SUNAYEN YESU GUDA ƊARI DA ƊAYA

GABATARWA

Akwai hanyoyin fa'incin Yesu masu yawa. Ana koyon waɗansu abubuwa game da shi cikin Katakisma, da cikakken labarinsa cikin Sabuwar Yarjejeniya ta Littafi Mai Tsarki. Muna ma tunani a kan shi ta hanyar Rosari, muna ma saduwa da shi a Cimar Ubangiji. Yana kuwa aikata a cikinmu, har ma duk rayuwarmu muna ta ƙara ganewarshi kamar abokin da muka saba da shi.

Mutane masu yawa sun taɓa tuntuɓe inda suka bayyana shi wanene. Wasunsu sun girmama shi kamar Allah, har sun shakka ko shi mutumin gaske ne. Wasunsu kuma sun yarda shi mutumin gaske ne, amma ba su yarda ba shi Allah da gaske ne. Kakanimmu cikin Ikiliziya sun rubuta littattafai masu yawa don su nuna gaskiyar abu.

Littafin nan ba ta bi hanyar makaranta ba, amma yana da addu'o'in da ke rungumar koyaswar Littafi Mai Tsarki, a duk wuraren da aka ambaci sunan Yesu.

Sunā muhimmin abu ne, don ya kan nuna menene wani abu. Yesu yana da sunaye masu yawa, domin "shi ne taska maɓoyar dukkan mafifitan hikima da sani" (Kol 2:3). Maganar ɗan-adan kuwa ba ta iya nuna duka a kan Yesu ta wurin suna ɗaya ko waɗansu kaɗan.

"Amma ku, fa, wa ku ke cewa na ke?" (Mt 16:15). Wannan tambaya muhimmi ne ƙwarai. Amsarmu za ta sa mu mu riƙa shi kamar Macecimmu, ko mu bar shi kamar annabi kawai, ko me bi addini dabam wurinda ba shi da matsayi ko kaɗan.

Sunayen Yesu waɗanda aka ba shi cikin Sabuwar Yarjejeniya da annabtan Tsohuwar Yarjejeniya suna shaida wa bangaskiyar Kirista a kan Yesu shi wanene. Suna can don mu riƙe su, mu kuwa biya su a zuci (Duba Lk 2:19).

Kuma muna iya gayyatar abokanmu Musulmi don su yi kallonsu, domin sun saba yin tunani akan sunayen Allah guda tisa'in da tara, su ma kan yi yabon Muhammadu ta hanyar sunaye ɗari biyu da ɗaya. Mu Kirista ma, mu kan yin tunanin Allah ta wurin sunayensa da ayyukansa, musamman cikin littafin Zaburai.

Bari sunayen nan na Yesu su taimake ku ku ƙara ganewarsa da ƙaunarsa.

A.  SUNANSA NA FARI

1.   Yesu, ko Maceci

kuma Mataimaki daga wajen Allah:
Mala'ika Jibrilu ya raɗa maka suna
kafin ka zauna a ciki.
—Ka ceci mutanenka daga zunubansu, muna roƙonka.
(Amsa: "Ya Ubangiji, ka yi jinƙai.")
(Maceci: Lk 1:31; 2:11,30; Yh 4:42; Ay 5:31; 13:23; Fil 3:20; Af 5:23; 2 Tim 1:10; Tit L4; 2:13; 3:16; 2 Bit 1: 1, 11; 2:20; 31,18; 1 Yn 4:14. Ceto: Mt 1:21; Lk 2:30; 19: 10; Yn 3:17; 4:42; 10: 9; 12:47; Ay 4:11-12; 15: 11; 16:3 1; Rm 1:16; 5:9-10; 10: 9; 1 Kor 1:18,21; 1 Tm 1:15; 2 Tm 2:10; Ibr 2:10; 5:9; 7:25; 9:28)

B.  SUNAYE MASU DANGANTA SHI DA IYAYENSA DA MUTANEN DĀ

2.   Jikan Adamu

Ka ɗauki asalin ɗabi'arka ta mutun
daga mutun na fari,
wanda ya yi laifi,
ya jawo wa duk 'yan'adan mutuwa.
Kai ne:

3.   Adamun Ƙarshe,

wanda ka yi biyayya
har ga mutuwa,
aka ma tashe ka
don ka ba 'yan'adan rai.
—Ka maida mu sabbin mutane
masu rayuwa ta Ruhunka, muna roƙonka.
(Jikan Adamu: Lk 3:38. Adamun ƙarshe: 1 Kor 15:20-22,45-49; Rm 5:15-21; Fil 2:8)

4.    Jikan Hawa'u,

wanda aka alkawarta
magabcin Maciji mai ruɗi:
Ka tattaka, ka rugurguje kan mai mulkin duniyan nan.
—Ka tsare mu daga Mugun nan, muna roƙonka.
(Far 3:15; Yn 12:3 1; 14:30; 16:11; 17:15)

5.   Jikan Ibrahim da Isiyaku da Yakubu,

kuma magajinsu wanda aka alkawarta masu:
Ta wurinka an yi wa dukkan al'umman duniya albarka.
—Bari dukan mutane su shiga mulkinka,
su gaji duk abin da aka alkawrta wa Ibrahim, muna roƙonka.
(Far 12:3,7; 26:4; 28:14; Mt 1:1; Ay 3:25; Gal 3:7-9,16,29)

6.   Gamzakin nan mai haske:

Balama ya gan ka daga nesa,
kana tasowa daga zuriyar Yakubu-Isra'ila,
riƙe da kandarin mulki
don ka ci nasarar abokan gabar jama'arka.
Da tashinka daga mutuwa
haskenka ya ci nasarar zunubi da mutuwa.
—Ka haskaka a gabammu,
kada mu bi ruɗin Mugun nan, muna roƙonka.
(Ish 24:17; 2 Bit 1: 19; Wah Yn 2:28; 22:16)

7.   Zakin nan na Kabilar Yahuda:

Yakubu ya yi faɗin anabci
na zuwanka daga zuriyar ɗansa Yahuda
don ka amshi kadirin mulkinsa,
ka yi sarauta a kan al'ummai har bangon duniya.
Ka yi nasara bisa Sheɗan da duniya,
ka ma maida su jama'arka mai tsarki.
—Ka tsare mu daga yin ƙeta da zalunci, muna roƙonka.
(Far 49:9-10; Mt 1:2; Wah Yn 5:5)

8.   Jikan Dauda:

Kamar wani ice ka ke,
zuriyar Dauda tana rayuwa a cikinka,
gama kai ne rayayyiyar sauyar Dauda
da tohon Dauda.
A cikinka ne aka cika anabcin Natan,
cewa sarautar Dauda za ta ɗore har abada.

9.   Sauyar Yassa (mahaifin Dauda), da Toho daga kututtaren Yassa:

Lokacin da jikokin Dauda ɗan Yesse suka rasa sarauta sam,
domin yaƙe-yaƙe sun sare mulkinsu sai ka ce itace,
ka toho daga sararren kututtarensu,
domin ka yi sarauta da hikima da ganewa
da shawara da iko
da sani da tsoron Ubangiji.
—Ka sa gaskiya ta inganta a tsakanimmu, muna roƙonka.
(Jikan Dauda: 2 Sam 7:16; Mt 1: 1; 9:27; 12:23; 15:22; 20:30-31; 21:9,15; 22:42; Rm 1: 3; 2 Tm 2:8. Shoot for David: Jer 23:5; 33:15. Tohon Dauda: Wah Yn 5:5; 22:16. Sauyar Yessa: Ish 11: 10; Rm 15:12. Toho daga kututtaren Yassa: Ish 11: 1-5. Toho: Ish 4:2; Ez 17:22-24, Zak 3:8; 6:12)

10. Mariƙin nan na mabuɗin Dauda,

wanda in ka buɗe, ba mai rufewa,
in kuma ka rufe, ba mai buɗewa:
—Ka buɗe mana hanyar watsa labarinka na alheri,
ka kuma buɗe mana ƙofa mu shiga Urushalima ta samaniya, muna roƙonka.
(Ish 22:22; Wah Yn 3:7)

11. Ɗan Budurwa Maryamu,

wadda ta yi cikinka ba da namiji ba,
amma ta ikon Ruhu Mai Tsarki, Maɗaukakin Allah:
Ka ƙaunaci mahaifiyarka,
mai fifikon albarka ce a cikin mata,
wadda ta taya ka farinciki da baƙinciki.
—Ka sa ta ta zauna kusa da mu
kamar yadda ta yi da Yohana, muna roƙonka.
(Ish 7:14; Lk 1:26-38; Mk 6:3; Yn 19:26-27)

12. Ɗan rukon Isuhu,

wanda ya ceci ranka, kana jinjiri,

daga baya kuma ya koya maka fanninin sassaƙa:
Da ya ke babanka, sai aka tsammaci mahaifinka ne,
kuma da ya ke mijin mahaifiyarka,
ya ba da misalin kirki da gaskiya.
—Ka tsare masu gidajenmu, duk da iyalansu,
ka ma maida su kwatancin Isuhu da iyalinsa, muna roƙonka.
(Mt 1:16,18-25; 2:13-15,19-23; Lk 1:27; 3:23; 4:22; Yn 1:45; 6:42)

13. Yesu Banazare,

wanda aka haife ka a Baitalaham,
birnin Dauda,
amma aka yi renonka a Nazaret,
ƙauyen ƙasar Galili ta al'ummai:
Ko da Nazarawa suka ƙi ka,
an kira mabiyanka Nasara, watau Nazarawa.
—Bari kowa ya ga kirkin a cikimmu
wanda ka koyo a Nazarat, muna roƙonka.
(Mt 2:23; 4:15; 13:53-58; Yn 1:45-56; 7:41-42; Ay 22:8; 24:5. Galilean: Mt 26:69; Lk 23:6)

C. WAƊANSU SUNAYEN DA TSOHUWAR YARJEJENIYA TA YI ANABCINSU

14. Annabin nan

mai zuwa duniya:
Musa ya yi anabcin Allah zai tashe ka
daga cikin jama'ar Isra'ilawa,
don ka koya masu cikakken abin da Allah ya umurta.
—Ka yi magana da zukatanmu,
don mu gane labarinka na alheri, muna roƙonka.
(Kub Shar 18:15-19; Lk 4:24; Yn 6:14; 7:40; Ay 3:22; 7:37)

15. Imanu'ila,

ɗan Budurwa Maryamu:
Ta wurinka Allah na tare da mu.
—Ka sa mu mu riƙa zama tare da kai,
ka kiyaye mu daga dukan mugunta, muna roƙonka.
(Ish 7:14; 8:8, 10; Zab 46:7,11; Mt 1:23)

16. Mashawarcin nan mai al'ajabi,

wanda ka fi Sulemanu hikima:
—Ka shawarce mu a kan abin da ya fi kyau mu yi, muna roƙonka.
(Ish 9:5; Mt 12:42)

17. Allah Alƙadiri,

wanda ka fi Dauda girma,
gama kai ubangijinsa ne:
—Ka yi mulkinmu,
ka ma taka dukan maƙiyanmu,
kana sa su ƙalƙashin ikonka, muna roƙonka.
(Ish 9:5; Zab I 10; Mt 22:41-45; 1 Kor 15:24-28)

18. Uba Madauwami,

watau shugaban jama'arka har abada:
—Ka lura da mu kullun, muna roƙonka.
(Ish 9:5)

19. Sarkin Salama:

Salamar da ka ke kawowa
ba wanda ya ke iya ɗauke mana ita.
—Ka kafa mu cikin salama,
ka ma kauda ƙiyayya da yaƙi, muna roƙonka.
(Ish 9:5; 2:4; 11:6-9; Zak 9:9-10; Zab 72:7; Lk 1:79; 2:14; Yn 14:27; 16:33; Af 2:14-17)

20. Ubangiji Adalcimmu:

In kana lura da mu,
mun kuɓuta mun amintu ke nan
daga shugabanni masu ɓaudewa masu wulaƙanta mu.
—Ka kwance mana duk mugunta mai ɗaure mu,
ka ma dawo da duk ranmu da duk zuciyarmu gareka, muna roƙonka.
(Jer 23:1-8)

21. Amintaccen Makiyayin nan:

Ka ba da ranka
domin tumakinka su sami rai
su kuma same shi a yalwace.
—Ka kirawo tumakinka da suka ɓace;
bari dukanmu mu saurari muryarka,
mu be ka kamar garke guda, muna roƙonka.
(Mic 5:1-3; Ez 34:23-24; Zak 13:7; Yn 10: 1-18,26-28; Ibr 13:20; 1 Bit 5:4; Mt 26:31; 18:12-14 = Lk 15:3-7)

22. Almasihu:

An shafe ka domin ka zama
23. Sarkin Isra'ilawa

da
24. Sarkin Yahudawa,

kuma sarkin dukan al'ummai:
Mulkinka ba na wannan duniya ba ne,
amma mulkin Allah ne bisa zukatan mutane da hankulansu.
—Ka kau da wauta daga jama'armu,
ka ma yi mulkin duk abin da mu ke yi, muna roƙonka.
(2 Sam 7:12-16; Zab 2, 89, 110, 132; Dan 7:13-14. Messiah: Mk 8:29; 14:61-62; Yn 1:41, 4:25; Ay 2:36; 3:18; 4:27; 17:3. King of Israel: Mt 27:42; Mk 15:32; Yn 1:49; 12:13-15 = Zak 9:9; Yn 18:33-39; 19:3,12-15,19-21. King of the Jews: Mt 2:2; 27:11,29,37; Mk 15:2,9,12,18,26; Lk 23:2-3,37-38)

25. Baran nan na Allah,

wanda Allah ke farinciki da kai ƙwarai:
An hukunta ka tare da maƙetata,
ka ma sha wahala mai yawa don ka warkad da mu.
—Ta ɗaukakar tashinka ka ɗebe cuce-cucemmu,
ka ma kwance gigar na mugunta daga hankulanmu da jikunanmu, muna roƙonka.
(Ish 42:1-7; 49:1-7; 50:4-11; 52:13- 53:12; Zab 22; Mk 10:45; Mt 8:16-17; 12:15-21; Lk 9:22,44; 18:31-34; 22:37; 24:26,45-46; Ay 3:13,26; 4:27-30)

26. Sokakken nan:

Mashin soja ya buɗe kwiɓinka
domin daga zuciyarka kugunan ruwa da jini su gudano,
kuma kowa ya yi wanka, ya sha.
—Ka sa mu mu yi kukan zunubanmu
lokacin da mu ke kallon abin da suka yi maka;
ta haka ba za mu bukaci mu yi kuka ba
lokacin da za ka sake zuwa kamar alkalin duk 'yan'adan, muna roƙonka.
(Zak 11:10; 13:1-. Yn 19:34,37; 7:37-38; Mt 24:30; Wah Yn 1:7)

27. Mai shan wahala

wanda aka raina shi, aka ƙi shi,
ya daure da wahala da raɗaɗi,
tamu wahala ke nan, namu raɗaɗi ne.
Aka yi masa rauni saboda zunubammu
—Komad da mu, warkad da mu;
sai mu kwatanci daurewarka da shirunka.
(42:1-9, 49:1-7, 50:4-11; 52:13- 53:12)

28. Ɗam Mutun:

Kai ne mutun da gaske, ka zo a cikinmu
domin ka nemi abin a ya ɓace, ka cece shi kuma.
Ka sha wuya mai yawa, aka ƙi ka, aka ma kashe ka,
sannan ka tashi, ka zauna wurin Uban.
—Lokacin da za ka sake zuwa cikin gajimare,
sai ka same su shiryayyu domin mu karɓe ka, muna roƙonka.
(Mai zaune a cikinmu. Mk 2:10,28; 13:37; Lk 7:34; 9:56; ll:30; 12:10; 19:9; 22:48. Mai shan azaba: Mk 8:31; 9:31; 10:33; 9:9; 10:45; 14:21. Mai zuwa da ɗaukaka: Dn 7:13-14; Mk 8:38; 13:26; 14:62; Mt 10:23; 13:41; 19:28; 24:39; 25:31; Lk 12:40; 17:22-30; 18:8; 21:36; Am 7:56)

D. SUNAYEN DA KE NUNA ASALINSA NA ALLAH

29. Mai Tsarkin nan na Allah:

Lokacin da aka yi cikinka
tsarkin Allah ka zo ya zauna a cikinmu,
kana korar aljanu,
kana ma ba da maganar rai madauwami.
Saboda haka bai yiwu a riƙe ka cikin mulkin kurwoyi ba.
—Ka tsare mu daga kowace irin ruɓa, muna roƙonka.
(Lk 1:35; 4:34; Yn 6:69; Ay 2:27; 3:14; 4:27; Wah Yn 3:7)

30. Adalin nan:

Ko da ya ke ba ka yi wani laifi ba,
ka sha mutuwa dominmu miyagu,
yanzu dai kana tsaya mana a gun Uba.
—Bari adalcin Allah, wanda ɗaya ne da jinƙansa,
ya mai da mu masu adalci cikin kamanninka, muna roƙonka.
(Ish 53:11; Ay 3:14; 7:52; 22:14; 1 Yn 2: 1; 1 Bit 3:18)

31. Managarcin nan,

wanda a cikinka alherin Allah da ƙaunarsa suka bayyana:
kai ne makiyayimmu da malaminmu mafifici,
kai ma ka yi komai da kyau.
—Bari mu yi tarayyar nagartarka,
mu kuma zama cikakku kamar yadda Ubanmu na Sama ya ke cikakke, muna roƙonka.
(Mk 10:17-18 = Mt 19:16-17 = Lk 18:18-19; Mk 7:37; Yn 10:11; Ay 10:38; Af 3:7; Tit 3:4)

32. Mafiyin nan na Inusa,

wanda ya yi kwana uku dare da rana
a cikin wani babban kifi,
sai ya fita, ya yi wa'azi ga mutanen Ninaba:
Ka yi ran Jumu'a zuwa ran Lahadi
a cikin ƙasa,
sai ka tashi, ka cika ba da labarin alheri
na rai mara fid da zuciya.
—Ka ƙara mana bangaskiya,
gama kana da maganar rai madauwami, muna roƙonka.
(Mt 12:39-41. Jonah 2:1;3)

33. Mafiyin nan na Sulemanu,

wanda hikimarsa ta jawo masa yabo
daga bangon duniya.
—Ka ba mu basira mu ƙara saninka,
mu gwammace hikimarka da kowane irin ilimi, muna roƙonka.
(Mt 12:6)

34. Mafiyin nan na Haikali,

domin cikin jikinka
Ruhu Mai Tsarki ya zauna
tare da cikakkiyar ɗaukakar Allah:
—Ka sa mu mu girmama jikinka da jininka
cikin cimar da ka bar mana;
ta haka ne za mu ji daɗin ibadar da ka ke yi a cikinmu, muna roƙonka.
(Mt 12:6)

35. Ubangijin nan na Asabaci:

Ka soke guragun dokoki
waɗanda suka mai da mutun bawan ayyukan nafila,
ka ma yi aikin Uban a ran Asabaci
ta warkad da cuce-cucen mutane,
domin su iya bauta wa Allah
da 'yanci da farinzuciya da yin godiya.
—Ka gafarta mana zunubanmu,
ka ma cece mu daga dukan mugu,
domin mu iya yabon Allah kullum da salama da farinciki da murna, muna roƙonka.
(Mt 12:8 = Mk 2:28 = Lk 6:5; Mt 12:1-12; Yn 5:17)

36. Ni ne ɗin nan,

wanda ya ke madauwamin:
Ta wurinka aka yi dukan abu.
Tun kafin a haifi Ibrahim ka ke;
kai ne a yanzu, kai ne a dā, kai ne kuma nan gaba.
—Ka kai mu tare da kai
zuwa ɗaukakar Uban,
wurin da ka rigaya ka tafi, muna roƙonka.
(Yn 8:24,28,58; 13:19. Ex 3:14; Wah Yn 1:4 etc.)

37. Hikimar nan ta Allah,

wanda aka ɓoye cikin Allah kafin duniya ta wanzu:
Ka fito daga bakin Maɗaukaki
kamar yaro mai koyon ilimi daga wajen iyayensa.
Amma ka buɗe mana taskar ɓayayyar dukiya
ta mafifitan hikima da sani na Allah.
—Ka ba mu Ruhunka
don mu gane asiran hikimar Allah,
waɗanda hikimar duniya ba ta iya sani ba, muna roƙonka.
(1 Kor 1:24,30. Prov 8:22; Ish 7:25-26 Sir 24:3; Lk 2:40,52; 11:31; Mt 13:54; 1 Kor 2:7-8; 1 Af 3:10; Col 2:2-3; Rm 16:27)

38. Ikon nan na Allah:

Ka bayyana cikin raunin mutun,
watau mutuwarka a kan gicciye.
Ka ma kunyata ƙarfafan mutane
ta sa rarrunan mutane su rinjayi kowace mugunta.
—Ka ƙarfafa mu
don mu iya yin duk abin da ya kamace mu, muna roƙonka.
(1 Kor 1:24. 1 Kor 1:18; Rm 1:16; 2 Kor 4:7-11; 12:9-10; Fil 4:13)

39. Kalman nan ta Allah:

Kai ne bayanin ikon Allah da hikimarsa
waɗanda ya halicci duniya ta wurinsu.
Ko da duniya za ta sauya ta shuɗe,
kai, wanda ka zama mutun, ka zauna a cikimmu,
duk ɗaya ne a jiya, da yau, har abada ma.
—Bari mu karɓe ka kamar 'ya'yan Allah,
kuma mu ƙara shan falalar madauwamiyyar ƙaunarsa, muna roƙonka.
(Wah Yn 19:13. Ish 55:11; 40:8; Zab 33:6; Sir 42:15; Ish 18:14-16; Yn 1:1-4,10,14; 1 Yn 1:1; Mt 24:35; Ibr 13:8)

40. Ubangiji Maɗaukaki:

A cikinka ɗaukakar Allah ta ke,
wadda ido bai taɓa gani ba,
kunne bai taɓa ji ba,
zuciyar mutun kuma ba ta ko riya ba.
—Ka ba mu ƙauna ga Allah,
don mu cancanci ɗaukakar da ya shirya mana, muna roƙonka.
(1 Kor 2:8)

41. Hasken nan na ɗaukakar Allah,

kuma
42. Ainahin kammanin nan na Zatin Allah:

Haske daga Haske,
kana riƙe da dukkan abubuwa ta ikon faɗarka.
—Ka sa hikimar bishararka
ta haskaka zukatammu, muna roƙonka.
(Ibr 1:3. Duba ƙasa kuma, #43.)

43. Surar nan ta Allah mara ganuwa

Kuma madubi mara aibu na ikon Allah:
—Ka sauya mu mu ɗauki kamanninka,
don mu ƙara nuna kyan Allah kamar madubi, muna roƙonka.
(Col 1:15. Ex 24:16; Ish 7:25-26; Rm 8:29; 1 Kor 15:49; 2 Kor 3.18; 4:4,6; Col 3:10; Ibr 1:3)

44. Ɗan Allah Maɗaukaki,

kuma

45. Tilon nan na Allah ko Makaɗaicin Ɗa

da

46. Majidaɗin nan na Allah, ko Ƙaunataccen Ɗa ko Yarima,

haifaffe ne daga wurin Uban gaban dukan zamanai:
Lokacin da ka zama mutun ma, Maryamu ta haife ka.
Kai kaɗai ne daga cikin 'yan'adan
ke da ɗabi'ar mutun da ɗabi'ar Allah.
Ka zo ne don ka mai da mu 'ya'yan Allah,
waɗanda aka sake haifuwa ta wurin mutuwarka da tashinka.
—Ka haɗa mu da ƙaunarka
sai ka zo cikin mulkinka, muna roƙonka.
(Ɗan Allah Maɗaukaki: Mk 5:7; Lk 1:32; 8:28. Son of God: 2 Sam 7:14; Zab 2:7; 89:26; Mt 2:5; 3:17; 4:3,6; 8:29; 14:33; 16:16,28; 17;5; 21:37-39; 22:2,42-45; 26:63; 27:40,43,54; Mk 1:1; 3:11; 5:7; 9:7; 12:6,35; 14:61; Lk 1:35; 3:22; 9:35; 20:13; 22:70; Yn 1:18,34,49; 3:16-18,35-36; 5:19-27; 8:35-36; 10:36,40; 11:4,27;. 14: 11; 17: 1; 19:7; 20:31; Ay 8:37, 9:20; 13:33; Rm 1:3-4,9; 5:10; 8:3,29,32; 1 Kor 1-.9; 15:28; 2 Kor 1:19; Gal 1:16; 2:20; 4:4,6; Af 4:13, Col 1:13; 1 Tas 1:10; Ibr 1:2,5,8; 3:6; 4:14; 5:5,8; 6:6; 7:3,28; 10-29; 2 Bit 1:17; 1 Yn 1: 3,7; 2:22-24; 3:8,23; 4:9-10,14-15; 5:5,9-13,18,20; 2 Yn 3,9; Wah Yn 2:18. Makaɗaicin Ɗa: Yn 1: 14,18; 3:16,18; Ibr 11:17; 1 Yn 4:9. Ƙaunataccen Ɗa: Mt 3:17 = Mk 1: 11 = Lk 3:22; Mt 12:18; 17:5 = Mk 9:7 = Lk 9:35; 2 Bit 1:17; Lk 20:13; Yn 3:35; 10:17; 15:9; 17:24; Af 1:6; Col 1:13)

47. Allah da kansa:

Maryamu ta haife ka,
duk inda cikakkiyar ɗabi'ar Allah
ta ke tana zaune a jikinka.
Kai ne ainahin Allah da ainahin mutun,
Macecin da ya mutu ya kuma tashi.
—Ka ba mu cikakken rai ta haɗuwa da kai, muna roƙonka.
(Fil 2:6; Col 1:15; 2:9; Tit 2:13; Ibr 1:8; 1 Yn 5:20)

E. SUNAYENSA DA KE NUNA AIKINSA NA CETO

48. Hasken alfijir:

—Ka ɓullo mana,
daga can cikin sama ka haskaka
waɗanda ke zaune cikin duhu a bakin mutuwa,
ka ma bishe mu hanyar salama, muna roƙonka.
(Lk 1:78. Mal 3:20; Ish 41:2; 9:1; 42:7; Yn 8:12; 2 Bit 1:19)

49. Ɗan Ragon Allah:

Ka yarda a kashe ka
kamar haɗayarmu ta Idin Ƙetarewa,
domin ka ɗauke zunubin duniya.
Yanzu dai dukan amintattu
a duniya kuma a lahira
suna bauta maka.
—Ka tsare mu daga maƙiyanka,
ka ma sa mu mu bi ka duk inda ka je, muna roƙonka.
(Ish 52:7; 53:11-12; Yn 1:29,36; 10:17; Ay 8:32; 1 Kor 5:7; 1 Bit 1:19; Wah Yn 5:6,8,12-13; 6:1,16; 7:9-10,14,17; 12:11; 13:8,11; 14:1,4,10; 15:34; 17:14; 19:7,9; 21:9,14,22-23,27; 22:1,3)

50. Yesu Almasihu gicciyayye:

Albarkacin mutuwarka a kan gicciye ne
muka ya da sha'anin duniya,
duniya kuma ta ya da sha'animmu.
Cikin halin raunana iran wannan
kana mai da mu sabbin halittu,
cikakku da ikon Ruhun Allah.
—Ka sa kada mu yi taƙama
sai dai game da gicciyenka, muna roƙonka.
(1 Kor 21; Gal 3:1; 6:14)

51. Haɗayar kau da zunubai:

A gareka babu zunubi,
amma ka ɗauke zunubammu a jiki a kan gicciye,
ka ma miƙa haɗaya guda kammalalliya ta kanka
don ka fanso mu daga la'annar da ke bisa 'yan'adan.
—Ka haɗa mu da kai ta gangaskiya,
domin kada zunubi ya zauna a cikimmu, muna roƙonka.
(Ish 53:5-10; Rm 3:25; 8:3; 2 Kor 5:21; Gal 3:13 = Kub Shar 21:23; Af 51; Col 2:14; Ibr 9:23.18; 1 Yn 22; 3:5; 4:10; 1 Bit 2:24)

52. Adalcimmu:

Ta zub da jininka a kan gicciye
kuma ta tashinka daga matattu
ka kuɓutad da mu daga zunubi,
ka ma mai da mu abun karɓuwa ga Allah,
don mu zama adalai kamar yadda Allah ya ke adali.
—Ka albarkace mu da aikin adalci mai yawa
don ɗaukakar Allah da yabonsa, muna roƙonka.
(1Kor 1:30. Ay 13:39; Rm 1:17; 3:22-26; 4:25; 5:9,18; 10:4; 1 Kor 1:3; 6:11; 2 Kor 5:21; 2:16-17; Fil 1:11)

53. Tsarkakewarmu

Ta jininka da ruwan babtisma
ka tsarkake mu daga dukkan zunubi,
don ka mai da mu gaɓoɓin Ikiliziyarka mai ɗaukaka,
tsarkaka, marasa aibu,
ba tare da tabo ko tamoji ba,
ko wani irin abu haka.
—Ka riƙa keɓe mu a tsarkake,
don mu zama naka har abada, muna roƙonka.
(1 Kor 1:30. Yn 17:17-19; 1 Kor 1:2; 6:11; Af 1:4; 2:21; 5:26-27; Col 2:22; Tit 2:14; Ibr 1:3; 2:11; 9:13-14; 10:10.14,29; 13:12; 1 Yn 1:7)

54. Fansarmu

da

55. 'Yantarwarmu:

An daɗe ana sauraron zuwanka,
sai ka zo ka ba da ranka
don ka rushe aikin Iblis,
ka ma ɓalle wa mutane masu ɗimbin yawa
ƙangin zunubi da na al'adun banza da wofi.
—Ka kwance mana kowace igiya
mai hana mu yi maka hidima,
ka ma sa ƙaunarmu ta zama cikakkiya
lokacin da za ka sake zuwa
ka 'yantad da duk ɗabi'armu daga bautar ruɓewa, muna roƙonka.
(Fansa: 1 Kor 1:30. Ish 40:2; 52:9; Zab 19:15; 78:35; Mt 20:28; Lk 1:68; 2:38; 21:28; 24:20; Rm 3:24; 8:23; Af 1:7,14; 4:30; Col 1:14; Tit 2:14; 1 Bit 1:18; Ibr 9:12,15; 11:35. 'Yantarwa: Mt 17:26; Yn 8:36; Rm 6:18; 8:19-23; Gal 5:1,13)

56. Salamarmu ko Amincinmu

da

57. Sulhuntarwarmu:

Ta zub da jininka a kan gicciye
ka sulhunta 'yan'adan da Allah
da 'yan'adan da junansu.
—Ka sa salamar da ka bar mana
ta zama da mu kullun,
don mu yi aikin jakadunka,
waɗanda ta kanmu ka ke sada mutane da Allah, muna roƙonka.
(Salama: Af 2:14. Yn 14:27; 16:33; Ay 10:36; Rm 5:1; Col 1:20; 3:15; Wah Yn 1:4. Sulhuntarwa: Rm 5:11; 2 Kor 5:18-20; Af 2:16; Col 1:20-22)

58. Taƙaman nan tamu:

Duk abin da mu ke yi banza ne
in ba ka aikata a cikimmu ba.
A cikin wahala da gicciye,
kana ƙarfafa mu ga hidimarka,
kuma ta ayoyin al'ajabi da ikon Ruhu Mai Tsarki
kana kiran wasu mutane da dama su taya mu sanin Allah da ƙaunatarsa.
—Ka sa kada mu dogara ga kanmu,
amma mu ƙara amincewa da kai,
domin mu iya yin ayyuka masu yawa
mu yi taƙama da su
lokacin da za ka zo don yin shari'a, muna roƙonka.
(Rm 15:17; Fil 3:3. Rm 5:2-3,11; 1 Kor 1: 31 2 Kor 10: 17; 11: 30 12:9; Rm 4:2 Af 2:9; Gal 6:14; Fil 1:26; 2:16)

59. Shugaban nan namu:

Ka daure da gicciyen har mutuwa,
ba ka ma kula da wulaƙancin ba,
duk domin ka raya mu ga Allah.
Allah ma ya tashe ka,
ya zaunad da kai a hannun damansa,
don ka buɗe wa kowa hanyar tuba
don su bi ka.
—Ka ba mu daurewa cikin wahala,
domin mu dace da alkawaranka, muna roƙonka.
(Ay 3:15; 5:31; Ibr 2:10; 12:2)

60. Manzon nan

Allah ya aiko ka duniya
da shaidar mu'ujjizai,
don a zamanin nan na ƙarshe
a yi mana cikakkiyar maganarsa
ta ikon Ruhu Mai Tsarki
wanda ke tare da kai ba da iyakancewa ba,
gama kai Ɗan Allah ne
wanda ka zo domin ka ceci duniya.
—Ka sa mu mu saurare ka,
mu ma yi duk abin da ka ce mana, muna roƙonka.
(Ibr 3:1. Mt 21:37; Mk 9:37; 12:6; Lk 20:13; Yn 3:17,34; 4:34; 5:23-24,30,36-37; 6:29,3839,44,57; 7:16,18,28-29,33; 8:16,18,26,29,42; 9:4; 10:36; 11:42, 12:44-45,49; 13:20; 14:24,26; 15:21,26; 16:5; 17:3,8,18,21,23,25; 20:21; Ay 3:26; Rm 8:3; Gal 4:4; Ibr 1:2; 1 Yn 4:9,14)

61. Shugaban limanci,

wanda ke daidai da mu ta kowane hali
sai dai ba ka ɗau zunubi ba:
Allah ya zaɓe ka
don ka wakilce mu ga al'amarin Allah,
kana miƙa jikinka
haɗayar kau da zunubammu.
—Ka kiyaye mu daga zunubi,
ka ma ƙarfafa bangaskiyarmu, muna roƙonka.
(Ibr 2:17; 3:1; 4:14-15; 5:5,10; 6:20; 7:26; 8:1; 9:11, 10:10,21)

62. Matsakancin nan

Ka sadad da sabuwar yarjejeniya
tsakanin Allah da mutane,
don ka shafe zunuban da muka taɓa yi,
ka ma ba mu dauwamammen gadon
da Allah ya alkawarta mana.
—Ka ba mu tsarkakakkiyar zuciya ɗaya
da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya,
don mu bi ka banda ja da baya
zuwa Wuri Mafi Tsarki inda Allah ya ke, muna roƙonka.
(1 Tm 2:5; Ibr 8:6; 9:15; 12:24. 10:19-22; Gal 3:19-20)

63. Mai yi mana addu'a

kuma

64. Mataimaki:

Allah, wanda ya zaɓe mu,
ya ma aiko ka ka zama haɗayar kau da zunubai,
har yanzu yana sauraren addu'arka domimmu.
—Kada zunubi ya sake mallakarmu,
kuma a kowace irin wahala
sai ƙaunarka ta yi girma a cikimmu, muna roƙonka.
(Mai yi mana addu'a: Rm 8:34; Ibr 7:25; 9:24. Mataimaki: 1 Yn 2:1)

65. Macecin duniya:

Allah yana son dukkan mutane su sami ceto,
su kuma kai ga sanin gaskiya.
Saboda haka bai aiko ka duniya ka yanke mata hukunci ba,
sai dai don ka cece ta,
kuma ka tattaro 'ya'yan Allah da ke warwatse ko'ina
su zama jiki ɗaya.
—Ka ji tausayin milyoyin mutanen da ke cikin wahala,
a warwatse kamar tumaki ba makiyayi,
ka ma yi amfani da mu don taimakonsu, muna roƙonka.
(Yn 4:42; 1 Yn 4:14. Yn 1:9-10,29; 3:16-17; 6:33; 11:52; 12:47; Rm 5:12-19; 2 Kor 5:19; 1 2:4; Mt 9:36-38)

F. SUNAYEN DA KE NUNA KULAWARSA DA MU

66. Amintaccen Mashaidin nan na gaskiya:

Ka shigo duniya musamman don ka shaidi gaskiya;
sai koyad da tafarkin Allah sosai ka ke yi,
ba ka ma nuna zaɓe,
don ka ɗauki kowa da kowa daidai.
Ta kanka ne Allah ya ke cewa "I", ba "A'a" ba,
haka ya ke cika dukkan alkawaransa.
—Kada mu yi shakkar koyaswarka
ko ƙaunarka da nufinka da ke mallakarmu, muna roƙonka.
(Wah Yn l:5; 3:7,14; 19:11.Mt 22:16 = Mk 12:14; Yn 7:18; 8:14,45-46; 18:37; 2Kor 1:19-20)

67. Likitan nan

wanda ka zo don taimakon marasa lafiya:
Kana zagawa ko'ina da ƙaunarka da ikonka mai warƙaswa;
ta haka ne makafi ke samun gani,
guragu ke tafiya,
a ke tsarkake kutare,
kurame ke ji,
a ke ta da matattu.
Kuma mafi duka, shi ne kana kawo bishara
mai fid da kowane irin aljani.
—Kada mu yi shakka cikin bangaskiyarmu gareka,
don ikonka ya yi aiki a cikimmu, ba mai hanawa, muna roƙonka.
(Mt 9:12; Lk 4:23. Lk 7:21-23; Mk 5:25-34; 6:5; Ay 10:38)

68. Mai yin bishara,

kuma

69. Bisharan nan da a ke wa'azinta:

Ruhun Ubangiji ya aike ka
gun matalauta da ɗaurarru
da makafi da waɗanda ke danne.
Ka zaga ko'ina, kana aikin alheri,
kana warkad da kowa.
—Ka aiko da masu wa'azi su yi aikin nan'don kowa na duniya duka, muna roƙonka.
(Wa'azi: Mt 4:23; 9:35; Mk 1:14; Lk 4:18. Ish 41:1-2 etc. Wanda aka yi wa'azinsa: Ay 8:5; 9:20; 19:13; Rm 16:25-26; 1 Kor 1:23; 15:12; 2 Kor 1:19; 11:4; Gal 2:2; Fil 1:15; Col 1:23; 1 Tas 2:9; 1 Trn 1: It; 3:16)

70. Malamin nan:

Kai kaɗai ne malamimmu mai gaskiya
wanda ka zo daga wurin Allah.
Kana koyaswa da tabbas,
har kowa ya yi mamakin koyaswarka.
Amma kamar yadda ka wanke wa almajiranka ƙafa,
ka koya mana mu yi hakan ga juna.
Kuma kamar yadda aka la'anta ka da zargi,
ka koya mana kada mu guji hakan saboda aikin gaskiya.
—Ka sa mu mu tsaya a kan koyaswarka,
mu kuma aikata ta, muna roƙonka.
(Mt 7:24,28-29; 10:24-25; 22:16,23; 23:8; 26:25,49; Mk 1:22,27; 9:5; 11:18,21; 12:14; 14:45; Lk 4:32; 6:40; 12:12; 20:21; Yn 1:38; 3:2; 7:16; 8:28; 13:13; 15:20; 20:16; 2 Yn 9)

71. Mai sanyin hali mai tawali'u:

Muna zuwa gareka don ka hutashshe mu.
—Ka tuɓe mana kaya masu danne mu
waɗanda ba ka nufi mu ɗauka ba;
bari mu bauta maka
ta ɗaukar kayanka waɗanda ba su da nauyi,
domin mun ɗauke su bisa ga nufinka kaɗai,
kuma ƙarfinka yana cikimmu, muna roƙonka.
(Mt 11:29. Ay 15:10; Gal 5:1)

72. Hasken duniya:

Ka haskaka waɗanda ke zaune cikin duhu da innuwar mutwa
don ka maishe mu ga mulkinka na haske,
muna yin ayyukan haske
domin ta haskenka
mu kuma mu zama hasken duniya.
—Ka sa mu mu yi kyakkyawan amfani da haskenka tun muna da dama
kafin mu wuce dufun mutwa zuwa ga rai dauwamamme,
inda kai ne haskenmu na har abada, muna roƙonka.
(Yn 1:4-5,9; 8:12; 93; 12:46. Ish 9:1; 42:6; 58:10; Mt 4:16; 5:14; Lk 1:78-79; 2:32; 16:8; Yn 3:19-21; 11:9-10; 12:35-36; Rm 13:12; 2 Kor 4:6; Af 5:8-14; Col 1:12; 1 Tas 5:3; 1 Bit 2:9; 1 Yn 1: 5-7; 2:8-11; Wah Yn 21:23-24)

73. Ƙofan nan

Dole ne a shiga ta cikinka
ga duk mai son ya haɗu da tumakinka,
ya sami rai da makiyaya,
ko mai son yi kiwon garkenka
ya zama mai hidimarka.
—Ka sa mu mu yi ƙoƙarin shiga,
mu kuma bi da sauran mutane su ma su shiga,
kome ƙunƙuntar ƙofar da mu ke gani,
kafin a rufe ta har abada, muna roƙonka.
(Yn 10:7,9. Mt 7:14; Lk 11:52; 13:24-27; 1 Bit 5:2; Yn 10:1-2; 21:15-17)

74. Hanyan nan:

Duk wanda ya gan ka, ai ya ga Uban;
kuma duk wanda ya bi ka, ai ya kai wurin Uban.
—Ka sa mu mu bi ka ta hanyar mutwa,
don a buɗe mana labulen,
mu ga ɗaukakar Uban, muna roƙonka.
(Yn 14:6. Mk 15:38; Ibr 10:20)

75. Gaskiyan nan:

Ta wurinka mu ke sanin Uban,
kuma muna yi wa Uban ibada mai karɓuwa
ta ruhu da gaskiya.
—Bari gaskiyarka mai 'yanta mu
ta zauna a cikimmu,
ta kuma bi da mu cikin dukan ayyukammu, muna roƙonka.
(Yn 14:6. Yn 4:23; 8:32; Af 4:21; 2 Yn 2,4)

76. Ran nan

wanda mu ke gaskata wa,
mu ke bi kuma:
Muna da rai madauwami
ta sanin Uban, Allah Makaɗaici na gaskiya,
da kuma kai, Kalmar rai, wanda ya aiko.
—Bari jikinka da jininka, waɗanda mu ke karɓa,
su kiyaye mu zuwa ga rai na har abada, muna roƙonka.
(Yn 14:6. Yn 1:4; 3:15-16,36; 5:21,24-26,40; 6:27-58,63,68; 8:12; 10:10,28; 11:25; 12:50; 171-3; 20:3 1; Ay 3: 15; Rm 5: 17-18; 8:2; 2 Kor 4:10-12; Col 3:4; 1 Tm 1: 16; 2 Tm 1: 1; 1 Yn 1:1-2; 2:25; 4:9; 5:11-13,20; Yahuda 21; Wah Yn 2:7,10; 3:5; 7:17; 21:6,27)

77. Rayayyen nan:

Ko da ya ke an kashe ka saboda kana rarrauna,
duk da haka a raye ka ke har abada
ta ikon Allah, Ubanka.
—Ka sa kada mu yi raywa ta kammu,
amma kai, ka rayu a cikimmu,
don zumunci da kai ya zama manufar rayuwarmu, muna roƙonka.
(Wah Yn 1: 18; 2:8. Lk 24:5; Yn 6:51,57; 14:19; Ay 1: 3; Rm 14:9; 2 Kor 13:4; Gal 2:20; Phi 1:21; Ibr 7:25; 1 Bit 2:4)

78. Mai ta da matattun nan,

wanda ka wuce daga mutuwa zuwa rai:
Ka ba ruhummu sabon rai ta wurin babtisma,
ka ma alkawarta za ka kiyaye ran nan har abada
har cikin jikunammu
waɗanda za ka tasa a ranar ƙarshe.
—Ka sa mu rayu ta kanka da ikon tashinka,
mu kuma yi tarayya da kai cikin shan-wuyarka,
har mu zama kamarka wajen mutuwarka,
don ko ta ƙaƙa mu kai ga tashin nan daga matattu, muna roƙonka.
(Yn 11:25. Yn 5:21,28-29; 6:39-40,44,54; Rm 4:25; 6:4-11; 7:4; 8:11; 1 Kor 15:12-57; 2 Kor 4:14; Fil 3: 10-11; 1 Bit 1: 3; 3:21)

79. Burodin nan mai ba da rai

Kai ne hakikanin burodi daga sama
wanda rayayyen Uba ya aiko
don ka ba duniya rai madauwami.
—Ka sa mu mu cancanci cin jikinka da shan jininka,
don mu rayu ta kanka kullum,
muna zaune a cikinka, kai kuma a cikimmu, muna roƙonka.
(Yn 6:35,48. Yn 6:22-59; 1 Kor 11:23-31)

80. Itacen inabi na hakika,

wanda mu ke rassanka:
Kana ba mu rai da 'ya'ya
in mun zauna a cikinka,
kai kuma a cikimmu.
—Har abada kada a datse mu daga cikinka,
amma sai Uban ya tsarkake mu
daga duk abin da ke mara amfani ko mai sa mu laifi, muna roƙonka.
(Yn 15:1,5; Mt 5:29-30; Yn 15:1-17; Ibr 12:5-11)

81. Kan nan

na jikinka Ikiliziya
da na dukkan sarauta da iko
a duniyan nan da kum lahira:
Kai ne tushen rai da haɗa kai na Ikiliziyarka.
—Kamar yadda ka ba da kanka domin Ikiliziya,
mu ma mu ƙaunaci juna haka,
har mu sha kowace irin wuya
don mu cikasa abin da ya saura
ga wahalad da ka sha
don lafiya da cingaba na jikinka, muna roƙonka.
(Af 1:21-22; 4:15; 5:23; Col 1: 18; 2:10,19. Rm 12:4-8; 1 Kor 6:15; 10: 16-17; 11:3; 12:12-27; Af 5:25,30; Col 1:24)

82. Dutsen nan da magina suka ƙi:

Ka zama

83. Mafificin dutsen gini,

kuma

84. Harsashin gini

na Ɗaki mai tsarki wanda ya ke Ikiliziyarka:
Kana tokare masu ba da gaskiya,
amma kana sa masu ƙin ba da gaskiya su yi tuntuɓe,
sai ka afka masu ka niƙe su kamar gari.
—Ka sa a gina mu bisa kanka,
mu ma miƙa maka baikon ayyuka masu kirki
waɗanda ka ke yi ta Ruhunka a cikimmu, muna roƙonka.
(Zab 118:22; Ish 8:14-15; 28:16; Lk 20:17; Ay 4:11; Rm 9:33; Af 2:20-21; 1 Bit 14-8)

85. Sazuciyarmu

cewa za mu ga ɗaukakar Allah,
wadda ba mu gani,
amma an tanada mana ita a sama:
Ba za ka săce mana iska ba,
domin Allah ya rigaya ya ba mu Ruhu Mai Tsarki
ya ma kwarara ƙaunarsa a zukatammu.
—Ka ba mu jimirin shan-wuya,
domin mu ƙara sazuciya,
mu kuma sami karɓuwa wurin Allah, muna roƙonka.
(Col 1:27; 1 Tim 1:1. Rm 5:5; 8:24-25; Col 1:5)

86. Mai ƙaunarmu:

Ka ba da ranka domimmu
da ƙaunar da ba a iya aunawa,
ta ma fi gaban sani.
—Bari ƙaunarka ta mallake mu,
domin mu saka maka da ƙauna,
kuma kada wani abu ya raba mu da ƙaunarka, muna roƙonka.
(Ƙaunarshi garemu: Yn 131,34; 14:21,23; 15:9-13; Rm 8:35; 2 Kor 5:14; Af 3:19; 5:2,25.  Ƙaunarmu gareshi: Yn 8:42; 14:15,21-24,28; Af 6:24)

G. SUNAYENSA DA KE NUNA ƊAUKAKARSA

87. Mai nasara:

Ka rinjayi duniya
da mai mulkinta, Mugun nan,
da dukkan mabiyansa
waɗanda ke yaƙinka da mabiyanka.
—Ka ƙarfafa mu
waɗanda ka kira, ka zaɓa, ka amince wa,
don mu yi yaƙi tare da kai har mu ci nasara, muna roƙonka.
(Yn 14:30; 16:33; Wah Yn 5:5; 17:14. Our victory: 1 Yn throughout; Wah Yn 2-3; 12:11)

88. Ɗaggaggen nan

daga ƙasa
a kan gicciye,
sannan ga hannun dam a na Allah a sama:
Ka rigaya ka ja mu gare ka ta bangaskiya.
—Ka mai da mu naka kwatakwata,
ka ma wadata mu da baye-bayenka,
har ka ja mu gare ka cikin ɗaukaka wata rana, muna roƙonka.
(Mk 16:19; Lk 9:51; Ay 1:2,11,22; 1 Tm 3:16)

89. Angon nan

na mabiyanka,
Ikiliziyarka ke nan:
Muna farinciki ƙwarai da jin muryarka,
muna ma jin daɗi muddar kana tare da mu.
—Ka taimake mu lokacin da ka ɓoye mana,
kuma mu ke baƙinciki, muna hana kanmu abinci,
don mu zauna a faɗake da tsarkakakkiyar zuciya,
mu dinga ce maka "Zo", muna roƙonka.
(Mt 9:15 = Mk 2:19-20 = Lk 5:34-35; Mt 22:1 = Lk 14:15; Mt 253-12; Yn 3:29; 2 Kor 11:2; Af 5:23-32; Wah Yn 21:2,9; 22:17)

90. Ɗakin ibadan nan ko Haikali

da

91. Fitilan nan

na sabuwar Urushalima:
Ka fi tsohon haikalin nan na dā
wanda mutane suka gina,
duk da kyan gine-ginensa na dutse.
Jikinka sabon haikali ne
wanda aka rushe,
amma bayan kwana uku Allah ya sake gina shi,
ya sa ya haskaka da ɗaukakarsa.
Saboda haka birninka ba ya bukatar hasken rana ko wata ko lantarki.
—Ka sa Ikiliziyarka, wadda ta ke jikinka
da tsarkakken mazaunin nan na Allah,
ta zauna a tsarkake daga kowane irin ɓaci, muna roƙonka.
(Haikali: Wah Yn 21:22. Mt 12:6; 21:12-13; 24:1-2 = Mk 13:1-2 = Lk 21:5-6; Mt 26:61 = Mk 14:58; Mt 27:40 = Mk 15:29 = Yn 2:19-21; 1 Kor 3:16-17; 6:15,19; 2 Kor 6:16; Ep 2:21. Fitila: Wah Yn 21:23. Lk 11:33-36; Wah Yn 22:5)

92. Ɗan farin nan:

A gareka ne aka halicci dukkan komai,
kuma kai ne makomarsu.
Don haka sai ka zama na farko
na waɗanda aka sake haifuwa
ta wurin tashi daga matattu,
ka ma zama mafificin magajin dukkan komai.
—Ka sa mu 'yan'uwanka
mu ƙara ɗaukar kamannin kirkinka,
don mu yi tarayyar ɗaukakarka, muna roƙonka.
(Rm 8:29; Col 1:15,18; Wah Yn 1:5; Ibr 1:6. Zab 89:28; Ibr 1:2; 12:23)

93. Tumun fari cikin waɗanda suka yi barci:

An rufe ka cikin ƙasa kamar sauran matattu,
amma ka tsiro sai ka ce irin da aka shuka
tare da ɗaukaka da ƙarfi da dauwama.
—Bari mu bi ka a kan kari,
mu kuma sami rabon madauwamin mulkinka, muna roƙonka.
(1 Kor 15:20,23. 1 Kor 15:35-38; James 1:18; Wah Yn 14:4)

94. Mai yi wa rayayyu da matattu shari'a

Uban ya danƙa dukkan hukunci a hannunka,
ka ma san nufin zuciyar kowa
da ayyukan da su ke yi a asirce.
Yanzu kana ba masu jin maganarka rai madauwami.
Waɗannan ba za a yi masu hukunci ba
a ƙarshen zamanin nan,
lokacin da za ka kirawo dukkan matattu daga kaburbura,
ka wauware nagargaru da miyagu.
—A ran nan ka sa mu mu tashi, tashin rai,
ba na hukunci ba, muna roƙonka.
(Ay 10:42; 2 Tm 4: 1; 1 Bit 4:5. Mt 19:28; 25:31-46; Yn 5:21-29; Ay 17:3 1; Rm 2:16; 14:9; 4:5; Wah Yn 1: 18)

95. Alfa da Omega,

96. Na Farko da na Ƙarsen nan,

97. Azal da Matuƙa:

Kana nan tun fil'azal,
madauwamiyar Kalma ta Uba.
Bayan da ka zama mutun,
ka mutu, ka kuma tashi;
ga shi yanzu kana raye har abadan abada.
—Ka sa kada mu ji tsoron kome,
gama kana tare da mu kullun, muna roƙonka.
(Wah Yn 1:17; 2:8; 22:13. Ish 41:4; 44:6; 48:12; Col 1:17-18; 1 Yn 1:1; 13-14; Wah Yn 1:8; 21:6)

98. Sarkin sarakuna,

kuma

99. Ubangijin iyayengigi:

Kai ne

100.  Mai mulkin sarakunan duniya

Allah ya kallafa komai ƙarƙashin ikonka,
duniya da dukkan sarauta da mulki da iko.
Duk mai yin yaƙi da kai
zai faɗi a cikin nashi jinin,
amma duk mai bin ka
za a raya shi ta naka jinin.
(Wah Yn 17:14; 19:16; 1:5. Yn 18:36-37; 1 Kor 15:24-28; Ibr 2:8-9)

101.  Ubangiji

An ɗaukaka ka a hannun dama na Allah,

inda ya ba ka sunan nan
da ke birbishin kowane suna.
Kowa ya yi addu'a da sunanka,
in ya gaskanta kai, Yesu, Ubangiji ne,
zai sami ceto,
kai ma za ka zo gunsa da wuri.
—Amin. Ka zo, ya Ubangiji Yesu: Muna roƙonka.
(Ay 2:21 = Joel 3:5; Ay 2:33-36 = Zab 110; Ay 4:10-12; Rm 10:9; 1 Kor 2:8; 8:6; 12:3; 2 Kor 4: 5; Fil 2:9-11; Col 2:6; Wah Yn 22:20)

ƘARSHEN MAGANA

Ana iya ƙara sa wa Yesu sunaye masu yawa. Sai mu ari kalmomin da Yohana ya ce: "In da za a rubuta kowannensu ɗai-ɗai, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba" (Yh 21:25). "Amma an rubuta waɗannan ne, don ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta gaskatawa kuma ku sami rai madawwami albarkacin sunansa" (Yn 20:31).