyaye dokokinsa,
su tsare shari'o'insa.
Ku yabi Ubangij.
106
Ku yabi Ubangiji!
Ku gode wa Ubangiji, domin shi managarci ne;
domin alherinsa na jurewa har abada.
Wa ke iya faɗan manyan ayukan Ubangiji,
ko kuwa ya nuna dukkan yabonsa?
Albarka ta tabbata ga masu kiyaye hukkunci,
da wanda ke aikata gaskiya a kowane lokaci.
Ka tuna da ni, ya Ubangiji,
da ƙaunand da ka ke yi wa mutanenka;
ka kula da ni mana ka cece ni/ da cetonka,
don in ga arzikin zaɓaɓɓenka;
kuma in yi farincikin al'ummarka;
in kuma sami ɗaukaka game da gādonka.
Mun yi zunubi, mu da kakannimmu;
mun yi mugun aiki;
mun yi aikin mugunta.
Kakannimmu ba su fahinci abubuwanka na mamaki a Masar ba;
ba su tuna yawan tausayinka ba;
amma sai suka yi tawaye a cikin teku, wato a Bahar Maliya.
Duk da haka kuwa ya kuɓutad da su saboda sunansa,
don ya sa a san ƙaƙƙarfan ikonsa.
Ya kuma tsawata wa Bahar Maliya sai kuwa ya bushe;
ta haka ya ja su ta cikin ƙwaryar bahar ɗin, kace a cikin jeji.
Ya kuma cece su daga hannun maƙiyinsu,
ya kuɓutad da su daga abokan gaba.
Ruwa kuma ya sa kan abokan hamayyarsu;
ba ko ɗayansu da ya rage.
Sa'an nan ne suka gaskata da maganarsa;
suka yi waƙoƙin yabonsa.
Nandanan kuwa sai suka mance da ayyukansa;
ba su jira shawararsa ba.
Amma sai suka yi ta jaraba ƙwarai a cikin jeji,
suka gwada Allah a cikin hamada;
sai kuwa ya biya musu bukatarsu,
amma sai ya raunana zukatansu.
Suka kuma ji ƙyashin Musa a cikin sansani
da kuma Haruna tsattsarkan Ubangiji,
sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datana,
ta binne rundunar Abirama.
Aka hura wuta a sansaninsu;
wutar ta ƙone miyagu.
Suka yi ɗan maraƙi a Huraba
suka yi wa sura ƙeraniya sujada.
Ta haka sai suka musanya ɗaukakarsu
da kamannin sa mai cin ciyawa.
Sun mance da Allah Macecinsu
wanda ya yi manyan abubuwa a Masar,
da ayyuka masu bam mamaki a ƙasar Hamu,
da kuma abubuwa masu ban tsoro a kusa da Bahar Maliya.
Saboda haka ya ce zai halaka su,
ashe Musa zaɓaɓɓensa
bai tsaya a gabansa ba a ....
don ya juya/ huce/ hushinsa don kada ya halaka su.
Kai, sun raina wannan ƙasa ta yanzu,
ba su gaskata da maganatasa ba.
Amma sai suka yi gunaguni a cikin ɗakunansu/ bukkokinsu,
ba su saurari Maganar Ubangiji ba.
Saboda haka ya cira hannunsa a kansu
don ya wantsala su a jeji
yă kuma watsad da zuriyarsu a cikin al'ummai,
yă watsa su a ƙasashe.
Har wa yau kuma sai suka gama kai da Ba'albora,
suka ci hadayar matattu;
ta haka suka tsokani Allah
ya yi hushi, wato ayyukansu,
sai kuma aloba ta sauko musu.
Sai kuma Finahasa ya tsaya ya yi shari'a,
sai kuma aka tsai da alobar.
Wannan kuwa an ɗaukaka masa a kan aikin gaskiya ne
har ya zuwa a kan dukkan zuriya har abada.
Sun kuma husatad da shi a ruwan Maribaha,
har ya yi hushi da Musa saboda su;
domin sun yi wa ruhunsa tawaye,
sai kuma ya yi magana marar daɗi da bakinsa.
Ba su halaka mutanen ba
kamar yadda Ubangiji ya umarce su,
sai dai suka garwaya da al'ummai,
suka koyi ayyukansu.
Suka kuma bauta wa gumakansu,
waɗanda suka zame musu tarko.
Kai, har ma sun miƙa 'ya'yansu maza
da 'ya'yansu mata ga aljannu;
sun zub da jini ba da hakki ba,
wato jinin 'ya'yansu maza da 'ya'aynsu mata,
waɗanda suka yanka suka miƙa ga gumakan Kan'ana;
ƙasar sai ta ƙazantu da jini.
Ta haka ayyukansu suka ƙazantad da su
suka nuna bijirewa da abubuwan da suka aikata.
Saboda haka hushin Ubangiji ya kasu akan mutanensa,
sai kuma ya ƙi waɗanda ya gada;
sai ya bashe su ga/ sa su a hannun/ al'ummai;
waɗanda suka ƙi su ɗin nan
kuma sia suka yi mulki a kansu.
Magabtansu kuma suka matsa musu lamba,
sai aka riƙa iko da su a hannunsu.
Sau da yawa yana cetonsu,
amma su masu tawaye ne a zuciyarsu,
an kuwa ƙasƙantad a su saboda mugun aikinsu.
Duk da haka dai sai ya dubi baƙincikinsu
sa'ad da ya ji kukansu.
Sai ya tuna alkawarinsa a kansu,
ya kuma yafe su bisa ga yalwar rahamarsa.
Ya sa suka zama ababan a ji tausayi
dukkansu su da aka kama a bauta.
Ka kuɓutad da mu, ya Ubangiji Allahmmu,
ka raba mu daga cikin al'ummai,
don mu yi wa tsattsakan sunan nan naka godiya
mu kuma ci nasara a yabonka.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allahn Bani Isra'ila,
tun fil'azal, har ya zuwa har abada!
Dukkan mutane su ce "Amin!"
Ku yabi Ubangiji!
107
Ku gode wa Ubangiji, don mai alheri ne,
domin rahamarsa mai ɗorewa ce har abada.
Kuɓutattun Ubangii su faɗi haka,
waɗanda ya kuɓutar daga hannun abokan hamayya.
Ya fid da su daga ƙasashen,
daga gabas da yamma,
daga kudu da arewa.
Sun yi yawo a cikin jeji ta hanyar hamade,
ba su sami garin zama ba;
sun ji yunwa da ƙishriwa,
harsun suma.
Sa'an nan suka yi kuka ga Ubangiji a cikin wahalarsu,
ya kuwa tsamo su daga baƙincikinsu;
ya kuma ja su ta miƙaƙƙiyar hanya,
don su je cikin birni.
Mutane su yabi Ubangiji mana saboda alherinsa,
da kuma ayyukansa na bam mamaki ga bil'adam.
Domin yana ƙosad da matsukaci [?],
yana kuma cika marashi da kyawawan abubuwa.
Kamar waɗanda suka zauna a cikin duhu da bakin halaka,
waɗanda ke ɗaure da tsananin wahala da kuma ƙarfe,
domin sun tayar wa Maganar Allah,
sun kuma haure shawarar Mafi Ɗaukaka.
Saboda haka sai ya sauko da zukatansu tare da whala;
sun faɗi, kuma ba mataimaki.
Sa'an nan sai suka yi kuka ga Ubangiji a cikin wahalarsu,
ya kuma cece su daga baƙincikinsu.
Ya fito da su daga cikin duhu da bakin halaka,
ya kuma raba rundunoninsu daban daban.
Mutane su yabi Ubangiji mana saboda alherinsa
da kuma ayyukansa na bam mamaki ga bil'adam.
Domin ya kakkarya ƙofofin tagulla,
ya kuma karya ƙarafu.
Wawaye sun cutu saboda laifinsu
da kuma miyagun ayyukansu;
ransu ya ƙi kowane irin abinci/ nama,
sun kusaci ƙofofin halaka.
Sa'an nan suna kuka ga Ubangiji a cikin wahalarsu,
yana kuwa kuɓutad da su a cikin baƙincikinsu;
yana aikowa da maganatasa yana warkad da su,
yana kuma cetonsu daga halakarsu.
Mutane su yabi Ubangiji mana saboda alherinsa,
da kuma ayyukansa na bam mamaki ga bil'adam.
Su ba da baikon godiya,
su kuma faɗi ayyukansa da waƙa!
Su masu tafiya cikin bahar a jirage,
masu yin hidimomi a cikin manya manyan bahar;
waɗaannan su ne ke ganin ayyukan Ubangiji,
da kuma abubuwansa na mamaki a cikin teku.
Domin yana umartar iskar hadiri,
yana kuma ta da ita,
wato wadda ta ke ta da raƙuman ruwa a nan.
Suna hawa sama, suna kuma sauka har ƙasa;
sukan narke saboda wahala;
suna kaiwa suna kawowa,
suna tangaɗi kamar bugagge,
suna kuwa gab da batan basira.
Sa'an nan suna kuka ga Ubangiji a cikin wahalarsu,
yana kuwa tsamo su daga cikin baƙincikinsu.
Yana sa hadiri ya yi shiru,
har ma raƙuman ruwan su yi shiru.
Sa'an nan ne za su yi murna domin sun yi shiru;
saboda haka yana kawo su sama inda za su kasance.
Mutane su yabi Ubangiji mana saboda alherinsa,
da kuma ayyukansa masu bam mamaki ga bil'adam!
Su kuma ɗaukaka shi a cikin taron mutane,
mu kuma yabe shi a wurin zaman manya.
Mai da koguna su zama daji,
ƙoramai kuma su zama ƙaiƙasassu;
ƙasa mai ni'ima tă zama hamada mai kanwa
saboda mugun aikin mutane da ke zauna a cikinta.
Yana mai da jeji ya zama ruwa ya mamaye shi,
ƙaiƙasasshiyar ƙasa kuma ta zama mai ƙoramai.
A nan ya ke zaunad da mayunwata
don su shirya birnin zama;
su shuka gonaki, su dasa garkar inabi,
su sami itatuwan turare.
Su ma yana yi musu albarka,
har suna yaɗuwa ƙwarai;
dabbobinsu kuwa ba ya jarabtarsu da cuta.
Har wa yau kuma ana rage su,
ana ƙasƙantad da su
ta tsanantawa da wahala da baƙinciki,
ya jibga wa sarakuna wulakanci
ya sa su suna yawo a cikin kangaye, inda ba hanya;
amma ya kau da mai bukata daga wahala,
ya yi masa zuriya kamar garken tumaki.
Mai gaskiya zai gan shi, yă yi farinciki;
dukkan muganta kuma za ta daina.
Duk mai hikima zasi kula da waɗannan abubuwa;
kuma za su duba alherin Ubangiji.
108
Ya Ubangiji, zuciyata a zaune ta ke,
Zan yi waƙa, kai, zan yi waƙar yabo,
wato da ɗakakata.
Ku farka mana, garaya/ kuntigi/ da molo.
Ni kaina zan farka da wuri.
Zan gode maka, ya Ubangiji, a cikin mutane.
kuma zan yi waƙoƙin yabo gare ka a cikin al'ummai.
Domin tausayinka mai yawa ne a birbishin sammai,
gaskiyarka kuma tana isa sammai.
Ka ɗaukaka, ya Allah, birbishin sammai!
Ɗauakarka kuma birbishin ƙasa/ duniya/ duka.
Don a kuɓutad da ƙaunataccenka;
ka kuɓutar, da hannunka na dama,
ka kuma amsa mana.
Allah ya yi magana a cikin tsarkakatasa:
"Zan yi farinciki; zan rabe ƙasar Shecema,
in raba ƙasar Sakkwato.
Gilida tawa ce; ƙasar Manassaha tawa ce;
ta Afraimu ma wurin tsarona ne;
Ƙasar Yahuda sandar girmana ce.
Muwaba ...
a kan Iduma zan tuƙe takalmana;
a kan Filistiya zan yi tsawa."
Wa zai kawo ni birnin da aka shinge?
Wanene ya jawo nil Iduma?
Ashe ba kai ne ka jefad da mu ba, ya Allah?
Kai kuwa ba ka wuce gaban da rundunarmu ba, ya Allah.
Ka taimake mu a kan magabta,
domin taimakon mutum na banza ne.
Za ka yi abin kirki ta kan Allah;
domin shi ne ke tattake magabtammu.
109
Kada ka hana amincinka,
ya Allah, wanda na ke yabo.
domin sun buɗe mini bakin mugunta da bakin zamba;
dun yayyanka mini ƙarairai.
Sn kuma kewaye ni da maganganun ƙiyayya,
sun yi faɗa da ni ba wani dalili.
Domin waɗanda na ke ƙauna su ne magabtana;
amma na ba da kaina ga addu'a.
Sun kuma rama mini alheri da mugunta,
sun yi ƙiyayya saboda soyayyar da na nuna.
Ka ɗora mugun mutum a kansa;
ka kuma sa magabci ya tsaya a hannunsa na dama.
In an yi masa shari'a, yă zama mai laifi;
addu'arsa a juya ta ta zama zunubi.
Kwanakinsa su yi ƙaranci,
wani ya ɗauki matsayinsa.
'Ya'yansa su zama marayu,
matatasa kuwa gwauruwa.
'Ya'yansa su zama 'yan iska, su yi bara/ roƙo,
su nemi abincinsu a wurarensu ba da kowa.
Mai zalumci yă riƙe duk abin da ya ke da shi;
baƙi kuma su ɓata aikinsa.
Kada a sami wani mai jin tausayinsa,
kada kuma a sami wani mai jin tausayin marayun 'ya'yansa.
A yanke zuriyarsa;
sunansu ya ɓace a cikin zamani mai zuwa/ zuriyar gaba.
A tuna da mutungar kakanninsa ga Ubangiji,
kada kuwa a shafe zunuban uwatasa.
Su kasance a gaban Ubangiji koyaushe;
don ya shafe sunansu aduniya.
Domin bai tuna yin tausayi ba,
sai ya tsananta wa gajiyayye da mai bukata,
yana ba su tsoro da kisa.
Kai, yana son la'ana;
ta kuwa sauko a kansa.
Ba ya jin daɗin sa albarka;
sai kuwa ta yi nisa da shi.
Ya kum tufad da kansa da la'ana kamar tufafi,
ta kuwa ratsa jikinsa kamar ruwa,
kamar mai/ kitse/ a cikin ƙasusuwansa.
Ya zame masa kamar tufafin da ya sa da ɗamarar,
da ya ke ɗamara da ita a koyaushe.
Wannan shi ne sakamakon magabtana daga wurin Ubangiji,
da kuma na masu yi mini baƙaƙen maganganu.
Amma ka kula da ni, ya Allah Ubangiji
saboda sunanka;
domin alherinka mai kyau ne,
ka cece ni.
Domin ni gajiyayye ne,
kuma mai nema ne;
zuciyata kuma ta ɓaci har can ciki.
Na tafi, kamar inuwar da ta ƙare;
ana ta jujjuya ni sama da ƙasa kamar fara.
Gwiwonina sun yi sanyi
saboda rahsin cin abinci;
naman jikina kuma ba shi da kitse.
Na zame musu abin kyama;
in sun gan ni, sai su girgiza kansu.
Ka taimake ni ma, ya Ubangiji Allah.
ka cece ni mana bisa ga rahamarka.
Don su san wannan shi ne hannunka,
cewa kai Ubangiji, kai ne ka yi haka.
Bari dai su zaga, amma ka kă yi albarka.
in sun tashi za su ji kunya,
amma bawanka zai yi farinciki.
Bari magabtana a lulluɓe su da wulakanci;
su rufe kansu da kunyar kansu kamar da mayafi.
Zan yi godiya mai yawa/ babban godiya/ ga Ubangiji da bakina;
kai, zan gode masa a cikin taron mutane.
Domin zai tsaya a hannun daman mai bukata,
don ya kuɓutad da shi daga masu hukunta shi.
110
Ubangiji a ce da ubangijina,
"Zauna a hannun damana,
sai na sa ka tattake magabtanka."
Ubangiji zai aiko da sandanka
na ƙarfi daga Sihiyona
Ka yi mulki a tsakan abokan gabanka.
Mutanenka suna ba da kansu da raɗin kansu
a kwanakin ikonka, a cikin kyan tsarkaka.
Tuna daga asuba/ dare/ kana da raɓon/ yawun/ bakina.
Ubangiji ya rantse
ba kuwa zai yafe ba
"Kai malami ne na har abada
kwatankwacin Malkizada."
Ubangiji a hannunka na dama;
zai buge sarakuna a kwanakin hushinsa.
Zai yi hukunci a cikin al-ummai,
zai cika wurare da gawaurwaki;
zai buge kawuna a ƙasashe da yawa.
Zai sha ruwan rafin da ke kan hanya,
saboda haka zai ɗaga kansa.
111
Ku yabi Ubangiji.
Zan gode wa Ubangiji
da dukkan zuciyata,
a cikin majalisar masu gaskiya,
da kuma cikin taron jama'a.
Ayyukan Ubangiji manya-manya ne,
masu yin murna da su kuwa duka suna nemansu.
Ayyukansa ɗaukaka ne da iko,
gaskiyatasa kuwa tana jurewa har abada.
Ya sa ana tunawa da ayyukansa masu bam mamaki;
Ubangiji mai alheri ne, mai tsananin tausayi.
Ya ba masu tsoronsa abinci;
zai riƙa tunawa da alkawinsa har abada.
Ya nuna wa mutanensa ƙarfin ayyukansa,
ta ba su gadon al'ummai da ya yi.
Ayyukan hannunsa su ne gaskiya da hukunci;
dokokinsa duk tabbatattu ne;
an kafa su har abada abadin,
an yi su ne a cikin gaskiya da tsai da magana.
Ya aiko wa jama'atasa ceto;
ya umarci alkawarinsa har abada.
Sunansa tsattsarka ne,
kuma abin tsarkakewa.
Tsoron Ubangiji shi ne farkon hikima;
dukkan masu aikata su suna da kyakkyawar fahimta.
Yabonsa yana jurewa har abada.
112
Ku yabi Ubangiji.
Albarka ta tabbata ga masu tsoron Ubangiji,
waɗanda suka murna ƙwarai da umarninsa.
Zuriyarsa za ta zama mai ƙarfi a duniya;
za a yi wa zuriyar masu gaskiya albarka.
Wadata da dukiya suna gidansa;
gaskiyatasa kuwa za ta wanzu har abada.
Haske na sauko wa mai gaskiya daga cikin duhu;
shi mai alheri ne, mai tsananin tausayi, da gaskiya.
Mai aikata alheri ya ke kuma
ba da aro/ bashi/ yā ji daɗi,
zai sami sakamakonsa a wajen shari'a.
Domin ba zai jijjiga ba har abada;
za a riƙa tunawa da mai gaskiya har abada.
Ba zai ji tsoron miyagun maganganu ba;
zuciyasrsa a tsaye take,
tana gaskatawa da Ubangiji.
Zuciyarsa a kafe ta ke,
ba zai ji tsoro ba,
sai ya biya bukatarsa
game da abokan hamayyarsa.
Ya watsad da dukiyarsa, ya ba masu bukata;
aikin gaskiyarsa yana nan har abada;
za a ɗaukaka gwaninsa da ɗaukaka.
Miyagu za su/ Mugu zai/ gan shi su/ ta yă/ yi baƙinciki;
zai game haƙoransa, ya shuɗe;
bukatar mugu za ta halaka.
113
Ku yabi Ubangiji.
Ku yi yabo, ya ku bayin Ubangiji,
ku yabi sunan Ubangiji.
Yabo ya tabbata ga sunan Ubangiji
tun daga yanzu har ya zuwa har abada.
Tun daga hudowar rana har zuwa faɗuwatata
sai a yabi sunan Ubangiji.
Ubangiji shi ne birbishin dukkan al'ummai,
ɗaukakarsa kuma tana birbishin sammai.
Wanene ke kama da Ubangiji Allahmmu,
wanda ke da kursiyyi a cikin sama,
wanda ke ƙarƙartowa don ya ga abubuwan
da ke sama da waɗanda ke ƙasa?
Yana ta da matalauti daga cikin ƙasa,
yana kuma ɗaga mai bukata daga juji,
don ya haɗa shi da sarakuna,
har ma da sarakunan ƙasarsu.
Yana sa juya ta tsare gida,
ta kuma zama uwar 'ya'ya, mai farinciki.
Ku yabi Ubangiji.
114
Sa'ad da Bani Isra'ila suka fita daga Masar,
wato gidan Yakubu daga mutane masu harshe daban,
Yahuda shi ya zama tsattsarkan wurinsa,
Bani Isra'ila kuma mulkinsa.
Bahar ya gan shi/ gani/ ya gudu,
an kori Urdun.
Duwatsu suka yi tsalle kamar raguna,
ƙananan duwatsu kuma kamar 'ya'yan raguna.
Me ke yi maka ciwo ne, kai teku/ bahar, har ka ke gudu?
Kai kuma Urdun, har ka ke ja da baya?
Ku kuma duwatsu, har ku ke tsatte kamar raguna?
Da ku kuma ƙanana duwatsu
har ku ke tsalle kamar 'ya'yan raguna?
Ki yi makyarkyata, ya ke ƙasa,
a Zatin Ubangiji,
a Zatin Allahn Yakubu,
wanda ya mai da dutse ya zama tafkin ruwa,
mulmulallen dutse kuma ya zama ƙorama.
115
Ba a gare mu ba, ya Ubangiji, ba a gare mu ba,
sai da ka ɗaukaka sunanka,
saboda rahamarka, kuma saboda gaskiyarka.
Har al'ummai su ce,
"To, yanzu ina Allahn nasu?"
Amma Allahmmu a sama ya ke;
ya yi duk abin da ya aikata.
Gumakansu azurfa ce da zinariya,
aikin hannun mutane.
Suna da bakuna, amma ba sa magana;
suna da idanduna, amma ba sa gani.
Suna da kunnuwa, amma ba sa ji;
suna da hanci, amma ba sa sansanawa.
Suna da hannaye, amma ba sa kama wani abu;
suna da ƙafafu, amma ba sa tafiya;
ba sa kuma magana ta maƙogwaronsu.
Waɗanda suka yi su za su zama kamar su;
kai, har ma wanda ya ba da gaskiya gare su.
Ya Bani Isra'ila, ku ba da gaskiya ga Ubangiji.
Shi ne mataimakinsu, kuma garkuwarsu.
Ya ku gidan Haruna, ku gaskata da Ubangiji.
Shi ne mataimakihsu, kuma garkuwarsu.
Ku masu tsoron Ubangiji,
ku ba da gaskiya ga Ubangiji.
Shi ne mataimakinsu, kuma garkuwarsu.
Ubangiji ya kula da mu; zai yi mana albarka;
zai yi wa Bani Isra'ila albarka;
zai yi wa gidan Haruna albarka;
zai yi wa mai tsoron Ubangiji albarka,
manya da ƙananan duka.
Ubangiji yă ƙara ku gaba-gaba,
ku da 'ya'yanku.
Ku ne Allah ya yi wa albarka,
wanda ya halicci sama da ƙasa.
Sammai samman Ubangiji ne,
amma ƙasa kam ya ba bil'adam.
Matattu ba sa yabon Ubangiji,
haka kuma duk wanda ya gangara cikin shiru.
Amma mu za mu yabi Ubangiji
tun daga yanzu har ya zuwa har abada.
Ku yabi Ubangiji.
116
Ina ƙaunar Allah domin ya ji
muryata da roƙona.
Domin ya kasa kunnensa gare ni;
saboda haka zan riƙa kama sunansa muddar ina raye.
Igiyoyin mutuwa sun kewaye ni;
azabar mahalaka kuma ta kama ni;
na sami wahala da baƙinciki.
Sa'an nan sai na kira sunana Ubangiji:
"Ya Allah, na roƙe ka, ka ceci raina."
Ubangiji mai alheri ne,
kuma mai gaskiya;
Kai, Allahmmu mai tausayi ne.
Ubangiji na kiyaye mai sauƙin kai;
a cikin talauci aka goya ni, ya kuwa cece ni.
Ka koma hutunka, ya kai raina;
domin Ubangiji ya maka bajinta.
Domin ka kuɓutad da raina daga mutwa/ halaka,
ka ceci idona daga yin hawaye,
ƙafafuwana kuma daga faɗuwa.
Zan yi biyayya a gaban Ubangiji
a hanyar rayayyu.
Na gaskata, domin zan yi magana,
"An jarabce ni da cuta ƙwarai";
A cikin hanzarina na ce,
"Dukkan mutane maƙaryata ne."
Me zan ba Ubangiji
saboda dukkan alherin da ya yi mini?
Zan sha ƙoƙon ceto
in kira sunan Ubangiji,
zan cika wa'adina game da Ubangiji
a gaban dukkan mutanensa kuwa.
Mutuwar tsarkakan Ubangiji
kyakkyawan abu ne a idonsa.
Ya Ubangiji, hakika ni bawanka ne;
ni bawanka ne, ɗan kuyangarka.
Ka kwance mini ɗaurina.
Zan miƙa maka hadayar godiya,
zan kuma kira sunan Ubangiji.
Zan cika wa'adina game da Ubangiji
a gaban dukkan mutanensa kuwa,
a cikin ɗakunan gidan Ubangiji,
a tsakiyarki, ya ke Urushalima.
Ku yabi Ubangiji.
117
Ku yabi Ubangiji, ya ku dukkan al'ummai.
Ku yi masa waƙar yabo, ya ku dukkan mutane.
Domin rahamarsa babba ce gare mu,
kuma gaskiyar Ubangiji tana jurewa har abada.
Ku yabi Ubangiji.
118
Ku gode wa Ubangiji mana,
domin shi mai alheri ne;
domin alherinsa yana wanzuwa har abada.
Bari yanzu kuma Bani Isra'ila su ce,
"Alherinsa na wanzuwa har abada."
Bari kuma gidan Haruna yanzu su ce,
"Alherinsa yana wanzuwa har abada."
Bari masu tsoron Ubangiji yanzu su ce,
"Alherinsa na wanzuwa har abada."
Daga cikin baƙincikina na kama sunan Ubangiji;
Ubangiji ya amsa mini, ya kuwa sanya ni a babban wuri.
Ubangiji yana wajena, ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?
Ubangiji a wajena ya ke,
a cikin masu taimakona;
saboda haka zan ga biyan bukatata
a cikin waɗanda suka ƙi ni.
Ya fi kyau a amince da Ubangiji
a kan amince da mutun.
Ya fi kyau a amince da Ubangiji
a kan a amince da sarakuna.
Dukkan al'ummai sun yi mini geme;
amma da sunana Ubangiji
zan yarɓad da su.
Duk sun yi mini geme, kai, sun fa kewaye ni;
da sunan Ubangiji zan yarɓad da su.
Sun kewaye ni sun yi mini zuma,
an shafe su kamar wutar daji;
da sunan Ubangiji zan yarɓad da su.
Ka jarabce ni da cutuwa don in kasa,
amma Ubangiji ya taimake ni.
Ubangiji shi ne ƙarfina, kuma abin waƙata;
kuma ya zama macecina.
Muryar fainciki da ceto
tana ɗakunan masu gaskiya:
"Hannun daman Ubangiji yana aikata jarumtaka.
hannun daman Ubangiji ɗaukakakke ne,
hannun daman Ubangiji yana aikata jarunta."
Ba zan mutu ba, amma zan/ sai dai in/ rayu,
in faɗi ayyukan Ubangiji.
Ubangiji ya tsarkake ni da cutuwa,
amma bai miƙa ni ga mutuwa ba.
Ka buɗe mini ƙofofin aikin gaskiya,
zan shige su
zan gode wa Ubangiji.
Wannan ita ce ƙofar Ubangiji;
mai gaskiya zai shige ta.
Zan gode maka, domin ka amsa mini
ka kuma zama macecina.
Dutsen da magina suka ƙi
ya zama babban dutsen harsashin gini.
Wannan aikin Ubangiji ne;
abin mamaki ne a idanummu.
Wanna ita ce ranar da Ubangiji ya yi;
za mu farinciki mu yi murna a cikinta.
Mun roƙe ka, ya Ubangiji,
ka yi ceto yanzu.
Mun roƙe ka, ya Ubanhgiji,
ka aiko da wadata yanzu.
Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.
Mun yi maka albarka daga gidan Ubangiji.
Ubangiji Allah ne,
ya kuwa ba mu haske.
Ku ɗaure abin hadaya da igiya,
a kan wurin yim baiko.
Kai ne Allahna, kuma zan gode maka;
kai ne Allahna, zan ɗaukaka ka.
Ku gode wa Ubangiji mana,
domin shi mai alheri ne;
domin alherinsa yana wanzuwa har abada.
119
א
Albarka ta tabbata ga waɗanda ke kamilallu a cikin hanyar addini,
masu bin dokokin Ubangiji.
Albarka ta tabbata ga masu kiyaye shaidatasa,
masu nemansa da dukkan zuciya;
ba sa yin rashin gaskiya kuwa;
suna bin hanyoyinsa.
Ka umarce mu da dokokinka
don mu bi su da himma.
Ina ma a ce hanyoyina a tabbace su ke
don im bi kiyaye dokokinka.
Sa'an nan ba zan kunyata ba,
in na sami yin biyayya ga dukkan umarninka.
Zan gode maka da gaskatawa a zuci,
sa'ad da na koyi hukuncinka na gaskya.
Zan kyaye dokokinka;
kada ka yashe ni ɗungun mana.
ב
Ta yaya saurayi zai tsarkakae hanyatasa?
Sai ta lura da ita bisa ga maganarka.
Da dukkan zuciyata na neme ka;
kada ka bari in bauɗe daga umarninka.
Na tara maganarka a zuciyata,
don kada in yi maka zunubi.
Albarka ta tabbata gare ka, ya Ubangiji;
ka koya mini dokokinka.
Da bakina na faɗi
dukkan hukuncin da ka faɗa.
Na yi farinciki a cikin hanyar shaidarka,
haka kuma a cikin dukkan arziki.
Azn yi ta tafakkuri a kan dokokinka,
in yi wa hanyoyinka biyayya.
Zan yi farinciki da dokokinka;
ba zan manta maganarka ba.
ג
Ka riƙe bawanka komai a yalwace
domin in rayu; ta haka zan kiyaye maganarka.
Ka buɗe mini idona domin in ga
abubuwan mamaki a cikin shari'arka.
Ni baƙo ne a duniya;
kadaka ɓoye mini umarninka.
Raina na ƙuna saboda zaƙuwad da ya ke yi
ga hukuncinka a kowane lokaci.
Ka tsawata wa masu girman kai waɗanda aka la'anta,
waɗanda suka bauɗe wa umarninka;
ka ɗauke mini mugun abu da wulakanci,
domin na kiyaye dokokinka.
Sarakuna ma sun zauna sun yi maganar saɓa mini,
amma bawanka ya yi tafakkuri a cikin dokokinka.
Shaidarka kuma ita ce farincikina,
kuma mai ba ni shawara.
ד
Raina ya sarai har ƙasa;
ka raya ni bisa ga magnarka.
Na faɗi hanyoyina, ka kuwa amsa mini;
ka koya mini dokokinka.
Kă sa in fahinci hanyoyin manufarka,
ta haka sai in yi tunanin ayyukanka na bam mamaki.
Raina na narkewa saboda nauyi;
ka ƙarfafa ni mana bisa ga maganarka.
Ka kau da maganad da ba gaskiya ba a gare ni;
ka yi mini baiwa da shari'arka game da alheri.
Na zaɓi hanyar bangaskiya,
na sanya hukuncinka a gabana.
Na ɗafe ga shaidarka, ya Ubangiji;
kada ka kunyata ni.
Zan bi hanyar umarninka,
a sa'an nan za ka buɗa zuciyata.
ה
Ya Ubangiji, ka koya mini hanyar dokokinka mana;
ni kuwa zan kiyaye ta har matuƙa.
Ka ba ni fahimta, ni kuwa zan kiyaye shari'arka/ dokarka;
kai, zan ma kiyaye ta da dukkan zuciyata.
Ka sa in bi hanyar umarninka,
domin a cikinsu na ke farinciki.
Ka karkato da zuciyata ga shaidarka,
ba ga kwaɗayi ba.
Ka karkatad da idanuna daga ganin mugun abu,
ka raya ni a cikin hanyoyinka.
Ka ƙarfafa maganarka ga bawanka,
wanda ke tsoronka.
Ka juyad da baƙincikina/ mugun aikina/ wanda na ke tsoro,
domin hukuncinka na da kyau.
Ga shi, ina ɗokin ganin dokokinka;
ka raya ni ga bin gaskiyarka mana.
ו
Alherinka kuma yă zo mini, ya Ubangiji,
wato cetonka, kamar yadda ka faɗa;
ta haka zan sami amsad da zan ba wanda ya munana mini,
domin na gaskata da maganarka.
Kada ka ɗauke maganar gaskiya ɗungum daga bakina,
domin na sa zuciya ga hukuncinka.
Haka zan kiyaye shari'o'inka koyaushe,
har abada abadin;
zan kuwa riƙa zama a cikin 'yanci
domin na nemi ka'idodinka.
Zan kuma yi maganad shaidarka a gaban sarakuna,
ba kuwa zan ji kunya ba;
zan kuma yi murna a cikin/ game da/ umarninka,
waɗanda na ƙaunata.
Zan kuma ɗaga hannayena ga umarninka waɗanda na ƙaunata,
zan kuma yi ta tunanin dokokinka.
ז
Ka tuna wa bawanka maganar,
domin ka sa na yi sazuciya.
Wannan sanyaya mini ne a cikin wahalata
domin maganarka ta raya ni/ farfaɗo da ni.
Masu alfarma sun yi mini ba'a ƙwarai,
duk da haka kuwa ban kauce daga shari'arka ba.
Na tuna da hukuncinka na zamanin da,
ya Ubangilji, na kuma sanyaya wa kaina rai.
Haushi mai tsanani ya same ni saboda miyagun
da suka ya da shari'arka.
Dokokin sun zama su ne waƙata
a gidan ziyarata.
Na tuna da sunanka, ya Ubangiji, a cikin dare,
na kuwa kiyaye shari'arka.
Na sami wannan
domin na kiyaye dokokinka.
ח
Ubangiji shi ne rabona;
na ce, "Zan kiyaye maganarka".
Na roƙi alherinka da dukkan zuciyata;
ka ji tausayina bisa ga maganarka.
Na yi tunanain hanyoyina,
na kuma juyo da tafiyata ya zuwa ga shaidarka;
na yi hamzari, ban yi jinkiri ba,
na kiyaye umarninka.
Igiyoyin mugun sun rage ni,
amma ban mance da shari'arka ba.
Da tsakad dare zan tashi in gode maka
saboda hukuncina na gaskiya.
Ni abokin tafiyar dukkan masu tsoronka ne,
da kuma waɗanda ke kiyaye dokokinka.
Duniya cike ta ke da rahamarka, ya Ubangiji;
ka koya mini dokokinka mana.
ט
Kā kyauta wa bawanka,
ya Ubangiji, bisa maganarka.
Ka koya mini kyakkyawar shari'a da sani,
domin na gaskata da umarninka.
Kafin in cutu sai da na yi ɓatan kai,
amma yanzu ina kiyaye maganarka.
Kai mai alheri ne, kuma kana yin kyakkyawan abu;
ka koya mini dokokinka.
Masu alfarma sun ƙaga mini ƙarya;
zan kiyaye dokokinka da dukkan zuciyata;
sun yi ƙiba kamar alade,
amma ni da hukuncinka na ke farinciki.
Alheri ne a gare ni da na cutu,
don in koyi dokokinka.
Dokokin bakinka sun fiye mini
dubban zinariya da azurfa.
י
Hannayenka ne suka halicce ni, suka kuma siffanta ni;
ka ba ni fahinta don in koyi umarninka.
Masu tsoronka za su gan ni, su yi farinciki,
domin na sa zuciya ga maganarka.
Ya Ubangiji, na sani hukunciknka na gaskiya ne,
kuma ka shafe ni da cuta a cikin gaskiyarka.
Na roƙe ka, ka sa alherinka na ƙauna ya zama na jin daɗina
bisa ga maganarka ga bawanka.
Tattausan alherinak yă zo mini don in rayu;
domin hukkuncinka shi ne farincikina.
Bari masu girman kai su ji kunya,
domin sun jefad da ni ta hanyar rashin gaskiya;
amma zan yi ta tunani da ka'idodina.
Bari masu tsoronka su juyo wurina,
za su kuwa san shaidarka.
Bari zuciyata ta zama kamila game da dokokinka
don kada in ji kunya.
כ
Raina na/ Ina/ suma saboda cetonka,
amma ina sa zuciya ga maganarka.
Idanuna sun kasa saboda maganar
sa'ad da na ke cewa, "Yaushe za ka sanyaya mini?"
Domin na zama kamar kwalba a cikin hayaƙi,
amma duk da haka ban mance da dokokinka ba.
Kwanakin bawanka nawa su ke?
Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?
Masu alfarma sun haƙa mini rami,
waɗanda ba sa bin shari'ata.
Dukkan umarninka na bangaskiya ne;
suna tsananta mini ba bisa gaskiya ba; kă taimake ni.
Sun yi kusan halaka ni a duniya,
amma kuwa ban ya da dokokinka ba.
Ka farfaɗo da ni a cikin halin alherinka na ƙauna;
ta haka zan kiyaye shaidar bakinka.
ל
Maganarka ta tabbata/ zauna/ a sama
har abada, ya Ubangiji.
Gaskiyarka tana ga/ kan/ dukkan zamanai;
kai ne ka kafa duniya, tana kuwa zaune.
Suna zaune har ya zuwa yau bisa ga dokokinka;
domin dukkan abubuwa bayinka ne.
Ba don hukuncinka ya zama sanadin farincikina ba,
da na halaka a cikin wahalata.
Hara abada ba zan mance da dokokinka ba;
domin da su ne ka farfaɗo da ni.
Ni naka ne, ka cece ni;
domin na nemi dokokinka.
Miyagu sun jira ni su halaka ni,
amma ni zan yi aiki da shaidarka.
Na ga ƙarshen dukkan kammala,
amma umarninka mai faɗi ne ƙwarai.
מ
Kai, wace irin ƙauna na ke yi wa shari'arka.
Ita ce abar tunanina wuni zubur.
Umarninka na sa ni mai hikima fiye da abokan gabana,
domin koyaushe suna tare da ni.
Fahimtata ta fi ta dukkan malamaina,
domin shaidarka ita ce abar tunanina.
Ina fahinta fiye da tsohi,
domin na kiyaye dokokinka.
Na ɗauke ƙafata daga kowace irin muguwar hanya
domin in kiyaye maganarka.
Ban bauɗe daga hukuncinka ba
domin kai ne ka koya mini.
Kai, maganarka da daɗi/ zaƙi/ ta ke gare ni.
Kai, har ma ta fi zuma zaƙi!
Ta dokokinka ne na sami fahimta;
saboda haka na ƙi kowace irina hanyar ƙarya.
נ
Maganarka fitila ce ga ƙafafuna,
tana haskaka hanyata.
Na yi rantsuwa, na kuwa ƙarfafa ta,
cewa zan kiyaye hukuncinka na gaskiya.
Na cuta ƙwarai;
ka farfaɗo da ni, ya Ubangiji, bisa ga maganarka!
Ya Ubangiji, na roƙe ka, ka kar bi baiwad da na yi da bakina don kaina,
ka kuma koya mini hukuncinka.
Raina yana hannna a koyaushi,
amma duk da haka ban mance da shari'arka ba.
Miyagu sun kafa mini tarko,
amma duk da haka ban bauɗe daga dokokinka ba.
Na ɗauki shaidarka a kan gādo na har abada,
domin su ne farincikina.
Na kallafa zuciyata in aikata dokokinka,
har abada, har ya zuwa matuƙa.
ס
Na tsargi masu ciki biyu,
amma ina ƙaunar shari'arka/ hukuncinka.
Kai ne mafakata, kuma garkuwata;
da maganarka na ke sa zuciya.
Ku yi nesa da ni, ku masu mugun aiki,
don in kiyaye umarnin Allahna.
Ka tallafe ni bisa ga maganarka, don in rayu,
kada in ji kunya saboda sazuciyata.
Ka tallafe ni, sai in yi zaman lafiya,
sai kuma in yi biyayya ga dokokinka a kowane lokaci.
Ka maida dukkan masu yin kuskure a cikin dokokinka sun zama ba komai ba,
domin yaudararsu ƙarya ce.
Ka ture dukkan miyagun duniya kamar ƙazanta;
saboda haka na ke son shaidarka.
Jikina na rawa saboda tsoronka,
ina kuma tsoron hukuncinka.
ע
Na yi hukunci, na yi gaskiya;
kada ka ƙyale ni ga masu matsa mini.
Ka lamunci bawanka a kan kirki;
kada ka bari mai alfarma ya matsa mini/ zalumce ni.
Idanuna suna kasawa saboda cetonka,
da kuma maganarka ta gaskiya.
Ka yi da bawanka bisa ga rahamarka,
ka kuma koya mini dokokinka.
Ni bawanka ne, ka ba ni fahimta,
don in san shaidarka.
Lokacin da Ubangiji zai yi aiki ya yi,
domin sun banzantad da hukuncinka.
Saboda haka na ke son umarninka
fiye da zinariya; kai, fiye da kyakkyawar zinariya ma.
Saboda haka na ke ganin girman dukkan dokokinka,
game da daidaitakar dukkan abubuwa;
na kuwa tsargi dukkan hanyar ƙarya.
פ
Shaidarka mai bam mamaki ce
saboda haka ne na ke kiyaye ta.
Farkon maganarka ya kan ba da haske;
ya kan ba sabon shiga fahimta.
Na buɗe bakina ƙwarai, na yi haki,
domin ina ɗokin umarninka.
Ka karkato gare ni, ka ji tausayi ne,
kamar yadda ka saba yi wa masu son/ ƙaunar/ sunanka.
Ka shirya tafiyata da magnarka;
kada kuwa ka bari miyagun abubuwanka su mallake ni.
Ka kuɓutad da ni daga zaluncin ɗan'adam
ta haka sai in kiyaye umarninka.
Ka sa fuskarka ta yi haske a kan bawanka,
ka kuma koya mini dokokinka.
Hawaye na gudu a idona kamar ƙorama,
domin ba su kiyaye dokokinka ba.
צ
Kai mai gaskiya ne, ya Ubangiji,
hukuncinka kuwa gaskiya ne.
Ka umarci shaidarka da gaskiya,
da kuma bangaskiya ƙwarai.
Himmata ta tauye ni,
domin abokan gabana sun mance da maganarka.
Maganarka tsattsarka ce ƙwarai,
saboda haka ne bawankake son ta.
Ni ƙarami ne, kuma rainanne,
duk da haka kuwa ba na mancewa da umarninka.
Gaskiyarka gaskiya ce ta har abada,
shari'arka kuwa ita ce gaskiya.
Wahala da azaba sun kama/ riƙe/ ni,
duk da haka kuwa umarninka shi ne farincikina.
Shaidarka ta gaskiya ne har abada;
ka ba ni fahinta, sai in rayu.
ק
Na yi kira da dukkan zuciyata;
ka amsa mini mana, ya Ubangiji.
Zan kiyaye dokokinka.
Na kira ka, ka cece ni;
zan kuwa kiyaye shaidarka.
Na ƙi gari ya waye, ina ta ƙara,
na sa zuciya ga mganarka.
Idona ya hana lissafin lokatan dare,
don in yi tunanin maganarka.
Ka saurari muryata bisa ga alherinka na ƙauna;
ka farfaɗo da ni, ya Ubangiji, bisa ga hukuncinka.
Masubin muguwar hanya suna matsowa,
nesa su ke da shari'arka.
A kusa ka ke, ya Ubangiji,
dukkan umarninka kuma gaskiya ne.
Tun zamanin da na san shaidarka
cewa ka kafa su har abada.
ר
Ka dubi wahalata, ka kuɓutad da ni,
domin ban mance da shari'arka ba.
Ka taimaki sha'anina, ka kuɓutad da ni;
ka farfaɗo da ni bisa ga maganarka.
Kuɓuta nesa ta ke ga miyagu,
domin ba sa neman dokokinka.
Tattausan alherinka/ Tsananin tausayinka/ da girma ya ke, ya Ubangiji;
ka farfaɗo da ni bisa ga hukuncinka.
Masu tsananta mini da magabtana suna da yawa,
duk da haka ban bauɗe daga shaidarka ba.
Na ga masu aikata mugunta, na yi bakinciki,
domin ba sa kiyaye maganarka.
Ka dubi yadda na ƙaunaci umarninka.
Ka farfaɗo da ni mana, ya Ubangiji, bisa ga alherinka na ƙauna.
Jimlar maganarka gaskiya ce;
kuma kowane ɗaya daga cikin hukuncinka na gaskiyan nan
yana tabbata har abada.
ש
Sarakuna sun tsananta mini ba gaira ba dalili,
amma kuwa zuciyata tana tsaye tana tsoron maganarka.
Ina farinciki da maganarka
kamar wanda ya sami ganima mai yawa.
Na tsargi ƙarya, na ƙi ta,
sai dai hukuncinka na ke ƙauna.
Ina yabonka sau bakwai a kowace rana
saboda hukuncinka na gaskiya.
Masu ƙaunar hukuncinka suna da ƙasaitaccen aminci;
ba su kuwa da wata hanyar tuntuɓe.
Na sa zuciya ga cetonka tuni, ya Ubangiji,
na kuwa aikata umarninka.
Na kiyaye shaidarka,
ina kuwa ƙaunarta matuƙa.
Na kiyaye umarninka da shaidarka
domin sukkan hanyohyina suna gabanka.
ת
Bari kukana ya zo kusa da kai, ya Ubangiji,
ka ba ni fahimta bisa maganarka.
Bari addu'o'ina su zo gabanka;
ka kuɓutad da ni bisa ga maganarka.
Bari in yi yabo da bakina
domin kana koya mini dokokinka.
Bari harshena ya yi waƙar maganarka,
domin dukkan umarninka gaskiya ne.
Hannunka yă shirya don taimakona,
domin na zaɓi umarninka.
Na ƙwallafa rai ga cetonka, ya Ubangiji,
hukkuncinka kuwa shi ne farincikina.
Bari raina ya rayu, zai kuwa yabe ka,
bari kuma hukuncinka yă taimake ni.
Na sangarta kamar ɓatacciyar tunkiya,
ka nemi bawanka mana,
domin ban mance da umarninka ba.
120
Na yi wa Ubangiji kuka a cikin baƙincikina,
ya kuwa amsa mini:
"Ka ceci raina, ya Ubangiji,
daga faɗin ƙarya
da kkuma harshe mai sa zamba."
Me za a ba ka,
me kuma za a sake yi maka,
ya kai harshe mayaudari?
Tsinana kiban masu ƙarfi ne,
da tankar dibino mai cin wuta.
Kaitona da na zauna a Mashica,
da na zauna a cikin sansanin Kadara.
Raina ya daɗe da yin gida
tare da wanda ke zaman lafiya.
Saboda aminci na ke;
amma sa'ad da na yi magana,
su a shirya su ke su yi yaƙi.
121
Zan ɗaga kaina in dubi duwatsu.
Daga ina ne taimakona zai zo?
Taimakona daga Ubangiji ya ke zuwa,
wanda ya halicci sama da ƙasa.
Ba zai bari a kau da ƙafarka ba;
duk mai kiyaye ka ba zai yi barci ba.
Ga shi, wanda ke kiyaye Bani Isra'ila
ba zai yi gyangaɗi ba,
ba kuwa zai yi barci ba.
Ubangiji shi ne mai kiyaye ka;
Ubangiji shi ne inuwarka
ta hannun dama.
Rana ba za ta gasa ka da rana ba,
wata kuma ba zai lamshe ka daddare ba.
Ubangiji zai kiyaye ka daga dukkan mugunta;
zai kiyaye ranka/ ka.
Ubangiji zai kiyaye shgarka da fitanka,
tun daga yanzu har ya zuwa har abada.
122
Na yi farinciki sa'ad da suka ce da ni,
"Bari mu je gidan Ubangiji."
Ga mu a tsaye
a ƙofarki, ya Urushalima.
Ya ke Urushalima, ke da aka gina ki birni
a haɗe gu ɗaya,
inda kabilu ke hawa,
wato kabilkun Ubangiji,
saboda shaida ga Bani Isra'ila,
su yi wa sunana Ubangiji godiya.
Domin akwai gadajen sarauta
na hukunci waɗanda aka tanada;
wato gadajen sarauta na gidan Dawuda.
Ku yi addu'a saboda amincin Urushalima.
"Masu ƙaunarka za su arzuta.
Aminci yă tabbata a cikin kewayen ganuwarki,
arziki kuma a cikin fadarki."
Yanzu kuma sai in ce,
"Aminci yă tabbata a cikinki,"
saboda 'yan'uwana da abokaina.
Zan nemi alherinki
albarkacin ɗakin Ubangiji Allahmmu.
123
Gare ka na ke cira idanuna/ ɗaga kaina,
ya kai da ke zaune a sammai.
Ga shi, kamar yadda idanun bayi
ke duban hannun ubangijinsu,
kamar idanun baranya
gauwargijiyatata,
haka idanummu ke duban Ubangiji Allahmmu,
sai yā ji tausayimmu.
Ka ji tausayimmu, ya Ubangiji,
ka ji tausayimmu,
domin mun zama ababan renawa gaya matuƙa
Rammu ya cika matuƙa
da zagin masu zaman holewa,
da kuma rainin mai alfarma.
124
Ba don Ubangiji da ke tare da mu ba,
da sai yanzu Bani Isra'ila su ce,
ba don Ubangiji da ke tare da mu ba,
sa'ad da mutane suka tasam mana,
da sun haɗiye mu da rai,
sa'ad da suka fusata/ husata/ da mu;
da ruwaye sun sha kammu,
da ƙoramai sun cinye mu;
da ruwaye masu alfarma
sun sha kammu.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
da bai ba da mu
sun ciccinye mu ba.
Mun kuɓuta kamar tsuntsun
da ya kubce wa 'yan karko;
tarkon ya tsinke,
mu kuwa mun tsira.
Taimakommu na ga sunan Ubangiji
wanda ya halicci sama da ƙasa.
125
Waɗanda suka gaskata da Ubangiji
kamar dutsen Sihiyona su ke,
wanda ba a iya motsa shi,
yana nan dai a zaune har abada.
Kamar yadda duwatsu ke kewaye da Urushalima,
haka Ubangiji ke kewaye da mutanensa,
tun daga yanzu, har ya zuwa har abada.
Domin sandan mugunta ba zai zauna ga mai gaskiya ba;
masu gaskiya kuma ba za su sa hannunsu ga rashin gaskiya ba.
Ka yi wa masu aikata kyakkyawan abu alheri, ya Ubangiji;
ka yi wa masu gaskiya a zuciyarsu kuma.
Amma waɗanda ke juyawa zuwa ga karkatattun hanyoyinsu
sai Ubangiji ya ja su tare da masu aikata mugun abu.
Aminci yă tabbata ga Bani Isra'ila.
126
Sa'ad da Ubangiji ya juya baya
ga kamun bauta a Sihiyona,
kamar masu yim mafarki mu ke.
Sa'an nan sai muka cika da dariya, muna waƙa;
sa'an nan sai suka ce a cikin al'ummai,
"Ubangiji ya yi musu manyan al'amura."
Ubangiji ya yi mana manyan al'amura,
mun kuwa yi murna da su.
Ka sauya mana kamun nan mana, ya Ubangiji,
kamar ƙoraman da ke kudu.
Masu shuka a damshin hawaye,
za su girba a cikin farinciki.
Ko da ya ke ya tafi yana kuka,
yana ɗauka da irin,
zai sake dawowa da farinciki,
yana zuwa da dammunansa.
127
Im ba Ubangiji ne ya gina gidan ba,
duk masu gina shi wahalar banza su ke sha.
Im ba Ubangiji ne ya kiyaye birnin ba,
masu tsaro suna faɗake a banza ne kawai.
Aikin banza ne gare ku ko kun tashi da wuri,
in kun makara wajen hutawa,
kuna kuma cin aiki;
domin ta haka ya ke ba da barci ga ƙaunatattunsa.
Ka ga yara gādon Ubangiji ne,
albarkar mahaifa kuma tasa ce/ ladansa ne.
Kamar yadda kiban su ke a hannun ƙaƙƙarfan mutun
haka 'ya'yan ƙuruciya su ke.
Mutumin da kwarinsa ke cike da su,
mai farinciki ne
Ba za su ji kunyata ba
sa'ad da suka tanko/ tanku [?]/ da abokan gabansu a ƙofar gari.
128
Albarka ta tabbata ga duk mai tsoron Ubangiji,
wanda ke bin tafarkinsa.
Domin za ka ci amfanin wahalar hannunka;
za ka zama mai farinciki,
abin kuma zai yi maka daɗi.
Matarka za ta yi albarka kamar iccen inabi
a can cikin gidanka;
'ya'yanka kamar bishiyoyin zaitun
a kewaye da wurin cin abincinka.
Ka ga haka za a yi wa mutumin albarka
wanda ke tsoron Ubangiji.
Ubangiji zai yi maka albarka
a/ daga/ cikin Sihiyona,
kai kuma za ka ga kyan Urushalima
a dukkan kwanakin rayuwarka.
Kai, har ma za ka ga jikokinka.
Aminci yă tabbata ga Bani Isra'ila.
129
"Sau da yawa suna cutata tun daga ƙuruciyata,"
bari kuma yanzu Bani Isra'ila su ce,
"Sau da yawa suna cutata tun daga ƙuruciyata,
duk da haka kuwa ba su cin mini ba.
Masu huɗa sun huɗe gadon bayana;
sun yi dogayen kunyaki/ rumaniya."
Ubangiji mai gaskiya ne;
ya yanke igiyoyin miyagu kat.
Bari dai su kunyata, a juyo da su,
dukkan waɗanda suka ƙi Sihiyona.
Bari su zama kamar ciyawar kan soro,
wadda ke bushewa kafin ta girma,
waɗanda ma mai noma su
ba ya cika hannunsa da ita,
haka kuma mai ɗaura daminsu
ba ya cika ƙirjinsa da ita.
Masu wucewa kuma ba sa cewa,
Allah yă yi muku albarka.
Muna sa muku albarka
da sunan Ubangiji."
130
Daga can cikin zurfi/ teku/ na ke kuka gare ka, ya Ubangiji.
Ya Ubangiji, ka saurari muryata.
Ka kasa kunnuwanka
ga muryar addu'o'ina.
Ya Ubangiji, in dai za ka rubuta laifuffuka,
wa zai tsaya?
Amma akwai gafara a gare ka,
domin a tsorace ka.
Ina dakon Ubangiji, raina na dako,
kuma a cikin maganarsa na ke sa zuciya.
Raina na duba hanyar Ubangiji
har ma fiye da yadda masu gadi ke duban wayewar gari.
Kai, wane masu gadi da safiya.
Ya ku Bani Isra'ila, ku sa zuciya ga Ubangiji.
Domin akwai rahama ga Ubangiji,
akwai kuma fansa mai yawa ƙwarai a gunsa.
Zai kuwa fanshi Bani Isra'ila
daga dukkan zunubansu.
131
Ya Ubangiji, zuciyata ba mai alfarma ba ce,
idanuna kumaba manya ba;
ba na kuwa aikata manya[manyan abubuwa/ al'amura,
ko kuwa in yi abubuwan da na al'ajabi ƙwarai a gare ni.
Hakika na kwantad da raina
kamar ɗan da aka yaye da uwatasa;
raina na gare ni kamar yayayyen yaro.
Ya Bani Isra'ila, ku sa zuciya ga Ubangiji
tun daga yanzu har ya zuwa har abada.
132
Ya Ubangiji, ka tuna Dawuda mana,
da dukkan whalce-wahalcensa;
yadda ya yi wa Ubangiji rantsuwa
ya kuma ɗauki wa'adi da ƙasaitaccen nan na Yakubu;
"Hakika ba zan zo cikin majami'ar gidana ba,
ba kuma zan hau gadona ba;
ba zan bar idona ya yi barci ba
ko kuwa in bar idona ya yi gyangyaɗi,
sai na sama wa Ubangiji wuri,
majami'a saboda Ƙasaitaccen nan na Yakubu."
Ga shi, mun ji labarinta a cikin Afrataha,
mun same ta a cikin saura.
"Za mu shiga majami'arsa;
za mu yi sujada/ bauta/ a matashin ƙafarsa.
Ya Ubangiji, ka tashi daga wurin hutunka,
kai, da sunduƙin ƙarfinka.
Malamnka su tufatu da aikin gaskiya,
tsarkakanka kuma su ɗaukaka murya saboda farinciki.
Kada ka juyad da fuskar shafaffenka
saboda baranka Dawuda.
Ubangiji ya rantse wa Dawuda a cikin gaskiya;
ba zai juya daga gare ta ba;
"Tsatsonka ne zan ɗora a kan gădon sarautarka.
In 'ya'yanka za su kiyaye alkawarina
da shaidata da zan koya musu,
to, sai 'ya'yansu ma su hau gadon sarautarka har abada."
Domin Ubangiji ya zaɓi Sihiyona;
ya bukace ta saboda zamansa.
"Wannan shi ne wurin hutuna har abada;
a nan zan zauna, domin na bukace ta.
Zan yi wa ababan cikinta albarka mai yawa;
zan ƙosad da gajiyayyunta da abinci/ burodi.
Malamanta kuma zan tufatar da ceto,
tsarkakanta za su ɗaukaka murya don murna.
A nan zan sa ƙahon Dawuda ya tohu;
na ƙaddara wa shafaffena fitila.
Zan tufatad da magabtansa da kunya,
amma kambinsa zai yi albarka a kansa."
133
Duba, yadda ya ke da kyau da kuma daɗi
ga 'yan'uwa su zauna gaba ɗaya suna haɗe.
Kamar kyakkyawan mai ya ke a ka,
mai gudana a kan gemu,
wato gemun Haruna,
wanda ya gudano har kan hannun rigarsa.
Kamar raɓar Hamuna
mai saukowa daga dutsen/ duwatsun/ Sihiyona;
domin a can ne Ubangiji ya yi umarnin albarka,
wato rai na har abada.
134
Kun ga, ku yabi Ubangiji, ya bayin Ubangiji dukanku,
waɗanda ku ke tsaye agidan Ubangiji dad dare.
Ku ɗaga hannayenku ga tsattsarkan wuri,
ku yabi Ubangiji.
Ubangiji yă yi maka albarka a cikin Sihiyona,
wato shi da ya halicci sama da ƙasa.
135
Ka yabi Ubangiji. Ku yabi sunan Ubangiji,
ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji,
ku da ke tsaye a gidan Ubangiji,
a cikin ɗakunan gidan Allah.
Ku yabi Ubangiji, domin shi Ubangiji mai alheri ne;
ku yi waƙoƙin yabon sunansa domin da daɗi.
Domin Ubangiji ya zaɓa wa kansa Yakubu,
da kuma Bani Isra'ila a kan dukiyarsa wata daban.
Domin ni na san Ubangiji mai girma ne,
kuma Ubangijimmu na sama da dukkan iyayengiji.
Duk abin da Ubangiji ya ji daɗinsa shi ne ya aikata,
a sama da ƙasa,
da bahar da dukkan teku.
Yana sa tururi su yi sama daga bangon duniya;
yana yi wa ruwan sama walƙiya,
yana kawo isak daga cikin taskokinsa.
Wanda ya mauje 'ya'yan fari na Masar,
na mutane da na dabbobi duka;
ya aiko da alamomi da abubuwan mamaki
a tsakiyarki, ya ke Masar
kan Firauna da dukkan bayinsa;
wanda ya mauje al'ummai da yawa,
ya kashe sarakuna da yawa;
Sihuna sarkin Amurawa,
da Ugu sarkin Bashana,
da dukkan masarautun ƙasar Kana'ana;
ya ba da ƙasarsu a gado,
gado ga mutanensa Bani Isra'ila.
Sunanka yana tabbata har abada, ya Ubangiji;
tunawa da kai aka yi, ya Ubangiji, a dukkan zamani.
Domin Ubangiji zai hukunka mutanensa,
yă kuma yafe wa bayinsa da kansa.
Gumakan al'ummai azurfa ne da zinariya,
aikin hannu.
Suna da bakuna, amma ba sa magana,
suna da idanu, amma ba sa gani,
suna da kunnuwa, amma ba sa ji,
ba kuwa wani numfashi a bakinsu.
Waɗanda suka yi su za su zama kamarsu ne,
kai, har ma wanda ya gaskata da su.
Ya ku Bani Isra'ila, ku yabi Ubangiji.
Ya ku zuriyar Haruna, ku yabi Ubangiji.
Ya ku zuriyar Lawi, ku yabi Ubangiji.
Ya ku masu tsoron Ubangiji, ku yabi Ubangiji.
Yabo yā tabbata ga Ubangiji daga cikin Sihiyona,
wanda ke zaune a Urushalima.
Ku yabi Ubangiji.
136
Ku gode wa Ubangiji mana, domin mai alheri ne,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
Ku gode wa Allahn alloli mana,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
Ku gode wa Ubangiji iyayengiji mana,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
a gode masa wanda shi kaɗai ne ya yi manya-manyan abubuwan mamaki,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
a gode masa wanda ya yi samammi ta fahimtarsa/ saninsa,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
a gode masa shi da ya shimfiɗa ƙasa birbishin ruwa,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
a gode masa shi da ya yi manyan hasassaki,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
rana tă yi zamani da rana,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
wata da taurari su yi zamani daddare
domin tausayinsa na dawwama har abada.
a gode masa shi da ya mauje 'ya'yan fari na Masar,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
ya fito da Bani Isra'ila daga cikinsu,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
kaƙaƙƙarfan hannu, da kuma miƙaƙƙen damtse,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
a yabe shi, shi da ya raba Bahar Maliya ya rabu daban daban,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
ya kuma sanya Bani Isra'ila su wuce ta tsakiyarta,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
amma sai ya birkice Fir'auna da rundunarsa acikin Bahar Maliya,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
a yabe shi, shi da ya ja mutanensa ta cikin jeji,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
a yabe shi, shi da ya mauje manyan sarakuna,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
ya kuma kashe shaharrarrun sarakuna,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
Sihuna, sarkin Amurawa,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
da kuma Ugu, sarkin Bashana,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
ya ba da ƙasarsu aka gada,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
wato gādo ga Bani Isra'ila bayinsa,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
Wanda ya tuna mu a cikin ƙasƙancimmu,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
ya kuwa cece mu daga abokan gabammu,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
yana ba kowace halitta abinci,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
Ku yabi Allah mai sama mana,
domin tausayinsa na dawwama har abada.
137
A can muka zauna a kusa da kogin Babila,
har muka yi kuka,
sa'ad da muka tuna da Sihiyona.
Mun rataya molayemmu
a jikin bishiyoyin "willow".
Domin a can ne waɗanda suka kama mu
suka so mu yi musu waƙoƙi;
waɗanda suka suɗe mu, suka so
mu yi musu fara'a, suna cewa,
"Ku yi mana wata waƙa a cikin waƙoƙin Sihiyona mana."
Yaya za mu yi waƙoƙin Ubangiji
a wasu baƙin ƙasashe?
Idan na mance da ke, ya Urushalima,
to, sai hannuna na dama yă manta da wayonta.
Bari harshena ya yi manne wa kanɗata
in dai ban tuna ki ba,
in dai ban fi son Urushalima
a kan babban abin farincikina ba.
Ya Ubangiji, ka tuna munin 'ya'yan Iduma
a ranar Urushalima,
waɗanda suka ce, "A rushe ta, a rushe ta,
har harshinta."
Ya ke 'yar Babila, wadda za a halaka ki.
Farinciki ya tabbata ga wanda ya sāka miki
kamar yadda kika bauta mana.
Wanda ya ɗebi 'ya'yanki ya fyaɗa da dutse,
zai zama mai farinciki.
138
Zan gode maka da dukkan zuciyata,
zan yi waƙoƙin yabonka a gaban gumaka;
zan yi sujada a gaban tsattsarkan ɗakinka na ibada
in kuma gode wa sunanka saboda alherinka na ƙauna da gaskiyarka;
domin kā ɗaukaka maganarka
birbishin dukkan sunanka.
A kwanakin da na yi kira,
kā amsa mini;
kā ƙarfafa ni da ƙarfi a zuciyata.
Dukkan sarakunan duniya za su gode maka, ya Ubangiji,
domin sun ji maganar bakinka.
Kai, za su ma yi waƙar hanyoyin Ubangiji,
domin ɗaukakar Ubangiji mai girma ce.
Domin ko da ya ke Ubangiji maɗaukaki ne,
duk da haka yan girmama mai ƙasƙanci;
amma daga nesa ya ke sanin mai alfarma/ mutakabbiri.
Ko ina tafiya a tsakan wahala,
za ka tsamo ni;
za ka miƙa hannunka ka kare hushin magabtana,
hannunka na dama kuwa zai kuɓutad da ni.
Ubangiji zai kammala abin nan da ya shafe ni.
Ya Ubangiji, tausayinka na dawwame har abada.
Kada kaya da aikin hannunka.
139
Ya Ubangij, ka bincike ni,
ka kuma san ni.
Ka san zamana, ka san tashina;
ka san tuanina tun daga nesa.
Ka binciki hanyata da kwanciyata,
ka kuma saba da dukkan hanyoyina.
Domin ba wata kalma/ magana/ a bakina,
sai dai ga shi ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.
Ka sanya ni a baya da kuma gaba,
ka kuma ɗora hanunka a kaina.
Wannan irin sani ya zame mini abin mamaki ƙwarai;
ɗaukakakke ne, ba zan iya samunsa/ kaiwa gare shi/ ba.
Ina kuma zan je daga Ruhunka?
Ko kuma ina zan gudu in ji daga Zatinka?
In na hau sama, kana can,
In kuma na kwanta a Mahalaka, can ma kana nan.
In na bi fuffuka safiya
na zauna a bahar ma fi nisa,
ko can ma hannunka na dama ne zai kai ni,
hannunka na dama ne kuma zai riƙe ni.
In na ce, "Hakika duhu zai tsorata ni,
hasken da ke kewaye da ni kuma zai zama dare,"
ko da duhun ma ba a ɓoye ya ke gare ka ba;
amma dare haske ya ke yi kamar rana;
duhu da haske duk ɗaya ne a gare ka.
Domin kai ne ka mallakar ragamata,
kai ne ka rufe ni a cikin mahaifiyata.
Zan gode maka, domin halattata abar tsoro ce, abar mamaki kuma.
Ayyukanka da bam mamaki su ke.
Ni kuwa na sani sarai.
Jikina ba a ɓoye ya ke gare ka ba,
sa'ad da aka halicce ni a asirce,
aka siffanta ni da mamaki a wuri mafi ƙasƙanci a duniya.
Idanunka sun ga kayana marar kammala;
gaɓoɓina duka kuma a cikin littafinka su ke rubuce,
wato waɗanda a ke siffanta su kowace rana,
sa'ad da kuwa babu ko ɗayansu yanzu.
Tunaninka a kaina da daraja su ke, ya Ubangiji/ Allah.
Adadinsu da yawa ya ke.
Da zan ƙirga su, da sun fi yashi yawa.
Sa'ad da na farka duk ina tare da kai har yanzu.
Hakika za ka kashe mugu, ya Allah.
Saboda haka sai ku rabu da ni, ya ku masu son kisan kai;
domin suna saɓa maka a maganarsu ta hanya marar kyau,
magabtanka kuma suna kama sunanka a banza.
Ashe ba ƙin waɗanda suka ƙi ka na ke yi ba, ya Ubangiji?
Kuma ba baƙinciki na ke yi da waɗanda suka tayar maka ba?
Na ƙi su da cikakkiyar ƙiyayya;
na ɗauke su akan magabtana.
Kă bincike ni, ya Allah, kă san zuciyata.
Ka jarraba ni, ka sa tunanina.
Kă gani in akwai wata hanyar mugunta a zuciyata,
ka ja ni ta hanya madawwamiya.
140
Ya Ubangiji, ka kuɓutad da ni daga mugun mutun;
ka kuɓutad da ni daga mafaɗacin mutum,
waɗanda ke riya fitina a zukatansu,
a kai a kai suka taruwa don su yi yaƙi.
Sun wasa/ koɗa/ harshensu kamar maciji;
dafin kasa na nan a bakinsu.
Ya Ubangiji, ka cece ni daga hannun miyagu;
ka cece ni daga mafaɗacin mutum,
wanda ya yi niyyar ɗebe sawayena.
Masu alfarma sun haƙa/ ɗana/ mini tarko da igiyoyi,
sun baza raga a gefen hanya;
sun kafa mini tarko.
Na ce da Ubangij, Kai ne Allahna;
ka kasa kunne ga roƙona, ya Ubangiji.
Ya Allah Ubangiji, ƙarfin cetona,
kai ne ka rufe kaina a ranar yaƙi.
Kada ka yarda da bukatar mugu, ya Ubangiji;
kada ka inganta miyagun dabarunsa,
domin kada su ɗaukaka kansu.
Shugaban waɗanda ke kewaye da ni kuwa,
bari fitinarsu ta bakinsu ta rufe so.
Bari garwashi ya zubo musu.
bari a jefa su a wuta;
cikin rumuka masu zurfi
don kada su sake tashi
Mai mummunar magana ba za a tabbatad da shi a duniya ba;
mugunta za ta nemi mafaɗacin mutum ta ka da shi.
Na sani Ubangiji zai riƙi al'amarin wanda a ke wahalarwa,
da hakkin mai bukata.
Hakika masu gaskiya za su yi wa sunanka godiya;
masu gaskiya za su zauna a zatinka.
141
Ya Ubangiji, na kira ka;
ka hanzarto gare ni.
Ka kasa kunne ga muryata
sa'ad da na kira ka.
Bari a gabatad da addu'ata kamar turaren wuta a gabanka;
ɗaga hannuna kamar hadayar maraice.
Ka riƙa duba bakina, ya Ubangiji,
ka kiyaye bakina.
Kada ka karkatad da zuciyata ga wani mugun abu,
har ta shantake ga yin miyagun ayyuka
tare da mutane masu aikata mugun abu.
Kada kuwa ka bari in ci abincinsu.
Bari/ Gara/ mai gaskiya ya buge ni, alheri ne;
bari ya tsawata mini, zai zama kamar mai de a ka.
Kada kaina ya ƙi shi,
domin ko a cikin muguntarsu ma
zan ci gaba da addu'ata.
An jefad da alkalansu a gefen dutse
za su kuwa ji maganata domin tana da daɗi.
Kamar sa'ad da mutum ke huɗa ne,
ya ke tsaga ƙasa,
ƙasusuwammu suna barbaje a bakin kabari.
Domin idanuna na gare ka, Ya Allah Ubangiji;
Gare ka na ke amincewa,
kada ka bar ni gajiyayye.
Ka kiyaye ni daga tarkon da suka kafa mini,
da kuma tarkon masu aikata mugunta.
Bari miyagu su faɗa tarkonsu,
ni kuwa in tsira daga gare shi.
142
Na yi ɗaukaka murya ga Ubangiji,
da muryata ga Ubangiji na ke roƙo,
ina bulbula ƙarata gare shi,
ina nuna masa wahalata a gabansa.
Sa'ad da ruhuna yatsorata a cikina,
kai ka san hanyata.
A kan hanyar da na ke bi
suka kafa mini tarko.
Ka dubi ta hannuna na dama ka gani,
ba wani mutumin da ya san ni;
na rasa mafaka,
ba wanda ya kula da raina.
Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;
na ce, Kai ne mafakata,
rabona a cikin ƙasar rayayyu.
Ka kula da kukana;
domin an ƙasƙantad da ni ƙwarai.
Ka kuɓutada da ni daga masu tsananta mini,
domin sun fi ni ƙarfi.
Ka fito da raina daga kurkuku
don in gode wa sunanka.
Masu gaskiya za su kewaye ni,
domin za ka riƙe ni da nagarta.
143
Ka ji addu'ata, ya Ubangiji;
ka kasa kunne ga roƙona.
Ka amsa mini a cikin gaskiyarka/ da gaskiyarka.
Kada ka sa bawanka a gaban shari'a;
domin ba wani rayayye da zai kuɓuta don aikinsa a gabanka.
Domin magabci ya tsananta mini,
ya buge ni har ƙasa;
ya sa na zauna a wurare masu duhu
kamar wanda ya daɗe ta mutuwa.
Saboda haka ruhuna ke tsorace a cikina;
zuciyata ta wofinta a cikina.
Na tuna zamanin da;
ina tunanin dukkan ayyukanka;
ina jin daɗin aikin hanuna.
Na baza hannayena gare ka;
raina na ƙishirwarka
kamar ƙasar da ta ke da ƙishi.
Ka hanzarta amsa mini, ya Ubangiji,
ruhuna na suma.
Kada ka ɓoye mini fuskarka daga gare ka,
don kada in zama kamar masu faɗawa rami.
Ka sa in riƙa jin alherinka na ƙauna da safe,
domin kai na ke gaskatawa.
Ka sa in san tafarkin da zan riƙa bi,
domin ina ɗaga raina gare ka ne.
Ya Ubangiji, ka cece ni daga maƙiyana;
na gudo gare ka, ka ɓoye ni.
Ka koya mini yin nufinka,
domin kai ne Allahna.
Ruhunka mai kyau ne ka ja ni
ka kai ni ƙasar gaskiya.
Ka farfaɗo da ni, ya Ubangiji,
saboda takwarana/ albarkacin/ sunana.
Ka fito da raina daga cikin wahala
ta hanyar gaskiya.
Ka yanke magabtana saboda alherinka na ƙauna,
ka kuma halaka dukkan masu wahalshe ni,
domin ni bawanka ne.
144
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, dutsena,
wanda ke koya wa hannayena yaƙi,
yatsuna kuma faɗa.
Alherina na ƙauna,mafakata;
hasumiyata, macecina,
garkuwata, wanda kuma na gaskata da shi,
wanda ya biyar mini da mutanensa na hau kan su.
Ya Ubangiji, wanene mutum,
har da za ka dube shi,
ko kuwa ɗam mutum,
har da za ka kula da shi?
Ai mutum kamar banza ya ke,
kwanakinsa kamar inuwa ce mai wucewa.
Ya Ubangiji, ka naɗe sammanka, ka sauko.
Ka taɓa duwatsu, sai su yi hayaƙi.
Ka sauko da walƙiya, ka watsa su,
ka aiko da kibanka, ka hana su sakewa.
Ka miƙo hannunka daga sama,
ka kuɓutad da ni, ka cece ni
daga manyan ruwaye/ gawurtaccen ruwa,
daga kuma ƙasar waɗansu,
waɗanda ke muguwar magana,
hannunsu na dama kuwa
hannun daman ƙarya ne.
Zan rera maka sabuwar waƙa, ya Allah;
a kan garaya mai tsirhiyoyi goma
zan yi maka waƙar yabo;
shi ne mai ba sarakuna ceto,
wanda ya ke ceton bawansa Dawuda
daga takobi mai cutarwa.
Ka cece ni, ka kuɓutad da ni daga hannun baƙi,
waɗanda bakinsu ke muguwar magana;
hannunsu na dama kuwa hannun daman mugunta ne.
Sa'ad da 'ya'yammu maza za su zama kamar shuka ce
a lokacin ƙuruciyatasu,
'ya'yammu mata kuma kamar duwatsun kusurwa
waɗanda aka sassaka kamar na fada.
Sas'ad da rahoniyummu suka cika,
muna da kowace irin ajiya;
tumakimmu kuma hahhaifi dubban 'ya'ya
a kan dubbai agonakimmu;
sa'ad da muka/ aka/ lallabta takarkarammu
sa'ad da ba shiga ba fita/ ba tsaiwa ba tafiya,
ba kuma kuka a hanyoyimmu.
Farinciki yā tabbata ga waɗanda wannan abu ya shafa.
Kai, farinciki yā tabbata ga waɗanda Ubangiji ke Allahnsu.
145
Zan yabe ka, ya Allahna, ya Sarki,
zan kuma yabi sunanka har abada abadin.
Kowace rana zan yabe ka,
zan kuma yabi sunanka har abada abadin.
Ubangiji da girma ya ke,
ya kuma isa a yabe shi ƙwarai;
girmansa kuwa marar ƙididdiguwa ne.
Wata zuriya za ta yabi ayyukanka ga wata,
za ta kuma faɗi manya-manyan ayyukanka.
Maɗaukakin ikon nan na girmanka,
da kuma ayyukanka na mamaki,
su zan yi ta tunani.
Mutane kuma zasu yi ta maganar
girman ayyukanka masu ban tsoro,
ni kuwa zan faɗi girmanka.
Za su faɗi tunanin girman alherinka,
za su kuma yi waƙar gaskiyarka.
Ubangiji mai alheri ne,
kuma mai tsananin tausayi ne,
mai jinkirin hushi,
mai tsananin tausayi kuma.
Ubangiji mai alheri ne ga kowa,
kuma tsananin tausayinsa na ga dukkan ayyukansa.
Dukkan ayyukanka za su gode maka, ya Ubangiji,
tsarkakanka kuma za su gode maka.
Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka,
su kuma yi mangar addu'arka,
don ya sanad da manya-manyan ayyukansa ga 'yan'adan,
da kuma ɗaukakar ikon mlkinsa.
Mulkinka mulki ne na har abada;
mallakarka kuwa dawamammiya ce cikin dukkan zamanai.
Ubangiji na tallafar dukkan abin da ke faɗuwa,
yana kuma ɗaga duk abin da ya sunkuya.
Idon kowa na ganin hanyarka,
kai ne kuma ka ke ba su abincinsu a kan kari.
Kai ne ka buɗe hannunka,
ka ke ƙosad da/ biyan/ bukatar kowane mai rai.
Ubangiji mai gaskiya ne a ckikin dukkan hanyoyinsa,
mai kuma alheri a dukkan ayyukansa.
Ubangij kusa ya ke da dukkan waɗanda su ke kiransa,
waɗanda su ke kiransa ta hanyar gaskiya.
Zai cika burin masu tsoronsa;
zai kuma ji kukansu, yă cece su.
Ubangiji na kiyaye dukkan masu ƙaunarsa;
amma zai hallaka dukkan miyagu.
Bakina zai yabi Ubangiji,
ya kamata kowane mahaluki
ya yabi tsattsarkan suansa har abada abadin.
146
Ku yabi Ubangiji.
Ka yabi Ubangiji, ya kai raina.
Zan yabi Ubangij muddar ina raye;
zan yi waƙoƙin yabo ga Allahna tun ina raye.
Kada ku dogara da sarakuna,
ko ɗan'adan wanda ba ya iya taimako.
Numfashinsa na fita,
shi kuwa ƙasa zai koma/ ƙasa makomatasa,
a ranan nan tunaninsa zai halaka.
Farinciki ya tabbata ga wanda Allahn Yakubu ne mataimakinsa,
wanda taimakonsa ke ga Ubangiji Allahnsa,
wanda ya halicci sama da ƙasa,
da bahar, da duka abin da ke cikinsu;
wanda ke riƙe da gaskiya har abada;
wadda ta ke zartada da hukunci
ga wanda aka zalunta;
ita kuma ta ke ba mayunwaci abinci.
Ubangiji shi ke sakin ɗaurarru.
Ubangiji shi ke buɗe idon makafi.
Ubangiji shi ke ɗaga waɗanda suka sunkunya/ aka ƙarƙartar;
Ubangiji na ƙaunar masu gaskiya.
Ubangiji na kiyaye baƙi;
yana renon marayu da matan da mazansu suka mutu;
amma yana birkita hanyoyin miyagu.
Ubangiji zai saran har abada,
wato Allahnki, ya ke Sihiyona, a kan dukkan zamanai.
Ku yabi Ubangiji.
147
Ku yabi Ubangiji.
Domin kyakkyawan abu ne a yi waƙoƙin yabo ga Allahmmu;
domin yana da daɗi, yabo kuma ya dace.
Ubangiji lalle yana gina Urushalima;
yana tattara Bani Isra'ila da aka kora/ watsa.
Yana warkad da masu karaya a zuci,
yana ɗaure musu raunukansu.
Yana faɗar adadin taurari;
yana sa musu dukkan sunayensu.
Ubangjimmu da girma ya ke,
mai ƙaƙƙarfan iko;
fahimtarsa ba ta da iyaka.
Ubangiji na tallafar mai tawali'u,
yana sauko da mugu har ƙasa.
Ku yi wa Ubangiji waƙa tare da gode masa;
ku yi waƙoƙin godiya a cikin molo ga Allahmmu.
Wanda ke lulluɓe sama da gajimare,
wanda ke yin ruwa saboda ƙasa,
wanda ke sa ciyawa ta tsira a kan duwatsu.
Yana ba dabba abincinta/sa,
da kuma 'ya'yan hankaki masu kuka.
Ba ya farinciki da ƙarfin doki,
baya kulawa da ƙafafuwan mutum;
Ubangiji na jin daɗin masu tsoronsa,
da waɗanda ke sa zuciya ga rahamarsa.
Ki yabi Ubangiji, ya ke Urushalima.
Ki yabi Ubangijinki, ya ke Sihiyona.
Domin shi ya ƙarfafa ƙyamarenki;
ya yi wa 'ya'yanki albarka a cikinki.
Yana haddasa aminci a iyakokinki;
yana cika ki da alkama mafi kyau.
Yana aiko da umarninsa duniya;
maganarsa tana gudana da sauri.
Yana ba da 'snow' kamar uku;
yana watsa 'hoar frost' kamar toka.
Yana zub da ƙanƙaratasa kamar loma;
wa zai iya jure wa sanyinsa?
Yana aiko da maganarsa
yana narkad da su;
yana sa iskatasa ta busa,
ruwa kuma yă yi gudu.
Yana nuna wa Yakubu maganatasa,
da dokokinsa da hukuncinsa ga Bani Isra'ila.
Bai y haka da kowace al'umma ba;
ba su kuwa san hukuncinsa ba.
Ku yabi Ubangiji.
148
Ku yabi Ubangiji.
Ku yabi Ubangiji daga sama,
ku yabe shi daga can sama.
Ya ku mala'ikunsa duka, ku yabe shi,
ya ku rundunarsa duka, ku yabe shi.
Ya ke rana da kai wata, ku yabe shi,
ku yabe shi, ya ku taurari asu haske.
Ku yabe shi, ya ku sammai na can ƙololuwa,
da kuma ku ruwayen da ke birbishin sama.
Bari su yabi sunan Ubangiji.
Domin unarni ya yi, sai aka halitta su.
Ya kuma tabbatad da su har abada abadin;
ya yi ka'idad da ba za ta wuce ba.
Ku yabi Ubangiji daga duniya,
ya ku dodanni da ku tekuna,
da wuta, da ƙanƙara, da 'snow', da tururi,
da iska mai hadiri mai cika maganarsa.
Da manyan duwatsu da tuddai,
da bishiyoyi masu haifuwa, da rimaye.
Da dabbobin jeji, da na gida duka,
da masu jan ciki, da tsuntsaye.
Da sarakunan duniya da dukkan mutane,
da 'ya'yan sarakuna da dukkan alkalan duniya.
Sammari da 'yam mata duka biyu,
da tsofaffi da yara.
Sai su yabi sunana Ubangiji,
domin sunansa ne kaɗai maɗaukaki;
ɗaukakarsa ta fi sama da ƙasa.
Ya kuma ɗaukaka maceci saboda jama'arsa,
abin yabon dukkan tsarkakansa,
wato Bani Isra'ila, mutanensa na kusa da shi.
Ku yabi Ubangiji.
149
Ku yabi Ubangiji.
Ku yi wa Ubangiji sabuwar waƙa,
da kuma yabonsa a cikin taron tsarkaka.
Sai Bni Isra'ila su yi farinciki da wannan da ya yi shi;
mutanen/ 'ya'yan/ Sihiyona su yi farinciki da Sarkinsu.
Su yabi sunansa game da rawa;
su yi waƙoƙin yabo da turumbel da molo.
Domin Ubangiji yana jin daɗin mutanensa;
zai kyautata mai sanyin hali da ceto.
Tsarkaka su yi tsananin farinciki game da ɗaukaka;
su yi waƙa saboda farinciki,
suna kwance kan gadajensu.
Bari maɗaukakin yabon Allah ya kasance a bakinsu
da kuma takobi a hannunsu,
don su zartad/ don su rauna/ da ramwa a kan al'ummai,
su kuma hori mutane,
su ɗaɗɗaure sarakunansu da sasura,
manyan ƙasar kuma da mari,
su zartad da ramuwannan a kansu wadda aka rubuta, wato,
Wannan ɗaukakar ta dukkan tsarkakansa ne.
Ku yabi Ubangiji.
150
Ku yabi Ubangiji.
Ku yabi Allah a cikin tsattsarkan wurinsa;
ku yabe shi a cikin al'arshinsa na iko.
Ku yabe shi saboda manya-manyan ayyukansa;
ku yabe shi bisa ga mafificin girmansa.
Ku yabe shi da busan kakaki;
ku yabe shi da garaya da molo.
Ku yabe shi da turumbel da rawa;
ku yabe shi da abubuwan wasa
masu tsirkiya da sarewa.
Ku yabe shi da kuge mai ƙara;
ku yabe shi da kuge mai amo ƙwarai.
Kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.
Ku yabi Ubangiji.