THE CANTICLES IN HAUSA

1 Tarihi 29:10-13

Yabo gare ka, Yahweh, * Allah na kakanmu Yakubu, * tun filazal har abada.

    Girma da iko naka ne, Yahweh, * da daraja da nasara da ɗaukaka.

    Dukan abin da ke a sama da ƙasa naka ne, Yahweh, * da mulki da sarautar kome da kome.

    Wadata da ɗaukaka daga wajenka suke, * kai ne ke mulkin duk kome.

    Daga hannunka ke ƙarƙo da iko, * daga hannunka ke girma da sarautar duk kome.

Yanzu, ya Allahnmu, muna gode maka, * muna yabon sunanka mai daraja.

1 Samaila 2:1-10

Zuciyata tana murna da Yahweh, * ina samun ƙarfi daga wurin Yahweh.

Ina yi wa maƙiyana dariya, * ina matuƙar murna domin ka taimake ni.

    Babu wani mai tsarki kamar Yahweh, * babu Dutse kamar Allahnmu.

    Kada ku ƙara yin magana ta girman kai, * kada fahariya ta fito daga bakinka.

    Gama Yahweh Allah ne masani, * Mai Iko ne wanda ke auna ayyuka.

        An kakkarya bakan jarumai, * amma aka sa wa raunannu ƙarko.

        Ƙosassu suna wadago don abinci, * amma mayunwata ba su bukatar aiki.

            Bakarariya ta haifi yaya bakwai, * amma mai yawan yaya ta rasa su.

            Yahweh na kashewa, ya kuma rayar, * yana kai wa Shawol, ya ma jawo.

            Yawheh na talautarwa, ya ma arzuta, * yana ƙasƙantarwa, ya ma ɗaukaka.

        Yana ɗaga matalauta daga ƙura, * ya tā da mabukata daga wurin bola,

        don ya zaunad da su tare da yan sarakuna, * ya ba su kursiyi mai daraja.

    Domin harsassan duniya na Yahweh ne, * a kansu ya kafa duniya.

    Yana lura da tafiyar masu bautarsa, * amma miyagu za su halaka a Duhu.

    Domin ba ƙarfin mutum ke sa ya yi nasara ba, * Yahweh zai kakkarya masu yi masa tawaye.

Maɗaukaki zai tsautar daga sama, * Yahweh zai hukunta har iyakokin duniya.

Zai ba sarkinsa iko, * ya tā da ƙarfin shafaffen sarkinsa.

Daniyel 3:26-7,29,34-41

Yabo gare ka, Yahweh, Allah na kakanninmu, * sunanka ya cancanci yabo da ɗaukaka har abada.

    Gama kai mai adalci ne a duk abin da ka yi mana, * dukan ayyukanka na gaskiya ne.

    Hanyoyinka kuma ba su da aibu, * ai, dukan shariunka na zahiri ne...

        Ai, ta zunubanmu da ƙin manufa ne, * muka bauɗe maka.

        Mun yi saɓo a kowane abu, * ba mu yi biyayya da dokokinka ba....

            Don darajar sunan nan naka, * kada ka ba da mu kwatakwata, * kada ma ka zare yarjejeniyarka.

            Kada ma ka janye jinƙanka daga gunmu, * saboda Ibrahim ƙaunataccenka,

            da kuma Isiyaku bawanka, * da mai tsarkin nan naka, Israila,

                waɗanda ka yi alkawari ta kansu, cewa * jikokinsu za su yi yawan gaske,

                kamar taurarin sama, * ko rairayin da ke bakin teku.

            Yanzu, Yahweh, mun fi sauran alummai salwanta, * an ma yi mana ƙasƙanci kwanan nan a dukan duniya, * saboda zunubanmu ne kuwa.

            A wannan lokaci ma ba mu da sarki ko annabi, ko shugaba, * ba hadayar ƙonawa, ko hadaya, ko baiko, ko turaren ƙonawa,

            ba gun da za a miƙa hadaya a gabanka, * ta neman jinƙai.

        Duk da haka, don muna da karyayyar zuciya da ruhun tuba, * sai ka karɓe mu.

        Kamar dai yadda ka karɓi hadayun ƙonawa na raguna da na bajimai, * da kuma na yayan raguna masu kiɓa dubbai bisa dubbai,

        haka ma ka karɓi hadayarmu ta yau, * domin muna binka sau da ƙafa.

    Gama duk wanda ya dogara gare ka, * ko kaɗan ba zai kunyata ba.

Yanzu mun bi ka da dukan zuciya, * kanmu ƙasa, hannunmu baya, * muna neman fuskarka.

Daniyel 3:57-88,56

Maimaitawa: Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.

Ku yabi Yahweh, ayyukan Yahweh duka, * ku yabi Yahweh, malaikun Yahweh.

Ku yabi Yahweh, sammai da birbishin ƙasa, * ku yabi Yahweh, ruwayen birbishin duniya.

Ku yabi Yahweh, dukan ikokinsa, * ku yabi Yahweh, rana da wata masu haske.

Ku yabi Yahweh, taurarin sama, * ku yabi Yahweh, tsattsafi da raɓa.

Ku yabi Yahweh, iska da hadari, * ku yabi Yahweh, wuta da zafi.

Ku yabi Yahweh, jaura da sanyi, * ku yabi Yahweh, ƙanƙara da dusar ƙanƙara.

Ku yabi Yahweh, dare da rana, * ku yabi Yahweh, haske da duhu.

Ku yabi Yahweh, walƙiya da girgije, * ki yabi Yahweh, ya ke duniya.

Ku yabi Yahweh, duwatsu da tuddai, * ku yabi Yahweh, mabunƙusa ƙasa.

Ku yabi Yahweh, maɓuɓɓugan ruwa, * ku yabi Yahweh, tekuna da koguna.

Ku yabi Yahweh, kifaye manya da ƙanana, * ku yabi Yahweh, tsuntsayen sama.

Ku yabi Yahweh, dabbobin duniya, * ku yabi Yahweh, yan adan.

Ku yabi Yahweh, Israilawa, * ku yabi Yahweh, firistocin Yahweh.

Ku yabi Yahweh, bayin Yahweh, * ku yabi Yahweh, masu halin adalci.

Ku yabi Yahweh, tsarkaka masu sanyin hali, * ku yabi Yahweh, Hananiya, da Azariya, da Mishayel.

Yabo ya tabbata gare ka a sararin sama, * a yabe ka, a girmama ka har abada.

Daniyel 3:52-57

Yabo gare ka, Yahweh, Allah na kakanninmu, * a yabe ka, a girmama ka har abada.

Yabo ga tsattsarkan sunanka mai daraja, * a yabe ka, a girmama ka har abada.

Yabo gare ka a Haikalin ɗaukakarka mai tsarki, * a yabe ka, a girmama ka har abada.

Yabo gare ka, a bisa kursiyinka, * a yabe ka, a girmama ka har abada.

Yabo gare ka, wanda ke zaune a bisa kerubobi, * a yabe ka, a girmama ka har abada.

Yabo gare ka, mai duba zurfin duniya, * a yabe ka, a girmama ka har abada.

Yabo gare ka a sararin sama, * a yabe ka, a girmama ka har abada.

Ku yabi Yahweh, ayyukan Yahweh, * ku yabe shi, ku girmama shi har abada.

Maimaitawar Sharia 32:1-12

Ku saurara, ku sammai, zan yi magana, * bari duniya ta ji kalmar bakina.

Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama, * kalmata ta faɗo kamar raɓa,

kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa, kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.

    Gama zan yi shelar sunan Yahweh. * Ku yabi girman Allahnmu!

    Dutsen nan, aikinsa cikakke ne, * dukan hanyoyinsa masu adalci ne.

    Allah mai aminci ne, baya yaudara, * mai adalci ne, mai kirki.

        Sun aikata ƙeta a gabansa, * su ba yayansa ba ne saboda lalacewarsu, * su muguwar tsara ce, karkatacciya.

        Haka za ku sāka wa Yahweh, * ku wawaye marasa hikima.

        Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba, * wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku?

            Ku fa tuna da kwanakin dā, * ku yi tunani a kan shekarun da suka wuce.

            Ku tambayi mahaifanku, za su faɗa maku, * ku tambayi dattawanku, su za su gaya maku.

        Saad da Maɗaukaki ya ba alummai gādonsu, * saad da ya raba yan adan,

        ya auna iyakokin alummai, * don kowacensu ta sami ɗan allahnta.

        Amma Yahweh ya zaɓi Israila don kansa, * Yakubu shi ne rabon gādonsa.

    Ya same shi a cikin hamada, * a jeji mai rurin iskoki.

    Ya kewaye shi, ya lura da shi, * ya kiyaye shi kamar ƙwayar ido.

Kamar gaggafar da ke lura da sheƙarta, * tana rufe yayanta,

haka ya miƙa fukafukansa, ya ɗauke shi, * ya tafi da shi a kan fukafukansa.

Yahweh ne kaɗai ya bishe shi, * ba wani baƙon allah tare da shi.

Fitowa 15:1-4a,8-13,17-18

Zan raira waƙa ga Yahweh, * gama ya ci gawurtacciyar nasara.

Doki da mahayinsa * ya jefar cikin bahar.

Yahweh ƙarfina ne, ina yabonsa, * shi ne wanda ya cece ni.

    Wannan ne Allahna, zan girmama shi, * Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.

    Yahweh mayaƙi ne, * sunansa Yahweh.

        Karusan Firaauna da rundunarsa * ya jefar cikin bahar...

        Da hucin lumfashin hancinka * ruwa ya tattaru.

        Rigyawa ta tsaya kamar tudu, * zurfafan ruwaye suka daskare a tsakiyar bahar.

            Magabcin ya ce, * "Zan bi, in kama su,

            in kwashi ganima, * muradina a kansu zai biya,

            zan zare takobina, * hannuna zai halaka su."

                Ka hura iskarka, * bahar ta rufe su,

                suka nutse kamar darma * cikin manyan ruwaye.

            Yahweh, wanene kamarka cikin alloli? * wa ke kamarka cikin ɗaukaka da tsarki?

            Mai banrazana ta yin alajibai, * mai aikata muujjiza.

            Ka miƙa hannunka na dama, * ƙasa ta haɗiye su.

        Amma da ƙaunarka ka ja gorar * jamaarka da ka fansa.

        Ka bi da su da ƙarfinka * zuwa tsattsarkan mazauninka...

    Za ka kawo su, ka dasa su * a kan dutsen da ka zaɓa,

    wurin mazauninka, * wanda kai, Yahweh, ka kafa,

    tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, * wanda hannuwanka suka yi.

Yahweh zai yi mulki * har abada abadin.

Ezekiyel 36:24-28

Ga abin da Ubangiji Yahweh ya faɗi: * "Zan kwaso ku daga cikin alummai,

in tattaro ku daga dukan ƙasashe, * in kawo ku cikin ƙasarku.

    Zan yayyafa maku tsabtaccen ruwa, * za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku. * Zan tsarkake ku daga dukan gumakanku.

        Zan ba ku sabuwar zuciya, * in sa sabon ruhu a cikinku.

        Zan cire zuciyar dutse daga gare ku, * saan nan in sa maku zuciyar nama.

    Zan sa ruhuna a cikinku, * in sa ku bi kaidodina, * ku himmanta ga aikata hukuntaina.

Za ku zauna cikin ƙasar * da na ba kakanninku.

Za ku zama mutanena, * ni kuma in zama Allahnku."

Habakuk 3:2-4,13a,15-19

Yahweh, na ji labarinka, * Yahweh, ayyukanka sun ba ni tsoro.

Ka maimaita su a zamaninmu, * a kwanakinmu ka sanar da su! * Duk da fushinka, ka tuna da yin jinƙai.

    Daga Teman Allah ke fitowa, * daga Dutsen Faran Tsattsarkan nan ke tahowa.

    Ɗaukakarsa ta rufe sammai, * duniya kuwa ta cika da girmansa.

        Ƙyallinsa yana annuri kamar hasken rana, * walƙiyoyi na fitowa daga hannuwansa, * can ne maɓoyin ikonsa...

    Ka fito saboda ceton jamaarka, * saboda ceton shaffafen sarkinka...

    Da dawakanka ka tattake teku * da haukan ruwa mai ƙarfi.

    Da na ji, sai jikina ya yi rawa, * leɓunana suka raurawa,

    ƙasusuwana suka rabke, * ƙafafuna suka girgiza.

        Amma da kwanciyar rai ina jiran masifar * da za ta auko wa waɗanda suka kawo mana yaƙi.

    Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba, * ba kuma yaya a kuringar inabi,

    zaitun kuma bai ba da amfani ba, * gonaki ba su ba da abinci ba,

    tumaki sun ɓace daga garke, * ba kuma shanu a turaku,

    duk da haka zan yi farinciki da Yahweh, * in yi murna da Allah Macecina.

Yahweh Ubangijina shi ne ƙarfina, * yana sa in yi tsalle kamar barewa, * yana kuma bishe ni zuwa kan duwatsu.

Ishaya 2:2-5

A kwanaki masu zuwa, * dutsen gidan Yahweh zai kafu

bisa sauran duwatsu, * zai fi dukan tuddai tsawo.

Dukan alummai za su malalo gare shi, * mutane masu yawa za su zo, su ce:

    "Bari mu je dutsen Yahweh, * zuwa gidan Allah na Yakubu,

    don ya koya mana hanyoyinsa, * mu kuwa bi labobinsa.

    Domin dokokinsa na fitowa daga Sihiyona, * maganar Yahweh kuwa daga Urushalima.

    Zai hukunta tsakanin alummai, * zai sharianta mutane masu yawa.

Za su naɗe takubbansu su zama garemani, * masunsu ma su zama laujuna.

Alumma ba za ta yi yaƙi da wata alumma ba, * ba za su ƙara koyon yaƙi ba.

Gidan Yakubu, zo, * mu yi tafiya da hasken Yahweh.

Ishaya 12:1-6

Ina yabonka, Yahweh, ko da yake ka yi fushi da ni, * gama fushinka ya wuce, ka yi mani taaziya.

    Hakika, Allah ne Macecina, * ina da sazuciya, bana tsoro.

        Yahweh ƙarfina ne, ina yabonsa, * Yahweh ne wanda ya cece ni.

    A ranan nan za ku jawo ruwa da farinciki * daga idon ruwan ceto,

    kuna cewa: "Ku gode wa Yahweh, * ku yi kirarin sunansa.

        Ku sanar wa alummai alajibansa, * ku bayyana yadda sunansa yake da girma.

    Ku raira waƙa ga Yahweh saboda manyan ayyukan da ya yi, * bari dukan duniya ta ji labarin.

Mazaunan Sihiyona, ku yi sowa da waƙa, * domin Tsattsarkan nan na Israila girma gare shi a cikinku.

Ishaya 26:1-4,7-9,12

Muna da birni ƙaƙƙarfa, * garunsa da ganuwarsa na tsare mu.

Ku buɗe ƙofofinsa, * a bar alumma mai gaskiya ta shiga.

Suna kiyaye aminci, * aniyarsu ta tabbata.

    Kana ba su cikakkiyar salama, * domin sun dogara gare ka.

    Ku dogara ga Yahweh har abada, * domin Yahweh madauwamin Dutse ne...

        Hanyar mai gaskiya daidai take, * kana mai da labinsa bai ɗaya sumul.

        I, ta bin hanyar hukuntanka, * Yahweh, muna sa zuciya gare ka.

    Sunanka da shahararka, * su ne abin da muke marmari.

    Raina yana marmarinka da dare, * ruhuna a cikina yana begenka.

Gama da hukuntanka suka zo duniya, * mazaunanta sun koyi gaskiya...

Yahweh, kā ƙaddara mana salama, * domin dukan ayyukanmu, kai ne ka yi su.

Ishaya 33:13-16

Ku da ke nesa, ku ji abin da na yi, * ku da ke kusa, ku gane ikona!

A Sihiyona masu zunubi ke firgita, * makyarkyata ta kama marasa ibada, suka ce:

"Wanene daga cikinmu zai iya zama da wutan nan mai cinyewa? * Wanene daga cikinmu zai iya zama da dauwamiyyar gobara?"

    Wanda ya bi adalci, ya yi maganar gaskiya, * ya ƙi kuɗin cuta,

    ya hana hannuwansa karɓar toshi, * ya toshe kunnuwansa ga maganar kisan kai, * ya rufe idanunsa ga muguwar dabara,

wannan zai zauna a wurin mai sama, * mafakar duwatsu matserarsa ce.

Za a kai masa abincinsa, * ruwan shansa ba zai ƙare ba.

Ishaya 38:10-14,17b-20

Na ce, "A gaɓar ƙarfina * ina ta ƙaura.

An sanya ni a ƙofofin Shawol * sauran rayuwata."

Na ce, "Ba zan ƙara ganin Yahweh * a duniyar masu rai ba.

Ba zan ƙara ganin mutun * gun mazaunan Gidan Hutu ba."

    An tumɓuke ɗakina, an naɗe shi * an ɗaukan mani shi kamar alfarwar makiyayi.

    Kamar masaƙi kā naɗe rayuwata, * kā yanke ta daga gindin saa.

        Da rana da dare kana tsananta mani, * ina ta kuka dukan dare.

        Kamar zakin da ke kakkarya ƙasusuwana, * kana tsananta mani dukan yini.

        Ina kuka da ɓacin rai kamar tsattsewa, * kamar kurciya ina ta yin waƙar makoki.

        Idanuna na duban sama da gajiya, * ya Ubangiji, ina shan wahala, ka lura da ni...

    Kā hana raina * shiga Ramin Halaka.

    Kā jefa dukan zunubaina * a bayanka.

Gama Shawol ba za ta gode maka ba, * Mutuwa ma ba za ta yabe ka.

Masu gangara wa Kabari * ba su jiran tausayinka.

    Sai dai masu rai ne za su yabe ka, * kamar yadda nike yi yau.

    Uba zai faɗi * wa yayansa amincinka.

Yahweh, ka cece mu, * za mu kuwa yi maka waƙa

dukan kwanakin rayuwarmu * a gidan Yahweh.

Ishaya 40:10-17

Ga shi, Ubangiji Yahweh na zuwa da iko, * yana mulki da ƙarfin dantsensa.

Ya rigaya ya sami lada, * yana da amfanin aikinsa.

Kamar makyayi ne yana kiwon garkensa, * yana tattara yan raguna da hannuwansa,

yana rungumarsu a ƙirjinsa, * yana bi da tumaki kuma.

    Wa ya taɓa ƙirga yawan ruwan teku da hannunsa, * ko ya auna sararin sama da tafinsa?

    Wa ya taɓa ƙirga yawan ƙasa da buhu, * ko ya auna nauyin duwatsu a maauni da tuddai da mizani?

        Wa ya taɓa auna ruhun Yahweh, * ko ya zama mashawarcinsa mai ba shi labari?

    Wa ya taɓa shawarta don ya fahimce shi, * ya kuwa koya masa hanyar hukunci,

    ya koya masa ilimi, * ya nuna masa hanyar fahimi?

A gare shi, alummai kamar ɗigon ruwa ne a bokiti, * ko ƙura bisa maauni, * garuruwan da ke gaɓar teku ba su fi toka nauyi ba.

Kurmin Labanan baya da isasshen icen wuta, * ko dabbobin da ake bukata don baikon ƙonawa.

Dukan alummai ba kome ba ne a gare shi, * banza a banza ne gunshi.

Ishaya 42:10-16

Ku raira sabuwar waƙa ga Yahweh, * har bangon duniya ku yabe shi,

ku masu tafiya a kan teku da duk da ke cikinsa, * ƙasashen da ke gaɓar teku da mazaunansu.

    Ku ta da murya, ku ƙauyukan daji, * da sansanan mutanen Kedar kuma!

    Ku yi sowa, ku mazaunan garin Dutse, * ku yi kururuwa daga ƙwanƙolin duwatsu!

    Ku yi shelar ɗaukakar Yahweh, * ku yabe shi da mutanen da ke gefen teku!

        Yahweh na fita kamar jarumi, * kamar mayaƙi yana ta da aniyarsa.

        Yana gunzar kirarin yaƙi, * yana kai wa magabtansa hari, yana cewa:

        "Na daɗe ina yin shiru, * ina haƙuri ba tare da magana ba.

        Amma yanzu ina kamar macen da ke naƙudda, * ina ƙugi da nishi da haki.

    Zan lalatar da duwatsu da tuddai, * in busar da dukan ciyawarsu.

    Zan mai da kwaruruka hamada, * in busar da fadamu.

Saannan zan yi wa mutanena makafi jagora * a hanyoyin da ba su taɓa bi ba.

A kan labunan da ba su sani ba * zan bi da su.

Zan sa duhu ya zama haske a gabansu, * karkatacciyar hanya ta zama daidai.

Ishaya 45:15-25

Lalle, kai ne ɓoyayyen Allah, * ya Allah na Israila Maceci.

    Masu yin gumaka * sun kunyata, sun sha ƙasƙanci,

        dukansu tare, * sun zama abin kunya.

        Amma ceton Israila daga wurin Yahweh yake, * dauwamammen ceto ne.

    Ba za su kunyata ko su sha ƙasƙanci ba * a zamanai duka nan gaba.

    I, Yahweh ne, * Mahallicin sama,

        Allah ne, * wanda ya shata ƙasa, ya yi ta, ya kafa ta.

            Bai halicce ta hamada ba, * amma wurin zaman mutane.

            In ji shi, "Ni ne Yahweh, * ba wani Allah.

        Ba a ɓoye na yi magana ba, * ko a duhun lungun duniya.

    Ban taɓa cewa da jikokin Yakubu, * Ku neme ni a hamada ba.

Amma ni, Yahweh, ina faɗin gaskiya, * ina sanar da abin da ke daidai.

Ku tattaru, ku zo wuri guda, * ku masu tsira ta gudun hijira.

    Ba su san kome ba, * su da ke ɗaukar gumakansu na ice,

        suna addua ga allolin * da ba su iya yin ceto.

        Bari su yi magana, su gabatar da matsalarsu, * su shawarci juna.

    Wanene ya sanar da abin da zai faru tun dā, * ya kuma yi annabci tuntuni?

        Ashe, ba ni ba ne, * Yahweh Allah, * da ba wani sai ni?

            Ba Allah na gaskiya, * mai yin ceto, sai ni.

            Ku juyo gare ni don ku kuɓuta, * ya mutanen koina a duniya,

        domin ni ne Allah, * ba wani.

    Na yi rantsuwa da kaina, * na faɗi gaskiya, * ba canjin abin da na ƙaddara:

        Gwiwar kowa za ta durƙusa a gabana, * kowa zai yi shahada, cewa:

        Daga Yahweh ne * nasara da iko ke zuwa."

    Amma duk masu yi masa tawaye * za su zo gabansa da kunya.

Ta wurin Yahweh dukan jikokin Israila * za su sami nasara da ɗaukaka.

Ishaya 61:10- 62:5

Ina farinciki ƙwarai da Yahweh, * na yi murna da Allahna.

Domin ya suturce ni da rigar ceto, * ya sa mayafin nasara a kaina.

Ina kamar angon da ya sa rawani, * kamar amaryar da ta sa adonta.

    Kamar yadda ƙasa ke fitad da tohonta, * lambu kuma ke tsirad da yabanya,

    haka Yahweh zai sa gaskiya da yabo * su tsira a gaban dukan alummai.

        Ba zan yi shiru a kan Sihiyona ba, * ba kuwa zan bebance game da Urushalima ba,

        sai cetonta ya fito kamar haske, * nasararta kuma ta haskaka kamar fitila.

            Alummai za su ga nasararki, * dukan sarakunansu kuma ɗaukakarki.

        Za a kira ki da sabon suna, * wanda bakin Yahweh zai raɗa.

        Za ki zama kambin ɗaukaka a hannunYahweh, * da rawanin mulki a hannun Allahnki.

    Ba za a ƙara kiranki "Korarriya" ba, * ko ƙasarki "Kufai",

    Amma za a kira ki "aunatacciya", * da ƙasarki "Amarya".

    Gama Yahweh na jin daɗinki, * don yana auren ƙasarki.

Kamar yadda saurayi ke auren matarsa, * haka Mai Gininki zai aure ki.

Kamar yadda ango ke murna da amaryarsa, * haka Allahnki zai yi murna da ke.

Ishaya 66:10-14

Ku yi murna tare da Urushalima, * duk masu sonta, ku yi farinciki tare da ita!

Ku yi murna tare da ita yanzu, * dukanku da kuka yi makoki dominta!

    Yanzu ku sha, ku ƙoshi * daga mamanta na taaziya.

    Yanzu ku sha, ku ji daɗi * daga ƙirjinta mai yawan nono.

        Gama, in ji Yahweh, * "Yanzu ina sa salama ta malalo mata kamar kogi, * da wadatar alummai kamar rigyawa.

    Za ta goye ku, ta yi renonku, * za ta kuma rungume ku a ƙirjinta.

    Kamar yadda uwa ke taaziyar yaronta, * haka ni zan yi taaziyarku, * za ku taazantu a Urushalima.

Da kuka ga wannan zuciyarku za ta faranta, * jikunanku kuma za su yi yabanya kamar ciyawa.

Irmiya 14:17-21

Idanuna suna zub da hawaye * dare da rana,ba denawa,

saboda babbar masifar da ta faru * ga budurwar da ke jamaata, * sai ta raunana ƙwarai.

    Idan na tafi cikin saura, * sai in ga waɗanda aka kashe da takobi.

    Idan na shiga birni, * sai in ga waɗanda ke fama da yunwa.

    Har annabi da firist * suna yawon neman abinci inda ba su san kowa ba.

        Ka ƙi Yahuda ke nan ɗungum? * ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne?

    Me ya sa ka buge mu, * har da ba za mu iya warkewa ba?

    Muna zuba ido ga samun salama, * amma ba wani alheri da ya zo.

    Muna sa zuciya ga warkewa, * amma sai razana.

Yahweh, mun san muguntar da muka yi, * da wadda kakanninmu suka yi, * gama mun yi maka zunubi.

Saboda darajar sunanka, kada ka yashe mu, * kada kuma ka rena Sihiyona, kursiyin ɗaukakarka.

Ka tuna da yarjejeniyar da ka yi mana, * kada ka ta da ita.

Irmiya 31:10-14

Ku ji maganar Yahweh, ku alummai, * ku yi shelarta har ƙasashen hayin ruwa.

Ku ce: "Wanda ya warwatsa Israila zai tattaro shi, * zai kiyaye shi kamar yadda makiyayi yakan kiyaye garkensa."

Gama Yahweh ya fanshi Yakubu, * ya ciro shi daga hannun da ya fi shi ƙarfi.

    Za su zo su yi waƙa a bisa ƙwanƙolin Sihiyona, * za su gudano ga alheran Yahweh,

    ga hatsi da abinshan inabi da mai, * ga yan raguna da na shanu.

    Rayuwarsu za ta zama kamar lambu, * ba za su ƙara yin yaushi ba.

    Yan mata za su yi rawa da farinciki, * samari da tsofaffi za su yi murna.

Zan mai da makokinsu ya zama murna, * in taazantar da su, in ba su farinciki maimakon baƙinciki.

Zan wadaci firistoci da abinci mai yawa, * jamaata kuma za su ƙoshi da alherina.

Bayahudiya 16:1-2,13-16

Ku soma yi wa Allahna waƙa da tambura, * ku yi wa Yahweh yabo da kuge.

Ku raira masa sabuwar waƙa mana, * ku ɗaukaka shi, ku kuma kira bisa sunansa.

    Gama Allah mai tattake yaƙe-yaƙe, * shi ne Yahweh...

    Ai, dole in raira wa Allahna sabuwar waƙa., * Yahweh, ai, kai mai girma ne da ɗaukaka, * mai tsananin iko, ba mai iya karawa da kai.

        Ka sa dukan halittunka su yi maka hidima, * gama magana kawai ka yi, sai suka wanzu.

        Kai ne ka aiko da numfashinka, ka halitta su, * ai, ba mai iya yin jayayya da kalmarka.

    Gama ko da an jijjige gindin tsaunuka da zurfin tekuna, ko da duk duwatsu sun narke kamar dano a gabanka,

    ga masu tsoronka * za ka nuna jinƙai.

Gama kowace irin hadaya mai ƙanshi ƙaramar aba ce, * haka ma hadayun ƙonawa masu kitse.

Amma duk mai tsoron Yahweh, * shi ne mai girma har abada.

Hikima 9:1-6, 9-11

Ya Allah na kakannina, Ubangijin jinai, * wanda ka halicci kome ta kalmarka,

ta hikimarka ka sifanta mutun, * don ya mallaki abubuwan da ka halitta,

ya mallaki duniya da tsarki da adalci, * ya zartad da sharia da adalcin zuciya,

    ka ba ni hikimar da ke kewaye da kursiyinka, * kada ma ka ware ni daga cikin yayanka,

        gama ni bawanka ne * kamar yadda iyayena suke dā,

        mutun ne kuma, ina da kwanakin rai yan kaɗan, * na kasa gane sharia da kaidodinka.

            Ko da ɗan adan ya zama cikakke, * in ya rasa hikimarka zai fāɗi ba nauyi...

        A wurinka hikima take wadda ta san aikinka, * a kan idanunta ne ma lokacin da ka halicci duniya,

        ta san abin da ke faranta maka rai, * da kuma abin da ya wajaba a bi cikin dokokinka.

    Sai ka kwararo ta daga sammanka masu tsarki, * ka ma aiko ta daga kursiyin ɗaukakarka,

don ta zauna da ni, ta yi aiki a cikina, * ai, ta haka ne zan san abin da ke daidai a gabanka.

Gama ita ta sani, ta kuma gane dukan kome, * za ta kāre ni da himma a cikin aikina, * ta bi da ni da ɗaukakarta.

Sirak 36:1-5,10-13

Ka cece mu, ya Allah na dukan halitta, * ka sa sauran alummai su ji tsoronka.

Ka nuna wa maƙwabtan alummai ƙarfi, * domin su ga ikonka zahiri.

    Yadda ka hore mu domin ka nuna masu tsarkinka, * ka hore su, su ma, domin ka nuna mana ɗaukakarka.

    Ka sa su san ka, yadda muka san ka, * su sani, ba wani Allah sai dai kai.

        Ka koma wa aikinka na alajabi, ka yi sababbin alamu, * tashi, ka gwada dantsenka....

        Ka tara dukan kabilan Yakubu, * don su gaji ƙasarsu, kamar yadda yake a dā.

    Ka yi jinƙai a kan alummar da ake kira da sunanka, * a kan Israila wanda ka kira ɗan farinka.

    Ka ji ƙan tsattsarkan birninka, * Urushalima, mazaunin zatinka.

Ka cika Sihiyona da darajarka mai girma, * Haikalinka kuma da ɗaukakarka.

Tobi 13:2-8

Yabo ga Allah wanda ke raye har abada, * gama mulkinsa ya tabbata har abada!

Yana raunanawa, yana yin jinƙai, * yana aikawa da mutane Zurfafan Lahira,

ya kuma zaro su daga babbar halaka, * ai, ba mai iya kuɓuta daga hannunsa.

    Ku yabe shi a gaban alummai mana, ku Israilawa, * ai, ko da ya yi ɗaiɗai da ku a tsakaninsu, * a can ma ya nuna muku ikonsa a fili.

    Ku ɗaukaka shi a gaban dukan mutane, * gama shi ne Yahweh Allahnmu, * shi ubanmu ne da Allahnmu, har abada abadin.

        Ko da yake ya hore ku a kan zunubanku, * ai, zai ma ji tausayin dukanku.

        Zai tattaro ku gu ɗaya daga sauran alummai, * daga duk inda aka yi ɗaiɗai da ku a dā.

            In dai kun juya gare shi da dukan zuciyarku, * kuna aikata aikin gaskiya a gabansa,

            Saannan zai juyo gare ku, shi ma, * ba kuma zai ƙara ɓoye muku fuska ba.

            Ku dubi dai irin abin kirkin da ya yi muku, * ku gode masa mana, kai jamaa!

            Ku yabi Ubangijin adalci, * ku kuma ɗaukaka Sarkin dukan zamanai!

        Ai, ni ma nakan yi waƙar yabonsa * a lokacin da nake bawan yaƙi a wani gari.

        Na sanar da ikonsa da girmansa a fili * ga alummar da take yin saɓo.

    Ai, ku masu saɓo, sai ku juya gunsa, * ku dai kasance da hali mai kyau.

    Lalle zai yi muku alheri, * ya kuma ji tausayinku.

Ni ma ina ɗaukaka Allah, * raina kuma yana yin fari fat da Sarkin nan na Sama.

Bari girmansa ya zauna a bakin dukan mutane, * a yi waƙar yabonsa a Urushalima.

Tobi 13:8-14

Bari girmansa ya zauna a bakin dukan mutane, * a yi waƙar yabonsa a Urushalima.

Ya Urushalima, birni mai tsarki, * Allah ya raunana ki a kan gumakan da kika yi, * amma duk da haka zai ji tausayin yayanki, adalai.

    Ki gode wa Allah saboda alherinsa, * ki yabi Sarkin dukan zamanai!

    Domin za ki yi farinciki * da ganin an sāke gina masujadarsa a cikinki.

    Zai kuma dawo miki da bayin yaƙinki, * ya taazanta su a cikinki.

    Dukan waɗanda ke baƙinciki zai ƙaunace su a cikinki, * har dukan zamanai masu zuwa.

        Ai, hasken haske zai haskaka * a kan duk sashe na duniya.

            Kabilai za su bangazo gare ki daga wurare masu nisa, * daga wannan bangon duniya zuwa wancan, * domin su ji labarin alherin da Yahweh ya yi miki,

        suna da kyautai a hannunsu * domin Sarkin Sama.

    A cikinki, tsara za ta bi tsara, * suna bayyana matuƙar farincikinsu a kanki.

    Har ga yan zamanin nan na gaba, * kowa zai san Allah ya zaɓe ki.

    Yanzu dai, sai ki yi murna * da yayanki adalai,

    gama za a tara su duka a gu ɗaya, * su yabi Ubangijin dukan zamanai.

Albarka ta tabbata gun masu ƙaunarki, * da waɗanda ke naam da zaman alamarki.

Masu albarka ne kuma su da suka yi makoki * a kan dukan wahalarki.

Filibiyawa 2:6-11

Ko da yake surar Allah yake, * Yesu bai mai da daidaitakan nan tasa da Allah * abar karabkiya ba,

sai ma ya mai da kansa baya matuƙa * ta ɗaukar surar bawa, * da kuma kasancewa da kamannin ɗanadan.

    Da ya bayyana da siffar mutum, * sai ya ƙasƙantad da kansa ta yin biyayya,

        har wadda ta kai shi ga mutuwa, * mutuwar ma ta kan gicciye.

    Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, * kuma ya yi masa baiwa da sunan nan * da ke birbishin kowane suna,

don dai kowace gwiwa sai ta rusuna * wa sunan nan na Yesu, * a sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa,

kowane harshe kuma ya yarda cewa * Yesu Almasihu Ubangiji ne, * don ɗaukaka Allah Uba.

Wahayin Yahaya 19:1,5-8

Halelu-Yah! Yin ceto, da ɗaukaka, da iko, sun tabbata ga Allahnmu,       Halelu-Yah!

    don hukuncinsa daidai yake, kuma na gaskiya ne.                        Halelu-Yah, Halelu-Yah!

Halelu-Yah! Ku yabi Allahmmu, ya ku bayinsa,                                       Halelu-Yah!

    ku da ke jin tsoronsa, yaro da babba.                                            Halelu-Yah, Halelu-Yah!

Halelu-Yah! Gama Ubangiji Allahmmu Maɗaukaki shi ke mulki,             Halelu-Yah!

    mu yi murna da farinciki matuƙa, mu kuma ɗaukaka shi.             Halelu-Yah, Halelu-Yah!

Halelu-Yah! Don bikin Ɗan Ragon nan ya zo,                                          Halelu-Yah!

    amaryatasa kuma ta kintsa.                                                           Halelu-Yah, Halelu-Yah!

Halelu-Yah! An yarje mata ta sa tufafi lallausa                                          Halelu-Yah!

    mai ɗaukar ido, mai tsabta.                                                           Halelu-Yah, Halelu-Yah!

Halelu-Yah! Ɗaukaka ga Uba da ga Ɗa da ga Ruhu Mai Tsarki,               Halelu-Yah!

    yanzu da har abada.                                                                      Halelu-Yah, Halelu-Yah!

Afisawa 1:3-10

Mai albarka Allah da Uba * na Ubangijimmu Yesu Almasihu!

Gama ya yi mana albarka da kowace albarka mai ruhaniya * a muƙaman sama * ta kan Almasihu.

    Allah ya zaɓe mu ta kansa * tun ba a halicci duniya ba

mu zama tsarkaka, * marasa aibu a gabansa.

        Ta ƙaunarsa ya ƙaddara mu *ga zama yayansa

            ta kan Yesu Almasihu * bisa nufinsa na alheri,

                don mu yabi ɗaukakar alherinsa * wanda ya ba mu kyauta hannu sake ta kan Ƙaunataccensa.

            Ta gare shi ne muka sami fansa * albarkacin jininsa, * watau yafewar laifuffukammu,

        bisa yalwar alherin Allah, * wanda ya yi mana falala * da matuƙar hikima da basira.

    Ya sanasshe mu * zuzzurfan alamarin nufinsa:

    — bisa alherin da ya yi wa Almasihu * don ya shugabanci cikar zamanai —

a harhaɗa dukan abubuwa ta kan Almasihu, * watau, duk da ke sama * da duk da ke ƙasa.

Wahayin Yahaya 4:11; 5:9-10,12

Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahmmu, * ka sami ɗaukaka da girma da iko.

Don kai ne ka halicci dukan abubuwa, * da nufinka ne suka kansance kuma aka halicce su...

    Ɗan Ragon Allah, macancanci ne kai * ka ɗauki littafin nan, * ka ɓamɓare hatimansa.

        Domin dā an kashe ka, * kuma ka fanso wa Allah mutane ta jininka * daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jamaa, da kowace alumma.

    Ka mai da su jamaa, * kuma firistocin Allahmmu, * suna kuwa mulki a duniya...

Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka yanka * ya sami iko,

da wadata, da hikima, da ƙarfi, * da girma, da ɗaukaka, da yabo.

Kolasiyawa 1:12-20

Ku gode wa Uba, * wanda ya maishe ku isa samun rabo

cikin gadon tsarkakan * da ke cikin haske.

    Ya tsamo mu daga mulkin duhu, * ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ðansa,

    wanda ta gare shi ne muka sami fansa, * watau gafarar zunubammu.

        Shi ne surar Allah mara ganuwa, * Magaji ne tun ba a halicci kome ba,

            Don ta gare shi ne aka halicci dukan kome, * abubuwan da ke sama da abubuwan da ke ƙasa, * masu ganuwa da marasa ganuwa,

                ko manyan malaiku, ko masu mulki, * ko masarautu, ko masu iko,

            watau dukan abubuwa an halicce su ne ta kansa, * kuma shi ne makomatasu.

        Shi adimi ne gaba da kome, * kuma dukan abubuwa shi ke riƙe da su.

    Shi ne Kai ga jikin nan, watau ikiliziya, * shi ne Tushe,

    Na Farko cikin masu tashi daga matattu, * don ta kowane abu ya zama shi ne mafifici.

A gare shi dukan cikar Allah ta tabbata, * don Allah na farinciki da haka,

da nufin ta kansa * Allah ya sada dukan abubuwa da shi kansa,

na ƙasa ko na sama, * yana ƙulla aminci ta jininsa na gicciye.

Wahayin Yahaya 11:17-18; 12:10b-12a

Mun gode maka, ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki * wanda yake shi ne a yanzu, shi ne kuma a dā,

saboda ka ɗauki ikonka mai girma, * kana mulki.

    Alummai sun husata, * hushinka kuwa ya sauko, * lokaci ya yi da za a yi wa matattu sharia,

    a kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako, * da masu jin tsoron sunanka, * yaro da babba...

        Yanzu fa ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahmmu, * da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana.

        Don an jefa mai saran yanuwammu ƙasa, * shi da ke saransu dare da rana a gun Allahmmu.

    Sun kuwa yi nasara da shi * albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, * da kuma albarkacin maganad da suka shaida,

    don ba su yi tattalin ransu ba, * har abin ya kai su ga kisa.

Saboda haka sai ku yi farinciki, ya ku sammai, * da ku mazauna ciki!

Wahayin Yahaya 15:3-4

Ayyukanka manya-manya ne, kuma masu ban mamaki, * ya Ubangiji Allah Maɗaukaki!

Hanyoyinka na gaskiya ne, kuma daidai suke, * ya Sarkin alummai.

    Wanene ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, * ya kuma ɗaukaka sunanka? * domin kai kaɗai ne tsattsarka.

Dukan alummai za su zo * su yi maka sujada,

don hukuncinka na gaskiya * yā bayyana.

1 Bitrus 2:21-25

Almasihu ya sha wuya dominku, * ya bar muku misali * ku bi hanyarsa.

    Bai taɓa yin laifi ba faufau, * ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba.

    Da aka zage shi * bai rama ba,

    da ya sha wuya kuwa bai yi ƙwafa ba, * sai dai ya dogara ga wannan Mai shariar gaskiya.

    Shi da kansa ya ɗauke zunubammu * a jika a kan gungume,

    don mu fita shaanin zunubi ɗungum, * mu yi zaman aikin gaskiya.

    Da raunukansa ne * aka warkad da ku.

Dā kun sangarce kamar tumaki, * amma yanzu kun dawo ga Makiyayi, * kuma Mai kula da rayukanku.

Luka 1:47-55 Waƙar Maryamu

Zuciyata na ɗaukaka * shi Ubangiji

Allah Macecina * da shi ruhuna ke ta farinciki.

    Domin fa shi ya dubi * ƙasancinta ne baiwa tasa,

    ai ga shi jamaa ta dukan zamani * mubarika ce za su ce mani nan gaba.

        Domin Mai iko yai mani manya-manyan alamurra, * sunansa ko labudda tsattsarka yake.

            Daga zamani har dai zuwa wani zamani, * tausansa na ga waɗanda ke tsoronsa.

        Alamari babba da ƙarfinsa ya yi, * ya watsa duk mutakabbirai sun watse.

    Ya firfitad da sarakuna a sarauta, * ya ɗaukaka masu zaman ƙasƙanci.

    Mayunwata ya yalwata da abubuwan alheri, * ya sallame su da babu, masu wadata.

Ya taimaka wa baransa Israila, * domin yana tune dai da yin rahamarsa.

Ita ya yi alkawari ga kakannimmu, * tutur ga Ibrahim da duk zuriyarsa.

Luka 1:68-79 Waƙar Zakariya

Ubangiji Allah na Israila * a gare shi ne lalle yabo ke tabbata, * don ya kula, ya fanshi ma jamaa tasa.

Ya ta da Maceci mai iko domin mu, * daga zuriya ta baransa Dauda,

    yadda a tuntuni ya faɗa fa ta bakunan * su annabawa nasa tsarkakan nan:

    ya cece mu a gun su abokan gabammu, * har ma a hannun dukan maƙiyammu.

        Don nuna rahama ne ga kakannimmu, * ya tuna da alkawari nasa tsattsarkan nan.

        Shi ne rantsuwan nan wadda yai wa Ubammu Ibrahimu, * y cece mu gun su abokan gabammu,

        ya ba mu baiwa don mu dai bauta masa, * a gabansa ba a cikin halin tsoro ba ne,

        sai dai cikin tsarki da halin gaskiya, * dukan iyakar kwanakin nan namu.

    Kai kuma, yaro, za a kira ka annabi ne na Maɗaukaki, * za ka riga Ubangiji gaba, ka shisshirya hanyoyi nasa,

    ka sanad da su cetonsu su jamaa tasa, * watau na samun gafarar zunubai nasu.

Saboda tsananin rahamar Allahmmu, * daga can sama ne hasken alfijir zai keto mana,

har ya haskaka su na zaune can cikin duhu a bakin halaka, * har ma ya dai bishe mu hanyar lafiya.

Luka 2:29-32 Waƙar Simiyan

Yanzu kam ya Mamallaki, * sai ka sallami bawanka lafiya, * bisa faɗan nan da ka faɗa.

    Don na ga cetonka zahiri, * da ka shirya a gaban kabilun nan duka,

Haske mai yi wa sauran alummai buɗi * abin kuma ɗaukaka jamaarka Israila.